Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta kalli jama'ar da suke tururuwar daukanta a hotuna, ta gane Faduwa, ta gane Hanif, sannan da ta sake wurga ido gefenta sai ta hango wani mutum wanda ko a mafarki ta ganshi tabbas bacci zai katse saboda razana. Nan da nan tayi sauri ta kawar da idanuwanta daya gefen don bata son ta sake ganinsa, sai ta yi kicibus da wata fuska wacce take tunanin ko idanuwanta ne suka fara yi mata gezau. Taji zuciyarta ta harba bom! Kai kace tayar mota ce zata fashe. Ta sake bude ido ta dube su sosai cikin firgici da mamaki marar misaltuwa, su dinne dai mace da namiji wadanda bata taba zaton zata gansu a wannan waje ba kuma bata addu'a ta gansu din, dan basu rufa mata asiri ba a lokacin da take neman sutura, suma a hotuna suke daukarta basu daina ba har ta koma kujerarta ta zauna suma sannan suka koma suka zazzauna. Sun ga alamar ta razana da ganinsu kuma ba tayi farin ciki da ganinsu ba saboda tana ganinsu yanayinta ya canja, duk da kuka take yi daman amma tana dariya a cikin kukan, ganinsu yasa ta fashe da kukan takaici hade da fushi. Babu abunda yake yi mata zillo a zuciyarta sai sunayensu ta dinga fada tana maimaitawa. ''Abdul-Basi, Lamijo. Me ya kawo ku wajena? Me yasa zaku zo inda na ke? Me yasa zaku dawo cikin rayuwata, alhali rashin ku ne ya sa na tarki tafiya na rabu na bar *yan uwana da *ya*yana? Sai abubuwan da suka yi mata a baya na rashin kyautatawa suka yi ta dawo mata a jejjere, hawaye ya gagara tsayawa daga idanunta. Ana kiran dalibai suna tasowa a layi suna karbar takardar sakamakonsu. Aisha Bingyal ma ta karbo nata, dukkansu sun karba suna tsalle suna murna saboda kowa yayi kokari dan babu wanda bai fito da sakamako mai kyau ba daga cikin *yan garinsu. Sai dai Umaimah ce kadai baqa data sami 1st slass a wannan shekarar a makarantarsu. Tunda Umaimah ta ga Lamijo da Abdul-Basi bata sake fahimtar abubuwan da ake cewa ba a wajen. Hankalinta ya kada can yayi hanyar waje babu abunda ta fi so irin tabar wajen kada ma su sake haduwa. Ai kuwa babu damar fita dole sai angama sannan kowa zai tashi, ta kagu ma a gama dogayen jawaban nan da ake ta faman yi a tashi. Ta kasa kurbar ko ruwa balle ta figi naman kaji da abinci iri-iri da aka yi ta jerawa kowa a gabansa. An ci, an sha, kamar yadda aka yi a na su AbdulSabur. Da aka kammala taro sai kowa ya tashi ya nufi wajen *yan uwansa, tafiya Umaimah take tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki bata son ta karasa wajen *yan uwanta, badan mutuncin Baban Hanif ba da arcewa zata yi a neme ta a rasa sai dai su hadu a filin jirgi ranar da zasu tafi. Ta ci sa'a Faduwa ta zo ta figo hannunta daga cikin yuyar mutanen da suka baibaye ta suna tambayarta adireshinta da lambar wayarta. Ta cika da mamakin dalilin da yasa mutane suke tambayarta adireshi da lambar wayarta alhali duk fararen fata ne turawa, Indiyawa da kuma *yan Maley. Tabbas haka ake yi a turai wanda Allah Ya bawa wata baiwa ta daukaka zasu dinga tururuwar son yin mu'amala da shi. Abun burgewa ne a gansu da shi sun yi hoto ko ya rubuta sunansa a cikin wani abu nasu hankicin ko dan littafi. Da Faduwa ta figo hannun Umaimah bata dire ta a ko ina ba sai tsakiyar *yan Nigeria a gaban Hanif da Babansa, sai ta durkushe ta gaishe da Baban Hanif. Ya yi mata addu'a mai kyau ya yabe ta sosai kuma ya jinjina mata ya ce ta burge shi yana alfahari da ita. Lamijo ce a gefensa mowarsa kenan, da ita ya zo. Sai kallon Umaimah take kasa-kasa amma bata yi mata magana ba. Darajar mijinta ya sa Umaimah ta ambaci sunanta sannan ta gaishe ta, gami da tambayarta lafiyar Ummarta. ''Lafiya kalau''. Kawai Lamijo ke cewa. Umaimah ta san dai ba dan ita Lamijo ta zo ba saboda Hanif ta zo bata zaci zata ganta ba dan tana yi mata kallo irin na takaici da bakin ciki. Umaimah ta gaggauta barin wajen iyayen kawayenta da wakilan gwamna. Zubewa a kasa kawai take yi tana kwasar gaisuwa cikin ladabi da biyayya. Amsawa suke yi cikin kulawa da kaunarta game da jero mata addu'oin alkhairi. Daga karshe aka jeru aka dinga yin hotuna iri-iri ita da su. Abun mamaki sai ta nemi Abdul-Basi ta rasa a wurin, bata san inda ya kutsa ba, haka bata damu da ta gan shi ba daman. Da suka fito daga ciki sai aka taru a waje daya aka tsayar da shawarar kowa ya koma masaukinsa sai bayan kwanaki uku za'a hadu a 'Royal Bingtang Hotel' da karfe goma na safe in da makarantar su Hanif wato 'Legenda' za su gudanar da nasu bikin suma. Faduwa an sami abunda ake so, dan ita babban burinta shine ta ganta cikin *yan uwanta *yan Nigeria ta shiga cikinsu tayi ta yaren Hausa suna mamaki, sai ta hau basu labarin cewa itama *yar Nigeria ce Babanta dan Sokoto ne. Ta dinga hira da su kamar wacce ta shekara da saninsu, kowa ya ji yana sonta ya na so ya saba da ita har da musayar lambar waya suka dinga yi. Umaimah ta kagu su tafi ta san halin surutun Faduwa bata ki a kwana ana yi ba, dakyar ta jawo ta suka tafi. Umaimah ta bi Faduwa a motarta suka tafi dan bada motarta ta zo ba a motocin makaranta aka kawo su, Faduwa tana tuki ta juya ta dubi Umaimah wacce taga alamar damuwa a tattare da ita sai ta zungureta ta tambayeta. ''Lafiya? Yau ranar farin cikinki, kowacce zata yi fatan ta zama ke. Me yasa kika shiga damuwa? Na ga alamar bayan kukan murna kina cikin damuwa kuma. Umaimah ta sake barkewa da kuka, cikin shesshekar kuka take magana. Ta ce, ''Abdul-Basi da Lamijo na gani a wajen. Shine na ji duk raina ya baci, tunanin abubuwan da suka yi min a baya ya dawo min. Faduwa ta zabura ta ce, ''Haba dan Allah? Ai abun farin ciki ne ke a wajenki, ba shikenan ba sai ku shirya da aminiyarki, ta daina zarginki da mijinta ba. Ga mijinki uban danki shima ya dawo kuje a daura muku sabon aure ku yi zamanku. Umaimah ta girgiza kai ta ce ''Ba saboda ni Lamijo ta zo ba kuma na san bata zaci zata ganni ba anan, ko ma dai menene ya kawo ta bata yi min magana ba, albarkacin mijinta ni na gaishe ta. Abdul-Basi kuwa zai yiwu shi dan ni ya zo amma bana jin bayan gaisuwa zai ga fuskar yi min wata maganar. Babu zancen kome a tsakaninmu, dan ni ba zan iya zama da shi ba kwata-kwata, shima haka yanzu zai sha wahala idan ya ce zai zauna da ni. Saboda zaman da muka yi ada zama ne da yake yi mana mulki, son nuna isa, takama da son girma. Ya kira mu kauyawa, ya daka mana tsawa, duk abunda yake so dole shi za mu yi, ba mu da zabin kanmu. Haka yayi mana ni da Nasiba musamman ma ni da ba zabinsa ba kuma ya ganni yarinta sosai. Zamansa da Zulayha Senegal kuwa ita take sonsa, take binsa, take kashe masa kudinta, daga lokacin da ta gama gulmar ta daina yi masa biyayyar, bayan ta samu ta aure shi kenan, na san daga lokacin masifa ta kunnu. Ya fito mata da halinsa na rashin mutunci itama daman ta fi shi iyawa suka babe. Dr. Faduwa ba zan iya auren kowa ba yanzu a duniya in ba mai irin halin Abdul-Sabur ba. Halayensa sune: Hakuri, kulawa, damuwa da halin da mutum ya ke ciki, tattali, karamci, kyauta, tausayi, nasihohi masu taushi, ga lallausan lafazi, wasa da dariya, iya hira, amfani da hankalinsa baya taba damunka idan kana cikin fushi ya san yadda zai zauna da kai a duk yanayin da kake ciki. Faduwa ta dade tana kallonta sai ta kasa yin magana, can tayi ajiyar zuciya. Ta ce ''Ni yanzu ba gashi na hakura nayi aurena ba tunda nasan ba zan same shi ba. Umaimah ta yi murmushin karfin hali ta ce ''Amma kina son Sagir sosai, kuma a rashinsa ne ma har Abdul-Sabur ya burgeki. Ni kuwa bana son Abdul-Basi tun farko ma, Abdul-Sabur na fara so a duniya, ban tantance ba har sai da na rasa shi, sannan na tabbatar duk duniya babu mai yimin kulawar da yake min alhali ada na tsane shi akan ya damu da ni. Faduwa ta ce, ''Gara ki auri wanda yake hannunki Umaimah, kada ki yi biyu babu. Umaimah ta yi *yar siririyar dariya ta ce, ''Anti Faduwa, daman sauri ne aure? Bana sauri ko yanzu da babu Abdul-Sabur babu dalilinsa, na tabbatar na rasa shi ba zan same shi ba, ba zan koma wajen Abdul-basi ba dan bashi da kirki. Ya kore ni a lokacin da nake tsananin son zama dashi, a lokacin da babu in da zan zauna inji sanyi sai gidansa. Sai yanzu da na zama mutum, nake da yadda zan yi sannan zai dawo min. Ba Abdul-Sabur nake jira ba amma ba zan auri Abdul-Basi ba. Zan ci gaba da yin addu'a Allah Ya turo min da miji na gari. Faduwa ta yi dariya ta ce, ''Allah Ya turo miki Kamal kika ki shi, kullum ni da Sagir yake damu ya ce yana ta kiranki bakya amsawa. Ashe Umaimah ba za kiyiwa kanki fada ba ki auri dan larabawa ba, ga kyau ga kudi. Zai kula da ke sosai dan mazanmu suna da rikon aure. Umaimah ta yi dan murmushi ta ce, "Yi hakuri Antina, ba zan iya auren shi ba, kema kinsan dalili. Daidai lokacin Faduwa ta ja ta tsaya a kofar gidan Umaimah ta ce, "Kin san nayi nauyi yanzu bana yawo, saboda ke ne ma na fito yau. Ba zan iya hawa sama ba yanzu, zan je gidan kawata in jira direbana ya zo ya mayar da ni 'Putra Jaya' dan ba zan iya dogon tuki ba. Umaimah ta ce, ''Allah Ya sa ki haihu a cikin satin nan kafin na tafi in ga babyn ki. Faduwa tayi dariya ta ce, "Amin Umaimah, hakan zai iya faruwa saboda watan haihuwana ya kama. Umaimah ta bude kofar mota ta fito, ta yi mata godiya gami da yi mata fatan sauka lafiya. Tunda Umaimah ta shiga gidanta bata sake fitowa ba sai bayan kwanaki uku wato sai ranar bikin yaye su Hanif, Umaimah ta shirya tsaf, ta ce kwalliya ba ta kadan ba saboda ta ga yadda ake tsala ado idan za'aje bikin Graduation. Tana Allah.. Allah yasa taga dan Aunty a wajen ko xataji sanyi a xuciyar ta.. hmm. To Alhamdulillah. Allah yayi na cika alkawari.sai kuma gobe da yardar Allah xaku jini da cigaban kayattaccen, kasai taccen wannan littafin na Mashahuriyar marubucia wato Jamila Umar Tanko.. Naku a kullun mai kaunar nishadin ku. Abbas Abdulkadir Hada Hada (Marbass Dan Aunty). See translationMAKWABTAKA 42 Umaimah ta shirya tsaf, ta ce kwalliya ba ta kadan ba saboda ta ga yadda ake tsala ado idan za'aje bikin Graduation. Ta saka daya daga cikin tsala-tsalan shaddojinta data dinko daga Dubai. Ta dauki wayarta da mukullin motarta sai digital camera data rataya a wuyanta, ta nufi 'Royal bingtang Hotel' a cikin motarta, tana tafe tana sauraron wakarnan da take so ta mutumin Ghana 'Akuri Afomsa' wacce yake yi cikin yaren 'Asanti, wacce Abdul-Sabur ya bata. Babu abinda take tunawa sai Abdul-Sabur dinta ta tuna ranar da ya kaita Mantin wakar suka yi ta ji yana fassara mata. Ta ci karo da su Aysha Bingyal a bakin Hotel din, tana isowa kawayenta mata da maza suka yo kanta caa! Su na ta yabawa da tsananin kyawun da ta yi har suka ce basu gane ta ba da farko sai da tayi magana suka gane. Anya kuwa wannan kwalliya da Umaimah ta yi ba kwalele take yiwa Abdul-Basi ba? OHO! Wato a lokacin da ta nufo cikin Hotel din a cikin motarta sai da kowa ya zuba mata ido yana kallon halittar Ubangiji, sai kowa ya kagu da ya tantance ko wacece wannan, ashe Umaima Bello ce sai da ta fito aka shaidata. Umaimah ta dade a tsaye tana hira da kawayenta sai daga baya ta gane ashe Abdul-Basi ne a tsaye a gefensu shi da abokinsa Tanimu Wada. To ai ba dan ita su ka zo Malaysia ba saboda kanin Tanimu Wada suka zo wato Bashir Wada, ajinsu daya da Hanif. Tanimu ya karaso inda Umaimah take a tsaye ita da kawayenta cike da fara'arsa, yayin da itama ta juyo ta kalleshi tayi murmushi sai suka gaisa. "Shin ba ki gane mu ba ne? Tanimu ya tambaye ta. Sai ta cika da mamakin wannan tambaya tasa. Itama ta tambaye shin kamar yaya? "Naga da kika shigo kin kalle mu sanna kika watsar. Ta tabe baki ta kawar da kai dan taga alamar rai yake so ya bata mata. Ya nisa ya ce, "Ki zo ki gaishe shi mana. Ta dube shi duba irin na takaici ta kasa bashi amsa, har ya gaji da surutu ya yi mata sallama ya koma in da ya fito. Yana ta mamaki a zuciyarsa dan ya zaci Umaimar daya sani a da ce, da take zuwa ta durkushe a gaban abokan mijinta, ta kudindine a cikin hijabi ta shige lungu, ko me zata mika musu sai ta durkusa har kasa. Yanzu ya tantance ya gane akwai banbanci, dan shima Abdul-Basin daga dukkan alamu ya zaci irin ta da ce shiyasa yake daddakewa. Sai da ta juya taga Tanimu ya bace, acan ta hango shi yana bawa Abdul-Basi labarin abin da ya faru. Tanimu ya ce da abokinsa Abdul-Basi "Umaimar daka sani ada ba irin ta ba ce yanzu, akwai bambanci sosai. In har kana tunanin Umaimah zata zo ta gaishe ka yanzu to ba zata zo ba. Tunda biko ka zo to ka zo mu je kayi *yar murya ko Allah Zai sa ta amince maka dan na lura bata marmarin son zama da kai kuma. Abdul-Basi ya girgiza kai ya ce, "Haba nawa Umaimah take da za'a ce ni zan je in gaishe ta. Ai tana kallona bata zo ta gaishe ni ba tayaya ni zan je wajenta? Za ta kawo kanta ka kyale ta, guguwar digiri ne yake kwasar ta sai ta sake ta sannan, kasan *yan jami'a da ji da kai. Tanimu ya ce "a'a abokina ka cire girman kai ka zo mu gwada, ka san halin mace da jan aji balle ace ita aka yiwa laifi, kai ne fa me nema. Kai kake tsananin son ta dawo, kai kake kasa bacci dominta, kai kake hana ni sakat da hirarta, gara ka zo mu je tunda wuri. Abdul-Basi ya ce ba zai je ba sai dai ta zo ta gaishe shi. Girman kai rawanin tsiya ne! Su Umaimah ne suka fara shigowa ciki, suka sami waje mai kyau suka zauna daga gaba dan suga komai radau. Su Abdul-Basi ma suka shigo amma daga baya suka sami waje suka zauna suna hango su Umaimah da kwayenta, da lama babu abin da ya dameta, harkarta da kawayenta kadai take yi, suna ta wasa da dariya suna ta daukar junansu a hotuna. Da su Hanif suka shigo, sai aka hau tafi ana ta dasa musu hotuna kala-kala. Umaimah tabi Hanif tana dauka a hoto har saida ya zauna sannan ta dawo ta zauna itama. Babu abinda Lamijo da AbdulBasi suke yi sai mamakin Umaimah, suna kallon irin wannan kyau da tayi, da wayewa. Tabbas yanzu Umaimah tayi musu zarra tafi su komai, dan haka ta girmi wulakancinsu. Abunda ya fi tsayawa Lamijo a rai shine yadda taga Umaimah a Malaysia har tukin mota, ko ma dai menene a ransu basa gaban Umaimah ko kallon inda suke bata yi ba bayan farin ciki bata da wani abun yi. Taro yayi kyau, an rabawa su Hanif sakamakon jarabawarsu a hannu, sannan aka yi ta dogayen jawabi, aka ci, aka sha, sai aka watse. Sai kuma gobe war haka wani sabon bikin za'a yi na wadanda suka fita daga jami'ar 'Intii Nilai' su kuma a 'Radius International Hotel' za'ayi, tabbas gobe za'a sake wata sabuwar haduwar. Cancadi! Za'a kece raini da suturu da gwala-gwalai. Washe gari ma haka Umaimah Bello ta caba ado kai kace tarwada ce wacce take sheki, santsi, sulbi, yadda take karairaya idan tana takawa. Ta zama tamkar tauraruwa mafi haske a cikin *yan iwanta taurari wato 'Zahra'. To ko ita zata maye sunan kawarta wato 'MATAWATA? OHO! Ta hadu da Abdul-Basi da Lamijo a sanda ta je ta gaida Baban Hanif, basu yi mata magana ba dan sunga haduwar data yi ta wuce tunaninsu, da suka ganta sai suka kawar da kai gefe, sai ita ta je gare su ta duka ta gaishe su. Dan ta tuna kadan daga cikin irin halayyar Abdul-Sabur, idan ka gan shi ka share sai kaga shi ya zo yayi maka sallaman bawan Allah kenan me koyi da halin Manzon Allah (S.A.W). Ta gaggauta kaucewa daga bangarensu ta ta fi wajen masu kaunarta. Aka gudanar da biki yadda ya kamata kowa yana murna, da aka gama kowa ya watse. Daga nan ba'a sake yin bikin yaye dalibai ba sai da aka shafe kwanaki biyar, baki suka dinga cika dogayen motoci aka yi ta zagaye gari da su, suna kallon wuraren shakatawa iri-iri. Umaimah bata bi su ba saboda Lamijo da Abdul-Basi, babu yadda kawarta bata yi da ita ba akan ta zo su je su dinga raka su, ta ce ba zata je ba a gida zata zauna. Bata fito daga gida ba sai a ranar bikin yaye dalibai na jami'ar 'Subang Jaya' shi kuma a Capitol Kaula Lumpur Hotel ake yi. Me za'a fasa mutuwa ko tonar kabari? Inji masu iya magana. Ado ne dai Umaimah bata daina caba shi ba, kuma a dole sai ta zuba kyau, idan ta fito fili sai kowa ya kalle ta kuma sai ta burge, suturu ne Allah Ya hore mata kala-kala. Saura makaranta daya ce ta rage basu yi ba, su ba yanzu zasu yi ba saura wata guda, dan haka aka bawa dalibai hakuri dan ba zai yiwu a jira su ba saboda ba dole bane yin bikin. Abu mai muhimmanci dai shine karbar sakamako kuma za'a kawo musu har gida Nigeria idan ya kammala. Daliban makarantar basu ji dadi ba dai amma dole tasa suka hakura suka tarkato dan a taho gaba daya a tare. Dole ne a tafi sabida viser sati bibbiyu ce kacal aka bawa su Baban Hanif. **** gobe su Umaimah zasu tafi, tunda sanyin safiya ta dinga bin duk jama'ar data sani tana yi musu sallama, daga nan ta wuce gidan Faduwa a cikin motarta a inda zata yi mata sallama sannan kuma za'a sayi motarta, wata kawar Faduwa mai suna Salma ita ma *yar Egypt ce tana so zata saya. Bayan da aka gama cinikin mota, salma ta biya ta kudinta cif a hannu, da Dallar ta biya ta kamar yadda Umamai ta bukata dan ta canja gaba daya kudinta ya zama Dallar, saboda ta fi saukin canzuwa a nan gida Najeriya. Umaimah tana ji tana gani Salma ta haye motarta ta tafi, tana tsananin son motarta dole ce tasa ta rabu da ita. Faduwa ce ta hana ta tafiya da wuri, acan suka yini har zuwa yamma, Sagir ma ya zo daukar matarsa zai tafi da ita Cairo acan zata haihu koma a ce kacokan zata kaura ta bar Malaysia, har ta yi sallama da wajen aikinta suma saura kwanaki uku su tafi. Da Umaimah ta tashi tafiya direban Faduwa ne zai mayar da ita gida sai Faduwa da Sagir suka yi mata rakiya har bakin mota suka mika mata babbar leda a cike da alawowi iri-iri masu tsadar gaske suka ce ta kaiwa yaranta tsaraba, . Umaimah ta karba ta yi godiya sai kuma ta rushe da kuka ta rungume Faduwa itama tuni daman Faduwa ta fara kuka. Suka yi ta rusa kuka ba na wasa ba. Sagir ne ya dinga lallashinsu dakyar kukan ya tsagaita. Umaimah ta sharce hawaye ta ce, ''Ada na tsani MAKWABTAna, bana sonsu, nayi zaton dukka MAKWABTA haka suke basa bada hakkin MAKWABTAKA ashe ba haka ba ne. Anti Faduwa, daga kanki ke da Abdul-Sabur na fara son MAKWABTAna kuma daga yanzu duk inda zama ya hada ni da mutane zan zauna da MAKWABTAna lafiya. Kun yi jahadi da ku ka fahimtar da ni na san hakkin MAKWABTAKA. Allah Ya saka muku da gidan aljanna, ba zan manta da ku ba har abada. Faduwa ta sharce hawaye ta ce ''Ada na tsani *yan Najeriya saboda yadda *yan uwana suka musguna min, amma zamana da ke yasa na fahimci ashe wasunku kuna da kirki. Ke ce *yar Nijeriyar dana fara sani mai kamun kai, hankali, kunya da ladabi. Ke ce wacce kika sadaukar min da abunda kike so kika hakura da shi dan in samu. Ina jin ki a zuciyata tamkar kanwata uwa daya uba daya, saboda bani da kanwa ko daya a duniya.... Kuka ne ya ci karfin Faduwa ta kasa karasa bayananta suka sake kankame juna, ji suke kamar kar su rabu. Faduwa ta sake sharce hawaye ta juya ta dubi Sagir wanda shima sun saka shi hawaye dan tausayi duk da ba Hausa yake ji ba amma ya san kalaman rabuwa suke yi. Ta yi magana da turanci ta ce, ''Sagir ka taya ni cikawa Umaimah alkawarin da zan daukar mata idan na haifi mace zan saka mata suna Umaimah, saboda kauna da zaman amanar da muka yi. Sagir ya gyada kai ya ce, ''Na amince miki Yah Habitti. Umaimah ta fashe da kukam farin ciki ta ce ''Na gode muku, nima insha Allah kafin in bar duniya inda rabon nayi aure na haihu zan saka sunanki. Zasu sake kankame juna su sake bude wani sabon shafin kukan sai Sagir ya janya Faduwa ya ce Umaimah ta shiga mota ta tafi, kukan ya isa haka zasu sakawa kansu ciwon kai. Basu daina dagawa juna hannu ba har sai da suka yi nisa suka daina hango juna. Allah Sarki sabo, turken wawa. Ko da rabon a sake haduwa ko kuwa rabuwar ce har abada? Allah ne kadai Ya sani. Amma dai sun yiwa juna alkawari zasu ziyarci juna Egypt da Nigeria ba nisa sosai. *** Ba Umaimah kadai ce me himilin kaya ba dalibai da dama sun lodi kaya da yawa musamman ma matan. Ai kuwa ansha dogon turanci a tsakanin wakilan Gwamna da ma'aikatan Egypt air saboda himilin kayan da dalibai suka loda yayi yawa ainun. Duk da alafarma da rangwamen da suka yarda suka yi amma sai da aka biya makudan kudin awo. Su Umaimah suna gefe kamar ba akan kayansu ake hayaniya ba, suka yi lukus a gefe. Ka ga *yan gatan gwamnati, sai da aka gama komai aka miko musu 'tag label' din kayansu, suka wuce abinsu zuwa cikin jirgi, daga su sai *yar jakarsu ta ratayawa da jakar Laptop dinsu. Umaimah Bello da kawarta Aisha Bingyal ne suka shigo cikin jirgi sanye da riga da wando (jeans) sai suka dora bakar abaya akai, zo kaga farar fata a cikin bakin kaya yadda suka haska. Kananan hijabai ruwan madara masu kwalliyar fulawa baka suka dora akansu, suka saka takalmi masu tsini da kalarsa ruwan madara, suka dora farin gilasai a idanuwansu. Rigiji-gafji! Wani kaya sai amale. Kowa sai da ya dago ido ya dube su, dan su ne suka shigo daga karshe kasancewar sun bata lokaci a wajen awo aka dade ana ta hayaniya akan kayansu, sun yi kyau sosai, sai suka zama tamkar *yan tagwaye masu kama daya, kallo daya zaka yi musu ka tabbatar sunyi kama da masu digiri digirgir. Su na tafe suna hirarsu suna ta tuntsira dariya har suka shigo ciki, suka fara duba inda lambar kujerarsu take kamar yadda take a rubuce a jikin 'Bording pass' din kowanne fasinja. Dama tsakiyar jirgin lambarsu take dan haka suka wurwuce mutane da yawa kafin su isa mazauninsu. Tunda suka shigo suke aikin gaishe da iyayen kawayensu irin su Baban Hanif dan su tuni sun shisshigo. Tana juyawa gefenta Abdul-Basi da Tanimu ta gani suna zazzaune, sai ta duka ta gaishe su cikin girmamawa, nan da nan suka yi caraf suka amsa abunka da daman jira suke. Ta gaggauta wuce zuwa can baya inda kujerunsa suke tana tafe tana mamakin irin wannan isa da girman kai na AbdulBasi, ta shiga addu'a kada Allah Ya sa *ya*yanta su biyo halinsa. Sai yanzu ta sake curewa da jinjinawa Abdul-Sabur, sai da ya shekara yana bin ta yana yi mata magana tana share shi bai taba gajiya ba ya daina. ''Na yi rashin masoyi Abdul-Sabur. Ta fada a zuciyarta. Gaba daya *yan tawagar su Umaimah su dari biyu ne, jirgi kuwa mai cin mutane dari biyar ne dan haka aka batse da farar fata masu zuwa Cairo su dari uku. Bayan kowa ya zauna, sai aka kwararo addu'ar nan ta tafiya. Jirgi ya zabura ya tashi sama ya luma cikin gajimare yayin da Umaimah ta runtse idanuwanta, babu wanda take hangowa daga Abdul-Sabur sai Faduwa, hawaye mai zafi ya kwararo mata. Ta sake tunowa da kawayenta *yan Malaysia da *yan India, da malamanta da suka saba sun rabu da wuya su sake ganin juna kuma har abada. Ta dade tana ta kuka bata daina ba duk da lallashin da Aisha ta dinga yi mata dakyar ta daina. Tana cike da farin ciki dan zata je taga Baffanta, *ya*yanta da *yan uwanta amma ta san yanzu zata hadu da ce-ce-ku-ce da kananan maganganu, da masu shiga sharo ba shanu, masu fada ba'a tambayesu ba. Africa kenan sabanin nan da ba ruwan wani da wani. Sai wata rana Malaysia!!! CAIRO Tafiyar kwanaki biyu zasu yi sai da suka shafe awanni

Chapter 25 of 33