munafuka tambaya ma kike meyafaru ke baki ji kunya ba da aurenki amma kinabin wani wallahi se kinfadamun ina ahmad dina yake
Da kyar AK ya kwaceta a hannun sarah
Kallonta yake da rinannun idanuwansa yace tambayar ki nake ina ahmad kigayamun ko yanzu in cimaki mutunci abainan jama'a
Fashewa tayi da kuka tarikoshi tana fadin dan allah kayi hakuri wallahi bansan inda ahmad yakeba Ni yanzuma nashigo gidan nan ban San meyake faruwa
Nufota sarah tayi aguje tana fadin wallahi karya kike kinsan inda yake dazu batare naganku ba narantse idan baki fadi inda yake ba sena kasheki
Riko hannunta AK yayi sannan yakalli asma'u yana daka mata tsawa yace get out of my room
Fita tayi tana kara fashewa da kuka
Zaunar da sarah yayi bakin gado cikin sigar lallashi yace calm down sarah koma ina ahmad yake zan nemosa kuantar da hankalinki kar mutane sugane halin da ake ciki
Cikin sheshshekar kuka tace to Yaya adaura auren mana ai ba dole se yana nan ba
Girgiza kai yayi yana share mata hawaye yace ba yanda za'a daura aure batare da amincewarsa ba sarah kidan bani lokaci zansan abunyi
Kuantawa tayi akan gadon tana rera kukanta mai cin rai
Tsaye yayi yana kallonta nadan lokaci kafin yasauke nannauyar ajiyar zuciya yana fita daga dakin
Asma'u nafita takira wayar khadeeja tana tambayr ko taga ahmad
Da mamaki khadeeja tace a'a ammah bangansa ba meyafaru
" khadeeja ahmad bayanan annemesa anrasa kuma ana kiransa baya dagawa
ko yakiraki ne
" bansaniba naga kiranshi dazu amma bandauka ba nakashe wayar
" OK to ki kirashi yanzu muji ko zai daga
abangaren Momy ma Neman ahmad take har zata kira AK taji wayanta na ringing tana dubawa taga ahmad
Bayan tadauka tayi sallama
Cikin wata iriyar murya kaman mai shirin fashewa da kuka yace
Momy nafasa auren sarah khadeeja nakeso kuma ita zan aura kome zai faru yafaru nagama yanke hukunci
Murmushi Momy tayi tace
Ahmad kayanke hukuncin da yadace akurarren lokaci
amma ba komai haka allah yakaddara
Jin anturo kofa yasa ta ijiye wayar
AK ne yashigo cike da damuwa ko gaisawa basuyi ba yace Momy ina ahmad
"Banganshiba AK rabona dashi yatafi wurinka....
Bata karasa ba ya juya yabar palon
Yana fita ta kira Ahmad tace AK yazo nemansa
Kiran AK yayi awaya bugu biyu yadaga ahasale yace ai bandauka zaka iya kirana ba ahmad meyasa zaka mun haka meyasa kake so ka tozartani ne
Wai natambayeka miye laifin sarah da kake wulakanta ta
Cikin rawar murya ahmad yace AK katsaya kasaurare ni bakaga wasika...
Bai karasaba ya katseshi dafadin
Mezaka gayamun Wanda bansani ba
Bazaka iya auren sarah ba kanada wacce kake so
Soyayya soyayya
Koba abunda zaka gayamun kenan ba
To tsaya kaji zan iya yafe komai amma bana abunda yashafi familyna
Yana kainan yakatse wayar hade da dukan sitiyarin motar da karfe
Ahmad ma kuance yake acikin motar sa ga idonsa yayi ja kana ganinsa kasan yana cikin damuwa
Wayarsa ne yafara ringing yana dubawa yaga my flying bird
Saurin daukar wayar yayi yana fadin haba deeja meyasa zakiki daukar wayana kikasan mezan gayamaki
"Mezaka gayamun kwa banda kafasa auren sarah
Kasan halin da kajefa yayata aciki kuwa wannan shine sonda kake ikrarin kana mun ...
" deeja please dan allah kisaurareni inaso muhadu dake maganar bana waya bane
Shuru tayi nadan lokaci kana daga baya ta amince ya gayamata inda zasu hadu
Tana kashe wayar takira Asma'u tagayamata
Asma'u tace taje suhadu itama zata zo wurin suyi magana
Ganin magariba tagabato yasa akaba mutane hakuri akan anfasa taron bikin se wani lokaci
asma'u na idar da sallar magriba tafito danufin tafiya wurin su ahmad tahadu da aysha
Riko hannunta aysha tayi cikin sassanyar murya tace asma'u kiyi hakuri akan abunda yafaru kwanaki se yanzu nagane bakida laifi Ashe kanwarki ahmad keso bakeba yanzu gashi kina fuskantar matsala ta dalilin hakan
Murmushi Asma'u tayi tace bakomai nagode da kika fahimceni amma dan allah karki gayama kowa yanzu ma haka wurin ahmad zani narokeshi yadawo saboda nayarda sarah tana tsananin sonsa
Murmushi aysha tayi tace OK kunyi magana da ahmad yana ina
Batare da tunanin komai ba asma'u tagayamata inda zata sannan tawuce tana sauri
Da kallo aysha tabita tana murmushin mugunta sannan tanufi wurin AK da sarah dawata takarda ahannunta
Tana shiga Tamika ma AK takardar tana fadin gawannan nasamu adakinka kuma yanzu nahadu da asma'u zataje wurin ahmad
Karban takardar AK yayi yana karatawa afili kamar haka
I am sorry friend naso na hakura na auri sarah amma bazan iya jure ganin asma'u amatsayin matarka ba gaskiya idan dai kanaso na auri sarah to se kasaki asma'u tukunnan ...
Ur friend ahmad
Runtse ido yayi cike da takaici yace wai yaushe ahmad yazama hakane dama wannan ce wasikar dayake maganar ko nagani
Dafashi aysha tayi tana fadin AK to kasaki asma'un mana tunda yace hakan ne kawai zaisa ya auri sarah
Harara ya watsamata bashiri tayi shiru tana ja dabaya
Tambayarta yayi ina asma'u zataje
Tana fadamai ya dauki makullin motarsa yafita
Khadeeja na isa ahmad yatareta da damuwa yace deeja meyasa kike wahalar danine
Daure fuska tayi tace ko ni kake wahalar daniba kasan bazaka cikamun alkawari ba meyasa ka dauka akan wane dalili kafasa auren sarah
Ahasale yace wai khadeeja meyake damun kine meyasa kike takura zuciyarki kihanata abunda takeso kawai dan kifarantama wasu
Itama ahasale tace ni bantakurawa zuciyata ba Tarzan kawaidai sonka ne nadaina yi kakasa ganewa ada nasoka amma yanzu bana sonka saboda kai kajefa yayata ahalin da take ciki yanzu
Zaiyi magana kenan asma'u ta iso
Karasawa yayi wurinta yana fadin yawwa asma'u dan allh kima khadeeja magana tagane abunda nake kuatanta mata munason junanmu meyasa zamu takura kanmu
Daga inda khadeeja take tace bana sonka ni kuma bazan aureka ba
Janshi gefe Asma'u tayi cikin sassanyar murya tace ahmad meyasa zakamun haka seda nace karkaje ko ina amma bakajiba yanzu miye anfanin abunda kayi
Shafa kansa yayi yana runtse ido yace aunty kigane nibazan auri sarah ba naji da kunnena tana fadin daga na aureta AK zai sakeki to mezai sa na aureta
"Ahmad kamanta dawannan zanji dashi amma sarah tana mutuwar sonka ahmad kar kaso kaga halin da tashiga lokacinda ka tafi she lost her mind bcoz of u
Meyasa bazaka tausayamata ba
Zaiyi magana kenan sukaji karan rufe mota dakarfi
Juyowa sukayi atare dan ganin waye AK suka gani yana nufosu kamar mayinwacin zaki
Yana zuwa ya cakumi wuyan ahmad yahada shi da mota yana fadin how dare u ahmad kawai dan kaga ina kyaleka bakajin kunya kana kebewa da matar aure
Me kanwata tamaka kake wulakantata dame wannan tafita
Riko hannunshi asma'u tayi tana kuka tace ABI please stop it
Katsaya muyi magana atsanake kar....
Bata karasa ba yasaki ahmad ya riko kafadunta da karfi cikin kakkawsar murya yace maganar me zamuyi dawa zanyi maganar da matar da kecin amanar aurenta ko abokin da kecin amanar amininsa
Kawai dan kinga ina ragamaki
To na kyaleki ne saboda ina tunanin zargin da muke maki ba gaskiya bane amma yanzu nagane kuskurena
Sakinta yayi yana fadin shikenan bari nahutar daku base kuntsaya labe labe zan sawwake maki kawai kowa yahuta
Sarah kuma ba ahmad kadai bane namiji bare tamutu ba aure
ai khadeeja najin haka tayo kukan kura tacafki kafan AK tana kuka tace Yaya dan Allah kar karabu da yayata wallahi ba ita ahmad kesoba ni yakeso kawai Baku fahimci abunda bane amma dani ahmad ke soayayya ba ammah ba dan Allah kar kasaketa takarashe maganar tana fashewa da kuka
Cak ya tsaya yana kallon ahmad da mamaki yanuna khadeeja yana fadin yanzu ahmad wannan yar karamar yarinyar kakeso mekagani ajikin wannan dayabirgeka
Matsowa ahmad yayi yadago khadeeja daga kafan AK fuska ahade yake kallon AK yace
Eh ita nakeso AK kuma ita zan aura shi so nagaskiya ba yabukatar girma ko shekaru kafin afara shi amma bazaka fahimci hakan ba se ranar da kafada irin halin da nake ciki
Kana bani mamaki yanda kacanza lokaci guda ada kana son duk abunda nakeso amma ayanzu kai kake kokarin hanani abunda nakeso
Nagaji da boye boye AK zan fito nagayama kowa wacce nakeso idan aka takura ni kuma wallahi se indauketa mugudu
haba katsaya karamar kanwarka tana juyaka kamar remote control abunda takeso shikake yi kayi kokarin koyamata yanda zata nemi Abu dakanta saboda ba kullun kuke tare ba
Yana kainan yaja hannun khadeeja yatafi yana fadin ga asma'u nan kayi abunda kaga dama da ita amma kasan ka tanadi amsar da zakaba iyayenta dakuma grany
Kuka khadeeja tafara tana kokarin kwace kanta tana kiran asma'u amma yaki sakinta seda suka shiga mota yatada aguje yabar wurin shikanshi titi kawai yakebi aguje kamar zai tashi sama amma baisan inda zashiba
Da kallo AK kebin motar har tabacemai sannan yashiga motarsa yabar wurin
Durkushewa asma'u tayi awurin tana wani irin kuka mai ban tausayi tasan shikenan yanzu kowa zaisan abunda yake faruwa AK zai rabu da ita ga ummanta nafama da ciwon zuciya tun rasuwar abbansu yanzu idan taji tasan tabbas bazata ita jurewa ba ga abba da inna wane hali zasu shiga
Seda tayi kukanta mai isarta sannan tawuce gida
AK na isa gida bangaren grany yanufa yasanar da ita zancan ahmad kanwar asma'u yakeso kuma yafasa auren sarah
Lallashinshi tayi tana kuantar mai dahankali
Yaso yagayamata komai amma ganin bata cikin koshin lafiya yasa ya barshi akan idan taji sauki zai gayamata komai sannan yabata hakuri akan zai sawwakema asma'u tunda ba son junansu suke ba
Tana isa gida tazauna apalo hade da dafe kai tana tunanin ina ahmad zai kai khadeeja dan ba hanyar gida taga yanufa ba
jin anfizgota dakarfi yasa tadago atsorace dan ganin waye
Sarah tagani atsaye tana huci ga idanunta dasuka kunbura sunyi ja
hannunta tafara ja tana fadin dan ubanki ko mayyace ke yau sekinbar gidan nan
Fizge hannunta tayi tana fadin ke baki isa kifitar dani ba sekibari Wanda yakawoni yafitar dani dakanshi
Dariya aysha tayi tana tafa hannu tace kaji wani karfin hali to albishirinki AK da kansa yabamu izinin fitar dake daga gidan nan kije kijira takardarki zata biyoki daga baya
Hannunta tazo kamawa tayi saurin kawcewa tana fadin base kunfitar dani ba nizan fita dakaina
Sannan takalli sarah tace ke kuma kinba mata kunya wallahi kina ba kanki wahala kina hauka akan namijin da baimasan kinayi ba yayanki yana kokarin hadaki da Wanda kike so amma ke kinzama silar rabashi da amininsa kindaga mai hankali kin hanashi sukuni shame on u
Tana kainan ta juya tafita daga gidan tana sharan kwalla
[18/07, 15:05] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣0⃣0⃣
Tafe take akan hanya tana kuka tunaninta daya ummanta mezata ce mata wane hali zata shiga idan taganta awannan daren wai ankorota daga gidan mijinta
Amma yata iya yazama dole ummanta taji amma tasan dubarun dazata mata yanda abun bazai daga mata hankali sosai ba
Gudu ahmad yake amotar kamar zai bar gari se kuka khadeeja ke masa amma bai saurareta ba sunyi nisa sosai
Mai yakare amotar gashi ba kowa akan hanyar
Bude motar yayi yafita yana rufo kofar dakarfi
Fitowa khadeeja tayi cike da masifa tashiga gabansa tana fadin meyasa katsaya ai na dauka garin zamu bari what is wrong with u Tarzan
ahasale yace karki kara cemun Tarzan Duk bake kika sakani ahalin da nake ciki ba miye laifina
dan nasoki ko kuma dan nakasa saka son sarah araina
Wallahi da ina da hali da nacire sonki na saka nata koba komai nasan tana sona
Kuma da itace bazata taba hakura dani dan wasu ba koda kwa AK ne dakanshi
juyawa tayi tana fadin to kaje ka aureta mana tunda kasan tana sonka meyasa zaka daukoni ka kawoni nan
Binta yayi da kallo yakasa cewa komai seda yaga tayi nisa sannan yabi bayanta yana kiranta
Banza tayi dashi tana tafiya seda taga tafara shiga daji tsoro yakamata ta tsaya
Karasowa yayi cikin sigar lallashi yace deeja wai meyasa kin cika rigima ne kinga nan wurin baida kyew kizo mukoma can ko zamu samu wani ya tsammana mai mukoma gida nasan yanzu anfara nemanki
Kamar tafashe da kuka tace bani wayarka inkira Umma
"Wayana tafadi dazu awurin da AK ya iskomu
Ina taki wayar
"Ba caji
Juyawa yayi yanufi mota yana fadin
OK muje in munsamu mai se kiyi caji amota
Bin bayansa tayi suka dawo
Bude motar yayi suka zauna shi agaba ita abaya amma kofofin motar abude
Kuka tafara tana fadin yanzu gashi kajamun nasan ana nemana agida ni damuwata ma bansan wane hali yayata take ciki ba
Handkerchief yamika mata yace dan allah kidaina wannan kukan kinga wurin nan ba kyew ne dashiba kar ki tona mana asiri
Cikin kukan tace matsoraci kawai...
Dariya yayi yace ahaka kika gani kina so ba
Kauda kai tayi tace ni allah bana sonka
Shiru yayi baice komai ba yana sauke ajiyar zuciya
Grany ce tace AK ya kira mata asma'u zasuyi magana
Bayan ya fito ya dudduba ko ina baiganta ba yazo wurin su sarah dake zaune Palo yana tambayar asma'u bata dawo bane
Da mamaki aysha tace lafiya kake nemanta
zama yayi yana fadin Kawai dai grany ke nemanta
Kauda kai Sarah tayi tace mun koreta
What ???
Yafada yana kallon bangaran grany
Aysha tace bakaso mukayi hakan bane ko kafara damuwa da ita ne
harara ya watsamata yana fadin
come on shut up dallah !!
meyasa zaku koreta awannan lokacin ba kwa tunanin grany ne kunsan bata jin dadi dawanne kuke so taji
To kumasani ba ita ahmad kesoba kanwarta khadeeja itace budurwansa
Azabure sarah tamike tana fadin Yaya kasan me kake fada kuwa khadeeja fa kace
"Kwarai khadeeja da ita suke soyayya ahmad dakansa yafadamun kuma nagansu tare da khadeeja akan idona yadauketa suka tafi kawai kin gansu tare ne ke kuma kikayi tunanin itace yakeso nan yakwashe yanda sukayi yagayamusu
Yakare maganar dafadin
Yanzu gashi kun koreta me kukeso nagayama grany
riko hannunsa aysha tayi tana fadin AK kayi hakuri amma aikin gama ya gama kawai kasan yanda zakayi da grany
Kuace hannunsa yayi yanufi bangarensa
Damamaki sarah ke kallon aysha ahasale tace amma dazu wace takarda kika bama AK ina kika sameta
Yama naga zancan bai baki mamaki ba hakan yana nufin kinsan da maganar kome
Sosa kai aysha tayi tana kame kame tace yi hakuri sarah nima se dazu nasani naji tsoron idan AK yasan gaskiya bazai rabu da asma'u bane shiyasa naboyemaku zancan amma kiyi hakuri
Tsaki sarah tayi tace karki kara mun irin haka banaso da kingayamun tun alokacin da nasan matakin da nadauka
AK yana tura kofar palonsa yafara tuna asma'u kujeran da take bacci yakalla yatuna lokacinda yake tashinta da sassafe ya hanata bacci
Kauda kai yayi yawuce daki yana shiga ya hango blanket dinta aninke akan gado murmushi yayi da yatuna draman su tajiya
Zama yayi bakin gado yacire hularsa yana tuna lokacinda takemai dariyar bai iya sa hula ba
Saurin tashi yayi yanufi bathroom yana fadin mema yasa nake tunaninta
Umma nazaune apalo itada inna kasancewar sundawo nan gidan dazama
Cike da damuwa Umma tace inna wai kin aiki khadeeja ne
Inna ta tabe baki tace inafa zan aiketa da wannan daren yarinyar dako darana na aiketa setaga dama takezuwa
Shuru tayi nadan lokaci sannan tasauke ajiyar zuciya tace ni wallahi yau naji gabana na faduwa asma'u nayawan fadomun arai gashi bansan inda khadeeja tajeba rabona da ita tana wurin su Ummi kuma fa'iz yace tun dazu tabar can
Inna tace kikira asma'u mana kiji ko suna tare tunda dai khadeeja ba inda take zuwa da daddare
Daukan waya Umma tayi takira numban asma'u
Su sarah na zaune apalo sukaji waya na ringing
Dauko wayan aysha tayi tana fadin kinga mutuniyar ki tabar wayanta
Kauda kai sarah tayi tana jan tsaki
Aysha tayi dariya tace ba dai ummanta ce lagonta ba to bari mudan buga game
Daukan kiran tayi tana yamutsa fuska
Umma naji andaga kiran tace asma'u ya kike
Tundazu khadeeja tafita bata dawo ba kuna tare ne
Murmushin mugunta aysha tayi sannan tace ba asma'u bace
Da mamaki Umma tace to waye ina asma'u
"Kina magana da aysha
Karkidamu asma'u tana nan zuwa wurinki saboda mijinta ya korota daga gidansa
Kedai inaga bakiyi dacen haihuwa ba yarki khadeeja ma tagudu da saurayi yanzu haka suna tare da ahmad tasa yafasa auren sarah
ga babbar miji ya korota cikin dare
Ta kare maganar tana kwashewa da dariya ....
Nan take jiri yafara dibar Umma zama tayi akan kujera ta dafe kai tana salati
Dafata inna tayi tace lafiya meyafaru
Cikin rawar murya Umma tace inna kinji wannan yarinyar aysha tana mun maganar banza wai Abid yasaki asma'u kuma wai khadeeja sun gudu da ahmad
Salati inna tayi tana fadin anya kwa wannan yarinyar da gaske take nifa banyarda ba
Tashi Umma tayi tana yafa gyale tace inna ana karya da maganar saki ne kuma idan bahaka ba ina khadeeja take nakira wayar ta yafi akirga amma akashe ni gaskiya zanje naga asma'u
Hanyar fita tanufa tana fadin baiwar allah nasanta da zurfin ciki yanzu haka tana tunanin halin dazanshiga shiyasa taki zuwa
Binta inna tayi tana fadin ina zakije cikin wannan daran ki...
Bata karasa ba kawai taga Umma tayi baya tafadi kasa asume
Da gudu takarasa wurinta tana salati tashiga kwala ma Abba kira
aguje suka fito su duka aka nufi asibiti da ita
Fa'iz da baisan meyake faruwa ba ya kira wayar asma'u jin ba adauka ba yakira ta grany ya gayamata Umma ba lafiya tagayama asma'u
Sannan yafara Neman numban khadeeja amma akashe
Asma'u na is a gida tahadu da nusaiba abakin get nan tagayamata labarin da daga mata hankali
Ko gidan bata Shiga ba aguje tanufi asibitin akafa tana rera kuka 😭
ahmad yanata surutunsa khadeeja tayi banza dashi
Kuantar dakansa yayi jikin kujera yana magana shikadai
yace baby yaushe zamuyi aurene
never.....
Khadeeja tafada tana kauda kai
Juyowa yayi yana kallonta yace malama ba dake nakeba tunda kince ba kyasona nima baruwana dake dawata daban nake magana so stay out of it
Daure fuska tayi tace kasan tadi zaka zo wurin aljanar ka meyasa baka ijiyeni agidan mu ba kataho dani
Murmushi yayi yace saboda ina so kisan inada wacce tafiki dan haka kidaina jamun aji
Lumshe ido yayi yana hango khadeeja ranar dayafara ganinta
Murmushi yayi yana shafa kai ahankali ya furta
she was so beautiful like a flower in the garden
Ita dabance acikin mata komai tayi kyew yake mata
Takun tafiyarta daidai yake dakowane bugu naziyata
Idan nakalli idanuwanta yaruwata gaba daya nake hangowa acikinsu
Idan tana magana nakan shagala wajan kallon kyewawan lips dinta har bana iya fahimtar
Metake fada
Idan tayi murmushi jinake kamar nunfashina zai dawke
Idan tana dariya kuma ban kiba nazauna nayita kallonta har tsawon rayuwata
Bantaba sanin ina tsananin sonta ba se lokacinda nafuskanci kalubalen rabuwa da ita
Sunkuy dakai khadeeja tayi tana murmushi dan ko baifada ba tasan da ita yake
Murmushi yayi shima yacigaba dafadin zamuyi aure ta haifamun yan biyu talle da mudi
Saurin dago kai tayi tana fadin allah ya kyewta talle da mudi fa
Juyowa yayi ya kalleta yana dariya yace ke kuma asuwa zaki sakamana baki a firarmu
Kauda kai tayi tana daure fuska dan Sam bata masan lokacinda maganar tafito bakinta ba
Shuru sukayi basu kara cewa komai ba har bacci yadauki khadeeja amma ahmad yakasa bacci yana gadinta
A asibiti kuwa bayan doctor ya duba Umma yace masu zuciyarta ce tabuga zasu mata aiki amma senior doctor din bayanan dole ajira se yazo
Haka suka zauna jigum har asma'u ta iskosu suka gayamata abunda doctor din yace kuka tafara inna na lallashinta gashi annemi khadeeja anrasa
Suna zaune suna jira asma'u se zarya take office din doctor din yana gayamata baizoba sukara jira har safiya tayi shiru
Dasafe grany taja AK sukaje asibitin amma harsuka isa ba ayima Umma aiki ba
Inda tahango su inna azaune tanufa AK nabinta abaya bayan sungaisa Yaje kusan Abba yazauna ita kuma grany tana wurinsu inna
Da mamaki takalli asma'u tace yo kekuma asma'u sekitaho baki gayamun ba haka ake
Shuru asma'u tana sadda kai batace komai ba
Saurin mikewa tayi tanufi doctor din dataga yafito daga office tana fadin doctor har yanzu baizoba
Daure fuska yayi yanufi wani wurin yana fadin malama kinfa dameni sonawa zan gayamaki bai zoba da yazo aida kinganshi ko
Shan gabanshi tayi cikin kakkausar murya tace wai ba kwada tawsayine ??
Tunjiya baiwar allah take wahala amma ko ajikinku ko dabbace yakamata Ku tausayamata bare mace
ko zakaso ganin mahaifiyarka awannan halin
Wucewa yayi abunsa batare dayace kala ba
Durkushewa tayi awurin tana fashewa da kuka mai ban tawsayi tasowa inna tayi takamata tana lallashi
duk abunda suke AK na kallonsu sedai baiji dadin abunda doctor din yayi ba
tashi yayi ahasale yabi bayan doctor din ya cakumo rigarsa cikin daga murya yace mekuke jira ne dabazaku mata aiki ba
Atsorace doctor din yace sorry sir doctor din dazai mata aikine baizoba nakirashi kuma yace karna damesa daga karshema yace in nakara kiransa se yasabamun
Hannu yamika mashi yace bani wayanka
Jiki narawa ya Ciro wayar yayi dialing number yabashi
Seda takusa katsewa yadaga ahasale yace kai wai banace kar ka kara kirana ba wacece ita dazakadameni akanta bazasu iya jira bane ko zan iya hanata mutuwa ne in lokacinta yayi
Runtse ido AK yayi yana shafa kai cike da Bacin rai yace
Kana magana da AK hausawee kuma marar lafiyar mahaifiyata ce wallahi kaji na rantse nabaka nan da minti 30 idan ba'afara mata aiki ba senasa ankulle asibitin nan tunda banga anfaninshiba
Kasan bazaka kula da marasa lafiya ba uban wa yace kabude
atsorace yafara ba AK hakuri
Bai saurareshi ba yakatse kiran yamikamata doctor din yana fadin Ku kaita dakin operation yanzu zaizo
Juyowan dazaiyi yaga asma'u agabansa tana murmushi tana sharan kwalla
Tace
ABI nagode allah yasaka da alkhairi...
Kauda kai yayi yana daure fuska yace badan ke nayi ba
nadauki Umma matsayin uwata ne
kuma naga inna tana kuka ni kuma banaso
To karma kiyi tunanin saboda kene
Murmushi tayi tace duk dahaka ma nagode
Juyawa yayi yatafi baice komai ba
Kusan inna tadawo tazauna tana fadin wai inna ya akayi haka tafaru
Nan inna tabata labarin wayar da Umma tayi da aysha ce sila
ahasale tamike tanufi gidan AK
Da kyar ahmad yasamu mai yasa amotar kana suka baro wurin khadeeja nasa caji kiran fa'iz ya shigo wayar
tana dauka yagayamata halin da Umma take ciki
Asma'u na isa gidan tahadu da sarah da aysha sunfito zasu fita wurinsu tanufa fuska ahade
aysha naganinta tafara dariya tace mekuma yadawo dake ko wayarki kika.....
Bata karasaba taji saukan lafiyayyen marin da yakusa sa tasaki fitsari
Nuna ta tayi da yatsa cikin kakkausar murya tace
wannan kashedi ne idan kika kara irin wannan ni kaina bansan mezan maki ba
Idan ke bakisan darajar uwarki ba to ni nasani kuma wallahi idan wani Abu yasami ummata se nabaki mamaki
Tana kainan tajuya tana fadin banza mara kamun kai
Da kallo aysha tabita tana dafe da kunce har tafita sannan takalli sarah tace wai ni wannan yarinyar zata mara
Motar tashiga tana fadin wallahi sena nuna mata ruwa ba sa'an kuando bane
dayan gefen sarah tazauna tana murmushi tace mezaki mata bayan ta taxi
Tada motar tayi suka fita tana huci tace
badai saboda ummanta tamareni ba to agaban umman nata zan rama marina inyaso tamutu
[18/07, 15:05] Hubbey Frd Ameena Kn: asibiti ahmad yanufa direct khadeeja na gefe se kuka take duk ya gama rudewa ko parking bai gama ba tafita aguje tanufi cikin asibitin
Koda taje har anfito da Umma daga dakin operation tana dayan dakin amma bata farfado ba
Aguje tanufi dakin inna tayi surin riko hannunta ahasale tace
Daga ina kike mara kunyar yarinya ke yanzu bakiji kunyar zuwa nan ba
Rungume inna tayi tana kuka tace inna dan allah kuyi hakuri wallahi bazan kara ba dan allah kibarni inga Umma
Rikota Abba yayi yana fadin zo nan khadeeja daga ina kike meyafaru muna ta nemanki wayanki akashe
Shuru tayi taci gaba da kukanta takasa cewa komai
Shafa kanta yayi yace shikenan yanzu kije gida kuyi abinci keda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 35