Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kasar. Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''Umaimah ni da ke kasarmu daya, YARENMU daya Hausa/Fulani, ADDININMU daya musulunci. Da girmana na je Ghana amma ni dan asalin Nigeria ne. Faduwa ma *yar Nigeria ce saboda mahaifinta bakar fata ne, bahaushe dan asalin garin Sokoto, mahaifiyarta ce *yar Egypt, amma a wajen mahaifiyarta ta girma ita ta rike ta, duk da haka ta iya Hausa. Umaimah ta cika da mamaki, yayin da wasu gumaguman farin ciki suka dinga dirgowa a kahon zuciyarta saboda ta ba *yan gidata dafe haba da hannu tana jinjina kai, fadi ta ke, ''Ikon Allah, ashe ku duk *yan Nigeria ne? Abdul-Sabur ya ce, ''Kwarai kuwa, kuma muna yawan zuwa idan ta kama. Ta juya ya dubi Faduwa ya yi dariya, ya ce da ita, ''Bismillah, fara yara mata Hausa don ta yarda, na ga har yanzu tana kokonto. Faduwa ta yi dariya ta kurbi shayi, ta du bi Umaimah har yanzu dai cikin harshen Turanci suke magana. Ta ce, ''Kanwata wai da gaske har yanzu kina kokonto mu ba *yan kasarki ba ne? Umaimah ta yi murmushi ta gyada kai ta ce, ''gaskiya ina dan tantama. Abdul-Sabur ya furta kalmar Hausa, ya ce ''Da gaske muke yi, mu Hausawa ne, har wasu lokutan ni da Faduwa mu kanyi yaren Hausa, idan muna so mu yi maganar da ba ma so a ji a cikin mutane. Umaimah ta sankare a zaune, saboda ta san ashe ya gama jin duk zagin da ta ke yi masa a baya. Ashe yana sane yake kiranta da ''MAYE'' ramawa yake yi kenan? Faduwa ta kaikaice cikin harshen Hausa ta ke magana, duk da Hausar ba ta fita radau, amma ana ganewa tar! LABARIN FADUWA. Ta ce, ''Sunana Faduwa, sunan mahaifina Ahmad Sokoto. Mahaifina bakar fata ne bakikirin kuwa, dan asalin garin Sokoto ne gaba da baya. Mahaifiyata mai suna Zainab kuwa *ya asalin kasar Egypt ce, *yar cikin garin Cairo babban birnin. Ita dai ruwa biyu ce, mahaifinta ne dan Egypt, mahaifiyarta *yar kasar Saudia ce, don haka ina da *yan uwa a Saudia sosai. Karatu ya kai mahaifina Egypt, tun yana dan matashin saurayi shi da kannensa guda biyu Mansur da Adamu. Sun dade a Egypt har bayan sun kammala karatun ba su koma kasarsu ba, suna kasuwanci harma da aikin gwamnati, kasancewar mahaifinsu mai arziki ne, yana yawan zuwa Egypt shi ma ya zauna yana Hada-Hadar kasuwanci. Allah Ya hada soyayya tsakanin mahaifana, aure ya kankama a tsakanin fara da baki, duk da surutai da kyamar abin da dangin mahaifiyata ke nunawa a sanadiyyar auren nan Zainab kuwa idonta ya rufe, saboda soyayya ta ce ta ji ta gani zata aureshi haaka. Daman a lokacin marainiya ce, a hannun dangin mahaifinta ta ke, iyayenta duk sun rasu su duka biyun tun ma tana karamarta. Aure ya tabbata tsakanin Ahmad da Zainab da sharadin ba zai koma Nigeria ba, a Cairo zai bar ta. Zama na rufin asiri, saboda ya na da hali. Allah Ya albarkace su da samun haihuwa *ya*ya biyu, yayana Ibrahim da ni Faduwa. Ina da shekara uku yayana yana da shekaru biyar kakana ya rasu wanda ya haifi mahaifina, bayan rasuwarsa ne aka takurawa mahaifina da kannensa su dawo gida, tun da ba ran mahaifinsu don su ci gaba da kula da kasuwanci da iyayensu mata da kananan kannensu mata da maza. Nan fa rigima sabuwa ta fara don mahaifiyata ta ce ba zata biyo shi Nigeria ba, danginta kuma suka ce ba zai tafi ya bar ta da aurensa ba, sai dai idan ya sake ta. Yayi-yayi ta yi hakuri su koma Nigeria ko a ci gaba da auren yana zuwa yana dawowa, suka ce bazai yuwu ba, sai dai su rabu. Dole ya sake ta, sannan aka shiga rigimar daukar yara, ya ce sai ya tafi da mu, ita kuma ta ce ko da daya ba zata ba shi ba. Kamar daiza,a tafi kotu aka samu tsofaffi suka shiga aka yi sulhu, shi na mijin aka ba shi, macen aka barni a wajenta, da sharadin zai dinga kawo Ibrahim yana ganinta. Ta yi ta kukan rabuwa da danta tana ji tana gani aka tafi da danta, ni ma ina ji ina gani mahaifina mai sona, wanda muka shaku da shi ya tafi ya bar ni. Gidan da muke ciki kato ne sosai, ina yarinya sosai. A hankali har na soma mantawa da su, mahaifiyata da danginta kadai na sani, don su na budi ido na ga ina rayuwa da su. Aka saka ni a makaranta mai kyau, tun daga Nursiry har zuwa sakandire. Sai da na shiga aji uku na sakandire sannan Yayana Ibrahim ya zo Egypt, kanin babanmu uncle Mansur ne ya kawo shi, a lokacin ya gama sakandire. Kukan dadi Mamana ta yi data gan shi, don dama kullum addu,arta ke nan ta ga danta, sai ta shirya zata je Nigeria sai danginta su hana ta. Mahaifinmu tunda ya tapi gida ya manta da mu, ya auri mata biyu suna ta zazzago masa haihuwa, arziki ya kara bukasa. Sai a lokacin na san Yayana Ibrahim, ashe kamarmu daya da shi, dukka mahaifiyarmu muka biyo. Fari ne sol sak balarabe sai dai ki ji Hausa a bakinsa rangadadai irin ta Sakkotawa amma babu digo daya a jikinsa da ya yi kama bakar fata. Babu alamar wahala a jikinsa kasancewar a can a cikin daula suke, babu talauci har sun fimu jin dadi saboda Egypt ba kudi, ba albashin kirki a ma'aikata, babu kasuwanci da zai kawo kudi irin a Nigeria. Na zaci ma ya kauro kenan da na ga Baffanmu da ya kawo shi ya koma ya barshi. Da Ibrahim ya yi watanni hudu ya yi waya da *yan gida suka ce masa sakamakon jarabawarsa ya fito sai ya ce Nigeria zai koma ya yi jami,a. Babu yadda mamanmu ba ta yi ba kada ya tafi. Ya ce ya fi son ya tafi, saboda da can ya fi sabawa. Amma ya yi alkawarin duk shekara zai dinga zuwa hutu tunda ya ga hanya yanzu. Tabbas ya tausaya mana da ya ga muna ta kame- kame babu wadata shi ma ba kudin ne da shi ba, tikitin zuwa da komawa ya ba shi, sai *yan canji a aljihunsa. Mun shaku dashi sosai a wannan watannin hudu da ya yi damu. Munsha hira kala-kala, baya gajiya da jerin gwanon tambayoyin da na dinga jero masa game da mahaifinmu da kasarmu da kuma kannena na can. Allah Ya taimaka Mahaifina da kannensa sun koya larabci don haka da Larabci don haka da larabci muke magana, idan ta kakare ya juya Turanci. Ni kuma na fara koyon Hausa a wajensa kadan-kadan. Dalilina na yi masa tambayoyi akan kasata Nigeria shi ne, na karada cikin kawayena da cewa. Ni *yar Nigeria ce, amma ban san komai ba akan kasar, har suke karyata ni. Amma da Ibrahim ya yi min dalla-dalla na rubuta shikenan za su sha labari a makaranta. Bayan tafiyarsa ya sami damar shiga jami,ar Ahmadu Bello Zaria, yana karantar Engneering. A lokacin wayar land-line ta wadata babu wayar hannu, koda yaushe yana bugo mana waya mu yi ta hira, amma dai dai da rana daya Mahaifina bai taba cewa a ba shi ni ko Mamana mu gaisa ba. .. Muna farrin ciki da ganinsa har ma yana taho mana da tsaraba kamar su atamfofi, leshina dinkakku sai kukar kadi, garin masara, garin dawa, kubewa bushasshiya, harda daddawa. Da yake Mamana ta iya dafa abincin hausawa, zaman da ta yi da Babanmu ya koya mata, yana sawa ta dafa masa. Ni ma inajin dadin cin tuwo sosai, don haka na dage na koya. A lokacin da Ibrahim yake daf da gama jami,a ni kuma na gama sakandire da sakamako mai kyan gaske. Kai tsaye jami,a na wuce suka bani medicine. Kwakwalwa gareni, duk da ina da yawan surutu da son wasa, amma a aji idan aka sami na daya, to ni ce ta biyu. Ibrahim ya yi farin ciki da samun labarin ina karantar likita, ya kara min karfin gwiwa in dage in kammala. Sai a lokacin ne ma na taba jin muryar Mahaifina, Ibrahim ya bani shi a waya muka gaisa ya yi min addu'ar fatn alkhari. Sai na yi wa Mahaifina tambayar da ta girgiza shi jikinsa yayi sanyi. Na ce, 'Baba, au daman kasan kana da *ya ta cikinka a Egypt? Ka manta da ni dai-dai da rana daya baka taba zuwa ka ganni ba, ko ka neme ni a waya ko ka aiko da tikiti ka ce inzo in ganka, kuma inga sauran *yan uwana? Sai ya yi kasake ya kasa bani amsa, Mahaifiyata ta fusata ta kwace kan wayar ta ajiye ta hau ni da bambamin fada. Wai akan me zan ce ya aiko datikiti in je Nigeria? Sai dai in bayan ranta zan je Nigeria. Wai ina so in je nima su shanye ni kamar yadda suka shanye Ibrahim, ya kasa baro wajensu. Sai na yi ta kuka ina ta takaicin irin wannan kwamacalar aure da rabe-rabe tsakanin Mahaifana. Da Ibrahim ya kammala karatu ya yi bautar kasa, sai ya taho Cairo ya zauna tare da mu da takardunsa. Nan da nan kuwa ya sami aiki a wani kamfani Albashinsa mai kyau ne, idan aka hada da yadda ake biyan *yan kasa shi ya sami kari saboda suna daraja abin da ya karanta, kuma sun ga a Nigeria ya yi, Sai a lokacin na fara fuskantar matsaloli da goregore, saboda na isa aure ina da samari da yawa, idan maganar aure ta taso ranga-ranga sai iyayen mazan su bijire su ce ba a san ubana ba. Ko kuma idan suka bincika aka san ni ba shegiya ba ce, sai su ji cewa uban bakar fatane, ya gudu ya bar mu sai a ce ba za,ayi ba. Dan haka ni ba matar da zasu iya aura ba ce, dan zan iya sulalewa watarana na gudu kamar yadda Mahaifina ya yi. An yi haka ya fi sau uku, babu abin da nake yi sai kuka, Mamana da Ibrahim suna ta ba ni baki. Na shirya zan tafi Nigeria wajen Mahaifina ya fi a kirga, Mahaifiyata sai ta tubure ta ce bazan je ba. Shi ma kansa Ibrahim tunda ya zo ya fara aiki ta hanashi zuwa Sokoto shima kuma Mahaifinmu yana nuna halin ko'in-kula da mu, da zuwanmu da rashinsa duk daya ne a wajensa, saboda matansa na can sun dauke masa hankali akan mu, sun fi so su manta yana da *ya*ya a Cairo, *ya*yansu ne kadai *ya*yansa. To haka dai ake ta fama ni ina a asibiti ina samun kudi har na sayi mota, haka Ibrahim ma yana aikinsa da motarsa. Mahaifiyarmu ta fara jim dadin rayuwarta babu abin da ba ma ajiye mata. Mun tashi daga dan karamin gida mun sayi babba soasai da kayan alatu, matsalarmu daya ita ce a wajen maganar aure. Ibrahim ma ya sha neman aure ana hana shi saboda ba'asan Mahaifinsa ba, idan kuma an san akwai shi, to ana tsoron kada ya sulale watarana shima ya gudu kamar yadda ubansa ya yi. Babbar matsalata na fara girma, don na bawa shekaru talatin baya a lokacin, duk kawayena duk sunyi aure suna haihuwa, ni haryanzu abu ya ki yiwuwa. Idan na zauna ina kuka sai Mahaifiyata ta yi ta ba ni hakuri wai a hankali mijina zaizo wanda ba zai damu da bincike na ba. Ta ce in ma cire raina da cewar zanje Nigeria, saboda tana tsoron wadannen mutane ba su da kirki, za su iya salwantar min da rayuwata. Sai na tambayeta ''ta ya ya za su cuce ni bayan ni jininsu ce, me yasa ta aure shi tunda ta san ba su da kirki? Ya akayi ita ba,a cutar da ita ba har ta zauna da shi suka haife mu? Da yake tana da fada sai ta rufe ni da masifa ina ji ina gani laifi ya dawo kaina na koma ina ta ba ta hakuri. Da naga kabilancin *yan Cairo ya yi yawa a kaina wajen aure sai na yanke hukuncin na auri baki muzauna Egypt *yan Nigeria da yake akwai su da yawa, ko kuma a cikin bakaken da suke zuwa Nigeria ganin likita a asibitinmu. Duk inda na ga dan Nigeria sai na ji ina sonsa, musamman Bahaushe, ko ba ya so sai na tsokano shi da hira dan na sanar masa nima *yar uwarsa ce har ma in yara masa YARENA na Hausa, tunda na koya wajen Ibrahim, Mamana ma tana ji kadan-kadan. Ta haka sai na yi abokai da kawaye masu dumbin yawa, ko sun koma Nigeria suna da lambata sai mu yi ta waya da su ina cika bakin watarana za su ganni a Nigeria.Duk wani dan Nigeria da ya ke zuwa Cairo, musamman asibiti idan ku ka tambaye su Dr. Faduwa Ahmad sun sanni. Ina son mutane saboda ina da yawan hira a sanadiyyar hakan sai na hadu da manyan *yan Nigeria ma su kudi da mulki, kamar ambassadors, ministoci, kwamishinoni, *yan kasuwa manya-manyan masu kudi. Wasu suna sona da son fasikanci, wasu kuwa da aure suke sona. Bana boye-boye, baro-baro nake fadawa fasikan nan ni ba *yar iska ba ce, kada su sake shiga harkata. Masu sona da aure kuwa suna cewa idan sun aureni zasu tafi da ni Nigeria ba za su barni a Cairo ba, sai na rusa maganar dan na san ma bazai yiwu ba don mahaifiyarta ba zata yarda ba. Ni ma kuma bana son abin da zan jawowa *ya*yana raberabe kamar yadda na tsinci kaina. Da na ga abin ba kararre ba ne, aure ya ki yiwuwa saina yankewa kaina shawarar ko aikin nawa ne sai na bari na auri dan Nigeria na bi shi can mu zauna. Har na taba tunkarar mahaifiyata da maganar aurena da Alh. Murtala wani Bakano ne, dan kasuwa, yana da mata uku ni ce ta hudu, amma duk ban damu ba. Yana matukar so na, yana da kirki ga dukiya mai yawa, saboda son da yake min bai ki ya raba dukiyarsa gida biyu ya bani rabi ba. Kuka yake yi da idanunsa akan na daure na aure shi, gidana daban ba zai hada ni da iyalansa ba. Kuma zai dinga kawo ni akai-akai ina ganin iyayena. Koda na fadawa mahaifiyata wannan labari, sai ya dora hannu aka ta yi min kukan mutuwa. Ta yi ta kiran lambar *yan uwanta wai su yi maza su zo ga Faduwa zata kashe ta. Nan da nan kowa ya zargayo a gigice suka tarar ba kisan hannu zan yi mata ba, kisan zuciya zan yi mata. Nan da nan suka taru suka hada baki babu wanda ya amince min. Ibrahim ne kadai ya ke bani goyon baya, shi ma ba a tashi daga taron ba sai da aka tsige shi tas. Aka ce ba shi da hankali, ya za a yi ya bawa kanwarsa wannan muguwar shawara na auren namiji mai mata uku, kuma dan Nigeria narasa rike aure, wadan da ba su san muhimmancin haihuwa ba. Dole na yiwa Alh. Murtala sallama muka rabu, ba shi kadai ba ma akwai wani babba mai mulki shi ma daga Abuja yake, ya kawo Mahaifinsa asibitin da nake ciki muka saba, har soayyaya ta shiga. Matarsa daya da *ya*ya biyar shi ma da na fada a gida aka hana ni. Sai na hakura da maganar aure gaba daya, tunda na rasa miji a Egypt, an hana ni auren *yan Nigeria. Sagir dan asalin Cairo ne, sannan dan sanda ne. Shine tsohon saurayina da muka hadu da shi tun bayan da na kammala sakandire, tashin farko daman mahaifiyarsa ta ce ba ta yarda ba, ba zai aure ni ba. Dan bani da sali, *yar uwarsa zai aura mai cikakken asali ba ruwa biyu ba. Yana sona sosai ya kasa rabuwa da ni, duk da yasan aurenmu ba zai yiwu ba, yana ganin kamar wata rana zata iya yarje masa ya aure ni. Ashe ita ba ta san ma muna tare ba har tsawon shekaru da yawa, sannan ya sake gabatar mata da ni a matsayin wacce zai aura. A take ta nuna mishi sai dai idan bata raye, ba zai aureni ba. Ina kuka, yana kuka ya ce shi bazai rabu da ni ba, kullum yana gidanmu, idan ina gida idan kuwa bana gida ina asibitin da nake aiki, to zaka anshi a kusa da ni, sai dai idan nasa aikin ne ya hanashi zuwa. Mahaifiyarsa tana kiransa sama da sau goma kafin yabar wajena, kai ka ce duba ta ke yi. Muddin ya zo sai ta gane sai ta yi ta kiransa. Ka ji tana magana cikin fushi, kasaita da daga murya. ''Sagir, kana ina? Cikin fushi da takaici yake amsa mata. ''Mama ya kike tambayata kamar karamin yaro da zai bata a Cairo? Sai ta ce, ''Kana tare da wannan tsinanniyar Faduwar ko? To ka dawo gida yanzun nan, nan da awa guda mazamaza ka karaso. Sai ta kashe waya a fusace bayan kamar mintuna biyar sai ta kirashi kuma. Ta ce, ''Ka taho ne? Sai ya ce, ''Zan dai taho yanzu. Idan ta ji shuru bai iso ba, sai ta sake kira. Ta ce ''Ya banji karar motoci ba, bayan ka ce min kuma kana hanya? Aikin kenan sai raina ya baci na ce ya tashi ya tafi. Ana nan-ana nan ni da shi kullum muna ta shawarwari yadda zanu bullowa wannan matsalolin. Mun shirya duk yadda zamu yi rayuwar aurenmu cikin farin ciki. Tsalelen gida ya gina ya zuba kayan alatu. Ya nuna min bangarena da bangarensa da kuma bangaren *y *yanmu idan mun haifa, tunda ko yaushe muna hasashen zamuyi aure har ma mu hayayyafa.. A gidan muka yi liyafar cikarmu shekara goma sha biyu da haduwarmu (12 anniversary). Muka gayyaci kawaye da abokai, muka yanka kek, aka yi mana hotuna. Kowa ya tausaya mana ya yi mana addu,ar Allah Ya sa wannan aure ya tabbata, saboda yadda aka lura muna kaunar junanmu matuka. .. .. .. ..MAKWABTAKA 12 Tunda mahaifiyarsa taji labarin wannan liyafar da muka yi, ta ga hotuna sai hankalinta ya sake tashi, ta kirani ta zazzage ni, wai nabar mata danta kada na cinye shi. Na ga santalelen saurayi, kyakkyawa na makale masa, to bari ta fada min, ban isa na aure shi ba duk nacina kuwa. Wai tasan duk hanyoyin da na bi na mallake mata da, sihiri ne ita ma zata bi ta karbo danta daga mugun hannu. Na kame a zaune ina ta sauraronta, na ji tashin hankalin da ban taba ji ba a duniya. Na tsani wannan kalmar, 'SIHIRI'. Dana fadawa Mamana abun da matar nan ta yi min sai ta girgiza kai ta ce, ''Ki yi hakuri Faduwa, sannan ki yi addu'a sosai. Ban fadawa Sagir cewa mahaifiyarsa ta zazzageni ba, a can ya jiyo da hawayensa ya yi ta bani hakuri, ya ce, yafi kaunar mutuwarsa da irin wannan kuncin da mahaifiyarsa ta ke so ta cusa shi a ciki. Na ba shi hakuri na fada masa nasihar da mahaiyata ta fada min cewar, na yi hakuri, sannan na yi addu,a sosai, babu abin da ya gagari addu,a. Tsafi ya kan ci mai shi, sihiri gaskiya ne, ana yinsa idan Allah Ya nufa sai ya kama wanda aka yiwa. Ta fada da bakinta kuma ta aikata, saboda yadda naga Sagir ya sauya nan da nan. Idan ya zo wajena muna hirarmu ta masoya cikin farin ciki da annashuwa da zarar ta kirashi, sai ka ga jikinsa ya dau karkarwa, muryarsa na rawa. Idan ta ce masa. ''Kana ina? To duk inda kake ka taho gida yanzun nan, na baka minitina goma idan ba hakaba ranka zai baci. Tana kashe waya zai mike tsaye ya ce ''Mamana tana kira, na tafi, sai wani lokacin. Ina masa magana baya saurarona a guje zai je ya shige mota ya tafi ko waiwayena baya yi. Sabanin da sai ya gama hirarsa zai tafi ko zata yi waya sau dari. Ashe duk wannan somin tabi ne, abin takaici na gaba. Sai ma ta hanashi zuwa gidanmu, ga shi kirikiri munyi waya da shi ya ce min ya kamo hanyar gidanmu. In caba ado in zauna ina jiransa, sai ya yi min waya ya ce, ya koma gida mahaifiyarsa ta ce ya dawo. Hakafa ya ke sanar min ba tare da sakayawa ba, i dan ba dan furucinta da tayi min ba da sai na ce yanason kyauyaya mu'amalarsa da mahaifansa sosai, to amma furucin da tayi ya kauda komai. Tun ana haka har ya daina tarkar tahowa wajena, wayar ma jifa-jifa. Idan son sa ya yi min yawa sai na dauki motata na je na ganshi a gidansa ko a wajen aikinsa. Sai ta ji labari ina zuwa, sai ta sa shi ya fara kora ta. Wai ni Faduwa ni na zama abin kora a wajen Sagir, bayan a da babu wadda yake son kasancewa tare da ita kama ta. Sagir ba ya son ganina, har ta kai ta kawo ya fada min baro-baro da bakinsa. ''Faduwa ki rabu da ni, mu hakura da juna, saboda kina jawomin sabani tsakani na da mahaifiyata. Ni kuwa ba na son duk wani abu da ba ta so, koda kuwa shine zabin raina. Sai na ji jiri ya kwashe ni ina zaune na ji na kwanta can na dago na dube shi, sai na ga bana ganinsa sai duhu. Daga dukkan alamu suma ce na yi a ofis dinsa ne, sai ganinsa na yi da abokansa sun zagaye ni suna shafamin ruwan sanyi a fuskata. Da na warware sai na ga idanunsa sharkaf da hawaye, wanda har yau ba ya kafewa muddin na tuna Sagir ko na ji mai sunan sa, kuma ina tuna korar karen da ya yi min daga rayuwarsa. Da kyar na dauko jakata da makullin motata na fito daga ofishin na bar shi da abokansa suna tambayarsa me yake faruwa, don shima kukan yake yi. Tun daga ranar har rana irin ta yau ban sake ganin Sagir ba ko na jiyo muryarsa a dodon kunnena. Na hakura da shi koda kuwa sonsa shine ajalina. Faduwa ta rushe da kuka mai tsanani yayin da tausayinta ya cika zuciyoyin Umaimah da Abdul-Sabur, suma kwalla ta cika musu ido. Lokaci mai tsawo babu wanda ya yi magana a cikinsu, sai shasshekar kukan Faduwa ne ka tashi. Umaimah ta dinga shafa kafadarta tana jijjiga ta tamkar tana lallashin dan jariri, kalmar ''Sorry..... Sorry. Suke ta ambatowa Faduwa. Abdul-Sabur ya ce , ''Yaya rayuwarki ta kasance ke da mahaifanki? Faduwa ta sharce hawaye ta ce. ''Wannan shi ne mataki na farko da na fara takawa na tashin hankali a rayuwata. Daga nan abubuwa marasa dadi suka yi ta biyo ni daya bayan daya. Kusan kowanne dan Adam bisa kan mizanin kaddararsa ya ke, to haka nima na yi ta hawa kaddarorin rayuwata. Yayana Ibrahin ya kamu da ciwo, wanda aka rasa kansa. Abu kamar wasa tun yana iya fita ya je aiki har ya kasa fita. Tun yana kwance a bangarensa har Mamana ta dauke shi ta dawo da shi dakinta tana kula da shi, dom komai sai an yi masa. Gwaje-gwaje kala-kala an kasa gano kan ciwon sa. Kuma a cikinsa ya ke, ya shekara uku a kwance babu abin da ake sai kashe kudi, sai da komai namu ya kare, daman shi sun sallame shi a wajen aiki, sun ba shi kudin sallamarsa ya kare a magani (Wannan banzar dabi,ace da ke faruwa a kowacce kasa, wai adan ma,aika ci ba shi da lafiya, maimakon a taimake shi a dauki nauyin maganin ciwonsa, wata kilama a sanadin kulawar wajen aiki ya samu sauki, amma sai a yi biris da shi karshe ma a yi masa tagonashi da takardar sallama da dan kudin da ba zasu kashe masa kwarnafi ba). Duk albashina a magani yake tafiya, ta kai ta kawo sai da na siyar da motata na biya masa wani kudin gwaji (test) mai tsada. Daman shi tasa motar tuni an siyar, haka mahaifiyata ta sayar da komai nata abin da ya rage mana kwangwarmin gidan da muke ciki kadai. Faduwa ta sake fasa kuka mai cike da ban tausayi. Umaimah ta girgiza kai don tausayawa, ta ce, ''Allahu Akbar! Ba ku yi waya Nigeria kun sanarwa da mahaifinku ba? Faduwa ta matse hawayen da ke gurbin idonta, cike da takaici ta ce. ''Waya sau nawa kuwa, na yi waya har na gaji. Duk lambobin da Ibrahim ya ba ni na kira daya bayan daya. Daga ta gidanmu, danginmu da abokansa. Na sanar musu halin da Ibrahim ya ke ciki, kuma tunda sauran lafiyarsa ya buga waya ya fadawa Babanmu. Ashe boye mana ake yi shima a kwance yake irin ciwonsu iri daya (cancer) ce a hunhunsu, shi ma can duk kudinsa ya kare a neman magani. Sai su yi ta min hanya-hanya wai za,a turo daya daga Baffannina ya zo ya duba shi. Na gaji dai na fito barobaro na shaida musu kudi ne babu, ko ba zasu zo ba suturo mana da kudin asibiti. Sai alkawuran karya, ko sisinsu ban gani ba. Allah Ya karbi ran abinsa, yayana Ibrahim ya rasu ranar wata litinin a asibiti. Kuka mai tsanani Faduwa ta ke, yayin da Umaimah ta dafe kirji, ta ce. ''Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Abdul-Sabur ya dafe kai, ya girgiza don tausayawa, amma bai iya cewa komai ba, sai girgiza kan da yake cikin tsananin jimantawa. Cikin kuka Faduwa ta ci gaba da magana. ''Allah Ya sa mutuwa hutu ce, din da wata cutar gara mutuwa, tsananin wahala babu irin wacce bai sha ba, ko ruwa ba ya tsayawa a cikinsa, sai ya amayo da shi, ya rame ya yi baki, gashin kansa ya kade. Ba magana sai kaga hawaye na zuba daga idanunsa idan masifar tayi masifa. Sai ni sai Mahifiyata muka rage ga talauci saboda albashin ma ba ya isa ta, dumbin bashin da yake kanmu nake biya duk wata, wanda muka ranta aka biya kudin asibiti. Duk da kokarin da nakeyi ina ta biya ban daina fuskantar cin mutunci daga wadanda suke bina bashi ba, suna ganin cinye musu zan yi. Hakika ni da ita ba ma jin dadin rayuwarmu. Saboda rashin Ibrahim ga babban tabon da ya tafi ya barmu da shi, mun kasa mance tsananin wahalar da ya sha a sanadiyyar ciwon. Mun yi waya Nigeria mun shaida musu mutuwar Ibrahim, wasu da yawa sun kira suna yi mana gaisuwa. A lokacin ne ma aka ba wa mahaifina kan waya ya yi min magana, muryarsa na rawa yake bani hakuri akan abin da ya yi mana, ya shaida min shima a kwance yake bashi da lafiya sai an kwantar an tayar. Tsananin tsanar da na yi masa sai ta ragu son da na kullace shi sosai, na yi da-na-sanin da ya zama mahaifina tunda ba ya kaunarmu, ba ya kula da mu. Amma a lokacin da yayimin wannan bayanin sai na janye tsanar. Na yi masa fatan Allah Ya ba shi lafiya, daga yadda

Chapter 5 of 33