Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zasuyi dn hk gaba suka sa ta suna mata sannu dn dare ya tsala. Sai kusan karfe hudun asubahi sannan danlami ya nufi gidan su babasu. Malam usman yana cikin alwala yaji bugun kofa, sai daya saurara da kyau ya tbbtar nan ne sannan ya nufi kofa cike da fatn Allah yasa alkhairi ne ya kawo koma wanene. Sai daya tmbaya danlgmi ya tabbtr mishi shine sannan ya bude. Danlami cikin dmw yace mamanmu ba lfy tn ciki dare, ciwn ciki, ban zaci xata kai yanxu ba. Sai kusan karfe hudun asuba sannan danlami ya nufi gidan su babansu. Mal usman yana cikin alwala yaji bugun kofa sai da ya saurara da kyau ya tabbatar nan ne sannan ya nufi kofa cike da fatan Allah yasa alkhairi ne ya kawo ko ma wanenen.sai da ya tambaya danlami ya tabbatar mishi shine sannan ya bude. Danlami cikin damuwa yace mamanmu ba lafiya tun cikin dare,ciwon ciki ban za ci zata kai yanzun ba. Mal usman yace subhanallahi to bari in dauro alwala muje. Ya koma yayo alwala ya sanar da mai dakinsa sannan yazo suka dauki hanya. Shima ya tausaya mata yace bari suje sallah sai ya roki makocinsa cewa ya taimaka masa da mota.hakan yayi sun kai ta babban asibitin minna.sunga likita emergency an tura su gefen scan sun dawo likitan ya duba sakamakon tsakuwar ciki ce,yace musu aiki za'a mata a kwashe amma sai sun fara bata magani sun taru guri daya zuwa gobe. Kuma 30k ne kudin aiki. Mal usman ya dubi likitan da sauri,30k dana? Likitan yace,eh baba. Mal usman yace asibitin gwamnati fa. Likitan yace baba suna ne kawai ace asibitin gwamnati amma ba kayan aikin komai. Kasan dai shugabannin kasar tamu ba tausayin talaka. Sun fi son kansu fiye da kowa.ba sa bamu kayan aiki albashinmu ma sai an kai ruwa rana muke samu. Kudin kasarmu suke kwashewa su fita da iyalansu da kansu waje don karatu ko neman lafiya ko kuma shakatawa. Mal usman ya nisa yace haka ne to zanje na bubbuga mu gani. Danlami yace,mu baba da kudi a shagonmu sai dai kudin nafisa ne. Mal usman bai tanka shi ba don shi baya son jin ko sunan an ambata, ya fita. Yana tafiya Aminu yace ma danlami kirata ne kawai in ta ce a dauka sai a dauka tinda da kudin. Danlami ya kira lokacin bata tashi barci ba,ba ma a gida ta kwana ba. babban hotel din abj suka kwana ita da wani saurayinta. Tana daga wayar tace,yaya danlami ya ya ne? Yace,mama ba lafiya sosai aiki za'a mata muna babban asibiti, ta mike tsaye da sauri. Anyi aikin ne? Yace sai gobe,yanzun ma ba kudi a kasa shine muka ce ko mu cira cikin naki? Tace,baba fa? Yace ba kudi gurinshi,amma ya ce zaya buga-buga. Tace,yaya danlami ku dibi kudi ku canza mata asibiti na kudi wanda za su yi mata aiki yanzun nima ina tahowa yanzun. Waye gurinta? Suka ce su ne,tace ina iklima? Danlami yace bata sani ba,tsaki taja sannan ta kashe wayar,gida ta koma ta shiga shirin n minna. Su kuwa nan suka shiga shawarar yanda zasu yi. Aminu yace,muje mu dibo kudi kawai mu canza mata asibiti,ni dama wannan asibitin bai min ba,ina ganin ba su san aikinsu ba,in ba haka ba kuna ganin mutum cikin wani hali ku ce sai gobe? Danlami yace,amma ba ga shi sun mata allura har ta samu bacci ba? Sannan sun ce don stones din su taru guri guda ne shi yasa suka bari sai gobe. Aminu yace to me ka ke nufi. Danlami ya gyara tsayuwa tare da dubanta sannan ya dubi aminu. Muje mu shawarci Baba.Aminu Yace,da mun kyale shi kana ganin da muka ce ko a kirata banza yayi mana. Danlami yace,duk da haka dole ya sani. Gidansa suka koma,sun samu yana karyawa da koko da kosai,ganinsu ya fadar mishi da gaba. Yace,ya ya ba dai jikin ba? Suka ce,a'ah, nan suka zauna sannan suka gaida matarshi. Suma ta dire masu kwanon koko da ludayi,basu kalli kokon ba,danlami ya zayyano mishi komai,kala bai ce ba. Aminu yace,ba ka yi magana ba? Ya dubi aminun,yanda yake wani dacin rai,sannan yace shiru ma magana ce,ya rage naku ku fassara. Aminu ya mike.zo muje don Allah,lokaci yana tafiya. Danlami ya yi jim don yasan babansu ba da son ranshi ba ne,ya mike tare da cewa,baba mun tafi. Yace to Allah ya sauwake. Suna fita danlami yace da nafisa,da za ta ji shwara da ta bari,baba ranshi bai so ba da batun canjin asibitin nan. Aminu yace,to in ranshi bai so ba ya ya zai yi? Shi fa ba kudi ne da shi ba,don Allah kada ka kira ta. Danlami yace,yana da kyau nafisa ta nemi sulhu da baba. Aminu yace yanzun ba wannan lokacin ba ne,yanzun batun ciwo muke yi. In ba zaka canza mata asibitin ba ni na canza mata, shi fa baba da ka lura ma bai damu da mamanmu ba ne,in ba haka ba dubi yanda ya dawo gida yana cin abincinsa don yaga yana da wata matar. **Danlami yace wai kai me ke damunka ne? Za ya kasa karyawa ne don ciwo? Ya soma kiran layin nafisa,tana dagwa tace,ya ya jikin dai? nima gani nan ina shiri. Yace da sauki dama na kira ne in ce maki ko zamu bar Mama anan asibitinne domin ran baba bai so ba..." Ta katse shi,don Allah ya danlami bana son in rasa uwata,ku canza mata asibiti in don ra'ayin nan na baba ne sai ta mutu yana nan yana kaza yake so kaza ke bai so. Danlami yace shi kenan. Sun kaita asibiti mai tsadar gaske inda aminu yaje ya dibo kudi suka zube kafin kace hka kuwa kuwa tuni sun mata aiki sun fito da ita. Daya saura nafisa ta iso. Nan tasa suka je store dinta suka yi ta jido kalolin juice da ruwan sha. Ta tura su gidan abinci mafi tsada suka yo musu oda,tana bacci suka yi ta ci tamkar suna gida. Ita kuwa iklima bata sani ba,can matar babansu ta tuna ta kira nafiu tace,maza ka je ka sanar da iklima. Tana kokarin shiga da kuloli daki ta gama kwashe abinci kenan ya shigo. Tace,nafiu shigo,kai ne da rana haka? Mahmud na bakin gado ya dawo cin abinci lokacin nafiu yake cewa,mama ba lafiya tana asibiti za'ayi mata aiki. Iklima ta dafa kirji tana cewa,aiki? Mahmud sai yaji kamar nafiu yace,baba ba lafiya don haka da sauri ya fito yana cewa,baban za'ayi wa aiki? Iklima duk ta rude ta kasa magana. Nafiu ne yace mama na ce. Mahmud ya ce,ayyo sai na ji kamar kace Baba. Ya koma ciki yayi zamanshi har zuciyarshi ya ji da sauki tunda ba Baban ba ne. Yanda yayi abin yayi ma iklima ciwo,bata so yanda yake nuna ma mahaifiyarta ko cikin magana ne in ana batun iyaye sau da yawa in ta ce "mu ma haka mamanmu kaza" sai ya yi tsaki musamman in ta fadi wani abin kirki na maman tasu, ta zuba ma nafiu abimci yaci sannan tace ina nan zuwa wane asiniti ka ce ma? Yace ban san asibitin ba,baba ne kawai ya sani. Tace,to zan zo ta gidan in ji. Bayan tafiyar nafiu ta shiga dakin fuskarta daure,ta jera masa abincin sannan ta dawo falo ta zabga tagumi. Ya gama ya watsa ruwa ya fito har zai fita sai kuma ya dube ta. Lafiya ki ka yi wani zugum? Ta dube shi hawayen da take makewa suka zubo,ta ce a zatona mahaifiyata mahaifiyarka ce. Yace,to me aka yi? Ranta ya sake baci,tace ba'ayi komai ba. Ya zauna,kin san dai bana son bacin ranki ko? Ta dube shi cikin kukan shagwaba ta ce,sanin kanka ne ba ka min adalci akan mahaifiyata,bana son yanda kake nuna tsanarta karara.albarkacin auranmu komai tayi maka ai ka yafe mata. Ya riko mata hannu"ban tsane ta ba,don bata min laifi ba."ta matsa mashi hannu,"meyasa ka nuna ko in kula da kaji an ce bata da lfy?"ya saka dayan hannunshi yana share mata hawaye tare da cewa,"shi kenan yi hakuri,kiyi wanka muje tare,zan amso mashin din Hamza.hakan yayi maki?"Taye dan murmushi tare da daga gira.Mashin din Hamza ya amso ta shirya suka fita,ya dauke ta a mashin.Ko yaushe za su fita yakan so tayi ado,amma ita koda tayi a don sai ta rufe jikinta ruf,sannan tasa nikabi.Yasan a musulunce ta fi shi gaskiya,shi yasa baya magana. Gidansu suka je,matar Babansu ce ta shaida musu sunan asibitin,don lkacin da Danlami ya dawo ya shaida mata asibitin da suka canza mata Baban ya fita. Mahmud ne ya gane kwatancan asibitin,don haka suka dau hanya. Za su shiga Aminu za ya fito don Nafsa ta aike shi ya sai mata kati,shi ne ya nuno masu dakin daga nesa ya wuce. Suna tura kofar da Nafsa suka soma tozali,dukkan su sai da gabansu ya fadi. Ikilima tunda Nafsa ta bar gida kafin auransu sai yau ta kara ganinta Nafisa tana rike da waya me shegen tsada, tayi kyau ta kara kiba ta xama hajiar sosai, jikinta sanye da wani leshi me tsadar gaske. Sai da ikilima taci tuntube dn faduwar gaba. Mahmud yayi saurin taro ta xuwa jikinshi tare da cewa ki lura da kanki mana my baby". Wayar dake hannun nafira ta subuce ta fadi kan kafafun haule dake kwnce sharkaf kan gado, idanunta sun tsayu kan mahmud shi kuwa tmke fuska yai tamkr be taba daria ba. Ikilima ta isa kusa da ita ta dafa ta tana cewa sannu anty nafisa. Firgigit tai kafin ta kalli ikiliman, sannan ta daure fuska. Ikilima tace ina yini anty nafisa, ya jikin mama? Nafisa cike da masifa tace Yini bn ganshi ba, jiki km gashi nan ki tmbyeshi. Ta sake kallon mahmud, wnda fuskarshi ke daure yana kallon ikilima.a kauda kanta gefe, yaxo ya janyo kujera ya kamata ya dorata akai ta xauna, yai kasa da murya yace, bana so kina dmw kanwata, ki zauna zanje na dawo tnda tana bcci. Ikilima ta dube shi da murmushi, to sai ka dawo. Ka kular min da kanka kaima. Har ya kai bakin kofa zai bude sai ya kuma dubanta. Ya dawo ya sunkuya ya sumbaci lebunanta tare da shafa cikinta ya mike ba tare daya kalli ko inda nafisa take ba ya fita abinshi. Nafisa ta diro dg bakin gadon cikin tsananin kunan rai, ta shiga sintiri a tsakar dakin ji takeyi tmkr ta shake ikilma ta kashe. Dukkan abubuwan da mahmud yai ma ikilima ynxun nan su ne suke yawo cikin idanunta da kwanyarta. Ta dubi ikilima tana hura hanci. Ta nuna ta da yatsa "ke maci amana, macuciya. Ta soma hawaye. Kinci amanata kin auri masoyina, kina so ki nakasa rywta. Ta matso gabanta kinyi karya, lkci be kure ba ki rabu da mijina. Ikilima ta dubeta cikin harara, mijinki? Mijinki fa kika ce? Itama ta mike tsaye mijinki na can inda kika baro shi, mahmud nawa ne har abada. Ta sake zama kan kujerar, ta cgb da cewa bn cuce ki ba, kece kika cuci kanki kika yaudari kanki, kika br abin sonki kika auri kudi. Nafisa ta sauke mata mari mai karfi a kunci, daidai lkcn aminu ya shigo km marin shine yai sanadiyar farkawar haule dg bcci. Ikilima ta dafe kumatu, ni kika mara yaya nafisa, me nayi miki? Aminu ya isa gurinta yana cewa nafisa meya faru ne? Bata kula shi ba ta cgb da cewa baki ma san me kikayi ba ko? To ki sani dole ne ki bar min mahmud din yar iska kawai. Ikilima tace ni ba yar iska bace, km da ace farkon auran mu kikaxo da wannan bidi'ar kila in yarda, amma ynxun da sakonninsa suke yawo dani a sararin samaniya, Allah daya bani shine kawai zai iya raba mu da juna ba dan adam me kashi ba. Nafisa ta sake zaburowa, aminu ya riketa. Kiyi hkri kece babba. Ya dubi ikilima, baki da kunya ko? In tashin hnkli ya kawo ki mu ba shine a gabanmu ba, tashi ki kama gabanki. Tai shiru bata ce komai ba. Nafisa sai zaginta takeyi tare dayi mata mugayen kalamai. Nafisa ta sauke mata mari mai karfi a kunci, daidai lkcn aminu ya shigo km marin shine yai sanadiyar farkawar haule dg bcci. Ikilima ta dafe kumatu, ni kika mara yaya nafisa, me nayi miki? Aminu ya isa gurinta yana cewa nafisa meya faru ne? Bata kula shi ba ta cgb da cewa baki ma san me kikayi ba ko? To ki sani dole ne ki bar min mahmud din yar iska kawai. Ikilima tace ni ba yar iska bace, km da ace farkon auran mu kikaxo da wannan bidi'ar kila in yarda, amma ynxun da sakonninsa suke yawo dani a sararin samaniya, Allah daya bani shine kawai zai iya raba mu da juna ba dan adam me kashi ba. Nafisa ta sake zaburowa, aminu ya riketa. Kiyi hkri kece babba. Ya dubi ikilima, baki da kunya ko? In tashin hnkli ya kawo ki mu ba shine a gabanmu ba, tashi ki kama gabanki. Tai shiru bata ce komai ba. Nafisa sai zaginta takeyi tare dayi mata mugayen kalamai. Aminu sai lallashinta yake yana bata hkri, dayake ance me kudi bashi da wa sai kani. Ikilima kuwa sai kuka takeyi domin haule ma da take kwnce tana mgn da kyar fadi take mugun halinta irin na ubnta ne, don Allah ta fitar mata bata son ganinta. Nafisa na cewa ki rubuta ki ajje sai mahmud ya dawo hannuna sai kin wulakanta... Daidai nan mahmud din ya shigo. Bakin kofa ya tsaya idanunshi kan ikilima, km yaji maganganun da nafisan ke gaya mata. Ranshi na zafi ya isa gareta. Tashi muje gida. Ya mikar da ita, ta share hawayenta da bayan hannu sannan tace ka gaida mama ta farka. Ya dubi gadon, yaya jiki? Banza tai dashi, nafisa ce tace ana gaisheki. Haule tace da sauki. Ikilima ta kalli maman mun tafi mama, sai na sake zuwa. Bata tnka ba, ya kama hannunta suka fita. Nafisa ta bisu da ido, wani tukuki take ji cikin zucia, ta daga labule windon tana kallon ynda yake share mata hawaye tana kuka, sannan ya taimaka mata ta hau mashin din, ya tada suka tafi. Ta runtse ido wasu zafafan hawaye suna zuba. Shedaniyar zuciarta ta shiga raya mata cewa, ta raba su ko ta halin yaya. Ta xauna kan kujera tare da share hawaye, aminu yace nafisa ki daina damun kanki kan wannan mahmud din, har ynxu fa yana nan ynda kika sanshi bai kara komai ba sai ma kara tsiyacewa da yai. Ta kalli aminu, ai ynda ban aure shi ba itama dole ta barshi sbd ina son shi ynxun. Gidansu haule ta koma ta kwnta dn samawa zuciarta mafita, abinda take yawan tmbyr kanta shine, ynxun mahmud ya daina sonta? Ko ko yana so ya rama abinda ta mishi ne? Wata xuciar tace ikilima yake so da baya sonta ba zai yi mata ciki ba, dubi ynda koyaushe idanunsa ke kanta, kalli kulawar da yake mata. Ta tuno irin sumbar da yai mata a gabanta, abinda taso yai mata tuni yace sai sunyi aure, gashi yana yiwa kanwarta a gabanta. Da yake hausawa sunce laifi tudu ne, ka take naka ka hngo na wani. Sai ta furta a fili cewa mahmud kaci amanata, ka cuce ni. Zuciyarta tace A'a kece kika cuci kanki, gashi ynxun kina dana sani. Dubi ynda yake nuna so da kulawa ga yar'uwarki, kin zabi kudin da bana halak ba ga zunubin ludu da zina su kuwa suna cikin ryw me tsafta. Wata zuciar tace zafa ki same shi in kin dage, ynxu ki nemi mafita ne ta ina zaki fara? Tai shiru tana son ta tuno ta ina zata fara din. Shedaniyar zuciarta tace to bari in tsara miki ynda zakiyi in dai zaki bani daki-daki, to zaki cimma burin rywrki. Ta sake rungume filo dn saurare tare da hawa dokin zucia. Zuciar ta cgb da sheda mata cewa kisa a kona dan shagon da yake takama dashi, sai ki bude mishi ido da kudi, ki nuna masa su zunzurutu hr ynxun yana sonki zai aureki sai ki kashe auren ke in hk bata samu ba ma ki kai shi gurin bokanku mana. Ta sheke da daria, tabbas dk wadannan mafita ce km shawara ce amma zata fi so tasa yan daba ta basu kudi su kone shagon ko don ikilima ta kuntata.una? MABUDIN WAHALA 2**6 Har suka shiga daki ikilima hawaye take zubarwa, don dai idanunta na rufe ne cikin nikab shi yasan kuka take sbd yana jin shessheka. Ya rungumo ta zuwa jikinshi. Haba ikilima, nasan kin saba da halin nafisa, don tace sai na rabu dake na aureta sanin kanki ne tatsuniya take yi. Wlhy ko mata sun kare bazan aure ta ba, ynxun na daina sonta kece nake so. Ya cire mata hijabi ya cusa hannunsa cikin zaninta yana shafa cikinta. Kece uwar babyna da kannansa. Ya soma share mata hawaye. Haukanta take yi kada kisa komai a ranki. Ikilima ta dube shi, har fa marina tayi. Da sauri yace mene? Mari? Matata? Ya mike sai na ramo miki. Tace ai na yafe ka barta kawai. Ya rungumeta tare da cewa alkawari ne sai na gargadeta kar ta kara, dk lkcn da muka hadu. Ya zaunar da ita akan kujera tare da cewa, bari in nemo mana na karin safe tace to Allah ya bada sa'a. Kusan hudun dare yake jin bugun gida sama sama. Lkcin daya fito dukkan mazajan gidan sun fito tare suka nufi kofar kowa yana kissima dalilin bugun kofar. Shi dai mahmud yafi raya babanshi ne ko maman su ikilima. Suna bude kofar sai gasu musa kannanshi suka ce wuta a shagon shi. Nan suka dunguma, tsayawa kawai sukayi suna kallon wutar, sai ci takeyi har ta soma kama gidan da shagon yake. Mutane ne sukayi ta gudunmawa da ruwa har dai yan kwana-kwana suka zo. Cikin sa'a aka kashe wutar, sai dai ta lashe komai har ginin ta rusa, tnda da fridge a shagon kun san gas. An km rasa musabbabin wutar, sai dai anfi ba wutar nepa. Gida ya dawo su da mazan gidan nasu suna jajanta masa, har lkcin ikilima tana bcci gashi wasu masallatan sun tada sallah. Yayi alwala, sannan ya tasheta shi km ya nufi masallaci. Tana azkar ya dawo, ta gaishe shi ya amsa, ya zauna shiru. Tace au, na manta bari in tashi in shirya zamu asibitin kuwa? Ya dube ta a sanyaye, Eh, zamuje. Tace baka jin dadin jikinka yau ne? Yan jaje suna ta zuwa, babanshi ma har gidan yazo, yace yazo da dare yana nemansa. Haka nan babansu ikilima yazo har yake ce mata na shaida ma mamanku danaje asibiti dazun. Ikilima tace to. Abokanshi sun hada mishi dubu goma, kowa dai dai don ma wasu basu da kudi, yai godia sosai dasu ya sai musu kayan abinci. Sannan da dare yaje gurin mahaifin nashi. Alhajin ya sake jajanta masa, sannan ya soma da cewa, na kira kane don muji yaya za'ayi? Tnda kaga nima ynxun lamuran sun danyi tsauri, sana'ar tamu ba kasuwa irin da. Mun rage yin tafiye-tafiyen ma, don fatun ma in mun kai su sai dai bashi, ynxun da hk motata ta tsaya dk lamarin na kudi ne da sai a gyara shagon amma kai yanzun menene tunaninka? Mahmud yai shiru dn dama shi da mahaifinsa kawai yake takama, km hakika ya tbbtr mahaifin nashi ba kamar da bane. Ya nisa Alhaji sai dai mu cgb da addu'a, Allah zaya kawo mafita, domin uwar da ribar duk suna shagon, hatta kayan abincin mu suna ciki. Alhji ya jinjina kai tare da cewa "Allahu Akbar, to zamu ga ynda za'ayi. Tashi kaje amma ka shiga gurin su hajia su auna maka shinkafa ka dibi doya yace a'a abokaina sun hada min dubu 10 na siyo kayan abinci, yace to madalla tashi kaje Allah zai bada ynda za ayi. Lkcn daya shigo gidan ikilima tana zaune kan sallaya tana addu'oi, ta shafa ta mike tana ninke sallayar tana kallonshi da murmushi tare da cewa, sannu da shigowa. Yace yauwa. Ta kawo mishi abinci ya zabga tagumi, ta zauna tana zuba mishi cikin filet, yace yayi yawa fa, tace ni sai ka cinye, tnda abin nan ya faru baka wani cin abinci, meyasa kake dmw ne? Ya dube ta, ikilima na tsani yinin nan da nake a gida ba abin yi, in na fita sai dai gurin abokai. Ta koma kusa dashi ta kwntar da kanta a kafadar shi, niko ina son inta ganin gani ga ka koyaushe, yauwa zan baka wata shawara zaka samu abinyi, ci abincin tukunna. Haka tayi ta jan ra'ayin shi har yaci ya koshi, sannan yace to fada min. Tace zan fada maka sai munje bcci, ynxu yi wanka dai ga ruwan can. Da yake madafa yake nema ranar da wuri ya kwnta, tayi ta jan shi tare dayi mishi abubuwan da suka sa shi kai mata sakonnin shi domin tnda ya shiga wannan halin baya iya yin wani abu na nishadi, sai da suka nutsu sannan yace ikilima ba zaki fada min shawarar ba? Tace, yauwa ynxun zaka fi fahimta ko? Ta cgb, ka kwashe fridge dasu T.V duk kayan wutan mu dai ka saida kaja jari. Yace to ai ko gyaran shagon bazasu isa ba. Ko yaushe na kalli cikinki ina dmw, ba mu sayi komai ba. Ta rungumeshi "Allah zai kawo. Da safe ta matsa mishi ya amso mashin suje asibiti taga mamanta, yace a'a tace to in bazaka ba ni ka bar ni inje ko a kafa ne. Jin dai ta dame shi hk nan ya aro mashin suka tafi. Haule taji sauki dn har ta soma dan cin abinci, ba da wata kulawa ta ishe su ba ta dai yiwa mahmud jaje. Nafisa ta shigo ikilima ta gaisheta da kyar ta amsa ta zauna bakin gado ta bude jakarta ta ciro daurin yan dubu dai-dai guda 2, ta dubi mahmud ya akaji da abinda ya faru? Ya hade fuska, ikilima tace yaya tana maka mgn. Yace da godia. Ciki ciki yai magnr. Ta mika mishi kudi, ga tawa gudunmawar, Allah ya kyauta gaba. Ya dube ta cikin matukar daure fuska, kin samu lbrin ina neman taimako ne? Cikin daburcewa tace A'a, amma ko dn ikilima kanwata ai zan baka gudunmawa. Yace to bana so. Hatta ikilima bataji dadi ba, ta dube shi, ka amsa mana yayana yace kin nemi wani abu kin rasa ne? Ta girgiza kai. Haule tace bar kudinki dama sai dana ce kada ki bashi. Ta dube shi kin san talaka bai iya iskanci ba inya tashi yi. Nafisa ta katse ta, mama ba ruwanki nace don Allah. Ta sake duban mahmud din to zan nemo maka aiki, ka fahimta? Don ikilima zanyi. Ba tare daya kalleta ba yace ikilima in xaki tafi tashi muje in km naje na dawo ne to? Ta ce jeka dawo din. Ba tare da ya sake magana ba ya fita. Dakin yai shiru na wani lkci, haule ta sake cewa, matsiyaci, ko an sa shi a tandun mai haka zai fado fari kwal. Tnda yace baya so ki kyaleshi. Ikilima tace yaya nafisa mun gode. Zan shawo kanshi a hnkli. Nafisa tai shiru xuciarta na zafi, wlhy da ba don ikilima yaruwarta bace sai tasa an kashe ta. Amma ynxun tnda tana neman sulhu dashi har ta samu ynda zasu dinga hulda dole sai tabi takan ikilima. Ta dubi iklima,kanwata duk abinda ya faru ina fata ya wuce? Iklima tace ba komai,dama ban rike ki ba domin na san aikin shedan ne. Tace,to ina muku jajan abinda ya faru. Sannan na tausaya mishi yanda su Aminu ke bani labari. Iklima tace,wlh. Nafisa tace yanzun me ku ke bukata? Tace sana'ar dai ce in ba ita ba bamu da matsalar komai. Nafisa tace,zan fi son ya kawo takardunsa in nemar masa aiki,wlh in CBN yaje so zan samar masa kuma babban matsayi. Iklima tace zan lallaba miki shi insha Allah zamu zo tare. Nafisa tace,likitan ma yau zai sallame mu da dare in ya yarda gobe sai ku zo don jibi zan wuce abj. Tace to. Ta mika mata daurin kudin guda daya,ga wannan kwa dan ringa batarwa ko. Iklima ta amsa tare da godiya. Dama ba mu da ko sisi cikin dakin,in na lallaba shi zai amsa. Nafisa tace,ba komai. Daf da magrib ya dawo,bai shigo ba wata ma'aikaciyar shara ya aiko ta kira ta,nan tayi musu sallama ta fito. Nafisa ta biyo ta da harara ita kuwa haule tsaki taja tare da cewa,dukkanku haushi ku ke bani,an taba abu dole. Tunda yace ba ya so ai babu dole a ciki. Tunda suka dawo ta rasa ta ina zata soma yi masa zancan.har ya soma bacci tace,don Allah tana son suyi magana. Ya tashi zaune,ta ce dama kan wannan ne am.ya katse ta da cewa"ki mun magana mana bacci nakr ji. Ta kama hannunshi,yaya nafisa ta ce ka kai mata takardunka zata samar maka aiki ta hanyar mijinta ni a ganina ba wani abu ba ne.ya kamata yanda ta bar komai kaima ka bari dazun har hakurin abinda ta yi min rannan ta bani. Ta kalle shi sam tana ta zuba bata san ya cika yayi dam haka ba tamkar ya doke ta yake ji. Ta daga filo,ga ma wannan tace muyi cefane dama ba mu da sisi a dakin nan. Ya tashi zaune da sauri ranshi bace ya suri filo ya fita ya bar ta zaune da kudi a hannu. Ta biyo shi ta zauna gefen kujerar da ya kwanta. Yayana don Allah ka. Ya katse ta da cewa ke mara hankali,in kin sake min magana zan kashe miki fuska da mari. Ki gaggauta fitar min da kudin nan daga dakina ko in bala'in bata miki rai. In har zan kwana a dakin nan to kuwa kudin nan ba za su kwana ba. Ta yi shiru cikin jin haushi,me yasa shi sam ba ya fahimta ne? Nata ganin bai dace yayi gaba da danginta ba. Cikin zumbura baki ta ce,to ni yanzun ya ya zanyi da wannan kudin? Yace,oho miki,ni dai ba zasu kwanar min a dakina ba. Ta saka hijabi ta fita dakin maman ummi ta kwankwasa mijin ya bude ya fito tace daman gurin maman ummi na zo. Yace,to. Yaje ya taso ta,iklima tace,yi hakuri na tashe ki daga bacci.don Allah kudin nan zaki dan adana min zan amsa da safe. Ta ce,to nawa ne? Dubu dari ne. Inji iklima. Ta juya duk da hakan da iklimar tayi bai sa mahmud sakin fuska ba. Nashi ganin iklima bata da hankali,a ganinta Nafisa ba da biyu tayi mishi wannan kyautar ba. Koda zuciya daya ne baya so. Dama bata san darajar ta ba ne yasa shi jure miyagun kalaman da mahaifiyarta ta gaya mishi ba. Har zuwa washe gari bai kuma shiga harkarta ba. Da safe kuwa ko karyawa bai ba,yana yin wanka ya fita sai dare ya shigo, nan ma sallama kawai ya yi, sannun da ta mishi sai da ya gimtse fuska sannan ya amsa. Ita kuwa Nafi jin su shiru basu zo ba sai tasa Aminu ya kawo ta gidan bayan magrib. Iklima ta idar da sallah kenan ta zabga tagumi tana tunanin yanda zata shawo kan mijin nata. Sai yanzun itama ta ga wautar ta,tun a can

Chapter 11 of 20