tana kuka
bayanda baiyiba amma Sam taki yarda shiru yayi nadan lokaci sannan ahankali yakira sunanta cikin wata iriyar murya yace ASMA'U
seda taji gabanta yafadi dan har tamanta rabon dataji yakira sunanta dagowa tayi ahankali tana kallonsa carab suka hada ido lokaci guda taji tamanta ciwon dake kafarta
matso dafuskansa yayi dap datata har suna musayar nunfashi sannan yakai bayan hannunsa ahankali yashafo gefen fuskarta har zuwa lips dinta lokaci guda suna having eye contact
dayan hannunsa yakai ahankali kan kafarta yashafo tundaga kwabrinta harzuwa tafin kafarta sannan yazare kayar
Yar kara tasaki tana kankame hannunsa dakarfi
Murmushi yayi yaciro handkerchief a aljihunsa yadaure mata kafar yana fadin nafadamiki ki kula da inda kikesa kafarki kigodema allah ba maciji kika takaba
Sunkuy dakanta tayi kasa tanajin kunya takamata dan Sam batasan lokacinda yakai hannunsa wurin kayarba
dagata yayi tsaye yana fadin yawwa to tashi muga zaki iya takawa
Dingishi tafarayi tana langabe kai tace ABI mudan zauna muhuta mana
Girgiza kai yayi yace a'a chitti Hutu ba namu bane mutanan nan fa haryanzu suna binmu idan muka zauna anan kowane lokaci zasu iya iskomu
shiru tayi batace komai ba tana kallon kafarta dake zubarda jini
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: Dukawa yayi agabanta yana fadin haw ingoyaki
Dariya tayi tace goyofa inazaka iya goyona awannan halin
ganin dagaske yake yasa ta dane bayansa yagoyata sukaci gaba datafiya
Murmushi tayi tace ABI in tambayeka
"Ina jinki
"dawa dawa kayi missing acikin yan gida
Murmushi yayi cike dafarin ciki yace grany mana
"Uhm sewa?
"Se ahmad se inna ameena se inna se Umma se sarah se khadeeja se fa'iz se .......
Haka yayita jero yan gida ganin har yakai kan su amir yasa tace to banji kace aysha ba ?
dafe kai yayi yace ohhh namanta se aysha
Dariya tayi tace seda na tunamaka
Shiru yayi yana mamakin meyasa baya jin yayi kewar aysha ne shi har ma mantawa yake da ita
Murmushi yayi yace kema intambayeki
"Eh
Banda Umma da Abba da khadeeja dasauran yan gidanku wa kika fiso
Dariya tayi aranta tace kai nafiso ABI amma afili tace grany
"Se wa
"Se inna ameena
Shiru yayi nadan lokaci sannan ahankali yafurta sewa
"Se sarah ......
Haka tayita jerowa har akazo kan ahmad
alokacin AK yahasala jin bata ambaci sunansa ba sauketa yayi yana fadin sauakmmun abaya
Makalkaleshi tayi awuya tace haba ABI ban warkeba fa
Wucewa yayi yana fadin sedai kikira wa'yanda kike so su goyaki amma ni nagaji
Dariya tayi tabi bayansa tana dingishi har ta iskosa hannunta tadora kan kafadarsa suna tafiya tace wai fushi kayi ne to aini ban dauka harda mai tambayar ba
Daga kafada yayi yace meyasa zanyi fushi dama ai bance ki ambaci sunana ba
har wannan lokacin ahmad da yansanda nacikin dajin suna nemansu amma ko alamar su basu ganiba mutum biyu cikin yan sandan ne ma sukaga runfar su JJ da Inda aka daura yagiya ajikin bishiya nan take suka sanarda yan uwansu suka zo wurin
Da gudu Ahmad yakarasa wurin yarike yagiyar da hannunsa yana kallonta lokaci guda hawaye suka wankemai fuska
Dafashi dai daga cikin yan sandan yayi yana fadin kayi hakuri ahmad karkayi saurin karaya alamu sun nuna guduwa sukayi insha allahu ba abunda yasamesu muci gaba da nemansu
kiran grany yayi yagayamata su AK sun gudu daga hannun yan ta'addan amma har yanzu basu gansu ba
Cike da farin ciki tasanarda su Umma da sauran yan gida aka ci gaba da addu'a
da labari yasami aysha da jamilu ba karamin mamaki sukayi ba gashi suna kiran JJ basa samunsa sunkasa gane kan lamarin
suna cikin tafiya asman AK yatashi zo laga tashin hankali awurin Asma'u kamar zatayi hauka haka takeji
Tun yana tafiya ahankali har ya durkushe awurin yana nunfashi sama sama
durkusawa tayi kusa dashi cikin sheshshekar kuka tariko hannunsa tana fadin ABI meyake damunka ne dan allah karkamun haka ina zan sa kaina idan wani Abu yasameka kamanta kama Umma alkawarin zaka maidani gida ABI dan allah katashi
Damke hannunta yayi dakarfi yana kokowa da nunfashinsa cikin rawar murya yace chitti ru...wa .....ruwa...
Riko fuskansa tayi da hannu biyu cikin kuka tace ruwa kakeso ?
Kai yagayda mata yana runtse idanuwansa
kwantar dashi tayi awurin tana fadin to kuanta bari nakamaka ruwan kaji dan allah kajirani namaka alkawarin zan nemo maka ruwa
tashi tayi aguje tanufi cikin dajin Sam tama manta daciwon dake kafanta se jini yake amma bata San yanayiba
Tayi kusan awa daya tana yawo adajin taci kuka har tagaji tayi addu'a ba adadi da taimakon allah tahango wani dan karamin rafi da wata runfa akusa dashi da alama ta makiyaya ce
Aguje takarasa wurin tasamu wata yar roba tadibo ruwan aciki gashi roban afashe take se zuba ruwan yake hakannan dai tajuya aguje takoma tana bin sawunta inda tabiyo saboda jinin dake zuba dashi take gane hanyar databiyo
ahankali AK yafara bude idanuwansa har yagama bude idonsa saurin tashi yayi yana kallon gefensa baiganta ba azabure yamike yana kiran sunanta amma shiru
Nan take hankalinsa yatashi jinin dayagani akasa yafara bi yana kiran sunanta da kyar yake tafiya hannunsa daya akan kirjinsa yana ji kamar nunfashinsa zai dauke
Tundaga nesa ta tsinkayoshi yana tafiya aguje tanufi wurinsa tana kwala mashi kira da karfi ABIIIII
wani lallausan murmushi yasaki lokacinda ya hangota tana zuwa cikin karfin hali yakara saurin tafiyarsa har ya isa wurinta suka rungume juna dakarfin gaske kamar za'a rabasu
Cikin dasashshiyar muryansa da bata fita sosai yace chitti ina kikaje meyasa zaki tafi kibarni kin kwasan halin danashiga dana farka banganki ba
Kara shigewa jikinsa tayi cikin muryan kuka tace ABI I am sorry ruwa naje in kawomaka amma bazan kara tafiya inbarka ba I promise
sulalewa yayi awurin yana dafe kirjinsa
zaunawa tayi tana tallabosa tadora kansa saman cinyarta tana kokarin bashi ruwan amma yakasa sha
Se Jan nunfashi yake dakarfi kamar mai fitar rai
fashewa tayi dakuka tariko kansa tana fadin ABI katashi ga ruwan kasha naga wani waje acan wurin se muje muzauna kila musamu Wanda zai taimakemu
riko hannunta yayi yana murmushin wahala cikin rawar murya yace kukan me kike ba abunda zai sameni haka yakemun kidan jira anjima zai rage se mutafi amma kin tabbata ba gidan aljanu kika gano ba kuwa
Rungume kansa tayi akirjinta tana gashewa dawani irin kuka mai ban tawsayi sun jima ahaka kafin dakyar ta taimaka masa yatashi suka fara tafiya se jera mai sannu take har yagaji da amsawa
Koda suka isa wannan runfar yagama galabaita yar tabarmar datagani awurin tadauko tashinfida mai sannan ta taimaka mishi ya kwanta amma gaba daya tagama tsorata da halin dayake ciki
zama tayi akusa dashi tajanyo kansa tadora saman cinyarta tana shafa lallausan gashin kansa daya cukurkude kamar bashiba
Hannunta yakamo cikin rawar murya yace chitti I am sorry na yima Umma alkawarin zan maidaki gida amma inaga bazan iyaba I am dying saboda bantaba irin wannan ba
Fashewa tayi da kuka tana toshe mai baki tace a'a ABI dan allah kadaina fadan haka ba abunda zai sameka insha allahu kana son ruwa bari inje indibo maka
riko hannunta yayi yana tari hade da rintse ido cikin muryansa da bai fita yace a'a kibarshi banason ruwa kowane lokaci idan zanbaki hakuri akan wani abu bakyaso se kihanani ko kirufe mun baki
To yau kitsaya kiji mezan ce
Chitti nasan namiki laifi nabata miki rayuwarki na aureki badan allah ba bada kekkyewar niyya ba akan wata manufa tadaban banyi la'akari da makomar rayuwarki ba amatsayinki na ya mace
I am sorry chitti kiyi hakuri kiyafemun nasan ina damunki ina tsokanarki amma badan in bata miki rai nakeyiba sedan narage miki damuwar danajefaki aciki
Kuka take kamar ranta zaifita tama kasa magana se girgiza takai take tana kallonsa cike da tausayi tana ji dama itace ahalin dayake ciki da tafijin saukin radadin datakeji ahalin yanzu
hannunsa yasa akan bakinta yana fadin shshshsh
Kiyi shiru chitti kar wa innan samudawan su jimu
kinga ni tafiya zanyi nasan bazan iya cigaba ahaka ba kiyi kokari ki koma gida kinji kibama Umma hakuri kice nayi iya kokarina nakawoki amma nakasa kicema grany tayi hakuri kuma taringa shan maganinta akaikai ki kularmun da ita kinji nasan ke kadai ce zaki iya ga sarah nan itama ki kula da ita kinji kizabamata miji nagari Wanda yadace da ita kihadasu kinji nasan tanada taurin kai batajin magana amma tanada tausayi da saurin karaya ki koyar da ita halayanki masu kyew kinji
Murmushi yayi yanajin wani yanayi ajikinsa cikin dasashshiyar muryansa yaci gaba dafadin
Kicema inna ameena nace takoma wurin dan tsohonta tadaina takurama granyta kinji
Kicema aysha tayi hakuri nasan tanasona amma ina jamata lokaci naki aurenta kigayamata ina Neman albarkar grany akan duk abunda zanyi shiyasa ban aureta ba inaso se grany ta amince amma kice cikin samarinta tazabi Wanda yafi sonta aciki ta auresa
Khadeeja kuma kicemata nace takula da ahmad sosai tayimai biyayya tazauna dashi lafiya shima kice nace yariketa amana kar yacutar da ita
Kuma kicemasa karyayi wani aboki bayanni kinji idan yana bukatar wata shawara ko wani Abu yasameki kar ya yarda dakowa cikin abokananmu
Chitti kinada hali mai kyew kinda kirki kicigaba da haluri kinji idan namutu kar kizauna hakanan kisamu wani mutum nagari ki aureshi amma kar ki manta dani kinji ko
Rungumeshi tayi dakarfi tana sakin wani kuka mai cin rai tace ABI ya isa haka dan allah ba abunda zai sameka ABI katashi kaji tare zamu koma gida muci abincin grany mai dadi sannan inkamaka coffee dinka mai zafi kasha kaji ni bawanda zan aura ABI Kaine mijina dakai kadai zan rayu saboda kai nakeso I LOVE YOU!!!
dago fuskansa tayi tana kallonsa idonsa alumshe ba alaman nunfashi atare dashi atsorace tafara daddabashi tana kiran sunansa Amma shiru
Hannunta tasa tana bubbuga gefen fuskarsa cikin rawar murya tace a'a a'a ABI u can't do this to me dan allah katashi ABI idan kamutu ina zan sa raina wallahi nima mutuwa zanyi dan allah katashi ABI
Surutai kala kala take tana jijjigashi dakarfi amma shiru kakeji jadaba tafarayi tana toshe bakinta tajinginu da iccen runfar tana kallonsa se kuka take kamar ranta zai fita tajima ahaka can kuma tayunkura kamar antsikareta tanufosa da rarrafe tana kara kiran sunansa tafara danna mai kirji amma baimasan tanayiba
Sunkoyo dakanta tayi kan fuskarsa hawayenta na diga akan idonsa ahankali takai bakinta kan nasa tafara hura masa iska tajima tanayi amma taji shiru fadawa tayi kan jikinsa takara fashewa da kuka tana addu'ar allah yadauki ranta itama da wannan halin datake ciki
Kamar daga sama taji yafara tari kadan kadan saurin dagowa tayi cike dafarin ciki ta riko fuskarsa tana kiran sunansa
amma bai bude idoba kuma bai motsaba se nunfashinsa dake fita ahankali ""'"
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: surutai yaketayi shikadai jin shiru yasa yaduba gefensa amma baiganta awurin ba cike da mamaki yafara waige waige yana kiran sunanta
Can bakin wani shago yahangota tana daga mai hannu
Girgiza kai yayi yakarasa wurinta yana tambayar metake anan
Waya takarba ahannun mai shagon tamika mishi tana murmushi
saurin kai hannu yayi ya fizgi wayan yana dariya yace ohhh chitti gaskiya kin hadu bari mukira grany
Nunmaban grany yayi dialing seda takusa katsewa tadauka jikin asanyaye tayi sallama
Hannunsa yasa yatoshe bakinsa hawaye nazuba afuskansa tsabar farin cikin jin muryan grany dayayi yama kasa magana se mikama asma'u wayar yayi bayan yasa a handsfree
Har grany zata kashe wayar taji muryan asma'u na sallama
Zunbur tamike tsaye cike da farin ciki tana fadin wanake ji haka kamar asma'u
da mamki kowa yajiyo yana kallonta kowa yakosa yaji meyake faruwa ba
kallon kallon aka fara tsakanin aysha jamilu da kuma sadiya bakaramin tashin hankali suka Shiga ba jin an ambaci asma'u
Cikin rawar murya asma'u tace eh nice grany ya kuke ya ummata
Dariya grany tayi mai hade da kuka tafara kai kawo cikin palon tana fadin lafiryamu kalau asma'u Ku yakuke ina Abidi badai abunda suka muku ko
matsowa kusan wayan AK yayi cikin rawar murya yace grany!!!
dariya tayi mai dan sauti jin muryansa datayi batasan lokacinda hawaye ya wankemata fuska ba
"Abidi ya kake kuna ina ne
dariya yayi yana goge hawayen fuskarsa yace grany lafiyarmu kalau muna hanya yanzu zamuzo kigayama su Umma su....
Bai karasaba Asma'u taturo bakinta kusan wayar tana fadin grany yunwa mukeji kicema Umma tayimana kunun gyada ke kuma kiyimana tuwo inna ameena kuma tamana dambu yaji hanta sosai .....takarashe maganar tana lashe baki
ture kanta yayi yajuya mata baya yana fadin grany kihadamun coffee na mai zafi ki kara citta sosai saboda makogorona yabushe
Dariya grany take harda rike ciki rabonta da tayi farin ciki irin haka har ta manta
Kokowa suka farayi akan wayar kowa da abunda yakeso yafada seda katin ciki yakare sannan ya mikamata wayar yana fadin to ai gashi se kicinye ko duk awane cikin zaki saka abinci kala 7 oho
Kin karban wayar tayi takauda kai tana turo baki tace seda kacinyemasa katin se ka maida masa wayarsa
Juyowa yayi yana kallon mai shagon yana murmushin yake yace malan yi hakuri muncinye maka kati
Murmushi yayi yace ah ai ba komai dama nagayamata katin ba yawa
se alokacin asma'u tajiyo tana mai godiya sannan tace
dan uwa ina zamu samu motar dazata kaimu cikin garin abuja
dariya yayi yace to gaskiya yarinya sedai babbar motar dake kamana kaya idan kunaso yanzu se inrakaku muga in yayi lodi se yarage muku hanya
Juyowa sukayi suka kalli juna sannan AK yakallesa yana murmushi yace malan munaso sedai fa ba kudi ajikina ya za'ayi
fitowa yayi daga cikin shagon yanufi wata hanya yana fadin kuzo muguada sa'armu mugani amma gaskiya da kyar zai yarda dan bashida mutunci
Haka yayita musu surutu suna binsa abaya har suka isa wurin babbar motar da tacika makil da buhuhhuna
Sallama yama wani mutun yajiyo yana hura sigari batare da ya amsa sallamarsa ba yace ya akayi ne idan ma kayane kaje ba wuri se gobe....
dariya mai shagon yayi yana nuna su AK yace gali dama wa'innan bayin allah zaka taimakama ka rage musu hanya zuwa cikin gari
Juyowa yayi da jajayen idanuwansa yana binsu da kallo yace nima ai bawan allah ne nawa zasu biyani
Juayawa mai shagon yayi yakoma yana fadin gashinan kudaidaita zan koma nabar shago ba kowa
Kallon juna sukayi sannan asma'u ta sassauta murya tace gali taimakonmu zakayi ba ko kwandala ajinkinmu amma idan munje zamu biyaka konawa kakeso
Kallonsu yayi ya tintsire da dariya yana fadin yanmata kin ma rainamun hankali ki kalleni da kyew kinga nayi kama da Wanda zaku yawdara daganinku irin yarannan ne masu gudowa daga gidan iyayensu sushiga duniya ...
Yakarashe maganar yana zukan sigari yahura musu
Hannu AK yasa yana kabe hayakin sigarin yana yamutsa fuska yamatso kusan asma'u cikin rada yace chitti wannan dan jagaliyan yayi kama da dai daga cikin wa'inda suke binmu ko zamu hadashi da yan kauyan nan suci uba.....
Bai karasaba gali ya katseshi dafadin kai nifa tafiya zanyi kuna batamun lokaci idan bazaku ba gara ma kuware
tsaki AK yayi yana ji kamar ya haushi da duka
ganin zai shiga motar yasa asma'u tayi saurin riko hannun AK tana Nuna ma gali tace to ka rike wannan agogon jingina idan munje muka baka kudin seka bamu abunmu
Saurin kwace hannunsa yayi yana fadin ke bakida hankali ne kwasan tsadar wannan agogon zakice inba wannan dan ta'addan haka kawai
juyowa gali yayi afusace yanufo AK asma'u tayi saurin shiga gabansa tana basa hakuri sannan ta lallashi AK da kyar yaciro agogonsa taba gali
Sannan suka shiga gidan gaba suduka biyun yaja motar suka tafi
Fada akayi sosai tsakanin yaran JJ da yan sanda sedai bawanda aka kashe atsakaninsu kuma yaran JJ sunyi nasarar guduwa daga hannunsu guda daya suka kama JJ dakansa yaharbesa gudun kar yatona musu asiri
shidai ahmad damuwarsa su AK seyawo yake yana nemansu amma bai gansuba
Tuni grany tasanar dasu Umma wayar dasukayi dasu asma'u nan take gida yacika cike dafarin ciki kamar gidan bigi haka ake hidima kowa nakokarin girmusu abunda sukeso
Aysha jitake kamar tamutu dan bakin ciki ga wani bakon al'amari da yaziyar ceta na sauyin yanayin datake gani kwana biyu takasa fahimtar komai kuma taki zuwa asibiti saboda tana tsoron abunda result zainuna kar aje abunda take zargi yazama gaskiya
suna cikin tafiya AK se toshe hanci yake kamar zaiyi amai saboda saitin hamatan gali yake sedariya asma'u kemishi suna fira da gali shidai AK takaici ya isheshi ko magana bayason yi
Juyowa yayi yana kallon gali yace kai wai ina zaka saukemu
Baijiyo ya kallesa ba yace duk inda kakeso konan kace insauleka tsaba zan iya taka birki
tsaki AK yayi yace kai nafaga alama ka rainani dayawa bakasan koni wayeba ko?
dariya gali yayi yana kallon AK yace to waye kwa kai banda mutun dan uwana kuma dan kauye mai guduwa da budurwa
dariya asma'u tayi tana kallonsu batace komai ba
cike datakaici AK yace yanda make dinnan bansan ko kasan AK hausawee ba to nine
Baki bude gali ke kallonsa sannan ya kwashe da dariya harda dukewa yace kai amma guy dinnan ka rainamun hankali wai AK hausawee kodayake zaka iya fadan haka
Kaga nima akauyanmu salman khan ake kirana saboda yanda nake da kirar karfi
Dariya AK yayi har yana kuantoma asma'u yace wai salman khan amma wallahi zaginka sukayi baka saniba kuuuut
daure fuska gali yayi bai kara magana ba har suka iso inda zai saukesu sannan asma'u takarba wayansa takira driver tamai kuatancen inda suke
sun jima atsaye kafin kafin driver ya iso cike da fadin ciki suka rungume juna da AK yana mai barka
karban kudi yayi ahannun driver yamika ma gali yana kwace agogonsa daga hannunsa ya wuce mota
dariya gali yayi yana fadin eh dai jeka kana tunkaho da kudin budurwa gara ni gumina nakeci se gayu ba ko sisi
juyowa AK yayi ahasale yanufosa asma'u ta taresa tana dariya tama kasa magana
mota gali yashiga yana fadin hajiya allah kirabu dawannan yaron Sam Baku dace ba lashe money kawai
aguje AK yanufesa yayi saurin fadawa mota yatada yana daga ma asma'u hannu yayi gaba
Juyawa AK yayi yana watsamata harara yace to ai da kinbishi kuntafi tare kawai
Dariya take harda hawaye tanufi mota tashiga shima yashiga driver yaja suka tafi
suna shiga gari AK yafara washe baki yana kallon garin kamar dan kauye asma'u dai banda dariya ba abunda take yayi banza da ita kamar baisan tanayiba
kuantar dakansa yayi jikin kujera yana lumshe ido yace kai ba Inda yafi gida dadi
suna isowa gidan suka isko gaba daya mutanan gidan afilin gida ana jiransu kafin driver yagama parking suka fito aguje suka rungume juna se kukan farin ciki
Da kyar aka banbare khadeeja ajikin asma'u haka Umma da inna su grany ai ba amagana
Sunkusan awa daya ahaka kafin da kyar aka barsu suka karasa cikin gidan inda yasha gyara ba kadan ba se kanshin turaren wuta ke tashi ga kanshin girke girke kala kala
anan palon kasa suka zauna kan doguwar kujera sukasa grany atsakiya se Umma agefen AK inna kuma agefen asma'u khadeeja nazaune kan hannun kujera daga gefe se washe baki take
Kujeran kusa dasu kuma inna ameena ne da sarah dasu fa'iz se sauran mutane Abba kuma tundaga waje yakoma gida dan yaki shigowa ciki wai daga baya su samesa agida
tashi sukayi suka nufi dining kamar mayunwatan zakuna haka suka fara bude kuloli se dariya ake musu ko ajikinsu
Wayar khadeeja ce tayi kara tana dabuwa taga Tarzan cike da fadin ciki tadaga kiran tana fadin Tarzan albishirinka gasu amma sundawo suna gida yanzu haka
Dariya yayi yace dagaske kike to amma meyasa baki gayamun ba tun dazu ina cikin daji ina nemansu nayi fushi karki kara mun magana ....yana kai nan yakatse wayar yana murmushi cike dafarin ciki yakamo hanyar gida
abinci sukaci bana wasa ba seda sukayi tatil sannan suka dawo Palo aka ci gaba da fira
Ruwan dimi Umma tasa khadeeja takawo tagasa kafar asma'u lokaci guda suna basu labarin yanda abun ya kasance amma idan anzo wani wurin se suyi shiru suna sadda kai
tsakiyansu khadeeja tashigo cikin rada tace garama ku ijiye wannan kunyar agefe dan idan ahmad yadawo duk se kunbamu labarin abunda yafaru
kauda kai sukayi lokaci guda suka tuno abunda yafaru dazu
Saurin tashi AK yayi yana fadin ummm bari naje nayi wanka nagaji sosai
Dariya momy tayi tace ai gara kuje kuyi wankan kuhuta
Tashi su Umma sukayi suna musu sallama zasu tafi zunbur asma'u tamike tana fadin Umma Nima zanbiku muje
Kallonta sukayi da mamki inna tace jimun shashasha ina kuma zaki keda kika dawo yau kizauna kikula da mijinki bakya ganin yanda yadawo ne abun tausayi har kinfishi kumari da kyan gani
kallon juna sukayi da AK atare suka kauda kai yayi saurin wucewa bangarensa yana musu sallama
ba yanda batayiba amma sunki bari tabisu hakanan tahakura tazauna amma tana tunanin yadda zata kuana daki daya da AK dan se yanzu taji kunyarsa takamata
Shima haka abangarensa yana tunanin mezai cema asma'u idan takara gayamasa tana sonsa shi kunyarta ma yakeji yanzu yana tsaye apalo yana wannan tunanin yaji anturo kofa saurin juyawa yayi yana zaton itace jin muryan ahmad yasa ya juyowo dasauri suka rungume juna cike da farin ciki se dariya suke summa kasa magana
Sunjima ahaka sannan suka zauna kan kujera Ahmad yafara jera mai tambayoyi
Dafe kai yayi yace ohh ni wai yanzu sena kara maimaita labarin danabada dazu kaje wurin lhadeeja mana tagayamaka ai taji komai
Kauda yayi yana daure fuska yace banaso fada muke da ita nidai inzaka gayamun ka gayamun ai waka abakin mai ita tafi dadi
Gyara zama yayi yafara basa labarin abunda yafaru har wurinda suke zaune abakin rafi ya tambayi asma'u takosa taje gida ne...yana zuwa nan yayi shiru yana Sosa kai
Ahmad dayakashe kunne har da lumshe ido yana sauraronsa jin shiru yasa yabude idonsa yana fadin se tace me
Kauda kai AK yayi yana fadin se tace eh
jiyo dakansa ahmad yayi yana dariya yace ahh wallahi ban yardaba nasan bahaka tace wani Abu daban tafada gayamun metace u know I am ur friend naaaaa
Daure fuska AK yayi yana hararansa yace to kenan karya zan maka abunda tace kenan in kanaso inci gaba in bakaso kuma tashi katafi dama ni bacci nakeji
tashi ahmad yayi yana fadin bari inbarka ka huta amma kuma gobe ma ai zamuzo dole ma kubamu labarin abunda yafaru
tashi AK yayi ya wuce daki yana fadin kaida khadeeja dama jarida kukayi da yafiyemaku
dariya ahmad yayi yafita yana masa se dasafe
Haduwa sukayi da asma'u zatazo bangarensu tana ganinsa tajuya zata koma yayi saurin tarota yana dariya yace tsaya mana aunty munjima bamu haduba shine kuma kike guduna kamar kinga dodo
Washe baki tayi tana Sosa kai tafara kame kame
Dariya yayi yace karkidamu kitanadi amsoshin dazaki bamu gobe in allah yakaimu ina fata dai kin gayamasa kina sonsa dan har yanzu muna nan akan bakarmu indan baki gayamasa ba bazamuyi aure ba ....
Bata jira ya karasaba taruga aguje tashige bangarensu tana rufo kofar dakarfi
AK nazaune bakin gado yaji anturo kofa azabure ya kwanta yana tufa da bargo ya lumshe idanuwa kamar mai bacci
ahankali taturo kofar dakin tashigo tana lekensa
Ajiyar zuciya tasauke ganin yana bacci cikin sanda tawuce bathroom
Yana ganin tashiga yatashi zaune yajera pilullukan dasuke raba gadon tatsakiya sannan ya gyara kuanciyarsa yana lumshe ido
daren ranar aysha batayi bacci kuana tayi tana safa da marwa adakinta ga damuwar ta isheta ga batajin dadin jikinta ana gama sallar asuba tawuce asibiti bayan likita yadibi jininta yabama nurse tafita cikin minti 30 tadawo da result din yana dubawa yayi murmushi yace amm hajiya kinada aure ne ?
Kai tagirgiza mishi tana kafeshi da ido gabanta na dukan uku uku takosa taji mezai ce
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta yace idan bazaki damu ba inaso kidan kuanta anan zammiki scanning dan tabbatar da abunda kecikin result dinki
Gabanta ne yayi mummunar faduwa nan take idonta yaciko da kwallal jiki asanyaye tahau kan gadon duba marasa lafiya doctor yafara dubata
Yajima yana mata scanning din
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 35