like I can see and hear only one thing and that is you!!!
I will never let you go no matter what situation we are in I love and care about u for ever
Sunkuy dakanta tayi kasa tacigaba dafadin
I wish I could tell about my feelings in the morning ,middle of the night when I eats during sleep in happiness and in sadness I just want to tell u that ....
I LOVE YOU !!!
tafada cikin murya mai kaman rada tana kallon cikin idonsa
tsaye yayi kamar gunki tunda tafara magana yake kallonta seda yaji ta tabasa tana fadin ya kaji to
ajiyar zuciya ya sauke yana tafa hannu yace bravo!!!
Chitti excellent
gaskiya kin hadu ina fata dai ba ji kikayi anfada ba ko a film ko book
Daure fuska tayi tana barin wurin tace allah ninayi dan bakasan dauriyan danayi bane kafin nafada shiyasa
Rikota yayi yace ohh to ainace yayi kinyi kokari to be honest kinfi aysha kokari gaskiya kincinye gasar
Dariya tayi tace ok to yamaganar deal dinmu zaka daina kirana chitti daga yau
Sosa kai yayi yana fita daga dakin yace ehhhh toooh gaskiya bansaniba bakina yasaba da chitti amma zan daina tsokanarki daga gobe
Baki bude take binsa dakallo har yafita
cikin kuana biyu aka fara shirye shiryen bikin khadeeja da ahmad har many a sungama magana antsaida daurin aure ranar juma'a
Tuni asma'u suka fara gyara amarya
Ango ma yadawo dashi ake komai ranar da yadawo AK da asma'u sukaje tarbanshi a airport
Bayan sunkaishi gida suka zauan apalo suna fira
anan yaciro wasu agogo guda biyu masu kyew iri daya namace da na namiji yabasu amatsayin tsaraba
Kin karba AK yayi wai bazaiyi Abu iri daya da asma'u ba
Seda ahmad yarokesa yana gayamasa agogon yanada anfani ahaka zaka dauka agogo ne kawai amma yana da wani Abu ajiki inda idan dayanku yashiga matsala yana dannan nan
Ko a ina kake dayan agogn zai fara kara yana nuna jan danja alamun dan uwanka yana cikin matsala he need ur help sannan arrow zai nuna maka direction din inda dan uwanka yake har ka iskosa
karban agogon yayi yana dubawa dan tabbas ya birgesa amma bai yarda zaimasa wani anfani ba
cikin aljihu yasaka shi ita kuma asma'u tun alokacin ta daura nata ahannu
Yana zuwa gida yajanyo drawer yasakashi aciki
Duk abunda ake sarah tana sane amma Sam bata nuna damuwarta ba kawai dai bata shiga har Kansu ne kullun tana dakinta ko palon kasa azaune gaisuwa kawai take hadasu da AK se jefi jefi sukan dan taba fira
amma har yanzu tana nan da alwashin ko zata rasa ranta bazata bar khadeeja ta auri ahmad ba
Bangaren aysha da iyayenta kuwa komai ya cakude masu gaba daya sunkasa gane kan lamarin kwarai AK yafara janye jikinsa daga aysha sukan dan yi fira ko yadauketa sufita amma ba kamar da ba sedai har yanzu yana nan da niyyar zai aureta koda bai saki asma'u ba
tsakaninsa da asma'u kuma shakuwa mai karfi tashiga tsakani da taiamkon inna ameena sukan zauna suyi fira na tsawon lokaci yagan gayamata matsalolinsa kuma tabashi shawara sedai tsokanar se abunda yaci gaba basa zama na minti Biyar batare da sunyi fada ba kuma shike janyo hakan dagangan saboda yana jin dadin yanda take biyemishi
Sonsa se Dada karuwa yake aranta amma har yanzu tana kokarin dannewa bawanda yasan da hakan se khadeeja da ahmad bangaren AK kuma ba wata alama da ta nuna yakamu da sonta sedai yashaku da ita matuka
Ba yanda khadeeja batayi ba kan asma'u tagayama AK cewa tana sonsa kafin lokaci yakure mata amma taki hakan yasa suka hade kai da ahmad wai indai bata fada ba to bazasuyi auren ba
ita kuma taki fada saboda tana tsoron idan tafurta hakan tarasa kulawar datake samu daga garesa
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣4⃣0⃣
sarah ce tsaye tare da wani mutum suna magana
wani photo taciro daga jakanta Tamika mishi tana fadin JJ katabbata ba'asamu wata matsala ba dan aikin bana wasa bane ka kula
karban photon yayi yana kallo cikin muryan mashaya yace wacce daga ciki
wankan tarwadan kayi ahankali tanada wayo ba kyala bace please kar asamu mistake
Dariya yayi irin tasu sannan yasaka photon aljihu yana fadin hajiya bafa yau nafara aikinnan ba to kawai kije zakiga mai kyew nidai kawai inji alert dan alqur'an banda mutunci
Kallonshi tayi sama dakasa sannan tajuya tana fadin base kafada ba nasan bakada shi shiyasa nazo wurinka
tana tafiya yakira yaranshi guda biyu yabasu photon yana fadin gayu gafa aikinmu nayau kuma ga dukkan alamu zamu samu mai tsoka dan naga yarinyar yar masu Jan wuya ce
dariya suka sa gaba daya suka hada baki wurin fadin kai kaga wasu zuka zukan yan mata
daya daga cikinsu yace oga wane kalan aiki za'amusu
a'a guda daya zaku kwamusu mana amma bance kuyi mata komai ba kudai kawai Ku kawota address din yana jikin photon daga baya
"angama oga wannan ai karamin aikin mune wa'yannan yan yaran ai mutun daya ma acikinmu ya ishesu amma wacce daga ciki
juyawa yayi yabar wurin yana fadin kyekkyewar cikinsu kuma kuyi ahankali kar kowa yaganku lokacinda zaku kamata
kallon juna sukayi sannan suka kara kallon photon dayan cikinsu yace
bala kaji yallabai wai kyekkyewar cikinsu to ai suduka kyewawa ne
Dariya Wanda aka kira da bala yayi yana dora yatsanshi kan photon khadeeja yace amma dai kasan wannan tafi gogewa ko haka sukaci gaba da jayayya kowa dawacce tafimashi kyew
Tunsafe asma'u taje dawko khadeeja daga gida kasancewar yau ne ake sa lalle
Har sunkawo bakin get zasu fito khadeeja takoma wai tayi mantuwa fita asma'u tayi tanufi mota tana jiranta
yaran JJ suna daga gefe cikin mota suna jiran fitowar yarinyar daga gidan saboda yanda sukayi da sarah kenan ganin asma'u yasa dayan wanda yace tafi kyew yayi saurin nufar inda take cikin sanda yana ciro handkerchief a aljihunsa yana zuwa tabayanta yakai hannu zai shaka mata handkerchief din kawai yaji ana kokarin fitowa daga gida saurin jadabaya yayi yalabe bayan mota yana kallonsu har suka shiga driver yaja suka tafi
dunkule hannu yayi yanaushe iska cike da takaici ya koma wurin dan uwansa dake cikin mota
anan suka kira JJ suka sanardashi yanda akayi nan take ya hau zaginsu kuma yamusu kashedin idan suka dawo batare da yarinyar ba sai ya aikasu barzahu
sanin zai iya yin hakan yasa ba shiri suka bi bayan motar su asma'u
sarah tana ganin su khadeeja takira JJ tafara masifa akan ba haka sukayi dashiba idan yasan bazai iyaba ya dawo mata da kudinta tanemi wani hakuri yabata akan komai zai tafi daidai kawai dai tayi kokarin turo yarinyar waje sukuma zasu cika sauran aikin
Bayan asma'u takai khadeeja bangaren grany ita kuma tawuce dakinta dan tashirya
Tsaye take agaban dressing mirror tana gyara fuskarta
AK yashigo cikin shirinsa tsap na kananun kaya yayi kyew matuka kusa da ita yamatso yadauki turarensa yafara fesawa
Dagowa tayi tana kallonsa tace ABI ya isa haka mana turare in yayi yawa hawa kai yake kuma ma da lalle namata ne kawai why are u dressing up
daure fuska yayi yace stop treating me like a child I know what I am doing
Dariya tayi tace ohhh fita zakayi ne
"eh ko inzauna baki gaji da ganina ba
juyowa tayi tana kallonsa baki bude tace waaaaa meye anan dabazan gaji daganiba
Dariya yayi yajera da ita a gaban dressing mirror suna kallon Kansu yace kalla da kyew kiga ba yabon kaiba amma kema kinsan kinfini.....bai karasaba yayi sairin fadin I mean nafiki haduwa
Dariya tayi tana tafa hannu tace ABI bakinka yanaso yafadi gaskiya kana hanashi kama daina yaudaran kanka dan kasan nidin dabance
dariya yayi yana kallon bayan rigarta yace ohhh naga alama duk cikin gayun ne kika bar zip abude
Saurin juyawa tayi tana taba bayan rigarta tajishi abude
Murmushin yake tayi tana kokarin jan zip din tace nakasa zipping dinshi ne
"zo in taimaka miki
"to amma karufe idonka tukunna
Juyo da ita yayi yana fadin dan allah can mezan gani abayanki
kokarin Jan zip din yake amma yakiyi dagowa yayi yana kallonta tajikin mirror yace chitti wai dole se wannan kayan kicanza wasu mana
"kaja dakarfi mana se kace ba namiji ba
bata karasaba yaja zip din da karfi yayi sama dashi
thank you ...
tafada tana fita daga dakin
Zaro ido yayi yana kallon abun zip dinta dake hannunsa ahankali ya furta I am in trouble
bayan mutane sun taru aka fara shagali gidan yacika da mutane hakan yasa sarah bata samu damar aiwatar da aikinta ba gashi Sam khadeeja taki bata fuska bare tasamu damar fitar da ita waje
asma'u na hidima da baki Sam bata lura da zip dinta daya fara budewa ba AK yazo yana magana da grany kawai ya hango zip din abude gashi da mutane dayawa awurin har da yan samari
Kusa da ita yaje ya tsaya daga bayanta yana kokarin boye wurin
juyowa tayi da mamki tace miye haka wani Abu kake so ne
Kara dawowa bayanta yayi cikin rada yace muje dakinmu
Zaro ido tayi tace what kamar ya muje daki wai ma bakace fita zakayi ba
hannunsa yadora kan bayanta yace kedai idan munje zan miki bayani
kokarin juyowa take amma yahanata ga mutane sun fara kallonsu ana gulma
aysha dake gefe tana hangosu tuni idonta yaciko da hawaye sarah kuma ko ajikinta abunda yadameta daban
"ABI kabari mana baka ganin mutane suna kallonmu ne
Barin wurin yayi yana fadin shikenan nabari amma kinemi wani Abu kirufe bayanki dan har bra....
bai karasa ba tayi wata irin supper tashige gabansa tana fadin ya ....ya....kuma haka bayan kace kayi zipping dinsa
Matsawa yayi takara shiga gabansa tana fadin ina kuma zakaje tunda kai kabatamun kai zaka kaini na gyara
dariya yayi yace se kinroka kuma da girmamawa
langwabar dakai tayi cikin siriruwar murya tace ABI can u help me please nasan kanada kirki da taimako to nima kataimaka mun kaji
Dariya yayi yace se kince nafiki haduwa haduwa
bai karasa ba tayi saurin fadin haba ai fada ma bata baki ne yanda kake handsome dinnan ina zan hada kaina dakai
Now please muje kakaini daki
sun juya zasu tafi kenan inna ameena ta taresu tana danne dariyarta tace ina zuwa haka
Murmushi AK yayi yace inna daki zamuje akwai abunda zamuyi
kallonsu tayi sama da kasa tace naga alaaaaama to Ku koma bayanzu ba bakwa ganin da mutane ne
Langwabar dakai yayi yace inna please emergency ne yanzu zamu dawo
Dariya tayi tace ohhh bazaku iya jira har awatse ba
Zai yi magana kenan asma'u ta taka kafarsa cikin murya mai kaman rada tace u better keep quite daban abunda kake nufi ita kuma daban inda tafassara maganarka
basu kara cewa komai ba suka raba tagefenta suka wuce ita agaba shi abaya yadora hannunsa akan bayanta
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: Suna hawa kan stairs suka hadu da aysha tana atsaye taharde hannaye tana kallonsu
Meyake faruwa ne.....
tafada tana kallonsu daya bayan daya
Murmushi yayi yana kallon asma'u yace ba abunda yafaru kidan bamu waje muwuce
Fashewa tayi da kuka tana fadin AK wallahi abunda kake mun yafara isata ina alkwarin da kadaukamun haka mukayi dakai kuana biyu kacanza mun to wallahi zanje nafadama grany duk abunda yake faruwa
Saurin riko hannunta yayi yanuna mata bayan rigar asma'u yace kinga daki zan rakata ta gyara tunda ni nabata mata
Idan kuma zaki rakata shikenan
Murmushi tayi tana kallon asma'u tace eh zan kaita amma nima zaka fita dani
Mezai hana je kidawo
Hannunsa yakai yaja kuncinta yana fadin baby u know I love u na
saurin barin wurin asma'u tayi tana jin wani azababben kishi na dukan zuciyarta
juyawa sukayi shi da aysha suka fita da dabara dan kar wani yagansu
anyi shagali komai yatafi daidai amarya tasha lalle tayi tsap ga umm tun tuni tafara aikinta wato gyaran jiki kuana biyu khadeeja tayi fresh kyenta yakara fitowa yau zata koma gida saboda gobe daurin aure jibi kuma suci gaba da sauran shagulgulan kamar su sisters day dinner walima da dai sauransu
har yanzu yaran JJ suna waje suna jiran fitowar khadeeja amma shiru sarah najin asma'u da Ummi zasu maida khadeeja tayi saurin gayamusu
bayan asma'u takai Ummi da khadeeja tafito zata tafi tazo bude motar tajita arufe zagayowa tayi wurin driver tana knocking kawai taji an toshe mata hanci da handkerchief din dayasha powder
Kokarin kwace kanta take amma takasa sun jima suna kokawa dashi kafin daga karshi tafadi asume
saurin fitowa dayan yayi Yakama mishi suka sakata amota
Seda suka bar unguwar sannan suka kira JJ nan yagayamusu inda zasu kaita cikin wani dokar daji inda suka tanadeshi dan irin haka
Tafiya ce mai tsawo kafin sukai
bayan AK yadawo da aysha da daddare yawuce daki amma baiga asma'u baidamu ba yayi shirin kuanciyarsa ya kuanta dan atunaninsa tana bangaren grany suna hidimarsu
Ganin karfe daya tayi yaji yafara damuwa da rashinta adakin tashi yayi har zai fita se kuma yadawo yadauki wayansa yakirata tana ringing ba adauka
Yana nan zaune har karfe biyu tayi fita yayi daga dakin yanufi bangaren grany
Koda yaje har sun rufe Yajima awurin yana tunanin yatashesu ko yakyalesu amma zuciyarshi nabashi wani Abu yasamu chitti
Buga kofar yayi ahankali can anjima inna ameena tazo tabude da mamaki take kallonsa tace AK lafiya meyafaru...
Shiru yayi dan baisan mezai cemata ba
Kallon bayansa tayi tana fadin ina asma'u ko wani abune yafaru
Saurin dagowa yayi yana kallonta da mamaki yace inna bangane ina asma'u ba kina nufin batanan
anan dai suka fahimci asma'u tunda takai khadeeja bata dawo ba
Komawa bangarensa yayi ya kuanta hankali kuance yana fadin to wai meyasa nadamu da rashinta akusa dani murmushi yayi yace koda yake nasaba da shirmanta ne
da asuba Abba yafito zaije masallaci kenan yaga motar gidan AK awaje bai kulata ba yawuce saboda kar yamakara salla
Yana zuwa masallaci kuma yamanta se wajan karfe 7 fa'iz yamatso kusa dashi cikin rada yace Abba dazu dazan zo masallaci naga motar AK awaje
dafe kai Abba yayi yana salati yace kaga ni nama manta tashi muje muga allah sa lafiya kila paci tayi suka barta anan
Seda safe yaran JJ suka isa wannan wurin acikin dajin allah ko duhunsa kayane suna zuwa suka Shiga da ita runfarsu suka daureta ajikin iccan runfar sannan suka sanar da JJ sun isa
Cike dafarin ciki yace musu sukula da ita gayanan kan hanya
Su Abba nazuwa suka isko driver amotar knocking Abba yayi amma shiru seda yasakeyi dakarfi sannan drivan yatashi yana date kai yana runtse ido
Saurin gyara zamansa yayi yana kallon inda bude kofar yayi yafito suka gaisa da Abba kansa adaure yake kallon wurin yana kokarin tuna abunda yafaru jiya
kallon juna Abba da fa'iz sukayi sannan Abba ya kalli driver yana murmushi yace sannu ko allah sa dai Lafiya naga alama kamar anan ka kuana
Saurin riko hannun Abba yayi yana fadin malam ina madam
da mamki Abba yace wace madam kuma bayan tun jiya ta tafi gida
Shiru yayi nadan lokaci kana yazauna akan kujerar motar yana fadin dan allah zan samu ruwan alwalwala
kallon fa'iz Abba yayi yace jeka kakamasa ruwan alwalan daga nan kace khadeeja tadamo masa kunu ko tea yadan sha
anan wurin yashinfida sallaya yayi sallah nan khadeeja takamasa tea mai zafi karban tea din yayi ya ijiye yana kallon Abba yace wato malam jiya ina cikin mota azaune ina jiran madam tafito kawai naji ankwakwasa kofa lekowan dazanyi kawai naji anfesa mun wani Abu to daga nan kuma bansan inda nakeba se yanzu shiyasa kaji natambaya ina madam
salati Abba yayi cike da al'ajabi yace allah ya kyewta to miye dalilin haka oho mun gode allah dai tunda basu maka komai ba
Inaga asma'u tafito tajika shiru tazata bacci kake ga dare yayi shiyasa tawuce gida
Karasawa wurin motar khadeeja tayi tana kure wurin da ido tace a'a wani Abu ne yasameta
kallonta sukayi da mamki zugunnawa tayi takasa tadauko sarkan asma'u dake yashe awurin cikin rawar murya tace tabbas wani Abu yasami ammah ga alamun inda tayi kokarin kwace kanta nan ga jakanta akarkashin mota
Azabure suka mike suna nufo wurin hankali tashe fa'iz yaje yakira su Umma nan fa aka fara salati su inna tuni anfara kuka
Nan take khadeeja khadeeja takira wayar AK seda takusa katsewa yadaga yana dariya cikin muryan bacci yace
deeja karfe 2:00 ne daurin auren ko nine angon ai kya barni indan yi bacci ko
Cikin muryan kuka takatseshi da fadin
Yaya ammah tana nan ?
azabure ya zauna bakin gado yana fadin banganeba kardai kice mun ba anan takuana ba tunjiya bata dawo gidannan ba ai
Sulalewa tayi awurin tana sakin wani irin kuka mai cike da tashin hankali
dafata fa'iz yayi yana kuantar mata da hankali Abba kuma yana rarrashin Umma da inna
bashiri AK yasaka kayansa ko wanka baiyiba yafito agurguje daga bangarensa haduwa yayi da sarah ta rikoshi tana fadin
Yaya ina zuwa haka da sassafe
kuace hannunsa yayi yafita yana fadin gidansu asma'u zani akwai matsala zamuyi magana anjima
dakallo tabisa tana murmushin mugunta har yafita sannan ta wuce dakin aysha da gudu tafada kan gado tana murna
atsorace aysha ta tashi tana tambayar menene
Dariya sarah tayi tace gaskiya yau ina cikin farin ciki nacika burina yanzu tunda ahmad yarasa khadeeja ai dole yadawo gareni
da mamki aysha tace wai meyafaru ne kike wannan murnan
Kamo hannunta tayi tana murmushi tabata labarin duk abunda yafaru
Zaro ido aysha tayi tace to yanzu mezaki mata
Dage kafada tayi tace oho ni yanzu nagama nawa duk abunda suka ga dama sumata ba matsalata bace
Komawa aysha tayi ta kuanta tana fadin gaskiya sarah bakida dama se yanzu nakara yarda zaki iya yin komai akan ahmad
Murmushi tayi tadauki wayanta takira JJ yana dauka tace aiki yayi kyew JJ anjima kadan zakaji alert dariya yayi irin ta rikakkun yane fashi sannan cikin muryan mashaya yace nagayamiki aikinki bazai kuana ba kedai kawai ki tabbata kin biyani shine kawai
Karkadamu tafada tana katse kiran
AK na isa wurinsu Abba aka tabbar cewa wani Abu ne yasamu asma'u nan take yakira ahmad yasanar dashi ba bata lokaci ya iso wurin
Nan take suka wuce police station suka yi repot abunka da masu dashi nan take aka shiga Neman asma'u ruwa ajallo har sanarwa akasa gidan TV da Radio
Kafin gari ya waye kowa yasan da batan asma'u hankalin kowa atashe wasu nakuka wasu na rarrashi
AK da ahmad kuwa tare dasu ake nemanta amma har rana tafarayi ba ita ba labarinta
JJ na isa qurin yaran suka bude mashi fuskar asma'u
Saurin ja dabaya yayi yana zabga ashariya
Kallonsu yayi da jajayen idanuwansa yace dan ubanku wane dan jahila ne yakamota acikin
saurin nuna dan uwansa yayi yana fadin oga shine yakamota dama nagayamasa ba ita bace amma yaki saurarona
Cikin rawar murya dayan yace oga kaifa kace kyekkyewa kuma wannan tafi kyew
Wankeshi yayi da wawan wari cikin kakkawsar murya yace kai jahilin inane dan tasha kawai bakaga waccan tafi faso gari bane shine zaku faukomun wannan karamin alhakin inyime da ita
Shiru sukayi kansu akasa suna bashi hakuri
Ahankali asma'u tafara bude idanuwanta har tasaukesu akan wa innan rikakkun mazan saurin ja dabaya tafarayi amma tajita adaure atsorace take kallonsu cikin rawar murya tace su....suwaye Ku....menake anan
kusa da ita yamatso yazugunna yanafadin sorry yan mata tsotsayi ne yahau kanki nuna mata photon yayi yace wannan mukaso kamawa shine muka kamoki inda kike kuma nikaina bansan wurin ba
zatayi magana kenan wayarsa tahau kara ganin sunan sarah yasa yafita daga qurin yana daga wayar
Cike da masifa tace JJ wane kalan aikin banza kamun ne
katseta yayi dafadin hajiya kidan rage muryanki dan allah banason ana cikamun kunne da ihu inace dai kinbani aiki ko to matsalar da akasamu aciki tawace kuma ni zan gyarata kibarni nayi aikina kar kidameni
yana kainan yakatse kiran yana kunduma mata ashar
Dakallo sarah tabi wayarta cike da takaici tace jimun da iska nizai nuna ma dabanci
dafata aysha tayi tana boye dariyarta tace take it easy sarah kinsan mutanan nan ba imani ne dasuba kar su miki wani abun
banza tayi da ita tana zama bakin gado hade da dafe kai
Fita aysha tayi tanufi bangaresu tana murna tasanar dasu abunda yafaru cike dafarin ciki sadiya tarungume ta tana fadin allah sa ma sukashe yar banza wallahi da munji dadi
Dariya uncle jamilu yayi yace sarah nabirgeni akwaita da banzan hali Indai taso Abu to setayi duk yanda tayi tasameshi
dariya aysha tayi tace ni kuma ina anfani dawannan damar ina biyan bukatuna gashi yanzu ina kuance tagama mun aikina natabbata yanzu AK zai dawo kaina tunda waccan dai nasan ba dawowa zatayi ba
Har dare AK da ahmad natare da police suna nemata amma ba labari da kyar ahmad yaja AK suka koma gida saboda dare yayi kan gobe zasu dawo aci gaba da nemanta
komawa cikin gari JJ yayi yabar yaransa hudu tare da asma'u yatafi da biyu akan zai je yaga abunda yakamata yayi
kallonsu yayi yana hura sigari yace kar Wanda yamata wani Abu zanje indawo kafin nan muga abunda abunda yadace idan maidata za'ayi to idan kuma aikata zamuyi duk dai dayane
kuka tafarayi tana rokonsu surabu da ita amma bai kulata ba yafita sauran yaran kuma suka koma gefe suna kora giyarsu suna fira
Jiki asanyaye AK yashigo gida saurin yaroshi grany tayi tana fadin Abidi ya ake ciki har yanzu ba labari
Zama yayi kan kujera yana dafe kai yace har yanzu shiru grany ni ina mamkin suwaye zasu mata haka dafari nayi tunanin kidnapers ne to amma kuma har yanzu ba'akira kowa daga cikinmu ba abun yana dauremun kai
Zama tayi kusa dashi tana salati tace allah sarki asma'u ko awane hali take oho
Allah yakareta daga sharrinsu ...inji inna ameena
Ameen ....suka amsa gaba daya
Daran ranan Sam AK baiyi bacci ba duk Inda yakalla tunanin asma'u kawai yake yakosa safiya tayi yaje nemanta
da sassafe ahmad yazo gidan zasu wuce tare da AK yana shigowa AK yamike dama shikadai yake jira bangarensa yawuce dan yashirya sutafi
Asma'u nazaune banda kuka ba abunda take se rokonsu take su kwanceta tayi sallah amma sunki wai tabari intaje lahira tayi
Dasafe dai cikin yaran yakamata wata busashshiyar waina da pure water ya ijiye kusa da ita bakinsa duk warin giya yace gashi kija yan mata cikin nawa nabaki badan haka bama bazaki ciki komai ba
Kauda kai tayi tanaji kamar zatayi amai
Kuance mata hannu daya yayi yadaure dayan abaya har yajuya yadawo ya kwance agogon hannunta yana murmushi yawuce wurin yan uwansa yana fadin gayu kunga wani dan ubansun agogo kuwa
Kuka tasa tana rokon yabata agogonta amma basu kulata ba dayan yafara tattaba agogon yana fadin alqur'an bantaba ganin agogo irin wannan ba
AK yafito daga dressing room cikin shirinsa na kananun kaya lite blue din gins da farar shirt
Har zaifita kawai yaji wani Abu nakara daga cikin bedside drawer
Kamar yashareshi se kuma yadawo yana janyo drawer yaga agogon da ahmad yabashi yana kara yana nuna Jan danja
Saurin daukar agogon yayi yana sakin wani sassanyan murmushi aguje ya fito daga bangarensa yana kwalama ahmad kira
azabure suka mike tsaye suna kallonsa agogon yamikama ahmad yana fadin friend kalla agogon dakabani natabbata chitti ce ke kirana agogonta yana hannunta
Cike da farin ciki ahmad yakarba agogon yadanna wani wuri sega arrow din yajuya yafara nuna direction
kwace agogon AK yayi yanufi hanyar fita yana fadin friend bari naje kai kaje kutaho da yan sandan zamu rika magana awaya
saurin rikoshi ahmad yayi yana fadin haba AK inazakaje kai kadai bakasan wa yanne irin mutane bane kajira muje tare mana
girgiza kai yayi yana kuace hannunsa yace a'a Ahmad bazan iya jiraba akowane lokaci nashiga matsala tana tare dani har sai taga nawarware to nima gaskiya bazan bata lokaci ba kafin nataimaketa kaidai kawai kazo da police
Riko ahmad grany tayi tana fadin ahmadi yanada gaskiya barshi yatafi allah yana tare dasu
rungumeshi ahmad
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 35