taci abinci tasha wannan se kudan barta tahuta kadan anjima zan dawo
Godiya yama doctor din sannan sukayi sallama yatafi nura narike da briefcase dinshi suka fita
ahankali yatura kofar dakin yashiga aysha nabiye dashi abaya kusa da ita yazauna bakin gadon yana kallon yanda take sauke nunfashi ahankali lokaci guda duk tacanza tayi wujiga wujiga kamar ba sarahn dayasani ba yar gayu mai son kwalliya nan take yaji tawsayinta yakama da ahankali yashafi gashin kanta da ya barbage akan pilon datake kuance akai
Aysha nadaga gefe haushi duk yacikata ganin yanda duk yarude akan sarah har yake fadin wai ita da grany kawai yake gani yaji dadi to ita kuma ko oho kenan ko
Kusa dashi tamatso tadafa kafadansa tana fadin AK naga lokaci yana tafiya ko kama grany maganrmu
Wani gigitaccen kallo dayawatsa mata ne yasa tayi waje tana fadin bari nashirya mata abunda zataci idan tafarka dakallo yabita seda tafita sannan yamike ya gyara mata bargon sannan yafita
bangaren grany yanufa mamaki ne yakamashi ganin yan uwansu makil apalon wasu yaganesu wasu kuma bai sansu ba suna ganinshi suka haw shewar ango ango
Bayabo ba fallasa ya amsa gaisuwarsu ya wuce dakin grany tana zaune kan gado tana lissafa kudi
Tana ganinsa tawashe baki tana fadin ahh abidi karaso mana dazu naje dakinka banganka ba gaka baki ko
zama yayi abakin gado baice komai ba
Lafiya abidi grany tafada tana karantar yanayinsa
Ajiyar zuciya yasauke sannan yace sarah ce ba lafiya grany
Afirgice tace subhanallahi me yasameta
ba wani Abu bane dasauki ma yanzu doctor yaduba ta
Tashi tayi tana fadin bari naje naganta baiwar Allah ai bansaniba kasan ba shiri mukeba
a'a barshi kawai yanzu tana bacci anjima kyaje
Dawowa tayi tazauna tana fadin to Allah yasawake
Ameen yafada yana yana mikar da bayansa kan gadon
Baki grany tawashe tana fadin abidi kaga su bala da shehu sunzo ko
kai yagirgiza yace a'a ban gansuba suna ina
Suna sashen baki dazu suka zo gobe insha allahu zasuje suga magabatan yarinyar dazaka aura tunda ta amince
Damamaki yace ta amince fa kikace koda yake ba abun mamaki bane dan tayi saurin amincewa auren AK hausawee dama nasan za'arina
nan take yaji yarinyar bata kuanta mashi ba dan yafison mace mai aji ba mayyar abun duniya ba wani dogon tsaki yaja hade da kauda kai
Hade fuska grany tayi tace to ana maganar arziki mekuma yakawo tsaki yadai kamata kaje Ku gana da yarinyar taganka kufahimci juna
Mikewa yayi yanufi hanyar fita yana fadin tunda ta amince kafin taganni that means bata bukatar ganina abunda takeso daban
Baki bude grany ke kallonsa har yafita girgiza kai tayi tace gaskiya akwai abunda yake damun yaron nan
Ahmad ne zaune a dining yasa abinci agaba se juya cokalin yake amma yakasa koda loma dayane Momy dake gefe tana kallonsa tafahimci akwai abunda yake damunsa tunda yashigo gida dazu
Kujeran Kusa dashi tajo tazauna tana fadin ahmad wai meyake damunka ne kuana biyu naga kanada damuwa amma kaki fadamun kuma na lura kaman auren sarah ne bakaso to meyasa zaka takura kanka ana dolene
Sunkuy dakai yayi kasa baice komaiba
Dakai nake magana kayi banza dani
Dago kansa yayi yafara bata labarin abunda yafaru tun a airport har izuwa yau
Shiru tayi bayan tagama saurarenshi can tadago tace gaskiya baka kyewta ba ahmad amma banga laifinka ba shi mutum bayada ikon saka so ko cirewa sedai kawai ince Allah yashige mana gaba kuma kasamu AK kabashi hakuri yanada saukin kai nasan zai fahimceka kasan yanda yakeson kanwarsa
Shiru yayi baice komai ba
Murmushi tayi tace oh kai kwa duk yan matan da suke binka kamar hauka karasa wacce zaka so se khadeeja wannan karamar yarinyar
Se alokacin yadago kai yana murmushi yace kai Momy khadeejan ce Karama
Tashi tayi tana fadin nidai kahada ni da aiki da zaka kamun suruka trouble maker
Dariya yayi yace Momy ai irinsu akeso
Abangaren Umma da abba kuwa shiri suke bana wasa ba izuwa yanzu kowa a dangi yasan da zancan auren asma'u kowa yayi farin ciki da wannan ala'amarin
Bakamar khadeeja datake jin kamar tajanyo ranar tadawo yau
Bangaren asma'u kuma duk tafita hayyacinta tsakanin jiya da yau har wata yar rama tayi tana mamakin wane kalan aurene wannan da za'ayishi asati guda kuma har yanzu angon bai nemi yaganta ba bayan tanada tabbacin bai Santa ba
Dakin sarah AK yakoma daga bakin kofar yatsaya yana kallonta ahankali yabude idonta tasaukesu akansa
Saurin karasowa bakin gadon yayi yana fadin Ashe kinfarka murmushin dole tayi tana kallonsa ga hawaye na gangarowa agefen fuskarta
zaunawa yayi
daga gefenta aysha kuma tana tsaye gefen kanta tana kallon ikon rabbi
Yatsansa yasa yana goge mata hawaye cikin muryan lallashi yace stop crying kanwata kukan nan naki yana daga mun hankali ki kuantar da hankalinki Ahmad bashi kadai bane namiji aduniya ba zaki samu Wanda yafishi komai ....
Katsesa tayi dafadin bashi kadai bane namiji aduniya ba amma ni shikadai nakeso kuma shi zan aura he only belongs to me takarshe maganar tana kara fashewa da kuka
Nasan kina sonsa kanwata amma kiyi kokarin danne sonsa kimanta dashi
ahasale yakarashe maganar dafadin just forget him saboda yace bazai aureki ba
πI can't..... I can't Yaya bazan iya mantawa da ahmad ba and I won't let him go !!!
Kauda kansa yayi gefe guda yana jin wani irin haushin ahmad dayajefa kanwarsa awannan halin
Aysha ce tace ni ina mamakin wace yarinya ce wannan da ahmad yamutu akanta har yake wulakanta sarah
nima dai bansaniba AK yafada yana kallon sarah
Saurin tashi zaune tayi tafara Neman wayanta
Menene inji aysha tana tayata daga bargon dake kan gadon
Kan dressing mirror tanuna mata tana fadin bani wayana
Dauko wayan tayi Tamika mata
Tana karba tafito da photon asma'u Tamika ma AK tana fadin wannan ce yarinyar
Karban wayan yayi yana dubawa zunbur yamike yana fadin wannan ai nasanta
Kafeshi sukayi da ido suna son jin a ina yasanta
Kanshi yashafa yana fadin no wonder shiyasa ranan naganta agidansu ahmad kuma ina yawan ganinta a unguwar amma bansan ko wacece ba
Babanta malamin makaranta ne sunansa malam mahammadu amma ana kiransa magaji sedai yajima da rasuwa
Tunda tafara magana AK yakafeta da ido yanason tuna ina yataba jin sunan
saurin rikota yayi yana fadin wait kika ce babanta malamin makaranta ne sunansa magaji kuma yajima da rasuwa ko
Kai ta gyada mai alamar eh
Zama yayi akan gado tare dasa hannayensa biyu yana shafa sumar Kansa data hargitse lokaci guda
Kusa dashi aysha tamatso tadafashi tana fadin lafiya AK menene kasanta ne
Dago da kansa yayi yana kallon sarah yace itace yarinyar da grany takeso na aura
Dip suka dauke wuta ba mai motsi ba kamar aysha datake jin kamar tasaki fitsari
Wata nannawyan ajiyar zuciya ta sauke arenta take fadin ohh thank god kaga bazata amince da auren AK ba tunda tanason ahmad
Kamar yaji mai tace yayi saurin fadin ina mamakin meyasa zata amince da aurena bayan kuma tana son ahmad
Dirowa daga kan gado sarah tayi tana fadin haba nifa nasani seda nagayama ahmad yarinyar nan basonsa takeba kawai kudinsa takeso shine yanzu taji AK hausawee yana Neman aurenta mezai hana ta amince bayan tasan ya ninka ahmad kudi
To yanzu miye abun yi inji aysha datakejin kamar ta kurma ihu saboda tashin hankali
mikewa AK yayi yana fadin kawai zanje nasamu grany nagayamata abunda yake faruwa inada tabbacin ita dakanta zata nemi afasa auren
saurin riko hannunsa tayi tana fadin Yaya dan Allah kataimake ni kar kafasa aurennan
Shiga gabanta aysha tayi cike da Bacin rai tace sarah hankalinki daya kike fadan wannan maganar kuwa
Tureta sarah tayi seda takusa faduwa AK yayi saurin rikota tafado kansa
Cikin daga murya sarah tanunata dayatsa tace
da yayana nake magana bake ba so stay out of it
Gefen fuskarta AK yashafa da hannunsa yana fadin come down baby take it easy
meyasa kike so na aureta
Hannunsa takamo cikin dasashshiyar muryanta take fadin
Yaya kaga kai kasan yarinyar kasan cewa kudi ne kawai agabanta mayaudariya ce shikuma ahmad bai saniba ko zamu shekara muna fadamasa ba yarda zaiyi ba Idan har kafasa aurenta shi zai aureta kaga zata cutar dashi nasan kana son ahmad bazaka so wani Abu yasameshi ba so please help us !!!
No sarah I can't do this bazan iya auren yarinyar da ahmad yake mutuwar so ba
Yaya please kafahimci abunda nake nufi natabbata ba ahayyacinshi yake ba wayasani ma ko asiri tamasa kawai dan tacimma nufinta akansa kaga idan ka aureta zamu koyamata darasi shikuma ahmad zai gane ba dagaske take sonshi ba natabbata zai dawo gareni kai kuma ka ceto abokinka daga hannunta
Shiru yayi nadan lokaci yana tunani
Aysha ce tadafa kafadansa tana fadin AK dan Allah kar kayarda da shirmen sarah tayama zaka sauri wannan yarinyar bayan kasan ahmad yana sonta dawane ido zaka kalleshi
Katseta yayi dafadin
ZAN AURETA KODAN FARIN CIKIN KANWATA
Sannan naceto abokina daga tarkonta I will punish her senasa ta tsani rayuwarta se nasa ta durkusa gaban ahmad da sarah tanemi yafiyarsu
Rungumeshi sarah tayi cike dafarin ciki tana fadin Yaya thank u
You are my hero
Girgiza kai aysha tayi tafita daga dakin aguje tana sharan kwalla
Dakallo AK yabita yana yunkurin binta sarah tarikoshi tana fadin a'a barta Yaya zan mata magana nasan zata fahimceni
Ok bari nasa akawomaki wani Abu kici se kisha magani
Bakin gado yakaita yana fadin come and have some rest
Bayan kuana biyu......
Shirye shirye yakan kama atsakanin gidajen biyu dan tuni magabatan ahmad suka suka je sukasami abba da duk wani abu na al'ada kuma sukace basa bukatar komai daga wajan iyayen amarya abba yayi farin ciki matuka nan take aka tsaida dawrin aure ranar juma'a a central mosque
Umma ma shiri take bana wasa ba gyaran jiki asma'u kesha nafitan hankali Umma dakanta kemata dama guana ce awannan Wurin cikin kuana biyu asma'u ta canza tayi wani fresh da ita ko ina bata zuwa daga daki se bayi sedai daga ka ganta kasan tana cikin damuwa nakadan ba
Su khadeeja da nusaiba ba'akama hannun yaro kullun suna zirga zirgan zuwa kasuwa da shagon dinki damma abba yace bawani party ko dinner nan daza'ayi ana dawra aure akayi walima za'akai amarya dakinta
Bayanda basuyi dashiba amma yaki
haka suka hakura
Abangaren grany ma tagama shirinta tsap yau za'akai lepe akwatina goma shabiyu kuma tsadaddun kayane acike makil bawanda zaice a Nigeria ta hada lepenta ko yan uwansu sundawka akasan waje aka hado
Sarah ma tsake da ita ake komai tun grany tana mamaki har tasake sukaci gaba dashiri
AK kam idan bawanda yasani ba bawanda zaice shine angwan bayanda grany batayi ba dashi akan yaje Yaga asma'u kafin dawrin aure amma yaki ba inda yake zuwa daga daki sai masallaci rashin ahmad akusa dashi duk seyaji bayajin dadi kuma har yanzu yana jimamin tayadda ahmad zai fuskanci abun anya kwa baiso kansa dayawa ba wata zuciyar tace ai kayine saboda shi kuma sadaukarwa ce wata rana shidakanshi zai godemaka akan abunda kayimasa
Da wannan tunanin yake dan samun natsuwa amma ya yanke shawaran tura ahmad Turkey saboda bayaso yasan dazancen auren harsai komai ya kammala
Abangaren aysha kuwa
duk dacewa sarah tashayo kanta ta amince da maganar auren amma sam takasa sakewa tana tunanin matakin da iyayenta zasu dawka akanta idan suka dawo dan duk abunda yafaru itace sila
Ga inna ladidi da bashir sun sakata agaba da tsokana wai tayi kuantai wani lokaci tahade fuska ko tayi tsaki wani lokacin har kuka yitake
ganin abun yayi yawa tashirya zatayi tafiya amma AK yahanata wai tatsaya ta tayashi cin uban amaryarshi ....lolπ
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: ππππππ
π¨βπ§ _DOMUN KANWATA_ π©βπ§
Na( Maryam Muhammad jibril)
6β£5β£
Gida yasha gyara banawasa ba hatta paitin gidan ansake shi
sedai AK bai yarda kowa yasan da zancen aurensa ba saboda bakowa yasan asalin sunansaba kowa yafi saninsa da AK hausawee
tun ajiya yayi nasaran tura ahmad turkey kan harkokin kasuwancin su batare da ahmad yasan zancan auren aminin nasa ba haka yatafi yana kokonton akwai abunda AK keboye masa ko khadeeja ma se awaya yafada mata zancan tafiyarsa
seda grany tamatsama AK sannan ya amince akan zaije ya gaida abba da Umma sannan yaga asma'u daga can
Seda yafara zuwa wurin abba yagaidashi cike da ladabi da girmamawa yasamu tarba ta musamman daga wajan inna dan rasa inda zata sashi tayi
yadan jima awurinsu seda sukayi sallar isha'i sannan yawuce gidan su asma'u bayan ya ijiye mata bandir din kudi itada sauran mutanen gidan
Yana isa gidan su asma'u aka mishi iso har cikin palon gidan
Nan ma cike da ladabi yagaida Umma da sauran mutanen dasuka zo taron biki Umma tayi farin ciki matuka saboda tayaba da nagartar AK nan take taji ya kuantamata duk wani zargi yafita aranta tasamu nutsuwa
Bayan sungaisa da Umma tanufi ciki akan zata turo asma'u sugaisa
Dakin asma'u tanufa cike da farin ciki
Bakin gado ta iskota azaune khadeeja kuma tana gefe tana sallah
Kusa da ita Umma tazauna tana fadin asma'u tashi kije Ku gaisa ya iso
Tashi asma'u tayi jiki asanyaye tana fadin Umma kidan jira khady tagama tarakani mana
Daure fuska Umma tayi tace dan Allah wuce yana jiranki me khadeeja zata maku banda shirme da surutu
Tafa hannu khadeeja tafarayi alaman adan jirata
Dariya Umma tayi tace ai kuma sedai kiyi
Sannan tajuyo tana ma asma'u alamar ta tafi
Fita tayi daga daki tana gyara zaman gyalen data rufe fuskarta dashi
Tunda tanufo palon wani fitinannen kanshin turare yadaki hancin AK shakan iska yayi ya furzar yana lumshe ido yana hangota ya kauda kai yana daure fuska
Ahankali takaraso palon tazauna daga gefe ta takure wuri guda tana gaidasa
Wani kallon tsana yawatsa mata aransa yana fadin afuska kamar mutuniyar arziki dama kindaina ba kanki wahala dan nasan ainahin wacece ke
Mamaki ne Yakama asma'u jin bai amsa gaisuwarta ba kamar tadago takallesa se kuma tadake data tuna bawannan ne karo nafarko dayafara mata haka ba
Shuru sukayi apalon bawanda yace komai har natsawon lokaci
Wata karamar yarinya ce tazo wucewa ta palon AK yakirata
Tana zuwa kusa dashi tagaidashi yace ya sunanki tace nafisa
Yace yawwa nafisa je kicema Umma uncle zai tafi
Dagudu yarinyar ta tafi tana fadin toh
Haushi ne Yakama asma'u ahasale tamike tanufi dayan dakin tana jan tsaki
Da kallo yabita yana murmushin mugunta aransa yana fadin kin kusa shigowa hannu yarinya wannan tsiwar taki zata zama tarihi arayuwarki
Shigowan Umma ne yakatse mashi tuna ninsa mikewa yayi yana fadin Umma nizan wuce dare yayi se wani lokacin
Murmushi Umma tayi tace to Allah yakaimu ina ita kuma wannan yarinyar take
Murmushin yake yayi yafita yana fadin Umma kibarta kawai tahuta gajiya ce tamata yawa zamuyi waya anjima
Murmushi Umma tayi tace to shikenan ka gaida gida Allah yakiyaye
Khadeeja ce tafito aguje tana gyara zunbulelen hijabinta tanufi waje tana salati
Dakallo Umma tabita tana dariya
Dawowa tayi jiki asanyaye tazauna tana fadin haba Umma meyasa zakimun haka kinsan kwa yanda nakosa naga mutuminnan shine zaki mun cikas
Dariya Umma tayi tace to kuana nawa yarage khadeeja har sai kin gaji da ganinsa
Langwabe kai tayi tace Umma bazaki gane ba....
bata karasa ba tahango damen kudi akan kujerar da AK yatashi
Saurin tashi tayi tanufi wajan tana fadin umma ango yayi kwai
Kauda kai Umma tayi tana fadin kefa kin cika shirme wane irin kwai kuma
Kudin tadakko tanufi umma tana washe baki tace wannan shine fidduniya hasanatan
Karban kudin Umma tayi tace kawo khadeeja nabama asma'u wayasani ma ko yamanta ne mukuma mayun kudi kawai muhau kai ni wallahi da nagansu kafin yatafi da bazan karba ba
Kinga ko yanzu yamuka kare da tsegumi wai auren kudi mukama asma'u
Tsaki khadeeja taja tace Umma idan kika biye ta mutane to ko abinci bazakiciba Allah dai yabasu zaman lafiya kawai
Hannunta takai kan kudin tana fadin amma dai wannan kwan kikawoshi nasoyeshi
Bige hannunta Umma tayi tace dallah can matsa kudin nan ijiyesu zanyi khadeeja gaskiya bazan Ciba
Tashi khadeeja tayi tana kuasar hijab dinta tawuce daki tana fadin kawai dai ki ijiye inda bazan ganiba
Rana bata karya
Yau takasance juma'a kuma itace ranar daurin auren AK da asma'u
Dasafe misalin karfe 11narana sarah da aysha ne zaune abangaren AK suna fira
AK yadago yakalli sarah yana murmushi yace ya ake ciki ne wai zancan bikin nan wane shirye shirye kukeyi
Dariya tayi tace bawani shirin da ake ni abun ma dariya yake bani kaman wasan yara
Dariya aysha tayi tace amma ina mamakin meyasa dangin amarya ko kawayenta basu nemi wani Abu da yashafi kudi ko gudunmawa daga wajan angoba
Tashi AK yayi yanufi daki yana fadin abbanta yace bawani shagalin da zasuyi walima kawai ta isa
Sarah tace eh haka naji abakin grany
Mu kuma idan ankawota zamu hada dan kwarya kwaryan party anan gidan daganan kuma kowa ya watse
Aysha tace AK ya kukayi da momyn ahmad dataji zaka auri wata daban daki yashiga yana fadin bansan yasukayi da grany ba nasan abakinta taji
Misalin karfe 14:00 dubbanin jama'a suka shaida *auren* ABID da ASM'AU akan sadaki 500.000
a central mosque dake Abuja
Anci ansha anmore duk da dai bahaka akaso ba amma anji dadi grany da inna baki yaki rufuwa
asma'u kuma tundaga lokacin tafara kuka khadeeja natayata har izuwa lokacinda za akaita dakin mijinta kuka take kaman ranta zaifita tsam tarike Umma da inna taki sakinsu haka da aka kaita wurin abba yamata nasiha da kyar aka banbarota ajikinsa
Motoci na alfarma suka zo daukan amarya tasamu rakiyar mutane da dama su Ummi ne akan gaba se Momy da zainab din yahya da sauran dangi da yan uwa sedai ba kawayen amrya dan asma'u batada wata kawar data wuce khadeeja yan matan wurin duk kawayen khadeeja ne
Tun amota asma'u ke kuka khadeeja na gefenta tana lallashinta har suka iso dankareren gidan AK wato (hausawee Mansion)
Inda suka samu tarba ta musamman daga wurin dangin ango bangren grany akafara kaita bayan anmata nasiha da sauran abubuwan al'adarsu sannan aka nufi bangaren AK da ita baki bude kowa keyawo agidan tundaga get wasu sukafara santin gidan bare daga ciki aljannar duniya sekafita waje zaka San dare yayi yan mata sun zage se selfi ake ana turo baki
Da kyar so Momy suka tattara su suka fita dasu
Asma'u nazaune akan gado khadeeja tashigo kusa da ita tazauna tana fadin ammah kinga gidanki kuwa adduniya wama fiha Yasin aka sakeni tsab zan bata agidan nan gaskiya yahadu
Momy ce taleko tana fadin to khadeeja kuzo mutafi dare yayi konan zaki kuana
asma'u tayi saurin fadin eh Momy kubarta anan
Tashi khadeeja tayi tasukuyo saitin kunnen asma'u cikin rada take fadin ammah gara ma kibarni natafi I'm just 17 karku rudani gashi ahmad baya gari bare ayi namu gobe
Tureta asma'u tayi tana fadin Allah ya shiryeki kekam
Dariya Momy tayi tace tafara halinta ko saurin barin wurin khadeeja tayi tana fadin a'a Momy kawai cewa nayi zaman aure ibada ne yi nayi bari nabari
Dariya Momy tayi tabi bayanta tana ma asma'u seda safe akan se sunzo walimar gobe
Sunkuy dakanta tayi cikin guywowinta tana zubar da kwalla yaune karo nafarko dazata kuana batare da ummanta ko khady ba tunani dai iriiri take yi har dare yayi tsawo amma ba ango ba alamarsa
Gidan yayi shuru ba kajin motsin kowa
har karfe dayan dare amma AK baishigo ba tun tana tsoron shigowarsa har tafara damuwa
Ganin dare yaraba tafara tunanin ko lafiya
Shi kuwa AK yana can wurin aysha yana lallashinta dan tunda taji andaura aure tafara rusa kuka tana shagwaba iri iri
atakaicedai bashi yashigo ba se karfe biyun dare
Ahankali ya tura kofar yashiga tana zaune agefen gado tana gyangyadi
Tsaye yayi daga bakin kofa yana kallonta tana bacci batamasan yashigo ba
Cikin sanda yanufi dan karamin frig din dake gefe ya dauko goran ruwa mai sanyi yadawo tagefenta ya tsaya yana bude gorar ruwan yana murmushin mugunta
Daga goran yayi sama yafara kwarara mata ruwan tundaga kanta
afirgice tafarka tana Jan dogon nunfashi tana goge ruwan fuskarta tana fadin miye haka dan Allah
Wannan wane irin rashin iman....
Nunfashinta ne yakusa dawkewa ganin AK tsaye agabanta rike da goran ruwa fuskarnan tashi kamar baitaba dariya ba
Nunashi tayi dayatsa muryanta narawa take fadin kai....kuma...mekake anan
Kara daure fuska yayi yafara matsowa kusa da ita tana ja dabaya seda yakaita jikin bango
atsorace tarufe idanunta kam tana sauke nunfashi ahankali
Hannunsa daya yakai jikin bangon cikin murya mai kaman rada yake fadin
Kina mamaki ne ...
Son abun duniya ya rufe maki ido har takai baki damu dakisan waye mijinki ba Yaya kamaninsa suke Yaya halayensa suke wannan duk bai dameki ba tunda kinsamu abunda kike kwadayi
Da mamaki tabude idonta tana kallonsa cikin rawar murya tace ni bansan abunda kake magana akai ba
Ban nemi nasan kamanninka ba saboda badan haka na aureka ba
Juyawa yayi yana fadin yes!!! Dama nasan badan haka kika aureni ba sedan kinsan ina da kudi
Matsowa tayi daga jikin bango tana fadin Kaine kudi yadama ni basa gabana na amince da aurenka ne sedan kawai inada tabbacin abbana bazai zaba mun abunda zai cuceniba
Kuma nasan wacece grany shiyasa kawai na amince da na'aureka amma danasan Kaine wallahi daba abunda zaisa na aureka mezanyi da....
Juyowa yayi ahasale ya cabki wuyanta idonshi yayi ja nan take yarikide yazama tamkar wani zaki a tsorace asma'u ke kallonsa tana kokarin kwace wuyanta daga hannunsa amma takasa koda motsa hannunsa ne
Cikin kakkausar murya yake fadin ke bakyama jin kunyar fadan wannan maganr agabana ko kina tunanin bansan ko ke wacece ba idan kinyi nasara akan abokina to ni Nafi karfinki
sena hukuntaki senasa kin tsani rayuwarki I will make ur life a living hell
I will destroy ur happiness daga yanzu kinyi bankuana da farin ciki arayuwarki
ba abunda zai biyo baya se da kinsani danadama kuma bazata miki anfani ba
Turata yayi dakarfi akan gado tafadi tana tari tana shafa wuyanta daysha damka
Hanyar fita yanufa zai fita tayi saurin tashi tashiga gabansa cikin rawar murya take fadin
wai miye laifina da na cancanci wannan hukuncin daga gareka kawai dan na amince da aurenka
Idan kasan bakasona meyasa ka aureni
Kallonta yayi sama da kasa ganin yanda tayi wujiga wujiga ga doguwar rigarta tajike sharkab da ruwa
Kwashewa yayi da dariya wadda daga gani kasan taketa ce kyalkyalata yake bawasa har da dafe ciki baki bude asma'u ke kallonsa takasa magana
cikin dariyar yake fadin come on laugh kiyi dariya kila tazama itace takarshe dazakiyi arayuwarki
Sannan yatsagaita da dariyarsa yamatso kusan yana fadin
Tambayata ma kike wai miye laifinki ko to bari nafadamaki
kinsan ahmad
wane ahmad tafada tana ja dabaya
Wani malalacin murmushi yayi yace karma kice mun harkin manta da saurayinki da kika yaudara bayan kinsa yayi nisa asonki kika watsar dashi kika aureni dan kinji zancan kudi
Kikasa kanwata ta zubar da hawaye daga ranar da taganki a office dinsa daga ranan tadaina farin ciki
kika rabani da aminina tunda muke dashi bamu taba fada ba se akanki
Lokaci guda kika shigo rayuwarmu kika ruguza mana ita dayanzu mosoyiyata ce anan dakin amma adalilinki tana can tana zubar da kwalla
Wannan auren punishment ne agareki sekinyi dakinsanin rayuwarki senasa kin tsani rayuwarki sekowa yasan true color dinki sannan zan sakeki
Yana kainan yatureta daga gabansa yawuce yana banko kofar dakarfi
Nan take jikin asma'u yafara rawa durkushewa tayi awurin tafashe da wani irin kuka mai cin rai cikin kukan take fadin
πmeyake shirin faruwa dani ne menayima waya'nnan mutanen zasu dawki alhakina ni bansan meyake magana akai ba wayyo Allah nah!!!
Saurin safe kanta tayi data tuna maganganunsa
Cike datashin hankali take fadin ohh my god kenan ya aureni ne amatsayin budurwan ahmad ganin dasuka mun a office dinsa ranan tunaninsa nice khadeeja
Wayyo Allah nagodemaka daka kubutar da kanwata daga sharrinsu dayanzu itace ahalin danake ciki yanzu wayyo khadyta Allah yashiga tsakaninki dasu
Haka dai tayi rusa kuka tana sambatu iri iri jin kanta yana Sara mata yasa ta sulale awurin taci gaba da kukanta har bacci
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 35