You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ne ya janyo hakan saboda haka tayanke shawarar janye jikinta daga garesa amma taga hakan ba wani saukin dayakawo
yanzu aysha hankalinta ya kwanta saboda AK yana kulata ko baya gida yana kiranta awaya yaji ya take
Asma'u tadamu matuka da halin da AK ke ciki zaune take tana kuka kawai tayanke shawarar zataje office tasamesa suyi magana
Yamanta da duk abunda tafada dawasa take ba dagaske bane dan haka sudawo yanda suke da matsayin abokai
Sedai wannan ranar takasance bakar rana awurinta seda tayi nadamar zuwa company
Saboda anan taji aysha da uncle jamilu na maganar plan din dasuka shirya dan mallake dukiyar AK daga karshe intakama ma su kasheshi kuma su kori kowa nagidan har taji aysha nafadin
Dady itama sarah daka gani dukiyar nan takeso saboda naji da kunnena tace daga ranar da tashiga hannunta gabadaya zata kori kowa daga gidan haka ma inna ladidi itama dukiyar takeso shiyasa ta aiko bashir yana aiki anan .....
Bata tsaya tagama jin karshen maganar ba ta baro company din ko AK din ma bata ganiba
[19/07, 17:05] Hubbey Frd Ameena Kn: baki da hanci suka saki suna kallonta wasu kuma gulma nacinsu se fadin suke wannan kamar madam Asma'u
badan wannan shigar tata ba daba abunda zai hana muce itace dan gaskiya kamar tabace
Bakin takalmi ne akafanta (cover shoe👢) tana sanye da wando tight light blue se T-shirt dinta fara tadoro dark blue din jacket maidan tsayi daidai guywa tayi rolling dabakin gyale fuskanta yasha make up tana sanye da bakin glasses afuskanta wanda shi yakara fito da ainahin kyawun fuskarta
lafiyayyen agogon fata ne daure ahanunta se wani dan karamin zoben azurfa makale ayatsanta
tsayawa fadar haduwar wannan yarinyar bata lokaci ne kana ganinta zaka rantse ba yar Nigeria bace ko daga yanayin shigarta kawai ka kalla kasan kudi sun zauna
Glasses dinta ta cire ta sakala shi awuyan rigarta ko kadan ba alamun far'a afuskarta
Kallon ma'aikatan gidan tayi daya bayan daya sannan ta nuna wani dayatsa cikin siriruwar murya tace
Kai zo nan
Jiki narawa ya nufi wajanta yana washe baki ya durkusa har kasa yana gaidata
batare da ta amsa gaisuwarsa ba ta Tamika mai makullin motar tana fadin kashigo mun dakayana ciki
cike da kasaita take takunta kamar bata son taka kasa har ta isa dab da kofar palon sannan taja birki ta tsaya
Hawayen fuskarta ta goge sannan tamaida glasses dinta seda taja dogon nunfashi ta furzar sannan tasa kai cikin gidan
zaune suke gaba daya apalon gidan suna fira aunty sadiya da fitowarta kenan daga kitchen rike da plate din dambun nama bata San lokacinda ya subuce mata ba yafadi kasa ba
gaba daya suka juyo dan ganin meke faruwa sedai lokaci guda sukayin saurin mikewa tsaye suna kallon abin al'ajabi
Nunata sadiya tayi da yatsa baki na rawa tace wa...... Wa nake gani haka kamar asma'u
Kallon kallon akafara tsakaninsu sannan suka jiyo suna kallonta anrasa Wanda zaice wani Abu
ahankali take takunta kanta asama tana bin palon da kallo har ta iso wurinsu sannan ta tsaya tana binsu da kallo daya bayan daya fuskarta ahade ba alamar annuri
karasowa wurinta grany tayi tana kallonta sama da kasa cikin rawar murya tace a....asma'u kece?.... ina kika shiga har tsawon wata guda muna nemanki ?
Jin shiru yasa takara matsowa tana kureta da ido tace wai kodai ba asma'u bace
Ganin batada niyyar bata amsa yasa tajuya tana kallon bashir tace kai je kakira mana Abidi yazo yatayamu ganin ikon allah ....
bata gama karasa maganarta ba AK yashigo palon aguje dan tuni ma'aikatan gidan suka sanardashi zuwanta
Nufo inda take yayi da sauri sauri har yana tuntube yana dariya mai yar sauti yace chitti kece kika dawo haka wow gaskiya kinyi kyew amma wannan shigar ai se ta tsorata mu
yana isowa dap da ita ya tsaya cak yana kallonta tundaga kasa har sama cike da mamki azuciyarsa yana fadin kodai ba chitti bace wannan
Amma jikinsa yana bashi tabbas itace saurin rungumeta yayi dakarfi kamar zai maidata ciki cike da farin ciki yake fadin
Chitti dama kina raye Ashe zan kara ganinki me yasa kika barni alokacinda nafi bukatarki
Koma ina kikaje meyasa baki gayamun muntafi tare ba
Muryansa ne takarye yana kara matseta ajikinsa kamar zai yi kuka
yace chitti u have no idea how difficult it was for me to live without u
nasan namiki laifi but I am sorry bazan karaba zan dawo yanda muke da I promise kuma dama ina so ingayamaki chitti l lo.........
baikarasa ba ta tattaro illahirin karfinta gaba daya tasa hannayenta biyu ta turasa baya dakarfi har saida yakusa faduwa bashir yayi saurin tarosa tabaya
😱Shocking!!!
Zaro ido sukayi gaba daya suna kallon Abu kamar film dan haryanzu basu yarda ba wai dagaske asma'u ce tadawo ba
kara nufota yayi yana fadin chitti yau ni kike turewa haka nasan fushi kike dani har yanzu amma nace kiyi hakuri idan bazaki hakura ba u can punish me bu please don't ever leave me again
Glasses dinta tacire tana nunasa dayatsa cikin kakkausar murya tace kar kasake katabani *AK* ko kamanta cewa banada wani matsayi awurinka ne I am jus a stranger to u saboda haka u have no right to touch me
baki ya saki yana kallonta cike da mamaki yama kasa magana
Wannan wane kalan iskanci ne haka kananin mutane zaki daukemu idan kinmanta mutuncinki ai bazaki manta cewa shi mijinki neba ....uncle jamilu yafada cike da bakin cikin sake ganinta arayuwarsa
Juyowa tayi tana kallonsa fuska adaure sanann ahankali takarasa inda yake tsaye tana nuna AK da yatsa cikin murya mai kaman rada tace
Wannan tsakanina dashi ne ba girmanka bane shiga abunda bai shafeka ba so stay out of it idan zaka iya kallo kayi idan bazaka iyaba kuma se kabar nan
Fizgota aysha tayi ahasale tace malama ki iya bakinki duk fitsarar dakika koyo ta tsaya kansu amma kar kisaka babana aciki
Kuace hannunta tayi tana murmushi tace baban naki yakamata ki gayama ya iya bakinsa baniba
baki suka saki gaba daya suna kallonta cike da al'ajabi
cike da takaici inna ameena tace ke wai ma tukkuna wacece ke dan ni har yanzu banyarda asma'u bace dan ba abunda kuka hada banda kama
Saurin juyowa asma'u tayi tana tafa hannu tace good question inna kab cikinsu bawanda yamun wannan tambayar seke ?
yanzu kuwa zakuji koni wacece
Asma'u Mahammad Magaji ko kuce Asmy Magaji
sannan ina farin cikin sanar daku cewa I am the new owner of the hausawee properties ma'ana namallake duk wata kadara da ajiyayun kudi na AK hausawee
Wani irin wawan jiri ne yadibe jamilu se akan kujera tim nan take zufa ta hau karyomai kamar yashiga kasan shower
saurin dafashi aysha tayi tana mai alamar ya natsu sannan ta tsiyayi jus a copi ta mika mashi
What nonsense... AK yafada yana daka mata tsawa
toshe kunnenta tayi tana runtse ido nadan lokaci sannan tabude idanuwanta tana nufo wurinsa cikin sassanyar murya tace
Easy man ai abun bai kai haka ba idan kabini ahankali zaka fahimci komai
juyo da ita grany tayi afusace ta wanketa da lafiyayyen mari saurin dafe kuncinta tayi tana kalkon grany da mamaki tace grany ni kika mara
"An mareki idan akwai abunda yafi mari ma ya cancanci amaki ke bakiji kunyar furta wannan kazamin furucin agabanmu ba to idan ma wasa kike kidaina dan mu ba abokanan wasanki bane mara kunyar banza kawai
karasowa AK yayi yadafa kafadarta yana fadin yi hakuri grany mudan bita asannu kamar yadda tace inaga daga karshe zamu gane tasamu matsalar kwakwalwa ne shiyasa take wannan abun
Dariya bashir yayi yana fadin kai amma wannan haukar da dadin kallo take Yaya
akwatinta tanufa taciro wasu kardu tana murmushi Tamika ma AK tana fadin ga wannan shizai tabbatar maka da abunda nafada ba hauka bane
Karban takardun yayi yafara dubawa nan take jiri yafara dibansa seda yazauna kan kujera dagowa yayi yana kallonta da jajayen idanunwansa bakinsa narawa amma yakasa furta koda kalma daya
Saurin kauda kanta tayi ta koma gefe ta zauna kafa daya kan daya yafara magana kamar haka
nasan zakayi mamakin ganin abunda nafada gaskiya ne kuma kana so kasan ya akayi sa hannunka yazo kan takardun batare da saninka ba
AK kayi wawta matuka da kayarda cewa haka kawai nake zaune dakai bayan nasan cewa baka sona bana sonka
gaskiya ada nayi niyyar rabuwa dakai amma daga baya nayi wani tunani meyasa zan tafi nabar wannan tarin dukiyar batare Dana dibi kasona ba shiyasa nahakura naci gaba dazama dakai ahaka har zuwa lokacinda nacimma burina
Daga lokacinda nagane illahirin takardun kadarorinka suna wurin grany daga lokacin
nayi iya kokarina wajan cusa yardata azuciyarta har takai ta amincemun nashiga ko ina abangarenta ta wannan hanyar nayi nasarar sace takardun kai kuma nayi anfani da wata hanyar nasa kayi signing dinsu batare dasaninka ba
sanin cewa idan har zan rike dukiya irin wannan ina bukatar experience hakan yasa nashirya tafiya coast zuwa America batare dakowa yasaniba har natsawon wata daya gashi yanzu nagama cikin Sa'a nadawo zan kula da dukiyata yanda yakamata .....takarashe maganar tana kwantar dakanta kan kujera hade da lumshe ido
Tsit palon yayi tamkar anyi ruwa andauke bakajin komai sai saukar ajiyar zuciyoyi daga kowane gefe
AK kam tamkar gunki haka yadawo dan ko yatsarsa yakasa motsawa har yanzu yakasa yarda da abunda kefaruwa yakosa yafarka daga wannan rikitaccen mafarkin mai ban takaici wai chitti ta yaudaresa
Dafasan da bashir yayi ne yadawo dashi hayyacinsa dagowa yayi yana kallonsu daya bayan daya kamar baitaba ganinsu ba har yazo kan asma'u sannan da kyar ya bude bakinsa cikin wata iriyar murya yace but u said u love me
Dagowa tayi tana kallonsa sannan ta kwashe da dariya tace it's all part of my plan so karma kasa abun aranka
Shiru yayi baice komai ba yana kallon takardun hannunsa
Zunbur uncle jamilu ya mike cike da masifa yace kai ina walkahi bazai yiwu ba haba Abu sekace wasan yara tayama za'ayi ace wai keda kikazo jiya jiya har kin mallake gaba daya dukiyar ai baki isa ba wallahi
toshe baki aysha tayi jin katobarar da ya abka
Kallonsa asma'u tayi da gefen ido tana wani malalacin murmushi tace ohh kenan dama akwai masu neman dukiyar bani kadai bace
Zaunawa yayi yana share zufa dan se alokacin yagane subutar baki yayi
Tashi tayi tsaye tana kallon AK tace AK I know it hurts amma ya zakayi se hakuri karike wa innan takardun awajanka original din yana wajena idan kuma bakayarda ba zaka iya kai abun kotu I am ready for it
tana kainan taja akwatinta tayi bangarensu tana fadin I need to have some rest dan allah duk mai magana yajira zuwa gobe dasafe
Baki bude suka bita da kallo har tahaye sama sannan suka jiyo suna kallon juna tafa hannu inna ameena tafarayi tana salati tace oh ni ya'su jama'a kutayani ganin wannan abin al'ajabi
Zaunawa grany tayi rike da wayarta tana Neman numban Umma tace nidai gaskiya wannan Abu ya dauremun kai bari mu kira ummarta inmu tamana wasa da hankali ta rainamu ai bazata ma uwarta ba ko?
Umma nadauka tasanar da ita asma'u tadawo cike da mamaki tace grany asma'u fa kika ce
Tabe baki grany tayi tace aha'ab ai se kuzo kuga ikon allah
Shidai AK tunda ya zauna bai tashi ba ganin abun yake kamar almara wai chitti ta malakke dukiyarsa kuma wai karya take bata sonsa dafe Kansa yayi aransa yana fadin inna lillahi wa inna ilaihiraji'un
ba'afi minti talatin su Umma da khadeeja suka shigo gidan cike da farin ciki tanufo grany tana fadin grany ina asma'un take dagaske asma'u tadawo ina aka ganta
Shan gabanta aysha tayi tana fadin Umma yarki ba bata tayi ba kuma ba wani Abu yasameta ba tafiya tayi har na tsawon wata daya batare da sanninku ba
Cike da mamaki Umma take kallon mutanan palon dasukayi cirko cirko suna kallonta
Juyowa tayi tana kallon aysha tace tafiya kuma kamar ya ina taje
dariya aysha tayi tana tafa hannu tace ke uwarta baki sani ba taya za'ayi ni insani
Juyo da ita khadeeja tayi ahasale tace ke kisan abunda zai rika fitowa da bakinki kar kimanta da mahaifiyata kike magana
kwace hannunta tayi tana fadin ohhh Ashe dai ba dadi to awurin yayarki nakoya
Dawo da kallonta tayi kan Umma tana girgiza kai tace Umma dama tarbiyar da kike ikrarin kin bama yarki kenan kullun kina yabonta she is nice she have a good heart yarki diamond yarki gold to yau munga asalin wacece ita
katseta Umma tayi dafadin ke karki mun rashin kunya kinji ko
karasawa tayi wurin grany tazauna tana fadin grany wai meke faruwa ne ya naganku haka
ajiyar zuciya grany tasauke tashiga bata labarin abunda yafaru
Juyowa tayi tana kallon AK cike da mamaki tace kun tabbata asma'u ce kuwa dukiya fa kukace asma'u dako kudinta ma bai dameta ba bare har takai ga malakke wannan dumbin dukiya kuma wai ta mijinta kai gaskiya.....
Katseta uncle jamilu yayi yana share zufa yace to karya zamu maki kenan badai kinyi karatu ba to ga takardunan ahannun AK duba ki gani kuma wallahi bazata sabu idan shi ya kyaleta to ni bazan barta ba haka kawai shekara nawa ina ......
saurin taboshi sadiya tayi tana mai alama ya iya bakinsa
gyaran murya yayi yace ummm shekara nawa yayi yana wahala har yatara wannan dukiyar shine lokaci guda zata rabashi da ita kuma mubarta haka kawai
Umma dai har yanzu bata gamsu da bayaninsu ba nan take ta aika dai cikin ma'aikatan yakira mata asma'u
Seda tadauki tsawon lokaci sannan ta fito wannan karan idonta yayi jajir daganinta kasan taci kuka
Tunda daga nesa Umma da khadeeja suka saki baki da hanci suna kallonta har ta iso palon ta tsaya cak tana kallonsu
Saurin karasowa khadeeja tayi ta rungumeta tana kuka tace ammah ina kika shiga mukayita nemanki bamu ganki ba meyasa zaki tafi kibarmu kin kwsan halin da muka shiga na rashinki duba kiga yanda Umma tadawo kullun batada lafiya saboda tunaninki
Shiru tayi batace komai ba tana kallon Umma sama da kasa
ahankali Umma takaraso wurinta tana kallon shigarta da mamaki tace asma'u meyasameki haka ya kuma naganki da wannan shigar ina kika tafi batare da kinsanar damu ba
Kauda kai tayi batare datace komai ba
riko kafadunta Umma tayi tana kureta da ido tace asma'u meke damunki ne anya kuwa lafiyarki kalau ko dai abunda grany tafadamun dagaskene wai kin.....
Katseta tayi dafadin Umma kinsan dai grany bazata maki karya bako to dagaskene
Shocking.....😱
Kallon kallon aka fara tsakanin mutanen palon banda AK da ko dagowa baiyiba bare ya kallesu
Kallon khadeeja Umma tayi sannan takalli asma'u tana so tayi magana amma takasa
Riko hannunta khadeeja tayi cikin rawar murya tace ammah meyake damunki ne ....Umma ...kike ..yima magana haka kai tsaye
juyowa asma'u saitin Umma amma kanta akasa dan takasa hada ido da ita cikin dakewa tace Umma wannan fa ba wani Abu bane kawai dukiyar na mallaka amma kuma ni bance zan koresu daga gidan ba kawai dai.....
Hannu Umma tadaga zata mareta khadeeja ta rikota tana fadin a'a Umma kibarta kawai ni na tabbata akwai abunda yake damunta amma ko za'a akasheni bazan yarda cikin hayyacinta take ba something is wrong with her
Nuna ta Umma tayi da yatsa cikin kakkausar murya tace to wallahi bari kiji idan ma hauka kike ko kwaya kika sha to kisani ni nafi karfin ki tozartani nabaki nan da gobe ki mayar masa da dukiyarsa inba haka ba kuwa sedai kinemi wata uwar ba niba .....
tana kainan ta juya afusace tafita daga gidan khadeeja nabiye da ita
juyawa asma'u tayi aguje ta koma bangarensu tana shiga ta turo kofar hade da sulalewa awurin tafashe da wani irin kuka mai ban tausayi kuka take sosai har nunfashinta nadaukewa seda tayi mai isarta sannan ta tashi tana dafe kai ta wuce daki jacket dinta ta cire tarike ahannu ta tsaya gaban dressing mirror tana karema kanta kallo wasu sababbin hawaye nazubowa daga idonta tajima atsaye kafin ta wuce bathroom tayo alwala tazo ta zunbula hijabinta tayi sallah tajima azaune tana adduo'inta kafin ta tashi takoma kan gado tazauna tafara aiki a laptop dinta
bayan fitar Umma uncle jamilu ya mike afusace yanufi bangarensa sadiya da aysha sukabi bayansa
Daga nan kowa ya watse jiki asanyaye wasu kuma naji kamar su mutu dan bakin ciki
AK natashi wurin ahmad yanufa ya zayyane masa duk abunda yafaru
Dafari bai yardaba seda AK yanuna masa takardun sannan ya tabbatar cewa dagaskene cike da mamaki yace ammah har yanzu abun yana dauremun kai I mean...... why will she do that ?
ajiyar zuciya AK yasauke yana kuantar da Kansa kan kujere yace bansan meyasa tayi hakan ba amma I am sure she is hiding something tabbas ba banza ba chitti bazata taba yaudarar wani bama bare ni kawai dai dalilinta nayin hakan ne bansaniba
"To yanzu miye abun yi
"Ba wani abunyi ahmad ko ina akaje tafimu gaskiya saboda akwai sa hannuna akan takardun so banida ikon dazan kwato dukiyata amma abunda yafi bani haushi shine gaba daya komai yakoma kan sunanta hatta kudina na bank da da komai nawa ya daina aiki lokaci guda tamaidani fakiri wallahi yanzu dubu dari kawai nake magani itama a ranar da ta tafi nacirota zan yi wani Abu da ita namanta
Tagumi ahmad yayi cike da al'ajabi yana nazarin wannan al'amari amma shi kanshi bai yarda cewa asma'u zatayi haka ba yana zargin akwai abunda take boyewa ba banza ba
Tashi AK yayi yanufi hanyar fita yana fadin muje muyi sallah daga can muje wurin su Umma mudubata I know she must be worried
awurin Umma suka wuni ranan suna kuantar mata da hankali sannan suka tabbatar mata da cewa akwai dalilin dayasa asma'u ta kwace dukiyar AK ba banza ba kawai dai subita ayanda tazo asannu zasu gane dalilinta nayin hakan
[19/07, 17:05] Hubbey Frd Ameena Kn: AK yana zaune office din ahmad kamar kullum wayarsa ce ahannunsa yana dannawa
tsaki ahmad yayi cike da takaici yace
Friend wai meke damunka ne kwana biyu gaba daya kacanza kafita hayyacinka bakada aiki sedanna waya sekace wani bakauye
Baidago ya kallesa ba bare yasa ran zai tankasa
Karasowa yayi wurinsa yazauna cikin sassanyar murya yace
Base kafada ni nasan akwai abunda yake damunka idan kana ganin bai zama dole nasani ba fine u can keep it to ur self amma dan allah karage wannan damuwar tana damuna
murmushi yayi yana ci gaba da kallon wayarsa bai ce komai
Dafe kai ahmad yayi yana salati sannan yadago yana fadin wai dan asma'u tace tana sonka ne kake wannan abun
Girgiza kai yayi har yanzu dai yana kallon wayarsa se murmushinsa da yakaru har ana ganin fararan hakoransa
Cike da takaici ahmad ya kwace wayar yana fadin wai uban me kake kallo awayar nan ne dayake......
Cak ya tsayada maganarsa yana kallon photon asma'u dake kan screen din wayar da alama bacci ma take yadauketa photon yayi kyew sosai ga Zara zarn eyelashes dinta dasuka kwanta da dan karamin lips dinta da yayi kamar tasa pink lipstick kanta ba dan kwali gashinta duk ya bazu akan pilo sauran kuma akan fuskarta
Juyowa ahmad yayi da mamaki yana kallonsa baki bude yama kasa magana
Se can yayi yar dariya mai sauti cike dafarin ciki yace ohh my god friend are u in love ?
Hannunsa yasa yadan daki goshinsa kadan yana fadin I was so stupid ya akayi nakasa gane halin da kake ciki tun tuni
hannu AK yamika mai batare dayace komai ba ahmad yabasa wayarsa yana fadin friend kace wani Abu mana ur silent is killing me
tashi yayi yafita daga office din yana rike dawayarsa gam ahannunsa baiko kalli ahmad ba bare yayi magana
Da kallo ahmad yabisa rike da baki yace ohhh ikon allah kaikuma haka soyayyar tazo maka ni har ma kabani tausayi
komawa yayi yazauna kan kujerarsa yana Neman numban khadeeja dan yamata albishir
tafiya asma'u keyi akan hanya tana rangaji da kyar take daga kafarta hawayenta kuma har basa bare tana ganin hanya da kyew bata damu da sharesu ba dan gaba daya jikinta ya mutu lokaci guda maganganun da taji suna dawomata
ahankali ta furta meyasa ....meyasa
Sukeso suga bayansa bayan bayada wani buri da yawuce ya kyewtata musu duk wahalar dayake saboda su yakeyi baya samun isashshen bacci baya samun hutu baidamu da duk wani jin dadi irin namasu kudi ba kawai saboda baya iya yin komai se tare dasu amma burinsu shine sumallake abunda yasha wahala da guminsa yatara why....why...takarashe maganar tana durkushewa awurin hade dasakin wani kuka mai cin rai bata damu da mutanen dake kallonta ba dan ita kadai tasan halin da take ciki
Cikin kukan take fadin ina bazai yiwu ba bazan taba bari su cutar dakai ba se inda karfina ya kare I will fight for u ABI that's my promise
amma taya tana ina zan fara ko zan mutu ina rantsuwa ABI bazaka yarda da abunda zan fada ba ....
kanta takai kasa tana kankame jikinta cikin kuka tace ya allah kataimakeni I am helpless😭
bayan AK yadawo gida da yamma bangaren grany yawuce yagaidata se dube dube yake ta inda zai hango asma'u amma bai ganta ba hakanan yatashi yanufi bangarensu dan yasan tana can
Seda yafara leka dakin aysha ya iskota zaune da sarah suna fira daga bakin kofar suka gaisa ya wuce bangarensa
Murmushi sarah tayi tana kallon aysha tace sister wai miye sirrine naga kuana iyu Yaya yadamu dake ba kamar da ba
Dariya tayi suna tafa hannu tace ba wani sirri kinsan ance true love never end
Yana isa bangarensu yatura kofar yashiga da sallama sedai wayam ba kowa daki yawuce nan ma bakowa ahankali ya tura kofar dressing room har bathroom nan ma bakowa
Jiki asanyaye yadawo yazauna yana cire agogonsa duk se yaji baiji dadin rashin ganinta ba wayarsa yadauka kamar ya kirata se kuma ya ijiye yana fadin control ur self man kansa yadafe da hannu biyu yana cukurkuda gashinsa yace wai meyake damuna ne
wasa wasa har dare asma'u bata dawo ba tun yana hakuri har yagaji yakira wayanta amma akashe wayan khadeeja yakira tace yau Sam ma bataje gidan ba
Wurin grany yanufa itama tace bata San inda tajeba nan fa aka fara nemanta sama da kasa amma ba ita ba labarinta
Nan take gida yadauka ba asma'u yar karamar hauka AK yayi dan yarasa ta inda zai fara se safa da marwa yake yana neman numbanta amma baya shiga police station yaso yaje grany tace yayi hakuri har zuwa safe suga idan ba'aganta ba
cikin Daren ya kira ahmad suka fita nemanta se yawo suke sun rasa ta ina zasu fara nemanta
Haka ma khadeeja da fa'iz duk inda sukasan tana zuwa sunje amma ba'aganta ba
Har dare yaraba suna yawo amota da kyar ahmad ya lallashesa akan sukoma gida gobe dasafe sucigaba da nemanta
Badan yaso ba haka ya hakura suka kama hanyar gida
akan hanyarsu sukaga mutane sun taru ana kallon wani Abu
Tabo ahmad yayi yana fadin dakata friend bari muduba nan muga
Baijira amsa ba kawai yabude motar yafita cikin sauri yakarasa wurin mutanen yana tambayar meyafaru
Cike da tausayi wani mutum yace
Allah sarki wata yarinya ce mota takade yanzu suka nufi asibiti amma yarinyar kam gaskiya bance akwai sauran nunfashi atare da ita ba ....
Baijira yaji karshen maganar ba ya kutsa ta cikin mutanen yashiga ahmad nabinsa abaya
Jini malala awurin kai daga ganin jinin kasan da kyar yarinyar zata rayu
Nan take jikinsa yahau rawa durkushew yayi akan guywowinsa yana jiyo maganar mutanen wurin sama sama saboda tuni jiri yafara dibarsa baki bude yake kallon jinin
Ahankali yakai hannunsa yatabo jinin yana kallo lokaci guda wasu hawaye masu zafi suka ziraro akan kuncinsa
Dafa kafadansa ahmad yayi shikansa yakasa danne tashin hankalinsa cikin sassanyar murya yace AK control ur self ba lalle ne ya kasance asma'u ce tayi hatsarin ba
Dagowa yayi yana kallon ahmad da jayayen idanuwansa cikin
Book Chapters
Chapter 23
Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35