Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yashigo yana cire coat dinsa Ganin yanufo gadon yasa tayi saurin driwowa kasa tana zare ido Ko kallonta bai yiba ya ijiye coat din akan gado sannan yakalleta yana fadin kewai kallon namiye Ko kina tunanin zan kuana wuri daya dake ne idan kina bukata ta kibiyoni inda nake Kauda kai tayi tana fadin ba'abunda zanyi dakai so zaka iya tafiya Nasan kina so natafi dan kisamu daman zuwa wurin ahmad Sannan yamatso kusa da ita yace kina son ahmad ko? Eh... Tafada atakaice Girgiza kai yayi yace karya kike bazaki iya son kowa ba saboda kudi kawai kike so Matsawa tayi daga gurin tana fadin kai kuma bawanda zai soka saboda kanada bad altitude Dressing room dinsa yanufa yana fadin u will suffer nan gidan dakike kwadayin shiga seya zame maki prison saboda ba inda zakije Dakallo tabishi tana fadin idan dai har zakayi nesa dani badamuwa Juyowa yayi yana kallonta yace bakinki zai mutu ranarda nayi ball dake daga gidan nan ahmad ya auri sarah ni kuma na auri aysha Sannan yadawo kusa da ita yace kina mamaki kinji nace aysha ko to itace budurwata Tayarda na aureki ne dan tasan ko giyar wake nasha bazan fada sonki ba Dariya tayi tace ta amince ne saboda batasan me ake cewa so ba datana sonka dabata yarda ka auri wata ba Shiru yayi nadan lokaci kamar mai tunani can kuma yace tasan cewa kudi ne agabanki Kauda kai tayi ahankali tafurta ni bansan meyasa mutane suke haukan kana birgesu ba bayan ni kuma inaji kadameni Ahasale yace be quite kar ki manta agidana kike kuma adakina sannan yajuya yanafadin so yakamata ki girmama ni Itama ahasale tace kai kuma karka manta kana magana da matarka ne Juyowa yayi da mamki yana kallonta sannan ahankali ya furta mata?? Mata fa kikace?? To idan ma bacci kike kifarka wannan matsayin yafi karfinki kuma bazaki taba samunshi ba Nagaya miki this is just the beginning of ur suffering!! Kauda kai tayi tana fadin I am already regretting it Dariya yayi yace to ai baki maga komai ba tunda auren kawai kika gani senasa kin tsani kanki Karasowa tayi gabanshi tana fadin wai ma meyasa katsaya kana magana dani kamata yayi ace kana wurin budurwanka yanzu ni kahanani bacci katafi kawai gobe kaacigaba da cimun fuska nayarda nan din prison ne awurina all tnx to u Fita yayi daga dakin yana fadin u are welcome Dakallo tabishi sefa yafita sannan tadauke coat dinshi da ya ijiye akan gado tanufi dressing room tana mitar ta tsani taga kaya akn gado Cikin sanda AK ya sawko dwonstairs yanufi hanyar fita yana Satan kallon bangaren grany Har yakai kofa kamar daga sama yaji tace Abidi ina zuwa cikin wannan Daren Runtse ido yayi hade da cije lebe bai jiyowa ba kuma nai yi magana seda tace bada kai nakeba sannan ya juyo yana sadda kai irin na mara gaskiya Ganin ba wasa afuskar grany yasa ya kalalo murmushi yana Sosa kai yace grany zan dan fita ne ahmad yan jirana Daure fuska tayi tace ba inda zakaje wannan lokacin kamata yayi ace kana tare da matarka Buga kafa yayi da kasa kaman zai fashe da kuka yace haba mana grany bafa dadewa zanyi ba Amma bata saurareshiba ta tasa keyarshi seda taga yashiga bangarensa sannan ta juya tana masifa Asma'u har tayi shirin kuanciya cikin doguwar rigan baccinta har kasa mai kyew Taji anturo kofa Atsorace ta juyo ganin AK atsaye yasa tayi saurin daukan gyelenta ta yafa tana fadin Mekuma yadawo dakai... Tsaki yayi ya kauda kai yana yace daban ysaya fada dake ba dayanzu nafita amma gashi kinja zan bata lokacina anan Karasowa cikin daki Yayi yafara cire shirt dinsa afirgice takauda kanta tana fadin wai mekake shirin yi Kallon kin raina mun hankali yayi mata sannan yace kima daina acting kamar wata mutuniyar arziki bayan kinfi kowa sanin abunda nake shirin yi Sake kauda kanta tayi tana facing mirror tace abunda kake baka kyewtawa Karasowa yayi tabayanta yatsaya yana cire belt dinsa yace nan daki nane kuma ahaka nasaba kuanciya idan kinga bazaki iyaba zaki iya zuwa waje ki kuana ai bai gama rufe baki ba tayi waje aguje sedai tana fita ta tsinkayo grany tafito daga dakin sarah Saurin shan kuana tayi tadawo dakin tana rufe da idonta AK yana daga kwance kan gado ya lullube da bargo yarufe ido kamar mai bacci Sam baiji shigowarta ba Lalube tafara kan gadon tana Neman pilo by mistake ta taboshi Afirgice ya tashi yana bige hannunta Atsorace ta bude idonta tana Sosa inda ya bigeta Tsaki yayi yace to ke koda kinada bukata haka akezuwa ba notice Daure fuska tayi tadauki pilo tana fadin not interested Kwace pilon hannunta yayi yace wannan pilo nane kinema wani Dayan pilon tadauka hade da blanket takoma Palo kan 3sitter ta kuanta ta rufa da blanket din tana jin kewar Umma da khadeeja har bacci yafara daukanta taji AK na atishshawa Banza tayi dashi ta gyara kuanciyarta tana fadin alhakina kadai ma ya isheka Jin abun yayi yawa yasa tamike tanufi dakin Ahankali ta tura kofar tashiga Tana shiga taji AK nafadin to wai meke damuna ne ..? Remote din AC tadauka takashe sannan tanufi wurin kettle tadaura ruwa Damamaki yake kallonta yana fadin malama lafiya zaki kashemun AC wayasaki Banza tayi dashi seda ruwan yayi dumi sannan tazubo a cup ta kawomasa Damamaki yace what are u doing Kauda kai tayi tace kaina nakeyiwa saboda bazan iya yin bacci dawanan atishawar taka ba Karban ruwan yayi yana fadin ai daga yau kindaina bacci mai dadi sannan yakai ruwan bakinsa Da kyar yasha rabin Kofi ya mikamata sauran yana yamutsa fuska kin karba tayi tace idan bakasha dayawa ba bazaka warkeba Ijiye kofin yayi akasa yana fadin bazaki kasheni da ruwan zafi ba Daukan copin tayi tamaida tanufi hanyar tana fadin kuma kanemi kaya kasa kafin ka kunna AC Da kallo yabita seda tafita sannan yaje yakarasa hanye ruwan dumin dayarage yasaka riga ya koma cikin bargo Washegari dasafe...... Wayanshine keta ringing yana kwance yana bacci Jiyayi andafashi yariko hannun yana fadin baby I am not feeling well wannan yarinyar taban ruwan dumi naji dadinsu amma... Bai karasaba asma'u tamaka mai pilon dake hannunta Afirgice yatashi yana kallonta da mamaki yace mekike anan Dariya tayi tace mummunan mafarki kake ne Daure fuska yayi yana fadin kece mummunan mafarkina Wayarsa Tamika mai tana fadin dan Allah kadauki wayanka tadameni da kara Fizge wayan yayi ahannunta yana duba mai kiran Murmushi yakai wayan kunne yana fadin hi baby Tashi asma'u tayi tanufi dressing room Tadayan bangaren aysha cikin mryan shagwaba tace honey ina fata ba abunda yashiga tsakaninku Dariya yayi yace haba wa kema kinsan nafi karfin haka so kawai ki kuantar da hankalinki I only belongs to u Dariya tayi suka ci gaba da firarsu Sarah ce da AK zaune abangaren grany suna breakfast Can sarah tadago tace Yaya idan nasamu lokaci inaso zanyi tafiya Dagowa yayi yakalleta yace ina kuma zakije awannan lokacin Yaman ...nakeso naje akwai abunda zai kaini Sanin acan tayi karatunta shiyasa bai yiwata gardama ya amince Cike da farin ciki tace thank u Yaya amma kamun alkawarin bazaka kula wannan yarinyar ba Lomar abinci yakai bakinsa yana fadin kar kidamu ba abunda zanyi da wannan mai fuskan yara .. AK ne zaune ababban palon kasa yana kiran Nura dagudu Nura yakaraso yadurkusa yana fadin gani yallabai Kaje wurin grany ka karbomun coffee Washe baki nura yayi yace ai yanzu nafito daga can nabaro madam tana hada wa tace idan tagama zata kawo Wace madam din ... AK yafada cike da mamaki Sadda kai nura yayi yana fadin madam dai amarya Gyada kai AK yayi yana fadin takawo to ina jiranta Asma'u na bangaren grany tafaketa tana koyamata yanda akema AK coffee dan tace yanzu yayi aure bazata iya wahalar hadamai kofee so uku arana ba Kayan kanshi tadibo tazuba Damamaki asma'u tace kayan kanshi a coffee kuma grany Eh haka yake sonshi se kisa ido sosai ki kula Bayan grany tagama hadawa tabata takaimasa Yana zaune ta iso da coffee din a cup tadoreshi kan dan karamen faranti da teaspoon agefe se kanshi yake Grany nadaga nesa tana kallonsu amma baiganta ba Karban cup din yayi ya kurpa Saurin furzarwa yayi yana fadin wannan coffee ne kome Anya ma kintaba hada coffee kuwa Dawannan bagara naje nasaya natiti basha ba mema yasa grany bata hadamun ba se ke Karasowa grany tayi tana fadin Abidi dagaske baiyi dadi ba amma ai haka kake sonshi shiyasa nayishi haka kuma baka taba cewa baiyi dadi ba se yau Da mamaki yake kallonta dan Sam baisan tana wurin ba baki yawashe yana fadin haba ai ina dandana shi nasan ke kikayi yayi dadi sosai Daure fuska tayi tace to meyasa kakema asma'u magana haka badadin ji Dariya yayi yace grany mufa ma'aurata ne zamu iya tsokanar junanmu yana kara dankon kauna To shine kuma seka fara mata tunda sassafe Satan kallon asma'u yayi yana fadin saboda inaso itama ta iya Wanda yafi naki dadi shiyasa nakushe Wanda takawo Amma kiyi hakuri grany bazan karaba Murmushi tayi tace ba komai kudai kuhada kanku kuzauna lafiya kar kuji jiya yanda ake yabon Ku wallahi har cikin raina naji dadi Abidi dan Allah karike yar mutane amana kaji Tashi yayi yanufi sama yana fadin idan ma dan wannan ne saranki a inuwa grany Zaunawa asma'u tayi kusa da grany sukaci gaba da feransu Inna ladidi ce tafito tazauna asma'u tagadaita Bayabo ba fallasa ta amsa mata gaisuwar Sannan take gayama grany sunyi waya da aunty sadiya tace suna hanya yau zasu dawo Bashir ne yashigo ya zauna daga kasa kusan asma'u yana fadin matar yaya kintashi lafiya Lafiya kalau tafada tana murmushi Sannan yajuya yana kashema grany ido yace kin iya zabe nima kisamo mun Jifanshi tayi da pilo tana fadin kadai karata can akan yan matanka bazan kawo maka yar mutane kakasheta ba Dariya yayi sukaci gaba da firansu banda inna ladidi datadaure fuska Da yamma misalin karfe biyar su uncle jamilu suka iso Bayan sun huta anyi sallan magriba grany ta aika kiransa Yana zuwa ya gaidata yana washe baki yasan bai wuce zancan auren AK da aysha ba Sedai ga mamakinsa yaji sabanin haka yafara banbanmi yana masifa grany ta taka mai birki tace yaje ya tuhumi yar'sa ita taki amincewa auren tunda fari dahaka bata faru ba Ahasale ya banke kofar yafita bangarensa yanufa yana kwalama aysha kira Tana dakin aunty sadiya tana karban tsarabarta Atsorace tafara yarfa hannu tana fadin wayyo nashiga uku Dakin ya iskota yana zuwa yadaka mata tsawa yana fadin wane kalan shirme naji abakin grany wai ke kika ki auren AK hakane Atsorace tace abba yi hakuri amma ai daga baya nace nahakura amma ya..... Bata karasa ba taji saukan mari Dafe kuncinta tayi hade dafashewa da kuka Saurin rikota aunty sadiya tayi tana fadin lafiya abban aysha yau Kaine da Marin aysha meyake faruwa ne Fizgo aysha yayi ahnnunta danufin kara mata wani tayi saurin rike hannunshi tana bashi hakuri tace ya tsaya ya saurareta sakinta yayi yana fadin to gayamun meyafaru Nan tagayamishi cewa grany ce tazaba AK wannan matar amma shi baya sonta ita yakeso kuma har yanzu suna tare yamata alkawarin zancan aurensu yana nan wani dogon tsaki aunty sadiya taja tana fadin ni dama wallahi najima da sanin tsohuwarnan bason auren yaran nan take ba taga zamu samu abun arziki bari takawo yar uwarta saboda suji dadin cin dukiya to wallahi bata isaba Girgiza kai uncle jamilu yayi yana cije lebe sannan ya dafa kan aysha yace sorry baby raina ne yabace kinsan yanda najima da borin ganin kin auri AK to kuma lokaci guda naji bai aurekiba ya auri wata can daban kinga ai bazanji dadiba amma dakika mun bayani naji dadi kuma namiki alkawarin idan dai ina raye se mun cimma burinmu Murmushi tayi tarungumeshi tana fadin ba komai dady Daganan yanemi ganin matar AK Suna babban palo tafito tagaidasu aunty sadiya ce kawai tadaure fuska amma uncle jamilu Da far'arsa suka gaisa har yana tsokanarta wai tayi kama da yan India Hakan yabata mamaki matuka ba ita kadaiba har grany tayi mamakin yanda tasan jamilu da bakar zuciya taya yasakema asma'u Koda dare yayi asma'u tahadama AK coffee dakanta takaimasa tas yashanye shi har yana mitar takamasa dan kadan wayasanima ko ita tashanyeshi Bata kula saba tadauki pilonta da blanket tanufi Palo """ Urs......✍ πŸ‘©β€πŸ’»Maryam Mhd [18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š πŸ‘¨β€πŸ‘§ _DOMUN KANWATA_ πŸ‘©β€πŸ‘§ Na( Maryam Muhammad jibril) 7⃣5⃣ Washegari tunda yadawo daga sallar asuba ya wuceta akuance apalo tana bacci hankali kuance ga darduman datayi sallah nan agefe Har ya wuce daki se kuma yadawo kan daya daga kujerun palon yazauna sannan yadauki remote ya kunna TV Tana jinshi tayi banza dashi taja blanket tarufe kanta Kura volume din yayi karshe Bubbuga kafa tafara yi kaman tafashe dakuka ta tashi tana fadin wai miye haka dan Allah Daure fuska yayi yace yarinya tunda kika auri dan Babban gida to kinkare da baccin safe Kuma nan palona ne inada damar yin abunda naga dama aciki Tashi tayi tana mutsitstsike ido tanufi ciki tana gunaguni Bayi tanufa tayi wanka tasaka doguwar rigarta ta less mai kyew sannan tayafa gyale tafito Inda tabarshi anan ta iskoshi yana gyangyadi Fita tayi batare da tasake kallonsa ba Yana ganin tafita ya kashi TV yanufi daki yana hamma Babban kitchen din gidan tanufa Nan ta isko ma aikata nata aiki abinci kala kala an juyewa akula Wurin wata dattijuwa tanufa tagaidata Damamaki matar ke amsa gaisuwarta Bayan sun gaisa tace baba meyasa ba ajera abincin a dining ne Tabe baki tsohuwar tayi tace haka suke yan gidan nan sedai aje atambayi kowannensu meyakeso sannan akaimasa inda yabukata Gyada kai asma'u tayi sannan tafita Bangaren grany tanufa bayan tagaidata tace grany ni kwa meyasa ba ahaduwa wuri guda aci abinci ne tunda akwai Babban dining table din dazai dauki gaba daya yan gidan nan Dariya grany tayi tace hakane fa asma'u kinka shawara me kyew kinsan balokaci guda ake tashi agidan nan ba shiyasa amma yau insha Allah zanyi musu magana za'arika haduwa ana cin abinci Nan tazauna bangaren grany tashari baccinta se Tara ta farka kamar ance taduba dining kawai tahango mutum azaune yana breakfast Kuada kai yayi kamar bai ganta ba Fuska tayi itama tana gyara gyalenta da yafadi Grany ce tafito tanufi da murmushi afuskarta tace albishirinku Shiru AK yayi se asma'u ce tace goro fari grany Wata takarda Tamika ma AK tace ga visan kunan yafito nashirya muku honeymoon zuwa kanada Afirgice AK yace honeymoon kuma grany Eh .... Tafada tana daure fuska Ko bazaka bane Sadda kai yayi yana fadin gaskiya grany inada aiki agabana banada lokacin wani honeymoon Daure fuska tayi tace. To shikenan tunda ban isa nasaka Abu kamun ba dama can ina zargin baka kyewtatama yarinyar nan dan kaganta shuru shuru to wallahi kaji tsoron Allah Harara ya jefama asma'u yanaji kaman yashakota Shikenan grany zan je amma gaskiya kanada yayi nisa kuana hudu kawai zamuyi yanzu dai zamu fara zuwa Lagos inyaso karshen watannan semuje honeymoon din Baki tawashe tace ba komai ni dama sunake kusamu lokaci Ku kafahimci juna Tana kainan tayi gaba abunta Tashi yayi yafita yana kallon asma'u aransa yana fadin nasan ke kika cusa ma grany wannan ra'ayin inba haka ba ina tasan wani honeymoon Yana bangarensa azaune aysha tashigo tana zunbura baki tace wai dagaske honeymoon zakuje Tsakai yayi yace wane honeymoon niba inda zanje dawannan yarinyar ai se arainani To yazakayi da grany I have a plan yafada yana leken kofa Khaddeja lafiya kince kina son ganina Eh hakane Tarzan abunda muke zargi gaskiyane Haba dama nafada maki ni nasan ba banza ba kawai zanje nasamu AK inji akan wane dalili zai cutar da baiwar Allah akan wani selfish reason dinsa Dakatar dashi tayi dafadin a'a idan kamishi magana zaije ya sauke akan yayata ne mafita dayace Wacce kenan Ka auri sarah !!! Na aureta fa kikace khadeeja bayan kinsan bana sonta Amma ai kai kace mun zaka iya yin komai dan farin cikina nikuma farin cikin yayata shine nawa idan har ka auri sarah nasan AK zai daina muzguna mata zasu zauna lafiya Girgiza kai yayi cike da damuwa yace khadeeja nasan waye AK bazai taba son asma'u ba Ni kuma nasan yayata abune mai sauki tasa yasota kuma ni nafada maka wannan Idan har kana sona da gaske to ka auri sarah idan kuma bahaka kawai kamanta dani kar kakara nemana kafita daga rayuwata Tana kai nan ta juya ta tafi tana share hawayen fuskarta Dakallo yabita yakasa koda motsa yatsar sane Tafiya take tana kukan bakin ciki har tabacema ganinsa Grany ce ta tasa AK agaba akan seyaje da asma'u tayi ma su Umma ban kuana tunda gobe ne tafiyarsu Ba yanda ya iya haka yasa driver yajasu suka tafi gidan inna suka fara zuwa sunsamu tarba mai kyew abba ma yadawo suka gaidashi cike da fadin ciki yake kallonsu yanama Allah godiya dayaba asma'u miji nagari Sunjima agidan sannan suka nufi gidan Umma Dagudu asma'u tashiga gidan tana kiran umma !!! Umma!!! Fitowa Umma tayi da mamaki tarungumeta tana tambayar asma'u kece yanaganki haka kuma Bayan AK yashigo sun gaisa yake gayamata zancan tafiyarsu tayi farinciki sosai tamusu addu'a Fita yayi waje yana jiran asma'u tafito Khadeejace tazo shiga gida kamar daga sama tagansa akofar gida Tagefensa taraba tawuce amma batace komai ba Se yaji duk baiji dadin ganinta haka ba kamar yamata magana se kuma ya kyaleta Tana shiga asma'u tazo da gudu ta rungumeta Cikin sassanyar murya khadeeja tace ammah ya kike Lafiya kalau asma'u tafada tana mata alama fa kar Umma tagane Tadan jima agidan kafin da kyar Umma ta fito da ita waje tace tabar mijinta na jiranta tundaga gida sukayi sallama da khadeeja tana mamkin ina AK zai kai asma'u Umma ce tarakota har wurin mota sannan Tamika mashi wata leda tace gashi tashice zatamai anfani Godiya yamata sannan sukabar kofan gidan Seda suka biya wurin Momy itama suka gaidata amma basu sami ahmad agida Momy tafuskanci akwai matsala atsakaninsa da ahmad kamar tayi magana sekuma tayi shiru Tace intayi tsami maji Sundan jima awurinta sannan suka fito sunzo fita sukaci karo da ahmad zai shiga gida kauda yayi kaman bai gansu ba ya wuce ciki AK baiji dadin hakan ba amma yasan komai zai wuce Ahanya yabude ledar yaciro abunda ke ciki Wata sweater ce mai kyew irin tasakannan Rigan tabirgeshi amma kawai dan Neman tsokana Yadaga rigar sama yana fadin wai ni Umma zataba wannan rigar ai sedai ingoge window da ita Nan take fuskan asma'u ya canza idonta ya cicciko da hawaye cikin muryan kuka tace Umma fa tasakata da hannunta she gave it to u with love amma zaka fadi haka takarashe maganar tana fashewa da kuka Damamaki yace ohhh to ai ni bansani ba nadauka takice ai Batace komai ba taci gaba dasharan kwalla Leko fuskanta yayi yana fadin wai kuka kike Kauda kanta tayi batace komai se sheshshekar kukanta dake tashi Dafe kansa yayi yace dan Allah kiyi shiru natsani kuka arayuwata sannan yadago yakalleta yace idan ma jira kike nabaki hakori to gara ma kiyi shiru Nan madai bata daina kukan ba Yacema driver yayi playing music Ai kamar yakara mata kukan ne Bashiri yace yakashe Cikin sassanyar muryan dabata taba zaton yanada ita ba taji yace ok I am sorry rigan tayi kyew kuma ina sonta kawai dai nafada ne Damamaki tadago takallesa yayi saurin kauda kai kaman bashi yayi maganr ba Shiru tayi tana share hawayenta Daga nan bawanda yayi magana har suka karasa gida Suna isa yaran inna ladidi salma da amir suka zo dagudu suka rungumeshi Rungumesu yayi yana dariya yace yaushe kuka dawo Atare sukace dazu mukazo grany tace kamana aunty ina take Bayansa yanuna musu yana fadin gatanan zuwa Aguje suka je suna mata oyoyo Washegari tunda safe suka shirya sukama grany sallam suka fito kallon aysha yayi yakashe mata ido dariya tayi tana rufe bakinta datafin hannunta dan kar agane Driver ne kejansu basuyi tafiyar awa dayaba suka iso Barcelona hotel bayan yayi parking AK yafito yana mika sannan yaleka yacema asma'u to ai sekifito ko hajiya Fitowa tayi tana zunbura baki Bude but yayi yaciro akwati daya yayi gaba baice komai ba Dayan akwatin tadauka Tabi bayansa tana fadin inane nan kakawomu Airport.... Yafada atakaice Daure fuska tayi tace I am not a fool Murmushi yayi yace nasan dai baki taba shiga jirgi ba wannan ne karo nafarko Shiru tayi batace komai ba Wurin reception yanufa yana fadin jirani anan bari nakarbo mana passing cards dinmu Dakallo tabisa har yaje yakarbo makullin daki yadawo ya dauki akwati ya nufi wata hanya yana fadin muje karmu rasa flight Tsaki tayi tace wai mekadaukeni ne ko angayamaka banyi makaranta bani Wani daki yakaita bayan sun shiga yace Yarinya anan zakiyi honeymoon dinki kuana hudun nan se sunzame maki tamkar shekara 4 anan wurin Zama tayi bakin gado tace Tunda dai karaboni dawancan gidan kabiyani dama zaka barni anan har natsawon rayuwata da ina so Jan dayan akwatin yayi yafita yana fadin natafi wurin masoyiyata idan kina son wani Abu karki kirani Tasowa tayi tarufe kofar tana fadin Allah raka taki gona Bai kulata ba yayi gaba abunsa Farm house dinsa yanufa yana isa kiran aysha nashigo wayarsa yana dagawa tace ya ake ciki Dariya yayi yace yanzu na ijiyeta ahotel anjima zanzo To meyasa bazakazo yanzuba a'a kinmanta yaw Sunday inada program senagama zanzo Kashe wayar tayi tana wani malalacin murmushi tace zanyi farin ciki idan Maman asma'u takalli program dinka nayau zatasan karya kuke ba inda kukaje Yaronsa nagidan mai suna sani yakira yace ya Ciro mai akwatinshi abayan but Yana fito da akwatin AK yace Bude zakaga wata bakar jaket asama kabani Dariya ce ta kwacema sani yayi saurin danneta yana fadin yallabai wannan ai kayan matane a akwatin afirgice yace what !!! Dafe kansa yayi dayatuna yabar akwatinsa ahotel yadauko na asma'u Asma'u nafitowa wanka ta janyo akwati tabude Ido tazaro ganin kayan AK a akwati Gashi tariga tawanke nata yazatayi Hakanan tadauki kayansa tasaka Murmushi sani yayi yace hakan yana faruwa akan masoya yallabai Keep quite dan Allah!!! Shiru sani yayi yana danne dariyarsa Makullin mota yakarba ahannun driver yashiga aguje yabar wurin Yana isa yafara bubbuga mata kofa Tana kunce tasa eyepiece akunne tana bacci Yajima yana bugawa amma bata budeba gashi lokaci natafiya dole ya karbo spare key yabude dakin Bakin gadon yakaraso yana mamakin ya akayi bataji karan buga kofar ba eyepiece din yaciro yasa akunnensa yagirgiza kai yayi yana fadin shiyasa kagi nan ahargitse Kamar ance tabude idonta atsorace ta tashi zaune tana fadin wai meya dawo dakai kuma Damamaki yake kallon rigar dake jikinta Blanket din yafara janyewa yana fadin bala'i badai kayana kika sakaba Rirrike blanket din tayi cikin muryan mai shirin fashewa dakuka tace wai me kakeyine haka bakai katafi dakayana to mekakeso insa Wayanshine yafara ringing tsaki yayi yadaga yana fadin wallahi kicremun kayana kinji nagayamiki To idan nacire mezansaka haka zan zauna Dip nunfashin aysha yadauke sandarewa tayi awurin takasa cewa komai AK yayita hello hello yaji shuru wurgi yayi dawayan kan gado yana kallon Asma'u yace dakinsan tsadan rigarnan tajikinki to ko biyanki akayi bazaki sakata ba Yau inada program kuma ita zan saka dan haka cireta Cikin rawar murya tace to kabani tajikinka se inbaka wanna Cire rigarsa yafara yi tayi saurin kulle idonta tana fadin wai meyasa bakada kunya ne Jefo mata Rigan yayi yana fadin yi sauri banda lokaci Bayi tanufa tasanyo rigar tafito masa da waccan Fizge rigan yayi ahannunta yasaka yana mata dariyan yanda takoma acikin kayanshi Daure fuska tayi tana tattare wandon dayamata yawa Akwatinsa ya ja yana fadin kice abunda kike so kisha abunda kike so ki kalli abunda kike so Abu daya ne bazaki samu ba saurayinki ahmad dan tun aranar nasan yagama dake Kauda kai tayi tace eh naji dan Allah tafi Rigan jikinta ta shinshina tana yamutse fuska Fita yayi daga dakin yana fadin dakayannan zaki kare kuanakin ki anan Seda yafita shima ya shinshina rigar jikinshi yana yamutsa

Chapter 10 of 35