Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nusaiba se Ku kawo daga baya mayi magana tashi tayi jiki asanyaye tafito daga wurin tana sharan kwalla Karo sukaci da ahmad zai shiga atsorace yace deeja menene yanaga kinfito meyasami Umma Banza tayi dashi taje jikin mota takifa kai tana rera kuka dawowa yayi wurinta yana tambayar meyafaru Daidai nan su sarah suka iso asibitin aguje tanufo inda suke ta matse khadeeja jikin motar tana fadin allah yakamaki munafuka wallahi yau nizanyi ajalinki Kokarin rabasu ahmad keyi amma yakasa Kamar mahaukaciya haka sarah tadawo gashi tarike wuyan khadeeja gam taki sakinta Ahasale yafizgota daga jikin khadeeja yayi wurgi da ita gefe seda tafadi sannan yanunata da yatsa yace wallahi kika kara tabata se tattakaki awurin mahaukaciyar banza kawai Tasowa tayi tanufosa tana kuka tace eh nayarda ni mahaukaciya ce ahmad amma kuma kai kahaukatani Riko hannunsa tayi tana nuna khadeeja tace dame wannan tafini ahmad mezakayi dawannan karamar yarinyar dabata masan miye soba Nice nakesonka da gaske ahmad zan iya mutuwa in narasaka Kwace hannunsa yayi yabudema khadeeja mota tashiga sannan shima yazaga yashiga suka wuce Da kallo tabisu baki bude se hawaye dasuka wanke mata fuska Jan hannunta aysha tayi suka koma mota suma suka bar wurin Bayan dan lokaci Umma tafarfado tana kiran asma'u Aguje suka fada dakin su duka kusanta asma'u taje tazauna tana kuka tace na'am Umma Shafo gefen fuskanta tayi cikin muryar mara lafiya tace asma'u dagaske ne AK yasakeki da gaske khadeeja tagudu da ahmad Shiru asma'u tayi takasa cewa komai se hawaye dake diga daga idonta Damamaki grany tace wane saki kuma take magana kodai tayi mafarkine Shuru kowa yayi adakin bawanda yabata amsa Juyowa tayi tana jifan AK da kallon tuhuma Saurin matsawa yayi kusan gadon yakamo hannun Umma yana murmushi yace haba umma wace irin magana ce wannan taya zan saki asma'u haka kawai batayimun komai ba bayan ina sonta koma wa yafadamaki karyane kidaina damun kanki yan.... Bai karasaba takatseshi dafadin amma dagaskene ahmad yafasa auren sarah sun gudu da khadeeja ko Kauda kai yayi ya zare hannunsa daga nata yana fadin Umma kibar wannan maganar khadeeja tana nan bataje ko ina ba yanzu dai kina bukatar hutu kidaina daga hankalinki fita yayi yana fadin bari naje doctor nason ganina kudan barta tahuta Binbayansa asma'u tayi sukashiga office din doctor din Bayan yagama yan rubuce rubucensa yadago yana murmushi yace waye nata acikinku? Atare sukace ni.. Juyowa sukayi suka kalli juna sannan AK yakalli doctor din yace muduka ya'yanta ne meyafaru Cire glass din idonsa yayi yana sauke ajiyar zuciya yace well Wato zuciyarta ce tabuga sanadin ji ko ganin wani abunda yadaga mata hankali dama kuma tana fama da ciwon zuciya to yanzu dai munyi nasarar yimata aiki amma akiyaye nan gaba kar irin haka takara faruwa zaku iya rasata duk wani abunda zai bata mata rai akiyayeshi sannan akula sosai da maganinta Bayan yagama yimasu bayani yabasu list din magungunan daza abukata da sauran abubuwan sannan suka fito Wurin Abba AK yanufa yabashi takardar sannan yace zaije mota yadauko kudi se asiyo maganin Gudiya yamasa yana samai albarka Murmushi yayi yace Abba bana bukatar godiyarku ni Dane awurinku kome nayimaku addu'a kawai zakumun ita nafi bukata ba godiya ba Yana kainan yaraba tagefen asma'u yawuce batare da yakalleta ba Da kallo tabisa tana murmushi yar yabacema ganinta sannan tazauna tana sauke ajiyar zuciya Washegari da yamma aka sallami Umma gaba dayansu suka koma gida harda su grany Bayan sunci abinci sundan yi fira suka shirya zasu tafi Ganin asma'u batada niyyar tafiya yasa Umma tace asma'u kitashi kutafi mana Langwabe kai tayi tace Umma kidan barni nazauna har kiji sauki "a'a tashi kitafi ni naji sauki alhamdu lillahi kuma ga inna da Ummi ai ba nikadaibace Shagwabe fuska tayi tana kallon grany tace grany kirokammun Umma tabarni se gobe Murmushi grany tayi tace a'a ni ba ruwana tashi ga mijinki can awaje kitambayeshi idan yabarki ba matsala Ganin dagaske suke yasa bashiri tafito waje Neman AK Cikin mota ta iskoshi zaune yana jiransu Karasawa tayi jikin motar tatsaya kanta akasa tana tunanin mema zatacemasa Sauke glass din motar yayi yaleko yana fadin kinada magana ne Sosa kai tayi tace dama dama sonake inkuana anan harzuwa gobe Kauda kai yayi yana maida glass din motar yace u don't need to ask me dama zaki zauna gaba daya sonake Shuru tayi takasa cewa komai kuma takasa motsawa seda tadan jima kana tajuya takoma ciki tana mamakin meyasa taji zafin maganarsa bayan tasan ba sonta yakeba [19/07, 16:58] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚 👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧 Na( *Maryam mhd*) 1⃣0⃣5⃣ Washegari dasafe AK yasauko daga bangarensa yana naman sarah dan tun jiya rabonshi da ita aysha ya tambaya tace sarah tana dakinta tun jiya take kuka har yanzu bataci komai ba Dakinta yanufa ahankali yatura kofar yana sallama Can karshan gado ya iskota zaune tasa kai aguywa tana aikin kuka Yajima atsaye bakin kofar yana kallonta kafin ahankali yataka zuwa inda take Kusa da ita yazauna yana shafa kanta cikin sigar lallashi yace Sarah idan nace nasan halin dakike ciki nayi karya saboda duk yanda ake fadin soyayya ni bahaka nasanta ba nakanyi mamakin yanda mutane keshiga tashin hankali idan suka rasa masoyansu Nasan zakaji zafi amma bansan yazafin yakeba Ni hasali ma banyarda akwai wata aba ba wai soyayya ganinki awannan halin yasa nafara tawsaya ma masoya kuma hakan yasa tafita araina tunda ba komai acikinta se kunci dawahala Nasan kina son ahmad kina kaunarsa kina son rayuwa dashi amtsayin mijinki Amma inaso kigane akan yima mace auren dole tazauna amma ba namiji ba ada nadauka ahmad zai iya aurenki yazauna dake ahakan amma lokacinda nagansa da khadeeja natabbata koda kin auresa bazaki ji dadin zama dashiba saboda nafuskanci bakaramun so yakemata ba Dan haka kiyi hakuri kimanta da ahmad kiyi addu'ar allah yabaki miji nagari Wanda yafi ahmad kuma yasoki fiye da yanda zaki soshi Ko kuma ni kibani dama cikin abokanaina nazaba miki Wanda nayarda dashi nasan zakiji dadin zama dashi Tunda yafara magana bata dago takallesa ba sema kukanta dayakaru seda yasa hannu yadago kanta sannan tabude jajayen idanuwanta tana kallonsa Handkerchief yaciro a aljihunsa yafara share mata hawaye yana fadin kinyi shiru bakice komaiba ko kinbani damar nazaba miki ne Kauda kai tayi cikin dasashshiyar muryanta tace Yaya ni nagirma nakai lokacinda zan tantance abunda yadace dani da Wanda baidace ba basai kazabamun ba Ko limamin kasar maka zaka kamun bana bukatarsa kuma bazan so shiba ni ahmad nakeso kuma shi kadai zan aura idan bazaka sa ya aureni ba leave it to me ni zan iya ... Cike da mamaki yake kallonta tunda tafara magana Cikin wata iriyar murya yace sarah ni kike gayama haka Ni kike gayama kin girma kinsan abunda yadace dake Koda yake ba laifinki bane ni nabata ki tun kina Karama nareneki da hannuna duk abunda kikeso shi nake maki baki taba Neman wani Abu kinrasaba sedai inyafi karfina nayi kokarin bata abotar dake tsakanina da ahmad duk saboda ke amma yanzu ki kalli kwayan idona kina gayamun wai basai nazabamaki ba kinsan abunda yadace dake Tashi yayi yanufi hanyar fita daga dakin yana fadin Fine nabarki kizabi abunda yadace dake amma karki kara sakani cikin duk wata damuwarki Saurin tashi tayi tarungumo shi tabaya tana rusa kuka tace Yaya dan allah kayi hakuri bahaka nake nufi ba raina ne abace I am sorry janyeta yayi daga jikinshi yafita batare da yace komai ba bangaren grany yanufa bayan yayi breakfast yakwanta anan Palo yana kallo Fitowa grany tayi daga daki tazauna daga gefe tana fadin abidi yau kaje kaduba Maman su asma'u kuwa girgiza kai yayi alamar a'a "Bangane a'a ba to tashi kaje daga can ma kabiyo da matarka Pilo yasa yarufe kansa kamar zai yi kuka yace ooooo grany dan allah kibarni nadan huta ita batasan hanya ba da intaje ni nake zuwa dawkota Haba tarike tana salati tace yau naga abunda yafi karfina ni mairo Kai yanzu abidi matarka bata kuana gida ba amma kana mitar zuwa dawkota anya kwa abidi kanada cikakkiyar lafiya kuwa tashi yayi yana yarfa hannu yafita daga Palon zaune yake abayan mota driver ketukasa har suka isa fa'iz dake filin gidan yana buga kwallo ne yazo yabude masu get bayan yashiga yayi parking AK yafito daga motar yana kallon fa'iz dayayi kamar baisanshiba Murmushi yayi yakarasa wurinsa yafara buga ball din tsaye fa'iz yayi yana daure fuska yagaidashi ciki ciki kamar mai koyon magana Dafashi AK yayi yana amsa gaisuwarsa yace come on boy wai fushi kayi dan namareka ranan Kauda kai fa'iz yayi baice komai ba "OK I am sorry bansan meyakaika dakin ba amma nasan abunda tafada karyane She is my sister kaga bazanso hakan yafaru da ita ba Kaima kuma kanina ne bazan so ace ka aikata hakan ba Amma nagane rashin fahimta aka samu tsakaninku Karkato da kuncinsa yayi yana shagwabe fuska irin nayara yace Idan kuma kana fushine dan namareka to gashi Karama Dariya fa'iz yayi yana fadin haba yaya allah ya kyewta Dariya shima yayi ya wuce cikin gidan yana fadin bari nagaida Umma nazo muyi kwallo Yana tura kofar palon yahadu da khadeeja tafito daga kitchen rike da plate din indomie ahannunta Sunkuy dakai tayi tana gaidashi Bayabo ba fallasa ya amshi gaisuwarta yana zama apalon Ciki ta wuce ta sanardasu ga AK yazo Bayan sunfito suka gaisa yakoma kusan Umma yazauna yana fadin Umma ya kike ji yanzu bawata matsala daiko Murmushi tayi tace ba komai abid nagode da kulawa allah yasaka da alkhairi Ameen yafada yana kallon inna yace inna kefa nifa harmukaje asibiti banyarda Umma ce batada lafiya ba nadauka kece Daure fuska tayi tace ni makiyiyarka ko to ta allah bataka ba Dariya yayi yace allah baki hakuri daga magana ai ni masoyinki ne kallon khadeeja Umma tayi tana fadin Ashe abunda wainnan sakarkarun yaran sukayi kenan ai da kazanemun ita wallahi khadeeja bataji ko ina ita ina ahmad oho Tashi tayi tafita idonta cike da kwalla Murmushi inna tayi tace harkan yara se hakuri Sannan takalli AK tace kungaisa da Abba kuwa Girgiza kai yayi yace a'a ni yanzu nashigo yana nan ne "eh yana bangarensa Tashi yayi yanufi bangarensu Abba yana Isa ya iskosu zaune apalo suna fira harda asma'u Bayan sungaisa yashiga firan anayi dashi sedai jifa jifa yana kallon ALi da asma'u dasuka koma gefe suna tasu firar kiran khadeeja tagani yashigo wayanta da mamaki tatashi tafito daga palon karo sukaci da khadeeja zata shigo fuskanta sharkaf hawaye Gefe tajata tana fadin lafiya khady meyafaru kike kuka AK yamiki wata maganar ne Daidai nan AK yazo wucewa yatsaya yana sauraronsu Cikin rawar murya khadeeja tace baicemun komai ba amma naji kunyar hada ido dashi Gaskiya koda son ahmad zai kasheni dolene nahakura dashi saboda bandace dashiba Sarah tana sonsa idan ya aureta ahankali zai fara sonta Farin cikin sarah shine na AK ni kuma naki shine nawa Gaskiya dole ne ahmad yazaba ko ya auri sarah ko yahakura damu gaba daya amma ni bazan iya aurensa ba Barin wurin AK yayi yanufi motarsa yashiga fa'iz yabudemasu get yana fadin Yaya har zaka tafi bakace zamuyi kwallo ba Murmushi yayi yana daga mai hannu harsuka fita batare da yatankasa ba Yana fita yakira ahmad awaya seda takusa katsewa yadaga Bayan sungaisa sama sama AK yace kana gida ne eh..... Yafada atakaice Katse kiran yayi yagayama driver gidansu ahmad zaikaishi Numban sarah yakira amma har yamata 5 missed call bata daga ba Shuru yayi ya jingina da kujera hade da lumshe ido yana tunani kala kala aransa har suka isa yana isa bangaren ahmad yatura kofar yashiga zaune ya iskosa apalo Ahmad naganinsa yamike tsaye Kusa dashi yamatso yadafa kafadarsa yace Friend inaso ka rufe idanuwanka kamanta lokacinda muka fara samun matsala dakai kamanta lokacinda sarah da khadeeja suka shigo rayuwarka katuna lokacinda muke dagani sekai kana kirana supper hero ina kiranka supper man Lokacinda dayanmu baya iya bacci se yatabbatar da lafiyan dan uwansa lokacinda za'a dakeka amma nine zanyi kuka lokacinda banada lafiya amma kai ne kejinya lokacinda zanji ciwo amma sekafini jin radadinsa Shuru ahmad yayi idonsa arufe yana tuna duk abunda AK kefada seyaga kamar lokacin abun ke faruwa baisan lokacinda hawaye suka fara zuba daga idonsa ba Cikin rawar murya AK yace Yanzu gani agabanka ba amtsayin AK hausawee ba amatsayin supper hero dinka shin zaka amince ka auri wacce nakeso takasance matarka ?? Rungumesa ahmad yayi yana fashewa da kuka yace na amince supper hero nayarda zan aureta ko yanzu kake so muje adauramana aure wallahi zan zauna da ita kuma zan kula da ita Jan hannunsa AK yayi yana sharan kualla suka fita daga gidan Kofar gidansu khadeeja driver yayi parking da mamki ahmad yace amma wannan ai gidansu khadeeja ne nan nakawota jiya meyasa muka zonan Murmushi AK yayi yace inaso mubasu hakuri ne kuma kuyi bankuana da khadeeja kagayamata ka amince da auren tunda itama haka takeso Bude kofa ahmad yayi yafita baice komaiba Murmushi AK yayi yafito suka shiga tare tunda AK yafita sarah ke kuka tana ganin kiransa amma taki dauka aysha dake kusa da ita tace sarah AK yamiki 5missed call amma baki daga ba Kauda kai sarah tayi tana sharan kwalla Daukan wayan aysha tayi takira numban amma yabarta amota har takatse ba adaga ba Zama tayi kusa da sarah tana fadin meyasa baki dauki kiransa ba kikasan kome zai gayamaki Numban drivernsa takira bugu biyu yadaga yana gaidata Bata ansa ba tace kuna tare da AK ne "Eh munatare dashi amma yanzu sunshiga wani gida shida sir ahmad " ahmad fa kace wane gida suka shiga kenan "bansani madam amma naji suna zancan wai sir ahmad ya amince zai yi aure wurgi tayi dawayan tana daka tsalle tace sarah barka natayaki murna ahmad ya amince zai aureki Saurin tashi sarh tayi tana washe baki tace allah dagaske wa yagayamiki Kama hannunta tayi tana jujjuyata tace yanzu driver yacemun AK natare da ahmad kuma ya amince zai aureki tsalle sarah tayi tafada kan gado cike da farin ciki tana kankame pilo zaune suke apalon inna sunyi jigum jigum suna jiran abunda AK zai fada ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Umma yace Umma kintabbata bakida matsala akan duk hukuncin da nayanke Gyada tayi tace kwarai kwa abid nabaka dama kayanke musu duk hukuncin dayadace Murmushi yayi yana kallon inna yace inna kefa Tabe baki tayi tana juya furar dake hannunta tace yo ni meruwana dasu Fa'iz dake kusa da ita se hadiyar yawu yake nabin furar dakallo harara tabankamai yayi saurin kauda kai yana hade fuska sunkuy da kai AK yayi yace To ba wani Abu bane dama ahmad nazabama mata kuma ya amince da aurenta to shine nazo Baku hakuri akan abunda yafaru Dagowa ahmad yayi yakalli khadeeja suka hada ido tayi saurin kauda kanta tana share hawaye Murmushi AK yayi yana kallon ahmad yace Friend zan baka auren kanwata kariketa amana da gaskiya ka kularmun da ita yanda yadace idan kacutar da ita to zan manta kai abokina ne nayima rashin mutunci Shuru sukayi gaba daya ba Wanda yace wani Abu Idon asma'u ne yakawo kwalla tana kallon kanwarta cike da tawsayi Umma ma haka kawai dai juriya take Maida kallonsa yayi kan khadeeja yace Deeja ga abokina nan nasan kina sonsa to kiyimai biyayya kuzauna lafiya banda rashin ji idan har kika muzguna masa to kema zanmanta cewa kanwata ce ke zan iskoki har gidanki nahukuntaki kinji ko? Gaba daya suka dago suna kallonsa cike da mamaki Murmushi yayi yace yakuke kallona ko baku gane menake nufi bane cike da farin ciki ahmad yace friend kana nufin ka amince na auri khadeeja Gyada kai yayi yace bama amincewa kadai ba nizan shirya komai kuma agidana za'ayi komai Rungumesa yayi yana dariya mai sauti har yakasa magana Cike dafarin ciki asma'u tadaka tsalle tafada kan khadeeja suka rungume juna suna murna Ganin kowa ya rungume dan uwansa fa'iz yajuya yana washe baki garin rungume inna yabige furar dake hannunta tawatsamata afuska Sadap sadap yatashi yabar wurin tun kafin tabude idonta Sunjima ahaka kafin kowa ya natsu juyowan da AK zaiyi yaga fuskan inna sharkaf da fura har ba'aganin komai se idonta atsorace yamatsa gefe yana salati Se alokacin kowa yalura gaba daya suka kwashe mata da dariya seda sukayi mai isarsu tana zaune tana binsu da ido Daure fuska tayi tace kun gama ai kamar ta ce suci gaba suka kara sa wata dariyar Tashi tayi tafita tana kwalama fa'iz kira Umma tace amma abid idan akayi haka ba'ama sarah adalci ba Murmushi yayi yace Umma nasan zataji wani iri amma kuma hakan shine yadace Idan taga ahmad zai auri khadeeja dole tahakura dashi tunda tace batason kishiya " to shikenan amma gaskiya ba agidanka za'ayiba abun seyamata yawa Kusa da ita yazauna yana fadin ohhhh Umma kefa kikace duk hukuncin danayanke bakida matsala kuma tun ba'aje ko inaba kinfara complain Murmushi Umma tayi batace komai ba tana gode allah dayabata suruki irin abid Wanda yadauketa tamkar uwa Kallonsu Asma'u take da murmushi afuskanta tana jin wani yanayi datakasa fassara shi Daki tawuce khadeeja nabinta Abaya Rungumota tayi tabaya tace ammah I am so happy gaskiya AK daban ne what a wonderful surprise !!! Juyo daita asma'u tayi tana murmushi tace nima nayi farin ciki kanwata zata auri Wanda takeso Murmushi khadeeja tayi cikin sigar tsokana tace hmmmm kodai abunda kike ma farinciki daban ba ammah nahango wani Abu a kwayan idonki kamar kinfara son..... Bata karasaba asma'u tayi saurin fadawa bayi hade da banko kofar da karfi kamar mai tsoron akamata Dariya khadeeja tayi tafada kan gado tana ma allah godiya Mutanan gidan kowa nazaune apalo sarah da aysha suka sauko cike dafarin ciki aysha tace kushirya fa zamu sha biki ahmad ya amince zai auri sarah Carab grany ta amsa da fadin to in yakara guduwa fa Dariya akasa gabadaya Inna ameena tace nidai nashajin amarya tagudu ranan aure amma ango kam se akan sarah Bashir yace gaskiya wannan karon inyagudu za'afara tsoron sarah sadiya tace sedai muba dai cikin ma'aikatan mu ahasale sarah ta dakatar dasu akan zata gayama AK inyadawo bashiri sukayi shiru tashi AK yayi yama Umma sallama suka fita ita kuma tawuce daki kiran asma'u Suna bakin mota ta iskosu Bayn mota AK yashiga yana kallon ahmad yace muje ko?? dariya ahmad yayi yajuya yana fadin muje ina ?? Hahaha kuje dai ni sena gana da masoyiyata Kofar asma'u takama zata shiga yarike yana fadin malama ina zaki shiga Nan ...tafada tana nuna gefensa Harara ya watsamata yana nuna mata daga gaba kusan driver yace ga wurinki can inzaki shiga inbakyaso kuma dama kinsaba da hawa mashin Ganin ba alamun wasa afuskansa yasa tabude gidan gaba tashiga suka tafi [19/07, 16:58] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚 👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧 Na( *Maryam Mhd*) 1⃣1⃣0⃣ suna isa sarah tazo dagudu tarungumeshi tana fadin Yaya u are the best thank you so much Dagota yayi daga jikinsa yace banganeba why are u thanking me menayi karasowa wurinsu aysha tayi tana dariya tace hmmmm kana so kamana surprise ko to nariga nasani Ahmad zai auri sarah yanzuma daga wurinsa kake Kusa da grany yaje yazauana yana fadin Ahmad zaiyi aure amma khadeeja zai aura ba sarah ba kuma nariga nagama magana karnaji wani yace wani abu Cak sarah tatsaya tana kallonsa da mamaki bakinta bude amma takasa magana Juyawa tayi wurin asma'u dagudu tahadata da bango cikin gunjin kuka tana fadin wallahi basu isa ba sedai bayan ranta Saurin tasowa yayi yabanbaro sarah daga jikinta yana fadin sarah wai meyake damunki ne wai yaushe kika zama so stubborn ne Kwace hannunta tayi takara nufan asma'u tana surutai Fizgan hannunta yayi yanufi sama da ita yana zuwa dakinta ya wurgata kan gado cikin kakkausar murya yace wallahi kika kara tabata se nasabamiki what is wrong with u Da mamaki take kallonsa cikin rawar murya tace Yaya ...ni...akan waccan .. Katseta yayi dafadin ba laifinta bane sarah tayi kokarin hadaki da ahmad amma hakan baiyuwu ba ni nashirya auren dakaina badan nakuntata miki ba sedan kihakura da ahmad kinema wani Saurin dirowa tayi daga kan gadon tanufi hanyar fita tana fadin wallahi banyarda kai kayi hakan ba Yaya itace tashirya komai kuma wallahi bazan barta ba Janyota yayi tana kokarin kwacewa baisan lokacinda yadauketa dawani gigitaccen mari ba jikake tasssss Cak sukatsaya daga ita harshi kamar gumaka jadabaya tafarayi tana jifansa dawani irin kallo mai cike da mamakin abunda ya aikata Hannunsa yakalla sannan yakalleta yana matsawa kusa da ita cikin rawar murya yace sarah I am sorry bansan... Katseshi tayi dafadin karkatabani katafi kabani waje kai ba Yayana bane Yayana bai taba kai hannunsa ajikina danufin dukana ba Tabata yaje yi tayi saurin shigewa bayi hade da banko kofar da karfi tana kara fashewa da kuka Fita yayi daga dakin yanufi bangarensa Dakarfi yatura kofar yashiga hade dazama kan kujera yana dafe kai Kusa dashi asma'u tamatso adan tsorace tace Ya....sarah...take... is she ok... Girgiza kai yayi yace she is not amma komai zaiwuce dama nasan sarah zatayi abunda yafi haka idan tarasa ahmad Ruwa tazubomai mai anyi akopi tamikamai ahankali yakai hannu yakarba yasha sannan yamika mata sauran Zama tayi kusa dashi cikin siriruwar murya tace karka damu nasan tayi fushi yanzu amma zata sauko daga baya abunda zakayi shine kasamu wani Wanda kayarda dashi kasan zai iya jure wulakanci daga gareta kuma kasan yana sonta seka.... Katseta yayi da fadin se inyi me wai inhadasu aure ? nifa natsani hade haden nan.. Dawawa tayi gabanshi tazauna daga kasa tana fadin ha'an to kabari kaji mezan ce mana ai bangama ba Kauda kai yayi yace to inajinki Murmushi tayi tace yawwa idan kasamu sawrayin sekasan yanda zakayi kahadashi da sarah batare da saninta ba shi kuma kagayamasa idan har yana son kabasa auren kanwarka to seyanemi soyayyarta kafin nan Juyowa yayi yana kallonta yace to amma miye hikimar yin hakan Gyara zama tayi tana murmushi tace uhmmm kaga yanzu matukar sarah tana ganin ahmad kawai amatsayin saurayinta to bazata taba hakura dashiba amma idan taga Wanda yake haukan sonta tun tana wulakantashi tana koransa har tafara sawraronsa daga nan kuma bazama tasan lokacinda ahmad zai fita aranta ba Murmushi yayi yace wow!!! what a brilliant idea chitti dan kwalinta ta turo gaban goshi tana kauda kai tace ahh dabakaki saurarena ba Murmushi yayi yace hmmm I am really impressed amma kintaba soyayya ne Saurin joyowa tayi tana kallonsa tace no bantaba yiba banmasan ya akeyiba dariya yayi yace shiyasa naganki gaki ga kamarki amma wannan Ali din nagidanku ai nadauka saurayinki ne " ina ba saurayi na bane cousin dina ne da dai yaso ya aureni iyayenshi suka hanashi dariya yayi yace kice kema kintaba kwantai shiyasa kika samu experience akan rasa masoyi Hade fuska tayi tace allah ba kuantai nayiba kawaidai wai suna so ya auri wata yarinyane babanta yanada kudi to daga baya kuma yarinyar tafasa auren zaiyi magana kenan sukaji anturo kofa Aysha ce tashigo taci kwalliya tana taunan cingam Juyowa AK yayi yana kallonta yace ohhh hello babyyyyy!! Karasowa tayi cikin yanga tazauna kusa dashi tana hura hanci Kallonta asma'u tayi takwashe da dariya atare suka kalleta aysha na hade fuska Daure fuska AK yayi yace ke kinada hankali kuwa me akayi nadariya tashi tayi tawuce daki tana dariya hade fuska aysha tayi tace wallahi AK kasakema yarinyar nan dayawa tagama raina mutane Shiru yayi baice komai ba yana kallonta Da daddare AK na zaune bakin gado yana danna laptop ga Earp akunnensa yana jin waka se gyada kai yake yana bin wakar asma'u tashigo rike da coffee dinsa kan bedside drowa tadorashi tana fadin ga coffee dinka nan Baimasan tanayiba yamika hannu zai dauki wani Abu kawai yajishi cikin zazzafan coffee Yar kara yasaki yana yarfa hannun cike damasifa yace wayace ki ijiye anan baki gayamun ba Karasowa tayi tana duba yatsunshi tace bakajiba nace ga coffee dinka anan Kallon bakinta kawai yake yana motsi amma baijin metake fada Kuace hannunsa yayi yace dubawan me zakiyi bayan dagangan kikayi dakika kawo ai sekibani ko kigayamun "Wai bakaji menace bane "Jiki kawai bawani hakurin dazaki bani damamaki take kallonsa secan tahangi Earp akunnensa hannu takai tacire Earp din tawuce dressing mirror tana maimaita mishi abunda tafada dazu Painkiller tadauko takama hannunsa zata shafamai

Chapter 15 of 35