Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zan ba ka Abdul-Sabur shine, ka koma gidanka ka shige ka rufe, abin da babu ruwanka dadin kallo gare shi. Idan ta mutu tarube ta yi wari masu gadi za su gaji da warin su balla gidan su dauke ta su binne. Idan da *yan uwanta anan a sanar musu, ballantana ma ba ta da *yan uwa ko kawa, balle saurayi saboda bakin halinta. Ni dai kaga shiga ta gida, ina da abun yi, ba zan kare a wannan yarinyar ba. Ta juya a fusace zata shige. Dan Aunty. MAKWABTAKA 6 Ya yi sauri ya tari gabanta yana magiya cikin wata marainiyar murya mai tafe da tsananin damuwa, magiya da tausasa lafazai. Ya ce, ''Faduwa, ki yi taimako don Allah ba don niba, ba don ita ba, ba don halinta ba. Ki yi don cika hakkin MAKWABTAKA, kina da ilimi, kin san yadda Ubangiji Allah (S.W.A) Ya yi magana a alkur'ani mai girma akan hakkin makwabci akan makwabcinsa. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, a lokacin da Mala'ika Jibrilu ya ke isar masa da wahayi akan hakkin makwabci akan makwabcinsa ya ce, ya zaci za'a ce makwabci zai iya gadar makwabcinsa. Abdul-Sabur ya surnano da hawaye mai yawa. Ya ce, ''Allah Shi ne Sabur, ma,ana Mahakurci, na kasance Abdul-Sabur bawan Allah mai yawan hakuri. Bana rama tsiya da tsiya, sai da alkhairi. Haka bana fushi sabida darajar sunana. Faduwa yarinyar nan tana da hakki a kanmu a matsayinta na musulma, kuma makwabciyarmu. Mu cika hakkin daya rataya a kanmu ko da ita ta ki, zai yuwu jahilci ne ke damunta, rashin sani ko kuma wani dalili nata na daban saboda shirmen yarinta da yake damunta. Tana cikin halin wuya, ciwo mai tsanani tun cikin dare ba ta runtsa ba, ina jiyo rakinta. Dr. Faduwa ta yi kasake tana dubansa, domin ya daure ta da jijiyoyin jikinta. Ya fada cikin sassanyar murya, ta ce, ''Kana so na taimake ta ko? To ta ya ya zan iya taimakon yarinyar da ta kulle gidanta, kuma ta ce a ja mana kunne kada mu sake shiga harkarta? Abdul-Sabur ya marairaice, ya ce, ''Wajen masu gadi za mu je, mu sanar musu su debo mukullai su bude ta ta baya a ga halin da ta ke ciki. Sannan a matsayinki na likita kije da akwatinki na taimakon gaggawa (first aid box) ki taimaka mata kafin a kaita asibiti. Dr. Faduwa ta ce, ''Kaje ka sanar musu idan an bude gidan an tabbatar ba ta da lafiyar da gaske, kuma ta amince na zo sai ka kirani a waya na taho da akwatina. Abdul-Sabur ya dukar da kai kasa, ya yi godiya ya hanzarta sauka kasa wajen masu gadi, don ya sanar musu. Yayin da Dr. Faduwa ta shiga gida ta fara korowa kawayenta labarin abin da ya ke wakana tsakaninsu da Umaimah. Sun fusata dajin haka suna masu roko, magiya da ba wa Dr. Faduwa shawarar cewa ko Umaimah zata mutu kada ta taimaka mata. Ya yin da haushin Abdul-Sabur ya rufe su, suka yi ta Allah wadai da irin wannan rashin zuciya tasa. Bayan mintuna goma wayar Faduwa tayi kara, ta na dubawa ta ga sunan Abdul-Sabur ne, sai ta dubi kawayenta ta yi murmushi. Ta ce, ''Ga shi nan inajin zancen zai yi min. Suka ce ''Kada ki amsa, ki kyale su can su karata. Faduwa ta ki amsawa, sai kira yake yana sake maimaitawa amma ta ki dagawa. Kwatsam suka gan shi a gabansu, yayin da ya dubi Faduwa ya dubi wayar da ke kan cinyarta tana ruri, ma'ana amsawa ne kawai ba zata yi ba. Ya girgiza kai cikin rashin jin dadi, ya ce, ''Ashe Faduwa ba ki aminta da ayar da na kawo miki ba, game da hakkin makwabci akan makwabcinsa? A cikin suratul Nisa'i Aya ta 36 Allah Ya yi magana akan makwabta. ''Kuma ku bautawa Allah, kada ku tara shi da kowanne abu.Ga mahaifa a kyautata musu kuma ga ma,abocin zumunci da marayu da matalauta da makwabci ma,abocin kusanci da makwabci manisanci da abokin gefe da hanya da abubuwanda hannuwanku na dama suka mallaka. Lallaine Allah baya son wanda ya kasance mai takama mai yawan alfahari. Sadakallahul azim. Faduwa ta dubi kawayenta, ta ce, ''Kunji yadda yake daure ni da jijoyoyin jikina ko? Ai dole na je na duba yarinyar nan. Kawayenta suka hautsine da hayaniya suna cewa, kada ta je. Abdul-Sabur ya dube su a nazarce, ya sake tabbatarwa ba musulmai ba ne, kana ganinsu zuryan ka ga Hindu. Ya juya ya dubi Faduwa cike da takaici, ya ce, ''Har zaki tsaya kina sauraron Ahlul-kitabi, wadanda ba musulmai ba, ana miki maganar Allah da Manzon Sa, maganarsu har tafi maganar mahaliccinki? Haba Faduwa kada fa ki bata a sanadiyyar wannan abu ki rasa imaninki. Abu kalilan sai ya kai bawa aljanna, haka abu kankani sai yakai mutum wuta. A sanadiyyar taimakon yarinyar nan da zaki yi, ki ceto ranta za ki iya samun rahamar Ubangiji...'' Bai rufe bakinsa ba Faduwa ta yi cimak ta mike tsaye ta shiga daki ta dauko akwatinta, suka fice yayin da kawayenta suka bisu da harara babu abinda suke ji sai haushin Abdul-Sabur da ita da Faduwar da ta biye masa. Lallai Umaimah ta galabaita, bakinta ya bushe ko makwarwar ruwa babu a makoshinta. Ta tuje gashin kanta, haka rigar barcin da ke jikinta duk ta kanannade saboda burgima. A karkashin gado ma aka zakulota saboda burgima,, ta wahala har karfinta ya kare, don haka ko yatsanta bata iya dagawa balle ta bude ido ta kalli wanda ke kanta. Daga ta bude ido sai ta rufe luuu kamar sumammiya. Nan da nan tausayinta ya lullube zuciyoyin duk bil'adaman da yake gurin, scurity uku, Faduwa da AbdulSabur. A gigice Faduwa ta bude akwatinta ta dauko allurai da magunguna ta fara aiwatar da ayyuka irin na kwararriyar likita. Abdul-Sabur ya ruga kicin ya bude firij ya dauko ruwan sanyi ya kawo ya mikawa Dr. Faduwa. Ta ce, ''A,a kada a ba ta ruwan sanyi sai dai abu mai dumi kanar shayi ko Coka oat. Don haka Abdul-Sabur ya sake garzayawa kicin ya jona ruwan zafi a butar lantarki (kettle), ya bude lokokin kicin din sai ga komai a jere reras wajen kayan abinci daban, kayan shayi daban kwanuka,kofuna,cokula. Kicin dinta a tsare ya ke ga tsafta ko ina. Ya dauko kofi da cokali ya sake daurayewa sannan ya zuba sukari kadan, milo da madara, sannan ya zuga tafasasshen ruwan zafi akai, ya jujjuya ya dauko ya kawo. Dr. Faduwa ta karbi kofin ta dago kan Umaimah akan cinyarta ta dinga tarfa mata da cokali, sai sha take sabida tsananin yunwa da kishirwar da ta ke addabarta. Dr. Faduwa ta dubi security ta ce, ''tana bukatar karin ruwa da gwaje-gwaje a gano kan ciwon, dole a kaita asibiti. Sai suka gaggauta kiran wayar asibiti suka bukaci da su turo da motarsu (ambulance) za,a dauki mara lafiya. Abdul-Sabur ya bude durowar kayanta yana dubawa, ba tare da ya san wanda zai daukar mata ba. Kaya ne a goge a linke sanka-sanka, sai kamshi suke yi, daga baya ya riguna da bangarensu, siket, abayoyi, mayafai da dai sauransu. Ya jawo wata doguwar riga ja (abaya) da dan kwalin ya hada ya mikawa Faduwa, ya ce ta saka mata. Ya roki masu gadi da su fita falo su bari mace ta shityata. A falo ne ya isa kan teburin cin abinci a in da ta dora laptop dinta da takardunta, ya shiga babbankadawa, a nan ne ya ke ganin sunanta ajikin takardun, ta rubuta UMAIMA BELLO, a she ba sunanta MAYE ba? To me kalmar MAYE take nufi? Ya karanta a baiyane, ya sake maimaitawa, sai yau yasan sunanta. Ya ci gaba da bankada durorwoyinta da suke falon, takardu ne kala-kala duk na makaranta. A jikin durowar Talabijin stand ya ga wata *yar karamar jaka ya bude ya ga himilin hotunanta ne. Ya fara budewa cikin sauri yana dubawa, ya ganta ita da danginta mata da maza, yara da manya, da kuma tsofaffi. Wato iyayenta da kakanninta. Ya cika da mamaki da ya ga wasu hotunan, gashi babu wanda zai iya tambaya a yi masa bayani. Bai gama kallo ba ya ji jiniyar mota (zmbulance), kan kace kwabo sun hayo da gadonsu, suka shiga dakinta cikin gaggawa, suka dorata akan gadon mai taya suka turota a shassheme kamar gawa sai numfashi ta ke yi sama-sama. Abdul-Sabur ya shiga dakinta da sauri ya bude jakarta ya fara bincikawa yana neman I,D card dinta bai gani ba, sai dai yaga passport dinta. Ya yi sauri ya bude ya duba, ya ga hotonta da sunanta radau, sai yau yasan kasarta ashe yar Nigeria ce? Ya zakulo *yar karamar jaka (wallet). A cikin jakar ya bude anan ne ya ga I.D card dinta na makaranta wato FTMS, da wasu kuma na wasu makarantunta na can Nigeria. Ya hada ya mikawa malaman asibitin. Shi da masu gadin gidan ne suka kukkulle mata ko ina a gidan, sannan suka watse. Dr. Faduwa ta koma gidanta, security suna rike da makullin gidan suka koma dan dakinsu a bakin get, yayin da Abdul-Sabur ya koma gidansa. Umaima kuwa na can akan gadon asibitin ana ceto rayuwarta don ta galabaita, bata ciki hayyacinta. Daga asibitin aka yi wa makarantarta waya suka tura malamai mata guda biyu, su ne za su dinga zama da ita. Ya kasa zaune, ya kasa tsaye, balle ya kwanta, babu ma maganar cin abinci a wajen Abdul-Sabur, ya shiga damuwa sosai, saboda tausayin rai. Babban abun tausayin ma shine rashin hakikan *yan uwanta a kusa ga babu waya balle a buga a sanar musu. Ko saboda hakin mutuwa. Addu,a yake, Allah Ya sa ta rayu kada ta mutu, ba ya son ta mutu duk da ta tsane shi, ba ta ki ta ga ba ya doron kasa ba. A daddafe ya bari gari ya waye, da sassafe ya shirya ya fito wajen masu gadi, da suka gaisa sai ya tambaye su adireshin asibitin da aka kai Umainah. A rubuce suka bashi kamar haka:- Sime Darby Medical Center Subang Jaya Jalan SS12/1A 47500 Selangor Darul Ehsan, Malaysia. Babu wata matsala yasan ma asibitin, ba shi da nisa da makarantarsu. Sai ya yi musu godiya ya nufi asibitin. Yana hanya yana fargaba guda biyu. Na farko yana fargabar yadda zaiga jikinta, sauki ko tsanani. Sannan na biyu yana fargabar yadda za ta yi idan ta ganshi, farin ciki ko takaici? MAKWABTAKA 7 Ko ba a fada masa ba, yasan ta tsane shi, ba mamaki idan ta ganshi ta disga shi. Shi dai koma mai zai faru ya ji ya gani sai ya je ya saka a ransa duk abin da yake yi yana yi ne saboda Allah, kuma a wajenSa yake neman sakayya. Ya isa asibiti a reception, ya yi musu bayanin suna da yanayin ciwonta, na da nan suka fada masa hawa na uku ta ke, da lambar dakin da ta ke. Ya yi godiya ya nufi dakin, yayin da fargabar da yake ciki ta sake tsananta. Yana ta addu'a dai har ya isa kofar dakin, ya kwankwasa a nutse gami da yin sallama, sai yaji muryar wasu mata sun amsa masa sannan ya tura kofar ya shiga. Aka hau kallon-kallo tsakaninsa da matan biyu, daya *yar Malaysia ce, daya kuwa India ce. Yayin da Umaimah ta ke sheme akan gado ana mata karin ruwa, idanuwanta a rufe alama dai baccci ta ke yi. Ya karaso jikin gadon ya gaishe su, sannan ya gabatar da kansa cewar shi makocinta ne, sannan suka saki ransu don da sun yi masa kallon rashin fahimta. Ya tambayesu yaya me jikim? Suka yi ta koro masa bayanin abubuwan da suka faru da ita a jiya, cewar ciwon cikin ya tsananta, amma yau da safe ta sami sauki sosai, har ta sami bacci. A cikin bayanansu ya gane cewar ma,aikatan makarantarta ne, sai ya ji hankalinsa ya kwanta tun da ga masu kula da ita Allah Ya kawo. Ya je kanta ya tsaya ya yi ta tofa mata addu,o,i na neman sauki, afuwa, rangwame daga Rabbul-Samawati. Ya ce da su, ''Idan ta tashi a ce Abdul-Sabur yana yi mata sannu. Ya yi musu sallama ya tafi sai yanzu yaji hankalinsa ya kwanta, da ya ga jikin da sauki. Da yammacin ranar Dr. Faduwa zata tafi unguwa ta biyo ta gidansa ta iske shi a zaune a falo ya yi tagumi. Kallo daya ta yi masa ta san bayajin dadin rayuwarsa. Ta sami kujera ta zauna ta gaishe shi, sannan ta tambaye shi. Shin yana da labarin halin da marar lafiyar nan ta ke? Ya amsa mata da, ''eh ta sami sauki sosai, na je na duba ta ma dazu. Sai ta yi kasake tana kallonsa, da alama tana so ta ji yadda suka karke. Ta tambaya da sauri ''Ta ganka? Kun gaisa? Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''gaskiya bata ma san na je ba, saboda tana bacci. Dr. Faduwa ta yi ajiyar zuciya ta ce, ''Barkanka, na taya ka murna da ba ka sameta idon ta biyu ba. Ya yi mamaki dajin kalamanta, sai ya tambaya, ''Me yasa kika ce haka?'' Ta tabe baki ta ce, ''Da ba zata amsa maka ba, saboda yadda nasan tsanar da ta yi mana. Ya kyalkyale da dariya, ya ce, ''Kai Faduwa, ai abun bai kai haka ba. Ni dai uzirin da nake bata shine, na san tana da wani dalilinta na daban, aka bibiya laifin wasu ne ya shafemu. Ina yi mata addu'a Allah Ya sa ta gane. Faduwa ta ce, ''Ai ba don kai ba yarinyar nan ko zata mutu ba zanje kanta ba. Kai ne dai da naci ka kasa rabuwa da ita, na rasa dalili. Koda yake na fahimce ka, kana son yarinyar nan sosai, kuma har cikin zuciyarka. Abdul-Sabur ya gyra zama ya zazzare ido don mamaki, sai ya girgiza kai. Ya ce, ''Babu ko daya, da za ki yarda da ni yi miki rantsuwa, wallahi babu maganar so a tsakanina da wannan yarinyar. Haba Faduwa kamar ba ki san halina ba, shekararmu biyu da ke agidan nan, ya kamata ki fahimce ni ki kuma fahimci irin macen da take burge ni. Na daya, kin sanni da son macen da ta mallaki hankalinta, ta san rayuwar duniya sosai, ba *yan matan nan da suke rawar kai ba, wai su *yan boko. Umaimah yarinya ce karama ba sa,ar soyayyata ba ce. Na biyu halayenta kwata-kwata ba su yi min ba don ba ta da tarbiyya, fitsararriya ce, ba ta burge ni ba don ina son mace mai kunya da sanin darajar na gaba da ita. Na uku, musulma ce amma ba ta da ilimin aiwatar da addinin don ba ta bin abin da Allah ya ce, ba ta kyautatawa makwabtanta ba, bata bayar da hakkin MAKWABTAKA. Inajin tausayinta ne kawai kasancewarta mace, kuma yarinya karama a kasar da babu iyayenta, ba dangi ba kawayenta. Ina so na nusantar da ita tasan hakkin makwabci akan makwabcinsa, ko don gaba ma tasan yadda zata zauna da makwabtanta ko bayan ta yi aure. Na dauketa kamar karamar kanwata mai neman shawarata. Yanzu da na biye mata shirmen nan da ta ke na babu ruwanta da mu, da ta yaya za,a yi a san tana cikin gidan nan a kwance babu lafiya? Ai ko mutuwa ta yi ba za,a sani ba, sai dai idan ta mutun ta kwana uku ta rube wari ya ishi jama,ar gidan a balla kofa a ganta. Ina amfanin irin wannan alhalin mu dukka musulmai ne? Faduwa, ina tausayin mace, musamman wacce ba ta gaban iyayenta, ko hannun mijinta. Duk inda na ga matashiyar mace sai na ji ina sonta, saboda ina da kanwa wacce na fi sonta a duniya fiye da kowa da kuma komai da na mallaka. Dr. Faduwa ta yi murmushi, ta ce. ''Nasan da haka Abdul amma fa yarinyar can ba *yar mutunci ba ce. Duk inda ka kai ga nuna mata hanyar Allah ba zata saurare ka ba. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Wanda yake abu saboda Allah baya cewa ya gaji kuma baya fushi ya ce ya daina. Ina yi mata addu'ar Allah Ya ganar da ita, yanzu a matsayinki na likita idan kika duba yarinyar nan (psychologycally) za ki ga tana da matsala a rayuwarta. Zai yiwu an guma mata wani abu ne na takaici ta yi hijira ta dawo nan, amma ya za,ayi ace mace ita kadai ko kawa ba ta yi, balle saurayi ko miji, kuma ko wayar hannu ba ta da ita (handset). Wannan fa abin dubawa ne Faduwa. Dr. Faduwa ta gyada kai, ta ce, ''Na lura tana cikin damuwa, amma duk damuwarta ai ba ta fi ni ba, amma na ke daurewa na ke shiga jama,a na ke gaisawa da kowa lafiya. Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Ka ji ta, wai ba ta kai ki ba ni me yiwuwa duk na fi ku damuwa, amma nake daurewa. Kowanne mutum da kika gani a duniyar nan yana da tasa matsalar, kuma tasa kadai ya sani, sai ya yi ta ganin kamar ya fi kowa matsala. Dr. Faduwa ta ce, ''Haka ne, Allah Ya yaye mana. Zo ka raka ni 'KL Sentral zan je na ga wata kawata ta haihu. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''yi hakuri wallahi bazan iya zuwa ba. Bana jin dadi saboda bana iya cin abinci, ba na bacci kwana biyu ke nan. Dr. Faduwa ta mike tsaye ta yi dariya, ta ce, ''Lallai kai kafi kowa ma tausayi, akan ciwon yarinyar ne ka kasa bacci da cin abinci? Ai kuwa gara ma ka cire ciwon nan a ranka, kaci gaba da harkokinka idan dai wannan ce ina nan da kai tana warkewa zata ce ba ta san mu ba. Abdul ya yi dariya ya ce, ''Ke ma na ga alama kin kasa fahimta ta, amma ina fatan ki fahimce ni nan gana. Faduwa ta fice ba tare da ta sake cewa komai ba, ta bar Abdul-Sabur a nan a zaune yana tunani. Bayan kwanaki hudu, sannan aka sallamo Umaimah daga asibiti, sai da matan nan biyu suka raka ta har cikin falonta. Bayan sun roke ta ta dawo gidansu ta zauna har jikinta ya yi kwari saboda ba dadi zaman ita kadai ta ki amincewa, ta ce su barta zata iya zama ita kadai. Suka ba ta magunguna suka fita suka tafi a motar da suka zo. Fitarsu da kamar mintina goma, Umaimah na zaune har yanzu akan kujera tana tunanin tashi ta rufe kofa sannan ta shiga ta yi wanka, sai taji ana danna kararrawa a bakin kofar gidanta. Ta yi mamaki marar misaltuwa, ta taso da sauri ta daga labule don kofar a bude ta ke. Abdul-Sabur ta gani cikin kyakykyawar shigarsa ta wando baki (jeans) da riga fara (Shirt). Kamshin nan nasa na turaren (Dolce Gabbana) shi ne ya daki hancinta, kamshin nan ba karamin tuno mata baya ya yi ba. Ta yi mamak da jin yau ya ambaci sunanta 'Umaimah' maimakon 'Maye' da yake kiranta a baya. Sai ta ji saukin tsanar da tayi masa a baya. Ba ta amsa masa ba, ta ci gaba da sauraron abin da zai ce don ta matsu ya fada ya wuce, ba ta kaunar ya dade a bakin kofarta. Ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Ya ya jikinki? Ina fatan kin sami sauki sosai? Allah Ya baki lafiya. Ta saki labulen ta labe ba tare da ta amsa masa ba. Ya ci gaba da jiran amsar da zata ba shi, ya ji ta yi shuru. Sai ya gyara tsayuwa. Ya ce, ''Umaima, ba na binki da wata manufa illa alkhairi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, kada ka kwana ka koshi makocinka ya kwanta da yunwa. Haka ka dubashi idan bashi da lafiya. Idan har makwabci bai amince da makwabcinsa ba yana gudun zai cuce shi ta hanyar fada masa bakar magana, zagi ko duka, ko kuma neman halaka shi, to wannan makwabci ba shi da rabo a lahira. A kwai kissar wata mata da ta rasu bayan kuma an shaide ta da yawan sallah, azumi, kyauta sadaka. Amma aka ganta a wuta. Da Annabi (S.A.W) Ya binciki abubuwan da ta aikata a rayuwarta ta duniya sai aka shaide ta ta cika komai banda abu daya, shine ba ta kyautatawa makwabtanta. Tana musguna musu, ba ta zauna lafiya da su ba, wannan dalili shi kadai ne ya kaita wuta (Wa'iyazubillah). Don haka ya ke kanwata Umaimah ki yi hakuri ki zauna da MAKWABTANKI lafiya, ki ba ni ba ko don nan gaba. Na barki lafiya, duba ki na zo yi ina fatan Allah Ya baki lafiya, bissalam. Ya juya ya tafi gidansa. Sai ya wuce ya bar ta a nane da jikin labule ta kasa motsawa, daga dukkan alamu wa'azin fa ya shige ta, dan ta tsorata, tabbas ta san gaskiya ya fada mata tsagwaronta. Amma ba ta jin zata iya aiwatar da nasihohinsa, saboda dalilinta da yawa akan cuta da musgunawar da MAKWABTANTA suka dade suna yi mata a doron kasa. Ta girgiza kai ta fada a bayyane, ''Zam iya amincewa da kowa a duniya, amma ban da makwabtana, saboda sun zalunce ni.'' UHM to ai da sauki tunda ni ba makwabci bane, da fatan zaki aminta dani Umaimah MAKWABTAKA 8 Ta jawo kofarta a fusace ta datse, yayin da ta hau faman huci, ranta ya duguzuma ya baci. Ta tabbatar muddin ba ta bi nasihar Abdul-Sabur ba tana cikin halaka. Duk abin da ya fada gaskiya ya fada mata, amma kuma ya tuno mata da kasurgumin bacin ran da ya faru da ita a baya tsakaninta da MAKWABTA. Ta dade a zaune a falo tana tunanin yadda aka yi MAKWABTANTA suka san ba ta da lafiya, sai ta shiga mamakin yadda ma aka shigo gidan akasan bata da lafiya alhali kofarta a kulle. Ta tashi a hankali ta shiga dakin, ta tsaya tana kallon inda ta kwanta, ta shiga dauki ba dadi da kwakwalwarta tana kokarin tuno abubuwan da suka faru da ita kafin ta fara ciwon ciki. Abin da zata iya tunawa shi ne, ta saka rigar bacci ta kwanta akan gado, yayin da ta fara jin ciwon ciki mai tsanani ya turnike ta. Tun tana juyi harta fado kasa abin da zata iya tunawa kenan. Ta tsuguna kasa a hankali ta dauko rigarta a tsakar daki ta dudduba, sai ta shiga dogon tunanin yadda aka yi aka sauya mata rigar jikinta. To yaya ma aka yi aka san bata da lafiya? Shine abin da yake damunta. Tabbas ishara ce Allah Ya nuna mata, saboda mutum dadi ne da shi. Duk in da ka kai da kin mutane ka kwanta kai ka dai a cikin gida ka mutu dole mutane za su bude su dauke gawar, su bunneka, don haka dole mutum ya yi mu'amala da mutane. Ta dade a zaune tana tunani, har da koke-koke, dom ita ma ba haka ta so ta kasance tare da jama,aba, dole ce ta saka ta ko ta fito da niyyar gaisawa da jama,a tana ganinsu sai ranta ya baci ta fasa. Ta jima a zaune a gefen gado tana kuka, sannan ta tashi ta shiga wanka. Bayan ta yi wanka ta yi sallah, sannan ta lallaba ta shiga kicin don dafa abin da zata ci, saboda yunwar da ta ke addabarta. Ciwo ne yake samun mutum a lokaci guda, sauki kuwa sai a hankali. Babu ciwon cikin dai a yanzu amma ba ta jin karfin jikinta da dadin bakinta. Tana kuma shan magungunanta, don haka gaba daya satin Umaimah ta kasance a gida ba ta fita makaranta ba. Sai da ta tabbatar ta warware sosai, sannan ta shirya ta fito zuwa makaranta, ranar litinin da safe da misalin karfe tara kenan. A cikin lift Umaima ta hadu da Dr.Faduwa, mai hali ba ya fasa halinsa, ba ta yarda ta hada ido da Dr.Faduwa ba, balle ta yi mata sallama. Kasancewar su takwas ne a cikin lift din, sai ta sami lungu ta labe daga bayan Faduwa har suka iso kasa inda kowa ya firfito. Jefa kafarsu ke da wuya akan baranda suka yi kicibus da Abdul-Sabur daga dukkan alamu Faduwa yake jira. Daga yadda ya ga Umaimah ta zabura ya san ta yi mamakin ganinsa dai-dai wannan lokacin, kuma a wannan waje. ''Zo ki wuce''. Inji Abdul-Sabur ya ce da Umaimah gami da matsawa ya bata hanya. Ta sunkuyar da kanta kasa ta wuce abinta ba tare da ta gaishe shi ba kamar yadda ya ke sa ran samun gaisuwarta ko don wa,azin da yayi mata. Faduwa ta dube shi ta juya ta dubi Umaimah, ta girgiza kai ta ce da shi. ''Ka ga abin da nake fada maka ko? Ai mai hali ba ya fasa halinsa. Tafiya suke zuwa get din fita, yayin da Umaimah ke gabansu, sauri kawai ta ke yi, don kada ma ta jera da su. Amma duk da haka takan jiwo wasu abubuwan da suke fada a kanta. Faduwa fada ta ke yi da karfi kan rashin tarbiyyar Umaimah, yayin da Abdul-Sabur yake nemar mata uziri cewar, akwai dalilinta na yin haka kada tayi saurin yanke mata hukunci. Umaimah ta tabe baki ta ce a ranta, ''Koma dai me zaku ce matsalarku ce, ku ta shafa dan ba kwa gabana, da zaku rabu da ni, da na fi jin dadi. Ta kara daga kafa tana sauri, ta haye saman bene a inda zata haye gada zuwa makarantarta. Daga nan ba ta waiwayo su ba, bata san inda suka bulle ba kuma. Tana kyautata zaton tasi suka tsayar suka shiga. **************************************** Zangon karatu na karshen 2nd semester ya zo karshe, har an fara jarabawa a wasu makarantun, yayin da makarantar su Umaimah har sun yi nisa da farawa. Ta yi karatu cikin dare, ta yi da safe, ta yi da maraice, yayin da ta ji kwakwalwarta ta yi kamar zata buga don takura. Harta daina fahimtar abin da ta ke karantawa don haka sai ta harhada ta rufe. Ta fito baranda ta tsaya tana kallon titi, motoci da mutanen da suke giftawa. Iska mai sanyi ta yamma ce ta ke fifitawa, ta sake gyra tsayuwarta tana kallonsu, sai ta ji ta fara washewa daga damuwa da gajiyar karatu. Sallama ta ji an yi mata babu bata lokaci ta kalli inda muryar ta fito, ko ba a fada mata ba ta san AbdulSabur ne dan daga saitin gidansa muryar ta fito. Ta dube shi ta ga yana tsaye a barandarsa yana yi mata murmushi. Ya yi matukar mamaki da ya ji ta amsa da ''Wa'alaikassalam. ''Ya ya karatu? Ya yi karfin halin tambayarta. Wannan karon dai bashi da amsa, don haka ya ja fatar bakin ya kame, bai sake yi mata magana ba. A zatonsa zata koma cikin gida kamar yadda ta saba idan ta ganshi, sai ya ga ba ta tafi ba, amma ba ta sake daga ta dube shi ba. Ya dade a tsaye yana kallonta, sai ya koma ciki ya rabu da ita. Sai da ta ji ana kiran sallar magaruba ta koma cikin gida daga nan bai sake ganinta ba, sai da yammar washegari tana dawowa daga makaranta da alama dai jarabawa ta je

Chapter 3 of 33