kula da kanmu ai
Gyara zamanta tayi tana fadin ba inda zani se kungama kaidai sha kunun
Juyowa dakansa asma'u tayi takara kai kofin bakinsa tana murmushin mugunta
Ganin yakasa jure yajin kuma bayaso inna ameena tagani yasa yayi saurin tashi yabar wurin yana shakan iska yana fiddo harshe
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Cigaban 1⃣2⃣0⃣
tashi asma'u tayi tabishi tana dariya daki ta iskoshi zaune yana guma ruwan sanyi abakinsa
Dariya tayi tace ai shi dama ramin mugunta kamata yayi ka ginashi gajere gashi yanzu kai kafada ciki
Harara ya watsamata da ruwa abakinsa yace Gagagagagga
Dariya tayi har da rike ciki tace ni banajin mekake fadi amma bari nataimaka maka
Fita tayi ba adau lokaci ba tadawo da manja acikin dan karamin bowl yatsanta ta tsoma aciki tana fadin bude bakinka
Kauda kai yayi yana girgiza Kai
"Bude mana shafa maka zanyi zai rage maka zafin yajin
Ruwan bakinsa ya hadiye zaiyi magana ta tura yatsanta cikin bakinsa ta shafo man jan aciki
Saurin tashi yayi yanufi bayi yana yamutsa fuska
Fita tayi daga dakin tana dariya
Da daddare aka fara party kowa yazo cikin abokansu ahmad da kawayen khadeeja sarah senan nan take dabaki aysha ko haushi yagama cikata se masifa take tana hantarar kawayen khadeeja
apalon gidan ake komai wurin yayi haske kamar darana kowa naharkan gabansa ga daddadan sawti natashi khadeeja da ahmad sunyi matukar kyew kamar prince and princess se alokacin kowa ke ganin dacewarsu abokanansu se kodata suke suna fadin tafi ahmad kyew saura suga amaryar AK ita kuma yatake sunsan se tafi kanwarta kyew
AK nazaune adaki yana jiran asma'u
Can anjima tafito tana sanye da doguwar riga tasha katon gyalenta se kokowa take dashi
Tagumi yayi yana kallonta har zata fita tawaigo ganin bai tashi ba
tace muje mana ai nashirya
kallonta yayi sama da kasa yace muje ina ai da injera dake ahaka gara nazauna banje ko ina ba
dawowa tayi gaban dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta da mamaki tace me kuma nayi nifa nan karshen fitowata kenan
tasowa yayi yazo kusa da ita yana fadin wai ke chitti anya kwa a abuja nan aka haifeki yanzu saboda allah kodan yafa gyalen nan na yan mata baki iya ba allah inaga ko grany tafiki iya dawri mai kyew
Labace baki tayi kamar zatayi kuka tace to ni ban iyaba ya zanyi ka kira mun khadeeja to tamun
" ni kuma kawai se aganni nakira khadeeja wai zatama matata kwalliya haba chitti abokanaina zasu mun dariya
komawa tayi bakin gado tazauna tana fadin to shikenan tunda hakane ba inda zanje kawai katafi
Shuru yayi nadan lokaci kana yajanyo drowan dressing mirror din yana fadin badai akwai kayan kwalliyar ba zo kidanyi ko yayane mugani
Kin tashi tayi seda yajanyota ya zaunar da ita sannan yayi tsaye kusa da ita yana kallonta
Tureshi tayi daga wurin tana fadin to katafi bazan iya yi kana kallona ba
fita yayi daga dakin yana murmushi seda yadan jima sannan yaleka yana fadin wai haryanzu baki gama ba
juyowa tayi tana kallonsa yayi saurin ja dabaya yana salati yace chitti mezan gani haka to ai dawannan gara babu
muka fita haka ai watsewa za'ayi abamu waje ya salam!!!
Langwabar dakai tayi tace to ni gaskiya ban iyaba nama fasa fita kawai kacemusu bana jin dadi
Karasowa yayi wurinta yace je kiwanko fuskarki kizo namiki dakaina natabbata sena fiki iyawa
Tashi tayi tana dariya tanufi bayi tana fadin ashe kwa zamu kuana anan bamu gama ba
tana shiga bayi ya fiffito dakayan kwalliyar yana karanta yanda ake anfani dasu koda tafito yagama tsab yaware wanda zai bukata gefe guda tana zama ya nannande hannun rigarsa ya shigayimata simple make up yana yi tana mai dariya bayan yagama da fuska yakoma bayanta ya warware ribbon din data daure gashinta dashi kallonta yayi tajikin mirror yace chitti umma bafulatana ce ko buzuwa
Dariya tayi tace bakatapiya ce
Shima dariyar yayi yagyara gashin yamata parking mai kyew sannan yagyara mata gyalen
ba'adau lokaciba yagama yana murmushi yace to duba kiga
Mamaki tayi bakadan ba ganin yadda tacanza lokaci guda la lips din nan sunsha janbaki tayi kyew bakadan ba
Juyowa tayi tana kallonsa da mamaki tace ABI dama ka iya ne
girgiza mata kai yayi yamikar da ita yana fadin bantaba yiba se akanki yanzu muje kinga ahmad najirana amma dan allah bakinki alekum nasan ki talkative ce saura kigayama khadeeja ni namiki kwalliyar mushiga uku
suna fitowa kallo yakoma Kansu nan take aka hau tapi ana shewa da gudu khadeeja tazo tarungume asma'u tana dariya tace ammah kinganki kuwa gaskiya yau kinyi kyew bakadan ba
Juyowa tayi takalli AK sukama juna murmushi janta gefe khadeeja tayi tana fadin ammah zo gayamun miye sirrin nidai nasan baki iya make up ba
Hannaye taware tana fadin bansaniba ba
Khadeeja zatayi wata maganar ta kwace hannunta tabar wajan tana murmushi
Da kallo tabita tana fadin this is the beginning of ur love story sis
Karasowa ahmad yayi kusanta yana fadin deeja kina ganin abunda nake gani kuwa
Dariya tayi tace ohh ni tarzan ashe kaima ka iya gulma
Dariya yayi yace deeja asma'u da AK sun bala'in haduwa
"wallahi inama suna son junansu dase sunfi kyew
"Zama suso ne ai naga andawko hanya
tunda suka fara magana sarah ke kallonsu tana sharan kwalla kusa da ita aysha tamatso tana fadin sarah wai meyake damunki ne ni nasan wallahi karya kike kice kin hakura da ahmad yanzu gashi kinkasa juran ganinsu tare bare kuma ace sunyi aure
Barin wurin tayi batare datace mata komai ba
Khadeeja da ahmad sunzo wucewa kan stairs kenan kawai taji anturata dakarfi zata fadi kasa ahmad yayi saurin janyota tafado kansa da gudu asma'u da fa'iz suka karasa wurinsu suna tambayar lafiya
Rike kanta tayi tana runtse ido arude ahmad yadauketa yakaita bangaren AK
Kan 3sitter yakwantar da ita yana tambayar bataji ciwo ba
Dafe kanta tayi tana kallon asma'u tace ammah ba faduwa naje yiba turani akayi
Damamaki suka kalleta suna fadin turawa fa khadeeja to wa zai turaki
Murmushin takaici fa'iz yayi yana kauda kai yace ya wuce wannan busassar yarinyar aysha ai naga lokacinda tabi bayan Ku dazaku haura sama
azabure ahmad yamike zaifita asma'u tarikoshi tana fadin a'a ahmad barshi kawai zanmata magana dakaina ba laille ne yakasance ita bace saboda banga dalilin dazaisa tanemi hallaka khadeeja ba
girgiza kai ahmad yayi yace ammah bakisan suwaye wa innan matan ba zasu iya yin komai wayasani ko tana taya sarah kishine nasanta bata da mutunci
aysha ce tasigo dakin sarah tana tafa hannu tace Weldon sarah nice try natabbata nan gaba bazakiyi kuskure wajan aikata lahira ba
damamaki sarah tajiyo tana kallonta tace kamar ya ban...gane ...akan wa kike magana ba
Dariya aysha tayi tana zama kan kujera tadaura kafa daya kan daya tace sarah karki manta da aysha kike magana ba AK ko asma'u dazaki iya deceiving ba ko kinaso kicemun bake kika turo khadeeja daga sama ba
Shiru Sarah tayi tana kauda kai da hawaye a fuskanta
murmushi aysha tayi tace karkice mun a'a saboda da idona naga lokacinda kika turata kuma naga lokacinda kika zuba wani Abu a jus dazu kika bama nura yakai mata amma kafin yakai glass din yafadi yafashe kinji haushi har kika mareshi daga nan nafara samiki ido dan nasan dole akwai abunda kike shiryawa
sarah nasanki kamar yunwar cikina I know u will never change for good
Saitin window sarah takarasa ta tsaya tana kallon waje cikin muryar takaici tace
Kwata kwata yaushe tashigo rayuwarsa wacece asma'u bare wata kanwarta lokaci guda yamanta ni kanwarsa ce ya dauki farin cikina yadanka ma wata baare
Hawayen fuskarta tashare tana cije lebe tacigaba dafadin
sunyi wawta dasuka yarda cewa wai ni sarah nacanza
Dariyar keta tayi tajuyo tana kallon aysha tace banso kowa yasan abunda nake shiryawa ba amma bakomai tunda kece kika gani ba wani ba aysha ina ma ahmad sonda ni kaina bansan yanda zan fadeshiba
Tunda AK yariga ya yanke cewa Ahmad zai auri khadeeja to tabass zai aureta
amma kuma ai setana raye zai aureta ko idan har nacigaba da nuna adawata akansu to dazaran wani Abu ya sameta ni za'afara zargi shiyasa nafito dawannan hanyar
Nuna kanta tayi dayatsa tace idan har ni sarah ban auri ahmad to ba wacce ta isa ta aureshi
sedai idan bana nunfashi adoron kasa
asma'u ce taturo kofa tashigo sauri juyawa sukayi suna kallonta
Murmushi sarah tayi tace ohh hello sister karaso mana
Karasowa asma'u tayi fuska ahade tace nasan cewa faduwar khadeeja ba haka kawai bane someone is behind it
atsorace suka kalli juna sannan sarah takalli asma'u da damuwa tace to waye zai yi kokarin cutar da khadeeja akan wane dalili
kallon aysha asma'u tayi tana fadin aysha ce ta turata dalilin kuma shinazo inji daga gareta
Azabure aysha tamike tana fadin what nonsense
alama sarah tamata datayi shiru sannan takalli asma'u tace kintabbata itace ?
"To waye zaiyi hakan inba itaba
Juyowa sarh tayi tana kallon aysha cikin daga murya tace how dare u
akan wane dalili zaki aikata wannan shirmen idan ma kina tunanin kishi kike tayi to u are westing ur time saboda ni khadeeja matsayin kanwa nadauketa idan kika kara aikata makamancin wannan to ba abunda zai hana namikaki ga police
Kasheta kike so kiyi
baki bude aysha ke kallonta cike da takaici tama kasa magana
dafa sarah asma'u tayi tana murmushi tace kibarta kawai sarah basai takai ga police ba mutuncin gidan nan ne zai zube
sannan tajuyo tana kallon aysha tace wannan yazama na farko kuma nakarshe idan kika kuskura kikayi na biyu to ina tabbatar maki cewa u won't get another chance to do the last one
Tana kainan tafita tana banko kofar dakarfi
juyowa aysha tayi tana kallon sarah da mamaki tace miye haka kikayi akan me zaki dawra mun alifin da ba ninayi
ba
Zama sarah tayi kan kujera tana dafe goshi tace I am seeking tried of this girl wallahi ba karamin dakewa nakeba kafin natsaya agabanta ina mata magana
jdagowa tayi takalli aysha tace wai yakukayi da AK ne akan zancan barinta gidannan meyake jira da ita
tsaki ausha tayi tana zaunawa bakin gado tace na tambayeshi yatsaya mun kame kame wai muduba grany..... batada lafiya .....yana bukatr hujja kafin yasaketa
dariyar mugunta sarah tayi tana kuantar dakanta kan kujera tace hujja ko ???
To ni zan bashi hujja just wait and see
grany ce kawai zata bani matsala
Cike da farin ciki aysha tace idan ma grany ne bakida matsala saboda naji tace gobe zasuje Kaduna itada inna ameena amma kuana 2 kawai zasuyi
Murmushin mugunta sarah tayi tace good
Ina wannan Alin cousin dinta dakika ce yana damunki awaya
yamutsa fuska aysha tayi tace yana nan miye
Tashi tayi tafita tana fadin ki tabbata kunyi fira mai dadi dashi ayaw har ya yarda cewa kin amince dashi gobe zan gayamaki sauran plan din
Dakallo aysha tabita tana murmushi har tafita sannan takuanta tana fadin bakida kyew sarah ni kuma zanci gaba da binki ahaka har nacimma burina na auren AK daga nan kuma I will show u the worst part of me
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na(Maryam Mhd)
1⃣2⃣5⃣
Washegari dasafe sarah ta isko asma'u apalo kusa da ita tazauna tace sister dan allah wata alfarma nakeso kimun
murmushi asma'u tayi tace ina jinki menene
Rada tamata akunne asma'u tayi murshi tace OK badamuwa amma mezai hana kigayama AK ainasan bazai hana ba
Rungumeta tayi tace thank u sister amma banaso Yaya yasani nafiso semun daidaita tukunna
tashi asma'u tayi tanufi kitchen tana fadin to bari nadora yanzu kar yazo bamu gamaba
tana tashi aysha tazo tazauna kusan sarah tana fadin wow good acthing sarah naga kamar ta yarda ko?
"eh amma ina fata dai kinyi abunda nace
Nuna mata wayar ta tayi tana fadin kalla kiga garan har ya amince shima naga alama kamar dan hannu ne har da fadin wai inaga ba matsala idan yazo badasanin AK ba
Dariya sarah tayi suka tafa
Kowa nazaune apalo grany suka fito cikin shirin tafiya AK yayi jigum kamar zaiyi kuka se tsokanarsa asma'u keyi tana dariya
Amir yaron inna ladidi se yawo yake da camera ahannunsa yana musu video
Tashi sukayi gaba daya zasu raka grany airport ganin asma'u batada niyyar tafiya yasa AK yace chitti muje mana
Langwabar dakai tayi tace ABI kuje kawai banajin dadi bazan samu damar zuwaba
kureta yayi da ido nadan lokaci sannan yace anya kuwaaaa ni banga kinyi kama damara lafiya ba
Jan hannunshi sarah tayi tana fadin Yaya muje mana tace batajin dadi dolene
Sallama suka mata suka tafi bayan kowa yashiga mota suntafi aka bar aysha da sarh atsaye jikin motarsu kamar zasu shiga suna ganin kowa yatafi sarah taja hannun aysha suka koma ciki suka labe awani daki batare da asma'u tagansu ba cikin rada sarah tace aysha kintabbata zaizo kuwa
"eh mana yacemun yana hanya fatana dai kawai AK yadawo kar yakwapsa mana
"Karki damu nasan zai dawo
Suna nan atsaye Sega Ali ya shigo gidan se shan kanshi yake yana shafa saje
Dariya sukayi suka tafa hannu
kiran aysha yayi awaya tadauka cikin muryanta mai jan hankali tace sweetheart ka iso
"eh baby kina ina ne nakosa naganki
danni inba naganki akusa dani ba bazan yarda wai dagaske bane
Tabe baki tayi tace I am in my room can u meet me there
" tsalle yadaka yana cije yatsa yace why not baby just tell me where is the room
dariya tayi suka tafa da sarah sannan tamai kuatancen dakin su asma'u tace yasameta acan
Dakallo suka bisa har ya haura sama sannan suka fito suka shiga dakin aysha sarah tace idan muka tabbatar yashiga se murufe kofar kinga idan AK yadawo ba abunda zai hana yagansu tare daga nan kuma .....
Kinsan sauran
ahankali yatura kofar yashiga sedai yaga bakowa adakin zai juya kenan yaji motsi a dressing room
Komawa yayi ya kuanta kan gado yana fadin come out baby i can't wait to see u!!!!
asma'u na dressing room tana sa kaya batasan meke faruwa ba tana fitowa tagansa rigingine kan gado
cak ta tsaya tana kallonsa kamar amafarki tama kasa tantance mafarki takene ko gaske Alin datasani ne ko maikama dashi daga ina yake meyakawosa dakinta
tana nan tsaye taji anturo kofa atsorace suka kalli kofar suduka
Nunfashinta ne yakusa daukewa ganin AK tsaye bakin kofa kamar gunki se rawa jikinsa keyi ga idonsa daya rikide yayi ja kamar gawta
sorry.....
Yafada cikin wata iriyar murya yana barin dakin dakyer yake tafiya danwani jiri ne ke dibarsa
wasu zafafan hawayene suka zuboma asma'u cikin rawar murya tace Ali meyakawoka dakina mekakeyi anan Ali wannan wane kalan tumasanci ne kayi haka
atsorace yamike tsaye yana fadin asma'u mekike nufi kar kicemun nan dakinkine nashigo dan allah
Girgiza kai tayi tafita daga dakin tana sharan kwalla
apalon kasa ta isko AK azaune yadafe kai matsowa tayi kusansa adan tsorace tace ABI I....
Dakatar da ita yayi tahanyar daga mata hannu yace no don't say anything
Saboda komai zaki fada bazai maki anfani ba chitti u why ..........just leave
Juyawa tayi tana fashewa da kuka
karo sukaci da Ali yana sakkowa zaiyi magana tadakatar dashi cikin rawar murya tace
Bansan meyasa kayi hakan ba amma kasani idan har wani Abu yasami aurena I won't spare u
tana kainan tawuce da gudu tashige bangaresu
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: bayanda batayi da AK ba akan ya yarda da ita amma yaki cikin sheshshekar kuka tace ABI wai me kadaukeni ne
Taya kake tunanin zan aikata abunda tun ina gidanmu banyishi ba se yanzu dayagiyar aure ta haw kaina why will I do that
Dagowa yayi yana kallonta da jajayen idanuwansa cikin kakkawsar murya yace ni ne zantambayeki mekika daukeni asma'u da ace bani naganku da idona ba wani yagayamun dabazan taba yarda dashiba amma kinbani mamaki bansan dalilin dayasa kika kasance haka ba amma kisani na ysaneki banason ganin fuskar ki kije.....
atsorace takai hannu ta toshe mai baki cikin tsananin kuka tace a'a a'a ABI dan allah karkamun haka
katausayama ummata wallahi zata iya rasa ranta
ABI kayarda dani wallahi bantaba aikata irin wannan kazamin aikin ba bansan meyakawoshi dakina ba I am confuse ni kaina bansan meyake faruwa ba
Bige hannunta yayi daga kan bakinsa ya mike tsaye yana juya mata baya yace
Sanin kanki ne cewa koda ina sonki bazan iya cigaba dazama dakeba karma kiyi tunanin kishinki nake a'a kawai ina takaicin yanda kika ari rigar mutunci kike aikata abunda kikaso kowane mai laifi daya musanta lafinsa yana bukatar abashi dama yagabatar da shaida
Juyowa yayi yana kallonta yace to nima zan baki dama just 24 hours kikamun wata shaida dazata nuna baki aikata abunda nake zarginki akai ba yana kainan yaraba tagefenta yawuce yana fadin karki manta awa 24 kawai nabaki idan har suka cika baki kawomun shaida ba to karma kijira se nakoreki dakaina dan bazaki ji dadi ba
Dakallo tabisa har yabacemata sannan takuantar dakanta kan kujera tana rera dan marayan kukanta mai ban tausayi
sarah dake labe tana lekenta ta wuce daki tana kwashewa da dariyar mugunta seda tayi mai Isarta sannan aysha tace sarah nifa binki kawai nake a plan dinnan amma bangane Kansa ba
Dariya tayi tana zama kan kujera seda tajima tana dariyar keta sannan tanatsu tafara magana kamar haka
idan baki manta ba kintaba gayamun cewa kinji lokacinda asma'u ke ba AK labarin wannan Alin yaso ya aureta which means tsohon saurayinta ne
Su maza suna wani hali Wanda koda basa son mace to dazaran andaura musu aure da ita zakiga suna kishinta
Shikuma kishi yana daga cikin abubuwan dakesa maza saurin sakin mace musamman irin wannan
Nabukaci dakija hankalin Ali ajiya saboda inaso ya yarda cewa kinasonsa dan musamu yamana aiki cikin sauki
danatabbatr ya amince zai zo yau to se nafara tunanin hanyar dazanbi nahana asma'u fita raka grany batare dakowa yasan ni nahanata ba
Shiyasa naje nasameta dacewa akwai wani saurayina dazaizo yau kuma banaso kowa yasan dazuwansa inaso tazauna mumasa girki dasauran su ba bata lokaci ta amince
lakacinda taki tafiya raka grany nahango rashin yarda da ita karara a fuskan AK kuma hakan shiya taimaka aikina yazo dasauki
Bayan Ali yazo muka turashi dakin asma'u naso ace munje munkulle kofar dakin sekowa yadawo ya iskosu tare bansan meyadawo da AK dawuriba amma duk dahaka komai ya je daidai
Dariya aysha tayi tana tafa hannu ta jinjina ma Sarah sannan tace to ya ake ciki yasaketa ne
girgiza kai tayi hade da tashi tafara kaikawo adakin tana fadin baisaketa ba bansan meyasa yake tausaya ma wannan ummar tata ba
yabukaci takawomai shaidar dazata wanketa amma nasan ko mezatayi bazata taba samun shaida ba ina mai tabbatar miki dacewa nan da gobe dole tabar gidannan daga nan kuma senaji da khadeeja
dariya aysha tayi cike dafarin ciki aranta tana fadin Weldon sarah kinmaida mun aikina mai sauki batare Dana wahala ba
AK yana fita wurin ahmad yanufa yazayyane masa kap abunda yafaru har lokacinda yabama asma'u
damamaki ahmad ke kallonsa har yagama bashin labarin sannan yamike cike da takaici yace AK badai kana nufin kayarda asma'u zata aikata abunda kake zarginta dashiba bansan wacece itaba amma I am 100% sure bazata taba aikata haka ba
"oh to zanmata karyane ko kuma ni makaho ne incemaka da idona nagansa haba ahmad
adakina fa nagansa akan gadona she was standing there looking at him kuma kacemun wai bazatayi hakan ba
To gayamun meyakaishi dakina meyake akan gadona idan ziyara yakamata meyasa basu zauna apalo ba haba ahmad nifa ba sakarai bane
ajiyar zuciya ahmad yasauke yana zama kusa da AK cikin sassanyar murya yace
inaganin kamar dama yayi hakan dawata manufa ne maybe yanajin haushin auren datayi ne.... ko kuma har yanzu yana sonta ...badai banza ba AK amma baikamata kazargi asma'u ba tunda baka kamasu suna aikata hakan ba in fact bama wuri daya kagansu azaune ba so u have no right to accuse her
girgiza kai AK yayi yana dafe goshi yace ahmad bazaka gane bane saboda bakai ne ahalin danake ciki ba
Murmushi ahmad yayi yace are u jealous
"No I am not kawai dai ina kokarin kare mutuncina ne
Daddare asma'u tashigo dakinsu sedai cak tatsaya tana kallon yanda AK yayi watsi dakomai nadakin gabadaya yabirkita dakin bedsheets da pililluka duk yawatsar dasu gefe
Azaune tagangosa kan kujera yakuantar dakansa idonsa alumshe kamar mai bacci amma yana shafa goshinsa ahankali
adan tsorace take takunta har ta isa kusansa cikin rawar murya tace ABI are alright ?
azabure yamike yana damko kafadunta dakarfi seda nunfashinta yakusa daukewa saboda tsoro
matseta yayi jikin bango har tana jin bugun zuciyarsa
Hannunsa daya yasa ya damko kugunta yamatseta dajikinshi dayan hannun kuma ya zagayo dashi bayan wuyanta
Nan take jikinta yafara rawa muryanta har rawa take saboda tsoro
Kokarin kwace kanta tafarayi tana fadin ABI what are u doing let go of me please
Bakinsa yakai saitin kunnenta cikin rada yace meyasa zan kyaleki .....niba mijinki bane....tunda har zaki iya bari wani yatabaki why not me.....I see u can feel my touch why don't u like it
Tureshi tayi tana shigewa dressing room ta fashe dawani irin kuka mai cin rai
tajima tana kukan secan cikin dare tafito amma bataga kowa adakin ba ahankali ta tura kofa taleka Palo
Kuance tahangosa kan 3sitter da alama ba bacci yakeba dan har yanzu yana murza goshinsa
Komawa tayi tafara tattare dakin kamar wacce aka zarewa lakka banda kuka ba abunda take
bayan tagama tazauna abakin gado tana rungume pilo jin kanta take awani irin yanayi datakasa banbance wane iri ne tarasa meyasa take fargaban rabuwa da AK kuma tasan hakan yazama dole tunda batada wata shaidar dazata gabatar mashi dazai hana yasaketa gobe
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣3⃣0⃣
daren ranar haka asma'u tayishi banda kuka ba abunda take har garin allah yawaye idanuwanta sun kunbura sunyi ja
lokaci guda har tarame
bangaren Ali ma haka yawuni ya kuana cike da damuwar rashin sanin halin da asma'u keciki gashi tunjiya yakeso yagayama AK gaskiyar abunda yafaru amma yaki sauraronsa
har saida su inna suka fahimci akwai abunda kedamunsa ba tambayar dabasu masa ba amma yaki yace komai
kasa hakuri yayi safiya tayi ana gama sallar asuba yanufi gidansu asma'u
haduwa yayi da AK yafito daga masallaci yana ganinsa yakauda kai kamar bai gansa ba
yana kokarin shiga gida yayi saurin shan gabanshi yana hada hannayensa yace AK dan allah katsaya ka saurareni tun jiya nake bibiyanka kabani dama nama bayanin gaskiyar lamarinnan
dagowa yayi yana kallonsa da rinannun idanuwansa cikin murya mai kaman rada yace
mezaka gayamun Ali wane bayanine zakamun Wanda ban saniba darajar su inna kakeci narufama asiri amma idan katakuramun wallahi se Insa adaureka ...
yana kainan yayi gaba yabarsa atsaye yana binsa dakallo
Yajima atsaye yana kallon get din gidan jiyake kamar yashiga yaga halin da asma'u take ciki amma yana tsoron abunda zai biyo baya hakanan yahakura ya juya yana takaicin abunda ya aikata
yana isa gida yakira khadeeja tasamesa afilin gida damamaki tace Ali lafiya wai meyake damunka ne
shakan iska yayi yafurzar sannan yace deeja yau kunyi waya da asma'u ?
girgiza kai tayi tana fadin a'a lafiya
"I don't know amma dan allah idan bakya komai kidan lekata mana kiga yatake
matsawa tayi kusa dashi tana fadin Ali bangane naje nadubata ba meyasameta
zaiyi magana kenan sukaji anturo kofa atare suka juya ganin asma'u yasa khadeeja tayi saurin isa wurinta cike da damuwa take kallonta tace ammah meyasameki yanaganki haka bakida lafiya ne
Karasowa wurinta Ali yayi cikin rawar murya yace asma'u are u ok ina kiran wayarki kinki dagawa I was so worried ina fata dai ba....
bai karasa ba yaji saukan lafiyayyen marin dayahanasa karasa magamarsa
atsorace khadeeja tadafe kuncinta dan yanda taji marin bazata tadauka ita aka mara
cin kwalar shi asma'u tayi cikin sheshshekar kuka tace Ali menamaka zaka mun haka meyasa tunda baka shafamun bakin painti ba seda nayi aure meyasa.....
Takarashe maganar tana sulalewa akasa tadora kanta akan kafarsa tana fashewa dawani irin kuka mai ban tausayi
lokaci guda itama khadeeja tafara kukan durkusawa tayi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 35