Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fa ai ni na zata kema yana kawo miki.ta ce, ku kai mata, nasan nima zai siyo min.hajjiya hauwa tasa hannu ta ciri lashi biyu atamfa biyu, shadda biyu,komai ta diba har da kayan shafa ta zazzagebabbab akwatin na farko ta zuba mata kayan.zata yi magana ta hanata,ta ce musa dauki ka kai mata gida.hajjiya uwa ta ce,ko dai a bar su nan a kai dinki,kin san ta bashi zata yi hajjiya hauwa ta ce,hakan ne, ta dube shi ka bada kudin dinki.ya ce, too.zuciyarshi cike da zukkumi kayan da aka diba,kuma kalolin da shura tafi su,gashi har hajjiyar su ashura sai da ta nanata mishi cewa kada ya sake a taba kayan.koda suka dawo gida taguni yayi,ta dube shi ka bari in har sun bani zan baka.yayi sauri cewa,a a ki bar su dama zan sai miki ba komai,ta ce, a a , wadannan sunyi tsada da yawa sai amarya.kalmar ta duki shi,ya ce ban gane ba, ke ma ai irin su daman zan sai miki.ta ce, ni na yafe,in sun kawo ko bayan biki ne zan bata kayanta, Allah sa alkhari.ya ce, a a na ce ki sa daman zan sai miki.ta danne hawaye da ke son fitowa,ta ce a a kayi hakuri ba jajajja zan yi da kai ba,lefenta ne nima an min.ya ce,to naki ai ai ba irin wannan ba ne, tayi dan take,too auran so ne wannan ba irin nawa ba, kaga kowa da matsayinshi. ta tura bayi ta shige.duk da kokarinta sai da tayi kukan ta maiishi,yanda ba zai ji ba dole ta yo wanka don kada ya gane.shi ko maganarta ta saka shi cikin rudu.da ta fita ta shafa mai,ya ce ikilima! ta dube shi zaune bakin gado, ta ce na,am. yanzu ta ji dan sanyi cikin ranta saboda kukan kishi da taye. kishi kumallon mata,ya ce ni nace bana sonki? ta sunkuyar da kai,wallahi ikilima ina sonki,ba zan yi aure ne don na muzguna miki ba.bata ce kala ba,ya ce gobe ne nake ga ya dace mu koma sabon gidanmu,ko ya ki ka gani?nida zaka ma barni anan nafi so.ya ce, a a ki sa su hajjiya su tsire ni kenan,kiyi hakuri ban dai sai mana sababbin kaya ba,yanda na ci buri.amma in sha Allah in komai ya lafa zan siya.ta ce, too ai wadannan ma ba suyi komai ba,zaman duniya Allah na tuba sun ishe ni.shi dai haka ya koma ranan lahadi tare da yan kai lefe, sun samu tarba sosai, sai dai ba su samu tukuici ba, saboda lura da suka yi ba babban akwatin tare da sauran kaya.bayan tafiyarsu,ashura ta tada balli har da kuka.hajjiya kuwa ta tsare shi lalle sai ya fadi ina suke?ya ce, ya ba matarshi saboda bai samu halin yi mata kaya ba.daga ashura har hajjiya suka rufe shi da fada,me yasa bai dauki masu arha ba?bai samu sakar ba sai da ya sha alwashin biyanta bayan biki.hajiya ta hakura amma ashura sai masifa take yi,wannan yar kauyen banzan me ta sani da zata kwasar mata kayan masu tsada?nan take ya daure fuska tare da fita daga gidan. Ikilima sun tare, koina fes koda ba sabbin kaya daki suka sa ko ina ya birge mutane.hajiyan shi ma tana gidan don dama da gefen da ya yi na saukarta,sai coridor,cikin coridor din aka shirya dakunan bacci,ga na ikilima.na yara manne da nata.sai na marya manne dana yara maza,gefe na mahmood sai hayar kichin,kowanne da toilet ciki.shi kuma dakinshi ma kulle yake don ba ko katifa.duk gidajan biyu fannin ango da amarya ana ta shiri bare ma gidan amare.da yake ita dole ta aje aiki tunda ba za a bari suyi aure karkashin banki daya ba,sai dai ya sha mata alwashin sama mata a wani banki.kyua iya kyua ashura tayi,jiki ya gogu da dilka,kafafu sun sha lalle sai kamshi take,ga magungunan mata da ta dirka na tsiya.ango dama yana garin saboda aiki ranar juma,a abokan shi suka diro,ranar ce kuma za,ayi mothers night. Sun hallaci gurin,kyan da amarya tayi ya firgitata acikin jikinshi yake tamkar ya manna ta a cikin jikinshi don sha,awa, goma daidai aka tashi daga shagali.suna harabar ta arewa house suna ta daukar hotuna da kawayanta da abokanshi,tamkar kada ya bar gurin,abokin aikinshi ya sauki su muktar.shima can zaya kwana,sam ya manta da ikilima,don yau ko sau daya bai kirata ba.sai da ya kwanta abokanshi suna ta masa tsiya wai ya rage rawar kai ko kunya baya ji,sai uban zumudi yake ga dangenta suna ta yi maka dariya,ya ce, ka bari wallahi na kosa a gama bikin nan.muktar ya ce, in ko kaje kana wannan rawar kan nan a gaban ikilima zaka kure hakurinta.gaban shi ya fadi, sam ya manta da ita yau,ya mike ya shiga toilet ya ciro wayarshi a fili ya furta cewa,Allah sarki saboda ganin missed calls dinta har guda uku.ya soma kiran layen.suna kwance da yaranta,ta dauki waya taye guntun murmushi takaici,sannan tayi sallama.ya amsa yace daita.Don Allah kiye hakuri kanwata,wayar na silent ne.dama na ji shiru ne ba ka kira ba, na ce hausawa sun ce ka gaida mai gaisheka ka,shi yasa na kira.to na gode,ina yara? ta ce, sun yi bacci. kin sami dinkunanki? ta ce, ehhh.to mai kuma kuke bukata? ba komai.har ni?ya fada cikin marairaice murya.taye murmushi.kai ko ina bukatarka ka min nisa yanzu.to ko in zo ne?a a sai da safe.har kin gaji da hira da ni?kada na takura maka ne,kana cikin hidima.duk hidimar da nake ciki kin sha gaban hidimar.uhmm.ta fada cikin wani yanayi.ba ki yarda ba ko?to ya zan yi,ba dole in yarda ba. to bari na barki ki huta masoyiyata.ta ce, hummm!ko da bata yarda da abinda ya ce ba a kalla ta ji dadin yanda ya nuna kulawar shi,shi ko ana shi bangaren gani yake bai kyuata mata ba. washegari tun safen jumaa,a ke tururuwa gidajan biki , kide kide kuwa gidan da amarya suke ita da kawayanta ba dama ne. karfe daya daidai aka daura auren,suma can gidan ango dam da kawaye da dangi,ikilima tana sanye da atamfar da babanta ya yi mata kala biyu da zanin gado,danlamin su ya sai mata kuloliabinci sababbi,matan abokan shi kuwa sai surutu suke yi suna fadin ai maza maciya amana ne, kowa ya ce namiji uba ne zaya mutu maraya.waye waye.ta ce,ba haka bane.wallahi ni ban ga laifin namiji ba, Allah ne.suka yo mata caa.kannashi har suna cewa,ai ga shi nan kayan fadar kishiya sai da aka kwatar mata.ta ce, to ai ba addini ba ne,ba wata aya ko hadisi da ya ce don miji zai aure sai ya maka kaya.sai dai kyuatatawa yana da dadi.suka sake mata caa akan ta fadi haka,kowa da abinda yake fada mata.wannan su ce wawiya,wannan su ce sakarya,wasu su ce ta rako mata.karar wayarta ne yasa ta ce ku saurara min ga ango nan ya kira,ta nufi toilet da gudu,suna ta mata tsiya,tayi sallama ya amsa cikin zumudi ya ce da ita.kanwata an daura aure fa. wani abu yazo ya tokare ta a kirji,kadan ya rage numfashinta ya dauke.ta danne ta ce,to madallah, Allah yasa alkhari.Amin, nagode.ki fadawa su hajjiya,sannan su jamila su share dakin amarya,kun dai dora,musu abinci ko?don yanzu zamu dauko hanya ta kasa amsa shi,saboda kuka da ya subuce mata.tasa hanu ta toshe bakinta don kada ya jiyo ta,sai da ta hadiye kukan sannan ta ce kana ji na? ehh,yanzu ina jinki. na ce kun dora musu abinci?ehh zamu de dora yanzu. yayi dif don ya ji muryarta na rawa.yayi kasa da murya.kuka kike yi ikilima? MABUDIN WAHALA 3**8 A a. sai kuwa kukan ya subuce,taye maza ta kashe wayar.sai da ta sha kukanta mai isanta sannan tayo alwala ta fito tana cewa da su. too duk mai niyyar sallah lokaci ya yi,ta dauko hijabi ta tsada sallah lokacin ya yi.ta ji sanyi.da ta idar ta ce,to an daura aure fa jama,a ku taya ni da adu,a.ta nufi inda su mahaifiyar shi da su hajjia uwa ke zaune ta sheda musu sakon shi cewar an daura,sannan ta shiga hada kayan miya don yi musu girki.da guda suka shigo, misalin biyar na yamma.gaban ikilima ya shiga faduwa,sai kama anbaton sunayen Allah SAW,ta shiga yen zikiri cikin ranta.suka je yi dankin su dakin amarya fa ya ji kaya masu tsada,gado ma saiti biyu ne,dayan sai suka sa dakin shi.kichin kuwa sai suka tattara yan komatsanta gefe suka danke shi da kayan kicin masu aiki da naurar lantarki.aka gabatar musu da abinci,da guzurin su nan suka fito da naman kaji da kalolin lemuka suka shiga ci.kawayan ikilima sai surutu suke yi,wannan ta ce lallai kin ma zama raba danni kenan,sun danke dakin miji da kichin.ta ce, arziki ne, amma a ranta ta ji mamaki.kiran sallar magariba yasa kowacce tattara komatsanta don zuwa gida.wannan ta ce, na bani har magariba tayi ban ji ba,gashi ya ce hudu ta mini a gida.haka dai suka yi ta surutan su suna shiri kafin wani lokaci shiru ba kowa su watse,dangin shi ma duk masu aure, sun gagga dakin amarya sun kama gabansu.ikilima ta share dakinta ta turo kofa taye sallah tayewa yaranta wanka, tana musu shirin bacci sai gashi yayi sallama,tun da suka zo ma bata sa shi ido ba.ya ji wata danyar shadda sai kamshi yake, dama shi gwanin tsafta ne.ya shigo ta mishi sannu ya amsa, idanunshi na kanta,ya zauna kusa daita.Ikilima kin sani cikin wani hali,mai yasa ki kuka dazu?ta dube shi,ta ce ban fa yi kuka ba.ya matso ya rungumo ta jikinshi nayi miki abinda mata basa so,na sani ban kyuata ba ki yafe mini.ta kasa tare hawayen idanta,dole ta bar su su zuba.ta ce, ba ka mini laifi ba ni.ya dago fuskarshi yana share mata hawaye.yi hakuri, Allah yayi miki albarka.ina alfahari da ke.kin ga khalil na kallo mu kada ya zata dukanki nayi.ta mike tsaye ina maka murna cikar burinka,Allah bada zaman lafia.ta dauki ummita zo mu je kuye wa hajjiya saida safe.. Ya ce, wanka zan yi, kuma zan so ne ki min.ta dubi fuskarshi,ina zuwa. zamanta tayi suna hira da su hajiya,ya gaji ya tashi ya shiga wanka har ya fito yana cikin sa turare ta shigo.wani shegen yadi yasa fari tas tas,mai laush da tsada.sai kamshi yake.ya dube ta ta ce,kayi kyua.sallamar su muktar ce ta hana shi magana.ya dubi ikilima,to ga su nan za su min rakiya,ko za ki zo muje? A a saida safe. Allah ya kai mu. ya fada yana mata murmushi,sannan ya fita.ta kulle kofarta ta key,ta tsaya tsakiyar daki rike da haba,Oh ikon Allah!ta isa gado ta kwanta,ta lumshe idon tana asu,o i,ganin baccin yaki ta mike ta dauro alwala ta tada sallah,sai taji duk wasu lamuran duniya ta zubar su tunda ga ta gaban ubangejinta.ta yi kusan raka,a takwas kafin ta soma karatun qurani.sai guri uku da rabi bacci ya soma zuwa mata,don haka ta kwanta,sallar asubahi ne ya tashe ta,da ta idar ta nufi kichin don hada abin kari ta da wuri saboda baki.Turus tayi ganin yan komatsanta a gefe, taje ta kwashe ta kai dakin yaranta tunda ba su soma kwana ba, ta kunna risho ta shiga aikinta.su kuwa ango da yaga su sulaiman za su dauko doguwar hira sai ya ce su kama kansu,kawaye ma suna gefen baki,nan suka yi musu nasiha sannan ya raka su.Sun ci kazar su mai dadi da madara mai sanyi, ya duba text din da ikilimata turo mashi, cewa kada ya manta da sallar ma,aurata.Ya dube ta ya ce,muje muye alwala ta ce ni nayi sallah.ya ce, na sani. ta kashingida.to kuma ta mai zamuyi. Ta godiya da Allah da neman zaman lafiya,ta taba baki.har yayo alwala ya fito tana zaune can dai ta mike tana tsaki da mitar cewa ita duk ta gaji.suna idar da sallah ya dafa kanta ya yi mata adu,a sannan aka bude shafin soyayya.magungunan mata data dirka sun riketa shi,don haka bai san budurwa ba ce ko ba ita ba ce,illa dai kusan kwana yayi yana bata sako,wannan ya ja musu makara sai a daki yayi sallah bayan yayi wanka.lokacin da suka fita kusan goma saura,kawaye da yen uwanta duk sun shirya suna jiran fitowar su shi ne suyisallama,ikilima ta gama abin kari ta wadata kowa ya koshi,tayi wanka tasa dayan zanin na gurin babanta,ta dauki littafinta muwadda ta zagaya bayan dakinta tasa kujera tana dubawa.sai dai kun san kishin ranta sai zafi yake,ta ji har mahmood din ta tsana,kuma bata son kowa ya dame ta yana fitowa dakinta ya shiga,ba kowa. ya nufi gurin su hajjiya zaton shi tana can, suka gaisa bai ganta ba,khalil yazo ya gaishe shi ya ce khalil ina mamarka? khalil ya ce ta na dakinta.mohmood ya ce a a bata nan.ya mike ya koma dakin bata nan, ya kira wayarta dama ta kashe,duk ya firgice ya soma zaga gidan.khalil ne sai can ya tuna da gurin da take karatu,ya ce abba na san inada take karatu.ya rike mishi hannu sai ko ga su.ya jingina da bango yana kallon yanda ta tsura ma takardar idanu yasan ba karatu take ba tunani ne kawai.khalil ne ta ji ya kwanta a bayanta. Firgigit! tayi,sannan ta ji kamshshin turarenshi,nan take ta daure fuska tamkar bata taba dariya ba.ta kuma ki kallon inda take zaton yakr ta kai hannu da dafa khalil tare da cewa.ba na ce kaye wasa da ummita ba?bana son a damai ni karatu zanyi.ni da abbana ne.ta dan bude murya sama kadan.na ce karatu zan yi ko?oya koma gurin su hajiyakaye wasa da ummita.ta sake maida kanta ga littafintatamar tana karatu.ya iso ya tsugunna kusa da ita yayin da yake kokarin yi mata tattausan murmushi da yake zaton zai sanyaya mata zuciya. Barka da safiya ranki ya dade,ba tare da ta dube shi ba tace mishi.an tashi lafia breakfast dinku na kichin dinku too kalle ni mana.ya ce da ita.yi hakuri ina karatu ne,ta fada a tausashe.wayar shi ta soma ruri,yana dubawa yaga ashe amarya ce.daga inda take zaune tana jin muryarta,ta ce beby ka zo sun gama shirrin tafiya.ya ce, ina zuwa my.sai kuma yaye shiru don ya tuno a gaban wanda yake.abin ya kunnata,ta sake hade rai.yayi shiru sannan ya mike.ina zuwa,ya ce, ba sai ka dawo ba,ina bukatar kadaici ne.ya kara yin zuru yana dubanta,sannan ya wuce.ta rufe littafi tare da dora kanta bisa gwiwoyinta,gaskiya kishi ciwo ne.ta furta hakan a fili.lokacin da yaje yan uwanta suka ce,ta ina ne dakin mahaifiyar shi mu kaita.ya nuna musu lokacin su hajjiya uwa sunzo,bayan sun gaisa,sai suka ce ga fa yarinya amana,in tayi ba ga daidai ba a kwaba mata.hajiya ta ce,to.su uwa wannan aikin ku ne,in dai ba a nan nake ba,hajjiya uwa suka ce insha Allahu,Allah dai ya basu zaman lafiya.Hajjiya uwa ta ce,ku kai ta gurin abokiya zaman tata ku dan musu nasiha.mahaifiya shi ta ce kuma kuyi wa yarku nasiha sosai,mun san halin uwargidanta akaw kawaici. Suka ji haushi,wata cikin su tace too muma tamu batada matsala.suka mike fuu,ba su samu ikilima a daki ba, ya ce su zo gata nan.har sun ce a a ya kai ta da kan shi ya hada su, sai ya ce su dai kaita din. ganin su ta fadada fara,a tare da sakin fuska,ta ce su je dakin mana suka ce a a sauri suke yi daman dai su kawota gata nan amana a zauna lafiya,ta ce ba komai.suka ce mun wuce,ta biyo su tana musu adu,a Allah ya sauke su lafiya.ta nufi girki rana a inda tasa kayan girkinta.ya shiga gurin amarya ta ce,mai zaka basu zasu tafi?ya dube ta ba ni da kudi,dubu bakwai ne dani kuma kinga gobe ko jibi da asubahi zan tafi,dole ne na bar muku wani abu.Ta hada rai,yanzu don Allah shi kenan kuma yan uwa nawa suzo su tafi hannu rabbana?gaskiya wannan abun kunya ne. ya ce,ashura ba ni da kudi kin sani.dubu hamsin na dauki hayar motocin da dangin ki suka zo zuwa da dawowakwana daya,ban da motar kaya.ta ce, in dai ba zaka ba su ba shi kenan kawai.ya ciro kudin to ga dubu uku ta zaro ido dubu uku?bar su gaskiya.su raba nawa nawa? Ya ce,to ga hudu,nima mamana an jima zata tafi.ta amsa rai bace ta bi su ba tare da mishi godiya ba.ya nufi dakin ikilima,bata ciki.ha hangi khalil kofar dakin da yake matsayin nasu,ya nufe shi sai ya hange ta ciki tana yanka albasa,ya nufi ta da mamaki.me ki keyi a nan?ta ce.girki.ya ce.kichin din fa?ta ce, bazai ishe muba, kayan ta sun cika,yayi shiru,sannan ya nufi kichin din da kyua da tsaruwa da kichin din yayi bai ga amfanin shi ba,matsawar ikilima ba zata amfana da shi ba.ya dawo gurinta,ya ce ki koma kichin kiyi amfani da kayanta.ta dube shi da murmushi ai ba zai yiwu ba gaskiya,ba haka ake yi ba.ka barni kawai na dinga yin nawa anan.ya ce,sam gidanki fa kichin dinki ne in har ba ke ce za ki yi amfani da shi ba gara ba a gina shi ba.ya soma diban kayan yana maida su kichin ya kwashe wasu kayan ashura ya tara mata su gefe yasa na ikilima dole ta koma kichin.bayan ashura su hajjiya uwa da maman shi suka soma shiri tafiya.lokacinne suka shiga ganindakin amarya,gado ne dan italiya kujerun leda,ta kai su dakin shi hajjiya hajjiya ta ce nan ba dakin shi ba ne?ashura ta ce,eh, ai gadon shi ne.hajjiya tace,to ai ba zaya yiwu ba kuma kisa kayanki a turaka shi ne zai siyo yasa tunda ba ke kadai ba ce. Ashura taye turus,hajjiya ta dubi mahamood.lalle a cire kayan nan.ya ce mata too. dubu uku yabata ta ce a a ita tana da kudin motarta,ya ce shi dai ta karba ta amsa sannan ta hada ashura da ikilima ta musu masiha.ta kuma ja wa ashura kunne kan dole ne tabi ikilima.ashura fa an kaita bango,don haka suna tafiya ta shiga daki tana ta rusa kuka.da ya shiga ta ce,ita de zata tafi gida don baya sonta danginshi basa sonta.ya rungumaita ta wa ya ce bana sonki? yayi ta lalashinta da kyar tayi shiru.da dare ikilima taye abinci tasa tasa musu shi ne yakai musushi da amarya.ta kalli abincin ta yatsina baki,wai ita ba zata iya cin wannan abincin ba.kuma yiunwa take ji.ya ce, to me za ta ci?ta ce indomie .shi da kanshi ya shiga kichin yana dafa mata.ikilima ta shiga kwanukan da suka ci da yarantata ganshi,bai so ba ta ce Ah,ba ku koshi bane ?ya ce, a a ita ce dai take sonci wai bata son cin shinkafa.ta tsura mishi ido,sannan ta ce,hummm!ta nufi dakinta. Ya ce,don wahala? ki barsu a gida gamu.ashura ta ce,ni fa ba zan zauna ba, mu dan fita mana naga yanayin garin naku.ya ce, to.ikilima ta koma dakinta ta dauko jaka da nikab ta goya umminta tana daura nikab suka sake fitowa,ta yafo wani dan gyale sai kace na yan yara.yazo kusa da ikilima.ranki ya dade,ina makullen gidan?ta dauko mishi yasa hanu ya zaro ummita daga bayanta.zo muje mamana.ta ce, da ka barta baban khalil,kada ta bata muku gayunku.ya dubai ta sai kuma yaji nauyin yi mata magana.wane bata gayu? ya dube ta kina da kudin mota ne,don wallahi in zan tafi ma ban san ina zan samu na mota ba,na yi kaf. Ta ce, ina da shi,sai na dawo.ta maida zanin goyon ta rufe dakinta.ko yau a makaranta bata da nutsuwa,tana dai yin adu,a saukin ta ma kenan yau ma malaminsu sai da ya sake yi mata nasiha dan ya lura bata maida kai sosai kamar da.da suka fito juwairiya ta ce, ki nutsu ikilima,ke yarinya ce kada ki jawo ma kanki hawan jini da kuruciyarki.ranar bikin nan yan makaranta suna ta yabon ki,don Allah ki nutsu.ta ce, humm,kishi da zafi juwaira,yanda yake zumudi kanta da yanda yake rawar kai ke ban tsoro.yau fa shi daya suka fito sannan ta ce su fita taga gari,ko musu yace too.jawaira ta ce,ki dauke hankalinki,ki kama girmanki duk da naga wannan ta girme ki amma ki rike girman ki don Allah ya dora miki.shawarata da ke kenan,kin san ita amarya ko ta buzuzu ce sai an yi dokinta.ita da shi duk ki cire su gabanki. Ikilima ta ce,too juwaira,na gode,ni ma da kishi ne matsalata,sai dai ina ta yin adu,a.juwaira ta ce,shi ne kawai zakiyi.sanda ta koma gida a waje ta same su shi da yarann suka mata oyoyo,ta daga khalil ta sauke sannan ta daga ummita. sannu da zuwa mallama.ta daga nikab sannu,har kun dawo? ya ce, ehh, tuni.suka nufi kichin, amma ashura tana daki kwance tana bacci.haka da dare ta ki cin abinci yau ma,washegari yayi shiri da wuri,ya shigo dakin ikilima tana karatun ku,ani ya zauna gefe gadonta,ta kai aya sannan ta gaishe shi.ta tsuguna yayi kissing din yaran,ya ce zan tafi don Allah ki ta hakuri kin ji,sannan ba kudi gurina ko zan sami dubu biyu gurinki?ta tashi ta bude zif din jakarta,ta ciro dubu biyu kudin da ya ba hajiya shi ne zata tafi ta bata,ta ce , ga dubu biyu. ya kalle ta kina da wasu don yan matsalolin gida da zuwanki makaranta?ta ce,Allah zaya rufa asiri.ya ce amin. ta bashi ta na cewa,ka dauki komai ko?ya ce,ashura ta hada.ta ce, to Allah tsare, ka sauka lafiya.Ashura na tsaye kofarta sanye da kayan bacci ta mika mishi jakar ta ce beby sai mun yi waya.ya dubi ikilima sannan ya ce to don Alllah kuye hakuri da juna.ashura taye cikin dakinta,ikilima ta rakashi har waje,ya tafi yana mata byy.tun tafiyar shi ashura bata fito ba,koda ikilima tagama abin karin kumallo har daki ta bita ta buga ta bude,sannan ta ce lafiya?cikin wata yatsinar fuska,ikilima ta daure fuska don bata son raini.break fast dinkine.daina sa abincinki da ni,ni na ji ci zam fito in yi nawa.inji ashura.ikilima ta ce ok.ta juya ta tafi.tsaki taja ta maida kofar,tana jin haushin ikilimar nan don ta kula mahamood na ganin darajanta.don ta tuna yau da asuba ya tashe ta wai ta hada mishi kaya ta ce ya bar ta tagaji,wato bari ya je ikilima ta hada mishi,shi ne ta tashi da sauri tana hadawa.ta lura ikilima taga shgwaba shi ne,komai sai ya ce yi min kaza ita kam gaskiya ta gaji kamar dole?Shi kuwa daman daga nan office ya wuce,sai da ya taso sannan ya nufi gida,ranar ne fa ya fara gane ashura daban ce,da ya bude jakarshi kayan ba gyara,duk a hargitse wani ma riga ce babu wando babu neck tie kayan shafanshi su mai zuwa turare duk babu sai makilin ta saka babu brosh. Ya rike kai,dan canjin hanunshi shi ne ya je ya siyo duj abin da babu,don haka zakuwar shi yana tunanin bai ga ta zuwa gida wannan satin ba dole sai sati na sama,lokacin wata ya kare.ya dan samu wani abu.Sai da ya kwanta ya dauki waya sai ya soma tunanin waya zai soma kira?duk da ashura sau biyu tana kiran shi yana office ya ce mata ta bari zai kira text din ikilima ne ya shigo,a in da take cewa da shi.ango nasan yanzu kana nutsu,ina fatan kana cikin kwanciyar hankali.ni da yara munyi kewarka,kayi bacci lafiya.da yagama karantawa,sai ya yi murmushi a fili ya ce,ikilima yar aljannan ce.ya soma rubuta, Nima ina cikin kewarki yar aljannan,ba zan iya manta karamcinki ba. Zuciyata tana girmama ki tare da jin nauyi ki.gangan jiki tana jimain rashinki kusa,sakonnina sun rasa masaukin su na asali.Ina fata za,a share duk wani tsohon sako na da kafin na dawo.sai dai ina ga za ki ci gaba da hakuri tare da rike gidan na har zuwa sati na sama,don ke ce halifata in bana nan,saboda matsalar kudi zan bari sai karshen wata.i Ikilima tayi yar dariya bayan ta gama karantawa,sannan ta rubuta kada ka damu,zan lura da gidanka da dukiyarka har da masoyiyarka,ina nufin amaryarka.sai dai kada ka manta ita masoyeyarka ce zata ci gaba da karban sakoninka har zuwa lokacin da zata cinye kwanakin amarcinta,wato kwana bakwai. kayi kwana biyu kafin ka tafi in ka dawo kayi biyu,in ka muma dawowa haka in ka sake dawowa ne zaka yi daya.too sai dai zan yi maka aibishir dama lokacin aurenka ban baka gudumawa ba.A matsayina na ta hanun hagunka na yarda kayi ta sauka dakin amaryarka duk lokacin da ka dawo har zuwa lokacin da zaka ji da kanka cewa ka gamsu da gudumawata.Yana gama karantawa ya hade rai kamar tana kusa dashi,ya kira layinta.ta daga ya ce,ke in ji wa ya ce miki zan yarda da wannan shirmen naki?to bana son gudumawar,kina cewa kece ta hannun hagu karna sake ji.ikilima ta ce asalin kashin hakarkarin,sannan duk wandda zan so,sonta yana bayan naki ne,ta ce,to Allah ya baka hakuri,amma mu da aka yi auran hadi ba shiri fa in ka tuna yanzu ko so ya hada........... ya katse ta da tsawa,wai ba na ce ki min shiru ba ne?ta ce,too na yi me sona,na ji kana sona kayi hakuri.ya kashe sannan ya share sakonta na karshe. Ya kira kayin ashura ta daga cikin sigar shgwaba ta ce,beby sai yanzu zaka kira ni don Allah.ba sai na fada miki ba,kin dai san yanayin aikinmu. na sani, amma yanzu nasan kana kwance ne kawai,ya ce, ehh, kanwata na kira tukunna.tayi tsaki to ina ruwana da wata kanwarka?ni kaina na sani.niko kinga inada ruwa harda tsaki da ita.taja tsaki aje wannan topic din,kayi missing dina?ya ce a lots ma kuwa.ta ce,nima haka .ji nake kamar na janyo week end wallahi.Gashi sai na sama in mun samu wani abu sannan na dawo,yanzu ba kudi.ta ce, cikin shgwaba,haba bebyna,gaskiya ka sama min aiki a nan kadunan ba zan jure rashinka kusa ba.ya ce, a a bamu yi cewa kaduna ba.ta ce, to ina dai maka tuni da kayana da aka diba gidanka in kasamu kudi kasan shagon kuma kasan kudinsu.gaskiya ba yanzu ba,ina da al,amura sama da wannan sai na gama su.sai da safe.ya kashe wayarsa nan take ta kira mahaifiyarta suna gaisuwa ta ce, hajiya mahmood za su yi albashi,ki ce masa ya sai min kayana,ni na mishi magana wai ba yanzu ba,ta ce,too zan masa. Shi kuwa kwanciya yayi yana so ya daidata halin ikilima da ashura sai yaga sam ba za su hadu ba ma.zuciyarshi ta ce,zabin Allah bashi da mahadi,ikilima daban ce.haka suka ci gaba da zama ashura ko ummita ta rarrafo ta taba mata kofa da tsawa take koranta,bare khalil.duk ikilima kauda kanta tayi,alwashi ta sha ba za ta taba kula ashura suyi sa in sa ba,nata ganin in haka ta faru ta ci baya,girmanta kuwa zai fadi.amma in ta kame kanta dole ne ashura take shakkarta.Da ranar da zaya zo tazo tun safe ikilima ta shiga gidan makociyarta lubabatu yar birnin kebbi ce,mijin ta ma,akaci ne a abuja yake aiki,sun fi sabawa da ikilima ta ce, luba don Allah bani aron a,i me aikinki ta siyo min kayan kosilo.luba ta ce,ina da su bari na dibar miki.ikilima tace,ko dai bari ki satar mini?luba ta ce, sata kuma? ikilima ta ce,too ai kyauta da kayan miji baya nan sata ne,in bai sani ba.har sai in kin nemi izininshi sannan zaki bada.luba ta ce, to shikenan na daina.a,i zo ki siyo mata.yau baban khalil na hanya kenan?wallahi, na rasa ma kalar jus din da zan masa?ki masa na shinkafa mana.inji luba.ban iya ba.inji ikilima too kuna da shinkafar tuwo eee muna da ita.luba tace,too jika rabin gwangwani zan shigo. Ikilima ta koma gida ta shiga masa fred rice,ita kuwa ashura dama gidan sakina nan ne gurin zuwanta,ita ma makotansu ne amarya ce daga abuja aka kawo ta,irin yayan masu kudi din nan ne ga salo hali dai yazo daya.kullum in ta shiga gidan sai dare take dawowa.ko sharar dakinta bai dame ta ba bare cikin gidan,ashura daidai kayan girkinta

Chapter 18 of 20