Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fuska kamar yanda yaga tayi Aysha takasa hakuri seda taje farm house din AK tana isa sani yacemata ai yakoma wurin matarsa nan take taji jiri na deebarta Tafito kenan tahadu da AK zai shiga dan baisamu damar yin program dinsa ba lokaci yakure Damamaki yace me kike anan Kai zan tanbaya daga ina kake Daga gidan abokina Kusan shi tamatso tace daga gidan abokin naka ne kasamo turaren mata Kauda kai yayi baice komai ba Fashewa tayi da kuka tace AK meyasa zakamun haka kasan ina sonka amma inaga kaina kawai nakeba wahala gara ma kawai nahakura dakai Saurin rikota yayi yana fadin come on aysha stop this drama please Me kike tunani wai ina kula waccan yarinyar kome Kema kinsan she is not my type mezanyi da ita Kima daina tada hankalinki akan wannan Da kyar ya lallasheta tayi shiru sannan yajata suka fita shakatawa Da kyar Umma tashayo kan khadeeja takira mata Asma'u Bayan sun gaisa Umma ke tambayanta sun isa Eh ta amsa atakaice To ina maigidan nanki Yana bayi ... Karban wayan khadeeja tayi cikin sassanyar murya tace ammah ya kike Lafiya kalau khady ... I hate it when u lied to me Cike da mamaki Umma tace meke faruwa ne meyasa kika ce haka Saurin hannunta khadeeja tayi dan Sam tamanta agaban Umma take Cikin dakewa tayi murmushi tace kai Umma kincika tsoro kawai dai nasan bata zuwaba kuma tayi nesa damu dole zataji badadi Katse kiran asma'u hade da sulalewa akasa tafashe dawani irin kuka maiban tawsayi """" Urs.... *MHD* [18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚 👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧 Na( Maryam Muhammad jibril) 8⃣0⃣ Khadeeja ce tazo wucewa ta layin gidansu ahmad ta gansa yafito daga masallaci Karasawa wurinsa tayi tana boye hawayenta Yana ganinta ya kauda kai yana fadin why are u flowing me since u have no feelings for me Sadda kanta tayi kasa tace nazo ne naji wace shawara kayanke akan maganar da mukayi jiya Khadeeja kigane ni bazan iya abunda kike so ba Bazan iya auren sarah ba bana sonta Zaka sota daga baya just try it Bazai yuwo ba khadeeja mutum baya iya sakama kansa son wani Kenan haduwata dake da fadan da mukayi duk ke kika shirya a'a bani nashirya kawai yafaru ne To kigane so faruwa yake dan na auri sarah bashi zaisa AK yaso asma'u ba Nace miki kibarni ni zan daw mataki akai Bawani matakin dazaka dauka abunda AK yayi Yayishine domin kanwarsa Nima kuma zan hakura dakai ne saboda yayata kai kuma kahakura dani dan farin cikina idan har kana sona ... Tana kainan tajuya ta tafi tana sharan kwalla Dunkule hannu yayi yanawshi iska yana cije lebe Motansa yashiga yafigeta aguje kamar mai shirin barin gari zaune suke cikin katuwar runfar gidan suna hutawa bayan sundawo daga shakatawa AK nifa ina jin tsoro dan Allah kar wannan yarinyar ta rudaka Wai aysha so nawa zan gayamaki ba abunda zai faru baki yarda dani bane kome Mezanyi dawannan chitti din kawai jira nake ahmad ya auri sarah nayi waje da'ita Miye kuma chitti ?? Yaren India ne yana nufin karamin abu Dariya tayi tace nakosa naga ranar da asirinta zai tonu mu koreta daga gidan Shiru yayi kamar mai nazari yanaji bai kyewta ba dayama grany karyan yayi tafiya kuma baikamata yakai yar mutane hotel ya ijiyeta ba har tsawon kwana hudu Dafashi aysha tayi tace kana tunanin matarka ne Kauda kai yayi yana furzar da iska bai ce komai ba Asma'u nazaune adaki ita kadai Bayan AK ya aikomata da kayanta tasa Jitayi zaman ya gundureta tafito waje tasha iska Restaurant din wurin tanufa Daidai yahaya yazo wucewa ya hangota Cike da mamaki yake kallonta shidai yasan ance sunyi tafiya da AK to meyakawota nan kuma Wayarsa yadauka ya kira grany yana daga gefe Bayan sun gaisa yake tambayarta yallabai nagari a'a bayanan sunyi tafiya da amaryansa kuma kar wanda yadamesa da kira Lafiya kake tambaya .. a'a ba komai grany dama wata nagani kamar asma'u shiyasa nake tambayar ko sunfasa tafiyar ne Cike da mamaki tace a ina kaga asma'u Bai bata amsa ba yakatse kiran yana lalubo numban asma'u yana daga nesa yana kallonta amma ita Sam bata gansa ba Tana zaune taji wayanta na ringing mamaki tayi ganin numban yahya Afili ta furta yahya kuma to lafiya Tajima kafin tadaga wayar tare da sallama Bayan ya amsa sallamarta yace dama nakira ne naji kun isa lafiya Lafiya kalau Yaya... Kinga Lagos ko? Nasan baki taba zuwa ba ... Eh Yaya yanzu haka ma muna wurin hutawa gwanin sha'awa Ashe Lagos tanada kyew haka ya wajansu Umma Lafiya .... Yafada yana katse Kiran da mamakin meyasa sukayi karyan sunyi tafiya Me asma'u take ahotal ita kadai ina AK yake Dole akwai wani Abu Wani mutum ne yazo yazauna kusa da asma'u dawata jaka ahannunsa yana leken police din dasuka shigo restaurant din Tunda tagansa taji bai kuanta mata ba daure fuska tayi tace malam yi hakuri katashi ni matar aure ce Murmushi yayi yamike yana fadin yi hakuri ban saniba Karasowa police din sukayi cikin restaurant din suna bincika ko ina Da manager ya tambayesu suka ce sunsamu labarin anshigo da drugs restaurant din dan haka dole su binciki kowa anan Suna cikin bincike suka iso wurin asma'u Daukan jakan yayi yana fadin madam is this urs Atsorace tazaro ido tace no batawa bace Bude jakan sukayi sega drugs makil acikin jakar Murmushi yayi yace kinbani mamaki gaki kamar mutuniyar arziki Ashe ke annoba ce kina matsayin mace da darajarki amma kinwatsar da ita kina cutar ya'yan jama'a Kuka tafara tana fadin wallahi batawa bace nima seyanzu naganta anan dan Allah kasaurareni Kiran ogansa yayi ya nuna mashi nan take yabada umarnin ayi arresting dinta Karasowa yahaya yayi yana rokon sukyaleta yasanta wannan ba sana'arta bace yarinyar yar gidan mutunci ce Sunkuy dakanta tayi data tuna karyan datama yahya kenan dama yaganta awurin shiyasa yakirata Ba rokon da bai musu ba amma sunce sedai yabiyosu office yabada shaida Tana kuka haka suka tasa keyarta har cikin motarsu Lekowa tayi tana kallon yahya cikin muryan kuka tace yaya dan Allah kar ka gayama su Umma abunda yafaru dan Allah!!! AK na zaune da aysha suna fira amma baisan meyasa ba Sam baya jin dadi hankalinsa yakasa kuanciya Kamar daga sama yahango grany tana zuwa Azabure suka mike gaba daya suna kallonta har takaraso fuskarta adaure kamar bata taba dariya ba Cikin kakkawsar murya tace mekake anan Shiru yayi baice komai ba Badakai nake ba uban me kake anan tare da wannan mara kunyar Ina ka kai yar mutane kai yanzu baka jin kunya abid yaushe kazama haka ban saniba Hannu tadaga da nufin wanka meshi mari daidai nan sarah takaraso aguje tana fadin a'a grany Dakatawa tayi tana jifanta da wani irin kallo Sunkuy dakai sarah tayi tace yanzu Yaya yakirani yana cikin matsala ne Yayi signing contract ne dawani company kuma yau ne zasu gabatar da meeting idan har baijeba zasuyi tunanin ya yaudaresu ne kuma hakan zai jamai matsala shiyasa baisamu damar tafiya ba Kallon AK grany tayi cikin kakkawsar murya tace ina asma'u Sunkuy da kai yayi cikin rawar murya yace tana hotel dazu nabaro wurinta itace ma tabani kwarin guywar yin hakan tace zata miki bayani dakanta tasan zaki fahimta Juyawa tayi tana fadin muje ka kaini wurinta dan ban yarda dakai ba bin bayanta yayi suka fita Ajiyar zuciya aysha tasauke tazauna kan kujera tana fadin natsani yarinyar nan Tsaki sarah tayi tana hararanta tace ke bazaki iya hakura da AK na minti biyar bane se kin ruguza mana shiri Kauda kai aysha tayi tana fadin gwara ni ai... Suna isa dakin da asma'u take sukaga bata cike da mamaki yatambayi dai daga cikin ma'aikatan wurin shine yake bashi labarin abunda yafaru Al'amarin ya girgiza shi matuka Asma'u ce a police station tasasu agaba se kuka take masu tana fadin wallahi batasan komai akan wannan jakar ba Waya dan sandan yabata yace takira yan uwanta suzo Karban wayan tayi tana tunanin wazata kira itadai bazata iya kiran Umma ko abba ba Numban AK takira tana ringing baidagawa cikin muryan kuka tace ina kira baidagawa Dariya yayi yace saurayinki ... Kauda kai tayi tace mijina dai Yasunan mijinki ... Konafada bazaka yarda ba Saboda me koshima dan safaran kayan mayen ne Girgiza kai tayi alaman a'a Koshine wanda muka gani a restaurant ... Nan madai girgiza kai tayi Ahasale yace to waye a tsorace tace AK hausawee Gaba daya yan sandan suka kwashe da dariya Seda sukayi mai isarsu sannan dayan officer din yace yallabai kila kowani AK din take nufi Fashewa tayi da kuka tace shidai wanda kuka sani wallahi shine mijina idan baku yaradaba kuduba social media anyi posting pics dinmu Dariya sukayi sannan Babban su ya umarci asata a cell idan wani nata bai zoba zai watsata a news kowa yagani Kuka tafara tana rokonsu amma basu saurareta ba Umma da khadeeja suna zaune tana tambayarta meke damunta kuana biyu ta sawya Fa'iz dake gefe azaune yace Umma kila tana kewar asma'u ne Shiru Umma tayi nadan lokaci sannan tace ni yau inaji ajikina kamar wani nawa yanacikin matsala Saurin kallonta khadeeja tayi tana fadin Umma duk muna nan waye kuma amatsala Fa'iz yace to ko asma'u ce Hararansa khadeeja tayi tace ammah tana tare damijinta ba abunda yasameta Umma kidaina damun kanki kawai shedan ne kesamaki waswasi Tana rufe baki suka jiyo sallamar yahya daga waje Saurin tashi khadeeja tayi tanufi get tana fadin mekuma yakawoshi nan gidan Lekowa tayi bakin kofa suka gaisa Sannan yace Umma naciki Lafiya .... akan asma'u ne Saurin fitowa tayi waje tana fadin meyafaru Dazu naje hotel nahadu da ita to kuma ina nan tsaye sega yan sanda sunzo suntafi da ita Cike da damuwa tace yan sanda fa kace akan wane dalili suka kamata Zaiyi magana kenan sukaji Umma nafadin wa aka kama Murmushin dole khadeeja tayi tace ba kowa Yahya yamatso kusan Umma yana fadin karya take Umma asma'u yan sanda suka kama Innalillahi wa inna ilaihiraji'un Asma'u fa kace yahya a ina Riko hannunta khadeeja tayi cikin rawar murya tace Umma ki kuantar da hankalinki ba abunda zai sameta bari naje police station din yanzu naji meyafaru a'a khadeeja shiga ciki kizauna bari ni naje naga ko dagaskene dan ni har yanzu ban yarda asma'u bace suda sukayi tafiya da mijinta me kuma yahadata da yan sanda [18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: Da kyar AK ya lallashi grany takoma gida shikuma ya wuce police station Asma'u na cikin cell tana kuka fatan ta daya kar Umma tafahimci gaskiyar halin datake ciki wani dan sanda ne yazo ya fito da ita Tana zuwa ta isko Umma atsaye da gudu tazo ta rungumeta tana kuka Rikota Umma tayi tana tambayr ta meyafaru taya tazo nan ina mijinta Kuka kawai take takasa magana Jijjigata Umma tayi dakarfi tana fadin asma'u kigayamun meyake faruwa ne zatayi magana kenan taga AK yashigo office din fuska ahade Yan sandan sunyi matukar mamakin ganinsa Cikin kakkawsar murya yace akan wane dalili zaku kamata DPO ne yace sorry AK banyarda ba lokacinda tace Kaine mijinta Saboda me ? bazan iya auren ordinary girl bane I doesn't judge people by their looks but their character Juyowa yayi yana kallon asma'u yace meyasa baki gayamusu ke matata bace Matsowa tayi kusansa tace Nagayamusu amma basuyarda dani ba Kamar daga sama yaji ta rungumesa tana fadin I am glad u are here Cikin rada yace ke miye haka Dagowa tayi takallesa tana mai alama da ido cewa Umma tana kallo Saurin rungumeta yayi cikin kunne yarada mata Kindamu da ummanku ni kuma nadamu da grany Sannan ya dagota yana fadin is ok I am here U are safe now Murmushi tayi tace I am sorry for troubling u Hannunta yariko yace nagode allah Dana sameki anan Namiki alkwarin bazan kara barinki ke kadai ba kema kuma kar kikara yin nesa dani kinsan yanda nake sonki idan wani abu yasameki yazanyi I can't bear it Rungume juna suka karayi bakinta takai setin kunnensa cikin rada tace u are over reacting kafitar dani daganan wajan mana Murmushi Umma tayi tana kallonsu cike da birgewa Sabanin yahya da abun ya dawre mai kai Janye jikinsa yayi daga nata yana kallon dan sandan yace akan wane dalili kuka kamata Jakar yanuna masa yana fadin munsamu wannan jakar akusa da ita kuma drugs ne aciki Daukan jakan yayi yace yanzu daka ganta ahannuna seka kamani kace ina safarar drugs Wace hujja kake da ita datanuna jakan tatace Kasan zan iya yin karar ka akan bata mata suna dakayi Hakuri suka fara bashi akan basusan matarsa bace shiyasa Hannunta yaja suka fito daga police station din Su Umma nabiye dasu Wurin Umma yazo Yace Umma meyasa kika zo nan kinsan yanda asma'u tadamu da lafiyarki yanzu gashi kindaga mata hankali ni kuma natsani gabinta cikin damuwa Naji ance asma'u tana nan ne shiyasa nazo Hannunta yariko yana murmushi yace Umma ki kuantar da hankalinki asma'u matata ce hakki ne akaina na kula da ita wannan ma dayafaru kaddara ce amma namiki alkawarin zan kiyaye Murmushi tayi tace ba komai abid nidama nasan bada saninka haka yafaru ba allah yatsare gaba Ameen yafada yana kallon yahaya yace kamaida Umma gida tana bukatar Hutu Sallama suka musu yahya yaja motar suka tafi Cikin siriruwar murya tace I am sorry Juyowa yayi yakalleta takara cewa Sorry Baice komai ba yanufi motarsa Binbayansa tayi suka shiga tare Khadeeja nagida hankalinta atashe jin shiru Umma batadawo ba Fitowa tayi da nufin binsu taga ahmad akofar gida Daure fuska tayi ta kauda kai kaman bata gansa ba Karasowa wurinta yayi yana fadin yawwa dama ke nake jira Ya akayi kasan zan fito Kawai dai naji ajikina ne To me yakawoka wurina Cikin sassanyar murya yace gaskiyanki ne nagane nine mai laifi kuma ina so na gyara kuskuren da nayi na amince zan auri sarah !!! She was shocked Ni dai nasan mace daya nakeso arayuwata kuma bana tunanin zanso wata bayan ke Juyawa tayi takoma ciki tana danne kukanta Tana shiga tasaki wani irin kuka mai ban tausayi Tundaga waje yana jiyota runtse ido yayi yana jin zafin kukanta har kasan zuciyarsa yajima atsaye kafin ya juya jiki asanyaye yabar layin Seda Umma tadawo tabata labarin abunda yafaru a station tana fadamata tayi farin cikin ganin yanda AK ke kula da asma'u Shiru khadeeja tayi tana tunanin meyasa AK yake yaudaran kowa kawai saboda kanwarsa Suna isa gida bangaren grany suka nufa Tana zaune itada sarah suna jiran dawowarsu Tana ganinsu tamike tana Cike da farin ciki tanufo asma'u tana fadin Ba abinda yasameki dai ko meyasa baki kirani ba kinsa nashiga damuwa Riko hannunta AK yayi yace shikenan grany ba gashi na maidomaki ita ba Fizge hannunta tayi tana fadin dallah yimin shiru duk bakai kaja ba meyasa baka barta agidaba zaka kaita hotel Riko hannunta asma'u tayi tace Grany yi hakuri kidaina mishi fada laifi nane ni nace yatafi wurin aikinsa Kima daina goyon bayansa dan ba yarda zanyi ba yana kokari wurin aikinsa amma yakasa wurin kula da matarsa Nadauka idan yayi aure zai canza ashe nayi kuskure Shidai AK yana tsaye kansa akasa yakasa cewa komai Ba dole ne yadamu dani ba amma yazama dole yadamu dake amatsyinki na matarsa Juyowa tayi tana kallon AK tace To bari kaji nagayamaka idan har kasake maimaita irin wannan kuskuren zan dauki asma'u mubar maka gidan Kudi dai suna iya karewa daga karshe duk watsewa zasuyi subarka kai kadai matarka ce kawai zata zauna dakai Sekayi shawara... Tana kai nan tanufi hanyar dakinta rai bace Dagowa yayi yana kallon sarah da rinannun idanuwansa cikin wata iriyar murya yace Yaune karo nafarko da grany ta taba mun magana haka Juyowa yayi yana kallon asma'u yace are u happy now Kinsamu abunda kike so Dafari kin rabani da ahmad yanzu kuma kindawo kan family na gashi ta dalilinki grany tamun abunda bata taba mun ba wallahi jinake kamar.... Hannunsa yadaga da nufin marinta sarah tayi saurin rikoshi tana fadin calm dwon bro Kibarni kawai nakasheta all my problems will be over Dafashi tayi tace easy yaya abun bai kai haka ba tunda na auri yarinyar nan nayi ban kuana da kuanciyar hankali Kallon Asma'u yayi yace uban wa yace kifita daga dakin mekika jeyi a restaurant Nataimake ki a station saboda farin cikin ummar ki amma ke kin ruguza mun nawa banza ...shashasha... Rikoshi sarah tayi tana fadin yaya kabarta kawai Zama yayi yana fadin bazan barta ba ita dai zata barmun gidana... Fita asma'u tayi daga palon tana danne kukanta ... dafashi sarah tayi tana fadin relax Yaya wannan yarinyar tana anfani da grany ne wajan samun abunda takeso Kafin mu iya mata wani abu dole se grany tasan gaskiyar wacece ita Girgiza kai yayi yace I don't think that is possible Murmushi tayi tace kabar komai ahannuna nidai kawai kasa ahmad ya aureni Tashi yayi yafita yana fadin zan dawo maki da ahmad rayuwarki nikuma kifitar mun da wannan daga tawa rayuwar.... washegari dasafe... Cikin bacci takejin music natashi bude idonta tayi taga AK agefe yana motsa jiki (exercise) Yi yayi kamar bai ganta ba yaci gaba da abunda yake Cikin muryan bacci tace wanna wane kalan abune ... exercise... Yafada atakaice To kacanza kidan ko ka kashe music mana Haka nasaba yin abuna kuma da rock music tashi tayi tadauki blanket din ta zata wuce ta bige da exercise Weight dinsa yar kara tayi hade da dafe kafa Dariyar keta yayi yana fadin Inada medical glass idan kinaso zan taimaka miki Banza tayi dashi ta wuce daki tana dingishi Knocking akayi awaje yaje yabude Rebeka yagani atsaye Bayan sun gaisa tace yallabai yau tun safe grany bata fito kuma bata bude daki ba .... Bai jira ta karasaba ya fita aguje ya sauka kasa yanufi bangaren grany Asma'u da fitowarta kenan tayi saurin bin bayansa Yana zuwa ya isko gaba daya yan gidan akofar grany suna bubbugawa Saurin karasawa yayi yafara buga kofar yana kiran grany Nan take hankalinsa yatashi guba kofar yake kamar zai ballata yana kwala mata kira Ture asma'u dake gefensa yayi yana fadin bari nazagayo ta window naga Karsawa tayi jikin kofar cikin siriruwar murya tace grany!!! AK har yakai bakin kofa ya tsaya cak jin anbude kofa Saurin karasowa yayi wurin grany cikin rawar murya yace Grany duk ihun da nake kina jina kika yi banza dani... Katsesa tayi dafadin ni banji ba asma'u kawai naji takirani Kuma daga yau muryanta kawai zanji tunda kuma ba kwajin maganta duk mai son wani abu yagayamata tagayamun Grany meyasa kike mun haka bayan kinsan bazan iya yin komai batare dake ba ke kika San komai nawa menake ci menake sha .... Kanada kudi ai zaka iya dawko wa'yanda zasu kula dakai konawa kake so Juyawa yayi yakoma bangrensa rai bace Yanaso yacigaba da exercise dinsa amma yakasa hannayensa biyu yasa yadafe kansa Daidai nan asma'u tazo wucewa ya fizgota dakarfi Hannayensa biyu yasa yariko dantsenta dakarfin gaske Atsorace tadago tana kallonsa yanda idonsa yayi ja kamar bashiba Cikin kakkawsar murya yace Wai me kike shirin yine Ina tsananin kaunar grany ta shiyasa nake kiyaye macin ranta tun ina karami bata taba gayamun maganar danaji zafinta ba se yau Tunda kika shigo rayuwata kika lalata mun ita Idan kika sake kika shiga tsakani na da grany sena.... Katseshi tayi dafadin Ba abunda zakamun da yawuce wannan zama na anan kadai ya isheni NI ba abunda nafadama grany Burina shine na hadaku wuri guda Nafahimci yanda kake son grany kuma nasan akwai zafi idan Wanda kake tsananin so yayi fushi dakai banji dadin yanda grany tamaka fada akaina ba Alhali ni ba kowa bace face bakuwa acikin familynku Zanje namata magana nabata hakuri kuma na kuatanta mata nasan zata fahimta Tunda tafara magana yake kallon kwayan idonta ko kiftawa baiyi Riko hannunshi tayi cikin rawar murya tace u are hurting me Saurin sakinta yayi yaja dabaya yana fadin sorry .... Fita tayi daga palon tana share kwallan datazubo mata karo sukaci da sarah zata shigo Karasowa tayi wurin AK tana fadin yaya meyafaru Abunda asma'u tagayamasa ya maimaita mata yakare zancan dafadin Kuma danakalli kwayan idonta zalla gaskiya nahango acikinsu inajin tsoro kar ace .... Shiru yayi bai karasaba yana nazarin maganganunta Dariya sarah tayi tace Yaya kabani dariya sekace ba wayayye ba Bakasan halin yan mata mayaudara ba kenan Idan kuna magana zasuyi kokarin hada ido dakai to daganan zaka yarda da duk abunda yafito daga bakinsu Natabbata dawannan take anfani wurin ahmad da grany shiyasa tasiye zuciyarsu Gyada kai yayi yace shiyasa danake kallon idonta ba abunda nakeji se sautin muryanta Kice nadaina kallon hada ido da ita kenan Fita tayi tana fadin idan baka hada da ita ba ita zata hada da kai kawai kasan yanda zakayi kafitar da ita daga gidan ne gaba daya ... Yana zaune adaki ta shigo rike da mug ahannunta yana ganinta yakauda kai Mikamishi mug din tayi tace ga coffee dinka Kin karba yayi yace bayaso Ta juya zata fita Yace ta ijiye akan dressing mirror Girgiza kai tadora akai Tasowa yayi ya nufota yana kauda kai Yana so yadauko mug din yadako kwalban turare Da mamki tace wai mekake hakane kwaban turare fa kadauka Ijiye kualban yayi yadauki mug din yana fadin nasani dama gwadaki nake naga ko kina bukatar glasses Kauda kai tayi tace kafini bukatar su To zaki iya tafiya Karasawa tayi cikin dakin tana fadin inada abun yi Juyawa yayi yafita yakoma Palo Dakallo tabishi tana fadin mutum sekace aljani ... Urs.... *MHD* [18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚 👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧 Na (Maryam Mhd) 8⃣5⃣ Daddare AK na kuance akan gado yakurama TV dake jikin bangon dakin ido yana kallon wani horror film mai ban tsoro Kwance yake duk ya takure wuri guda gashi yakashe fitila se hasken TV kawai yadan haska dakin Yanajin anturo kofa yayi saurin kallon wurin adan tsorace ganin asma'u ne yasa ya hade fuska yacigaba da kallonshi Bata kulashiba tawuce bathroom Bayan wani dan lokaci tafito sanye dakayan baccinta dogon wando da riga mai dogon hannu kalan pink AK da yadukufa yana kallo yaji tasaki wata kara atsorace ya diro daga kan gadon yana tayata ihun Ganinta dayayi atsaye tana kallonsa yasa yawaske hade da daure fuska Cikin rawar murya tace dan ...dan Allah kacire wannan film din tsoro nakeji Tsaki yayi Yakoma kan gado yakuanta yana fadin ai ba danke nasaka ba bare kice nacire Yanda kike din nan ai bai kamata kiji tsoron aljanu ba Dan allah kacire ba kyewfa kallon irin wannan da daddare Dogowa yayi yakalleta sannan yamaida kallonsa kan TV can kasan makoshi Yace Saboda me Suna fitoma mutum dagaske ko kayita mugun mafarki Banza yayi da ita yaci gaba da kallonsa Towel tasa tana goge gashin kanta tanufi saitin gado zata dauki pilo da blanket dinta Sam baysan tabar wurin ba sedai yaji kamar Abu kusa dashi afirgice yamatsa daga kan gadon yana kunna bedside lamp Dariya tayi tace sekace dole kanajin tsoro ka kashe mana Blanket dinta ta dauka tayi hanyar fita tana fadin nidai in sunzo maka ziyara kar ka kirani a'a tsaya mana ina kuma zakije Juyowa tayi da mamaki tace kamar ya ina zanje ko kamanta inda nake kuana ne Daure fuska yayi yace ba inda zakije yau nan zaki kuana akan wane dalili Malama ba yanda zakijamun matsala awurin grany haka kawai tazo taganki kina kuana a Palo takara yin fushi dani dama da kyar ta hakura Buga kafa tayi da kasa kaman tafashe da kuka tace Allah ni bazan kuana anan ba Palo zan kuana haka kawai hahaha yarinya sama zuciyarki ruwan sanyi ba abunda zanyi dake I have better things to do Dawowa tayi tana zunbura baki tace wai kodai tsoro kakeji ne dan nace aljanu zasu zo maka ziyara Harara ya watsamata yana nuna mata gefen gadon daga kasa yace kishinfida blanket dinki anan coz I can't share my bed with u a'a ni gaskiya bazan shinfida anan ba Dayan gefen takoma tashinfida blanket

Chapter 11 of 35