Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya kwace yafara shafa ma kansa bathroom tawuce tayi shirin kwanciya cikin kayan baccinta wando da riga mai dogon hannu Bayan tagama tafito yana kuance kan gado yarufa da bargo Tsaye tayi daga gefe tana kallonsa idonsa arufe amma da alamun damuwa afuskansa kamar daga sama taji yace Malama idan abun kallo kike nema ga TV can ki kunna stop staring at me Saurin barin wurin tayi tanufi bookshelf( drowan litattafai) din dake jikin bangon dakin daga gefe tana fadin ina ai ni bana kallo da daddare sedai nayi karatu Wani storybook tadauko tadawo kan stool tazauna tafara karantawa afili sedaga baya tagane tatsuniyoyin naban tsoro ne Shiru AK yayi yana kara cusa kansa cikin bargo Kallonsa take tana kunshe dariyarta tacigaba da karantawa cikin muryan ban tsoro tace Dazaran yamma tayi se kowa ya kulle kofarsa saboda wannan aljanan tana yawo cikin dare duk Wanda tahadu dashi to yagama yawo Wannan tsohon yana kuance cikin dakinsa yalulluba dabargo yana karkarwa gashi garin ana wata irin iska mai karfi kamar daga sama yaji ana bugamasa kofa dakarfi ..... Daidai nan grany ta aiko Rebeka da wayan asma'u takamata kawai sukaji bugun kofa atsorace AK yafito dakansa daga cikin bargo yana kallon asma'u itama adan tsoracen take kallonsa atare suka juya suna kallon kofa Dariya asma'u tayi tana kallon AK tace wai yanaga kamar katsorata ne to bari na aje Daure fuska yayi yana gyara kuanciyarsa yace tsoron me zanji awannen shirmen cigaba tayi dakarantawa ... atsorace tsohon nan yatashi zaune jikinshi narawa jin ba akara buga kofan ba yasa yakoma yakuanta can anjima yakara jin anbuga kofar dakarfi .... daidai nan Rebeka takara kuankuasa kofar Wannan karon gaba dayan su sunkasa boye tsoronsu kallon AK tayi tana hadiye yawu tace ABI kaima kaji buga kofar koni kadai keji tashi zaune yayi yana fadin naji mana to amma waye zaizo awannan Daren Jin shiru ba abude ba yasa rabeka tatura kofar ahankali ta ijiye wayar kusan TV tafita ai sunaji anbude kofa asma'u tadaka tsalle tafada kan AK atsorace yaja bargon yarufesu tana kankame dashi har suna musayar nunfashi cikin rada yace inajin motsi anan dakin Itama cikin rada tace banan dakin bane Palo ne kuma kamar anfita muje muduba Ahankali yafito dakansa daga cikin bargon yana bin dakin dakallo ganin bakowa yasa ya sauko ahankali daga kan gadon Itama tasauko suka nufi kofa turata yayi gaba yakoma baya yana fadin lady first Saurin dawowa baya tayi tana fadin to ai kai namiji ne kamata yayi ma kace inzauna kaje kaduba Wata wahalalliyar dariya yana kara turata gaba yace to ai saboda naga yawanci nabaya akafi fara cabkewa shiyasa nasaki gaba wata zungureriyar kwalba tadauka tarike ahannunta dayan kuma tana bude kofar dashi seda suka dudduba ko ina bakowa sannan taga wayarta akan table Ijiye kwalban tayi tadauki wayarta tana kallon AK tace kamar wayata aka kawofa Murmushin yake yayi yana waskewa yace dama ai nasan ba komai kawai ina gwadaki ne naga ko kinada tsoro ashe ke matsoraciya ce kallon ka rainamun hankali take mai seda yagama sannan tasaki yar kara atsorace tana nuna bayansa Haba lokaci guda yadaka tsalle se gashi agabanta Dariya tafara mishi harda rike ciki tawuce daki Binbayanta yayi yana murmushi Suna shiga daki yadauke blanket dinta daga kasa yadora kan gado daukan blanket din tayi tana fadin miye haka malan kwace blanket din yayi yadora kan gado yace nan zaki kuana yau kina tare mun hanya idan natashi dasafe buga kafa tafarayi dakasa tana fadin ni gaskiya ban yardaba daacan bakace haka ba seyau dakake jin tsoro pilulluka yajera atsakiyar gadon ya kuanta yana fadin ga wurinkinan ki kuanta idan ma kina tunanin wuri daya nakeso mukuana Kuma kika ki allah gobe zan gayama grany gaskiya akan aurenmu zagayawa tayi takuanta tana zunbura baki Murmushi yayi yana Jan bargo yajiyo yana kallonta yace chitti Kyaleni..... Tafada tana juya baya [19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚 👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧 Na( *Maryam Mhd*) 1⃣1⃣5⃣ Gyara zamansa yayi yana kallonta dakyew yace aysha ni nakasa gane wannan lamari abun yadaina bani mamaki yafara bani tsoro tunda naga AK ya yima sarah haka akan yarinyarnan to tabbas akwai wani Abu atsakaninsu sadiya tace nima dai haka nagani Abba aysha halin da namiji ne bakisani ba yarinya kar azo garin kallon ruwa kwado yamana kafa tanadin da mukayi shekara da shekaru yazo yaruguje mana muzama yan kallo Dariya aysha tayi tana tafa hannu tace kai wallahi kun ban dariya ai wallahi ba Wanda zaishiga tsakanina da AK koda kuwa grany ce dakanta bare wata banza wai asma'u Ku kwantar da hankalinku dady insha allahu wannan dukiyar tamuce mu kadai bawanda zaicita se mu dariya jamilu yayi harda kyajyatawa yace ai nasanki ya'ta bakya wasa kunsan me duk lokacinda narufe idona kawai jina nake natashi daga jamilu nadawo jamil hausawee Dariya sadiya tayi tace ni kuma Mr's jamil hausawee Mikewa aysha tayi tafita tana fadin ni kuma Mr's AK hausawee ladidi da bashir ne zaune adaki suna fira ladidi tace wai kai bashir har yanzu ba'abaka albashinka bane Murmushin gefe yayi yace to in anbani meza'ayi dashi badai inbaki ba Daure fuska tayi tace kai kar kamun rashin kunya kaji ko wai kai kodan ciwa ciwa da babakere dinnan ma duk baka iya ba company nan fa nakune kabude aljihunka kadiba kudi amma katsaya wasa Girgiza kai yayi yace a'a mama nifa ba abunda yakaini wurin ba kenan nayarad idan ina son kudi intambayi AK yabani amma bawai insata ba " yo wayace kayi sata kai kowafa daka gani agidannan tasa ce takawosa kowa soyake yakwasa na kwasa kafin ayi waje dashi saboda haka kaima kasan nayi gaka jamilu da wannan kinibabbar matar tasa allah kadai yasan abunda aysha ke kwaso masu a aljihun AK amma kai katsaya wasa to tsaya kaji dazaran AK ya auri aysha to tamu takare agidannan dan wallahi gaba daya kawye zasu maidamu daga ita se iyayanta ne zasu muri wannan dukiyar yashi yayi yana fadin insha allahu ma bazai aureta ba dan da ace matar nan tasa ta kile irin yan duniyan nan ne to wallahi ko kallon aysha bazai yi ba tsaki tayi tana binsa da kallo har yafita sannan tace aikin banza ana ga maciji kana ga tsutsa dadin ya'mace kenan wallahi da ameena na nan dayanzu ta taimaka mun ga salma tayi Karama bata San komai ba ... sarah na kuance kan gado da photon ahmad ahannunta tana kallo idonta sunyi ja sun kunbura tun hawaye nazuba har sun kafe Tunowa tayi da AK kefadin wai tahakura da ahmad tunda khadeeja zai aura Wurgi tayi da photon tafara wawwatsa kayan dakin tana fadin ina bazai yuwu ba sedai idan bana raye bawacce ta isa ta auri ahmad seni Kwalba tadauka tarusa madubin dressing mirror tasulale akasa cikin dasashshiyar muryanta tana fadin nawa ne nikadai ....ni kadai nake sonshi...kuma ni zan aureshi...inba haka ba zan mutu Wayarta ta dauka takira numban khadeeja bugu biyu tadaga tare da sallama Shiru tayi nadan lokaci sannan cikin dasashshiyar murya tace sarah ce nakira namiki barka ina tayaki murnan samun ahmad amatsayin mijinki amma ni kuma zanbaku wedding gift din sekun mutu baku manta dani ba kigayama ahmad idan har bashi arayuwata to batada wani anfani tana kainan takatse kiran mamaki ne Yakama khadeeja tana maimaita wedding gift saurin kiran asma'u tayi tana dauka tagayamata yanda sukayi da sarah atsorace asma'u tamike tana fadin me sarah zata aikata ohh my god ....tafada tana fitowa dagudu daga dakin aguje tanufi dakin sarah tana bugamata kofa amma shiru aysha ce yazo wucewa tadawo tana fadin malama lafiya what is ur problem Banza tayi da ita takwala ma nura kira yazo suka fara balla kofar aguje tafada dakin sedai cak tatsaya tana kallon sarah dake kuance ga hannunta duk jni alamun yanka awurin Durkushewa tayi akusa da ita tana kuka aysha ma hannu tadora akai tafashe da kuka ganin jinin baitsayaba yasa asma'u tayi saurin yaga gualenta tadaure wurin sannan aysha ta taimaka mata suka kaita mota se asibiti Suna zuwa aysha takira AK awaya seda takusa katsewa yadaga yana fadin baby I am busy zan kiraki anjima Cikin rawar murya tace AK sarah ta kashe kanta kayi sawri kazo asibiti Dariya yayi yakatse kiran yana kallon ahmad dake kusa dashi yace kaji wani shirme wai sarah takashe kanta azabure ahmad yamike yana salati yace AK yana yiwa dagaske ne kasan sarah fa bata iya shiga damuwa ba "No wasa ne nasan aysha tana mun irin wannan wasan in tanason ganina Girgiza kai ahmad yayi yace a'a AK nifa tsoro nakeji kar azo dagaskene kakira grany ko asma'u mana Wayansa yadauka ya lalubo numban asma'u dayayi saving da chitti yakira yana fara ringing tadaga tana fadin ABI ina kashiga ina kiranka bana samu kazo asibiti sarah bata jin dadi Azabure yamike yana fadin meyasami sarah kina nufin dagaske tamutu cikin rawar murya tace a'a bata mutu ba ABI kaidai kawai kazo aguje yafita daga office ahmad nabinsa abaya Cikin minti 30 suka iso asibiti yana isa doctor nafitowa wurinsa suka nufa atare suna tambayar ya jikinta Kallonsu yayi daya bayan daya sannan yace dafari dai inaso insan wa yadaure mata hannu da kyalle baigama rufe baki ba aysha tayi saurin nuna asma'u dayatsa tana fadin wannan ce juyawa sukayi atare suna kallonta sanan suka maida kallonsu kan doctor itama asma'u kallonsa take dafargaban abunda zaifada Murmushi yayi yana kallonta yace gaskiya kinyi dubara mai kyew saboda badan kinyi hakan ba da kafin kuzonan tarasa jni mai yawa kuma jijiyarta zata ita bushewa ko iska yakai ga zuciyarta hakan kuma shi zaisa tarasa ranta amma yanzu alhamdulillah taji sauki zaku iya shiga kuganta sedai akula irin haka kar takara faruwa Sannan yakalli AK yace muje office ina son ganinka gaba yayi AK da ahmad suka bisa abaya aysha kuma tashiga dakin da sarah take Nuance take tana kallon sama hawaye nazuba a idonta ga igiyar Karin jini ana mata se hannunta da aka ma bandage Kusa da ita aysha tazauna tana fadin sannu sarah gaskiya AK bai kyewta miki ba koda yake ba laifinsa bane wannan munafukar yarinyar ce tasashi wayasan metagayamasa ... Muryan asma'u tajiyo tana fadin tashi kifita Juyowa tayi tana hararenta tace dawa kike kehar kin isa kice nafita dan karamin table din da ake dora magunguna ta rarumo tanufota dashi bashiri tayi waje aguje har tana bigewa da kofa ijiye table din asma'u tayi takarasa kusan gadon tana duba hannun sarah Kwace hannunta tayi tana fadin wayace ki kawoni asibiti meyasa baki bari namutu ba tunda natabbata abunda kike so kenan Kusa da ita asma'u tazauna tana fadin sarah kina bani mamaki idan kikayi wani abun kamar wacce batayi karatu ba yanzu idan kika kashe kanki riban me zakici Wanda kikayi danshi zai danyi jimamin lokaci kadan daga baya kuma yamanta yayi aurensa yacigaba da rayuwar farinciki Yanzu dazan tambayeki da allah da ahmad wakika fiso zakice allah amma kuma kinyi kokarin aikata laifin da allah bazai yafemaki ba saboda ahmad Akan rayuwar duniya kikayi kokarin ruguza ta lahirarki Miye laifin AK dazaki daga mai hankali yana matukar kokari wurin faranta miki amma ke kanki kawai kika sani bakya tunanin halin dazai shiga idan kika aikata wannan kazamin aiki Sarah kefa macece mata ansansu da juriya da danne soyayya aransu saboda gudun wulakanci amma ke kinkasa yin hakan shiyasa kike wahala Ki godewa allah dayabarki da ranki yana sonki shiyasa baidauki rankiba yabaki dama akaro nabiyu dan kyallen danasa maki bashi yahanaki mutuwa ba lokacinkine baiyiba Bakowa yakesamun irin damar dakika samu ba yau da kin mutu da zaki dawwama kina nadama har abada ina gayamiki hakane ba amatsayin asma'un dakika tsana ba Ina gayamikine amatsayin musulma kuma mace yar uwarki Ga glass nan da wukake kina iya dauka kikara yanka hannunki ko wuyanki amma kisani ba kyada hujjar dazata hana allah yakonaki tana kainan ta tashi ta fita daga dakin Tana fita AK da ahmad nashigowa aguje AK yakarasa bakin gadon yana kallonta cikin rawar murya yake fadin sarah why!! Why sarh!! Why!! yakasa cigaba da maganarsa se hawaye dake zuba daga idonsa Itama kukan take tana fadin yaya i am sorry dafasa ahmad yayi yace friend kaje waje zanyi magana da ita fita AK yayi yana sharan kwalla gefe guda yaje yazauna hade da dafe kai AK nafita ahmad yadawo kusan sarah yazauna cikin sassanyar murya yace Sarah base kinfadamun dalilin dayasa kika aikata hakan ba nasan saboda kinji zanyi aure shiyasa Na fahimci halin da kike ciki saboda nima nashiga wannan yanayin abaya sarah nasan kina sona kuma nagode da kaunarki agareni amma bayanda na iya sarah Ina miki kallon kanwata ne kuma kawata idan kika hakura kika manta dakomai zanci gaba da kallonki ahakan amma idan kika kara aikata wani abun to zaki rasa wannan matsayin awurina Shiru tayi tana kallonsa takasa cewa komai tashi asma'u tayi tanufi inda AK kezaune tazauan kusa dashi Dagowa yayi yakalleta yakara maida kansa kasa ahankali takai hannunta tadafa kafadansa cikin sigar lallashi tace kar kadamu kaji she will be fine dagowa yayi yana kallonta da jajayen idanuwasa cikin rawar murya yace chitti meyasa sarah zatayi abunda ko jahili bazai yiba meyasa zata zabi tarabu dakowa nata tahadu da fushin ubangiji akan tarasa ahmad bazatayi tunanin halin da zan shiga ba bana kewar iyayenmu saboda ita da grany aduk lokacinda nakalleta fuskan ummarmu nake gani atata hawayene suka zubo daga idanuwansa yacigaba dafadin Chitti nasan zakiyi tunanin nabata sarah dayawa ko duk abunda takeso ina mata kinsan dalili ? Girgiza kai tayi hawayen datake makalewa suka zubo cije lebensa nakasa yayi yana saita muryansa yace Tun ina karami nataso ina son yima iyayena hidima inaso naga sunkawo bukatrsu namusu kodan naga murmushi afuskansu ta dalilina Naci burin yi musu hidima na kyewtata musu in sungirma amma allah bai kaddara ba Kinga sarah to yadda take haka ummana take ita kuma grany sak yanda take haka abbana yake daga ranar da suka rasu daga ranar duk wani son danake masu da burin kyewtata masun danake yakoma kan sarah da grany haka nataso har kawo wannan lokacin banason ganin abunda yabata musu rai ko sun nemi Abu sun rasa amma gashi yau nakasa wurin farantama kanwata ...muryanshi ne yakarye yakasa cigaba damagana Hannu takai tana share mai hawaye cikin muryan kuka tace ABI kai ba allah bane mutum ne duk yanda kaso ka kyewtata musu dole wata rana sunemi wani abunda su rasa kuma dama haka rayuwa take kowa kaduba akwai abunda yakeso yakasa samu ABI u are not just a brother but u are a real hero kayi ita kokarinka sauran kuma sekabarma allah amma please stop blaming ur self Gyara zamanta tayi tana kallonsa cikin sigar tsokana tace Yanaga kayi saurin karayane ko kamanta maganr damukayi jiya idan bazaka iya samomata ba ni kabani dama nasamo mata handsome guy Murmushi yayi yace a'a nizan zaba dakaina ke kinsan handsome ne haka kawai kije kidaukomata dan jagaliya murasa yazamuyi dashi Kwaikwayon yadda aysha tashigo jiya tayi tana fadin wai me kadaukeni ne naga fa kana nema karaina mun class dina Dariya yayi yace to ya isa masoyiyar tawa kike kwaikwayo komai abunki dai bazaki kaita haduwa ba "Allah sedai in banyi niyya ba abun ai ba wuya ne dashiba nidai kawai banda lokacinsa ne tashi yayi suka nufi dakin sarah Rungumeshi tayi tana kuka tace Yaya na amince nahakura ahmad ya auri khadeeja Dagota yayi da mamki yace dagaske kin amince amma abunda da mamaki da zaki kashe kanki yanzu kuma kin amince kodai kin hango malakal mauti ne kara rungumesa tayi tana murmushi tace Yaya kabari banaso dariya sukasa gaba dayansu banda aysha dake jifan sarah da kallon tuhuma Dagowa tayi tana kallon asma'u tace sister nagode dakika ganar dani abunda nakasa ganewa tun tuni Gaskiya ke tadabance thank u once again Juyowa AK yayi yana kallon asma'u da murmushi afuskansa Sunkuy dakanta tayi itama tana murmushin Da yamma aka sallemesu suka dawo gida dakin sarah suka fara zuwa seda ta kwanta sannan suka fita akabari daga ita se aysha Bayan kowa yafita aysha tazo tarufe kofar da key takoma kusan sarah da mamaki tace sarah what is ur plan? kauda kai sarah tayi tace kamar ya ? "Hahaha sarah kar kirainamun hankali nafasanki kamar yunwar cikina u won't give up easily Ya akayi haka Share hawayenta tayi tace to aysha yazanyi ahmad yariga yazama na khadeeja Dana tsaya inaba kaina wahala ba gara nafita hanyarsu ba nima nayi addu'ar allah yabani mijinagari Hanyar fita aysha tanufa tana fadin kin bani mamaki sarah Ashe bama son Ahmad kike ba kawai cika baki ne Dakallo sarah tabita har tafita sannan tarufe idonta ahankali hawaye nagangarowa gefen fuskarta Aysha nafita wurin AK tanufa yana zaune apalo ta iskosa kusa dashi tazauan tana shagwabe fuska tace darling wai mekake jira da yarinyar nan ne naga bakada niyyar korarta daga gidannan Gefen fuskanta yashafo yana murmushi yace aysha kifahimci halin da grany take ciki kinsan tana son asma'u dayawa to kafin in rabu da ita ina bukatar hujja ko dalilin dazan kare kaina dashi awurin grany idan bahaka ba gaskiya bazan iya sakinta haka kawai ba to mezan gayama iyayenta idan ita tasan dalilin dayasa na aureta su basu saniba Murmushi tayi tace OK I understand amma dan allah kadaina shishshige mata dazu fa ina ganin lokacinda kuke dariya a asibiti Nidai gaskiya kadaina sake mata fuska kaga tafara raina mutane tun ba'aje ko inaba kauda kai yayi yana fadin nasan menakeyi base kin gayamun yadda zan zauna da ita ba Yana kainan yamike yanufi masallaci Dakallo tabisa har yafita sannan ta tashi ahasale tawuce dakinta dakarfi ta tura kofar dakin tashiga tana fadin ina bazai yuwu ba wallahi wannan ai shirmene dolema nasan abinyi ina ganin abun kamar wasa gashi yafara zama babbar barazana wa farin cikina """" [19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚 👨‍👧 _DOMUN KANWATA_ 👩‍👧 Na( *Maryam Mhd*) 1⃣2⃣0⃣ Da yamma aysha taraka sarah gidansu asma'u taje Neman khadeeja Bayan sungaisa dasu Umma khadeeja tarakosu har waje Juyowa sarah tayi tana kallonta da murmushi afuskanta tace to deeja nizan tafi se kinzo gobe kauda kai tayi tana daure fuska tace allah ya kaimu ahasale aysha taja hannun sarah tana fadin wai sarah meyake damunki ne kintsaya karamar yarinya tana daddaure maki fuska kar allah sa tazo Kwace hannunta tayi tana daka mata tsawa tace aysha ya isa haka karkimanta matsayinta awurina so behave ur self Dariya khadeeja tayi tadawo gaban aysha tatsaya tana fadin malama dafarko dai inaso kisan bani nagayyace Ku gidanmu ba so dole zaku Bini aduk yadda nakarbeku ku idan kinga bazaki iya ba hanya abude take Sannan tajuyo wurin sarah tace ke kuma sarah ina so kisan cewa koda gaba daya mutanen duniya zasu yarda da canzawarki to ni khadeeja bazan fada tarkonki ba Saboda nasan people like u won't change easily nasan kina da wata buyayyar manufa akan wannan fuskar mutuncin dakika ara nunata tayi dayatsa tace let me worn u sarah if u dare do something terrible to me or my sister I will make ur life a living hell that's my promise tana kainan tajuya tabarsu atsaye suna binta da kallo har tashige ciki sannan sarah tajuya jiki asanyaye tashiga mota aysha tabita tana jan dogon tsaki AK na zaune apalo asma'u tashigo tana kwasan gyalenta tawuce takusan shi zata shiga daki hannunta yakamo yajuyo da ita gabansa yana fadin zo nan hajajju ina so in tambayeki wani abu zaunawa tayi daga kasa suna fuskantar juna takure shi da ido batace komai ba kallon kallon suka farayi nadan lokaci kana yaja nunfashi yana Sosa kai yace mema zan tambayeki ? tashi tayi tana fadin bari natafi inada abun yi idan katuna seka kirani Janyota yayi yazaunar da ita yana fadin a'a dawo natuna nace wai me kika gayama sarah ne har tayi saurin gane abunda najima ina kuatanta mata murmushi tayi tace ni nama manta abunda nagayamata kawai dai magana namata kuma banmasan zata dauki abunda nafada ba kankance ido yayi yana kallonta yace um um chitti a iya sanina sarah ta tsaneki bata sonki amma ya akayi lokaci guda tafadi magana mai dadi akanki anya kwa ba magic dinnan naki kika mata ba kuwa ni kikoyamun yanda ake nama grany tafarayin duk abunda nakeso Dariya tayi tace wane magic kuma nidai bawannan ba gaskiya ABI bai kamata ayi bikin khadeeja anan gidan ba duk da sarah tahakura amma bazataji dadi ba zaiyi magana kenan sukaji sarah nafadin Ba abunda zanji sister anan zamuyi bikin kanwarmu kamar yadda Yaya yafada Juyawa sukayi suna kallonta da murmushi afuskansu Karasowa tayi kusa da AK tazauna tana kallon asma'u tace bama wannan ba sis kushirya gobe da daddare nahada dan kwarya kwayan party wa ahmad da khadeeja saboda inaso musanar da abokanansa da kawayanta zancan bikinsu kuma natayasu murnan cimma burinsu kallonta AK yayi cike da tausayi yace kintabbata ba wata matsala sarah can u bear it ? Dafashi tayi tana dariya tace Yaya come on I am not a kid ko kuma Baku yarda nahakura bane murmushi sukayi suna kallonta basuce komai ba da daddare har Sarah ta kuanta aysha ta iskota rai bace tace sarah ni nakasa ganeki wai ina sarahn da nasani wacce bata hakura da abunda takeso bare abunda nasan kinfi sonshi fiye da komai aduniya yaushe kika dawo hakane ko kema sallon yaudarar asma'u yayi tasiri akanki ne Daure fuska tayi tana kallonta tace aysha waini wacece dabazan gyara rayuwata ba ko kafiri yakan musulunta yazama nagari bare ni me kika daukeni ne to nagaji da abunda kike mun kar ki kara mun wannan banzar tambayar kinji nafadamiki ahasale tafita tana banko kofar dakarfi washegari dasafe AK d nabangaren grany yana breakfast kan dining asma'u nagefensa azaune tana kokarin zuba kunu akofi amma takasa saboda hannunta da yayanke wurin girki inna ameena nazaune daga gefe tana kallonsu karasowa tayi wurinsa tana murmushi tace AK kaga asma'u tayanke dazu ahannunta kazubamata kunun mana kabata kwarewa yayi yayi saurin daukan ruwa yakora yana kallonta da mamaki yace inna me ...mekikace ....nabata kunu fa daure fuska tayi tace yo miye ba matarka bace kai gaka ahaka kamar zakayi soyayya amma ashe ko wayewar ma bakayi ba Harara yajefa ma asma'u yana fadin to dabana nan waye zaibata kunun ko dolene ma setasha kunu tafa hannu inna ameena tayi tana salati tace oh ni ameenatu menakeji haka kamar gwaranci abakin AK amma wallahi kabani kunya se anyi magana kuce mana yan zamanin da to mudai bahaka mazan mu ke mana ba Kallon asma'u tayi tana fadin baiwar allah shiyasa da daddare sena koreki kike tafiya allah kadai yasan me yake miki labace baki asma'u tayi kamar zatayi kuka tace inna infadamiki wani Abu Zaunawa inna ameena tayi kan kujera tana fadin inajinki asma'u menene "Jiya ma haka ya..... bata karasa ba yayi saurin fadin OK fine....zan bata abar zancan gyada kai inna ameena tayi tana fadin dadai yafi maka inba haka ba yanzu nakira grany asma'u tafadi komai agabanta Kofin kunun ya fizge ahnnun asma'u yana ji kamar yarusa mata shi abaki seda yafaki idonsu ya ciko cokali da barkono ya zuba cikin kunun ya juya yana murmushin mugunta yakai kofin bakin asma'u yana fadin enjoy ur self baby !!! Kurban farko taji kunnanta ya amsa saboda yaji saurin janye bakinta tayi tana kallonsa Murmushi yayi yakara kai kofin bakinta yana fadin drink it badai kunu kike soba kallon inna ameena yayi yace kinga ai halin matan kenan tace kunu yanzu kuma nafara bata tana nuna bataso hannunsa asma'u takama takai kofin bakinta tana shan kunun kamar ba komai aciki Da mamaki yake kallonta seda tayi rabi sannan takai kofin bakinsa tana lashe baki tace to kaima kasha darling!! zaro ido yayi yana kokarin kauce bakinsa inna ameena tace kai kasha mana yau naga sakaran yaro asma'u zatayi magana kenan yayi saurin kama hannunta ya kai kunun bakinsa ya kurba saurin hadiyewa yayi ya kauda kai gefe yana huddo harshe Kallonsa inna ameena tayi da mamaki tace wai yanaga kana Abu kamar dayaji akunun ne dariya asma'u tayi tace inna yaji ya.... bata karasa ba yayi saurin katseta dafadin kaji inna kuma mezai kawo yaji cikin kunu waima banaji grany nakiranki ba kitashi kije mana zamu

Chapter 16 of 35