tamike tsaye suka tasa keyarta har lokacin batadago kanta ba kuma batayi magan ba seda suka wuce kusan asma'u sannan tadago tana kallonta da jajayen idanuwanta bakinta namotsi alamun tanaso tayi magana amma bata furta komai ba suka tafi da ita
Cike da takaici bashir yakalli AK cikin daga murya yace Yaya yau kaida kanka kamika sarah hannun yane sanda why.....metayi maku
Banza yayi dashi yajuya ahasale yakoma bangarensa itama asma'u tanufi hanyar fita batare datace komaiba khadeeja nabiye da ita abaya
Suna fita sukahadu dasu jamilu zasu shigo yana rike dajakan kudin dasuka ba sarah jiya cike damamaki suka kalli juna itada khadeeja sannan takalli uncle jamilu tana murmushi tace kamakara jamilu naso ace kananan kaga wata drama mai daukan hankali
kaga har nazargeka akan satar Zane ashe sarah ce mai laifin bakaiba
Kauda kai yayi yana daure fuska se kora jus dinsa yake hankali kwance
karban jakar aysha tayi ahannunsa tamikama asma'u tana fadin to mara mutunci ga kudinki se kishafa ma babana lafiya aje can akarata dason kudin tsiya
Nunata tayi dayatsa fuska ahade tace ke nasha gayamiki idan ina magana da ubanki kidaina sakamun kazamun bakinki kinji ko ...
dariya khadeeja tayi tana kallon jamilu cikin muryan maza tace to ai gyatumin naki ne mayen kudi tunda har ya iya sace makudan kudi irin wannan kuma yacinyesu lokaci guda har biya yagagaresa sannan ta Inda aka hau tanan ake sauka tunda a company yasaci kudin to acen zaimayardasu ba akofar gidanku ba
Daure fuska jamilu yayi cike dajin zafin maganrsa yace kaikuma waye
Shiga gabansa tayi tana babbankarewa tace PA dintane ni koda magana ne
karban jakan asma'u tayi tana murmushi tace kawonan kasan shi mugu ba'abarinsa damakami rabasu ake saboda tsaro sannan
karaso dap da uncle jamilu tatsaya fuska ahade cikin murya mai kaman rada tace this is just the beginning uncle...... Kai kafara wasan amma nice zankareshi ...tana kainan tamaida bakin sunglasses dinta tawuce tana wurgama khadeeja jakar kudin cak tacabeta tana murmushi takarbi jus din hannun jamilu tana fadin awannan shekarun naka shan abu maizaki its not good for your health.... kanemi jikeken maganin gargajiya ...saboda daga yanzu sukadaine zasu iya taimakama
tana kainan tawuce kusan aysha tana shafo cikinta da yar yatsa tace you are the next babyyyyyy
zaro ido tayi tana dafe cikinta amma takasa magana
se binsu dakallo sukayi baki bude har suka shiga mota sukabar gidan sannan aysha tajuyo tana kallon jamilu tace dady kaji meyace kuwa
tsaki jamilu yayi batare dayayi magana ba yasa kai cikin gidan aysha nabiye dashi abaya har lokacin hannunta nakan cikinta tana mamakin abunda khadeeja tayimata
[24/07, 05:50] Hassan Atk: sarah nazaune acikin sell tasa kai aguywa amma bakuka takeba tunda aka kawota take haka har wannan lokacin
wani officer ne yaleko cikin sell din yace sarah kabir fito kinada visitor kintashi tayi kuma batadago takallesa ba bayanda baiyi da ita ba amma ko kallonsa batayiba har yagaji datsayuwa yakoma wajen bashir dake zaune yana jiran fitowarta yasanardashi yanda sukayi
Cike da damuwa bashir yace yallabai kataimaka kabarni inshiga wurinta wallahi bajimawa zanyiba
"Gaskiya bazan bari kashiga ba ko yanzuma kawai kasada zanyi inbarka kaganta dan yallabai yace idan ba AK ne yazo ko matarsaba kar abar kowa yaganta
Wasu kudi bashir yaciro a alijihu yadamka masa yana fadin gawannan kakara akan nadazu hakuri zakayi kabarni naganta minti biyu yayi yawa please
Dakyar dan sandan ya yarda bashir yawuce ciki seda yabude mashi yashiga sannan yajuya yabasu waje
ahankali yakarasa wurinta yadurkusa da guywowinsa kasa cikin rada yakira sunanta sarah....
saurin dagowa tayi dajajayen idanuwanta tana kallonsa cikin rawar murya tace Bashir....kai...mekake anan
gyara zamansa yayi yana facing dinta yace zuwa nayi kigayamun waye yaturaki office din ahmad jiya
Kauda kai tayi tana daure fuska tace bawanda yaturani yin kaina ne kuma katashi lafita daga nan bana bukatar sake ganin kowa acikinku
Dafata yayi tabige hannunsa cikin daga murya tace nace katashi kafita daganan banason ganinka kuma karka kara zuwa nan
Rikota yayi dakarfi tana kokarin kwacewa amma takasa hartagaji tafada jikinsa tana fashewa dawani irin kuka mai cin rai
kyaleta yayi tacigaba dakukanta seda tayi mai isarta sannan tatashi tana share kwalla kallonta yake cike datausayi cikin sassanyar murya yace sarah please I am begging u kigayamun waye yasa kika saci zanen nan
shiru tayi batace komai ba wasu hawayen nakara gangarowa akan kuncinta haka yazuba mata ido yana kallonta har lokacinsa yakare yafita batare datagayamasa abunda yakeson sani ba
yana fita takuanta awurin tanaci gaba dakukanta har bacci yadauketa
yana barin wurin company yanufa ahasale yawuce office din asma'u bayan yanemi izinin shiga yasa kai cikin office din
Dagowa tayi tana kallonsa damurmushi tace karaso mana bashir
Karasawa yayi yatsaya daga gefe yana kallonta yace ma...dan allah alfarma nazo nema awajanki
"Fadi inji inzan iya...
fuskar tausayi yayi kamar zai fashe dakuka yace ma...kitausayama sarah dan allah kibata dama takarshe natabbata ba dason ranta tasaci zanen nanba tirsasata akayi saboda sata ba halinta bane
tasowa tayi daga kan kujerarta ta iso dap dashi ta tsaya tana murmushi tace bashir are u in love with her ?
kauda kai yayi dakyar ya iya furta no am not ..
"tsoro kake jine?
"tsoron me zanji kawaidai banasonta ne she is just my sister that's all
"Karya kake bashir kana sonta
juyawa yayi yana dafe kai hade da runtse ido yace yes.....ina sonta ...tun tana Karama nake sonta tare muka taso har girmanmu ni inamata kallon masoyiya ita kuma tanamun kallon dan uwa kuma abokinta nayi kokarin sanarda ita amma senafahimci kwata kwata hankalinta baya kaina aranar da tagayamun tana son ahmad mutuwa ne kawai banyiba kasancewar nasan halinta tun tana Karama idan dai taso Abu to bawanda ya isa yacanza mata ra'ayi shiyasa banba kaina wahalaba nahakura da ita amma nakasa cire sonta araina maimakon yaragu sema karuwa dayake aduk lokacinda naganta haka naci gaba da danneshi har zuwa yau danakasa jure ganinta awannan halin.....muryansa ne takarye yasa cigaba damaganarsa se sauke nunfashi yake kamar wanda yayi tsere
zaunawa asma'u tayi kan table dinta tana sauke ajiyar zuciya nadan lokaci sannan tadago tana kallonsa cikin sassanyar murya tace bashir meyasa kake ganin bazaka iya canzama sarah ra'ayi ba ....bakayarda da kankabane ko kuwa sonta ne baiyi karfi azuciyarka ba....aduk lokacinda kasa aranka cewa zaka iya yin abu to zakaga komai yazomaka dasauki ....just believe in your self ...mu mata munada raunin zuciya munfi bukatar asomu fiye da yanda zamu so ...duk son da sarah takema ahmad natabbata naka yafi nata da ace kanuna mata wanann son dakake boyewa datuni tamanta Wanda takema ahmad ....amma har yanzu lokaci baikure ba yanzu nema yakamata ka gwada karfin sonka agareta ....acikin so dayaki bashir this is ur fight u have to do it alone ....kaima namiji ne kamar kowa yanda kowane namiji zaikare wacce yakeso yatsaya mata alokacinda take bukatarsa haka kaima zakayi ....ina tabbatar maka dacewa idan har son gaskiya kake mata to wahalarka bazata tafi abanza ba koda bata soka ba aduk lokacinda katuna kataba mata abunda kowa yakasa yimata zakaji dadi aranka itama kuma bazata taba manta wanann alfarmar ba ...bashir ita zuciya tana son mai kyewtata mata sarah mace ce lokaci kadan zaidaukeka kacanza akalar zuciyarta tadawo kanka ...kaidai kawai kayi komai da kekkyewar niyya
Tunda tafara yake kallonta gaba daya yatattara hankalinsa kanta lokaci guda yaji son sarah nakara tsimashi duk Wanda yayi kokarin dannewa shekaru dayawa yajishi yadawo sabo tamkar yau yafara jinsa nan take yaji wani farin ciki ya lullubesa
Murmushi tayi tana nuna masa hanyar fita tace jeka ...jakayi aiki da guminka katara kudin belinta nikuma namaka alkawarin zan kara maka matsayi tayanda zaizo maka dasauki
Hanyar fita yanufa cike dafarin ciki har yakai kofa yajuyo yana kallonta da murmushi yace thank you ....
Jinjina mishi kai tayi batare datace komai ba yafita daga office din kanta tadaga sama tana maida hawayen fuskarta da murmushi afuskanta tace all the best Bashir
tana nan zaune ahmad da khadeeja suka shigo office din
Zaunawa sukayi suna kallonta ahmad yace aunty deeja tagayamun yanda kukayi gaskiya kinbirgeni
Murmushi tayi takoma kan kujerarta tazauna tana fadin yanzu dai bawannan ba ....zancan cikin aysha shine agabana har yanzu nakasa gane waye wannan mutumin natambayi securities sunce yana yawan zuwa gidan amma seda daddare ....kuma tundaga ranan bai kara zuwaba
ajiyar zuciya ahmad yasauke yana fadin insha allahu zamu ganoshi akwai wani abokina Nasir saurayinta ne zandanyi bincike tahanyarsa inga ko zamu samu wani abu
dariya khadeeja tayi tace kilama shine yayi mata cikin
Daure fuska yayi yana hararanta yace kai wai kamal meyasa kafiya son shiga shigula ne
Goran ruwan dake hannunta tajefamai tana fadin kai wai banace kadaina kirana kamal dinnan ba
dariya sukasa gaba daya sannan sukaci gaba dafiransu se dakyar asma'u takoresu a office din tacigaba da aikinta
Da daddare sarah tana zaune cikin sell ta takure wuri guda ga sauro daya addabeta yunwa kwa ba'amaganarta taci kukanta har tagaji
kamar ance tabude idonta ta hango mutun atsaye daga waje komai nasa arufe har tafukan hannayensa ya sadda kai akasa ba'aganin fuskarsa ganin yana kokarin shigowa yasa tamike tsaye tafara jadabaya tana kwala ihu cike da firgici take fadin JJ dan allah kayi hakuri kar kasheni wallahi ban gayama kowa ba ko yan sanda ban sanardasu ba please karka kasheni namaka alkawarin bazan gayama kowa ba
ganin ta tsorata yasa yayi saurin karasowa cikin sell din yana cire babbar rigar dayasaka yaciro wayarsa a aljihu ya haska fuskarsa yana fadin sarah kinga nine bashir ne fa
saurin rungumesa tayi dakarfi kamar zata shige jikinsa idonta arufe gam tana kuka tace bashir dan allah kafitar dani daga nan wajan ...tsoro nakeji...kagafa duhu bana ganin komai kuma nikadai ce anan dan allah ka kaini gida i will never do such thing again I promise.....
runtse idanuwansa yayi yana shafa kanta ahankali har tadaina kukan sannan ya janyeta daga jikinsa suka zauna anan kasa suna facing juna cikin sassanyar murya yace sarah wanene JJ ?
shiru tayi batace komai ba seda yakara tambayarta sannan tabasa labarin duk abunda yafaru tundaga aikin databa JJ har sanadin zuwanta nan wurin
Shiru yayi yana kallonta nadan lokaci sannan yasauke wata nannauyar ajiyar zuciya yace to yanzu intanbayeki ....duk wannan abubuwan sakika aikata for god sake miye ribar dakika ci aciki banda wahala da zubar da mutunci da kima a idon mutane dama shikanshi Wanda kikayi domin shi ...daga karshe gashi kinga inda kikadawo ki godema allah da sakamakonki yafito tun aduniya da seda kika mutune yazakiyi ....nanfa sell ne bake kadaibace akwai mutane dayawa azagaye dake akwai masu tsaronku iska yanashigomiki kina shaka kinsan cewa kobadade kobajima zaki fita daga cikinsa amma kinajin tsoro kinkasa hakuri kinkasa jurewa inaga ace cikin kabari kika tsinci kanki a inda kintabbata bazaki taba dawowa ba har abada kekadai zaki zauna har tashin alkiyama wannan zuwan danamiki yanzu aikinki ne zaizo miki dan tayaki fira ....sarah wane aiki kika aikata mai kyew dakike tunanin zaki iya zaunawa dashi ....sarah meyasa son ahmad yarufe maki ido har kika manta da allah da manzonsa Wanda su yafi dacewa kiso fiye dakanki kinmanta cewa abunda allah yakaddara bawanda ya isa yacanzashi kinmanta cewa sodayawa kakanso abunda bashine alkhairi agareka ba abunda kake ki kuma yakasance shine mafi alkhairi agareka sarah ubangiji ya making ni'imomi dadama amma maimakon kigodemasa se kike anfani dawannan ni'imar kina saba masa har kika fifita Wanda kikeso akan dokokin allah kuma ahaka kike tunanin zaki samu abunda kike so ?
Tunda yafara magana tasadda kanta akasa banda sheshshekar kuka ba abunda take bai karasaba tasa kai aguywa tana fashewa da kuka mai ban tausayi lokaci guda taji ta tsani kanta nan take tafara nadamar abunda ta aikata kuka take sosai yana rarrashinta dakyar tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya akai akai
wata leda yaciro daga cikin aljihunsa yaciro take awaye da spoon guda biyu ya ijiye atsakiyarsu ai kamar jira take tafara ci ido kawai yazubamata yana kallon yanda takecin abincin kamar bata taba cin irinsa ba dagowa tayi tana kallonsa tace kaci mana
Girgiza kai yayi yana murmushi yace Ni nakoshi kici Kawai
To nima bazan ciba nakoshi nakoshi.....tafada tana ijiye spoon dinta
daukan spoon din yayi yagwada kamar yanaci sannan itama tafara ci har saida takoshi sannan ta ijiye tasha ruwa tana gyatsa tace Kaan me ....
" sekinfada ...
gyara zama tayi tana murmushi tace bantaba cin abinci maidadin wannan ba kodan naji yunwa sosai ne
seda yakai lomar abinci bakinsa sannan yadago yana kallonta yace nima haka kuma kinsan a ina nasaya....abakin titi
Dariya tayi tace wannan shi ake kira ga arha ga dadi
haka sukaci gaba dafiransu yanata sata dariya dama ganshi gwanin barkuanci hartayi bacci sannan ya lallaba yafita bayan yadamka ma yansandan kudi masu dan yawa har ya isa gida yana tunanin abunda sarah tafadamai shi abunda yabashi haushi yanda aysha take kara ingiza sarah tana aikata abubuwa marasa kyew
Haka bashir yaci gaba da kula da sarah kowace rana zaizo dasafe yazo daddare shakuwa mai karfi tashiga tsakaninsu kullun yana kara yimata nasihohi masu rasa zuciya cikin kankanin lokaci tasauya kamar ba itaba tundaga maganganunta da yanayinta da ibadarta komai yana birgeshi afannin aiki kuwa yana bakin kokarinsa aiki yake bawasa yana Tara kudin batare dakowa yasani ba se asma'u kawai yakeba labarin komai
abangaren AK kuwa ba karamar damuwa yashiga ba akan halin da sarah take ciki amma yazama dole ya jure kodan hakan zaisa tagane kuskurenta kowani lokaci asma'u taganshi adamuwa setayi kokarin kawarmasa da ita kodai tatsokaneshi ko kuma ta jashi dole sufita aiki
ita dasu ahmad suna iya kokarinsu wajan gano waye uban cikin aysha amma abun yacutura saboda aysha tagano shirinsu kuma tana taka tsantsan sosai Sam bata yarda suhadu da salim sedai awaya shima secikin dare ta tabbata bawanda zaijita
ranan sukaci karo da bashir zafita wata uwar harara ya watsamata zai wuce tayi saurin shan gabanshi tana fadin wai bashir menamaka ne kwana biyu ko ga maciji bamayi akan wane dalili idan wani Abu namaka kasanardani mana ba wai kadauki gaba daniba
Juyowa yayi yana kallonta cike datakaici yace ke bakikai matsayin dazan dauki gaba dakeba kawai dai idan kasan halin mutum ne sekasan yanda zaka zauna dashi
Sake shiga gabanshi tayi tana banbamin masifa nunata yayi dayatsa yana fadin matsamun inwuce kar intakaki awajan
Kinmatsawa tayi shikuma azuciye yasa hannu yatureta daga gabansa yawuce yana Jan tsaki
turetan dayayi ashe tafadi baisaniba daidai nan asma'u tasuko daga sama tana ganinta akasa tarugo aguje tana kiran sunanta ganin bata motsi yasa bada bata lokaciba takira grany ta taimakata suka nufi asibiti da ita
[26/07, 00:20] Hassan Atk: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN kANWATA_ 👩👧
1⃣9⃣5⃣
Suna isa asibiti aka hau dubata se safa dawamarwa asma'u keyi cike da damuwa grany kam ko agefen gyalenta dan cewa tayi kinibibin aysha ne ba abunda yasameta suna nan tsaye khadeeja ta iso damamaki asma'u ta tareta tana fadin khady lafiya ....mekika zoyi asibiti
Seda suka gaisa da grany sannan tace wurinku nazo yanzu naje gida securities sukace kunzo asibiti waye ba lafiya....
Zaunawa asma'u tayi tana Ciro wayarta tace... aysha
tabe baki tay tana kauda kai kamar jira grany take tamike tana gyara gyalenta tace....to tunda ga khadeeja tazo bari ni inje gida in kintsa kinga daganan se asanar da iyayenta
Dakallo sukabita har tafita sannan khadeeja tajuyo tana fadin wai meyake damunta ne....
bata kulata ba takira Ak awaya tasanar dashi nan take segashi yashigo asibitin afujajan hankali tashe yakaraso wurinsu yana tambayar abunda yafaru
Mikewa asma'u tayi tana riko hannunsa tace kar kadamu ba wani abu bane anakan dubata yanzu .....nima bansan meyafaru ba I just found her on the floor....
juyawa yayi yana dafe kai cike da damuwa sannan yajuyo zaiyi magana kenan yahango khadeeja azaune cike da mamaki yace ke....kuma mekike anan dama tare kuke ne
Saurin mikewa tayi takoma gefensa tana fadin a'a ...ni baruwana da ita.. Kawai nazo karban magani ne naga grany anan ita tagayamun abunda kefaruwa shiyasa natsaya ....
atare suka wurgama asma'u harara sannan AK yakarasa kusan dakin yatsaya khadeeja nabiye dashi abaya tana kashema asma'u ido hade damurmushi
Suna nan zaune doctor yafito azabure suka nufeshi suna hada baki wajan tambayar lafiyarta
Murmushi doctor yayi yana gayamusu bawata matsala sudai kiyaye gaba idan irin haka tana faruwa za'a ita rasa abunda kecikinta
Murmushi AK yayi yanaba doctor hannu yace oh allah nagodema ....zamu iya shiga muganta
"eh ....amma yanzu zanturo nurse tamata allurar bacci dan tadan huta
atare suka fada dakin AK nagaba suna binsa abaya cike da damuwa yakarasa bakin gadon yana riko hannunta yace sannu aysha ....how can u be so careless...kullun inagayamaki kirinka kula dakanki ko kinmanta halin dakike ciki ne
Shiru tayi tana kallon su asma'u fuska adaure koda suka mata sannu ciki ciki ta amsa shi kwa AK se kallonta yake cike datausayi yana jin haushin kansa dayajefata cikin wannan halin kara damko hannunta yayi yana fadin baby tell me how did this happen ....garin Yaya kika fadi
Shagwabe fuska tayi tana kallon asma'u tace nidai AK gaskiya tsoro nakeji kafitar dani daga gidannan idan ba haka ba zata kasheni ko takashe abunda kecikina
Kallonta suke damamaki dan bawanda yafahimci Inda maganarta tadosa fashewa tayi dakuka tana kamo hannayen AK tace AK please ...do something our baby's life is in danger ....
Cike damamaki yace kamar ya bangane mekike nufi ba what is happening
kara kankamesa tayi tana nuna asma'u dayatsa tace gatanan itace ta turani nafadi kuma ranan ma haka tamun ....dama nagayamaka tace seta zubar dacikina amma bakayardaba tonidai gaskiya idan bakadau mataki ba zantafiyata zanyi nesa daku kodan naceci rayuwar dana tunda nalura kai bakasonsa dan batahanyar halal akasameshiba .....takarashe maganar tana fashewa dakuka
Juyowa yayi yana kallon asma'u da jajayen idanuwansa fuska adaure yamike daga zaunan dayake yafara nufota yana fadin you.....kinmanta abunda nagayamiki ranan ko ....ko kindauka wasa nakemiki kawai dan kinga ina kyaleki akan duk abubuwan da kike mun
Jadabaya tafarayi idonta pal kwalla cikin rawar murya tace wait....did u....just believed what she said ...AK karya takemun wallahi why will I do that....
Riko kafadunta yayi dakarfi cikin kakkausar murya yace shut..... up ...kinyi abubuwa dadama abaya nayi shiru nasamiki ido saboda bansan dalilinki nayin hakan ba amma ayanzu kina kokarin taba abunda nafiso fiye dakomai arayuwata ne idan ma kishi yakesaki kike aikata hakan u better stop it coz u have no place in my life .....yana kainan ya turata dakarfi yafita ahasale yana banko kofar
dagowa asma'u tayi tana kallon aysha nadan lokaci sannan tajuya afusace tafita daga dakin tana share kwallar datazubo mata
kauda kai aysha tayi tana Jan tsaki cike datakaici dan ita bahaka taso abun yakasance ba afusace khadeeja tanufeta tana fadin shegiya mai suffar agwagi bari naci ubanku daga ke har cikinki kinga sekiyi sharrin da hujja
Atsorace aysha ta tashi zaune tafara jadabaya tana kwalama AK kira kafin takai gareta nurse tashigo aguje tariko khadeeja tana bata hakuri suna cikin haka AK yashigo aguje yana tambayar meyafaru
aysha zatayi magana kenan suka hada ido da khadeeja tawatsa mata wata uwar harara bashiri tahadiye maganarta tana kalalo murmushin dole juyowa yayi yana kallon khadeeja kafin yayi magana tace Yaya kaje kawai bakomai bane ...adan tsorace takene shiyasa kasan masu ciki da rigima....
Murmushi yayi ya taimaka mata ta kuanta sannan yafita khadeeja tabi bayansa tana kallon nurse din tace sister dama kidankara mata ita awuya tayi mai gabadaya kowa yahuta
Dariya nurse din tayi tana shirya allurar tace a'a ba'ayi hakaba ai zaman tare sehakuri
suna fitowa AK yafita waje ita kuma khadeeja takarasa wurin asma'u tazauna tanata faman masifa itadai asma'u tayi shiru tana tunani ga wayan aysha ahannunta tana jujjuyawa
Dagowa khadeeja tayi tana kallonta cike datakaici tace wai mema yasa kikawota asibiti dakinbarta kawai tamutu awurin sedai aji labarin mutuwarta a social media kinga daganan ma se mugane shashashan daya duramata cikinnan
Saurin dago kai asma'u tayi tana kallonta cike dafarin ciki takamo kumatunta tana fadin kai khady u are too good tundazu ina tunanin abinyi gashi yanzu acikin shirmenki kinbamu shawara kuma ina tunanin zatamana aiki
"Kamar ya bangane ba....
gyara zama tayi tana kunna wayar tace ....khady yanzu wayoyi sunkawo sauki kwarai wajan yada labarai yanzunnan abu zaifaru idan kayi posting kafin minti 30 yagama zaga ko ina duk wani makusancinka zaigani to muma zamuyi anfani dawannan damar wajan yada rashin lafiyar aysha natabbata saurayinta zaigani kuma idan har yana sonta da abunda kecikinta to zaizo kinga mukuma se muga kowaye .....
Cike dafarin ciki khadeeja tarungumeta tana fadin kai gaskiya Amman kinhadu ni nayi maganar cikin Bacin rai ke kuma kinjuyata tadawo shawara ...how amazing
Murmushi asma'u tayi tamika mata wayar tana fadin yanzu gashi jeki daukomana pictures dinta kamar guda uku karki bari taganki kuma kiyi sauri kar ABI yadawo yasameki
Karban wayar tayi tanufi dakin da aysha take cikin sa'a kuwa ta iskota tana bacci har bakin gadon takarasa tayi mata guda uku masu kyew sannan takoma wurin asma'u nan take sukayi posting harda sunan asibitin da room no duka sukasa aikwa ko minti 5 ba'ayi ba sega kiran salim yashigo wayar sedai tayi saving da MD shiyasa basu canki kowaye ba lokaci guda seda yajera missed call sunfi 30 jin shiru yasa hankali tashe yanufo asibitin dan sanin halin datake ciki duk dacewa yanajin tsoro amma kuma sam yakasa natsuwa darashin daga wayarta
suna nan zaune aka kira sallah AK yanufi masallaci khadeeja kuma tashiga dakin da aysha take dan yin alwala asma'u dama tanada alwalarta sedan kwalin khadeeja tashinfida anan wurin ta tada sallarta
AK yazo fita kenan sukaci karo da salim shikuma yana sauri zai shigo juyowa yayi ahasale zaiyi magana ganin AK yasa yayi saurin sunkuy dakai murya can kasa yace sorry
Murmushi AK yayi yace bakomai niyakamata inbaka hakuri ban lura dakai bane
Murmushin yayi shima batare dayace komai ba yajuya yanufi dakin da aysha take
asma'u tana sallah haryawuce tagabanta yashiga dakin duk bata saniba yana leka dakin yaganta akwance cike da damuwa yakarasa kusanta yazauna ahankali yakai hannunsa yana shafa kanta hade dakiran sunanta
Kamar amafarki takejin muryan salim nakiranta ahankali tabude idanuwanta tana ganinsa tafara kokarin tashi tana fadin what are u doing here salim are u mad....meyasa zakazo nan ...yamma akayi Kasan ina asibiti
saurin rikota yayi yana kuantar da ita yace I am sorry sweetheart ...nasan nayi gangancin zuwanan sedai tun da naga kinyi posting rashin lafiyarki I can't control my self kiyi tunanin halin dazan shiga amatsayina na uba idan naganki acikin wannan halin
Zaro ido tayi tana kallonsa damamaki tace posting fa kace .....salim ni banyi posting din ko.....karan rife kofar dasukaji ne yakatsemata maganarta atsorace suka juya suna kallon kofar cikin rawar murya tace ohhh my god....salim please just get out of here ...we will talk later ...just leave
saurin mikewa yayi yana manna mata kiss agoshi da cikinta sannan yanufi kofar sedai koda yamurda yajita akulle bayanda baiyiba amma yakasa budeta juyowa yayi yana dafe kai yace aysha ankulle kofar daga waje
Hannu tadora akai tana fashewa dakuka tace dama nasani shikenan yanzu asirina yatonu nasiga uku ni aysha jin ana kokarin bude kofar yasa salim yayi saurin boyewa bayan labule ita kuma aysha takoma ta kuanta sedai hantar cikinta banda kadawa ba abunda take har wata zufa ke gangarowa agoshinta
khadeeja ta turo kofar tashigo se asma'u da AK abayanta suna bin dakin dakallo har bakin gadon AK yakarasa yana fadin deeja ni banga kowa ba kuma kince anan kika gansa zaune
Kofar bayi tabude taleka sannan tafito jiki asanyaye tana kallonsu tace Yaya allah dagaske nagansa kuma har nakulle kofar yana ciki baifita ba
Juyawa yayi damamaki yana kallon aysha yace aysha wani yashigo dakin nan ne
Girgiza kai tayi tana tabe baki tace to waye kwa zaishigo inaga dai abunda ya tsoratani dazu nakira sunanka shine itama ya tsoratata ....kasan yara da rigima
Sunkuy dakai khadeeja tayi tana mamakin ina mutumin yashiga kodai imagination dinta ne ...
Juyawa asma'u tayi zata fita kawai tahango takalmin salim daga kasa zaro ido aysha tayi atsorace ganin tanufi wajan labulen yasa takwala ihu tana dafe cikinta har wani fizgefizge take kamar mai fitan rai
Hankali tashe suka nufeta suna
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 35