Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ko mahmud na ckin gidannan kamin sallama dashi? Musa ya gane surkinsa ne don haka yace ga dakinsa nan,yace to yi min sallama dashi musa yace shigo kawai baba,yace ayi haka?musa yace ba damuwa. Malam usman ya shiga da sallama,mahmud dake xaune ya xabga uban tagumi ya amsa sallamar ganin baban su nfsa sai ya mike da sauri,malam usman ya mika masa hannu su gaisa amma ya noke tare da nuna masa kujera bismillah xauna baba,yace da ka bani hannu mun gaisa ba karamin lada bane ga kankare xunubi ga musulmi masu yin musabaha. Shi dai mahmud kanshi yana kasa suka gaisa ya sake tambayar shi jiki.malam usman ya kalli musa wanda ke shirin fita yace wannan ba kanin ka bane?mahmud yace danuwa na ne,malam usman yace to dawo ka xauna musa ya dawo ya xauna. Malam usman ya koro musu duk abinda nfsa ta mishi sannan yace ya yafe ta cikin yayan sa sannan yace naxo maka da albishirin baka iklima kuma xa a daura auran ne a ranar da akasa kai da nfsa. Mahmud ya dauki rigarsa dake kan katifa ya shiga share xufa sannan yayi karfin halin cewa baba mu bar ba2n iklima don kanwa ta na dauketa,nfsa kuwa na hakura haka Allah ya nufa xaya faru. Malam usman yace kada kayi saurin yanke hukunci kaga lokaci ya kure yau saura kwana4 daurin aure kayi shawara da magabatan ka. Shawara ta gare ka kada kace xaka ki iklima tafi nafsa komai,riba kaci don samun mace mai ilmi da addini ba karamin falala bane samun mace mai addini shine cikar mu2ncin da namiji. Mahmud yayi shiru,malam usman ya mike yace to duk yanda ake ciki naji xuwa da safe,mahmud yace mai sonta ina 2nanin ba xaya ji dadi ba,malam usman yace kada ka damu da wannan saboda magabatanshi basuxo gurin mu ba ya fita yana cewa Allah ya sawwake ina sauraron ka. Musa yace to mun gode baba,xanxo da safen,malam usman yace to kwa iya yin shawara da magabatanku. Ya fita Yana fita musa ya dube shi yaya kayi naxari in dai yana nufi yarinyar nan ce mai sanya nikabi mutane dayawa na sonta har dani,a ganina dami ka tsinta a akala yarinyar da taci gasar kara2n Al-Qur'ani mai girma na kasa yanxun haka xata tafi ta duniya gaba daya a kasar saudiya ranar asabar dinnan mai xuwa in an daura auranka da kwana1 nasan ka sani da gaske ne kalmar mahaifinta riba kaci. Mahmud yace son fa?ina son nfsa sosai wlh ban san irin son da nake mata ba sai yanxun da na rasa ta bana bacci. Musa yace ka amince in so samu ne ma baba kada muyi mishi bayani sai ranar,kayi kokarin ganawa da ita. Mahmud yace xanyi kokarin yin istihara yau da dare xan roki Allah in da alkhairi yasa min son lamarin cikin raina amma yanxun dai ko sunan mace ban son ji. Musa yace yauwa sai kabawa Allah xabi sai dai ina 2nanin Alhajin mu. Mahmud yace shi da bashi da burin da ya wuce na son inyi aure bana jin xai ki yarda don kasan baya son nfsa,musa yace haka ne yanxu dai bari in barka. Sukayi wa juna sai da safe ya fice. Daren ranar babu wanda ya runtsa cikin mu2m 3. Malam usman yana sallar nafila ne yana gaya ma Allah matsalar shi wato inda alkhairi auran iklima da mahmud Allah ya tabbatar,iklima itama zabin Allah take nema,shima mahmud haka. Nfsa kuwa dai dai wannan lokacin tana can akan tafkeken gadonta na gdan matar abokin Alhaji jamilu tana ta sharar bacci har da mafarkin ana yin bikin su ita da mahmud yana bata tsire a baki ita kuma sai narke masa take yi. Lokacin da gari ya waye ta tashi sai 2nanin mahmud ya dawo mata sabo tare da sonsa mai tsanani. Ta janyo filo ta manna shi a kirjinta tare da lumshe eyes tana rayawa kan faffadan kirjinda ta dora,kai dole ne ma in ta fizgi abinda xata fisga ta koma ta aureshi. Ta lura ba xata taba jin dadi ba matsawar bata tare dashi damuwar ta Allah yasa kada yayi auran huce haushi da wata,koda yake tasan bashi da kudin yin aure yanxu,2na hakan shi ne ya dan kwantar mata da hankali. 2nda ya dawo daga sallar asubah yaji ya samu natsuwa kuma yana ganin mafi a'ala shi ne ya amince da ba2n mahaifin nafsa domin yin hakan shine xaya kara yi masa shamaki da nfsa domin yanxun in da akwai wadda ya tsana to kuwa bata wuce nafsa ba. Sun zanta da kanin shi musa in da ya kara cusa masa ikliman kuma sunyi cewa xai je gurinta don jin bakinta. Iklima duk saurin da takeyi sai da taso tayi latti,ko kamun bata sha ba don ko karyawa bata tsaya yi ba. Yanke tabi bata son tabi layin su mahmud sai dai dogon lungun da ta shiga daidai xata fita daga lungun mahmud da abokanshi xasu shiga ta lungun suma. Gabanta ne yay mugun faduwa domin ta gane shi ckin frends ta ckin nikab tana ganin kowa mutane ne basa gane ta,gefe ta rabe suka shige lungun shima ya gane ta amma sai yayi tamkar bai ganta ba,sai dai yayi gaba ya juyo itama daidai lokacin ta juyo,da alma daga motsa jiki suke in ta lura da kayan dake jikin su da takalman su. Tana tasowa ko gda bata shigo ba ta wuce islamiyyar su don bita da takeyi saboda gasar kara2n su da xasuje ranar sati manyan malamai ne suke taruwa suna kara yi mata gyara. Sai 5 ta shigo gdan da alamu har yanxun mahaifiyarsu bata dawo ba,cikin damuwa ta shiga ta ajiye jakarta ta soma aikin gdan tare da girki. Danlami ya shigo da sallama ta mishi sannu da kasuwa sannan yace mama bata dawo ba?iklima tace walh bata dawo ba ina xaton ko dai baba baije gurinta bane, danlami yaja kujera ya xauna yana cewa walh sun je jiya dasu baba malam idi abokinsa yace ya maida ta tace bata maidu ba ita baxa ta dawo ba,tana gdan hajiya baba kawarta nima daxun da xan tafi kasuwa na biya tace min xata dawo ashe ba dawowa xatay ba,iklima tace basa bata shawara ne yan gdan da taje. Danlami yace xugata fa sukeyi ai duk shegiyar yarinyar nan nafsa ce taja mana,iklima tace Allah ya shiryeta yasa ta kuma gane da wuri amma in munyi sallah muje gurin mama muji ko xat yarda ta dawo Danlami ya dubi mahaifinsu yace baba xanuje gdansu mama inda maman take yace da kkunyi hakuri domin maman ku tayi nisa bata jin kira ni dai naje na sanar da ita na maida ita tace min baxa ta dawo ba,iklima tace xamuje mu gani yace to kuje kuji ni dama don ku ne da kuka matsa da baxan damu da dawowarta ba,har da aminu suka tafi suna fita shima ya taso nafiu suka fito waje su dan sha iska. Suna fitowa sai ga samari guda3 yayi musu sallama suka amsa ya basu hannu suka gaisa mahmud ne kamar ko yaushe ya make hannun shi,ya gyara tsayuwa kunxo gurina ne ko?ya juya bari in dakko tabarma, sulaiman abokin mahmud yace aa baba mun xo ne mu gana da iklima cikin jin dadi malam usman yace oho to ku dan yi jiranta yanxunnan xata dawo sunje nan ba nisa ita da yanuwanta,suka ce to,suka xauna shi kuma ya tafi. Su kuwa su iklima suna xuwa gdan hajiya baba kofar falon suka tsaya suna ta sallama amma su haule sun kaure da suru2 suna cin food suna kallon fim tare da wasu kawayensu irin su fati dillaliya da mairo uwar adashi. Suna jiyo muryar mahaifiyar su tana cewa niko ina sha'awar shiga wasan hausa dinnan ina ma xan samu na shiga?uwar adashe tace kin san Allah in har kina so ni ko xan miki hanya,haule tace Allah xanyi, hajiya baba tace kuma xaki karbu suka sheke da dariya suka tafa. Tace ai Alhaji jamilu yana xuwa gobe suka kaini gidan da ya sai min aka gama bikin nafsa kawai kawata ki hada ni da wanda xai kai ni fim din. Iklima kunnuwanta basa son jin kalmar don haka ta kuma dagewa tace "salamu alaikum" lokacinne suka ji suka amsa ganin yaran sai ta daure fuska,hajiya baba tace aaah yayana ne sannunku ku shigi. Suka xauna suna kallon mahaifiyar su kowanne da abinda yake kimsawa ckin ransa kaji ne a gaban su da kwalaban fanta. Iklima ta kara yarda mahaifiyarsu bata damu dasu ba haka nan sakin da baban su ya mata na gargadi bai xamar mata darasi ba,ta katse mata 2nani da cewa lafiya yayan baban su me kuka zo yi? Danlami ya fara gaidasu sannan yace munji shiru ne kince xaki dawo kuma baki dawo ba. Iklima tace mama 2nda baba yace ya maida ki a musulunce ke matarsa ce don Allah ki dawo mama,aminu yace ni dai ko baki dawo ba kada ki shiga fim,tace lah kuji mu da yaro dama 2ro ku yayi ku labe mana?sukace a'a tace ke kuma magana daya kice Allah yace annabi yace musulunci yace to ban maidu ba inma 2ro ku yayi ba yace xai rike yayansa ba nfsa ce yar banxa ya bar ma duniya to ni xan rike ta ta yata daya tamkar dubu don hausawa sunce da taron yuyuyu gwara daya kwakwara. Ni gobe war haka ma ina sabon gidana da mijin nfsa ya sai min an gama gyaran shi yau gobe xan tare in an gama xuba min kaya. Ckinku waga ni uwarsa ce xai xauna dani yaxo wanda kuma ya xabi xama a gidan jar kasa bulon kasa babu ko fulasta ya xauna. Nan yaran suka shga yi mata magiya, amma ta ce kada wanda ya ishe ta fa,haka suka taho jiki ba kwari,kowa xuciyarsa na kisima masa yanda rayuwar gidansu xata koma,in suka yi la'akari da itama iklima aure xatayi wa xai kula da gidansu,musamman ta fannin girki. Suna isowa kofar gdan iklima ta samu bakinta suna hira kasa kasa har xata gota muktar yace wannan ba iklima bace?ta isa gurinsu tayi musu sallama ckin girmamawa da sanyin murya suka amsa dukkansu,ta gaidasu ckin ladabi sannan tayi shuru tana sauraransu. Suleiman ne ya soma magana da cewa iklima kin sanmu?ta daga nikabinta ta saka shi a kanta kasancewar gurin da duhu baxasu iya ganin fuskarta ba tace nasan yaya mahmud ne kawai,sulaiman yace very good kuma nasan kin san halin da ake ciki game da ke dashi ko? ta sauke nunfashi sannan tace na sani. Yace yauwa to yanxun mun xo muji naki tsarin su wanene kawayanki saboda mu basu kudin sha'aninku muna nufin musan shagalin da xaku yi. Mukhtar yace saboda lokaci ya tafi sosai,ta gyara tsaiwa sannan tace bani da wani tsari sai na sunnar manxonmu (SAW) a musulunce walima ce kawai muka sani in mu2m yayi aure ko ya samu karuwa. Don haka kada ku damu kanku kuyi walima kawai domin ranar daurin auran da yamma xamu tashi xuwa saudiya inda xamuyi gasar kara2n alkur'ani ina neman addu'arku ta numfasa. Sannan tace inna dawo xanyi tawa walimar gaba 1 da fatan hakan ba xaya sosa raku ba. Sulaiman yace ai mu murna muke Allah kuma ya taimaka,ba2n kawayanki babu kenan? Ta ce wannan shine gaskiyar magana,suka ce shikenan ba damuwa. Mahmud dai kanshi yana duke kuma yana sauraron su. Mahmud yace muje kawai ai duk abinda xance kun riga da kun fada,ya mike iklima tace to Allah ya bamu alkhairi nagode,ta nufi gda. Mahmud yayi dan tsaki tare da cewa sam yarinyar nan bata yi ba,mukhtar yace me ya hanata yi?sulaiman yace in dai nutsuwa kake so da hankali wallahi yarinyar nan ta wuce da 2naninka. Mahmud yace kun kasa gane xabina,ina son mace yargayu mai kwalisa wannan koyaushe a lullube,addini ma fa ya bani damar naga irin matar da xan aura. Haka dai abokanan suka tafi suna karfafa masa gwiwa,yangidansu ma da su muktar sukace gara ya fada ya shaida musu sai kowa ya sshiga murna,kannanshi mata suka shiga alfaharin yayansu xai auri wadda suke jin kara2nta cikin waya. Shi kam da yayi xugum ckin daki mamaki yake yanda abokanshi,dangi nsa da kowa hatta mahaifinsa murna suke da wannan canji,mahaifinsa ne ma da yaso yaki yace duk a hakura dasu saida su Hajiya uwa sukayi masa bayanin yarinyar sai ya amince tare da murnar alkhairi. ***Ranar Alhamis dangin malam usman suka iso daga jalingo maxa da mata bos 2,lokacin da ya karanto ma kannansa abinda ya faru bayan tafiyarsu sun sha mamaki,baba hamza yace lallai nfsa ta cika yarkanta walh yaya ka barta ne baka karya shegiya ka xubar tsakar gida ka kuma daura mata auran in yaso tayi jinyar can a gidan mijin. Baba sale yace gara da ya barta duniya ce ta ishi kowa riga da wando itama xata haifa domin manzon Allah (SAW) yace ku yiwa iyayanku biyayya yayanku xasuyi muku biyayya. Kun ga yaya irin biyayyar da ya ma magabatanmu amma yarsa tayi masa haka,to ita yaya nata yayan xasu mata? Malam usman yace xatayi nadama lokacin da bata da amfani iklima kuwa ba xan daina alfahari da ita ba suma suka ce Allah ya shi mata albarka. Duk yanda ya kamata a ga gdan biki haka gdan malam usman yake cike da mutane ana ta girke girke ga makota da yan uwa da abokan arxiki amarya kuwa tana ta shirin tafiya gurin gasa,karfe 3 jirginsu xaya tashi karfe 1 aka daura aure. Daurin auren ya samu halartar mutane da dama ciki har da manyan malaman kasar nan,abokanan ango sun xo tare da ango,bayan an gama daurin aure sun xo ne don suy sallama da amarya,danlami ne ya same ta ta fito wanka tana sallah yace da kanwar baban su in ta idar kice mata angon yaxo don suyi sallama tace to baxayashigo ba mu ganshi mamudan? Danlami yace inta fito ta shigo muku dasu ya fita. Ta gama shafa mai dama kwalliyar ta bata wuce mai da hoda ,anty iyami matar baba hamza tace banda abinki amarya yau dai kamata yayi ace kinyi yan shafe shafe kina amarya,iklima tayi dan murmushin yake sannan tace Anty iyami yau bani da lokaci ina son in xama ckin shiri yan mintina ne suka rage mu tafi,ta ciro mata shadda ckin akwatin auran baxa wannan amarya,ta kalla tace kai gara dai ku bani atamfa,suka bata atmfa yan Ghana dinkin kuwa tamkar dama kayan ya xauna mata tace sun saka hijabi ma kuwa? Anty iyami ta dago tace kin ganshi nan guda1 ne sai gyalalluka ne. Iklima ta kalli hijabin tace wannan ya min karami sai dai ko in na xaman gida,danlami ya sake yin sallama yace iklima ki xo mana suna ta jira,ta saka hijabin ta sabo da ta dinka don xuwagurin gasar ta daura nikabi ta fita. Lokacin da ta daga labulan buhun kofar gidansu ta fito har yanxu akwai ragowar people yan daurin aure,idanunta suka sauka kan mahmud da abokansa kusan su 10,yana sanye da farar shadda yar ciki da malun malun yayi kyau da hularsa kube ta isa gurinsu ckin natsuwa sannan tay musu sallama duk suka amsa illa mahmud da fuskarsa ta nuna rashin jin dadin ganinta ita kuwa tana kallonsu duka ta ckin nikabinta,tace ina yinin ku?suka amsa lafiya lau amarya. Ishak yace har yauma da rufin face xa a xo mana?bata ce kome ba, mukhtar yace sallama mukaxo yi,sulaiman yace ya kamata ace da ango xa ayi tafiyar, iklima ta gyara tsaiwa tace lokacin ne ya kure domin daga gefena mu2m 1 xaya je da kanin baban mu aka shirya tafiya. Sadi yace to mu dai muna nan xamu kasa mu tsare a gaban tv Allah sa ki xama zakara,tace amin nagode. Sukay ta suru2 kafin daga bisani mukhtar ya dubi mahmud ango kai har xuwa yanxu bamuji ta bakinka ba ina ganin yanuwa mu basu guri ko?sukace hakane,to amarya yanxu sai dai muce Allah ya dawo daku fyn tace nagode sukay gaba tamkar ya bisu don bai san me xaya ce da amaryar tashi ba,abinda kawai ya sani yarinyar tana da irma a idanunsa batay kama da wadda xa a wulakanta ba saboda ilminta,yace malama ana ta yin shirin tafiya ko?tace in sha Allah nan da 30mins ko 1hr xamu tafi,yace to Allah ya taimaka tace amin na gode da adduarka,duk sukay shiru na dan lokaci sannan yace xamu koma tace na xaci sai kaga tashinmu?yace naso hakan nima sai dai abokaina sun kira walima kuma sunyita ne don ni bai dace ace bana gurin ba tace haka ne to sai mun dawo,yace Allah ya tsare. Ta tafi ya bita da kallo yanxu yarinyar nan matarsa ce sai dai bai san wa ya aura ba saboda nikabi. Uku daidai jirginsu iklima ya dauki hanya. Nfsa bata da labarin auren iklima da masoyinta don haka 2ni itama ta diro minna don shagalin nata auren da Alhaji jamilu kai tsaye gdan da Alhaji jamilun ya saima haule nan direban ya sauketa da tata motar sbuwa dal ta kudi kimanin 4mill Kuma ckin yan kwanakin da tayi gdan Anty hajara ta iya mota don dai ckin gari haka saboda tana da karambani,kudi ne iyaka kudi ya xube mata,akwa2na kuwashago mafi tsada suka xaga a garin Abj ta darji akwa2nan da takeso tare da kayan ciki,gwala gwalai kuwa sai da tace mishi ya barsu haka don shi da kanshi yay ta xabansu,cewa yayi ma don lokaci yaxo a kure ne da dubai xasu da indiya da china don kawai hado lefe. Haule kam da kawayanta da wasu daga danginta sai murna sukeyi da ganin kayan lefen duk da cewa ba wani nashi bane ya kawo direban shi ne. Kai ckin bkin baya ga abokinshi Alhaji kabiru babu wanda sika gani kuma basu damu su gani ba duk kawayanta shine ya saya musu anko na shadda wanda aka hada da leshi dinkin mutanan sanagal N20K haka ya dinga jidar musu. Ranar daurin auran kuwa 2n safe masu kidi suka kafa tare da hana kunnuwan mutanan layin sakat ita kuwa sai rawa suke tana canza kalolin kaya,xuwa karfe 1 aka daura auran su a wani masallaci karkashin waliccin kanin haule kawu idi amma sunyi wa limamin masallacin karyar cewa shi kanin mahaifinta ne. An daura auran bisa sadaki N500K duk wanda ya halacci daurin auran kuwa xaya baka labarin irin garar da ya diba ga kyaututtukan kalandu jakukkuna masu dauke da hoton ango da amarya duk wanda ya kalla kuwa xakaji yana cewa kyau na dukan kyau yayin da wasu ke ganin nfsa ta gama morewa a duniya. Koda yake itama haka take gani A ranar asabar dinne dai da dare mahmud yana zaune gaban mahaifin sa wanda yake masa nasihar cewa ya rike kyautar da Allah ya bashi da amana wato iklima sannan yace xaya kara masa jari don gyara shagon sai shi kuma ya nemi kudi don xuba kaya a ciki sai yace ai maman su ma tace xata bashi daya filinta yayi jari. Alhji Ibrahim yace hakan baxai yiwu ba saboda ba kai kadai ne dan da ta haifa ba kayi maneji da wanda xan baka in naga shagon naci gaba xan kara maka kudi amma yanxun kam kada ka sake inki labarin ka kuma saaida mata fili. Mahmud yace nima fa nace ta barshi itace ta dage yace a'a xan ganta mahmud yace shikenan nagode Alhaji, Alhaji Ibrahim yace kada ka damu ni matsalata kaine babba in har ka xama nagari nasan kannanka ma xasu xama haka ka rika tunawa kaine ubansu watarana. Mahmud yace xan kiyaye insha Allah. Alhaji yace to Allah yayi maka albarka yasa abokiyar arxikin ka ce ina kara horonka da ka rike ta da amana domin yarinyar itace xabin Allah a gurinka. Mahmud yace insha Allah xaya kula ya fita ya nufi gurin mahaifiyarsa da danginta inda babansa ya bar musu ainihin sashen sa har a gama biki.els BOOK MABUDIN WAHALA 1***10 Bayan ya fito ne ya samu abokansa suna jiranshi a bakin dakin sa na waje suka shiga dakin suna hira,mukhtar ya kunna tv don son yaga labarai sulaiman yace sai dai kaga newsline yau asabar ka manta?kafin ya bashi amsa idanunsu suka shagala da kallon dinner din da ake nunawa live. Shahararran dan siyasan nan ne Alhaji Jamilu a ke nuna auransa da nfsa yace a'a har auran nafsanka yaxo ne mahmud?dukkan su suka tsura ma tv idanu daidai lokacin da suke rawa anai musu ruwan naira kan mahmud ya sara. Yace mukhtar kashe talbijin dinnan kada ka min fami ba xan manta cin amanar da nafsa tayi min ba kuma xan manta cin amanar da nfsa tayi min ba kuma xan rubuta labarinta don kawai ya xama darasi ga wadansu maxajan masu xurfafa so irin na gaskiya da aka hore mu da muyi so saisa saisa don in karasa abinda kake so din sai kayi tawakkali. Mukhtar ya kashe kowa yace kada ka damu, Allah ya maka mafificin canji yace ni na karaya nawa ganin duk halin mata daya ne. Sulaiman yace Allah ya hana kudin goro akwai da yawa nagari. Ni yanxun damuwata yanda xan xauna da yarinyar da tsakanina da ita gaisuwa sai ko kira min yayarki,abokanshi suka ce wannan baxai xama matsala ba domin akwai wadanda basu taba ganin juna ba sai a matsayin mata da miji kuma sunyi xaman mu2nci da juna. Haka sukayi ta bashi shawara tare da kwantar masa da hankali. Ita kuwa nfsa daidai wannan lokacin 2ni suna Abja inda jirgin sama ya debe su,katafaran gda ne mai dankaran kyau duk shige shigen gdajenta na masu kudi bata gama xaga gidan ba kuma ganin dare ta mishi kai hatta da kawayenta sun rude haka danginta. Safna tace kawata kin debo mai xafi,mama xee tace ai tayi babbar sa'a mu kam gani nake maxajan mu basu fi yanaikin ku ba,ita kuwa sai daga kai tare da salo ga magungunan mata da take ta dankara tana fadi yanda ya gigitata da kudin shi haka nan itama take son gigita shi a daran farkonsu. Yato mata waya cewa su shirya xa a xo a kwashe su xuwa dinner wadda ake nunata su mahmud suka kalla,duk son kudin nafsa sai da ta firgita da irin wadanda ake likawa domin daloli ne ba ayi amfani da ko 1K ba ckin kudin mu na kasa,sannan taron dinner din kusan duk kusoshin kasar suna gurin inda ta kara yarda tayi babban kamu kenan. Sai dai dinner babu mata dayawa kamar yanda ta xata sai maxa matasa da yawan su sunyi irin shigar nan ta wizee wandon kuwa ass down ana ganin wandunan su na ciki,an shi ansha a gurin dinner an watsa kudi har kusan 3 na dare sai dai wasu sunyi tatul da giya inda ranta ya dan sosu kenan har tayiwa angon nata korafi da cewa darling me yasa kuka shigo da giya gashi duk wasu sai maye suke yi? Yace kada ki damu mu mun san yanayim mutanan da muka tara ne wani in bata ba xaya xoo ba. Koda suka koma gidan ta xata xai nemeta a sashin shi saboda mutane basu tafi ba amma taji shiru,kai har ta kirashi ckin waya tace taxo?yace a'a ta tsaya gurin kawayanta ba damuwa. Bata so haka ba domin itama abubuwan da tasha sun sata matsuwar su kasance da mijin nata don haka bata damu ba lokacin da yan rakiyar tata suka soma shirin tafiya bayan sun gama karyawa da kaji da sauran kayan dadi da xaki wani abin ma basu taba ci ba,sannan aka xaga dasu cikin dankareren katafaran gidan suka ganshi,ba kawayanta ba har ita kanta ta amince cewa sunanta ya bita babban gida babbar mota duk ba wanda bai rude ba,da xasu tafi yayi musu alkhairi mai yawa tare da basu direba ya kaisu har gida. Iklima wadda ke ckin farincikin isarta kasa mai tsarki don gudanar da gasar kara2 komai yana tafya yanda ya kamata,tsawon sati1 suka dauka suna gasar,kwarai da gaske iklima tayi kokari don itace taxo ta biyu. Sun samu kyaututtuka na kurani da litattafai ga kudi duk da ba itace 1st ba amma ta samu,bizarsu ta kwana10 ce don haka kwanaki ukun da sukayi mata saura ta kashe sune gurin yin ziyarori da ibada da adduoi. Tasha mamaki yanda kasar su ke karrama mahaddata kur'ani duk inda xata shiga da masu tsaronta,ranar da xasu dawo kuwa ji tayi tamkar kada ta baro kasar,kano suka sauka inda sarkin musulmi suka tare su tare da manyan malamai. Gwamnatin kasar nan tayi mata tarba tare da yin walima gareta,mahaifinta da mijinta da wanta sun samu halatta aka bata kyautar motadaga gwamnatin kasa sannan suka nufo minna gdan mahaifinta tare da kyaututtuka har da motarta,farinciki baya misaltuwa bata bata lokaci ba tace da mahaifinta tana son ya sai gida ne da kudadanta motar kuwa a samu wurin ajiye mata kafin tay nazari,mahaifinta yace shi kam yana son duk dangi da makota suma su shaida don haka xaya basu nasa su sa albarka mota kuwa taba mijinta. Tace a'a ya raba in kudin basu kai na gda ba sai ya saida motar a cika nafi so ka daina biyan haya,kannan mahaifinta suka ce hakan yayi.ranar ce kuma aka kai ta dakin mijinta gdan mahaifinshi da ya bashi ciki da fao sai bayi da kicin daga waje sannan da akwai yan haya mu2m 2. Bayan yan kawota sun tafi kasancewar bayan magrib ta fito tana kallon falon kayan da mahaifinsu ya siyo ne domin nfsa yarta kujeru ne guda 5 sai ledar tsakar dakinta da labulayanta duk kalar ja,a talauce ba a sarauce ba ta sani mahaifinta yayi kokari ga kuma,ckin dakin baccin kuwa gado ne 6 by 6 yaji katifa da mudubi gami da durowoyin sa sai yan kayan girkinta sune ma take ganin xata karo don ta gansu babu yawa 2nda baban su yace itama dole ta amshi wani abu ta rike in ta amsa ta kara abubuwan da take so. Gidan da xa a siya ma ya kafe kan cewa nata ne da sunanta xa a siya saboda halin rayuwa. Can kusan 10 sai taji sallamar su Mahmud da abokanshi ta amsa da sauri tare da shigewa ta sako hijabinta da nikab duk suka xauna kan kujeru wasu kuma a kasa,sulaiman ya dubi ango yace kira mana amarya mu gaisa mu sayi baki,mahmud wanda ke sanye da shadda light blue yayi kyau sosai ya sake hade fuska shi fa sam har yau iklima bata kwanta mishi a rai ba,mukhtar yace ta ango xo mana mu gaisa iklima ta fito hannuwanta rike da plate guda2 shakare da cin cin da alkali ta aje musu sannan tace ina yininku?suka amsa Basiru yace to amrya yau dai ai a cire murfin guskar mu gaisa aga juna ko?tace kada ku damu a musulunce hakan shine yafi alkhairi a tsakanin mu,mahmud ya sake jin haushin abinda tace dama fitowarta da nikabin ya dada shakar dashi,ta kawo musu ruwa suka mata murnar dawowa lafiya duk da cewa bata zo ta daya ba sun jinjina mata,tace nagode Allah ya saka muku da khairan,ta koma ciki sun kusan minti 30 suna hirarsu ta abokai irin da an rako aboki dinnan,wannan yace masa ka dage gobe mu samu yan2,sai mai cewa banda zalama duk dai bai tanka su ba kalma1 ya furta inda yace ina ma ace nfsa ce yau da babu wanda xaya kaini farin ciki. Sulaiman ya dube shi da sauri sannan ya kalli kofar uwar dakan ya sani cewa iklima taji don haka ya mike tare da cewa abokanaina ku tashi muje suma suka mike duk basu ji dadin jalmar shi ba ya biyo su don yin rakiya nan ko sukayi

Chapter 7 of 20