kusa da ita tana dafata tace ammah meyasameki meyake damunki ne yaushe kika fara boyemun damuwarki ..
Ganin asma'u takasa bata amsa yasa tamike tsaye tana jifan Ali dakallon tuhuma cikin wata iriyar murya tace mekamata tunda naganta awannan halin natabbata kamata abunda yafi karfin tunaninta
kauda kai yayi dan tuni kukan dayake dannewa yaci karfinsa cikin kukan yake fadin
deeja ni kaina bansan meyake faruwa ba jiya wannan yarinyar aysha tagayyaceni gidansu wai nazo tana son ganina ta amince dani dafari ban yardaba amma tunda ta turomun wasu banzayen pictures da videos dasuka sa narasa natsuwata kawai naji ba abunda nakeso irin na ganni kusa da ita amma wallahi banje gidan dawata manufa ba ...
katseshi asma'u tayi dafadin wannan zancan banza kake Ali idan har wurin aysha kaje dagaske meyakaika dakina akan gadon mijina what kind of rubbish is that
dafe kansa yayi yana fadin yes nasan nashiga daki amma bansan ko nawaye ba karki manta ni bako ne ita tamun kuatancen dakin tace mun natane nasameta acan amma ni bansan cewa dakinki bane kuma kema kinsan ba halina bane ...yana kainan yawuce cikin gidan rai bace
tunda yafara magana khadeeja kebinsa da ido tana jin zancan nasa banbanrakwai dan basosai ma takejin meyake fadaba saboda yanda maganar ke fita dakyar daga bakinsa
Durkusawa tayi tana share mata hawaye cikin sassanyar murya tace ammah dan allah kigayamun meyake faruwane ko naje nagayama Umma ne
a'a muje kirakani gida zan gayamaki...
fita sukayi daga gidan akan hanya take bama khadeeja labarin duk abunda yafaru har lokacinda AK yabata natakawo masa shaida ko tabar masa gida
takare zancan dafadin khady wasu lokutan baka sanin yakake ji agame damutum se karabu dashi bansan miye so ba bantaba yiba amma inada tabbacin abunda nakeji agame da ABI shine so kowa da yadda kaddarar soyayyarsa take zuwa masa arayuwa amma ni tawa inaga bata zomun a saa'a ba
ajiyar zuciya khadeeja tasauke datagama jin bayanin yayartata
cike da tausayi tace ammah inaga AK yabullo dawannan hanyar ne dan yasamu yarabu dake cikin sauki batare da anga laifinsa ba dama Yajima yana Neman hujjar dazata sa yasakeki to bare yanzu dayasameta ahannu gashi kuma grany batanan
kawai kisa aranki ba abunda zai faru sai alkhairi idan rabuwa kukayi ma kidauka hakan shine yafi maki alkhairi tunda dama can ba wani dacewa kukayi ba tunda bazaman aure kuke atsakaninku ba
Murmushin dayafi kuka ciwo asma'u tayi tana girgiza kanta tace khady bazaki gane bane nasan bazaman mata da miji muke dashiba amma kuma inason zama dashi ahakan duk danasan cewa hakan ba mai yuwa bane saboda banada wata shaidar dazata hana faruwar hakan
Shiru sukayi kowa da tunanin dayake aransa har suka isa gida seda khadeeja tarakata har bangarenta sannan tamata sallama akan se sunyi waya anjima
Tana fita tahadu da AK zai shigo nufota yayi yana fadin ohhh hi little sis yaushe kikazo
Tagefensa tabi tawuce batako kallesa ba bare yayi tunanin zata amsa masa
saurin shan gabanta yayi yana murmushi yace wait wait deeja ba fada me yakawo gaba ko baki ganeni bane nine fa ....
katseshi tayi dafadin Yaya wai ya kake acting kamar bakasan mekayi bane karo nafarko nahango rauni da kasawa a idanuwan yayata kuma duk tadalilinka
yaya bansan ya kagansu ba maybe atsaye ne ,azaune ko akuance wuri guda abu daya nasani shine koda mutanen duniyar nan gaba daya zasu taru su zargeta akan wannan abun to ni khadeeja (tafada tana nuna kanta dayatsa )
Zan shaideta akan bazata taba aikata makamancin wannan kazamin aikin ba
hawayen fuskarta tashare sannan cikin rawar murya tace Yaya gatanan kayimata abunda kaga dama amma kasani idan har wani abu yasameta tadalilin wannan case din to nmbanajin zan taba yafemaka
tana kainan tayi gaba abunta tana gyara fuskarta dayajike dahawaye
dakallo yabita yana murmushi har tafita sannan yawuce ciki
apalo yazauna yana kallo can anjima asma'u tazo zata wuce yakirata nan take taji gabanta yafadi dan tasan baiwuce zaimata tuni da lokacinda yabata bane
Jiki asanyaye takaraso wurinsa daga gefe tazugunna tana jira taji mezaice
Bring my coffee.... yafada batare dayakalleta ba
da mamaki tadago tana kallon fuskarsa bayabo ba fallasa juyowa yayi yakalleta suka hada ido tayi sawrin sadda kai kasa tana murza yan yatsunta
kureta yayi da ido nadan lokaci sannan yace matsalarki ta tashi daga kan ido takoma kan kunnene kome nace kikamun coffee dina ko bakijiba
saurin tashi tayi tafita ba'adau lokaciba tadawo dauke da coffee din sedai ta isko aysha apalon tana zaune kamar zata shigemai jiki se fira suke suna dariya
Mikamasa coffee din tayi tana daure fuska bata ma yarda tasake kallonsuba
Kin karban coffee din yayi ahnnunta seda yaga tana kokarin ijiyewa sannan ya karba yana kallon fuskarta yace yanaga kin dame fuska ne tunda saurayinki zai iya zuwa wurinki to miye dan budurwata tazo wurina
saurin juyawa tayi zata bar wurin yacabko hannunta cak tatsaya batare datajuyo ba shima kuma bai janyota ba cikin murya mai kaman rada yace inafata baki manta yanda mukayi dakeba
"ban manta ba
"zuwa gobe idan har baki kawomun ba zaki tafi gida
share hawayenta tayi da dayan hannun batare data juyoba tace
yaune ba gobe ba saboda haka yau din zantafi
Murmushi yayi shima batare da yadago yakalleta ba yace gobe zaki tafi saboda naga alama kinada bukatar Karin lokaci
shiru tayi batace komai ba dan tana bude bakinta kuka ne zaifito da kyar ta iya fadin free my hand
sakin hannunta yayi tawuce daki ta rufo kofar tana sulalewa awurin tasaki kukanta mai ban tausayi
cike da bacin rai aysha tace AK bangane ka karamata lokaciba ko shekara zatayi batada wata shaidar dazata gabatar garama kawai kabarta ta tafi
Juyowa yayi yana kallonta yace ya akayi kikasan bazata taba samun shaida ba tukunna ma ya akayi kika San inda maganar mu tadosa bayan nidai nasan bamuyita dakeba ko ita tagayamaki
Saurin girgiza kai tayi atsorace dan se alokacinma tagane subutar bakinda tayi
Da daddare asma'u tafara hada kayanta tana sakawa a akwati har wannan lokacin bata bar kuka ba rigar AK tagani acikin drowarta wacce ta taba sakawa a hotel dawkota tayi tadawo bakin gado tazauan tana tunano dramar dasukayi ranan rungume rigar tayi tanashakan kanshin turarensa hawaye na tsere akan kuncinta
jin anturo kofa yasa tayi saurin ijiye rigar tana share hawayen fuskarta
karasowa yayi bakin gado yana daga rigarsa yana murmushi yace ohh my favorite shirt kallon asma'u yayi cikin sigar tsokana yace ina data dai ba saceta zakiyi ba
kauda kai tayi batace komaiba
Ijiye rigar yayi saman akuatinta yana fadin ok I understand zakiyi missing dina shiyasa kike bukatar wani abu nawa dazaki rika tunawa dani ko
Runtse idonta tayi tana damke bedsheets dakarfin gaske aranta tana fadin yes zanyi missing dinka ABI amma bana bukatar abunda zai tunamun dakai saboda bazan taba mantawa dakaiba
Dawkan gyalenta yayi yana dariya yace nima kinga sekibani wannan lippayan taki dan inrinka tunawa dake ...yakarashe maganar yana labace baki irin nayara
kwace gyalenta tayi tana fadin bazan badaba mezakayi dashi kuma ba lippaya bane gyale ne
hannu yakai zai dauka tayi saurin rufe akwatin tana tureshi daga wurin tace ABI dan allah kabarni kar kakara tabamun kayana
Dariya yayi yace chitti tsaya mana miye nafada kuma muda zamu rabu gobe kinga kin huta dani kamata yayi yau mukuana muna fira tunda itace ranar karshe awurinmu
turasa tayi har bakin kofa tana fadin jeka banaso ko yanzu kabarmun abubuwa da dama dabazan manta ba ya isheni haka
bude hannayensa yayi yanufota yana fadin chitti I'm gonna miss uuuuu
saurin turasa tayi tana rufe kofa tana share hawaye tadawo tacigaba da hada kayanta
Dakin sarah yanufa ya iskota zaune da aysha suna fira zama yayi akaci gaba dafirar dashi
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣3⃣5⃣
washegari dasafe.....
daki tashigo rike da coffee din AK cikin flax da mug tadoroshi akan faranti har wannan lokacin tana hawaye jikinta gabadaya yayi sanyi kan bedside drawer tadorashi tana kallon photon AK dake ijiye awurin yana sanye da faran shirt da murmushi afuskansa yayi kyew sosai
ahankali takai hannu tadauki frame din tana murmushi tashafo fuskansa hawayenta nadiga akan frame din
rungume photon tayi akirjinta tana runtse idanuwanta hade da cije lebenta nakasa hawaye na tsere afuskanta
zama tayi bakin gadon tana kallon photon cikin rawar murya tace
ABI meyasa bazaka yarda daniba ABI nasaba dakai meyasa kake kokarin nisantani ga gareka lokacinda nafi bukatarka arayuwata
tayu natakuraka kana so karabu dani kodan ka auri wacce kake so
ABI it's very difficult for me to leave without u
Sarah ce taturo kofar dakin tashigo tana nunata dayatsa ta kwashe da dariya
saurin juyawa tayi da mamaki tana kallonta
karasowa tayi tadafa kafadanta sannan tasa yatsa tatabo kwallan dake kuncin asma'u cikin murya mai kaman rada tace
ohhhh abun ba dadi ko ?
nataba shiga wannan halin amma bawanda yadamu dahakan bawanda ya tausayamun bawanda ya rarrasheni
saboda haka kema kiji abunda naji
cike da mamaki tace sarah wannan wace kalan banzar magana kike gayamun
Dariya tayi tace kima gode allah kinsamu mai gayamiki banzar magana ni kallon banza ma bansamu wanda yamun ba
Idan baki manta ba nayi alkawarin senasa kin zubar da kwalla kamar yanda nayi I always keep my promises
ko baki fada ba nasani AK yasakeki saboda naga lokacinda yabaki takarda dasafe karki bata mana lokaci kitashi ki fice daga gidan nan kafin AK yadawo yasameki
Tashi tayi tafita daga dakin tana fadin idan kinje gidanku kyayi kukan da hujja
dakallo tabita har tafita tana takaicin hali irin na sarah
rungume photon tayi dakarfi tana fashewa dakuka mai cin rai tajima ahaka sannan da kyar ta tashi tana rike da frame din tasaka shi a akuatinta sannan tadauki farar takardar da AK yabata kafin ya fita tasaka ajakanta tana karema dakin kallo tafita kamar wacce batada jini ajikinta
ahankali take takunta tana janye da trolley dinta har ta iso palon kasa
azaune ta isko sarah da aysha suna jiran sakkowarta suna ganinta suka hau dariya suna gayamata bakaken maganganu
Dariya aysha tayi tana kallon asma'u taje sarah anya kwa bazamu duba akwatinnan ba kinsan halin yan can...
dariya sarah tayi tamike tanufi wurin asma'u tana fadin aysha ni bandamu da me tadauka ba kawai dai tabarmana gida shine damuwata
Jan hannunta tayi tanufi hanyar fita da ita itadai asma'u jikinta gaba daya yayi weak tamakasa magana ita abunda yadameta daban fatanta tasamu damar dazatama AK kallon karshe gashi rabonta dashi tunsafe
dakarfi sarah ta turata waje yar kara tayi zata fadi kawai tajita akan kirjin mutum
lumshe ido tayi tana shakar kanshin turarensa mai kuantar da hankali
Janyeta yayi daga jikinsa yana maidata gefe
su grany dake bayansa suka karaso dasauri suna tambayar meyafaru
Dagudu taje ta rungume grany tana fashewa da kuka
atsorace grany tarikota tana fadin asma'u lafiya menene ganin takasa bata amsa yasa tajuyo tana kallon sarah tace ke wai lafiya meyake faruwa ne
daidai lokacin khadeeja takaraso wurin tana riko asma'u tace ammah mesuka miki kike kuka kigayamun idan sun miki wani abu
karasowa sarah tayi ta finciko asma'u tana fadin karma ganin grany yasa kigara tunanin zakici gaba dazama anan gidan wallahi se kinfita tunda....
bata karasaba khadeeja tadauketa dawani wawan mari tana nunata dayatsa cikin kakkausar murya tace
Mind ur business winch gidannan ko rayuwarta ce aciki zata barshi saboda ba farin ciki acikinsa amma kibari mai gidan ya koreta bake ba
Kai wai meyake faruwane .....
Grany tafada tana daka musu tsawa
ahasale sarah tace grany barin gidan zatayi saboda AK yasaketa dalilin kamata dayayi tana cin aman....
Bata karasaba AK yadaka mata tsawa yana fadin sarah shut up
Juyawa sukayi gaba daya suka kallesa banda asma'u dakanta ke kasa tana murza yatsunta dakarfi har tana jin zafi
karasawa wurinsa sarah tayi tana riko hannunsa tace Yaya meyasa zanyi shiru bayan abune dayazama dole kowa yasani
Kuace hannunsa yayi cikin kakkawsar murya yace bai zama dole kowa yasani ba saboda duk abunda yafaru ba gaskiya bane kawai munzargeta ne akan abunda bata aikata ba
Saurin dagowa asma'u tayi tana kallonsa da mamaki
Haka ma sarah take kalkon asma'u da mamki tace yaya kamar ya bata aikata ba takawo maka shaidar ne
kallon grany yayi yafara bata labarin duk abunda yafaru sannan yakare dafadin
daga baya nagane duk plan ne shiryashi akayi dan afitar da ita daga gidan kuma bakowa bane yashirya se sarah
Yana fada yana nunata da yatsa atsorace tadago tana kallonsa da tsananin mamakin ya akayi yasan haka
Aysha kuwa jitayi kamar taruga da gudu saboda tsoro amma jin an ambaci sunan sarah yasa tasauke ajiyar zuciya tana lumshe ido
Juyowa sukayi gaba daya suna kallonta
Cike datakaici yace kinyi mamakin ya akayi nasani ko to kisani ita karya fure take bata ya'ya
Kwarai dafari nayarda cewa ta aikata hakan kuma nayi niyyar idan har bata kamun shaida ba zan saketa saboda Sam naji banason ganinta na tsaneta amma daga baya nasamu shaidar data nuna mun cewa sharri aka mata ke kika shirya komai dan kicimma burinki na korarta daga gidannan
Wayarshi yaciro daga aljihu yamika mata yana fadin gashi idan baki yarda ba zaki iya dubawa
Idan Baku manta ba ranar da su grany zasu tafi amir yana yawo da camera yana daukan video sarah takoresa daga wurin dan bataso yana daukanta
Shi kuma ganin haka yasa yaje dakinta ya ijiye camerar jiya bayan nadawo daga masallaci na iskoshi apalo yana kallon video din ranar dayadauka yana ganin nazauna yamika mun laptin din yace inkalla
Ban kulashiba saboda alokacin ina cikin damuwar abunda yafaru har zanrufe laptop din kawai naga abunda ya birkita mun tunanina lokacinda sarah take take bama aysha labarin yanda tashirya plan dinta
I was shocked saboda ban taba tunanin sarah zata aikata irin wannan kazamin aikin ba
Juyowa yayi yana kallon sarah cike da takaici yace I feel ashamed to call u my sister kin bani mamaki kinbani kunya sarah yaushe kika zama haka
fashewa tayi da kuka tana kallonsa cikin daga murya tace
Ni kaina bansan yaushe nazama haka ba amma komai nayi Kaine sila kasabamun komai nakeso kana mun amma lokaci guda da wannan tashigo rayuwarka kacanza mun kai dakanka kadawo kana ruguza mun farincikina wai dan kafaranta mata da yan uwanta kai kafi kowa sanin cewa duk abunda nakeso to zanyi komai dan ganin nasamesa
Saboda haka dole ne namallaki abunda nakeso kuma dole tabar gidannan saboda kasaketa
wurin asma'u tanufa tana jan hannunta tace wallahi dole kibar gidannan
Fizgota AK yayi yasaukemata lafiyayyen mari atsorace tadafe kuncinta tana kallonsa cikin sassanyar murya tace kamun duk abunda kaga dama amma koda zan rasa raina setabar gidannan
Hannu yamika ma asma'u yana fadin bani takardar
Tana mikamasa yawarware takardar yana nuna ma sarah
Ido tazaro tana kallon farar takardar daba komai aciki
" kingani saboda haka ba dalilin dazaisa tabar gidannan u can die if u want
saurin dagowa tayi tana kallonsa da jajayen idanuwanta dasuke zubar da kwalla
jadabaya tafarayi tana fadin AK kabani mamaki gaba daya kacanza mun yau Kaine kecewa namutu in inaso saboda wannan banzar
juyawa tayi takoma ciki aguje tana fadin AK natsaneka I hate u Ku dukanku senasa kunyi nadamar abunda kuka mun u won't get away With this
Saurin bin bayanta aysha tayi dan gudun kar adawo kanta
hannu grany ta tafa tana salati tace oh ni mairo wai ina sarah tadauko dabi'ar turawa ne gaba daya yarinya tacanza
cike da farin ciki khadeeja ta rungume asma'u tana tayata murna
Dariya inna ameena tayi tana kallon AK tace
To gaskiya kabatama matarka rai kacutar da ita se kabata hakuri
Kallonta yayi aransa yana fadin toh fah here comes the love teacher
daure fuska tayi tana fadin bada kai nakeba katsaya kana karemun kallo
karasawa yayi wurin asma'u yatsaya yana kallonta da murmushi afuskansa sassauta muryansa yayi yace
dagaske sena bada hakuri kin.....
baikarasaba yaji tarungumesa dakarfi kamar zata shige cikinsa
Cak ya tsaya nadan lokaci sannan ahankali yakai hannunsa bayanta yarungumota yana lumshe idanuwansa
Juyawa khadeeja tayi tana boye fuskarta ajikin inna ameena dariya sukayi inna tace kajita sekace batasan komai ba ai idan ma kunyar kikeji gara ma ki ijiyeta dan ahmadi bai San kunya ba
janyeta yayi daga jikinsa yana kallon grany yace
grany mukarasa mana kuhuta ga inna ameena ko jakan bata ajeba kodai dakudi acikine
saurin karban jakan khadeeja tayi tana fadin inna kikawo jakan kuje kawai zan biyoku da ita
dariya sukasa gaba daya suka wuce bangaren grany suna raha
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: Suna shiga ciki khadeeja takira ahmad awaya tana basa labarin abunda yafaru bai ma tsaya yagama jin karshen labarin ba yakatse wayar cike dafarin ciki ya yanufo gidan
yana zuwa aka bude sabon shafin fira anan suka tsaida magana kan bikin ahmad daza'ayi bada jimawa ba dazaran ahmad yadawo daga tafiyar dazaiyi gobe tunda komai ashirye yake kuma magabata sunsan damaganar
su ahmad baki yaki rufuwa se Satan kallon khadeeja yake yana ji kamar ya rungumota dan farin ciki
agidan suka wuni ranan sedare ahmad da khadeeja suka tafi
bayan AK yarakasu yadawo bangarensa yawuce yana kallon dakin sarah datuanin halin datake ciki ahakanli yataka har yaje kofan dakin hannunsa yakai kan handle din kofar kamar yashiga sekuma yajuya yanufi bangarensa
yana shiga dakin ya isko asma'u tana maida kayanta a drawer
coat dinsa yacire yadora akan gado sannan yagyara tsayuwarsa yasa hannayensa a alijihu yana binta dakallo
daukan coat din tayi daga kan gado tamaidata wurinta
Ganinsa atsaye kamar gunki yasa tajuyo tana kallonsa fuska ahade tace what??
kauda kai yayi yana shafa bayan wuyansa yace nothing kawaidai inaso nabaki hakuri ne akan zarginki danayi duk dacewa kinyi kokarin fahimtar dani amma naki sauraronki I am really so.....
Hannunta takai bakinsa tana girgiza kai da murmushi afuskanta cikin sassanyar murya tace
ABI baka bukatar bani hakuri saboda ko kadan banga laifinda kamun ba in fact ka rufamin asiri hatta iyayena bawanda yasan da maganar ni yakamata nagodemaka akan alfarmar dakamun thank you thank you
Janye hannunta yayi daga kan bakinsa yana murmushi yace come on chitti stop being romantic baya maki kyew
kauda kai tayi tana daure fuska tace wai ni komai sekace baya mun kyew kabar ganina haka fa kanemi karainamun class duk abunda wayayyar mace zatayi nima zan iya ko aysha kar nake kallonta dan ba abunda zata nunamun
Dariya yayi yace ohhh really so u can do anything
dan kwali ta turo gaban goshi tana karkada kafa tace kwarai kuwa idan baka yardaba bet me and see
"Ok tunda kince zaki iya yin duk abunda aysha tayi let's see
Aysha tafara cewa tana sona kafin nace ina sonta can u do that ?
dressing mirror tanufa tana fadin kai bazan iyaba saboda me zanyi karya bayan bana sonka after all ni bantaba cewa inason wani ba so it's not easy for me
Dariya yayi yana zama bakin gado yace dama nagayamiki har yanzu dasauranki kidaina hada kanki da aysha ita tafada dagaske ke kuma pretending ma kinkasa
Dawowa tayi wurinsa tatsaya tana fadin ok fine I will do it ai ba wuya ne dashiba
tashi tsaye yayi yana danne dariyarsa yace ok kuma kiyishi in a romantic way bawai kai tsaye ba
gyaran murya tayi tana saita nutsuwarta kanta akasa tace I ....I...
Dariya yayi yace accept ur defeat chitti bazaki taba iyawa ba I said in a romantic way amma kina Abu kamar mara gaskiya u....u....u what?
"ni gaskiya bazan iyaba I need to practice it kafin in iya yanda zanyi
dariya yayi yace ok to kije kiyi gasace nasamaki
Zama tayi bakin gado tace gobe zan gayamaka nasan zanci amma mezaka bani idan naci
Kusa da ita yazauna yana fadin me kike so
Shiru tayi nadan lokaci sannan tace yawwa idan naci ka yarda zaka daina kirana chitti kuma kadaina tsokanata
Nayarda kuma daga lokacin zan daina raina miki class ...
yafada yana kwaikwayon Yanda takeyi idan tana kwaikwayon maganar aysha
duka takaimasa da pilon dake hannunta ya tashi yana dariya yafita daga dakin
washegari dasafe....
Har lokacin sarah bata fito daga dakinta ba tana zaune ita kadai ko aysha tahana tazauna da ita ba kuka takeba amma idonta yayi ja zuciyarta takeji kamar zata fito saboda bakin ciki
asma'u na bangaren grany bayan sun gama breakfast tacemusu zataje gida tagaidasu Umma
da mamaki inna ameena tace ya zaki tafi gida ina AK fa bashi zai kaiki ba
Shiru tayi batace komai ba
Tabe baki inna tayi tana kallon grany tace Yaya nifa yarannan nabani mamaki anya kwa sunma San miye aure kuwa
kauda kai grany tayi tana fadin oho ganemun hanya wai makaho yaje gulma
Ni tun ina mamaki har nasaba inaga wayewar ce tayi yawa
Zatayi magana kenan AK yashigo tun bai gama karasowa palon ba tace yawwa AK dama nemanka nake
"ai ni dama kullun acikin nemana kike to gani nazo fadi matsalarki
dariya tayi tace dama cewa nayi kadauki asma'u mana kudan fita lunching mana
zama yayi kusa da grany yana fadin
bakuyi abinci bane yau ko kuma isarta ne baiyiba
Daure fuska tayi tana jefamai harara tace kai wai meyasa ba amaganar arziki dakai ne dan fitar dazakuyi kudan shakata shine wani Abu
Sosa kansa yayi yana kallon grany yaga ba alamun wasa atare da ita
tashi yayi yafita yana kallon asma'u yace muje
ahanya shiru sukayi nadan lokaci bawanda yake magana
juyowa yayi yana kallonta cikin sigar tsokana yace are u practicing ?
Gyada kai tayi tana gyara zamanta tace yes kuma zan baka mamaki
Kallon titin tayi tana tana Sosa kai tace wai ina zaka kaimu ne
Murmushi yayi yace badai abinci kike nema ba zan kai 5 stars abincinsu yahadu
girgiza kai tayi tace a'a nidai banaso irin wurinnan abincinsu bawani dadi sai tsada
"to ba 7 stars bare nakaiki idan kuma akwai ayi kauyanku se muje
"Mu bamada wani 7stars simple restaurant mukeda and the food was delicious.....
Tafada tana lashe baki
Karya kuana yayi yanufi unguwarsu yana fadin nayarda muje amma dasharadi
Juyowa tayi tana kallonsa tace wane sharadi ne
"Idan abincin yayi dadi nizan biya idan kuma baiyi dadi ba kece zaki biya
Kauda kai tayi tana fadin a'a gaskiya ban yardaba saboda ko yayi dadi zaka iya cewa baiyiba
Hannunsa daya yadora saman kansa yana murmushi yace I promise ba cheating idan yayi dadi zan fada
Haka sukaci gaba dafiransu suyi fada su shirya har suka iso restaurant din abakin titi yake ga mutane dayawa awurin dariya yafara mata yana fadin kuuut chitti mezan gani haka badai layi zamubi abamu abincin ba
daure fuska tayi tafita batace komai
Biyota yayi yana dariya se kokarin boye fuskarsa yake abayanta wai kar mutane sugansa
bayan sun gama cin abincin suka fita se dariya takemai wai yasha santi
Seda suka biya wurinsu Umma da Momy se yamma sannan suka koma gida
Da daddare AK yana tsaye yasa asma'u agaba yana jira tafadi cewa tana sonsa ita kuma takasa se kaikawo take
harde hannayansa yayi yana kallonta yace chitti please kifada nakosa naji
hararansa tayi tace to wai ma meyasa kakeso kaji nace inasonka kodan kasamu abun da zakajin dadin tsokanata dashi
Dariya yayi yace kawaidai inason naji ne ina tune lokacinda aysha tafada it was awesome
Kauda kai tayi tace to kajuya se infada kasan bantaba yiba
"Come on chitti kawai kidaukeni a matsayin friend dinki ba boyfriend ba
Juyawa yayi zai fita yana boye dariyarsa yace idan kuma bazaki iyaba shikenan se kidaina hada kanki da aysha
Saurin rikosa tayi tana fadin a'a tsaya mana allah zan iya amma kar kamun dariya
bazan yiba .....
Yafada yana gyara tsayuwarsa
Matsowa tayi dap dashi tatsaya seda taja dogon nunfashi sannan tarufe idonta tana jin sonsa nakara shiga har cikin ranta
Kallonta yake yana murmushi dan shi kawai yanayi ne dan Neman tsokana just to have a good time amma badan dagaske yana so tace tana sonsa ba
bude idanuwanta tayi ahankali ta saukesu cikin nasa nan take taji gabanta yafadi tana jin wani yanayi amma tadake cikin wata lallausar murya tace
ABI how can I explain my feelings to u its pain its numbness its
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 35