Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haka lbr ke yawo cikin garh, wasu su yarda wasu suce basu amince ba. Mutan gda kuwa tun daga santa aka fita da kayan da kujeru sukejin dadi suna tsegumi. Satinshi daya ya wartsake,masllaci kawai yake zuwa. Ya na kwance kan katifa, ita kuma ta sauke akwati ta zazzage zata ninke kayan data dibo daga shanya, yana rike da khalil ya dubeta cikin yanayin damuwa a fuskar sa. Banso kika saida kayanki ba, ikilima ta juyo a hankali ta kalleshi cike da mamakin abinda ya fada ta girgiza kai. Na fada maka ka daina cewa haka,bani na jawo ba ? Bakiga babana ya shareni ba? Ta karkade rigarshi tana cewa wai wace mata ce? Nifa banyarda da duk abunda akace ba, yace wata ce. Suka danyi shiru ya ce wlh bani da kalmar da zan gode abinda kikamin, nagodai ma Allah daya bani ke matsayin mata, hakika ke yar aljanna ce, dadi ya rufeta. Daidai lokacin da ta daga wani zani ta kakkabe letter ta fado ta dauk tana juyawa tare da cewa baban khalil na maka laifi innalillahi, duba lettar nan tun kusan fin sati aka kawo. Ya amsa tare da cewa letter kuma? Ni kam wanene ya kawo min? Tace wasu mutane ne. Ya bude itama kuma ta tsura ma fuskar shi ido ya duba lettar din a nutse. Ya dubeta Allah bashida abokin tarayya, shine maiyin yadda yaso, alokacin dayaso tace menene? Ya mika mata letter din da bankin GT sukayi dani tun shekara 4 shine suka turo min cewa sun daukeni aiki, amma sai na sake zuwa sun min iterview ranar sha hudu, yau wace rana ne? Tace gbe kenan yau sha uku Allah mun godai maka, Allah kasa muna da rbo yace amin. Washe gari yayi fes dashi cikin kana nan kaya, ta rakoshi har bakin zaure tana cewa Allah yasa mudace, yadubeta da murmushi yace amin. Aysha ta leka ta yafito maman ummi ta nuna mata so suka tallafe baki suna dariya, tare da cewa wannan batasan waye namiji ba. Tajuyo tagansu suna dariya dama tuni tagama gano ko su suwaye, dan haka sai tawuce dakinta. Suka kuma ciga da hasashe ko garin zaya bari tunda anyi abin kunya. Aysha tace ni itacema take ban mamaki, kan mamiji ta saida komanta, kinsan Allah sai na mata magana, maman ummi tace ki kama bakinki, amma! Aysha tace ina zuwa. Tana karyawa ta sameta itama ta zauna tace kina kari ne tace eh bismillah aysha ta tabe baki na koshi bana cin kwanannan abinci. Ta dubeta dama gurinki nazo, yanzun ke baki da mai miki fada ne cikin danginku? Kin sai da ko mai kan namiji kina wahala kina ci daku randa fa yayi kudi bazai saurara miki ba wata zai hararo. Cikin mamaki ikilima ta kalleta ta mike tare da cewa Allah ya baki hakuri in ranki baiso ba. Amma kiyi tunani namiji dai rigar kaya ne ko kinki sai kin cire. Ta fita ta bar ikilima baki bude. Ita dai bata son sa ido in ta kara zuwa zatace mata batason haka. Nafisa kuwa koda ta ko ma gida kuka ruru tayi, yanxun batasan kuma yaya zatayi ba tasan ko kallonta ma bazaya sake yi ba ko a hanya. Shedaniyar zuciyarta ta ce mata duk sanda kika tunashi kisha mayenki zaki ganshi kuna holewa. Tundaga sannan ta kara tsananta shaye shaye, inko tasha sai ta rinka ganinshi. Mijin hajara jikinshi ya shiga mataki na biyu na masu ciwon kanjamau, rama da kuraje sun baiyana dan haka wasu suke gudunshi, lokacin da hajara ta gane mijinta na da ciwon, sai hankalinta ya tashe domin sau da dama in ya kawo wani ya wtse da shi to shi wanin zai aikata sabon zina da ita. Tayi asibiti dan a gwada jininta, cikin lokaci kankani itama aka gano tana dashi. Tun daga lokacin take kuka tare da kira shiga uku, ta danna waya takira nafisa. Nafisa ta sameta shabe shabe ta ce lfy aunty? Hajara cikin kuka ta ce ina da cutar kanjamau HIV dama dagaske akwai ciwon nan? Kai ban yarda ba, ba kina amfani da kororo ba? Hajara tace kororo zai hana kamu da ciwon ne kema kije a gwadaki. Nafisa tayi yar dariya tare da cewa ni ras nake tace kada kice haka, domin kinsan munsha bin namiji daya ni dake ba'a gane ciwon a ido. Nafisa tayi shiru tana saurarenta zuciyarta tace kada kije watakila ita ba kowanne lokaci take amfani da kororon roba ba,Ke kuwa da ita kike amfani, dan haka sai tayi gidanta, amman abin na damunta washegari tayi asibiti jikinta sai bari yake tun lokacin da zaa dibi jinin nata. Ya tabbata nafisa ta kamu da qanjamau itama. Hankalinta ya tashi ta samu alhaji jamilu da kuka wiwi, shi dariya ma ta bashi sannan yace to dan kina da HIV menene? Kusan dukkan mu masu harkar luwadi muna dashi, ni ai ya shekara bakwai a jikina. Amman kinga alama? Ai in dai zaka qetare iyakar ubangiji ya maka dole ne ka samu ciwon nanan sai ki soma shan magani duk wannan baisa nafisa tayi shiru ba ta nufo minna hankali tashe amman ta kasa sanar da haule kwananta 2 ta juya. Tana dira gida hajara na shigowa, cikin kuka tace ma hajara na cuci kaina na zalunci kaina, na debo ma kaina ciwo mara magani, hajara tace inji wa? Ai na soma shan magani kema ki dinga zuwa kina amsa kina sha harka kuwa ba dainata zamuy ba, gara ma ni dake ko haihuwar fari baki ba kina ganiyar quruciyarki Nafisa ta sake sa kuka, kai ita ko data samu kudin tayi kudin bata huce takaici ba kenan kudin basuyi mata rana ba nan hajara ta shiga lallashinta da bata magana, da kuma nuna mata cewa yanda aka sadado aka sa musu suma suyi ta bazawa ga duk wanda kwadayi ya kawoshi. Shaidaniyar zuciyerta ta amince da haka, dan haka ta bi layin masu shan magani jama'a sai kuyi hattara ga irin su nafisa sunfi dubu. Ikilima tana bakin fanfo tana wanke kayanshi,yayi sallama. Ta dago suka kalli juna, sannan ta amsa sallamar. Murmushin da ya sake ne ya tabbatar mata cewa anci nasara ta nufi gurin sa tana cewa, sannu da zuwa. Ya dafa kafadarta, kasa kasa yayi da murya ya ce mata munci nasara, suka nufi daki maman ummi ta bisu da ido. Taja tsaki tare da cewa, acben tausayi. Ta shimfida masa tabarma ta bashi ruwa sannan ta shigo mai da abinci sai da ya ci ya koshi sannan ya ce da ita. Zasuyi mana training na sati 2 sannan ga takardar ka'idodinsu. Sun ce zasuyi aiki damu na wata 9 kafin su tabbatar damu, mu zama cikakkun ma'aikata, in mun kiyaye ba'a kamamu da laifi. MABUDIN WAHALA 3**2 Tace to har wata 9 baza a baku albashi ba? Ya ce zasu bamu amma in mun zama cikakkun ma'akata zasu biya mu kudin da muka kashe gurin siyan kaya kinsa fa sai mun sai kaya. Basason kaloli daga ash, sai yellow sai baki sa blue da sky sai ko fari. Sun fison komai set har takalmi in kuma kayan yarenka zaka sa shima ya zama set. Tayi yar dariya tare da cewa gaka dama maison ado shikenan sai kwalliya. To yanzun ina za a samu kudin siyan kyan? Ya ce nima tunani na kenan amma babu damuwa zamuga yanda za'ayi. Tace ko na baka ragowar kudin hanuna yace bari tukunna yafita. Ta debo ragowar zannuwarta na sunan khalil tayi gdan dilaliya dasu yana dawowa tace kayi hakuri na fita banfada ma kayi hakuri ta bashi dubu 8 duk da kudin hannaunta tace ga ragowar dubu 1 nan kaje ka siya da wannan yace rantowa kikayi? Tace zannuwana na siyar. Ya zuba mata ido baisan kalman da zaya godai mata ba, bayaso ya ce mata kudin baza su isa ba dan kada ta ce zata kuma aro masa, amma zaiyi maleji. Yace ikilima samun ki a matsayin mata ba karamar rahma ba ne, kina da iman, da tausayi. Tace haba baban khalil, daina wannan zancen, shi dama zaman aure zaman ibada ne na taimakon juna. Yace tunda mukayi aure kece kike taimaka min bansan sanda zan taimaka mikiba. Tace lokaci yana zuwa ta mike tare da cewa lokacin sallah yayi. Daga sallar isha'i gda ya wuce gurin su alhajin shi, har yanxu alhaji bai sake da shi sosai ba, hajiya uwa tana bude mishi abinci suna gaisawa, sannan ya gaida alhaji ya amsa sai dai ba kama yanda suka sa ba ba. Ya ce alh dama gurinka nazo yaci gaba dama aiki na samu a bankin gt. Ranar monday za'a soma yi mana training. Alhaji ya dubeshi cikin fara'a tare da cewa Allah ya sa albarka a ciki sannan mu2m yaji tsoron Allah ya tsare gaskiya da amana. Dubi abunda ya faru dakai kwanannan, akwai kaskancin da ya wuce kana zaune kaida iyalinka jami'an tsaro suzo su kamaka tare da tara maka jama'a? To dan haka ka guji son zuciya, dan malamai suna gaya mana ko yaushe. Dan haka ka rike gaskiya da amana,yace nagodai. Su hajiya uwa sunyi mishi murna sannan yaje gdansu ikilima gurin babansu ya sheda masa, tare da cewa yana son a yi masa addu'a shima dai yayi masa nasiha. Aiki gadan gadan mahmud ya kama abinka da saban ba, sai da yayi murar Ac saboda kullum cikin raba suke fatar shi kuwa ta goge in ya dauki wanka tamkar wani minsta. Matan gdan kuwa sun rasa gane ina yake zuwa haka' daga karshe aysha ce ta tambayi iklima. Wai ina mijinki yake zuwa ne' ko neman aiki? Tambayar tabama ikilima mamaki sannan ta murmusa ta ce aiki ne yazo har gda ya sameshi, don haka wani banki ya ke zuwa aiki tace al Allah ya sanya alkairi. Ta tafi ta tsegumtama maman ummi. Nan kuma suka shiga nuna bakin cikin su tace shiyasa yake iyayi, kiga ya dau gayu sai kace dan wani da wata. Aysha tace cen zaiga wata a bank. Maman ummi tace ni in da za'ayi haka ma da raina kar, ba ita bace sarkin bautar miji!. Mata kenan ya kamata maman ummi su soma ikilima abunda kuke sowa kanku. Tunda nafisa ta gamu da ciwon zamani duk dare sai tayi kuka, tasan lallai batun hausawa haka ne kwadayi mabudin wahala ne kuda kuwa gurin kwadayi yake mutuwa. Tazo mina gdansu safina taje ranar ta firgita ganin yanda safina ta dawo cikin kwanaki kadan da bata ganta ba, ta bushe ta tsotse ta rame kuraji caba caba babu kyan gani. Kuka ru rus suka shiga yi safina tace nafisa kinga yadda na koma? To har gara ni da mama zee, kwadayi ya kai mu ga halaka ni bansan na samu kanjamau ba sai da naje matakin karshe. Gashi mijina ya kwashe kayansa ya barmin gdan wai in na mu2 yazo ya saida gdan, ashe yasan yana da ciwon ya aure ni iyayena sun gujeni dan ban musu biyayya ba, uwata ce kuma take dan sato jiki duba ni dan babana ya ya hana kowa zuwa inda nake, don haka nafisa ki tuba tun kafin ciwon mazinata da yan ludu ya sameki. Nafisa ta sake rushewa da kuka ta ce na nawa kuma? Nima ina dauke da ciwon safina tace to kiyi maza ki sasanta da yan uwanki kafi kizo irin wannan matakinh bana iya tashi nan nake kashi da fitsari sai wanda Allah ya jeho sannan ya taimakamin amma kije ki ga zee mama, kudi ta baiwa safina ta fita tana kuka. Laillai gara safina da mama zee, ita tsutsa gabanta ke fitarwa, ko an kwashe sai su dawo su kuma cinkusowa, itama kuka take tace nafisa kina da damar tuba,tun baki gamu da masifun da muka samu kanmu ba. Ta janye zanin da aka rufa mata ga doyin da dakin keyi ta ce irin tsu tso tsin mai gda na keyi lokaci zuwa lokaci yana yinsu duk da wai an masa aiki a kasar waje. Mama zee ta ce, ciwon nan saka makon madigon da na dingayi ne nabi hajiyoyi da kawayen banza muna bin junanmu mata. Yau ga saka makon abin da nayi. Nafisa har dashewa muryarta tayi, tace nima ina da kanjamau mun shiga uku, sauran kawayenmu da basu bi hanyar da muka bi da muna ganinsu basu waye ba, ga abin sona mahmud tamkar ya kashe kansa don sona, amma naki shi na tozarta shi. Sannan kawayena na abuja sun sani na rarraba ma maza da yawa. Mama zee tace ki tuba ki nema gafarar mahaifinki, ki dinga shan magani kin istigfari ga Ubangijin ki, kinga mu mun makara sai abnda Allah yayi. Nafisa da kuka ta dawo gidan su haule, tace haule dama su safina da mama zee haka suka dawo? Tace wallahi dama ana rade-radin suna bin maza sai ko gasu sun hadu da munanan ciwo, ni ai tun da naje sau daya ban koma ba. Wannan mugun ciwo haka? Ai ko dana ne bazan iya yin wannan jinyar ba, mutum yaje ya dauka. Gaban nafisa ya fadi, dan haka sai ta fasa gaya mata. Washe gari ta shirya ta koma abuja. Wani tashin hankali ta samu sabo, Alhaji jamilu babban kamfaninsa yayi gobara, dama duk kwanakin cikin ciwo yake banda tsutsotsin. Likitoci sunce yana da suga da hawan jini da ciwon zuciya. Likitoci da malamai suna cin kudi son ransu, cikin haka ne zaben su yazo aka yi, yaci ya kuma hau sai dai ba lafiya, duk da ba wai da ka ganshi bane zaka gane hakan, duk da sabuwar daular dasu nafisa suka samu bai sa ta cikin nutsuwa ba. Shima ko yaushe jikinshi na kara gaba, kullum yana hanyar kasashen turai wajen neman lafiya. Wata safiya suka wayi gari alhaji kabiru ya mutu, lokacin da nafisa suka iso gidan abokansu duk sunzo da danginshi suna ta kuka, har lokacin babu wanda ya iya matsawa kusa da gawar bare yayi mata wanka. Hasalima tsoron gawar sukeji. Nafisa ta dubi hajara, anty har an hada shi ne? Tace a'a tun cikin dare ya mutu amma bai samu mai masa wanka ba. Nafisa tace to a nemo limamai mana. Hajara tace limaman unguwar nan anje amma yace su samu 'yan uwan sana'ar su wato 'yan ludu kenan masa. Ashe kallon mu kawai akeyi duk mutane sun san komai. Nafisa tace mun bani, to yanzun haka za akai shi? Hajara tace yayin shi sunje dinko likafani zasu mishi, dan basu san me yake aikatawa ba. Nafisa lamarin ya kara tsorata ta, yanzu dai su ya zama musu dole kenan su mishi wankan? Hajara tace eh dan ma yana dubo su bai zubar dasu ba, in ba haka ba da yanzu ya zanyi da yaran nan? Tagumi nafisa tayi, ita batasan dangin alhaji jamilu ba. Koda yake ina ruwanta da sanin danginshi tunda ba auran sunna sukayi ba, aure ne na jeka nayi ka. Sai dai in yayi mata irin mutuwar nan ya zatayi dashi? Kai duk wanda yace kwadayi dole yayi da nasani. Haka nan abokananshi wasu sun girgiza lokacin da sukaje rufe shi, kabarin uwa da 'yar sai ta matse, in sun buda sai ta matse. Karshe da 'yan uwan suka saka shi suka turbude daga shi sai halinshi. Tir da wannan irin makoma, Allah Ya tsare mana imaninmu , kasa mu cikin salihan bayinka, ka tsaida mu kan halas dinmu. Amin. Wasu cikin abokanan sun girgiza wasu kuwa sunce ko a jikinsu. Alhaji jamilu ma duk jikinsa yayi sanyi, sai dai bayan kwana biyu yaci gaba da harkokin shi. Ranar da mahmud ya soma amsar albashi, gaban ikilima ya zube su. Me kika ga ya dace muyi? Tace ka cirar ma baba da mama ko ba yawa, ina nufin alhaji. Sai ka sai mana kayan abinci. Yace sai dai alhaji da baba na gidanku. Tunda mama bata kusa wani watan a cirar mata. Ina bukatar waya (GSM) ko me sauki ce. Yayi kasa da murya dai dai kunnenta, sannan dole yau muci kaza. Sukayi dariya tace hakan ma yayi. Ya ciri dubu daya, ke ma rike wannan. Tace a'a nima gobe nike sa rai za a biya mu a makaranta, duk ga lissafin da kayi kudin kuma ba yawa na yafe, wani watan mu a bamu. Yace shikenan Allah ya kaimu. Ya fita zuwa gidansu, inda ya kaima alhajin abin da ya sawaka, yasa albarka tare da sake yi masa nasiha. Ya mallaki wayar sadarwa mai saukin kudi, sannan ya sai musu kayan abinci. Haka nan ya ziyarci gidan gasa kaji da tsaftatacciyar madara ya siyo musu lokacin da ya shigo tuni ta gama komai tayi shafa'I tayi wutiri, duk da babu kaya a dakin ya sharu tsaf yana kamshin turare. Tana sanye da riga da zani na atamfa ya zauna gefen katifa, me kike shirya min ne? Ta gane nufinshi tace komai ma yayana. Ya aje ledar ya sake dubanta, na kwana biyu ban kawo sako ba, saboda gajiya. Amma yau sun isheni. Ta tashi tana dariya baban khalil kenan, bari na kawo plate. Sunci sun sha sunyi dam sannan suka shiga bautar Allah. Sauran kwanakin da suka biyo baya duk cikin jin dadi da walwala suke, haka nan koda wata yayi nisa basu tagayyara ba, don ikilima ta iya tattali da lura akan duk lamuransu. Yanzu kam basu da matsalar abinci, haka nan shi mahmud duk kayan suna a don banki yana dasu, kusan duk budurwar da taga mahmud sai ta sake kallonshi. Shiyasa duk lokacin da zai fita ikilima zata rako shi har zaurensu (soro) tana bashi amanar kanta. Baban kalil dan Allah banda kallon mata, sai yayi murumushi sannan yace ikilima kenan, ki kwantar da hankalinki, ko na kalla da na tuna dake sai na gansu tamkar maza 'yan uwana, ina nufin sun daina birgeni. Takan yi murmushi ta bashi jakar tace Allah ya tsare.s BOOK MABUDIN WAHALA 3**3 Matan gdan sukanyi habaici suce ba girin girin ba tayi mai sabon kicifi ne raka miji har zaure? Su kwashe da dariya. Ba ikilima ba hatta mahmud yagama gane kalan matan gdan nasu, saidai yadda ikilima bata taba yimar maganarsu ba haka shima din baitaba dauko zancensu ba lamarin gbanta kawai takeyi sannan bata taba rikesu ba koyimusu mugunta. Matan gida sukanyi habaici da cewa ba giringirin ba tayi mai, sabon kicifi ne raka miji har zaure? Su kwashe da dariya. Ba ikilima ba har mahmud ya gama gane kalar matan gidan nasu. Sai dai yanda ikilima bata taba yi masa zancensu ba shima din bai taba dauko mata hirarsu ba. Lamarin gabanta kurum takeyi. Sannan bata taba rike su cikin ranta ba, ko yi musu mugunta. Har izuwa yau da mahmud ya zoma ikilima da labarin sun gama watannin su, yanzun za'a tabbatar da sune a matsayin cikakkun ma aikata, yace in sun tashi aiki suna da meeting, tace to Allah ya taimaka. Lallai lokaci ba wuya, khalil yana gudun sa ko ina, ita kanta tayi nisa da karatunta na sanawiya, domin tunda mahmud ya samu aiki yana musu bukata ta koma sanawiya da hadda in ta dauki albashi sai ya cika mata. Bayan ya dawo office da murna ya shigo, rungumarta yayi a tsakar gida lokacin ta zubar da shara tana dawowa daki, ya shigo itama ta kankame shi tasan sunyi nasara. Dan dama yana ta cewa kanwata ki tayani da addua, kuma duk sallah in takai sujjada ga Ubangiji sai ta sako bukatar mijin ta. Daki suka shiga suna dariya , suka zube kan katifa. Yayi rigingine ya daurata kan cikinshi, khalil ya rugo shima ya fada mishi kan kirji, tace yayana murnar me kakeyi haka? Yace mun zama cikakkun ma'aikata, an bamu kudin da muka kashe gurin sa kaya dana gida, da na abn hawa. Kuma duk karshen shekara za a dinga yi mana irin wannan biyan. Ta rungume shi tana murna, yace kudin nan sunzo daidai azumi ya kusa, tashi ma dai tun yanzun ki bani biro da takarda mu lissafa duk abubuwan da muke bukata. Ta mika mishi takardar yace sai da ina zaton ina cikin wadanda zuwa bayan sallah za'a turamu wani branch din zuwa wani state. Ta zaro ido, mu fa? Yace kuna nan mana, bari dai mugani. Ta zauna cikin jimami, bansan ko zan saba da rashin ka ba. Yace a'a kada kisa wannan tunanin cikin zuciyarki, ba dole bane ma a tura dani ba, yanzun zauna mu rurrubuta abubuwan da muke bukata. Tace abinci, yace dama wannan dole ne, ni bari kiji lissafina. Farko zamuyi fenti mu sai kujeru da gado, mu sai kayan azumi da na sallah, har ma mu sai ma mahaifan mu. Ta zaro ido, kudin da yawa ne? Yace sai dai in sun tura min cikin account zan gani. Tace toh Allah ya shige mana gaba. Yace amin. Musa kaninshi ya dora kan aikin fentin tunda shi yana yi, aikin shine ba zai barshi ba. Ikilima tace ta zabi ranar alhamis ta zama ranar da za ayi fentin saboda bata da makaranta. Su maman ummi sun ga tana fitar da kaya ita da nazira kanwar mahmud, sai suka koma gefe suna dariya, wai tana kwalimar daki kamar zaure. Maman ummi tace, in ni ce ita Allah ba zan fito da kayana tsakar gida ba, babu abn kirki cikin dakin sai katifa. Da musa suka zo da masu fenti suka fahimci fentin akeyi, sai suka ce alhaji ne kilan yasa a yi musu abn arziki, dubi yana aiki amma jiya iyau. Aisha tace sai dai kanshi yake kashema ba kya gani ya shiga wannan ya fita wannan, da ganin jikinshi ma kin san dadin shi yake ci can waje. Maman ummi ta sheke da dariya tare da cewa ya iya tsiya, ba ita ta maida kanta sokuwa shashasha ba? Haka suka cigaba da zantukansu na hassada. Tun daga toilet dinta har kitchen an gama sannan aka fente tsakar gida da kofar gida. Ladi makociyarsu ta shigo lokacin ikilima tana wanke wanken tarkacenta na kitchen su da nazira, suka gaisa da ladi ta dubi aisha tace. Aisha ana muku fenti ne haka? Tace um, maigidan ne ya saka. Tace aiko gidan yayi kyau, mijin maman khalil? Aisha tace a'a sirikinta ne nake ga. Duk ikilima tana jinsu amma bata tanka ba. Kayan sawan su kawai tamaida dakin amma sauran tarkacen ta zuba su cikin kitchen. Washegari da safe yana shirin fita office ita kuma tana fifita mishi shayi, saboda ya dan sha kafin ya tafi. Kullum haka sukeyi saboda yanayin aikin shi, ta mika mishi daidai lokacin daya gama daura neck tie, ya kurba ta dubeshi ya zauna gefen katifa. Shikenan na zauna. Tayi murmushi "Manzon Allah ne ya hana sha daga tsaye, kuma bai bambanta mana ba. Ina nufin bai ce ruwa ko tea ba. Amma ga hankalin mutum ai yasan dai abn sha din ya kamata ko menen mu zauna." Yace haka ne, ta mika mishi bread da ta shafe da butter kaci sannu har yanzu batayi ba. Yace na manta ki shirya da wuri musa da kabiru zasu zo kuje kasuwar 'yan gado da kujeru ki zabo har da carpet, mun gama magana dasu tun jiya. Tace baban khalil da sauri haka? Yace to me zamu jira ? Wannan fa tamkar bashine zan biya. Ta bata rai. Ni bana bin ka bashi, kyauta na baka. Yace to yi hakuri nima kyauta ce irin na miji da mata. Ta sirmiyo daga kan katifar, nagode sosai, Allah ya kara budi da fahimtar juna. Amin. Yace cikin murmushi, tare da dire kofin tace to wane kala zan zabo? Yace duk kalar da ya miki nima ina so. Tace to. Suka rako shi har zaure ita da khalil, kamar yadda suka saba. Yana dauke da yaron tana dauke da jikarshi ta office ta bashi jakar ta amshi yaron suna yiwa juna bye bye, shima khalil tuni ya haddace yanda akeyin bye bye. Kannanshi ya musu ihsani sannan ya ba musa ihsani yakaima uwarsu tundaga lokacin suke zamansu najin dadi suci mai kyau su sha mai kyau, muhallinsu tsaf. Maman ummi ta soma shigema ta in asha bata nan har daki take zuwa ta ce ai aisha ta ce miki kaza da kaza. Ita kuma ikilima sai ta ce ba komai, na yafe mata. Bana so mu dinga cin namanta. Da maman ummi taga ba guri sai ta daina zuwa. Sun shiga watan axumi cikin wadata a talauce ba'a sarauce ba yasai mashine dan zuwa gurin aiki, cikin axumine ta soma laulayin shigar wani cikin, ta yaye yaronta da sauri mahmud kuwa sai dariya yake mata yace ba in nazo da sakona ba kina cewa tsoron ciki gashi nan ya samu, tasha jinyan ciki kafun ta samu jikin ya danyi karfi. Kayan sallar su ta tsura ma ido nata kala takwas, na mijinta ma haka na khalil goma, ga takalma da sauransu, ta dinga godiya yace ina so ayi miki dinkin zamani da siket din nan suna bigeni. Tace haba babank khalil zannuwan babu kasa da dubu hudu sannan ayi siket? Nafi son zani ya ce to shi kenan yanda kike so haka zan miki. Ran jaji berin sallah ta kama lahadi, shi da musua suka shiga kasuwa yayima alhaji cepane shima yayi sai nan yasai kaji babanshi biyar babanta uku, sukuma bakwai ga naman miya sai da aka gyara sannan aka shigo da su. Ranar sallah da yayi wankan sallah iklima tace wayyo Allah baban khalil tamkar kada na bari ka fita,kayi kyau. Yace to nagode,kema kiyi hakan kafin na dawo yau da rana zan bada goron sallah,kin san dai laulayin baby ya dan takura ma sakonnina two days ko? Tace,sai ka dawo. Ta gama dafa abincinta,nazira tazo ta dinga yi mata rabo. Ta yi wanka ta cake cikin shaddar da yayi musu. Anko.da ya dawo yace"a'a cire in za mu ziyara gobe za mu sa. Na fi so ki samun jar atamfar nan. Tace to.sun zo da abokanshi sun ci abinci wanda zuwa yanzun duk sunyi aure kuma suna mutunci da matansu. Suka fita Nafiu yazo tasa mishi na mamansu dan nazira bata san gidan ba. Yace yaya nafisa ma tun jiya tazo.anty Iklima dama ki bar abincinki da kyar in mama zata karba,ta ce ka kai mata. Su maman ummi sai yan harare-harare don su sai ma ranar idin suka samu kajin,aisha kuwa naman shanu ne mijin ya siyo. Ta zuba musu sosai dan ita ta san hakkin makwabtaka tana bakin famfo ya shigo. Ya mata wani kallo da ta gane abinda yake nufi. Ta bishi dama khalil tun safe Musa ya tafi dashi kwantagora gurin mamansu. Zasu yi kwana biyu. Suka sakayo kofa maman ummi ta ja tsaki. Aisha daga cikin daki tace lafiya tace leko ki gani abinda aka saba. Tana ganin kofa a rufe tace kin san yau suna hutun sallah tunda ya samu aikin suka daina turo kofa da rana. Maman ummi tace,ni ko wallahi sai na je na ga kof. Tsaya ki ga yanda zamu yi. Ta wanke kwanon iklimar da ta basu abinci taje ta buga kofar a bugawa ta uku ne ya zo ya bude,ta ce dama kwano ne zan bata. Yace aje mata nan kofa tana aiki ne,ya maida kofar har da sakata. Suka shiga kicin din su suna dariya Tace kin san Allah aisha daga shi sai gajeran wando,suka ce jarababba. Kai jama'a ina ruwanku? Me za ku karu dashi in kun gani? Zaman aure fa suke ba zaman zina ba,shin ku ba kwayi ne?tir da masu irin wannan mugun halin. Shi kuwa mamaki ne ya cika

Chapter 14 of 20