Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yayi jikinsa asanyaye yace shikenan friend ka kula dan allah idan kaga wurin da hadari kar kashiga kajira se munzo kaji To yafada yana juyawa yafita bin bayanshi aysha tayi har yafita tarikoshi tana fadin AK wai mekake shirinyi ne Juyowa yayi yana fadin abunda yadace fashewa tayi da kuka AK yaruwarka fa zakasa ahadari saboda asma'u to gaskiya sedai kazaba ko ita ko ni idan har katafi wurinta sedai kahakura dani Shiru yayi nadan lokaci sannan ya kwace hannunsa daga nata ya juya yana fadin nabarki lafiya Saurin shangabanshi tayi tana kuka tace AK dagaske tafiya zakayi Gefen fuskanta yashafo yana murmushi yace aysha nasan kindamu dani shiyasa kike haka amma kiyarda dani ba abunda zai sameni insha allah Yana kainan yayi gaba dakallo tabisa har yashiga mota yatafi sannan tajuya ahasale tanufi dakin aysha tana shiga ta isko sarah na Neman JJ awaya hankali tashe yana dauka tace JJ wai kai wane kalan sakarai ne to kasani ga Yayana nan zuwa kuma wallahi kasake yakamaka kai kasani karma ka ambaci sunana tsaki yayi yace to seme inyazo ke nifa banason takura kingane ko inace ko gama biyana bakiyi ba kinzo kin isheni da surutu kibarshi yazo mana alqur'an ana kamani sunanki zan fada banza yar tasha kawai saurin katseshi tayi dafadin yi hakuri JJ raina ne abace yanzu kasan meza'ayi Kawai kasaki yarinyar kubar wajan kafin ya iso kunji dariya yayi yace ni banda matsala kawaidai kituran sauran kudina ni kuma zan sallameta tsaki tayi tana katse kiran tazauna bakin gado tana share zufan da takaryo mata se tsinema JJ take Juyawa aysha tayi tafita batare datace komai ba tanufi bangarensu Haduwa tayi da jamilu zai fita aiki fadawa tayi kan jikinsa tana kuka Rikota yayi atsorace yana tambayar meyafaru Cikin kuka tagayamasa duk abunda yafaru da tafiyar AK wurin asma'u zama yayi kan kujerar Palo yana cire hularsa yace ina bazai yuba gaskiya haka kawai muna gani munaji Abu zai rikice mana wallahi natsani yarinyarnan ga dukkan alamu AK yafara sonta Sadiya dashigowarta kenan palon tace yana fara kulata kuma zata fara zazzago Ya'ya daga nan kuma muntashi aiki daga karshe ayi waje damu Kallon aysha yayi yana fadin kinsan Wanda sarah tabama aikin gyada kai tayi tana share kwalla murmushin mugunta yayi yace jeki satomun numbansa amma karki bari tagane Fita tayi cike dajin dadi tanufi dakin sarah da dubara tasamu tadauki numban JJ tadawo bangarensu Karban numban uncle jamilu yayi yakira bugu biyu yadaga yana fadin waye ne Canza murya jamilu yayi yafara fadin Sunana basiru nasan sarah tabaka aiki akan kasace khadeeja bai mistake kasaci yayarta yanzu kuma tace maka kasaki yarinyar yin haka kuma hadari ne babba awajanka Katseshi yayi dafadin to malam basiru kake ko wa ?? abunda kakira ka gayamun kenan ? Dariya uncle jamilu yayi irin tasu tamanya sannan yace JJ nima fa dan ahnnu ne saboda haka aiki zanbaka bansan konawa sarah tabaka ba amma zan linkamaka konawane ka kashemun yarinyar kafin AK yaje wurin Dariya JJ yayi yana hura sigari yace angama yallabai irinku mukeso masu bamu aiki kai tsaye dariya jamilu yayi yace kardamu JJ yanzu zakaji alert narabin kudinka sauran kuma ina ganin gawarta zakagansu cike da farin ciki JJ yagayamasa kudin da account numban daza'a turamasa kudin sannan suakayi sallama nan take ya dibi yaransa suka nufi dajin da asma'u take kallonsa aysha tayi da mamki tace dady meyasa kace sunanka basiru Dariya yayi yace yarinya ai awannan harkar wawayene kawai ke fadan sunansu nagaskiya kinga yanzu koda wani Abu yafaru yansanda suka tuhumeshi zaice basiru ne yasashi to waye basiru?? Dariya sukasa gaba daya cike da farin cikin burinsu yakusa cika gudu AK yake amota kamar zai tashi sama yana mamkin nisan dayayi amma har yanzu arrow din baidaina nuna hanya ba seda yakai inda motarsa bazata Shiga ba yayi parking dinta yafara tafiya akafa yana ma Ahmad kuatancen inda yake Yayi nisa sosai adajin ahmad yakirasa awaya yace gaskiya ya jirasu gasunan zuwa sun isko motarsa awani wuri shi sam bai yarda da ..... Hello hello AK yafarayi dan baiji karshen maganar ahmad ba Jin shiru yasa yadago wayar yaduba zaro ido yayi ganin wayar amace yakunna kuma taki tashi Hannu yadora akai yana fadin namutu ni Abidi yanzu taya su ahmad zasu San inda nake cikin wannan dajin Jiyayi kamar yakoma wurin motarsa se kuma ya tuna baisan halin da chitti take cikiba Kallon agogon yayi sannan yayi shahada yabi hanyar dayake nuna masa har yamma tayi amma AK baikaiba har yafara sarewa da lamarin yana tsinema agogon ahmad shikadai se magana yake gashi ya gaji fatanshi daya allah d Sa ba banzan agogo bane wannan yabi ta karyan turawa zai kashe kansa jin karan agogon yakaru yasa yayi saurin kallonsa dariya yayi cike da farinciki yanufi inda yanuna mai baiyi tafiya mai nisa ba yahango runfar du JJ kuma nan agogon ya nuna masa Cikin aljihu yasaka agogon cikin sanda da dabara yakarasa wurin kwance suke suna bacci suduka bayan sunsha giya sun bugu ahankali yake takawa har yatsallekesu yashiga runfar can gefe ya hangota azaune tacusa kai aguywa tana kuka saurin karasawa yayi wurinta yana murmushi cikin rada yace chitti!!! kamar amafarki taji muryansa saurin dagowa tayi dan ganin koda gaskene zagayowa yayi tabayanta ya kuance mata daurin kamar jira take tafada jikinsa tana fashewa da kuka rungumeta yayi nadan lokaci sannan cikin rada yace kinga tashi mutafi idan munbar nan wajan se kiyi kukan dariya tayi ta tashi tana fadin ya akyi kazo nan Jan hannunta yayi yana mata alama tayi shiru suna fitowa sukaga ba yaran JJ awurin zaiyi magana kenan yaji ansamai bindiga abayan wuyansa cikin muryan mashaya JJ yace sannu da kokari AK hannayansa yadaga sama yana juyowa ahankali itama asma'u tayi yanda taga yayi atsorace jikinta se rawa yake kara saita bindigarsa yayi yana dariyar keta yace kayi Babban kuskure daka shigo gonata doka tace idan har nakama mutum yayi kokarin guduwa to kisa ne hukuncinsa saboda haka saita asma'u yayi da bindigarsa yana dariya yace kiyi addu'ar karshe yan mata saurin shiga gabanta AK yayi yana kallon JJ yace dakata dan allah kayi hakuri kabarta ta tafi lafina ne nizaka kashe ba itaba katausaya mata mana mace ce fa mezaka samu idan ka kasheta tukunna ma akan wane dalili ka kamata kafada konawa kake so zan baka amma kabarta ta tafi Kallon yaransa yayi suka kwashe da dariya seda sukayi mai isarsu sannan yasaita bindigar kan AK yana fadin to ai kaima ba kyaleka zanyiba tunda har kaganni kuma kaga mabuyata to dele kamutu janyo hannunsa asma'u tayi tadora bindigar kan goshinta cikin kakkawsar murya tace zaka iya kasheshi amma sedai kafara kasheni tukkuna saurin janyota AK yayi tafado jikinsa yana fadin chitti mekikeyi hakane Dariya JJ yayi yana kallon yaransa yace haba tundazu ina mamakin meyasa AK zai sadaukar da rayiwarsa yashigo wannan dajin saboda wata yarinya Ashe masoyane hahahhaha juyowa yayi yana kallonsu yace Romeo da Juliette banada isashshen lokaci kuazabi wazan fara kashewa acikinku ko kuma ni nazaba Shiru suakyi suna kallon juna hawaye nabin kuncin asma'u tana tuna halin da iyayensu zasu shiga idan suka ga gawarsu atare Shima AK abunda yake tunani kenan Dariya JJ yayi ya umarci yaranshi dasu rike mashi AK shikuma yasaita bindigarsa kan asma'u Sam bata damu da bindigar ba hankalin nakan AK dake kokarin kwace kansa daga yaran yana rokon JJ dayarabu da ita kallon juna suke lokaci guda suna tuna rayuwar dasukayi abaya hawaye nazuba akan kuncinta amma da murmushi afuskanta tana kallon AK kallonta yake shima baisan lokacinda hawaye ya zubo mashi ba cikin rawar murya yace JJ dan allah na rokeka kabarta ta tafi idan ma zaka kasheta dan allah kafara kasheni tukkuna I can't watch her dying dafe goshi JJ yayi yana kallon AK yace aK kamun shiru ni idan ina aiki banason hayaniya Kallon yaransa yayi yace gayu gaskiya tunda nake bantaba kashe masoya ba kuma gaskiya bazan iya barinsu sutafi ba dole ne su mutu ya za'ayi dariya sukasa dayan yace oga to mezai hana kabani bindigar nagama musu aiki Shiru yayi nadan lokaci sannan ya tuntsire da dariyar mugunta yace gawata dabara Bishiyar kusa dasu yanuna musu yana fadin kudauramun yagiya ajikin waccan bishiyar zamuga idan dagaske bazai iya ganinta tana mutuwa ba Nan take suka daura yagiya kamar yadda yace hannayensu yasa suka daure sannan suka nufi wurin bishiyar dasu duk yanda AK yayi kokarin kwace kansa amma abun yagagara sarkin yawa yafi sarkin karfi ga bindiga ahannunsu ita dai asma'u tuni ta saduda tagama sallamawa kawai mutuwa zasuyi to meyasa zata dami kanta Banda kuka ba abunda take se rokonsu take surabu da AK sukasheta amma ko kallonta basuyi ba har dare yayi ahmad nayawo da yansanda adajin amma sun rasa ta inda zasu nemesu gashi wayan AK akashe ba yanda baiyi da yan Saddan ba akan suci gaba da nemansu amma sunki wai dare yayi bazasuyita shiga cikin daji ba zasu koma idan sun shirya zasu zo aci gaba da nemansu Bayanda ya iya haka yahakura jiki asanyaye yakoma gashi khadeeja se kiranshi take tana tambayar yagansu sedai yabata hakuri yace zasu gansu acan gida kuwa gaba daya hankalinsu yakara tashi ganin ahmad yadawo batare dasu AK ba Umma ma seda ahmad yakira doctor yamata alluran bacci gudun kar ciwonta yatashi Abba kuma tuni yafada amasallaci atayasu da addu'a Khadeeja kwa banda kuka ba abunda take da kyar ahmad ya lallasheta tayi shiru Haka ma bangaren grany da inna ameena abinci da kyar sukeci dan gaba daya gidan ba dadi Ita kanta Sarah tashiga damuwar rashin AK dan tasan JJ bayada mutunci zai iya hadasu gaba daya yakashe gashi tana kiransa baya dauka daga karshema yayi blocking numberta Aysha ma tadamu ganin AK baidawo ba amma da jamilu yakira JJ seyacemasa AK baijeba asma'u kuma yakasheta kawai yajira gawarta nanan zuwa Se alokacin hankalinsu ya kwanta sukaci gaba da nuna fake damuwansu akan rashin dawowarsu kama asma'u sukayi suka ratayeta ajikin yagiyar ga hannayenta adaure Dai cikin yaran yana rike da kafafunta wanda daga yasakesu wuyanta zai sarke ajikin yagiyar Kuka AK yake kamar karamin yaro bashiri yasa karfinsa gabadaya yakwace kansa aguje yakarasa wurinta yana kuka yana rokonsu dan allah sukwanceta dariya sukasa gaba daya suna kallonsu yaron dake rike da ita yace oga nagaji pah yasin zan saketa karasowa JJ yayi kusan AK yana fadin zaka iya taimakonta ai dasauran dan lokacinda yaragemuku kafin wahala takarasaku durkusawa AK yayi akan guywowinsa aka Dora kafafuwan asma'u akan kafadunsa tayi tsaye Dariya sukayi dai cikin yaran yace oga kana ganin zai iya juran daukanta kuwa "To ai hikimar abun kenan shi dakanshi zai kasheta idan kuma bai kasheta ba ita zata kasheshi Haka zamu barsu su kwana har gobe idan basu mutu ba dasafe zamu kashesu kafin mu barnan juyawa sukayi suka koma gefe guda suka fara shan giyarsu suna fira Hawaye ne ke zuba akan kuncin asma'u kamar anbude panpo har suna diga sama kan AK ahankali yadago kansa yana lekenta yace chitti yayyafi akene kece asama zaki fini sani naji Abu nadiga akaina Cikin muryan kuka tace ABI why did u come "aw abunda ma zakice kenan maimakon kigode mun nazo taimakonki shine zaki ce meyasa nazo ko "To yanzu me zuwannaka ya anfanar ni bantsira ba gashi zamu mutu gaba daya murmushi yayi yace bazaki mutu ba chitti kafin Nazo nan wurin seda nabiya wurin Umma namata alkawarin zan maidaki gida to koda zan rasa raina insha allahu se kinkoma gida karkidamu sautin kukanta ne yakaru tace ABI ni nafiso namutu karayu akwai mutane dayawa akarkashinka ga grany da sarah wane hali zasu shiga idan wani Abu yasameka "Kema ai kinada responsibility ga Umma ga inna da khadeeja kece mai kula dasu yazasuyi idan bake Cikin sheshshekar kuka tace idan har kana nan bandamu ba nasan zaka kulamun dasu amma idan baka ni bazan iya komai ba ABI runtse idanuwansa yayi dan tuni kafadunsa sun fara zafi cikin muryan wahala yace yanzu dai abar zancan meyasa kincika surutu ne kina gabar mutuwa ma bazakiyi shiru ba to nidai ki kyaleni inyi istigfari dan nafara hango barzahu Shiru tayi hawayenta nakaruwa tana ji dama itace akasa dan tasan shikadai yasan meyakeji ahalin yanzu Har dare yayi su AK na ahaka tuni yafara gajiya dan har wani jiri jiri kedibansa kawai taimakon allah ne da jarumta irin tashi yasa har yanzu yake durkushe awurin amma guywowinsa da kafadunsa jiyake kamar ana Sara mai gatari gashi yanada asma tuni yaji tafara kokarin tashi asma'u ma haka tagaji da tsayuwa jikinta har rawa yake tun tana kuka har tagaji tayi shiru tana addu'a sedai jefi jefi AK yakan tsokaneta wani lokaci takulashi wani lokaci kuma sedai tafashe da kuka har takai lokacinda suduka sukayi shiru bamai magana """"" [19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š πŸ‘¨β€πŸ‘§ _DOMUN KANWATA_ πŸ‘©β€πŸ‘§ Na( *Maryam Mhd*) 1⃣4⃣5⃣ Kokarin janye kafarta tafarayi daga kan kafadunsa tana fadin ABI katashi katafi kabarni anan kawai koban mutu yanzuba anjima mutuwa zamuyi gaba daya dan natabbata bazamu iya kai safe ahaka ba kuma koda munkai ma kashemu zasuyi Kaga damu mutu gaba daya gara kai katsira koba komai abun zaima su Umma sauki Kokarin kuance hannayensa yafarayi yana fadin chitti miye haka kike kokarin yi stop moving ur legs dan allah u are hurting me kina so kikashe kanki ne idan natafi nabarki anan miye anfanin zuwana mezan gayama su Umma idan nakoma Cikin Sa'a kuwa ya kwance hannayansa har takusa sauke kafanta yayi saurin rikosu cikin rawar murya yace Chitti kinga na kuance hannayena kiyi kokarin kwance naki abun baida kwari sosai Shiru tayi hawaye nacigaba dazuba afuskanta yana rike da kafafuwanta akan kafadunsa yana cigaba da lallashinta har tafara kwance hannayenta da taimakon allah tayi nasaran kwancewa sannan tafidda yagiyan wuyanta atare suka fadi awurin suna maida nunfashi Cike da tausayi ta sunkuyo saitin fuskar AK cikin rada take jera mai sannu Yajima ahaka kafin dakyar ta taimaka mai yatashi yana runtse idanuwa saboda azaban da kafadunsa da guywowinsa kemasa Hannunta Yakama yana leken su JJ dake sharan bacci kaman matattu sunsha sunyi tatil Cikin sanda suka fara tafiya seda suka dan yi nisa sannan suka fara gudu suna kara shiga cikin dajin batare da sunsan inda suka dosa ba Sunyi nisa sosai asma'u taci birki tana fadin ABI gaskiya nagaji bazan iya cigaba da gudunnan ba mudan zauna mu huta mana bai musa mata ba dan shi kanshi juriya kawai yake amma bayajin zai iya tafiya mai nisa bai fadi ba Zaunawa sukayi suka jinginu da katuwar bishiyar dake wurin suna maida nunfashi sun jima ahaka kafin suka fara bin wurin dakallo se alokacin suka fahimci ba karamin daji suka shigo ba dan gaba daya wurin manya manyan bishiyoyi ne azagaye dasu kasan kuma ciyayi ne da ramummuka iri iri Adan tsorace asma'u tamatso kusan AK cikin rada tace ABI nan ina ne jinginar dakansa yayi jikin bishiya yana lumshe ido cikin dasashshiyar muryansa yace da a maiduguri muke dase ince wannan shine dajin sambisa amma yanzu bansan mezan cemaki ba shiru tayi nadan lokaci tana kallonsa sannan ahankali tadafa kafadansa cikin sigar tausayawa tace kanajin zafi ko Dagowa yayi yakalleta suka hada ido sannan yaballe bottom din rigarsa yafito dakafadansa yana murmushi yace ba sosaiba nagode allah bakida nauyi sosai da yau namutu Murmushi tayi da hawaye afuskanta tadora hannunta kan kafadarsa tana shafawa ahankali Jinginar dakansa yayi jikin bishiya idonsa alumshe yana jin dadin shafawar dakate kaman tana Sosa mai wurin ne juyo dakansa yayi yana kallonta ahankali yace kinajin tsoro ? Gyada kai cikin rawar murya tace eh amma basosai ba Kaifa? Murmushi yayi yana kallon wurin dasuke baice komai ba maidamasa wuyan rigarsa tayi tana maida masa maballan alokaci guda suna kallon junansu suna jin wani yanayin dasuka kasa fassara shi Mutsa bakinta tafarayi ahankali tana ji kamar tagayamasa tana sonsa amma kuma tana tsoron mezai biyo baya Suna cikin haka sukaji wani gurnani gurrrrrr atsoarace suka kalli juna cikin rawar murya asma'u tace ABI did u hear that ?? Kai ya gyada mata yana waige waige sekara shigema juna suke gurnanin suka kara ji anyi atsorace asma'u tarungumeshi da karfi tana jero addu'a Dariya yayi yana rike ciki yace chitti ba komai bane ciki nane fah Kallonsa tayi da mamaki tace cikin ka fah ABI wannan fa kamar zaki ne ko damisa janyeta yayi daga jikinsa yana shafa cikinsa yace cikina ne yunwa nakeji yau ba abunda naci tun jiya rabona da abinci itadai bata yarda ba se bin wurin take da kallo tana karanto duk addu'ar datazo mata tun yana mata dariya har shima yafara tsorata dayanayin wurin yafara tasa addu'ar Washegari dasafe dai daga cikin yaran JJ yafara tashi yaga ba su AK hankali tashe yatashi sauran yasanar dasu afusace JJ ya hausu dafada kamar su suka kwancesu bashiri ya rarrabasu acikin dajin suje su nemosu hankali tashe suka bazu nemansu hardashi JJ kuma yayi alkawarin yana ganinsu zai kashesu kowa yahuta tun safe ahmad yaje police station suka fara shirin fita Neman su agidama haka sun dage da addu'a tun suna kuka har sun hakura sun barma allah gidajan biyu sunzama tamkar gidan mutuwa Sam ba walwala ba farin ciki acikinsu lokaci guda khadeeja tarame tafita hayyacinta kowa yaganta seya tausayamata kowane lokaci suna waya da ahmad yana kara kuantar mata da hankali bangaren sarah ma abun yafara damunta saboda bata San halinda AK yake cikiba dan tasan idan dai JJ yagansa bazai kyaleshi ba aysha ma haka tana mamkin rashin dawowar AK tunda JJ yacemusu yakashe asma'u gashi kuma sunji shiru suna kiransa basa samunsa Kuance suke suna bacci hankali kuance AK yadora kafansa kan cikin asma'u ita kuma tayi reran dayan hannunta kan kirjinsa ahankali tafara bude idanuwanta tana bin wurin da kallo saurin tashi tayi tana ture kafan AK daga jikinta tafara tashinsa gyara kuanciyarsa yayi cikin muryan bacci yace chitti bring my coffee kafinnan zantashi Dariya tayi tana daddabashi tace wane kalan coffee kuma ABI kamanta inda muke ne janye hannunta yayi daga kan kafadarsa idonsa arufe yace jiya nayi wani mafarki mai ban al'ajabi idan kin kawomun coffee dina se inbaki labari Ganye ta tsinko tadora akan bakinsa tana dariya tace ba coffee sedai dambun nama inzakaci saurin tashi yayi zaune yana kakkabe bakinsa lokaci guda yana bin wurin da kallo Runtse idanuwansa yayi yakara budesu yanaso yatabbatar ko dagaske ba marfaki yayi ba tashi zaune yayi dakyar yayi mika yana salati kamar daga sama sukajiyo Tafiyar yaran JJ suna nemansu atsorace suka kalli juna suna mikewa tsaye asma'u ta cakumo rigarsa cikin rawar murya tace ABI... mun ..shiga uku za..... Bata karasaba yaja hannunta aguje suka cigaba da gudu suna kara kutsawa cikin dajin seda sukayi nisa sannan suka fara tafiya suna Jan kafa kamar bugaggu ga kishi da yunwa dasuka addabesu karfin hali kawai AK yake amma tuni yafarajin asman shi na kokarin tashi Tafe suke shi agaba ita abaya sekara kutsawa cikin dajin suke Karasowa asma'u tayi kusa dashi cikin dasashshiyar muryanta tace ABI I am hungry baijiyo yakalleta ba yace gani kici Dariya tayi tace ai koda inacin naman mutane ba'abunda zanyi danaka dan dagani ba dadi zai yiba Shiga gabanshi tayi tana rike cikinta kamar zatayi kuka tace ABI dagaske yunwa nakeji kuana biyu fa ba abunda naci ko ruwa bansha ba Kafadunta Yakama ya juyar da ita sukaci gaba datafiya yana fadin chitti ki kalli nan wurin da kyew kigani banda ciyayi da bishiyoyi ba abunda keda kwai Idan bamuyi gaggawan barin wurinnan ba mune zamu zama kalacin namun daji Saurin juyowa tayi tana fadin 😧namun daji fa kace kana nufin akwaisu anan Dariya yayi yawuce gaba yana fadin awannan dajin miye baza'a rasa ba kima kula da inda kike sa kafanki kar ki taka maciji saurin bin bayansa tayi tana riko hannunsa tace to wai aganinka suwaye wa'yannan kuma meyasa suka kamani "Ke baki sani ba taya za'ayi ni insani Shiru tayi batace komai sukaci gaba datafiya batare da sunsan inda suka nufa ba amma kowane da tunanin dayake aransa Tuni ahmad da yan sandan suka shigo dajin sedai abun takaicin basusan ta ina zasu bi sufara nemansu ba hakanan dai suka rarrabu gida uku sukashiga dajin dafatan ganin su ko ko sukama yan daban agida kuma tun safe grany da inna ameena suka je gidansu asma'u aka taru acan ana taya juna jaje da addu'ar allah yabayyana su har yanzu JJ nacigaba da nemansu AK acikin dajin nan saboda yanada tabbacin bai isa sunfita daga dajin ba dan yanada girma sosai za'ajima kafin akai kyawyukan dake kusa dawurin suna cikin tafiya asma'u tarangada ihu atsorace AK yajiyo yana duddubata yaga ko wani Abu yasameta Tsalle tafara cike dafarin ciki tana nuna mai bishiyar mangoron datahango tace ABI kalla kaga mangoro acan wallahi mangoro ne tsaki yayi yana kallon bishiyar mangoron shi kanshi tabirgeshi bai San lokacinda yasaki wani lallausan murmushi ba suka nufi wurin dutse yadauka yafara jifan mangoron amma yakasa samun koda guda dayane labace baki tayi kamar zatayi kuka tana kallonsa tace ABI haka bazai yiba kahau mana katsinko Baki yasaki yana kallonta yace nahaufa kika ce wannan katuwar bishiyar nasan miye akai haka kawai ke ki hau mana tureshi tayi daga wurin tana fadin yo se in hau mana ai ba yau nafara ba bishiyar ma dako tsawo batada Matsawa yayi yabata wuri tafara kokarin nawa se dariya yake yana tafa hannu yana fadin chitti!!!chitti!!!chitti!!! Tafara hawa kenan tayo kasa zata fadi yayi saurin tareta tafado kansa suka fani kasa tare Dafe bayansa yayi yana runtse ido hade dasakin yar kara atsorace ta riko gefen fuskarsa tana fadin ABI are u ok kaji ciwo ne ? Bude idanuwansa yayi yasaukesu cikin nata suna kallon juna nadan lokaci sannan yatureta yana fadin Dallah malama tashi sama na dama nasan dagangan kikayi Saurin tashi tayi tana Sosa kai Dakyar yatashi yana dafe baya yace dama zan samu naman dajin dazai cinye mun ke koba komai kashi hamsin na matsalolina zasu ragu Nuna mai mangoron tayi tana lashe baki tace please .... Bata karasaba yatattare kafan wandonsa yahaw bishiyan yafara tsinko mangoron yana jefomata Ita kwa se dauka take tana Tarawa ga daya ahannunta tana sha Lekowa yayi daga saman bishiyan yana kallonta yace to kijira insauko mana asha tare haka ake ni da wahala keda jin dadi seda suka Tara mai yawa sannan ya sauko suka zauna awurin Sunasha suna fira gutsuran mangoro yayi yadago yana kallonta yace Chitti acikin namun daji wanne yafi hadari Dgowa tayi tana kallonsa da mangoro abakinta tace me kadaukeni ne ABI ai kowa yasan zaki yafi hadari Dariya yayi sannan yakai mangoro bakinsa yana lumshe ido yace to shi zaki baida wani hadari saboda idan dai zaki iya dake nunfashinki kiyi kamar kinmutu to sedai yayita zagayeki ba abunda zaimiki kinsman bayason mushe yafiso yakashe dakansa sannan yaci tunda yafara magana take kallonsa baki bude seda yagama sannan tayi dariya tace kaidai kawai sha mangoronka amma wane dauke nunfashi mutum zai iya yi ga zaki na kewayashi dariya yayi yace to kindai fadi wannan fadi wani Zari ido tayi tana kallon macijin dake bayansa cikin rawar murya tace ma.....maciji Dariya yayi yace kaji wai kuma maciji yo miye hadari awurin maciji ai shi kina ganinsa kawai kiyi kokarin taka kansa se kisa hannunki ahankali ki kamo wuyansa kirike gam to kin gama dashi ba'abunda zaimiki Mikewa tayi tana wurgi da mangoron hannunta atsorace tace ABI ....maciji....abayanka zunbur yamike yana duba bayansa yana ganin macijin yadaga uban tsalle yabi tagaban asma'u aguje har yatafi yajiyo yaganta atsaye takasa motsawa se yarfa hannu take bashiri yadawo yaja hannunta suka bar wurin seda sukayi nisa sannan suka tsaya ai kwa nan asma'u tahau kwasan dariya tana tsokanarsa banza yayi da ita yayi gaba yana jinyar kirjinsa dake masa azaba amma ko kadan bayaso asma'u tagane halin dayake ciki suna cikin tafiya ta taka wata gundumemiyar kaya durkushewa tayi awurin tana sakin yar kara tana kallon kafar Saurin dawowa AK yayi wurinta yana mata sannu Hannu yakai zai taba kafar amma taki bari se rike hannayansa take

Chapter 20 of 35