rawar murya yace are.....are u sure ?
Shiru ahmad yayi yana kauda kai dan baisan mezai cemasa ba
Sun jima ahaka kafin da kyar ahmad ya dagosa yana fadin friend let's go home
Bin bayansa yayi suka tafi batare dayace komai ba amma har sukayi nisa yana waigen jinin dake kasa
Ahmad nagaba yana tafiya jiki asanyaye yana boye hawayen fuskarsa dan ba karamin tausayi AK yabasa ba fatansa daya allah yasa ba asma'u bace tayi hatsarin dan kwa in itace to gaskiya sedai suce allah yajikanta
Yana cikin wannan tunanin kawai yaji karan faduwan Abu abayansa saurin juyowa yayi dan ganin komiye
AK yagani akwance kamar gawa dagudu yakarasa wajansa yana kiran sunansa da karfi har saida mutane suka juyo
Durkusawa yayi kusa dashi yadagosa yana fadin heyyyyy friend....wake up miye haka .....katashi mana
Bubbuga gefen fuskansa yafarayi yana kiran sunansa dakarfi amma shiru cikin mutanen wurin ne akasamu Wanda suka taimaka masa yasaka sa amota se asibiti
Suna isa aka wuce emergency dashi har lokacin ba alaman nunfashi atare dashi
Nan take ahmad yakira gida yasanar dasu kan kace me har asibitin tacika da yan gida harda su Umma
Kuka inna take kamar karamar yarinya tana fadin bayin allah abun tausayi duka duka yaushe suka fita daga wata wahalar yanzu kuma ga wata shi wannan akwance ita waccan allah kadai yasan inda take
Ansha wahala kafin da taimakon allah aka shawo kan matsalar
Bayan anakaisa dakin hutu doctor yasanardasu cewa damuwa ce tamai yawa nan kowa yafara tofa albarkacin bakinsa kan canzawar AK cikin kuana biyu
bashi yafarka ba se dasafe bayan sallar asuba ahmad ne kawai zaune kusa dashi dan ba abarin mutun sama da daya sushiga in percent yana bacci
ahankali yabude idanuwansa yana bin dakin da kallo har yazo kan ahmad da yake faman jera mai sannu
Lumshe idanuwansa Lokaci guda yana tuna duk abunda yafaru
Saurin dago hannunsa yayi yana kallon jinin daya bushe akan yatsunsa
juyowa yayi yana kallon ahmad cikin dasashshiyar murya yace har yanzu batazo ba
Sunkuy dakai ahmad yayi yakasa cewa komai
"Kun gayamata cewa banada lafiya ...?
kagaymata cewa idan maganar da banayine yasa ta tafi to nadaina zan dawo yanda nake zan fara magana kamar da zan tsokaneta zan mata fira amma bazan iya rayuwa batare da ita ba tayi hakuri tadawo
tasowa ahmad yayi yazauna kusa dashi yana boye hawayen fuskarsa yace friend asma'u tana nan daranta ba abunda yasameta ba ita bace wannan yarinyar kadaina damun kanka kana bukatar Hutu
Riko hannun ahmad yayi yana fadin to idan ba ita bace tana ina meyasa har yanzu bata zoba duk lokacinda nashiga matsala she is always there for me to yanzu ya akayi ban ganta ba
kagayamata tazo kaji tell her that I am really sorry I feel lonely without her by my side
Tashi ahmad yayi yafita daga dakin yana share kwalla dan bazai iya juran ganin abokinsa ahaka ba
ta wurinsu grany ya wuce amma baice musu komai ba bin bayansa khadeeja tayi tana kiran sunansa
Saurin mikewa sukayi gaba daya suka shiga dakin
binsu yake da kallo daya bayan daya har yazo kan Umma sannan yasakemata lallausan murmushi yana mata alama da tazo
Karasawa tayi wurinsa tana sharan kwalla tace sannu abid
Riko hannunta yayi yana murmushi yace hmmm Umma kinsan me ?
Girgiza kai tayi wasu hawayen nakara gangarowa
Cije lebe yayi yana runtse ido yace ur daughter was a little disturbed
taga mun damu da ita shiyasa take bamu wahala ko
Daga mishi kai tayi bakinta narawa takasa cewa komai
Murmushi seda hakoransa suka fito lokaci guda hawaye na gangarowa daga idonsa cikin rawar murya yace ance uwa tana ji ajikinta idan wani Abu yasami yarta now tell me is she ok ?
Kwace hannunta tayi tafita daga dakin tana fashewa da kuka
Karasowa wurinsa grany tayi tana shafa kansa tace Abidi kazama jarumi mana idan kai kana haka mu kuma matan yazamuyi ka kuantar da hankalinka ba abunda yasameta kaji insha allahu za'aganta
Rungumesa sarah tayi tana gashewa da kuka dan ba karamin tausayi yabata ba
Hannunsa yakai yana shafa kanta se alokacin yagane halin da tashiga lokacinda tarasa ahmad baiga laifinta ba dan koshi yanzu ji yake ba abunda bazai iyaba indai asma'u zata dawo
Kuanan su biyu a asibiti aka sallamesu har lokacin AK baidawo hayyacinsa ba gaba daya yazama kamar mai tabin hankali maganganunsa kadai sun isa Susa mutun zubar da kwalla
Har wannan lokacin ba asma'u ba labarinta ahmad kullun yana zarya police station amma bawani labari mai dadi se antsinci gawar wata ansamu wata tayi accident ansamu wacce aka ma fyade har bayason zuwa dan kullun yaje se ranshi yabace
Kuance yake akan gado gefen da asma'u ke kuanciya idonsa alumshe kamar mai bacci amma yayi zurfi cikin tunani
Ahmad ne yashigo rike bowl din fruit salad aciki dan seda dubara yake cin abinci
Kusa dashi yazauna yana fadin Mr Romeo dan tashi kaci wannan mana
Banza yayi dashi yana gyara kuanciyarsa yabashi baya
Shiru yayi nadan lokaci sannan yace da wane suna ma asma'u ke kiranka .......miye ma
Murmushi AK yayi batare da ya juyo ba yace ABI
Dariya ahmad yayi yace ehhh haka fa ABI to ABI wannan fruit salad din ranar da asma'u zata tafi tayishi tasa a frig saboda tasan zaka bukace shi
Tashi yayi yafita yana fadin gashinan idan baza kaci ba zan turo nura ya dauka
Yana ganin ya fita ya tashi zaune yana murmushi yadauki bowl din yafara sha harda lumshe ido
haka dai yacigaba da jinyar zuciyarsa shi kadai yasan halin da yake ciki lokaci guda ya rame gaba daya yafita hayyacinsa ba inda yakezuwa daga bangaren grany se wurin Umma kullun firarsa bata wuce ta asma'u shiyasa yakeson zama da khadeeja dan tayita bashi labarin rayuwarsu shikuma yana dariya
kullun da tunaninta yake kuana yake wuni idan abun ya isheshi sedai ya shige daki yarungume kayanta yayita rusa kuka se yayi mai isarsa dan kanshi ya hakura wayarsa kuma sallace kawai kerabasu kullun tana hannunsa yana kallon photon asma'u
Zaune suke da ahmad apalo yana tayasa cin abinci
Cike da tausayi ahmad ke kallonsa yace AK kasan kana son asma'u meyasa baka gayamata ba
Murmushin dayafi kuka ciwo yayi yana hadiye lomar da kyar yace
nadamar danake ako dayaushe kenan nayanke shawar gayamata amma inaso in mata surprise in shirya komai yanda zai tsaya akwakwalwarta har karshen rayuwarta naso najiyamata dadin dako wace ya'mace keburin samu agidan mijinta
Ahmad bantaba sanin cewa inason chitti ba seda tabarni bansan a ina take ba awane hali take amma jikina yana bani tana raye
Dafasa kafadansa ahmad yayi cikin sugar lallashi yace
Nima ina fatan haka amma kacigaba da hakuri kuma mudage da addu'ar allah ya bayyana mana ita
Share kwallansa yayi yace shiyasa akace idan kanason mutum kagayamasa maybe lokacinda zakaso yasani ko zaka shekara kana ihu bazai jikaba
Kawai sonake naganta koda so dayane nagayamata cewa ina sonta
Shiru ahmad yayi baice komai yana ni dayasan inda take dako birnin seen ne se yanemota kodan abokinsa yafita daga wannan halin
abubuwa dayawa sun canza gaba daya farin ciki ya kawaracewa gidajen biyu ahmad da khadeeja kuwa tuni sun ijiye zancan urensu gefe
Kasuwancin AK gaba daya yakoma baya saboda kokadan ba abunda yake kaishi office ahmad kuma shikadai abun yamasa shima yana kokarin bude nasa companyn a Lagos so baicika zama ba kullun yana zirga zirga ga damuwar halin da AK keciki ko yana gari to kullun suna tare da AK
Su uncle jamilu sun samu abunda sukeso se yayi Kane Kane a company wadaka suke da dukiya son ransu
Aysha kuma tana nan tana renon cikinta tana jira lokaci yayi dazata fara aikinta
sarah ma gaba daya jikinta yayi sanyi da yanayin da yayanta yake ciki ko baifada mata ba yanzu tasan yana son asma'u shi yasa take tausayamasa dan tasan irin wannan yanayin narasa Wanda kakeso
Su Umma da grany kuma tun suna kuka har sun gaji sun fawwala wa allah komai amma kowane dare na allah se Umma tayi kukan rashin sanin halin da yarta take ciki
Khadeeja ma juriya kawai take amma gaba daya ta canza duk wannan rahar da masifar tata duk tadaina tadawo so silent karatu kawai sukasa agaba itada fa'iz sedai ko a aji ta tuna asma'u sedai kawai aga tana rusa kuka sedai tafita waje tayi mai isarta ta hakura tun fa'iz natayata har yagaji sedai ya lallasheta
💔💔🕐🕒🕓🕕🕖🕗🕘🕙🕚🕛💔💔
*Bayan wata daya....!!!*
wata safiyar lahadi misalin karfe 9 ruwan sama ya sauka gari yayi sanyi ga wani daddadan iska dake kadawa mai dauke da kamshin damuna
AK nazaune agarden ya harde hannaye yana kallon fararen tantabaru dake zagaye dashi kamar zasu hau jikinsa saboda sabon dasukayi dashi cikin wata daya kullun awurinsu yake wuni sallace kawai kefitar dashi se bacci
daidai wannan lokacin wata arniyar mota ash color kiran BMW sabuwa gal tayi parking aharabar gidan
Bakin glass din motar shi yahana agane Wanda keciki
gaba daya ma'aikatan gidan sunyi cirko cirko suna kallon motar baki bude sunkosa suga waye aciki
motar takai kusan minti goma da tsayuwa amma bawanda yafito daga ciki
Ahankali aka turo murfin motar kusan minti biyar tadauka kafin tafito daga motar tana tura murfin dakafarta tarufe motar sannan ta gyara tsayuwarta tana bin gidan da kallo
[19/07, 17:05] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣6⃣0⃣
cikin sanda tashigo bangaren grany tana leken palon ganin grany ne ce kadai azaune yasa ahankali takarasa cikin palon tayi tsaye daga nesa tana kallon grany idonta pal kwalla
Dagowa grany tayi tana kallonta nadan lokaci sannan............. tasaki wani lallausan murmushi tana fadin karaso mana asma'u
saurin karasawa tayi tafada jikin grany tana fashewa da wani irin kuka mai cin rai
Shafa kanta grany tayi cikin sigar lallashi tace a'a asma'u miye kuma na kuka ai ba haka mukayi da keba
Cikin muryan kuka tace grany bazan iya ci gaba da wannan aikin ba bazan iya jurar ganin ABI awannan halin ba kuma fa kinji me Umma tace wai sedai in nemi wata uwar ba ita ba
Katseta grany tayi dafadin zaki iya asma'u tunda fari nasan zaki iya shiyasa nasakaki kimanta da Abidi nasan shi yanada juriya da tawakkali ba abunda zai sameshi kuma naga alama bai yarda cewa yaudararsa kikayi ba ita kuma ummanki ranta ne yabace amma ba abunda zata miki kici gaba da aikinki wata rana dakanta zata yi alfahari dake
Shiru tayi tana share hawayenta sannan tadago tana kallon grany tace kin lura da uncle jamilu dazu kinga yanda yake subutar baki
Tabe baki grany tayi tace hmm bari kedai ai tun da kika shigo nakafesu da ido se alokacin nakara yarda da abunda kika fada mun godema allah dakika jiyo zancansu dasedai muje mu asalansa
Dariya asma'u tayi tace amma grany kince in nazo zaki bani labarin yanda ABI da bana nan
Dariya grany tayi har tafa hannu tace kedai bari asma'u ai ni naga ikon allah ke mutuminki Ashe yana sone yana kai kasuwa bawan allah da kinganshi lokacin se kin tausayamai
Fuskar tausayi asma'u tayi tace gashi naga duk yarame kamar ba shiba
"hmmm ba kin dawoba ai yanzu zai maida kibansa amma gaskiya kinyi kokari da inata tsoron kar aje kikasa yin abunda muka tsara shirinmu ya lalace
"Grany ai ba karamar dakewa nayi ba kafin nayi wannan acting din bama danaga Umma ji nayi kamar inzo dagudu in rungumeta
Kallon kofar dakin inna ameena grany tayi sannan tace ai gara da kika dake kinga daganan mutananki zasu fara shakkar ki dan na hango tsoro karara afuskarsu
Shuru tayi nadan lokaci sannan tace yanzu gobe insha allahu zan fara zuwa office nasan ansamu canji sosai kasancewar ABI da Ahmad basa zama kuana biyu duk yanda ake ciki idan nadawo zan sanardake
shuru sukayi nadan lokaci sannan grany tadago tana dariya tace yi fa hakuri dazu nawankeki da mari
Itama dariya tayi tana shafa kuncinta tace ba komai ai duk cikin aikin ne sannan ta tashi zaune tana riko hannun grany tace amma gaskiya dazafi nan gaba inzaki mareni kidan min signal dan nashirya dan gaskiya na tsorata dazu
Dariya suka sa gaba daya daidai lokacin inna ameena ta turo kofar dakinta tafito
Grany na ganinta tayi saurin kwace hannunta cikin kakkausar murya tace eh anmareki din ko zuwa kikayi kirama ne
alama tama asma'u da ido sannan taci gaba da fadin tanbayar ki nake ko zaki rama ne
tashi tsaye asma'u tayi tana kallon grany fuska adaure tace ba ramawa nazo yiba zuwa nayi inmaki kashedin kar ki kara kai hannunki jikina da nufin marina namaki hakurin nayau saboda rashin sani amma nan gaba kika sake banajin zan iya kyaleki
Tana kainan ta juya tafita ko kallon inna ameena batayi ba bare tasan taganta
Saurin karasowa inna ameena tayi cikin palon tana fadin nashiga uku ni ameenatu wai kenan dai dagaske yarinyar nan take tazama mara mutunci
tsaki grany tayi tana kauda kai kamar dagaske tace nayi nadamar aura ma abidi yarinyar nan ina tunanin namishi zabi na kwarai ashe na dauko abun zai cutar damune ......takarashe maganar tana sharan kwalla
Dafata inna ameena tayi cike da tausayi tafara lallashinta
ahankali ta tura kofar dakinsu tashiga tsaye tayi tana kallon AK dake kuance kan gado idonsa alumshe kamar mai bacci
Dagowa yayi yana kallonta nadan lokaci sannan ya gyara kuanciyarsa ya juya mata baya
kallonsa taci gaba dayi hawaye masu zafi na tsere akan kuncinta
Jin kamar ana kallonsa yasa ya juyo ahankali yana kallonta saurin kauda kai tayi tawuce dressing room
can anjima tafito sanye da kayan baccinta riga da wando takwanta agefen datake kwanciya da
yana jin ta kwanta yamike tsaye hade da daukan pilo yabar dakin
Da kallo tabisa har yafita sannan tarungume pilo tana fashewa da kuka mai ban tausayi har bacci yadauketa
washegari dasafe tana cikin dressing room tana saka kayanta a drowanta AK ya fito daga bathroom daga shi sai towel aqugunsa suna hada ido yayi saurin juyawa yakoma ciki yana fadin what are u doing here
Ci gaba da aikinta tayi tana fadin meye kuma zaka wani juya bayan kasha cire kaya agabana
daga cikin bayin yace daba ni agaban chitti nake cire kaya bakeba lady boss
Rigarsa tamika mishi tana fadin fito kabani waje wanka zanyi kar namakara
Kwace rigarsa yayi ahannunta yana fadin karki kara tabamun kayana with ur dirty hands
juyawa tayi tafara Ciro dogayen rigunanta daga drawer tana sasu adayan drowar
Saurin saka rigarsa yayi yafito yana fadin ke wai mezakiyi
Bata kallesa ba tace wai meyasa kakeson shiga abunda bai shafeka bane kayana zan saka awurin
Janyeta yayi daga wurin yana maida kayan cikin drowa yace kinemi inda zakisa fitsararrun kayanki nan drowar chitti ne dan haka baki isa kicire mata kayanta aciki ba kuma I can't share my closet with u
Se alokacin tadago tana kallonsa da murmushi tace karfa kamanta nan gidana ne inada damar dazan ijiye kayana aduk inda nakeso
lokaci guda fuskarsa ta canza yana kallonta ko kiftawa ba yayi yajima ahaka sannan yariko kafadunta dakarfi cikin wata iriyar murya yace bansan meyasa kika yi hakan ba amma kisani ko kadan hakan bai bata min rai ba abunda yafiyi mani zafi shine karyar dakika mun cewa kina sona idan kudi kikeso ko nawa kika tambayeni ni mai iya bakine saboda kinfimun komai arayuwata ada amma ayanzu bakida wata kima a idona u can do what ever u wont with my money amma kisani ina nan dake sena kwato dukiyata ahannunki nan bada jimawa ba....yana kainan yasaketa yana daukan kayansa a drawer ya wuce daki
Durkushewa tayi awurin tana toshe bakinta dan kar kukan ya fita seda tayi mai isarta ganin lokaci yana tafiya yasa ta wuce bayi tayi wanka sannan ta dawo dressing room ta shirya cikin wasu riga da wandon bakake sannan tadoro jacket irin tajiya ruwan toka tayi rolling da karamin gyale shima ruwan toka se takalmin kafarta kalan gyalen tayi kyew matuka kamar bala rabiya tana fitowa AK yabita da kallo tundaga sama har kasa aransa yana fadin wai dama haka chitti tahadu bansaniba ganin tana kallona yasa yayi saurin kauda kai yana daure fuska
Dressing mirror tanufa tafeshe jikinta da turare sannan tazana light make up shap shap tagama tadauki jakarta sauri sauri tanufi hanyar fita tana duban agogon hannunta
dakallo yabita har tafita sannan yaci gaba da abunda yake yana fadin zamuga yanda zakiyi aikin yarinya tunda angayamaki make up ne dazaki iya koyanshi cikin wata daya
tana sakkowa kasa ta isko gaba daya mutanen gidan azaune apalo ana jajanta abunda yafaru jiya harda grany acikinsu
tana sakkowa suka hau daure fuska suna tabe baki
Ko kallonsu batayi ba tahau kwalama masu aiki kira dagudu suka karaso wurinta suna mika gaisuwa
kallonsu tayi dayan bayan daya sannan tace
Bakomai yasa nakiraku ba sedan insanardaku cewa daga yau aikinku ya kare anan gidan mungode da zaman mutuncin da mukayi da Ku abaya amma ayanzu bama bukatar yan aiki anan gidan
Dafe kirji dattijiwar cikinsu tayi tana langwabar dakai kamar zatayi kuka tace madam meyafaru idan wani laifi mukayi amana hakuri zamu gyara amma wannan aikin dashi muka dogara dan allah ataimaka
Murmushi tayi tana dafa kafadarta tace ba kuyi komai ba baba kawai dai lokaci ne dayakamata ace kuma kun huta
Check taciro acikin Jakarta ta bisu daya bayan daya ta mikamusu tana fadin ga wannan ya isheku Ku kama kowace irin Sana'a kukeso se kuje kuyi allah yabada sa'a sannan idan kuna bukatar wani taimako awurina to zaku iya zuwa kusameni akowane lokaci
washe baki suka hau yi cike dafarin ciki suna mata godiya
Mikewa mutanen gidan sukayi cike da mamki suna kallonta cikin daga murya inna ladidi tace to yanzu da kika kuresu uban wa zaiyi aikin gidan
Karasowa tayi dap da ita tana murmushi cikin sassanyar murya tace nanfa gidana ne ni nakeda ikon sawa ayi ko abari acikinsa ina ganin girmanki dan haka kija bakinki kiyi shiru
Juyowa tayi takalli aunty sadiya sannan tamaida kallonta kan inna ladidi tana fadin bakuyi tsofan dayakama ace kun daina aikin komai ba saboda haka kuzaku kula da tsabatce gidannan ciki da wajansa
Dariya akasa gaba daya palon ana kallonta dan su kallon mai tabin hankali suke mata
Itama murmushi tayi tana kallonsu sannan takarasa wurin aysha da sarah tana kallonsu tace munada tika tikan yan mata kamarku bama bukatar masu girki saboda haka daga yanzu kuzaku rika yin girkin safe da yamma saboda yanda kuke dayawa bazan iya cidaku so uku arana ba
Kallon juna sukayi sannan suka kalleta suna kwashewa da dariya
Banza tayi dasu tana kallon grany tace ke kuma grany.....
Bata karasaba inna ameena takatseta da fadin ita kuma me rashin imanin naki har yakai ki kalli girmanta kice zaki sakata aiki
Murmushi tayi tana kallonta tace to ai bakijira kinji mezan ceba ....
kallon grany tayi taci gaba dafadin dake da inna ameena zaku kula da bangarenku idan taga zata iya setayi gaba daya ke kuma ki huta amma yakamata ace kinadan aiki saboda motsa jiki yanada kyew
Wani dogon tsaki uncle jamilu yaja yana gyara zamansa kan kujera
Juyowa tayi tana kallonsa tace ohh uncle ashe kana nan nibanma ganka ba ai se yanzu
Kallon bashir tayi sannan tamaida kallonta kan jamilu tace uncle kaida bashir kuna wasa da aikinku sosai yanzu karfe Tara amma banga kunada niyyar zuwa office ba
Kallon agogon hannunta tayi sannan takallesu tace yanzu zan wuce office idan har narigaku zuwa to wallahi kunji narantse zan sallameku a aiki
Zaro ido sukayi suna kallonta amma basuga alaman wasa a tattare da ita ba
Juyawa tayi zata fita sukayi saurin mikewa atare suka wuceta har zasu fita tace yawwa bashir zonan dawowa yayi ya tsaya agabanta yakosa tafadi abunda zata fada ya taxi dan uncle jamilu tuni yafita
Makullin motarsa takarba tana fadin a wuri daya kuke aiki banga dalilin dazaisa Ku dauki motoci biyu kufita dasuba
Zaiyi magana tadaure fuska tana fadin nakune ?
Girgiza kai yayi yana fadin a'a nakine
baijira mezata ceba yafita aguje ya isko uncle jamilu har zai tada mota yabude gidan gaba yashiga
Juyowa yayi yana kallonsa fuska ahade cikin kakkausar murya yace kai miye haka
janyo sit belt yayi yadaura yana fadin kai dai uncle muje kawai zamma bayani ahanya
tsaki yayi yatada motar suka fita aguje kamar masu shirin barin garin
wayar Asma'u ce tayi ringing tana dagawa tace kazo ....to kashigo kawai
Dariya aysha tayi suka tafa da sarah tana fadin yau ni ke kallon film ganin idona
Dariya sarah tayi tace jifa wai mune zamuyi aiki base taganmu bama bare mu mata girki
Murmushin mugunta asma'u tayi tana kallon kofa tace gali shigo mana
😳😳😳😳😳
zaro ido sukayi atare suna kallon Wanda yashigo palon cikin shiga ta rashin mutunci kana ganinsa kaga dan kwaya ga idonnan yakade yayi ja fuska ahade ba alamar far'a ko wasa atare dashi
Cike da isa ya karaso palon kanshi Asama yana bin ko ina da kallo
Murmushi asma'u tayi tana kallon su sarah tace wannan shine zai rika kula da aikinku idan bakuyiba dan allah to zakuyi dan wuya
juyowa tayi tana kallon gali tace gali katabbatar komai yatafi daidai duk wacce tama rashin kunya acikinsu kanada damar hukunta ta wacce taga bazata iya ba kuma zata iya tafiya ba dole
dariyar mugunta yayi yana binsu da kallo yace angama hajiya nayi na banza ma bare inda za'a biyani ai karki damu kije kawai
Murmushi tayi tafita daga palon dagudu gudu tashiga motarta tafigeta aguje tafita daga gidan
ahanya bashir se ihu yakema uncle jamilu kan baya gudu tukin ma ashe bai iya ba
Sunzo daidai traffic light uncle jamilu ya juyo cike da takaici Kai kafa isheni fa dan ubanka wayace kabata makullin motarka idan kaga bazaka iya ba kafitarmun amota inyaso ni innaje inga inta isa takoreni aikin banza kai
Kauda kai bashir yayi yana zunbura baki bai kara magana ba har suka isa
suna fitowa daga motarsu motar asma'u tashigo companyn kusan tasu tayi parking tana fitowa takallesu tana murmushin gefe tace allah yaaa taimakeku
Tagefensu tawuce tana maida glasses dinta tasa kai cikin company
Da kallo bashir yabita har tayi nisa sannan ya jinginu da mota yana sauke ajiyar zuciya yace ohhh thank God
Wani banzan kallo uncle jamilu ya watsamai sannan ya wuce ciki yana Jan tsaki
[20/07, 18:48] Hassan Atk: Da daddare asma'u nadaki kan kujerar dake gefen gadonsu tana aiki a computer
AK yashigo dakin yana satar kallonta ya nufi kan gado ya kwanta
Har yarufa ya hango coffee dinsa dake kan bedside drawer
Kallon asma'u yayi aransa yana fadin grany batada lafiya kenan ita tayi wanann coffee din
tashi zaune yayi yajanyo flax din ya zuba a mug sannan ya gyara zamansa yana Satan kallonta yaga ko dagowa ma batayi barema tagansa
Kurban coffee din yayi ya furzar yana yamutsa fuska yace
Wannan wane kalan coffee ne...... koma waye ya hada bai iyaba .....kuma kar yakara hadamun dan ba kowane kalan kazanta nakesha ba
dagowa tayi takallesa sannan sadda kanta tace kaga idan kana son kanka to karkayi wasa da coffee dinnan
ada sau uku kake sha arana yanzu kuma ni nake saya da kudina dan haka nayi niyyar baka so daya arana idan kazubar da wannan to kaida wani kuma se gobe warahaka now it's up to u
wani malalacin murmushi yayi yace haba ai wannan fada kawai kike dan bakinki yasha iska amma ai kema kinsan baki isa ki hanani shan coffee agidannan ba
Ci gaba da aikinta tayi tana fadin muzuba mugani inace kap makullan ahannuna suke ko..... to sedai kaje kasha awaje amma banawa ba ....ko kasiyo grany tahadamaka .....wannan duk bai dameni ba
Ni yanzu kaina kawai nasani duk abunda zan karu dashi shizanyi kowa kuma yaji da matsalarsa
"To meyasa dazu kika shiga damuwa da kika ga grany akuance
"Saboda nasan kudi zan kashe wurin sayan maganinta shiyasa amma ba wai ainahin rashin lafiyarta bane yadameni ko kai dakaga nadamu akanka ba tausayi kabani ba kawai dai rigakafi namaka dan naga alama kaima kana shirin jamun wani kashin kudinne....shi yasa nabaka ruwan sanyi dan kar jininka ya hau
Shiru yayi yana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 35