Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
musu. Ummana Fuse ta yi mamaki da ganin yadda dangin mahaifiyarmu ke da yawa kuma akwai masu rufin asiri. Har ta bude baki ta yar musu da magana, ta ce, ''ashe kuna son su amma ku ka tankada keyarsu Ghana? Sai kuka yi wuki-wuki, mu ma kunya ta rufe mu, ni da Khausar. Da Shamsuddin ya ta shi zuwa, sai ya taho tare da danginsa maza hade da kudin aurensu, har sadaki. Sai muka karba aka tsayar da maganar aure. Bayan wata guda har ya hada lefe mata suka kawo, aka daura uare gami da *yar kwarya-kwaryar liyafa. Muka rakata har katafaren gidanta na Mina. Bayan danginsa sun gan mu sai muka dungumo Accra tare da su ango da amarya nan ma aka gabatar da angon Khausar da dangin Babanmu. Na sha zagi dai ba adadi saboda na kai Nigeria dangin uwata sun daura mata aure. Ban damu da surutansu ba saboda na san ni da kakata ne kadai muka raine ta babu wanda ya san cinta da shanta a cikinsu. Khausar ta yiwa Accra sallama ta biyo mijinta mai sonta zuwa Abuja, a nan suke da zama din-din-din. Yanzu haka *ya*yansu uku, haihuwarta biyu na farkon tagwayene, mace da namiji Habiba da Abdul-Sabur, sai na biyu mace ce aka saka mata sunan Ummana Fuse, wato Usaina. Nima a Gwarzo na sayi fili na yi mana katafaren gini inda idan muka je mu dinga sauka a unguwar iyayen Mahaifiyata. A Kano kuma a kusa da dangin Malam Barau na yi gini don a nan na saba duk da ya rasu ina taimakawa iyalansa a koda yaushe. WANNAN SHI NE LABARINA. Umaimah da Faduwa har lumshe ido suke yi saboda dadin labarin da Abdul-Sabur yake ba su sun fi jin dadin labarin da aka zo gurin ci gaban rayuwarsa sai suka ji tamkar almara saboda komai yana tafiya yadda ya kamata. Umaimah ta yi murmushi ta dubi Abdul-Sabur ta ce, 'To a ina ka yi karatun kur'ani, ka sami ilimin addini haka? Abdul-Sabur ya yi dariya ya ce, 'Duk inda na je kuma ko me nake yi ina samun makarantar islamiyya na shiga. Kinga da farko daman na fada muku da girmana na shiga makarantar boko kinga tun tashina a makarantar allo nake, anan na koyi baki na iya rubutu a allo na da kaina. Sai da nayi nisa sosai muka tashi daga Kano muka koma Gwarzo a can ma na shiga allo ko sanda na shiga sakandire ta kwana idan anyi hutu ina ci gaba da zuwa. Da muka dawo Ghana Ummana Fuse ta saka mu a islamiyya a nan na koyi Fikhu da Hadisai. Da na dawo Ingila duk ranar asabar da lahadi muna zuwa gidan wani Balarabe mutumin Syria ne yana koyar da mu Kur'ani da Hadidai. Da na fara zuwa Indonesia sarinn kaya ina zuwa wajen malamai daban-daban ina neman ilimi, ina samun karuwa da tasu baiwar. Na yi saukar kur'ani mai tsarki fiye da sau goma, yanzu haka na haddace shi ina sake maimaitawa. Umaimah da Faduwa suka jinjina kai, Faduwa ta ce kaji dadi, ni ma dai na yi sauka tun ina yarinya kafin na gama sakandire, daga baya boko ya hana ni ci gaba. Amma ina da burin ci gaba da karatun addini a kasar nan idan na nutsu na ga akwai makarantun matan aure na islamiyya. Abdul-Sabur ya ce, ''Yana da kyau a nemi ilimin gaskiya. Ke fa Umaimah ba kya sha'awar shiga islamiyya? Ta yi murmushi, ta ce, ''Ina da niyya idan Allah Ya so zan shiga nima. ''Kin yi nisa ne a kur'ani? Abdul-Sabur ya tambaye ta cike da zumudi. Ta yi dariya ta gyada kai ta ce, ''Alhamdulillah, ni ma dai na sauke kur'ani tun ina matashiyam bayan na girma na ci gaba da karatun har na fara hadda. Abdul-sabur ya ji dadi da jin haka, da ya zaci Umaimah jahila ce da yaga yadda take danne hakkin MAKWABTAKA. Ya yi murmushi ya ce, ''Alhamdulillah, mu dukka mu godewa Allah da Ya ba mu ilimin saninSa. Allah Ya ba mu ikon yin amfani da shi. Su dukka suka ce ''Amin. Faduwa ta gyara zama ta ce, ''Abdul-Sabur ba ka gama labarinka ba. Ban ji ka yi maganar matarka da *ya*yanka ba. *Yar ina ka aura, Ghana, Najeria. Ingila ko *yar Indonesia? Abdul-Sabur ya kwashe da dariya, ya ce, ''Kai Faduwa ta yaya za ki jero min wadannan kasashe Ingila da Indonesia daga zuwa ci-rani sai na hau yin aure? Ai ba zan yi wannan kuskuren ba, na auren matar da ta ke wata kasa wacce ba kasata ba. Ashe zan maimaita kuskuren da iyayena suka tafka, suka haife mu muka shiga garari a duniya ba tare da mun san dangin da zamu bi ba, duk a rarrabe?. Faduwa ta ce, ''Yar Accra ko Kano ka aura? Ya sake yin dariya ya girgiza kai, ya ce,, ''Babu ko daya wallahi. Faduwa ta harare shi, ta ce, ''Ban fahimce ka ba kana nufin ba ka taba yin aure ba ne? Ko dai kun rabu ko ta mutu? Umaimah ta dube shi ita ma cike da rashin yarda ta ce, ''Me kake so ka ce mana, ba ka da mata? Matar da na ganka tare fa a Saudia kuna dawafi ka dafa ta? Faduwa ta gyada kai, ta ce, ''Af har ma kin taba ganinsu ko? Da har zai boye mana. Ai na san kana da mata, tunda baka dadewa sai ka je gida ka gan ta sannan ka dawo. *Ya*yanka nawa? Har yanzu Abdul-Sabur dariya yake yi musu ya kasa amsa jerin tambayoyin da suke jeho masa. Can ya yi ajitar zuciya ya gyara zama ya dube su, ya ce, ''Babu maganar boye-boye a tsakaninmu, ku kannena ne tamkar na jinina mun zama daya. Ban yi aure ba har yanzu balle na sami *ya*ya, ga shi kuwa wannan shekarar zan cika shekaru arba'in a duniya. Na zama tuzuru nima kamar Faduwa. Su dukka ukun suka kyalkyale da dariya. Faduwa ta ce, ''Kai ai namiji ne, kai zaka nemi aure kuma duk irin wacce ka nema zata so ka saboda kana da kudi, kyau da ilimi. Watakila dai zabe kake yi har yanzu kana ruwan ido. Abdul-Sabur ya kyalkyale da dariya ya ce, ''Haka ne, amma dai yadda kike tunani ba haka nake ba. Ni dai kawai ba ni da ra'ayin auren ne saboda a tsorace nake da matan, kuma mata suna sona su yi ta bibiyata ina zukewa. Tunda nake a rayuwata ma sau daya na taba yin budurwa wacce na ji ina sonta har na taka gidansu da sunan hira, sunanta Aminat a Ingila muka hadu, asalinta *yar Bauci ce. Ta so ni sosai, ta so na aure ta na ki saboda wasu dalilaina. Yanzu ta yi aurenta har ta hayayyafa a garin Manchester gidanta ya ke. Yanzu dai a takaice Allah ne bai kawo lokacin yin auren ba, da zarar ya zo sai ku ga Allah Ya hada ni da matar, sai mu yi aure mu hayayyafa. Ko ba haka bane *yan mata? Umaimah wannan matar da kika ganni tare da ita a Saudia ba wata ba ce, kanwata ce Khausar. Tana son zuwa Umra duk shekara mijinta kuma ba shi da lokaci koda yaushe to da naje Najeriya a cikin hutu sai ta ce na yi mata namijin biza mu je muyi umarar kwana biyar, shi ne kika gan mu tare. Ita ma haka ta tutsiye ni da tamabaya wai ina na sanki, ko dai ke budurwata ce. Sai na fada mata ke makwabciyata ca a Malaysia, da farko ta ki yarda amma da nayi mata rantsuwa sai ta yarda daga baya, don dai ta san bana yin budurwa. Su dukka ukun suka yi dariya a lokaci guda. Abdul-Sabur ya dubi Faduwa ya juya ya dubi Umaimah, ya ce, ''To *yanmata kunji tarihin AbdulSabur daga farko har tsakiya, Allah ne kadai Ya san karshen abin da zai faru. Idan akwai mai tambaya ta tambaye ni akan abin da ba ta gane ba, ko wanda na manta ban fada ba. Suka yi dariya, Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Babu tambaya, ni dai a nawa bangaren. Allah Ya jikan wadanda suka rasu, mu kuma Allah Ya kyautata namu zuwan. Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Amin, na gode kanwata. Faduwa ta ce, ''Allah Sarki Abdul abokina, dan uwana, maraya kuma tuzuru. Allah Ya jikan iyayenmu, Ya bamu abokan zama na gari. Abdul-Sabur ya kyalkyale da dariya ya ce, ''Faduwa kin cika abin dariya, koda yake addu'a ce mai kyau. Amin Ya Rabbu''. Abdul-Sabur ya juya ya dubi Umaimah wacce ta yunkura tana shirin tashi ta tafi. Ya ce, ''Kin ji tarihinmu, yanzu kin san mu, kin san asalinmu. Ko zamu iya saninki ke ma?. Ta mike tsaye gaba daya tana murmushi, ta ce, ''Eh, za ku san ni, amma sai nan gaba. Yanzu zan tafi gida, ina da *yan aikace-aikacen da zan yi. Ai muna tare, komai daren dadewa tunda kun hana ni tashi daga gidan nan, za ku san ni. Faduwa ta jawo hannun Umaimah ta zaunar da ita, ta ce, ''Babu inda zaki je, yau a nan zamu yini har la'asar. Sai kin bamu tarihinki kamar yadda kika ji namu.'' Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce ''A,a kada ki takuta mata Faduwa, ki bari a hankali wata rana sai ta bamu. Faduwa ta ce, ''Wannan yarinyar, lallai ba ka san halinta ba, yanzu idan ta shige gida ba zamu kara ganinta ba, ko mun buga ba zata bude ba''. Suka tuntsire da dariya su dukka, Umamah ta ce, ''Ai da ne, yanzu ba haka ba ne, za ku ganni mana. Faduwa ta ce, ''Ni dai ban yarda ba, yanzu nake so a bani labari na ji. Umaimah ta ce, ''To zan bayar, amma ki bari na je gida na yi sallar walha tukunna, sai na dawo. Kina ganin har goma da rabi ta yi''. Faduwa ta ce, ''To muje na kai ki ban daki sai ki yi sallar a nan, ni fa har yanzu tsoronki nake''. Umaimah ta yi murmushi kawai ba ta ce komai ba, tana biye da ita har katafaren dakinta a inda kayataccen ban dakinta yake ciki. Gidajen iri daya ne har kayan ciki, yadda na Umaimah yake haka sak na Faduwa ma. Gida ne mai dauke da dakuna biyu babban daki da bandakinsa a ciki, sai wani karamin daki, bandakin kuma a waje (coridor). Kowanne daki da gado, madubi da durowar kaya da labulaye na alfarma kalar kore (lemon green), sai katafaren falo mai dauke da dinning area duk an zuba kujeru da dinnin table da labulaye koraye. Kicin ma babu abin da ba'a saka ba, kama daga injin wanki, gas cooker, firij da duk wani abun da ake bukata a kiicin kamar tukwane, farantai, cokula. Kofuna da dai sauransu. Duk kasan gidan tiles ne launin kore da fari, haka kofofin gidan farare ne sun kayata. Faduwa sarkin kwalliya, ta kayata bandakinta da kyalkyali, komai ruwan hoda ne (pinc color). Umaimah ta yi sha'awar bandakin nan tas-tas kamar mutum ya kwanta ya yi bacci. Da ta idar da alwallar sai ta fito ta iske Faduwa har ta yi mata shimfida da sallaya da tsaftataccen hijabi. Umaimah ta yi godiya yayin da ta shiga saka hijabi ta fara haramar yin sallah. Faduwa ta fito daga daki ta iske Abdul-Sabur ya fito daga daya bandakin ya dauro alwala shi ma. Ta yi sauri ta shimfida masa abin sallah a falo ya tayar da ikama. Faduwa ta yi murmushi ta ce, ''Wato ku dukka sallar walha ku ke yi ashe, ni kadai ce bana yi? Gaskiya da sake, na daina yarda kuyi min wayo, ni ma zan yi wa kaina fada na fara yi. Tana gama magana ita kadai, har ta shiga kicin a inda ta bude firij ta dauko dankwaleliyar kaza a gidan kankara ta shiga wankewa, ta bankare ta ta zuba mata kayan hadi, yayin da ta turmutsa ta a cikin oven don gasawa. Kan ka ce kwabo kamshi mai dadi ya gauraye gidan, ta fara tururi. Yayin da ta dora shinkafa fara amma fa irin dahuwarsu ta *yan Egypt. Farar shinkafa ce ake dafawa kafin ta dahu sai a saka gishiri, maggi, koren wake (green beans da peans), karas sannan a yayyafa dan man kuli. Ba sai an yi miya ba, sai a ci hade da gashasshiyar kaza. Kafin su idar su hallara a falo har Faduwa ta fara jera musu abubuwa akan dinnin table. Kamar ruwa, lemon (juice) ayaba, lemo, abarba, kayan shayi da dai saauransu. ''Abincin mai zamu ci kuma yanzu bayan mun yi karin kumallo? Umaimah ta tambayi Faduwa a lokacin da ta ke duban ta tana dariya. Faduwa ta yi dariya ta ce, ''Abincin hantsi zaku ci. Na ga duk ba mu ci abincin ba dazu saboda tashin hankalin labarina, duk muna kuka, ruwan shayi kadai muka kukkurba. Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Ruwan shayi ma ai abinci ne, ni ba don ku bama da ba zan karya ba, don ni bana yin karin kumallo ma kwata-kwata. Ai shi yasa kike ta sake dunkulewa kina yin kiba kin cika ci. Suka kwashe da dariya su dukka, Faduwa ta ce ''Au tsiya kakemin a gaban kanwata? To zan rama''. Umaimah ta ce, ''Mu je kicin din na taya ki aiki, ko nima na koyi irin abincinku na Larabawa. Na ji kamshi sai fitowa yake yi. Faduwa ta wuce gaba, Umaimah na biye da ita har kicin a inda Faduwa ta shiga yi mata bayanin abincin da ta ke dafawa da yadda ake yi. Tabbas Umaimah ta karu don ba ta taba sanin irin wannan launin girkin ba, don ba irin namu ba ne na Hausawa. Suka karasa yi tare suka zo suka jere akan dinnin table, kamshi ne ke tashi tururu. Da suka gama shiryawa sai suka gayyaci Dan Aunty zuwa kan tebur. Lolx.. Kowa ya maida yawun sa ni kadai aka gayyata banda gayyar sodi. Gani ga... Alhamdulillahi. En uwa ina godia a gareku na nuna kulawa da soyayya da kuka taimaka mana da Addu'oi daga bakunan ku masu Albarka. Alhamdulillahi. Masu jiki da sauki sosai dan daya yayan nawa an sallame shi saura kanin namu. Allah yasaka muku da Alkhair. Ina mai kara godia a gare ku baki daya. Allah yabar xumunci. MAKWABTAKA 17 Da suka gama shiryawa sai suka gayyaci Abdul-Sabur zuwa kan tebur. Tun kafin ya karaso ya hango abincin gwanin ban sha'awa, kai ka ce a hadadden hotel suke. Gwanin sha'awa idan ka kalla, haka kamshinsa abin so ne balle ka kai baki ka ji dandanonsa. Cokula (forks da spoons) da faranti (plates) aka ajiyewa kowannensu a gabansa, ga kufuna da robobin lemuna (juice) kala-kala, shinkafa da kaza suna manyan farantai. Faduwa ta shiga daddatsa dankwaleliyar kazar nan gashasshiya gunduwa-gunduwa. Kowa ya shiga zuba daidai cikinsa da kansa. Yayin da sanyin A.C ya fara ratsa hudojin jikinsu, sanyin lemon ya dinga kwaranya a cikin hanjin jikinsu. Sannan dadin abincin ya daki harshensu zuwa tumbinsu. Nan da nan kowannansu ya tsinci kansa yana cikin farin ciki da annashuwa a fuskokinsu. Abdul-Sabur ya hadiye lomar abincin da yake tauna a bakinsa, ya kora da lemo mai sanyi (apple juice) ya dubi Umaimah ya yi murmushi. Ya ce ''Muna sauraronki Umaimah, layi ya zo kanki''. Faduwa ma ta kura mata ido kallo ko kyaftawa ba ta yi, daga dukkan alamu ita ma ta kagu ta ji abinda Umaimah zata fada. Cikin jin kunya Umaimah ta yi murmushi, ta sunkuyar da kai kasa. Can ta dago ta dube su daya bayan daya, sai ta yi fari da ido. Ta ce, ''Yau dai kun rantse sai kunji labarina ko? To babu damuwa ku bude kunnuwanku da kyau ku ji tarihina mai taken MAKWABTAKA''. Ai kuwa sai taga suna gyara zama, gami da sake miko hankalinsu gaba daya a kanta. LABARIN UMAIMAH. ''Sunana Umaimah Muhammad Bello, muna kiran mahaifinmu da suna Baffa, mahaifiyata kuwa sunanta Mariya ita ma muna kiranta da Yafindo. Iyayena dukka biyun fulani ne, sun fito daga riga daya, sunan rigarmu Dugge a karkashin karamar hukumar Dukku jahar Gombe, a kasar Nigeria. Mahaifiyata ita ce mace ta uku a wajen Baffa Bello, ta same shi yana da mata biyu, Nene da Inna, kusan su dukkansu sun haife ta ma. Sai dai ba su taba haihuwa ba a gidan, sai a kanta ya fara samun haihuwa. Aka haifi Yayata mai suna Nasiba. Nasiba ta girme min da shekaru biyar, sannan aka haife ni, bayan shekaru biyu aka haifi kanina Sabitu. Rayuwa ce ta kauye daga kiwo, sai noma, surfe da casa, shi kenan sana'armu. A gidan kasa dakin yumbu da rufin ciyawa, sai katangar zana, ba mu da komai bayan wannan. Yaren Fulatanci kadai na tashi na ji ana yi a gidanmu, don yaren Hausa ma sai daga baya na koya a birni. Muna zuwa makarantar allo kadai ita ma makarantar da fulatanci muke karatun, bayan Fatiha babu wani abun da malaman suka iya. Ita kadai na san na koya, duk sauran karatu rawawu fulani ne shirme ne kawai, don haka ilimi ya yi mana karanci a Dugge. Babu abin da *yan mata da yara kanana suke yi mata da maza sai wake a dandali da yamma. Ko kuma a yi wasan shadi idan bukunkuna sun taso, mu taru muna kallo, shi ne babban nishadin *yan kauyen. Abdul-Sabur da Faduwa har lumshe ido suke yi saboda zazzakar muryar Umaimah da daddadan labarinta. Har yanzu harshenta bai warware daga illar lauyewar da Fulatanci ya yi masa ba. Kana jin Hausar ka ji ta Fulani, amma sai hakan ya sake dadada yaren suka ji tamkar ba yaren da suka iya ba ne. Hausa ta fi dadi a bakin Umaimah fiye da a bakunansu. Don Abdul-Sabur Hausar *yan Ghana ce fal a bakinsa, yayin da Faduwa kuwa ta larabawa ce wasu kalaman dai sai dai ta soka da Larabci. Umaimah Bello ta yi murmushi, yayin da fararen hakoranta suka sake haskaka, sai kyawunta ya sake bayyana. Ta ci gaba da cewa. ''Ba kamar ni ma ina son wasan gada, raye-raye da wake-wake, da son kallon shadi da garaya. Idan aka zo dandali kika fito kina waka kawayenki sai su yi miki amshi su wake miki saurayinki. Da yake tun muna *yan shekaru biyar-shida kowacce za a lakaba mata saurayin dandali, wasu su zarce har su girma ya kai su ga yin aure, wasu kuwa na yarinta ne su zubar da samartakan a dandali. Sunan saurayina Isma'il, ana kiransa da Ilah makwabcinmu ne, katangar gidanmu daya, daga hannun dama. Ilah ya girme min sosai, sa'an yayata ne Nasiba tare aka yi goyonsu, babu wanda ta hadamu samartaka a dandali, shi ne daman ya ke matukar sona tun ina goye a baya. Duk da ni ban san so ba amma na tashi na budi ido da shi yana yawan kyautatamun a rayuwata. Kullum sai ya siyo min rake, mangwaro, ko ya tatsomin nono da madara kullum ne wannan, saboda mahaifiyarsa tallar nono ta ke yi kasuwa-kasuwa. Mahaifinsa na da garkunan shanu guda biyu suna kiwo. Ilah shi ne karami a gidan, kuma su dukkan yayyansa maza ne guda hudu ba su da *ya mace ko daya a gidan, kuma mahaifiyarsu ita kadai ce mata a gidan, ba ta da kishiya. Muna kallonsu a matsayin masu arzikin Rugarmu. MAKWABTANMU daga hannun hagu kuwa gidan Baffa Modibbo ne, suna da *ya Zahra'u. Zahra'u kawata ce sosai, tare aka yi goyonmu ma, kamar yadda muka tashi muka tarar da Innarta da Yafindona suna kawance mu ma sai muka jone. Kowa yasan tauraruwar nan da ta fi sauran taurari haske, wato 'ZAHRA' da ake cewa matar wata ce saboda a koda yaushe tana kusa da wata. To itama kawata Zahra'u ana kiranta da 'Matawata', babu ma wanda yake kiranta da Zahra'u a garin, kowa da Matawata ya san ta. Ni da Matawata koda yaushe muna tare kanmu daya, farinmu daya, yanayin jikinmu daya, har ma ake cewa mun juye kamarmu daya kamar wasu tagwaye. Allah Ya dora min tsananin sonta kamar yadda nake son Sabitu da Nasiba, komai a bani a gida ko a waje sai na boye na rago mata, haka ita ma ta ke yi. Tun iyayenmu suna dungure mu su yi mana fada har suka fara kashi da mu. Don haka a gidansu ina da kasona, haka itama a gidanmu idan dai Yafindo ce ta yi rabo zata raba da Matawata. Dan haka hasken Zahra ya haskakamin fuskata zuwa zuciyata ita ce kadai wacce na fi so a cikin kawayena na Dugge da kewaye. Ita ma tana da saurayi a dandali mai suna Lawwali, kusan sa'anmu ne ko ya girmemu da kadan. Muna ta ji dadin rayuwarmu a haka, don mu ba mu san akwai wani jin dadin rayuwa ba a duniya wanda ya wuce haka. Duk ranar asabar kasuwar garinmu ta ke ci, mu dunkule *yan nairorinmu nu je mu yi siyayya kamar Aya, Rogo, Gyada, Magarya, Kurna, Kuli-kuli, mu yi kallon Garaya da Shadi ko kalankuwa mu dawo gida. A kasuwar muke haduwa da fulanin wasu garuruwan kusa da garinmu kamar *yan Konare, Nzagala da Shuwe. Mu ma ranar kasuwarsu muna zuwa mu saya mu sayar. Idan muka je rafi dauko ruwa sai mu shiga mu yi ta wanka har sai an turo babba ya koro mu, don ba zamu kawo ruwan da wuri ba, idan tukunya ce ta tuwo aka dora har sai an sauke saboda ba mu kawo ruwan girkin ba. Daman ba mu tashi mun ga ruwan famfo ba balle wutar lantarki, fitilar kwai ce mai lagwani da kalanzir, ko aci-bal-bal fitilar kwalba a zuba kalanzir da tsumma a kyasta ashana ya dinga ci a hankali..... Faduwa ta zazzare ido, ta ce, ''Kuna iya rayuwa babu firij ba fanka?'' Umaimah ta yi dariya, ta ce, ''Ba mu san shi ba balle mu saba da su. Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Wannan ita ce rayuwar *yan Africa ziryan. Ci gaba da labarinki Umaimah don ina jin dadin sauraronki. Da ace Turawa za su ga garinku da sunyi fim da *yan garin don su irin wannan rayuwar suka fi so. Umaimah ta yi murmushin takaici tare da ciza lebenta, ta ce gaba da cewa. ''Muna da Sarkinmu, wato Dagacin garinmu da *yan fadarsa irin su mahaifina dattijan gari, shi ne mai fada a ji, su ne masu yin shari'a idan rigimar gado ta taso, ko rigima akan shanu, ko rigimar manoma da makiyaya da rigingimun cikin gida tsakanin kishiya da kishiya ko mata da mijinta, duk dai wata rigima. Ana tsoron hukuma don haka kowa yake ta kiyayewa ana zaune lafiya sumul babu tashin hankali. Cikin gidanmu rigimar da sauki, saboda mahaifinmu a tsaye yake akan iyalansa dai-dai karfinsa yana ba wa kowacce mata hakkinta. Daman dai bai wuce ranar girkinki ba ya bude rumbu ya auno miki dawa ko Gero kwarya daya, sai ya dora miki da *yar Murtala (naira Ashirin) kudin cefane. A ciki zaki sayi abin kadi ki yi tuwo da miyar kuka ko kubewa ba nama, sai dai ki watsa wake a ciki idan da hali. Daman wannan a aje yake, ke zaki zuba a turmi ki surfa, ki bakace ki dake har sai ya zama gari. Daga baya ne ma injin tahuna na surfe da nika ya shigo garinmu mata suka huta da dakan hannu ko nikan dutse. Idan mun gaji da cin tuwo sai a matso nono a sha da fura, ko kuma a yi mana dawa da wake, dambu, fatefate, ko gero da wake. Ko kuma wasa-wasa. Shinkafa kuwa daman sai ranar sallah kowanne gida ake yin tuwonta, ita din ma dai *yar Hausa. Nama kuwa sai a layya wasu gidajen kalilan ne suke iya yanka Akuya ko Bunsuru. Shanu da Raguna kuwa na kiwo ne ba na ci ba, ban ki ba dai idan Sa ya kasa dole ne a yanka a kai kasuwa a siyar a cika a sayo wani, a ci kadan daga cikin naman. Don haka dukkanmu muke tafiya a kemare saboda babu abincin da zai gina mana jiki. Duk wannan labarin da nake baku dukka shekaruna ba su wuce takwas ba a lokacin. Bikin nadin sarauta ya tashi a Gombe, aka gayyaci Dagatan kauyukan da jama'arsu don su je taya murna hade da duk wani dan wasa da za,a nishandantar da bikin. Dagacinmu ya zazzabi *yan matan garinsa wadanda suka kware da iya wakoki da rawar Fulani za a kai su wajen taron. Nasiba yayata tana daya daga cikin *yanmatan da aka zaba zuwa birni. Ita ce ma zabiyar da zata bada waka,, sauran su yi mata amshi, saboda Allah Ya yi mata kyau da zazzakar murya. Fara ce sol tamkar Balarabiya ga kyawun kirar jiki, don haka samarin kauyen suke ta shan dambe a kanta saboda kowa yana so. Mu kanana ne ba a zabe mu ba, don kada muje mu bata a cikin taro. *Yan mata goma sha biyu aka zaba, *yan samari biyar sune masu kada musu ganga da garaya da kuma yi musu goge. Abin gwanin ban sha'awa aka koyar da su duk irin rawa da wakokin da zasu yi a wajen. Ranar taron aka ba su sababbin atamfofi suka saka iri daya aka zuba su a mota suka tafi, yayin da sha'awarsu ta lullube duk wanda ba a tafi da su ba. Na sawa a raina zan dage da iya rawa da rera waka kafin na girma don ni ma a tafi da ni nan gaba. Ilah saurayina ya ci sa'a an tafi da shi, ya yi min alkawari zai siyo min *yar tsana da kifi a birni. Suka kyalkyale da dariya su dukka ukun. Faduwa ta ce, ''Gaskiya ina jin dadin labarin nan naki, kamar tatsuniya. Mahaifiyata ce ta ke ba ni shigen irin wannan labarin da ina yarinya a matsayin tatsuniya ashe dai irin hakan na faruwa? Umaimah ta nisa ta dago ta dube su daya bayan daya ta yi murmushi, ta tauna naman da yake cike da bakinta ta hadiye. Ta ce, ''Kamar yadda yake faruwa yau Umaimah ta na zama a irin wannan muhalli ba? Gaba daya suka sake yin dariya, sannan Umaimah ta ci gaba da cewa. ''Ba *yan garinmu kadai ba duk Kauyukan da suke karkashin karamar hukumar Dukku suma an gayyace su kamar: *yan garin Birni, Gombe Abba, Konare, Nzagala, Zange da dai sauransu a cikin garin Dukku suka taru a unguwar Se'ngo, daga nan aka debe su zuwa cikin garin Gombe kofar fada. A ranar yini muka yi a karkashin bishiyoyi mu ka ki shiga gida muna jiran dawowarsu. Tun daga safe har zuwa bayan magruba ba mu shiga gida ba sai da suka dawo. Muna ganin dogayen bus guda biyu muka rugo da gudu muna murna. Dagacinmu da jama'arsa ne suka firfito daga daya bus din, yayin da su Nasiba suka fito daga dayar. Su dukka fuskokinsu cike da annuri hannayensu cike da ledoji da alama sun samo kyaututtuka. Nan fa aka hau murna da ife-ife. Wajen Ilah na ruga na ce, ''Ina alkawarinmu?'' Ya miko min *yar tsana da kifina, sai na hau tsalle ni da kawata Matawata. Yayin da bakin ciki ya rufe sauran kawayenmu wadanda ba su da *yar tsana kuma suna tunanin bazan basu aro ba, ba ma wasa

Chapter 9 of 33