Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi,iklima tace yayana baki muka yi ko na fada maka kayi hakurin dare. Yace kwano ne in ji matar gidannan,nace ta aje miki nan waje.iklima tace wlh ba zanyi kaffara ba tsegumi ne ya kawo ta,ni kana bani kunya fa. Ya zauna kusa da ita bani kunyata to. Tayi dariya Allah in na fita suyi ta kallona.haka yan gidannan suke. Yace ke baki da wayi,tunda suna kallonki sai kiyi alfahari da mijinki yana sonki ko kin fi son in nemi na banza a waje? Ta kwanta a jikinshi kayi hakuri ajizanci ne ke sa ni sonyi maka gaddama. Wajibina ne in amsa gayyatarka cikin kowane hali matsawar bai ci karo da abinda musulunci ya haramta ba kamar misalin haila ko biki. Yayi dariya,ya malam kenan shi yasa kullum kike kara shiga raina,nagode Allah da ya ban ke. Da dare ya shigo da waya cikin kwali tana kallon labarai ya zauna tace yayana kashe-kashe ua soma yuawa a kasarmu dubi yanda wai aka shiga gidan wannan mutumin aka yi masa yankan rago. Yace na gani dazun a gidan mukhtar in dai mai kisan yayi hakuri da wanda zaya kashe ma ya mutu tunda ko ba su yanka shi ba ba zaya wuce ranar ba. Tace hake ne Allah ya saka masa. Ya dube ta,bani goron albishir yanzunnan. Tace me kake so? Yace sumba daya mai kyau. Ta san yanda yake nufi dan haka ta zura harshenta cikin bakinshi. Ta zauna tana dariya ganin yanda jikinshi yayi laushi. Ya dora mata wayar bude ki gani, ganin wayan tayi tsalle ta fada jikinshi. Yace ke kada ki zubar min da dan yarona fa, baiyi kwari ba. Sukayi dariya, ya koya mata. Washegari suka nufi ziyara bayan sun dauki wankan shadda iri daya, sai dai tashi ta dan fi tata duhu kalar makuba, hijabinta yau bai kai can kasa ba, da tace ita bazata sa. Shi kuma ya ce ai ya rufe jikinki. Bata daura nikabi, yace yanzu haka zamu fita yau sallah ki hakura da nikabin nan mana. Tace a'a fuskata da adona kai daya ke da ikon gani sai wadanda Ubangiji ya amince wa, wato muharramaina. Bai ce komai ba suka fito, su maman ummi suna raba abinci lokacin da ta fito shi yayi waje ita kuma ta nufi gurinsu dan yi musu sallam suka ce ga abinci tace Allah ya amfana zamu fita ne. Ya tada mashin ta dafa shi ta hau yace kyan shi ace yanda kika yi kyau dinnan gyalenki kika yafa yafa kalar jakar ki da takalminki, da sai kinfi bada ma'ana. Tayi dim domin duk lokacin da yayi furuci mai kamar wannan sai ranta ya sosu. Sai da suka dauki hanya sannan tace baban khalil ban san me yasa ba, sam baka kishina. Yace bana kishinki fa kika ce? Kin san me kike fada kuwa? Tace nagani ne maza da yawa suna son suga matayensu suna irin shigar da nake yi, amma basu samu ba, kai kuma shigar tawa bata birge ka. Yace ra'ayina ne kawai ba wai kishinki ne banayi ba, ki daina fada min haka. Tace Allah ya baka hakuri. Suka tsaya a kofar gidan suka shiga, duk yaran gidan sun tafi yawon sallah, suka shiga dakin hajiya uwa. Tace alhaji na nan cikin dakinsa. Suka shiga suka gaishe shi cikin jin dadi da fara'a ya amsa tare da cewa khalil yana kontagora ko? Suka ce eh, ya shi musu albarka, ta mike ta fita dakin hajiya rabi ta shiga suka gaisa sannan ta koma dakin hajiya uwa. Sun dan jima ya fito shi da alhaji ya miko dari biyar gurin hajiya uwa yana cewa gashi a bata ta aje ma khalil goron sallar shi. Ikilima tace dama ya barshi, tunda baya nan. Hajiya uwa ta ciro kudi a gefen kujerarta naira dari ce tace duk da ya gudu dan kada ya bamu goron sallah, gashi ba dinkin sallah nima ga nawa. Ta hada ta ba ikilima suna dariya dukansu. Tace angode Allah ya maimata mana. Rabi ma ta miko nata tana cewa mara cefane ne ba. Suka fita suna dariya. Alhaji ya ce kada ka manta ku bi ta gidan alhaji jinjiri da alhaji ado tunda sallah ce zaka same su gida suna yawan tambayarka. Yace to zamu biya. Abokin alhajin ne duk basu da nisa suka shiga suka gaisa yayi musu ihsani, suma sun bada goron sallar khalil, yace yanzun can gidan zan kai ki? Tace eh, da dare sai kazo mu tafi. Yace a'a biyar zaki dawo don ni ba zan samu zuwa bama. Tace kai dan Allah, ba ka ganin bani da lafiya? Yace in dai biyar tayi banzo ba ki dawo, tace shikenan. Gobe sai naje mu wuni masu baba. Yace eh, bayan ta sauka yayi parking mashin din suka shiga. Nafisa ce kwance a palo tana amsa waya, bata san ma su waye ke sallama ba, ta dai amsa. Suka zauna. Ko yaushe ikilima tazo gidan tamkar bakuwa takeyi, ta kasa sabawa. Nafisa tace, duba anty hajara ni na gaju kawai ba zan dawo ba nake ganin sai dai in debe kayana, sa san shi fa wari yake yi dan masifa koyaushe sai na dau G na roban nan na tuttura muishu ni kuma ya tilasta ni sai na kwanta ya min, ga wari har fa da tsutsa wani sa'in ni bazan iya ba. Hajara tace ai kinyi kokari ma in nice bazan yarda ka rabeni kana wari ba. Ta tashi zaune tace kinji dalilin dawowata. Abn duniya ya isheni. Ta sauke idanunta kan mahmud wanda idanun shi ke kallon TV kuma yana sauraron duk abn da take fada. Sai dai bai fahimci me kalaman nata ke nufi ba, wayar hannunta ta subuce ta fadi kan kujera, abubuwan da suka faru cikin hotel din suka dinga kai kawo cikin zuciyarta. Ikilima ta katse ta da cewa yaya nafisa mama fa? Cikin in-ina tace tana...tana kicin. Ta mike tare da kallonshi. Yaya bari na kira ta ku gaisa. Yace to tare da kallon agogo. Kiyi sauri dan zamu fita dasu muktar ne. Tana fita nafisa tace don Allah mahmud ka yafe min, wallahi alhakinka dana babanmu sai bina yake yi, na cuce ka da yawa. Baiko kalle ta ba, don shi gidan bakikirin yake kallonshi. Ikilima tana shigowa nafisa tayi shiru, mama ta fito suka gaisa. Yayi mamakin sakin fuskar maman har da ce mishi ina khalil? Har da godiyar abincin sallar da aka kawo mata daga wajen shi. Bayan ta fita ne ikilima ta raka shi har gurin mashin dinsa saidai sam babu walwala cikin fuskanshi, shi kuwa sharrin data masa ne har gaban alkali ke cizonshi. Ikilima ta ce habba baban khalil, sai inga kana daure fuskan ka in kazo nan gdan. Dan grman Allah ka yafe musu. Yabuga mashin dinsa batare da yayi magana ba. Ta tsura masa ido har saida ya bace sannan tako ma gda. Kuka sosai tasamu nafisa tanayi haule tana tsaye kanta tana fada. Kin soma kular dani kan batun yaronnan. Shin mai yafi sauran maza zaki damai ni da cewa kin cuci kanki kina sonshi maisa kika ki shi? Nafisa ta ce mama ke kika zugani ke kika kasheni da kanki. Ta dubi nafisa sha sha sha to da kin aure shin wannan gdan da yanxu muna cikinsa? Koko daular dakike ciki da yanxu kina cikinta?. Nafisa tasake fashewa da sabon kuka tace kazamar daula, daular da bata Allah da Annabi ba dana aureshi da ban hadu da ciwon zamani ba, ban zama yar maye ba..... Kuka yafi karfinta maganar ta doki zuka tan haule da ikilima, a tare sukace yar maye? Wanne ciwo kike dauke da shi? Nafisa bata tanka ba saida tayi kuka mai isarta, ikilima ta cire hijab ta a jiye hannunta yana rike da hankacif saboda zubar da miyau. Haule ta katse shirun da cewa nafisa ina tambayarki wanne irin ciwo kike dauke da shi? Ikilima ta matso kusa da ita yaya nafisa dan Allah ki daina wannan kukan ni na auri mahmud ne don fitar da baba da kuma ke daga zagin da jama'a zasu yi muku sannan kuma in shirya barakar dake tsakanin baban mu da maman mu. Ban da kina da aure zan iya neman mijina ya sahale min ya aure ki... Ta daga ido ta kalle ikilima da sauri cikin wani sabon kuku ta rike hanunta gam. Na sani yar uwata kina s tuntuni nice dai ba...bakiyi da ce da yaya ba inaso...so ina so ki sani ko banida aure mahmud yayi mini nisa bazai saurare ni ba dan na cutar dashi kuma na cuci kaina ikilima tace zan tursasashi sai ya yafe miki,tayi saurin katseta babu tursasawa a yafiya. Ta mike ta soma kai kawo a tsakar falon. Bazanga laifin mahmud ba dan yace bazai yafemin ba. Ya taba baki lbrin ni ce na hadashi da yan sanda har kotu? Ta fashe da kuka kafun ta tsahirta ta ci gaba nice na bada kudi aka sama shagonsa wuta, dan kawai na jefashi cikin kunci. Ikilima ta zaro ido tana kallon nafisa, batakuma san lokacin da bakinta yana tambayar saboda mai? Bata dubi ikilima ba saboda soshi. Haule tace dama nafisa kece hajiyar da'akazo ana lbr? Bata amsawa haule ba taci gba da kallon iklima bansan ina son mahmud ba sai lokacin da'aka kaini gidan alh jamilu yadda naga rana haka na raya daran da kuka. Randa alh jamilu ya shgo dakina ranar na soma nadamar auransa domin ranar nasan cewa shi dan luwadi ne na aura... Numfashin iklima yakusa daukewa dakyar ta janyoshi sannan tace ludu? Nafisa ta kwashe komai ta sanar dasu sannan tace sakamakon kwadayi yau gani da ciwon kanjamau. Haule sai da ta zube kasa, iklima kuwa kuka ta saka haule tace amma nafisa Allah ya isa naturaki zina ko aure? Nafisa ta dubeta duka kika turani domin ke bakida burin da ya wuce kudi, gurinki na san kwadayi. Ta dubi ikilima wadda ke fatan ace duk wadannan abubuwan cikin mafarki ne, cikin raunanniyar mury tace kin tuna ikilima lokacin da mama take ce mana muna da kyau kada mu saurari takaka? Kin tuna lokacin da ta ke ce mana babban gda babbar mota? Lokacin kika ki sauraronta nice na biye ma zuciya da kwadayin duniya. To yau gani cin nadama mama kin cucen kinci amanata, kin zalunceni kin turani ga hakaka... Tasake fashewa da kuka haule ta mike tana cewa kin dai cuci kanki nace kiyi zina? Ki tattara ki koma dakin mijinki ni banzauna da mai kanjamau ba. Ikilima cikin matukar sanyi jiki tace yaya nafisa gaskiya kin tafka babban kuskure ki soma neman gafarar Allah hakika kin gafala da yawa. Nafisa ta matso kusa da ita tace ta ina zan fara yar'uwa ta? Wlh har sallah nadaina yi, bazan tuna ranar danayi sallah ta karshe ba. Wa'iya zubillah iji iklima. Iklima zufa ya shiga tsatstsafo mata daga dukkan wata kofa ta jikinta, kinyi kuskure babba banyi mamakin laifukan dakika aikata ba, domin duk wanda ke barin sallah daga lokacin tama Allah ya fada azaba ta tabbata gareshi , bare wanda ya barta. BOOK MABUDIN WAHALA 3**4 Ikilima ta taba nafisa tare da rada mata cewa ta gaishe shi, sannan ta soma neman gafarar shi. Koda tace baba ina kwana? Bai tanka ba, tace dama nazo ne ince ka yafe ni, wallahi na gane kuskuren da nayi. Ya girgiza kai, baki gane kuskuranki ba tukunna, lokacin bai yi ba da saura. Haule tace don Allah malam kayi mana aikin gafara. Ya dubeta "ni bansan laifin da kuka min ba. Mahmud yasa baki da cewa baba ba kai ba, ko mu mun san laifin da tayi maka, ta gane kurenta dan Allah ka yafe mata taji da lalurar da ta ke tare da ita. Mal usman ya gyara zama , to inda wanda aka cuta aka zalunta ai kai ne, don haka kai zata roka. Mahmud yace baba ai tuni na yafe mata kafin tazo. Domin in na ci gaba da fushi ban gode ma wannan baiwar da Allah yayi min ba. Ya fadi haka yana nuna ikilima, sannan ya cigaba da magana. Canjin da Allah yayi min ya bani ikilima baiwa ce don haka ka yafe su baba. Yace mahmud basu dauki darasi ba tukunna, ko na yafe musu in dai wannan mai kwadayin ce..." Ya nuna haule, da wannan magajiyar tata sai sun yi wanda yafi na yanzu. Ikilima tace wallahi baba sun dauki darussa. Nan ta shiga baiwa baban labarin mijin da nafisa ta aura da halayan shi da silar dukiyar shi. Ba mal usman ba hatta su danlami sun girgiza da jin batun. Don ma bata shaida mishi irin shagalar da nafisar tayi ba. Nafisa kuka wiwi ta rinka yiwa ikilima godiya sannan haule tace ni dai nafison ta koma gidanta, tunda ance ciwon nan daukarshi ake, ikilima tace ba'a dauka sai ta hanyar haduwar jini ko ta hanyar da ta samo. Nan ne ma akafi saurin dauka. Biyar daidai ya kira wayarta , abnka da sabon shiga tayi ta zumudin dauka, yace ki taho ina jiranki zan baki sako. Tace zan taho amma maganar message sai a hankali, don ina cikin wani hali. Gani nan zuwa yanzunnan. Ta soma shiri, hauke tace ki zuba abnci kici mana tunda kika zo baki ci komai ba, amma mama dan Allah kada ki nuna mata tsana. Taski haule tayi tare da cewa, bar ni inji da kaina. Tunda ta shiga daki take aikin kuka, ko a mafarki bata taba zaton irin wannan kwamacalar zata faru cikin zuri'arsu ba. Ciwon kanjamau da suke jin labarin shi can nesa har ya matso kusa yazo gidansu kuma a dakinsu. Mahmud ya shigo duk da yazo da uzurinshi amma halin da ya same ta aciki ya shafe nashi uzurin, nan ya rungumeta yana son jin damuwarta. Dolen ta ta fada ko dan halarcin yayi mata, inda wani ne yayarta tayi sanadin zuwanshi hannun hukuma yaci duka kan ta zai zo ya sauke. Amma shi bai ko fada mata ba, in ma tana son lamuran su warware dole sau yaji. Tace mahmud. Ya dube ta da sauri don bai taba jin sunan daga bakinta ba. Ta katse mishi tunani da cewa dama yaya nafisa ce tayi sanadin kai ka gurin hukuma? Yace inji wa? Tace in jita, nan ta shiga zayyano mishi duk yanda lamuran suka faru, daga karshe tace yanzun haka tana dauke da ciwon kanjamau... Maganar ta tsorata shi, lallai wannan abn jaje ne. Ikilima tace yaya nafisa taki amince wa ne kawai tun farko na sanar da ita duk wanda yace shi ba zai tsaya inda Allah ya ajiye shi ba, karshen shi nadama. Don Allah baban khalil ka yafe mata. Allah yana yafewa bayinsa masu yafiya. Shiru kawai yayi yana tuna artabunsu a hotel, da yabi son zuciyarshi da yanzu yana dauke da ciwon shima. A fili yace Allah na gode maka da ka kare ni, ya dubi ikilima ni tuni na yafe mata. Allah zata roka sai ko mahaifinta. Ikilima tace baban khalil ina rokon wani arziki, yace na me? Tace kai zaka jagorance mu zuwa gurin babanmu, don ta nemi gafara. Yayi shiru tace don Allah. Ya dube ta yaushe? Tace da safa. Ya dan rausayra da kai ba tare da yace komai ba. Har garin Allah ya waye ikilima bata iya bacci ba, juyi kawai take yi. Abubuwan suna zuwa mata tamkar cikin mafarki. Da safe yana kwance ta gama duk shirye shiryenta sannan shima yayi wanka suka tafi lokacin da suka iso gidan haule tana zaune a falo cikin tagumi ta daga ido tana kallon ikilima. Cikin sanyin jiki tace lafiya da sassafe? Ikiilma tace lafiya lau, daidai nan mahmud yayi sallam ya shigo. Tace a'a tare kuke? Ta sunkuyar da kai tanai musu sannu da zuwa. Yau ce rana ta farko da hauke ta soma jin nauyin mahmud. Suka gaida ta, ikilima tace una yaya nafisan ne? Ta nuna dakin da nafisan kan sauka in tazo. Tana nan ciki. Ikilima ta shiga, haule ya dube shi, baka zauna ba ka zauna mana, ya zauna tace don Allah duk naji abnda ya faru gurin nafisa, dan Allah ina neman gafararka ka yafe mu. Mahmud ya dube ta tamkar zata zubda hawaye yace bakomau mama, ya wuce. Tace nagode. Daidai nan suka fito. Nafisa zubewa tayi gwiwa biyu tana rusa kuka tare da neman gafararshi. Yace ya wuce in dai nine na yafe miki. Ikilima tace mama zamu je ne da ita gurin baba don neman gafararshi. Mahmud yace kamata yayi ace har maman za aje don an fa bata mishi rai ba kadan ba. Haule ta mike bari muje din. Ya buga mashin yayi gaba. Tsaye suka same shi kofar gidan shi da nafiu, su kuma sunci karo da danlami da aminu, don haka tare suka dunguma. Yau ce rana ta farko da nafisa da haule zasu shiga gidan. Yana shan shayin da matarsa Hama ta hada masa, ita kuma tana ninke kayan nafiu suna 'yar hirarsu cikin nishadi, sai sukaji sallama. Ikilma ce a gaba tace a'a haj ikilima ce da sassafe? Tace mu ne mama, koda malam usman ya daga ido ya sauke su kan nafisa sai ya kware. Kwaruwa mai tsanani har sai da mahmud da danlami suka rike shi, ya dan lafa sannan ya nuna nafisa yace wannan ta fita daga gidana, bata cikin ahalina. Nafisa ta soma kuka mahmud yace yi hakuri baba, ka dubi girman Allah ka saurare mu. Ya kalli mahmud tamkar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Hama ta shimfida musu tabarmi suka zauna, hama dai tsakar gida ta fita ta kama 'yan aikace aikacen ta. Ikilima ta taba nafisa tare da rada mata cewa ta gaishe shi, sannan ta soma neman gafarar shi. Koda tace baba ina kwana? Bai tanka ba, tace dama nazo ne ince ka yafe ni, wallahi na gane kuskuren da nayi. Ya girgiza kai, baki gane kuskuranki ba tukunna, lokacin bai yi ba da saura. Haule tace don Allah malam kayi mana aikin gafara. Ya dubeta "ni bansan laifin da kuka min ba. Mahmud yasa baki da cewa baba ba kai ba, ko mu mun san laifin da tayi maka, ta gane kurenta dan Allah ka yafe mata taji da lalurar da ta ke tare da ita. Mal usman ya gyara zama , to inda wanda aka cuta aka zalunta ai kai ne, don haka kai zata roka. Mahmud yace baba ai tuni na yafe mata kafin tazo. Domin in na ci gaba da fushi ban gode ma wannan baiwar da Allah yayi min ba. Ya fadi haka yana nuna ikilima, sannan ya cigaba da magana. Canjin da Allah yayi min ya bani ikilima baiwa ce don haka ka yafe su baba. Yace mahmud basu dauki darasi ba tukunna, ko na yafe musu in dai wannan mai kwadayin ce..." Ya nuna haule, da wannan magajiyar tata sai sun yi wanda yafi na yanzu. Ikilima tace wallahi baba sun dauki darussa. Nan ta shiga baiwa baban labarin mijin da nafisa ta aura da halayan shi da silar dukiyar shi. Ba mal usman ba hatta su danlami sun girgiza da jin batun. Don ma bata shaida mishi irin shagalar da nafisar tayi ba. Yayi shiru, Allah ya sani bai kai fasikancin mutumin nan har haka ba, ana shi zaton mutumin ma'aikacin gwamnati ne barawon gwamnati kenan, ashe abn ba haka bane. Yace to yanzu me take so in mata? Ikilima tace yafiya take nema. Yace in yafe mata taje ta cigaba da zama dashi ko in yafe mata ta rabu dashi? Da duk abn da ya mallaka? Duk suka dubi nafisa wadda har dashewa muryarta tayi, saboda kuka tace baba ai na bar shima ba zan sake komawa inda yake ba. Yace to da sharadi guda 2 zuwa 3, na farko sai dai in silai nashi dake gurinki zaki maida mishi, sannan uwarku ta dawo nan ta hakura da kadan da Allah ya bani, don ba zan kuma shiga wannan gidan ba, na karshe kuma taje ta baiwa 'yan uwana hakuri ta nemi gafararsu. Ba tare da dogon zance ba tace na amince baba, zanyi duk yanda kace indai zaka yafe min. Yace na yafe miki, sai ki tattara kazamar dukiyarshi ki maida masa, ko bai nan ki ajiye masa. Danlami yace yaya za'ayi da kantinan da ta bude mana? Mal usman yace duk ta tattara ta maida masa, domin kudi ne ba masu tsarki ba, haramun ne kuma Manzon Rahama (SAW) ya shaida mana duk jikin da ta ginu da haram bazata shiga aljanna ba. Ki kuma zo ki duka neman gafarar mahaliccinki. Haule ta dube shi, mal dan Allah nima ka yafe ni, zan dawo nan din sai dai zanso a raba mana gurin kwana da nafisa don tana dauke da cutar kanjamau.... Da sauri ya kalli nafisa, domin a wannan lokacin ciwon bai yi yawan da za a ce ai wane na dashi wane ma yayi ba, ciwon a wannan lokacin duk me shi zai kasance cikin kyama, tsana da tsoro gurin mutane kuma zai zama abn gori da zuri'arsu , musamman ma in wanda ke gidan miji yasa mata. Yace ya akayi kika san cewa kin da wannan ciwon mai karya garkuwar jiki? Cikin rawar murya tace anyi min gwaji. Yace shi kenan dole kuzo neman gafara tunda kin samo ciwon mutuwa, Allah ya kyauta suka ce amin. Suna fitowa mahmud yace muje gida mu karya kin dawo nan din, su kuma suka nufi can gidann. Nafisa ta dubi mahmud ya dauki iklima sun tafi, ta lumshe ido cikin kunan rai, hakika ta cuci kanta. Haule dai tayi gaba dan ta tattara kayanta, cikin ranta kuwa cewa take ba komai zata bata ba, boye gwala- gwalai zatayi. Isar su gdan sai ga yan sandan ciki nan take sukayi ciki dasu sai abuja, tuhumarsu alh jamilu yake da cin kudinsa tunda tace bata aurenshi, to ta dawo mishi da komai nashi. Washe gari yan sanda suka tasa keyarsu har minna ta kaisu kantunanta, a gda kuwa ko kayan sawa basu bari sun dauka ba sukace shegu alh yace komai shi yake siya muku, kantinanta na abuja kuwa dama tuni yasa an amshe, dole suka dawo gdan ikilima karkashin malam usman din ba komai a tsiyacansu. Sai ma ciwon nafisan ke dauke dashi, iklima ce tasai musu katifu madaidaita, dakyar maganarsu da alh ta mu2 ya bata saki. Haka suka ci gaba da zama, haule ko tsakar gda saidai alwala, abinda yakara sa nafisa nadama, yanda haule ke nuna tsanarta karara. Ko dakinta batason nafisa ta shiga, mamaki ta dingayi. Lokacin baya kadan da ya wuce kafin tasan nafisar tana dauke da ciwon, ji take da i ta tamkar tsoka daya a miya. Duk daular da taci ta manta, wannan damuwar da rashin shan maganainta kusan sune suka taru suka sa mata ciwon kai mai tsanani, wanda sai da hama da babansu sukazo kanta. Sai kuma zawo kafin kwanai duk ta rame, malam usman shine ya nemo wani yaro mai kemis yadan yi mata karin ruwa. Duk iklima batasan halin da'ake ciki ba domin tundaga ranar bata koma ba, ga islamiyya, sallah na wucewa suka koma da zafi zafi. Tagama girki kenan ta shirya khalil zata kaishi gdansu mahmud daga can ta wuce islamiya. Sai ga nafiu, suka gaisa tace yau bakaje makaranta ba? Yace mune fa zamu zana jarabawar j.s.s. Kin manta? Tace au ranar litinin kenan zaku fara? Yace eh, yanxu ma fa jikin yaya nfisa ne bata jin dadi har anyi mata karin ruwa shine naga baki zo ba na ce bari inzo in sanar dake. Cikin Damuwa ta ce, to in na dawo daga makaranta zan biyo, zan kira baban khali a waya in shaidamasa, yace to. Nafiu ya juya ya tafi, duk jikin ikilima yayi sanyi, tana tausayawa yar'uwarta. Suna tashi daga islamiyar ta kirashi, ya daga yana tsaka da aiki, tace zan biya gdan mu in duba yaya nafisa, yace, minti nawa? Kinsan nakusan dawowa, bana son in zo gda bakya nan. Tace awa daya, yace a'a minti talatin, karki wuuce haka, ina tare da bakine ya kashe wayar, tayi dan murmushi ta maida wayar jakarta. Na tsorata da irin ramar da yaya nafisa tayi, cikin kuka nafisa take fadawa ikilima irin rashin kulawar da haule take mata, tace kinsan dai mama itace ummul'aba'isin shigata wannan halin ko? Kuma lokacin dana samo wannan kazamar daulan tafi kowa ci, amma yanxu tafi kowa tsanata, matar baba ma tafi lura dani da kuma tausayamin, hatta baaba duk da irin laifi da nayi masa yana tausayamin tare da bani kulawa. Ta nuna mata wasu zannuwa wadancan falle biyvn ma jiya ya siyo min su, bayan wadanda kika kawomin. Ikilima itama cikin zubar hawaye tace, kiyi hakuri yaya nafisa, ba'ance ana bada maganin shi a babban asibiti ba? Nafisa ta share hawaye tare da cewa maganin da tsada yanzun banida wanda zai saimin. Ikilima tace baban khalil ya cemin kyautane duk karshen wata,yakamata gobe ki fara zuwa,zan tambaya in ya yarda zanzo na rakaki. Nafisa tace, ikilima nagodai,amma bazan so muje dake ba tunda duk garin nan nasan yanxu sun san inada ciwon nan, kar nagoga miki bakin jini. Zan zo in har ya barni, don Allah ki daina ma fadin haka. Ikilima ta kalli agogo , minti talatin ya bani, bari in sallami su mama duk yanda tayiwu dai gobe kije asibitin, tace to. Takawo dari biyar ta bata, ki rike wannan a hanunki. Kibarshi, kina dawainiya dani iklima. Come on, amsa yaya in ban miki ba in yi ma wa? To, nagodai Allah ya bar zumunci. Ta fita nafisa ta tsura ma kudin idanu. Ta tuna wasu kwanaki da suka shude , dari biyar bata maida ta kudi ba. Duk da bata sadaka, haka zaka gansu a dakinta, in kuwa canji ne ya rage bata karba don gani take tamkar naira biyar ce. Yau ga ta an bata tana murna, kai ya kamata jama'a muyi hattara da kwadayin abn duniya. Ikilima ta sallami su mama, dari bibbiyu ta basu. Sannan tace da mama "gobe zanzo muje asibiti da yaya nafisa ta soma amsar magani, in kuma bai bar ni ba to mama kuje tare don Allah. Wa!! Ba in da zani, na tura tata debo ciwo? Kema ina gargadinki ki rage shige mata, in kin kwasa ke kika sani. Ikilima bata ce komai ba, ta fita don taga zatayi latti, cikin sa'a tana fita baba zai shigo suka gaisa a gurguje ta shaida mishi batun magani, yace yi zamanki, haule ce ta dace suje tare. Ikilima tace in ya bar ni zanzo muje. use Facebook in Free Mode. OK HAUSA Novels BOOK MABUDIN WAHALA 3**5 Ta fita nafisa ta tsura ma kudin idanu. Ta tuna wasu kwanaki da suka shude , dari biyar bata maida ta kudi ba. Duk da bata sadaka, haka zaka gansu a dakinta, in kuwa canji ne ya rage bata karba don gani take tamkar naira biyar ce. Yau ga ta an bata tana murna, kai ya kamata jama'a muyi hattara da kwadayin abn duniya. Ikilima ta sallami su mama, dari bibbiyu ta basu. Sannan tace da mama "gobe zanzo muje asibiti da yaya nafisa ta soma amsar magani, in kuma bai bar ni ba to mama kuje tare don Allah. Wa!! Ba in da zani, na tura tata debo ciwo? Kema ina gargadinki ki rage shige mata, in kin kwasa ke kika sani. Ikilima bata ce komai ba, ta fita don taga zatayi

Chapter 15 of 20