Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cewa nace bazan aureshi ba don ubanki ke ki aureshi mana kin san ni waye ai talaka ba abokin tafyata bane. Muryar baban su ta jiyo yana cewa sannu yar karuna ya iso ya haska su da tocila don ganin wa take caba ma magana irin haka?ya wa take caba ma magana irin haka?ya sha mamakin ganin mahmud,dama kaine take cewa baza ta aura ba? Mahmud kanshi kasa yace nine baba. Malam usman ya jinjina kai sannan yace ina fata ka raba katin gayyatar daurin aure?mahmud yace kwarai muna kan rabawa,yace to kada ka fasa kaji ko?tashi kaje Allah ya maka albarka a kuma cigaba da shirye2. Cikin kwarin gwiwa mahmud ya tashi yayi sallama da yunus da ke can gefe yana kallon duk diramar da akeyi ganin haka nfsa ta nufi gda tana kuka tare da cewa nifa baban mu bana sonshi fa yace nima gidan xan shigo in na karaso kya shaida min,ya dubi iklima kema sallami bakon naki kizo ki shiga gida kuma haka nan,tace to,da sauri taje tace masa malam sai da safe shima ya mike don yaji abinda babanta yace tare da cewa mu kwana lafiya. Malam ya shga gdan daidai nan nfsa tana cewa maman mu ni dai wlh ba xan auri mahmud ba kinji babanmu wai su cigaba da shiri wlh ni kam xan shiga uwa duniya...jin haka yasa malam usman waige waigen madoki idanunshi suka sauka kan faskare ya isa gurin ya dauka ya nufi dakin,saukar duka taji a gadon bayanta ihu ta saki tare da hayewa gado,ya bita yana cigaba da kirba mata,haule itama cikin ihu ta rike shi tana fadin malam! malam! yayi wurgi da ita ta tashi tana cewa jama'a ku kawo dauki malam kada ka kashe ta fa,iklima itama sai kuka takeyi tana cewa baba kayi hakuri,sai da yaga ta daina ihu don wuya lokaci guda kuma ta daina motsi ya yarda itacen.kinyi kadan kice xaki maida ni karamin mu2m shekera da shekaru yaron yana yin wahala a kanki iyayansu sun zo na basu ke da yardarki da amincewarki yanzun sai da aski yaxo gaban goshi sannan xaki ce baki son shi? yana huci ya nuna haule wadda ke rabe gefe tana kuka yace ki maida hankalimki dani don nasan ke ce mai hure mata kunne,ya fita. Ta nufi gurin nfsa wadda numfashinta ke fita sama sama ta dago ta jini na xuba daga kumatunta iklima ta taimaka mata suka nufi kyemis inda ta anshi magunguna da allura tare kuma da gyaramata gurin ciwo suka kuma tarairayota suka dawo da ita gida. Har gari ya waye kuka take kuma bakinta bai mu2 ba,rantsuwa take tana karawa kan cewa ba xata auri wanda bata so ba,iklima kuwa cewa take ya nfsa don Allah ki bar wannan xancan kin san baba ba xaya canxa ba gashi kin ja ya dake ki irin haka. Nfsa tace kada ki dame ni,adake ki irin haka. Nfsa tace kada ki dame ni,ai ke ma munafuka ce. Cikin kwana 2 ta ware sai plasta da ke kuma2nta.s BOOK MABUDIN WAHALA 1***7 Sun shiga kasuwa da haule da hajiya kande sunyo siyayyar kayan sawa da naci da gwala gwalai har da katifa don kwanciyar nfsa,fanka,TV,tare da kasinan kallo. Iklima tana hada icce danta dora girkin sai ga su sun shigo niki niki da kaya mota guda suka dauko shata,makota sun xata kayan aure ne haka iklima ma da ta gansu da risho da tukwane ga xatonta kayan aure ne sun hakura sai taga haule ta bude fos dinta ta ciro gudar dubu1 ta jefa mata tare da cewa iklima kada ki hura siyo lagwanin risho da kalanzir Allah ya hutashe mu,ta saka hijabi da nikab da safa ta fita su ko nan suka shiga gyaran dakuna su haule har da labulaye da zannuwan gado,iklima dai tana kallon ikon God. Suna cikin haka sai ga sallamar mutan gidansu mahmud dauke da akwatinsu katuwa guda1 da kit,haule ta shige daki tana cewa hajiya kande kice su tafi ba fa xa ayi ba,haj kande tace bar su amsar kaya ai ba aure bane. Nfsa dama tana bayi da taji yan kawo kaya ne sai taki fitowa illa xuciyarta da ta cika da haushi gami da tsanar mahmud. Haj kande sun duba kayan sun bada tukwuicin 2K suna tafiya nfsa ta fito ta kalli akwati cikin isgili tace wannan daki barin akwatin ai ba aji na bane. Haule tace yanda suka kawo kayansu haka xasu xo su dauka duk fadan baban su wannan karon sai dai in murajiha. Haj kande tace ke kike nuna kina tsoronshi ki xakalkale masa haka kawai ga gidan hu2! Haule tace ke dai gane mini hanya amma shi ana ga annabi yana runtse ido. Haj kande tace rabu dashi in kin bi ta tashi kya yi biyu babu. Iklima dai tana jinsu tana jajjage. Koda baban su ya dawo daga sallar ishai da dare ya kira haule tana dakin yaran taxo ta xauna tana ta wani cika da batsewa yace gobe kafintan da naba aikin gadon nafsa yace aje a kwashe 2nda ba lokacin damina bane sai a jingine su a can. Haule tace malam shin wai baxa ka hakura da xancan auran nan ba? yarinya tace bata so amma kaki yarda yanxun in ta tafi uwa duniya wa mukayi ma?shi ba sai ya diba wata ya aura ba yan gidansu ma daxun har suna wani kawo akwati. Ya dube ta kin san Allah in dai nine uban da ya haifeta ba2n aure babu fashi kuma ko ta shiga duniyar sai na daura in yaso tayi ta yawon da auran sa duk ranar da ta dawo sai ta tare haka nan in dai shiga duniya ne taje ba kanta farau ba bare ya kare kanta,taje ta bincika a matan da suka shiga dunya me suka tsinta ciki? Yaya rayuwar su ta kare? Haule tace to ni dai nace maganin kada ayi kada a fara ya katse ta rufe min baki mara kirki duk xan iya da ku, haule tace ni dai da ta shiga duniya gara an fasa. Yace kin sanni ai in kin cika matsa min da ba2n fasawa zan saba miki kema. Ya dauki buta ya fita. Shi kuwa ango duk da irin damuwar da yake cki ya kasa sanar da danginsa halin da ake ciki don haka su kam shiri suke ba kama hannun yaro. Gidan da xasu zauna kuwa yasha gyara da fenti. Abokananshi kuwa suma suna ta shiri tare da yin mitin din yanda xasu hada kudin yanmata da na walimar da xasuyi bayan daurin aure. Amma shi ango maimakon murna sai damuwa tare da 2nani domin 2n daga wannan ranar da yaxo taki amsar kati bai kuma samun ganin ta ba. Gurin nafiu ya samu labarin dukan da babansu yayi mata, hankalinshi ya tashi yaxo gidan ya aika fiye da shurin masaki amma sakon da take aiko masa dashi duk ba masu dadin ji bane duk ya rame ya fita daga hayyacin shi Ya sani abin kunya ne yanxun ya 2nkari wani da wannan ba2n domin babu wanda bai gaya masa gaskiya ba game da yarinyar sai ya toshe kunnuwansa tare da kauda kansa yaki sauraron kowa sai gashi yanxun nfsa xata kware mishi baya. To in auran nan bai kasance ba kila sai dai ya bar garin domin ko mahaifinshi babu lallashin da bai masa ba ya nemi wata amma ya kafe. Nfsa ta daga wayarta ta tashi xaune da sauri ganin lambar Alhaji jamilu jiki na bari tace Alhajin Allah ya garin ne?yace gamu a kofar gdanku tace to gani nan xuwa da sauri ta mike tana kwala ma mahaifiyar kira,ta shigo lokacin nfsa na murza hoda da 2rare tace yaya akayi ne yarinya mai tsada? Ckin zumudi nfsa tace Alhaji jamilu a kofar gida,haule tace maxa maxa kada ki tsaya sanya. Cikin wata dirkekiyar mota suka xo ta nufi gurin cikin takun kasaita ta isa bakin motar cikin murmushu tace sai ga ka?yace wallahi ki shigo mana. Nfsa ta shiga ta lafe kan lallausar kujerar motar,sanyin AC ya ratsa jikinta, kamshin 2raransu suka doki juna. Alhaji jamilu ya kai dubanshi ga gidan yace gidanku kenan? ta dan taba baki tare da kallon gidan tace ka sha mamaki ko?gidan ma ba namu bane na haya ne,ni kaina ina takaicin kamar ni nan muke zaune. Yace gaskiya sam ban xace ki a irin nan ba,ya ciro magazine din bikin kalle ki a nan fa,babu wanda ba xaya zaci cewa ke yar wani kusa ce a gwamnati ba. Ta rausayar da kai gefe ka bari kawai ina takaici sosai nasan xaya yi wuya ka aure ni,yace sam wannan ba xai shafi auran mu ba don kuwa ina sonki sai dai dole ne in canza muku gida kafin lokacin saboda yan daurin aure. Nfsa cikin murna tace kai aiko mun gode da ta 2no da waye baban su sai kuma ta dan daure fuska tace ina shakkar baban mu da kyar in xaya amshi kyautar yace saboda me?tace yana da tsatsauran ra'ayi sannan kuma yana son aurar dani ga wani da bana so. Alhaji jamilu yace kada wannan ya dame ki kudi suna saka mai tsatsauran ra'ayi nfsa tace to Allah yasa ya yarda. Yau fa sauran kwana 9 ya daura min auran kana ganin har xaka aure ni xuwa wannan kwanaki?bana son in rasaka. Tayi kwal da ido tamkar xatayi kuka yayi murmushi bari in ga tsohon naki komai xaya daidaita yana ciki ne?tace a'a ya tafi sarkin fawa xaya dauko doya amma gobe kaxo baya xuwa ko'ina saboda juma'a yana gida yace to xan samu masauki xan dawo. Ya xamu dan fita ne kiyo shopping?tace to bari in shiryo da murna ta shiga gida ta shaida ma haule yanda sukayi a gaggauce ta shiryo haule tace ki xabo min leshi don Allah jiya na manta ban saya ba nfsa tace to,iklima ma ko takalmi ne xan sayo mata. Da sauri haule tace kyale ta kada ki sai mata ita nan da samu kudi ba ubanta ta baiwa ba. Nfsa tace ta bamu zannuwa ki dai bari in sai mata. Iklima dai bata da ra'ayin saka ko dankunnan da xa a samo daga mu2min nan wanda xuciyarta bata yarda dashi ba duk da bata taba ganinsa ba. Sun zaga duk wani kanti da ya ansa sunansa da ke cikin garin minna. Siyayya ba a magana sannan ya dawo da ita gida a xatonta in sun fita xay nemi suje masaukinsa sai taga sam shi ba irin haka bane. Masu tsaron shi yasaka su kayi ta shiga mata da kayan cikin gida inda shi kuma suka cigaba da hirar in an daura auransu ya sai mata gida a nan ko tafi son Abuja?da sauri tace haba darlind dina kai ma kasan ba wanda xai bar Abj kaf cikin naija sai dai in waje xaka fita yayi dariya to shikenan. Sai ga Mahmud kamar an jeho shi da yake gilasan motan masu duhu ne bai san tana ciki ba ya jingina da bangon gidan yana jiran dan aike, yazo ne don ya tambayeta a ina abokanshi xasu gana da kawayan nata? in ta ga dama ta fito. Ta dubi Alhaji to kaga fa wanda babana yace xai bani don Allah anyi min adalci?kalle shi fa ka dube ni. Alhaji jamilu ya xuba ma mahmud idanu to ai bashi da makusa,tace yana da makusa kuwa 2nda bashi da aikin yi kyan siffar xanci a gidanshi? Alhaji yace kema kinxo da uxuri,yace to kije gurin shi mu xamu tafi tace Allah ba xani ba kan shi fa har dukana babana yayi, Alhaji jamilu yace to kira min shi,tace da xakaji tanawa da ka bar shi. Ya daga waya ya kira bodyguard din shi guda daya yace kaje ka kira min wancan yaron. Mahmud yana xaune yana ta hamma mu2min yace yane? Mahmud ya dube shu lafiya lau,kana neman taimako ne? Ya daga kafadunshi alamun wuce nan,oga na ke kiranka ina xaton xaya taimaka maka ne,mahmud ya kai duba ga motan da 2ni yake kallonta ga xatonshi babu kowa cikinta yace ina ogan naka?ya nuna motar. Mahmud ya mike tare da kakkabe wandonshi ya nufi motar,murfin motar ya wangale ga mamakinsa sai idanunsa suka sauka kan nafsa kishingide kusa da kyakyawan mu2min wanda daga gani ya jike da hu2. Wani abu ne ya taso ya tokare mishi a kirji numfashinsa na fita da sauri kamannin shi suka sauya idanunshi suka ciko da kwalla tamkar xasu zubo. Ya nuna ta da yatsa nafsa ni xakiyiwa haka?dama kudin wannan mu2min ne yake rudarki?amanata zakici ko? Tace kai wa ma kake?ni dama nace ina sonka ne?dole xa ayi min. Kanshi ya soma juyawa don furucinta cikin karfin hali yace gaskiya ne nfsa kudi babu abinda basa saka mu2m yau kece da bakinki kike cewa dama can ba sona kikeyi ba dole akay miki ko? Dole kice haka 2nda kin tsiyata ni kije na barki da Allah kuma ki rike a ranki wata rana xaki neme ni in nadama ta riske ki...ta katse shi naji don Allah ni dai kuxo ku kwashe komatsanku. Alhaji jamilu ya dubi mahmud kaima dan saurayi kayi ganganci ya dafa kafadar nafsa wannan xubin manya ne da ita ka hakura in ta karya maka jari ne xan dora ka,daga # 1mil ha10 mil,kaje kayi naxari kafin jibi don in ma ka cije to baxa ka same ta ba kuma babu kudin. Mahmud ya katse shi da cewa baxan amshi ko sisinka ba koda ba xan same ta ba saboda ban san asalin kudin ka ba, kai ba maka da wani abu da xaka bani wanda ubangiji ba xaya bani ba ya juya xaya tafi. Alhaji jamilu yace kada ka yanke hukunci da sauri,na baka xuwa gobe zan amshi numbarka gurin gimbiyata zan kira ka inji kayi hakuri na sani rabuwa da masoyi da zafi. Ran mahmud yafi da baci ya dubi nafisa ko a jikinta tana ta taunar cingam tare da yin kwai tana tauna shi kas-kas,ya juya ya tafi xufa na tsiyaya daga jikin shi duhu yake gani duk da kasancewa rana ce. Duk da horn din da mai mashin din ke masa bai ji ba sai da ya bangaje shi har ya fada cikin wani kwalbati,mu2m biyu ne suka taimaka masa gurin ciro shi duk da bai ji ciwo ba yayi dumu dumu cikin kwata,ya dubi jikin shi bakin ciki tamkar ya hadiye kanshi. Wani mai 2ra ruwa yaxo xaya wuce aka tsaida shi inda aka soma diddila mashi ruwan a jikin shi,shi kam kasa motsi yayi. Ya isa gida inda yana shiga ckin gdan hankalinshi ya sake tashi ganin dangin mahaifinshi da ke sokoto sun xi biki gefe juma ga kannenshi suna ta gwada dinkunan ankon su. Hajiya rabi tace a'a ango daga ina haka jiki sharkaf?yayi karfin halin cewa mashin ne ya 2ra ni cikin kwata ya nufi bayi ya sake ma kanshi shawa ba tare da ya cire kayan ba,ya jiyo muryar kanin sa musa ya leko yace musa dauko min jallabiya ta a daki musa yace to,cikin karfin hali yayi wanka ya fito. Ya xube kan katifa ya rasa wa xaya gaya wa wannan kayan bakin cikin da takaicin? Sulaiman ya shigo da sallam ya zauna kan kujera tare da mishi kirari ango kasha kamshi daga gani 2nanin amarya kakeyi to kayi hakuri ta kusa zuwa. Mahmud tamkar ya tashi ya naushi sulaiman don bakin ciki amma babu dama shi kuma ba abin ya gaya mishi abinda nfsa ta mishi ba domin duk sun gaya mishi gaskiya yaki sauraron su. Sulaiman yace na ganka wani iri ya dai?dan tsaki yaja sannan yace bana jin dadi ne,sulaiman yace na lura to kasha magani?ya daga kai alamun eh,sulaiman ya sake cewa Allah ya saukaka yanxun ina xamu ga kawayanta? Mahmud yace don Allah ka bar su in sun matsu su neme ku sulaiman yace shikenan bari in barka ko xaka samu bacci ya fita. Mahmud yana dai kwance ne amma kwakwalwar shi tana dawo mishi da duk abubuwan da suka faru yau itace ranar nadama a gurinshi domin ansha bashi shawara ya rabu da ita amma yaki alhalin hausawa sunce in so cuta ne hakuri magani ne. Abokan shi sukayi ta xuwa don suga yanmatan amarya amma sai dai su samu ango kwance ba lafiya hakan ya kara daga hankalin shi kafin dare doke akayi asibiti dashi. Musa kanin shi ne ya nufi gdan su nfsa ya shaida mata ba tare da sanin mahmud ba 2nda basu san me yake faruwa ba. Bata nan sai mahaifin ya samu dawowarshi kenan xaya shiga gida suka gaisa ya shaida masa,malam usman yace assha Allah ya bashi lafiya in na shiga na shaida musu kayi masa sannu sai nazo,wane asibiti ne? Musa yace babban asibiti. Ita kuwa nfsa lokacin da mahmud ya tafi wani gefe na xuciyarta yana kokawa yayinda mafi rinjayen yake tayi mata murna, da zasu rau da Alhaji bayan siyayya jakar ranar nan ce ya bude mata yace ta diba. Cikin xumudi ta shiga jidar sabbin yan dubu dubun sai da ta dibi dauri 12 ta kalle shi tace sun isa nagode. Yayi murmushi tare da jinjina kai cikin zuciyarsa yayi ma2kar mamakin son kudi irin na nfsa wannan ta dama shi ta shanye kan son kudi,ta runguma ta nufi gidan su. klima ta xaro eyes lokacin da taga nafsa ta shigo rungume da kudi tace "A'uzubillahi" nafsa tace shaidan kika gani?kaji iskanci fa. Haule,haule fito kixo ki gani da gudu ta fito itama 2rus ta tsaya tare da dafa kirji tace ni haula2 me xan gani haka?tace Alhaji jamilu ne yace in diba niko na jido. Haule jiki na bari ta amsa sukayi daki tace kuma yace xai sai ma Baba gida sai dai ina tsoro da kyar ne baba xai amince. Haule tace ya siya in yaki amincewa mu sai mu koma,kina tsammanin xan yarda in sha wahala ga saauki yaxo min? Nfsa tace ki adana su dasu xamu siyo kayan daki haule kam duk ta rude nafsa ta shiga koro mata yanda sukay da mahmud suna ta sheka dariya. Ranar ma yini sukayi lissafin abinda xasu saya na daki ita dai haule fadi take waya zaki fara sai min wannan karon. Lokacin da malam usman ya shigo gdan da nafsa ya soma cin karo ta fito wanka yace yauwa kinji yaron nan mahmud ba lafiya yana babban asibiti ko? Ta danyi dim sannan tace ban sani ba,yace to ai ya 2ro kanin shi ne ya shaida miki muka ci karo ya juya. Cikin rashin damuwa tace Allah ya sauwake yace amin sai kuje ke da yar uwarki ku gaida shi. Ina iklimar? Nafsa tace to iklima an aiketa,ta dai amsa ne amma ba don xata je ba. Lokacin da malam usman yayi xaman cin abinci kan tabarma sai yayi mamakin ganin sababbin kuloli yace daga ina?2nda yasan daidai da cokali in ba saya yayi ba haule baza ta siya ba koda kudin xaya kashe ta ne. Ya buda kular maimakon 2won garin masara yasan suke dashi sai yaga farar shinkafa da taliya na miyar kuma sai yaga ferfesun kaji ne,2ni kamshi ya cika hancinsa yawun sa ya tsinke amma duk da haka ya ruufe murafun ya kalli jug din ruwan shima sabo ne. Ya koma ya kishingida tare da kwala ma iklima kira da sauri taxo gani baba, yace kira min mamanku. Haule ta iso sanye da sabuwar atamfa wadda ba shi ya saye ta ba. Yace xauna ina son xamu yi magana,ta xauna cikin fargaba amma a xuciya tana raya yau kam sai dai suyi ta in dai ba2n mahmud ne. Yace haule ina aka samu wadannan kwanukan tace saya nayi,yace me kika saida kika samu kudi?tace daga Allah suka xo ya bude kulolin wannan girkin fa?tace duk ni nayi,ya nuna zanin jikin ta wannan xanin fa?shima ke kika saya?ta ce eh ya kafe ta da idanu tare da cewa gaya min inda kika samu kudi ya rike habar shi yana kallonta bayan ya 2re kulolin gefe,tace mai son nafi ne yaxo ya bani, ckin sauri yace ya shigo min gda bana nan?ckn sauri itama tace a'a ita ya aiko. Malam usman yay shiru xucyar sa na tafasa har sai yaushe matar nan xatay hankali?an kusa auran yarinya kuma tana amsar kudin wasu?ita kuwa haule jin yayi shiru ta xata yayi ladab ne don haka ta cigaba yana ma son ganinka ya ma ce xaya saya maka gida,ya xuba mata eyes cikin takaicin kalamanta amma da yake dare ne bata fahimci haka ba,ga nata xaton ya yarda ne 2nda tasan a rayuwa bashi da burin da ya wuce gidan kanshi sabida wulakancin masu gidan haya, tace yana da kudin sosai ko yau daurin kudi 12 ya bama nfsa kuma duk yan dubu dubu. In ka bashi hadin kai wallahi har jari mai tsoka xaya baka kaga kana sauke motocin doya shi gurin shi kyautar kudi ba wani abu bane. Dubu dari fa sau 12 ya ba.... Ke da Allah yi min shuru ballagaxar uwa mara hankali,haba yanxune na gane dalilin da yasa yarinyar ta soma 2burewa maganar auran dama me kudi kuka gani?ya tashi tsaye tare da yin kwallo da kular miyar yace ina nafsa?ta fito da sauri ya nuna ta ya nuna haule yace baku isa ba kunyi kadan ku maida ni tsohon banza ku saka ni in saba alkawari har xaki xauna kina shaida min yace xaya saya min gda Allah yasa gari xai bani ko duniya da kayan cikinta ba xan canxa ra'ayi ba,kudi kuwa in yaso ya baku world bank shi ne dai bankin duniya ko? Haule tay karfin halin cewa malam banda abinka wa yaki hu2?tsaki yaja sannan ya fita yana fadan cewa in bakay dace da mace ta gari ba hkika kana ckin wani hali. Manzon Allah(SAW) yayi gaskiya da yace mu xaba ma yayayenmu uwa ta gari. Su kuwa yana fta nfsa tace ni ko a jikina ina kan bakana haule tace barshi kinji ke dai abinda xance miki duk wuya duk runtsi ki jajirce. Nfsa tace har ma sai an fada min? yaushe xan yarda inyiwa kaina black stomach? haule tace a to gane min hanya. Da safe Malam usman ya shirya ya nufi asibiti don dubo mahmud yaci sa'a zuwan mahaifin mahmud kenan gurin suka gaisa ya duba mai jikin da yake ta bacci yace da musa kanin shi idan ya tashi ka shaida masa ina gaida shi,musa yace to xan gaya masa. Malam Usman suka jero da Alhaji Ibrahim suna tattauna ba2n daurin auran nan da kwana7. Sukayi hannu a bakin titi tare da yin sallama,malam usman ya tare mashin ya hau. Shi kuwa mahmud da ya farka musa yace masa baban su nfsa yaxo yace a gaishe ka da jiki ya samu baba a nan,mahmud yace nafsa fa?musa ya taba mouth nikam ban ganta ba,mahmud yayi shiru can yace xata xo amma koda wani ya tambayeka kace taxo musa yace to. Mahmud ya lumshe eyes yana naxarin yanda mata suke juyawa tamkar wahainiya. Ya sani nfsa tana ma2kar sonsa amma ta amince ta sadaukar da son saboda kudi 2ni ta manta da son da yake mata da dukkan dawainiyoyin da yayi mata ita da mahaifanta a can baya. Nfsa ta kira wayarshi Alhaji jamilu ya daga tace yawwa kaxo in kana kusa baban mu yana nan yanxun, Alhaji jamilu yace to,kusam 30mins yaro ya shigo da sallama haule ce a tsakar gida ta amsa yace wai ana sallama da mai house din tace to,ta daga murya ta kira nafiu ya amsa daga cikin daki sannan ya fito tace kace da baban ku ana sallama. Malam Usman Yana fita kofar gida ya shiga waige waigen ina mai sallamar dashi?mota kawai ya gani ba kuma ya xaton cewa da wani mai mota da xaya xo gurinsa bai gama 2nani ba motar ta bude masu lura da lafiyar shi ne suka fito daga gaba sannan suka bude mishi bayan motar ya fito. Sanye yake da shadda irinta karshen kudi yar ciki da malun malun mai ruwan blue takalmi,hula n sandarsa duk bakake ne. Ya nufo Malam Usman yana dogara sandarsa ba don yana dingishi ba sai don kawai gayu da kuma giyar kudi,kasancewar shi fari shigar ta amshe shi. Ya mika wa malam usman hannu sukayi musabaha sannan yace nine mai son ganinka malam usman yace to Allah dai yasa lafiya? Alhaji jamilu yace lafya lau in sha Allah ko xakaxo mu shiga mota?malam usman ya girgiza kai ba xan shiga motarka ba bari in saka yaro ya kawo tabarma,ya leka ckin gdan ya kwala wa nfiu kira yace ya kawo tabarma. Ya shimfida sannan yace bismillah bayan shi ya xauna ga mamakin malam usman sai yaga masu tsaron nashi sun daga but din motar sun ciro wata kujera sun xo sun bude ta ya zauna. Ya kalli malam usman yace baba barka da warhaka anyini lafiya?malam usman yace lafiya lau Alhaji jamilu yayi gyaran murya yace baka sanni ba ko?malam usman yace eh Alhaji jamilu sunana ina aiki ne a Abuja kuma naga nafsa ne ina so shine nake son in 2ro waliyaiyna. Yayi shiru yana sauraron malam usman wanda ranshi ya baci to ko ba auranta xa ayi ba yaushe xaya yarda ya ba wannan yarshi?sam bashi da tarbiyya. Yace Allah sarki gashi kuma anyi mata miji yau sauran kwana 7 bikinta. Alhaji jamilu yace nasan haka ina so a bar xancan yaron 2nda tace bata so in ma kana 2nanin abinda yaron ya kashe ne xan biya fiye da abinda ya kashe kai kuma xan saya maka gda a cikin unguwar 2rawan garinnan in baka jari naira 5mil tare da kujerun makka 10 danginka kuma in.....hannu malam usman ya daga mishi sannan yace noman kudi kuke a gidanku?ya mike tare da nade tabarmar yana cewa in sayanta xaka yi to albarka bata saidaawa bace ya nuna shi da yatsa bana bukatr sake ganinka a kofar gidana baxan ci amana ba. Alhaj jamilu yace malam da ka amince da lalama domin nan duniya ban taba neman abu na rasa ba,malam usman yace wannan karon kasa a ranka cewa ka fara in dai nine ubata ya juya xaya shiga gida. Alhaji jamilu yace in ka canxa shawara ka sanar da ita xata shaida min. Lokaci kadan xaka shiga sahun masu rufin asirin unguwar ku. Malam usman yace kai sakarai hala kai jahili ne?kai ka isa ka azurta mu2m? Allah shi ne kadai me iya azurta bawa ya buga kirjinshi yana cewa ni nan da ka ganni Allah ya bani arxiki saboda ya bani wadatar xuci. Alhaji jamilu yace kai matsiyaci ni kake xagi?in kayi wasa xan sa a tsare ka har abada kuma in auri yar taka in ga yanda xakayi. Ya juya fuuu!!! Mamaki ya hana malam usman motsi har suka tada kura suka bar layin..,. Ya shiga gida yana kishingide bakinciki da takaici sun ki hana shi sukuni,iklima tayi sallama ta shigo gidan duk da kayan makarantar boko ne a jikinta kafarta sanye da safa,fuskarta rufe da nikabi malam usman ya bi kamilar yartasa da kallo duk kokacin da ya kalle ta yana alfahari da ita,ita kuwa bata lura dashi ba sai da ta gota sannan ta ganshi ckin sauri ta dawo baya ta tsugunna tace baba lafiya kuwa?yace bana jin dadi ne yau duk ban fita ba cikin tausayawa ta xauna tare da cewa yaya jikin me ya same ka ne? Yace zazzabi ne tace Allah ya sawwake kasha magani ne?

Chapter 5 of 20