Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yadauketa AK kuma yana fita daganan farm house dinsa yanufa cikin Daren dayake banisa acan ya kuana se dasafe yanufo gida Cikin sanda yashigo gidan dan kar kowa yagansa da gudu gudu ya hawra sama yana waigen bangaran grany yana isa yatura kofar yashiga akuance ya iskota inda yabarta jiya da alama tun baccin jiya da yadauketa bata farka ba da har yanzu kayan jiya ne ajikinta Toilet yanufa batare da yasake kallon inda takeba Karan knocking din dataji ne yatasheta daga baccin datake ahankali tafara bude idonta tana fatan duk abunda yafaru jiya yakasance mafarki ne ba gaske ba Wasu sababbin hawayene suka gangaro afuskanta lokacinda take karema dakin kallo tana tuno abunda yafaru jiya Jin anata knocking yasa tatashi jiki asanyaye tanufi kofa Sam bata lura da yanayin datake ciki ba Grany tagani tsaye abakin kofa rike dawata kwalla tana washe baki Dip murmushin fuskarta yadauke lokaci guda tana kallon asma'u sama da kasa cike damamaki ta ijiye kwallar Tana fadin lafiyanki kuwa asma'u yanaganki haka meyasameki ina abidi din yake Zatayi magana kenan taji anrungumota tabaya atsorace ta juya dan ganin waye AK tagani atsaye yana mata murmushi cikin shirinsa tsab yayi kyew matuka sekanshi yake zubawa janyota yayi jikinsa yana fadin good morning darling ... Baki bude take kallonsa ko kifatawa batayi Takasa cewa komai Juyowa yayi yakalli grany dake tsaye tana kallonsu tana murmushin jin dadi Yace Ohh grany ashe kina nan kintashi lafiya sannan yamaida kallonsa kan asma'u yana murmushi yace kinganta ko gajiya ce tamata yawa tun jiya dasuka zo take bacci se yanzu da kyar natasheta Juyawa grany tayi tana murmushi tace kuyi sawri kushirya ana jiranku akasa kashiga da wannan kwallan ciki Yana ganin grany ta tafi yajanye jikinsa daga asma'u ya wuce batare da yace komai ba Dakallo tabisa har yafita sannan ta dauki kwallan tashiga da ita ciki Zaunawa tayi abakin gado tana share hawaye Sarah ce tashigo dakin rike dawasu kaya ahannunta ta ijiye abakin gadon tana fadin amarsu ta ango ina kwananki Lafiya asma'u tafada tana kauda kai Murmushi tayi tace ko dayake ban damu dasanin ya kika kuana ba dan nasan Yayana yakula dake yanda yadace Kayan tanuna mata tana fadin ga wannan kiyi sawri kishirya ana jiranki AK ne yashigo yana fadin kidan Zane mata fuska da kawalliya karta tsorata mana yara da jajayen idonta Dariya suka samata ahasale tadauki kayan tanufi bayi tana fadin Kune abunda tsoro bani ba tana shiga ta turo kofar dakarfi Sedai mamaki ne yakamata ganin bawani alamun wurin wanka awurin Wani makeken wurine dafadinsa har yafi nadakin girma Drowa ce gaba daya azagaye dawurin Cike makil da kaya kamar anbude shago dayan gefen kayantane awurin amma yawancinsu dogayen riguna ne se English wear masu bala'in kyew dayan gefen kuma kayan AK ne Jere awurin daga kasa kuma takalmansa ne kala kala gefe guda kuma turaruka ne da kayan shafa kala daban daban sewani daddaden kamshi ketashi awurin seda ta kwashi tsawon lokaci tana zagaye wurin amma bataga alamun kofa ba tsaki taja tafita tana fadin yanda mai dakin yake arikece haka komai nasa yake ahargitse ahankali tabude kofar ta leko kanta dan ganin ko suna nan AK kawai ta hango azaune yana waya tsaye tayi tana kallonsa tana wasa dayatsunta Har yagama wayar ya jiyo ahasale yana fadin Malama tundazu me kika tsaya yi dabakiyi wankan ba ko kina jira nazo namaki dakaina ne Kauda kai tayi tana zunbura baki tace Allah ya kyewta ni wurin wankan ne bangani ba Dariya ce takusa kwacemasa yadake yamike yana Jan tsaki ya nufota yana fadin banza yar kawye Matsawa tayi tabasa hanya yashiga tabisa abaya tana zunbura baki tana gunaguni [18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚 👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧 Na ( Maryam Muhammad jibril) 7⃣0⃣ Yana shiga yadanna wani Abu daga gefe kawai drowowin suka bude Sega hanyar dazata sadaka da bathroom tafito tsakanin drowan kayanshi data Asma'u Baki bude take kallon ikon allah seda taga ya waigo wurinta sannan tayi sawrin kauda kai tana daure fuska Hanyar yanuna mata yana fadin dallah zo ki wuce Gefenshi taraba tashiga tana zunbura baki Leko kansa yayi cikin bayin ya nuna mata irin abunda yadanna awaje yana fadin idan kin gama wannan zaki danna inbaki iyaba kuma ki kuana aciki Saurin danna abun tayi kofar tafara rufewa tana hararansa tace to jeka malam naji Sabon shafin kallon tabude datashiga bayin saboda bayin har yafi dakin girma Komai nabayin farine tas gawani katon madubi daya mamaye rabin bangon daga gefe anjerishi da duk wasu abun bukata Sewani katon shower irin natsaye dinnan daga gefe guda gawata drowa daga gefe anjereta dasabulan wanka da shampoo kala kala wani wuri taga anzagayeshi dawasu manyan labulai kalan golden kamar kar taje se kuma takarasa ahankali tayaye labulen Wani dan faffaden bathtub tagani awurin wanda girmansa kaman dan madaidaicin seeming pool Daga gefe anjera sabulai da turarukan wanka kala daban daban Cike da birgewa take kallon wurin jitayi kamar tashi se kuma taba zuciyarta hakuri takoma wurin shower Seda tashafi kusan awa daya kafin tafito mai kawai tashafa se turare tasaka kayan da sarah takamata Wata doguwar riga ce milk color mai kama da wedding gown se tayafa gyalen rigar duk da batayi wata kwalliya ba amma tayi kyew sosai seda tajima atsaye kafin ahankali ta turo kofar tafito atsaye yake yakafe kofar da ido da alama ita yake jira Yana ganin tafito yayi hanyar fita batare dayace komai ba Seda yakai bakin kofa ya waigo yaganta atsaye inda take batada niyyar motsawa Iska ya shaka ya furzar sannan yadawo inda take atsaye Tana ganin yanufota tafara jadabaya tana fadin me kuma nayi Baice komai ba yacapko hannunta yayo waje da ita seda yarufo kofa sannan yasaki hannunta yayi gaba yana fadin to yanzu idan kinga dama kizo ko kizauna Haryayi nisa tayi saurin bin bayansa dan ko za'akasheta batasan hanyar dazata kaita kasa ba juyowa yayi ita kuma tataho suka kusa cin karo Saurin cin birki tayi tana daure fuska Kusanta yamatso fuska ahade cikin murya mai kaman rada yace Wallahi kinji narantse idan har kika bari grany tafahimci abunda kefaruwa senamiki abunda se kinmutu baki manta dani ba Kauda kai tayi aranta tana fadin ko yanzu ai kamun Kina jina ... Yafada yana daka mata tsawa Atsorace tadaga kai tana fadin eh eh allah naji Gaba yayi tana binsa abaya har suka sawko babban palon gidan inda yasha decoration da manyan furanni da balalan masu kyew gawani daddaden sawti natashi ahankali Wurin acike yake da zalla matasa samari da yanmata yawancinsu duk kawayen sarah ne dana bashir da kuma sauran family Manyan kuma suna bangaren grany suna tasu walimar Tunda suka sawko kowa kebinsu da kallo dan sun hadu iya haduwa amma fuskarnan tasu ahade ba alaman far'a DJ naganin sun iso ya sawya salon kidansa inda yakoma na soyayya nan take aka hau shewa da tapi Seda suka fara zuwa bangaren grany suka gaida su sunsha tsokana daga wurin kakannin AK Sedai kawai Suyi murmushi su sadda kai Sun dan jima awurin kafin suka dawo Babban palon Sarah da aysha nabakin kofa suna tarban baki amma aysha naganinsu hankalinta duk yakoma Kansu nan take taji wani bakin ciki ya lullubeta Fa'iz da nusaiba ne suka iso gidan se washe baki suke suna bin gidan da kallo sunci ado sunyi kyew cikin shiga ta ya'yan masu kudi dan abba na kokari wajan saya musu sutura daga su har khadeeja Takusan su sarah suka wuce amma sam basu gane suba khadeeja nadaga baya suna gaisawa da yahya datagani aharabar gidan Tunda tanufo wurin Tagane sarah sadda kai tayi kasa tana fadin badai wannan bace kanwar Ak datake son ahmad To ko dayan ce dakwa nayi abun kunya amma ai sune basuda gaskiya awaccen ranar Dawannan tunanin takaraso wurinsu Sunkuy dakanta tayi zata wuce sarah tace Ke !!! Tsayawa tayi bata juyoba Karasowa gabanta tayi tana leken fuskarta Cak tatsaya tana kallonta tana son tuna inda tataba ganinta Cikin kakkawsar murya tace Ke mara kunya uban me kike anan me kika zoyi Daure fuska khadeeja tayi tace ubanda kowa yake anan shinazo yi saurin riko sarah aysha tayi tana fadin sarah stop it kanwar amaryan mu cefa tafada tana kefta mata ido wucewa khadeeja tayi tana jan tsaki Cike da takaici sarah tace no wonder tunda nafara ganinta naji natsaneta Khadeeja tana Shiga ta isko asma'u na gaisawa dasu fa'iz da gudu takarasa ta rungumeta Bayan sungaisa asma'u tace ina Umma Murmushi khadeeja tayi tace Umma tana gida jiya kuana tayi tana fira cike da farin ciki kamar ba itaba Fuskan tawsayi asma'u tayi batace komai ba Dafata khadeeja tayi tace ammah lafiya naganki wani iri ne Murmushin dole asma'u tayi takauda kai tana fadin kawai ina missing din Umma ne Kauda zancan khadeeja tayi dafadin meyasa bakiyi make up ba dase kinfi kyew Fa'iz ne ya zunguri khadeeja yana nuna mata AK dake gefe Azaune yana waya Baki tawashe tace laaaaa wallahi kwa shine kai ammah gaskiya kun bala'in dacewa guy dinnan yahadu dayawa Ashe mijin ammah tane Sadda kai asma'u tayi batace komai ba Karasawa wurinsa khadeeja tayi tana washe baki Yana ganinta yadaure fuska hade da kauda kai dan koba'a fadaba yasan tahada wani Abu da asma'u saboda kamar dayagani afuskanta Tana isa wurinsa tazauna akujerar kusa dashi tana gaidashi Bayabo ba fallasa ya amshi gaisuwarta Murmushi tayi tace baka sanni bako? Girgiza kai yayi alaman a'a Kanwar matarka ce .. Tafada tana kokarin gano yanayin fuskarsa Murmushin yake yayi yakauda kai yace Sannunki toh ya Umma lafiya .. Tafada atakaice Satan kallonsu asma'u keyi tana tsoron kada khadeeja tagano halin da ake ciki Sadda kai khadeeja tayi cikin sanyin murya tace i hop u like my sister Saurin kallonta yayi Da mamaki yace meyasa kika ce haka Saboda ban hango farinciki atattare daku ba nasan inada kananun shekaru amma daga kallon kwayar idon yayata nakan tantance halin datake ciki Nasan yanda aurenku ya kasance kunyishi batare da kun fahimci juna ba Amma yayata tanada sawkin kai kuma tanada hali mai kyew idan kabata hadin kai dan lokaci kankani ya isa kafahimci wacece ita She has a golden heart please don't break it Takarashe maganar muryanta narawa Maida kallonsa yayi kan asma'u yaganta tana Gyara ma nusaiba dawrin dan kwali suna dariya Yajima yana kallonta sannan ya jiyo ya kalli khadeeja yana murmushi yace Bana so nakaiga zuciyar bare har nakaryata Murmushi tayi amma badan tagane meyake nufi ba Tashi yazo yi tayi saurin rikoshi tana fadin tsaya mana ai bamu gama ba Zaunawa yayi yana girgiza kai sedai baisan meyasa ba Sam bayajin haushinta Dariya tayi tace sorry ni haka nke sedai kayi hakuri amma har yanzu baka gayamun ya kaga yayata ba Kallonta yayi yace what is ur name Dariya tayi tace khadeeja..... Juyowa yayi suka fuskanci juna sannan yace Deeja I've found ur sister like a very big book look interesting but very boring Bude baki tayi dashirin magana yayi saurin katseta da fadin ohhh khadeeja ina fatan kizama yar jarida nan gaba Zakiyi ma kasa anfani Tabe baki tayi tace kana nufin inada surutu kome Dariya yayi baice komai ba Itama dariyar tayi tamatso kusa dashi cikin rada tace wai acikin yan matan nan biyu nawaje wacece kanwarka Mai kama dani...yafada atakaice To dayan fa wacece My girlfr..... baikarasa ba yayi saurin fadin no she is my cousin Zatayi magana kenan kiran ahmad yashigo wayarsa Tashi tayi tabashi wuri takoma wurinsu asma'u sukaci gaba da fira Daga wayar AK yayi tare da sallama Tadayan bangaren ahmad ya amsa sallamar yana fadin friend nifa na iso yanzu haka ina company OK yafada atakaice Shiru ahmad yayi nadan lokaci yana mamakin haryanzu AK yana fushi dashi jin karan music na tashi yasa yayi kasa da murya yana fadin kana ina ne naji hayaniya Ina gida mana.. Ok kuna wani shagali ne Nayi aure friend ... Dip nunfashin ahmad ya tsaya cike da mamaki yace aure fah kace AK Eh... jiya kuma .... Cikin sassanyar murya ahmad yace Aysha... ka aura ne?? a'a... watace daban Wakenan ?? Idan kazo zaka ganta I know u will be shock Ok .. Ahmad yafada yana ajiye wayar da mamakin wacece AK ya aura kuma meyasa bai auri aysha ba AK yana gama wayar ya juya baiga khadeeja ba girgiza kai yayi yana murmushi sannan yama sarah alama tazo tana zuwa yace sarah munyi waya da ahmad ya iso yanzu kuma yana hanyar zuwa nan gidan Murmushi tayi cike da farin ciki tace wow!!! Kai amma naji dadi har nakosa yazo dan naga ya zai yi idan yaga budurwarsa amatsayin matarka Kauda kai yayi da damuwa afuskarsa dan karfin hali kawai yake amma bayason ganin bacin ran ahmad MC ne yafara sanarwa na kowa yasamu wuri yazauna zasu fara shirye shiryensu Dariya fa'iz yayi ya kalli khadeeja yana fadin deeja yau zamu rakashe ... Dariya tayi tabashi hannu suka kashe Sarah dake kallonsu tawuce wurin aysha tana murmushin da bansan kona miye ba Bayan kowa ya zauna MC yabukaci kowa yashigo fili yataka dan taya ango da amarya murna Haka kowa yatashi yafara rawa fa'iz da khadeeja nadaga zaune banda dariya ba abunda suke Cike da takaici sarah ke kallonsu Tana fadin wallahi yaran nan haushi Duke bani ni Sam banga lokacinda suka wuce ba da ban barsu sunshigo ba Dariya aysha tayi meyasa bazamu dan buga wasa ba Tsaki sarah tayi tace wasa dawa? Dasu man badai kin iya rawa ba ? To bari kiga Tana gama fadan haka tamike tanufi wurin MC wata magana tamasa akunne naga yayi murmushi Sannan yanemi kowa Yakoma yazauna Bayan kowa yazauna sannan ya nemi ganin kannin amarya guda biyu Kallon kallon aka fara tsakanin fa'iz da khadeeja Sannan tamai alama dasuje Tsakiyar filin suka je suka tsaya cike da birgewa kowa ke kallonsu saboda Kansu daya gashi suna yanayi wasuma sunzata yan biyu ne Bayan sun gaisa dakowa sannan MC yabukaci ganin kannin ango guda biyu Nan take aka hau tapi da shewa ganin sarah da aysha sun fito cikin shiga tariga da wando sunyi kyew sosai Juyowa asma'u tayi takalli AK dake gefenta azaune tana fadin wai mezasuyi?? Hannayensa yaware yace ohoo yanda kike da ido biyu nima haka nakedasu to muzubasu muyi kallo Kauda kai tayi cike dajin haushin kanta dan Sam bata San lokacinda ta tambayesa ba MC yabukaci kowa ya nutsu yanzu za'a kalli gasan rawa tsakanin kannin ango da amarya Cike da firgici khadeeja takalli fa'iz Sedai ga mamakinsa murmushi taga yanayi Zunguranshi tayi tana fadin kai wai kaji abunda yace Kuwa Dariya yayi yace haba deeja wani ma yayi rawa bare dan makadi haka kawai ma mun zage mun tiki rawa bare kuma abikin ammah shima kuma wai gasa Kansu sarah aka fara inda suka zabi wakar dasuke so dakansu Nan take DJ yasaki kida su sarah da aysha suka fara takawa rawa suke bata wasa ba amma sarah tafi aysha iyawa Har suka gama su khadeeja nagefe suna kallonsu Tapi aka hau yi ana shewa kowa nayaba rawansu Bayan hayaniya talafa MC yabukaci kannin amarya su shigo fili Fa'iz yakalli khadeeja yana fadin deeja muje mana Jadabaya tafarayi tana fadin gaskiya fa'iz bazan iyaba mutane sunyi yawa kunya nakeji Nan take aka hau nunasu dayatsa ana dariya Juyowa AK yayi yana kallon asma'u yaga fuskanta ta canza tana kallon fa'iz daya sadda kai yakasa motsawa Sarah da aysha kuma se dariya suke suna tapa hannu (ni kwa nace girma yafadi😏) Dariya yayi yace inaga kanwarki bakinta kawai ta iya sarrafawa amma banda gangar jiki hahaha Sadda kanta tayi kasa batace komai ba Kallonta khadeeja tayi setaji duk bataji dadi ba kamar takoma amma tayaya Karban microphone din fa'iz yayi cikin dakewa yafara fadin Hello guys!!! kanwata ba guduwa tayiba kuma batsoro taji ba Kunsan duk macen da tacika mace ansanta da Jan aji da basarwa Rawanta Nada tsada so u have to beg for it !!! nan take aka fara tapi ana kiran deeja!!! Deeja!!! Deeja!!! Karasowa fa'iz yayi kusa da ita cikin rada yace deeja please u have to this for our sister kalla kiga yanda angonta kemata dariya duk danasan wasa ne amma bazataji dadiba Murmushi tayi tace ok let's do it Hannunta yakamo suka dawo filin rawan nan aka hau tapi ana daukan su photo saboda sunbirge kowa awurin Karban microphone din MC yayi yana fadin ok twins which song are u ready to dance on ?? Kallon mutanen wurin khadeeja tayi tana fadin mun basu zabi Tapi aka haw yi ana shewa kowa nafadan wakan dayakeso Nan dai DJ yasakar musu wakar humma song suka fara rawa Haba ai nan take kowa yamike akafara daukansu video saboda yanda suke bin kidan suke rawa kuma komai tare suke yinshi gwanin sha'awa Shi kanshi AK sunbirgeshi Tun kafin sugama kowa yafara tafa musu ana basu winning Haushi ne Yakama sarah cike da takaici taja aysha suka bar wurin Har suka gaji amma anki bari su sauka daga wannan wakar takare se asaka wannan se da kyer suka kwace kansu Dariya asma'u tayi tamike tsaye tana kallon AK tace Inafata kanada isashshen jinin da za'adiba akarama kanninka dan naga sunada bukatarsa Zai yi magana kenan ya hango ahmad atsaye agabansu kaman gunki yana kallonsu Murmushi yayi ya mike yanufosa yana fadin ohhh welcome back Friend Shuru ahmad yayi yakasa magana yana mamakin me kuma yayar khadeeja take anan Asma'u kuma data basu baya Sam bataga ahmad ba Hannu AK yasa yajanyota yana fadin meet my wife Cike da masifa ta jiyo da nufin magana amma cak tatsaya ganin ahmad agabanta Sadda kanta tayi kasa bawanda yace komai Wani malalacin murmushi AK yayi daya hango mamaki karara afuskar Ahmad Jadabaya AK yayi yana murmushi yace bari nadan Baku waje kuyi magana sannan ya juya yanufi wurin da yahango aysha atsaye Yana tafiya ahmad yakalli asma'u cike da mamaki yace wai dama kece AK ya aura garin Yaya dama kunsan juna ne Dagowa tayi ta kallesa cikin rawar murya tace yanzu ba lokacin magana bane Ahmad khadeeja tana nan wurin ga sarah dan Allah katafi banaso sugane akwai wani Abu atsakaninku Tana kainan ta juya tanufi bangaren grany tana boye kwallar data cika mata ido Da kallon tawsayi yabita ahankali ya furta something is fishy Sarah ce tazo kusa dashi tana murmushin mugunta tana girgiza kai tace ohhh so sad !!! Kayi mamakin ganin budurwanka anan gidan ko sannan ta langwabar dakanta tacigaba dafadin to ya na iya naso nafita hanyarka amma nakasa shiyasa nadauki wannan matakin Wani kallo mai cike da tsana yawatsa mata yaraba tagefenta zai wuce tayi saurin riko hannunshi tace tsaya mana Yaya baka tambayeni ya akayi yarinyar dakake ikrarin tana sonka tayi saurin amincewa auran wani batare da saninka ba Daidai nan khadeeja tazo wucewa tahangosu kamar ance yadaga kansa kawai ya hangota tana barin wurin da sauri har tana hadawa da gudu Cike da takaici yabige hannun sarah yana fadin kirike tatsuniyarki bana bukatarta Sannan yabi bayan khadeeja yana kiran sunanta Ahasale sarah tanufi bangarenta tana fashewa da kuka Tafiya kawai khadeeja take bata Masan inda tanufa ba sedai kawai taganta a garden shakan wani iska mai dadi tayi ta lumshe ido sannan tazauna adaya daga kujerun wurin tana kallon katon seeming pool din dake gabanta Kusa da ita ahmad yazo yazauna Sunjima ahaka bawanda yace kala Secan tasauke ajiyar zuciya batare data kalleshiba tace yaushe kadawo?? Dazu.... Yafada atakaice batare daya kalleta ba shima Meyasa baka gayamun ba Nakiraki wayanki akashe Daganan kuma suka kara yin shiru nadan lokaci kana cikin cikin sassanyar murya ahmad yace I am sorry... Se alokacin tajuyo takalleshi tana murmushi tace no I'm sorry Kallonta yayi yana murmushi baice komai ba Sadda kanta tayi kasa ahankali tafurta I missed u Missed u more yafada cikin jin fadin maganarta dagowa yayi yana kallonta yace meyasa baki gayamun AK yana son yayarki ba Fuskar tawsayi tayi tace nima kaina bansan AK ne zai aureta ba sedaga baya damamaki yace kamarya ?? Nan tabashi labarin abunda yafaru Ajiyar zuciya ya sawke Dayagama jin bayaninta sannan yadago yakalleta da damuwa afuskarsa yace deeja ni inada shakku akan wannan auren Meyasa kace haka Ranarda asma'u tazo office dina sarah taganta kuma aranar nake gayamata bazan aureta ba inada wacce nakeso to setayi tunanin asma'u ce wacce nakeso din Shakan iska yayi ya furzar sannan yacigaba da fadin Deeja nasan wacece sarah tana kokarin ganin tasamu duk wani abunda takeso Shikuma AK zai iya yin komai dan farincikin ta Ni bansan meyake faruwa ba amma hankalina yakasa kuanciya da aurenan Cike da damuwa khadeeja tace nima nayi wannan tunanin saboda dazu nazo wucewa naga AK tare dawannan cousin din tasa aysha kuma ayanda nagansu hankalina bai kuanta ba shiyasa nazo inaso na tambayi ammah Sekuma naganka da sarah Ahankali ta furta meyake faruwa ne ki kuantar da hankalinki balalle ne abunda muke zargi yazamo gaskiya ba Saurin barin wurin tayi tana fadin bari naje naga ammah Asma'u ce tashigo bangarensu azaune taga AK apalo yadafe kai tsaye tayi tana kallonsa aranta tana fadin to shikuma wannan meke damunsa Dagowa yayi ya kalleta cikin kakkawsar murya yace kallon me kike mun bayan duk ke kika sakani awannan halin Shiru tayi tasadda kanta kasa batace komai ba Tasowa yayi yakaraso wurinta yana fadin duk lokacinda abokina yayi tafiya idan zai dawo ni nake Zuwa natarboshi na rungumeshi nakawoshi gida muci abinci tare muyi fita tare amma yanzu ta dalilinki ko sannu dazuwa mai kyew nakasa yimai Kin ruguza mun rayuwata kin rusa mun farin cikina kin cutar da aminina bazan taba yafemaki ba Yana kainan ya tureta daga bakin kofar seda tafadi ahasale yabanke kofar yafita Cak yatsaya yana kallon khadeeja dake tsaye abakin kofar fuskarta sharkap da hawaye tana jifanshi dawani kallo mai cike da tsana tagefenta yaraba ya wuce batare dayasake kallonta ba Kamar kartashiga har ta juya sekuma tasa kai cikin dakin asma'u naganinta ta tashi azaunen datake akasa tana share hawayen fuskarta Rungumeta khadeeja tayi tafashe dawani irin kuka mai ban tausayi Dafa kanta asma'u tayi cikin rawar murya tace khady menene lafiya meyafaru Cikin kuka khadeeja tace ammah meyasa !!! Meyasa!!! Kika boyemun halin da kike ciki Mutuwar tsaye asma'u tayi dan Sam bataso khadeeja tasan halin datake ciki ba Dagota tayi tafara Share mata hawaye cikin rawar murya take fadin Ni ba abunda yake damuna khady I like the house ... the family was nice.. And I like my husband he is good man ... And grany was taken care of me .. Kuma kince Umma tana farin ciki Wannan kadaima.. ya isheni... Katseta khadeeja tayi dafadin a'a ammah bazai yuwu ba mutanen nan basa sonki kawai yaudarar ki sukayi Sam baki dace dasuba Jan hannun asma'u tanafadin kizo mukoma gida kawai Rikota asma'u tayi cikin muryan kuka tace no khady please bazan iya tafiya ba kiyi tunanin kuana daya da bikina aganni agida me mutane zasuce za'ama su abba dariya wane hali Umma da inna zasu shiga kinsan basuda cikakkiyar lafiya idan abba yaji kanshi zai dorawa laifi zaice shi yajamun bazai yafema kansaba Kuma narabu dasu kanki zasu koma bazasu kyaleki ba Sulalewa kasa khadeeja tayi tana wani irin kuka mai cin rai dogowa tayi takalli Asma'u data safe kai saboda bata iya jurar kukan khadeeja Cikin muryan kuka khadeeja tace ammah Tun ina Karama kike wahala akaina yanzu na girma ma amma baki huta ba zaki kara fuskantar wata rayuwar akaina wallahi hakan yasa natsani kaina ... Saurin toshe mata baki cikin rawar murya tace a'a khady kidaina fadan haka wannan nadaukeshi amtsayin jarabawa ne daga Allah kuma nakarbeta hannu biyu inafata Allah yabani ikon cin jarabawar Kin manta kintaba gayamun cewa inada hali mai kyew zaki tayani da addu'a Allah yabani miji nagari ba kya tunanin addu'ar ce Allah yakarba Da kyar asma'u ta lallashi khadeeja tayi shiru sannan ta roketa akan kar tagayama kowa halin datake ciki ahmad tabari dakanta zata mai bayani bayanin datama khadeeja shitama ahmad amma da kyar ta shayo kansa ya hakura da zacan da cewa yayi se yaje yasanar da grany halin da ake ciki Bayan angama taro kowa ya watse tun aranar yane uwansu suka koma Ahmad ne yamaida Momy dasu khadeeja gida Gidan yayi shuru har antattare angyara yakoma yanda yake da Kowa na bangarensa asma'u har ta kuanta taji anturo kofa afirgice ta tashi zaune ta kure kofar da ido 😳 [18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: AK ne

Chapter 9 of 35