Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yanzu Dr. Faduwa ba ta daina buga kofar ba gami da danna kararrawa ba kakkautawa. Umaimah tana jikin kofar tana kallonta ta ki ta bude, fiye da mintina goma. Daga karshe Dr. Faduwa ta zaro wayarta ta kira Abdul-Sabur cikin harshen turanci ta ke shaida masa tana ta bugawa ba,a bude ba, da alama dai babu kowa a gidan. Ba ta ji amsar da ya bata ba, sai taga ta kashe wayar ta ci gaba da kai-kawo a koridon. Ba jimawa sai ga AbdulSabur ya bayyana, sanye yake da doguwar riga jallabiyya fara da carbi a hannunsa, daga dukkan alamudai daga masallaci ya ke. Ya hau bugun kofa da karfi, yana danna kararrawa shi ma kamar yadda Dr. Faduwa ta yi ta gaji ta bari. Umaimah na labe tana kallonsu ko kwakwkwaran numfashi ba ta yi balle ta yi tari. Banda haushin su ba abin da ta ke ji, ta rasa dalilin shishshigin da suke yi mata, sun takurawa rayuwarta. Saboda takura ta baro kasarta ta zo inda ba,a taba saninta ba. To saboda me za su saka mata ido, dole ne a yi mutuncin? Ta ci gaba da saka yadda zata bullowa Abdul-Sabur ya kyale ta, ta yi rayuwarta ita kadai, yadda ta tsarawa kanta. Nan dai ta ga su Abdul Sabur suna tsaye suna shawarar yadda za su yi. Sun yi shawara kala-kala, sun yi shawarar kiran jami,an su zo su balla kofar su gani, ko suje makaranta su fada, ko kuma su sanarwa masu gadin gidan (security). Shawarar da suka tsaya mafi sauki, ita ce su fara sanarwa masu gadi. Nan da nan taga sun juya sun nufi lift ta tabbatar bakin get suka tafi. Ta ruga daki da gudu ta je ta saka kayanta, wata doguwar rigar leshi ce (gown) ta saka da dan karamin hijabi ta dawo bakin kofar ta tsaya tana jiran wanda Allah Zai kawo. Ba jimawa sai ga security guda biyu a bakin kofarta, hannayensu cike da makullai suna kokarin soka makulli a jikin kofar gidanta, sai ta yi wuf ta bude ta bayyana a gabansu cike da mamaki a fuskarta. Cikin harshen Turanci ta tambaye su, ''Lafiya me yake faruwa ne? Sai suka yi cirko-cirko suna kallonta amsa daya ta gagare su. Da kyar dayan ya bude baki ya ce. ''Makwabtanki ne suka lura sati guda ba sa jin motsinki, kuma ba,aga fitarki ba, sun buga ba ki bude ba, shine suka sanar mana za mu bude gidan mu ba ko lafiya? Ta hade rai tare da yamutsa fuska, ta ce, ''Ina nan, lafiyata kalau. Sai dai inaso ku jawa wadannan makwabtan nawa biyu kunne, mace da namiji su fita daga harkata, musamman namijin yana takurawa rayuwata. Ku fada masa ba shi ba ni, ya rabu da ni tunda ba zamansa nake yi ba. Suka amsa mata da, ''To zamu sanar musu... Basu rufe bakinsu ba, sai ga Abdul-Sabur da Dr. Faduwa sun taho da sauri hankalinsu a tashe suka nufo su. Kafin su karaso Umaimah ta ce da ma'aikatan ''Good night. Ta shige gida ta banko kofa ta datse ta ci gaba da lekensu ta jikin hudar kofar. Dr. Faduwa ta tambaya a dimauce, ''Kun bude gidan, tana nan lafiya? Sai suka shaida musu duk abin da ya faru, kuma suka dora da sanar da su sakon da ta bayar a fada musu. Dr. Faduwa ta dubi Abdul-Sabur shima ya dube ta, sai ya sunkuyar da kai kasa cikin jin kunya ya rasa abin da zai ce. Ma'aikatan suka wuce suka barsu a nan a tsaye suna ta kallon kofar gidan Umaima. Can Dr. Faduwa ta nisa cikin kufula. ta ce, ''Abdul tsayuwar me muke yi anan? Mu koma gidajen mu mana, ai maganinmu kenan da shiga shirgin da babu ruwanmu. Kai duk ka jawomin harna fara baccina mai dadi ka ishe ni da waya in zo in duba ta. Ashe duk bugun nan da muke tana jinmu don tsabar rainin hankali ta kyalemu saboda tsabar tsana. To ma ye ya yi zafi zamu zauna muna wulakanta kanmu, muna yar da girman mu akan *yar yarinya karama kamar wannan? Allah Ya gani mun fita hakkin MAKWABTAKA. Abdul-Sabur ya gyada kai ya ce, ''Kin fadi gaskiya Faduwa, ki yi hakuri da na jawo miki, insha Allah bazan kara jawo miki irin wannan ba. Sai suka juya suka tafi, yayin da Umaimah ta jingina ajikin kofar ta dade a tsaye, ita kanta ta rasa dalilin da yasa ta ji aranta ba dadi. Ta san tabbas bata kyauta musu ba, ai wanda ya kulaka ya damu da hakin da kake ciki mai kaunarka ne. Amma ba laifin ta ba ne, zuciyarta ne batason makwabtaka. Ba ta so adinga bada hakkin KAKWABTAKAR. **************************************** Gaba dayansu jarabawa suke yi, don haka kowannensu ba ya zama a gida, gari na wayewa sai su fice makaranta, sai da magaruba kuma. Wasu lokutan Umaima tana rigasu dawowa, tana daga kan barandarta ta ke hango dawowar su, sai tayi sauri ta koma cikin gida, don kada ma Abdul-Sabur ya hau sama ya bude barandarsa ko wundo ya ganta. Shi ma ya sha hangenta tana tafiya, ko tana dawowa daga makaranta, amma bai sake marmarin saukowa su hadu ba. Ya cika da mamakin dalilin da yasa ta ke wannan muguwar zuciya kamar ba musulma ba, harya fara tunanin kilama ba musulma ba ce, hijabin dai kawai take sakawa don ta saje da *yan kasar kamar yadda wasu baragurbi ke yi idan suna son su cimma wasu manufofi nasu. A haka suka ci gaba da zama har suka gama jarrabawar semester, aka rufe makarantu. Da yawa daga dalibai suna ta shirin tafiya gida hutu, saboda yana da yawa yayin da wasu irin su Umaimah suka mike kafa ba in da za su je. Abdul-Sabur ya yanki tikitin jirgin sama na komawa kasarsu Ghana don yin dogon hutun nan. Haka Dr. Faduwa ita ma a satin zata tafi kasarsu Egypt. Don ta shekara ba ta je ba. Ranar da Abdul-Sabur xai tafi harya saka kayansa a tasi sai ya garzaya gidan Umaima ya sakale wata farar takarda a jikin kofarta, ya juya da sauri ya tafi. Jirginsa na dare ne dan haka kwana da yini suka yi a hanya ya isa Accra babban birnin Ghana. Sai bayan tafiyar Abdul-Sabur da kwana uku Umaima ta fito zata je Bukit bin tang za ta yi cefane, sai ta razana da ganin doguwar wasika a jikin kofarta, alhali bata da kowa, kuma ba ta san kowa ba a kasar. Ta dade tana tofa addu'o'i kafin ta taba takardar, sannan ta dangwala hannu a kikin takardar, ta yi sauri ta cire hannunta alamun tsoro, kai ka ce wuta ce ta done ta. Ta sake mika hannu a karo na uku kamar mai tsantsani, kamar wacce zata taba kashi ta zaro takardar ta bude a tsorace. MAKWABTAKA 4 Ba komai ba ne a cikinta illa zankadeden rubutu cikin wani kayataccen turanci. Ta fara karanta saman, sallama ce cikakkiya aka yi mata. Ko waye mai wasikar nan cikakken musulmi ne, don haka ta sami kanta da kosawa ta karanta abin da ya ke cikin takardar. Cikin nutsuwa ta hanzarta karanta cikakken sunan marubucin wasikar Abdul-Sabur Abdul-Rashsid, wannan ne ya sa ta yi kokwanton ko ba ita aka yi wa takardar ba, kuskure ne aka samu don ba ta jin ta taba cin karo da mai irin wannan sunan. Ta manta a lokacin da mutumin nata mai kiranta da MAYE ya fada mata sunansa. Ko da ta fara karanta layi na biyu daga cikin wasikar sai ta ga kalmar 'MAYE' ta bayyana, don haka ta tabbatar ta tabbatar wasikar ta ta ce, daga makwabcinta ta ke. Sai ta ji ranta ya baci, ta yi kwafa ta gyada kai saboda takaici. Ta yamutse fuska ta fara karantawa a shelake. Ta gyara tsayuwarta, ta gyara gilashin idonta sosai ta ci gaba da karantawa, nan da nan taji kafarta kamar ba zata iya daukarta ba, saboda sagewa hade da tashin hankali. Sai ta ji ba zata iya fita ba kuma, ta koma cikin gida ta zauna a gefen gadonta tana karantawa. Ta na sake maimaitawa, yayin da taji kanta ya yi mata nauyi, zuciyarta tana ta bugawa kamar zata fashe. Ta jji ta shiga damuwa marar adadi, ta ji kamar an zare mata lakka. Wai shin me yake faruwa? Me Abdul-Sabur ya rubuta mata ne da ya ta ba zuciyarta haka Oho? Allah Shi Ya barwa kanSa sani. Har ta kwanta cikin dare ta ji maganarsa tana yi mata yawo a kwakwalwarta, sai ta laleba fitilar da ke gefen idonta ta kunna ta sake jawo wasikar a karkashin filonta ta karanta, ta sake maimaitawa. Hakika maganganun gaskiya ne, amma tana ganin ba zata iya bin gaskiyar nan ba, don zata takura. Daman masu magana suna cewa, gaskiya daci ne da ita. Abin da ya rubuta kuwa ba wani abu ba ne illa aya ce guda ya dauko sukutum don ya wa,azantar da ita, don yana tunanin jahilci ne yake damunta. Da Turanci ne amma ga fassarar kamar haka:Assalamu alaikum warahamatullahi wa barkatuhu. Ya *yar uwata musulma 'MAYE' ina matukar jin ciwon halayenki a matsayinki na musulma. Shin ko kin san MAKWABCI a musulunci? A'a ba ki sani ba, don da kin sani da kin dinga amsa sallamar MAKWABTANKI. Idan ni namiji ne kina zargin zan cutar da ke. Dr. Faduwa fa? Ki yi tunani ki gyara halayenki. A cikin arba,una hadis, hadisi na goma sha biyar Manzon Allah (S.A.W) ya ce, ''Duk wanda ya zama ya bada gaskiya da Allah da ranar lahira, to ya kyautatawa makwabcinsa. Ki sani makwabci ba karamin hakki gare shi akan makwabcinsa ba. Daga karshe ina yi miki sallama na tafi kasata Ghana. Allah ya kaddara saduwarmu, amin. Daga Abdul-Sabur Abdul-Rashid. **************************************** Dr. Faduwa ma ta tafi kasarta Egypt, bayan tafiyar AbdulSabur da kwanaki uku. Sun tafi sun barwa Umaima gidan sai ta yi ta leke-lekenta ita kadai babu mai kulata bare ya takura mata. Tama yawan tsayawa baranda ta yi ta kallon titi, idan ta gaji da tsayuwa akan baranda, sai ta jawo doguwar kujera (stool) ta zauna, idan ta fara gyangyadi sannan ta tashi ta shiga cikin gida, ta kwanta akan doguwar kujerar falonta, ko kuma ta wuce daki kan gadonta. Ba ta cika yin girki ba, sai dai tayi ta shan shayi da biskit, ko lemo (juice) da biskit abincinta ke nan. Sai jifa-jifa take dafa abinci, shima ba wani kayatacce ba ne, shinkafa da wake da mai da yaji ne saboda ba ta da walwalar da zata nutsu ta shiryawa kanta abinci mai dadi. Tana sallah ta yi addu,a sosai, haka kuma ta ke ware lokacin da take shirgar kuka, kusan kullum sai tayi wannan kukan saboda tuna baya. Tabbas kawai rayuwa ta ke amma ba ta jin dadin rayuwarta, tana iya kwana biyar bata furta kalma daya ba, banda karatun sallah bata magana. To idan ta yi maganar ma da wa za ta yi? Daman da tana da waya ne ta amsa waya ta kira ko a kira ta, to ba ta da waya don bata bukatar asan tana raye. Anya kuwa rayuwa zata yiwu a haka? Ace mutum shi kadai zaiyi rayuwa a duniya, babu dangim babu MAKWABTA, babu abokai? Kai abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, inji masu iya magana. Umaimah dai haka ta zabarwa kanta, sai ta dade tana kallon barandar Abdul-Sabur, ta ga kamar zata ganshi amma sai taga wayam! Idan iska ta kada wundon kabule ya kada, sai ta bude ido tana kallo, sai ta zaci motsinsa ne sannan taga ba shi ba ne. Ashe dai ko ya ya mutum yake dadi ne dashi? Tabbas tana jin ba dadi da ta zamo babu wanda ya san da ita. Ga shi anyi hutun makarantu balle ta je makaranta duk da ba hira ta ke da kawaye da abokai ba, amma dai tana dan jin sanyi a ranta, kuma tana rage lokaci akan dogon zaman da ta ke yi da ta ke yi agida ita kadai. Dare ya ki yi da wuri, idan da daddare ne ta ga gari ya ki wayewa da wuri. Dogon hutu ne aka basu na tsawon watanni uku, gashi ko wata daya ba ta cika ba, zaman duk ya gallabe ta. Tana ta sassaka abubuwa aranta. Ta yi shawarar ko ta tafi Negeria, amma garin da ba a taba saninta ba ta je ta gama hutunta ta dawo? Ko kuma ta tafi dubai ta shakata ko zata ga abubuwan da za su nishadantar da ita, ta ga jama,u kala-kala daga kasashe daban-daban? Amma tana fatan kada Allah Ya sa ta hadu da *yan kasarta *yan garinsu wadanda suka taba saninta a rayuwa. Domim dubai ta zama matattara, kuma cibiyar cinikayya mutane daga kowacce kasa a duniya zuwa suke. Sai ta ga da taje Dubai me zai hana ta tafi Saudia don tayi umara ta fadawa Allah bukatunta duk da tasan duk inda bawa yake ya yi addu,a Allah Yana ganinsa, kuma Mai amsawa ne. Yadda rayuwa ta kuntata a gare ta ina ita ina maganar nishadi? Ai gara ta je Saudia, ta kaura Ka,aba da Shabbaki, tunda ita a ranta ta fi kaunar mutuwa da ace ta ci gaba da rayuwa a haka. Sai ta surno da hawaye zafafa a lokacin da take binciko Passport dinta, tana tunanin yadda rayuwa ta cunkushe ta cakude mata cikin dan kankanin lokaci tana karamarta. Ta fada a bayyane yayin da ta saka gefen hannunta ta sharce hawaye. ''Alhamdu lillah alah kulli halin''. Ta fada a bayyane. Yadda taga dare haka ta ga rana, tana ta sake-sake iri-iri a ranta. Kafin gari ya waye zuciyarta ta tsayar mata da shawarar gwara ta tafi Saudia. Gari na wayewa laraba ce, misalin karfe goma sha daya na safe Umaima ta fito a shirye tsaf cikin kyakykyawar shigarta, dogon hijabi ne har kasa. Babu abin da ake iya gani a fuskarta sai tafukan hannayenta. Ta ratayo jakarta mai dauke da Passport dinta da kudi masu yawa. Sannan ta hado da ATM Card dinta, don idan kudi bai isa ba ta fitar da wani. Tana fitowa titi, sai ta tsayar da tasi tana zama ta ce ya kai ta, 'JALAN AMPANG' unguwar da ofisoshin Embassy suke. Ta shaida masa Embassy Saudi Arabia ta ke so ta je. Ba tare da bata lokaci ba suka tafi, Riggit goma sha tara ne dai-dai, ta bashi ashirin ta wuce ba tare da ta karbi canjin ba. Shigarta ke da wuya sai ta ga ma'aikata na girmamata, sun karbeta cike da fara,a saboda shigarta da ta burge su. Ta koro musu bayanin cewar Visa ta ke nema zuwa Saudiyya har tsawon wata guda saboda tana so taga likita a can. Nan danan aka yi ta dogon Turanci da cike-ciken takardu aka ce ta dawo bayan kwana biyu, bayan sun karbi Passport dinta Sai ta tsinci kanta tana mai farin ciki tun bata tabbatar za su ba ta ko ba zasu ba ta ba. Tana komawa gida ta kama harhada kayan tafiya ta zuba a akwati. Kirga awanni kawai ta ke yi don ta kagu kwana biyu ta cika taje ta karbo Visa, tikiti kawai zata yanka ta hau jirgi ta isa kasa mai tsarki. SAUDI ARABIA Haka kuwa aka yi, kafin sati ya zagayo Umaimah har ta hada komai ta isa gari mai albarka, Madina. Satinta biyu a Madina ta kaura kacokan Shabbaku, bacci ne kawai ya ke dawowa da ita dakinta na Hotel. Addu'a kawai ta ke akan dimbun bukatunta da kuma fatan cikawa da imani. Sannan ta dawo Makka a inda ta ci gaba da gudanar da ibadunta. Kwana take a harami tana dawafi, da nafilfili. Addu'a ta ke, amma fa kuka ta ke da hawaye tana fadawa mai kowa mai komai abin da yake addabarta. Takan saki nikaf dinta ta rufe fuskarta idan ta hangi *yan uwanta bakar fata, musamman idan ta ga *yan Nigeria ne Hausa/Fulani, saboda ba ta so dai-dai da rana daya ta hadu da fuskar da ta sani. A ranar da ta cika wata guda cur a ranar kuma zata koma gida Malaysia, da daddare misalin karfe tara tana cikin dawafin bankwana sai ta yi kicibus da wani abu daya firgita ta, ya ba ta mamaki, ga shi cikin rashin sa,a ba ta saka nikafinta ba. Fuskarta a bude take tarr ! A fili ga hasken lantarki tamkar da rana. Kamar yadda ta hadu da mummunan faduwar gaba mai dauke da dimbin mamaki a bayyane a fuskarta haka ta ga ya faru da su su ma. Ta tsaya cak tana kallonsu yayin da suma suka kame suna dogon kallonta. Abdul-Sabur Abdul-Rashid na hannunsa na sakale a kafadar wata mata daga dukkan alamu dai matarsa ce, wacce yake matukar so da kulawa. Sai Matar ta yi mamaki da razanar da Umaimah da Abdul-Sabur suka yi da suka ga junansu. Nan aka hau kallon-kallo tsakaninsu su dukka ukun ba tare da wani daga cikinsu ya iya furta kalma daya ba. Umaimah ce ta fara gaggauta barin wajen, ta kutsa cikin jama,a tun suna hango ta har ta bace musu. MAKWABTAKA 5 Umaimah ta sauka a kasarta Malaysia a cikin gidanta. Tabbas addu,a ba ta faduwa kasa, Allah Ya na amsa addu'ar bayinSa a duk sanda suka rokeShi. Ta riki Allah Ya yaye mata kunci da damuwa nan da ta addabi zuciyarta. Haka kuwa ta sami saukin damuwar nan da ta dankare mata a zuciya. Ita kaidai agidanta amma tana ta nishadi. Wannan muguwar faduwar gaba da mugayen tunani na tuna abubuwan da suka faru da ita a baya duk suka ragu. Haka Allah Ya amsa addu'arta Ya rage mata tunanin matattun da ta rasa a cikin danginta, ta sami tawakkali a ranta cewar sun tafi ba zasu dawo ba. Ta yi tawakkali da *yan uwanta jinin jikinta, masoyanta na hakika da ta rabu da su karfi da yaji. Ta tattara tunaninta, rayuwarta da lamuranta ga mahaliccinta. Shi kadai ne gatanta, kuma Shi ne mai taimakonta. Ta sami nutsuwa nan ta jawo takardun karatunta ta yi ta karatun abin da za su yi nan gaba tun ma kafin a koya musu. Don haka daga dukkan alamu zata fi *yan ajinsu ganewa. Karatu ne ake yinsa cikin sauki babu neman wani biro da littafi ana dogon rubutu (note), a computer (internet) za ka yi ta dubawa, kowa yana da printer sai dai ka yi ta fitarwa a cikin takardu kana karantawa. Bayan nan ta mallaki manyan littafan karatu (text books) wadanda suke bayani filla-filla game da abin da ta ke karanta, su ma suna taimaka mata wajen ganewa sosai da sosai. Da hutu ya kare sai ta ci gaba da zuwa makaranta tana daukar darasi. Kullum ba ta fashi asabar da lahadi ne kawai take zama a gida ta yini tana bacci safe da rana, da yamma kuma ta tsaya akan baranda tana kallon titi. Idan dare ya yi sai tayi karatun boko ko kur'ani, sai ta yi dan kallo ta tashi ta fara salloli (kiyamullaili), abubuwan da take gudanarwa a rayuwarta kenan a kasar nan. Har yanzu Dr. Faduwa da Engr. Abdul-Sabur ba su dawo ba, ba wai ta damu su dawo ba, amma koda yaushe suna fado mata a rai. Har ma ta fi kaunar kada su dawo balle su fara shiga rayuwarta. Ba ta ki ace da suka tafin nan ba sun tafi ke nan har abada, zai fiye mata sauki don ba ta son a dinga gaisawa kamar yadda suka bukaci haka daga gare ta. Tasan sun fi ta gaskiya, kuma ba ta kyauta musu ba. Maimakon ta yi ta rashin kyautawar ai gara ace ba sa nan, ba ta gansu ba, basa ganta ba. Don ba zata iya yi musu abin da suke bukata daga gare ta ba wannan alkawari ne ta yiwa zuciyarta babu ita babu wani MAKWABCINTA har abada. **************************************** A yammacin ranar lahadi misalin karfe biyar na yamma, Umaimah na zaune a babban wajen shakatawa na sun way Lagoom tana bangaren da aka killace namun daji (zoo). Tana zaune a gefen wani dutse wanda ke bulbulowa da ruwa, tana hango namun daji da dandazon Turawan da suke ta layin kallo da daukar hotuna. Iska mai sanyi ce ta ke ta kadawa har cikin kanta ta ke jiyo sanyin iskar duk da dan karamin hijabin da ta saka. Riga da siket ne a jikinta *yan kanti masu launin fari da baki, sannan ta saka takalmi fari mai tsananin tsini da jakarsa fara. Turawa biyu ne mace da namiji daban-daban sukazo suka roke ta ta yarda su dauki hoto da ita saboda ta yi kyau sosai. Sai ta tsinci kanta tana duban jama,a tana murmushi ita ma kamar yadda suke yi mata murmushi da zarar sun hada ido da ita. ''Assalamu alaikum''. Kalmar da ta jito kenan cikin kamilalliyar murya a saitin kunnenta na dama. Nan da nan ta wurga ido ta dubi inda muryar ta fito. Kafin ta gama waiwayowa kamshin turarensa ya daki hudojin hancinta, ko ba a fada mata ba tasan kanshin wannan disigner ne (Dolce Gabbana) ya fesa. Ta daga ido da sauri ta dubi kyakykyawar surar jikinsa, har zuwa zukekiyar fuskarsa. Yayin da idanuwanta suka tsaya cak tana kallon wasu fararen hakoransa yana yi mata dariya. Ta yi matukar mamaki da ganinsa a wannan waje kuma a dai dai wannan lokaci. Ba ta amsa masa ba, sai ta dukar da kanta kasa. Abdul-Sabur ya sake matsowa gare ta cikin harshen Nassara ya ce, ''Kin yi min izinin na zauna tare da ke? Ta girgiza kai alamar a'a Sai ya yi murmushin karfin hali ya ce, ''Ni ne Abdul-Sabur makwabcinki, yau satina guda da dawowa. Wannan kalmar ta makwabci ita ta sake saka mata tsanar ya kasance a kusa da ita, don haka tun bai rufe bakinsa ba, ta yi cimak ta mike tsaye da sauri ko waiwayowa shi ba ta yi ba, ta nufi get din fita. Kira ya ke, ''Maye! Maye!! Ta ki waiwayowa a inda kalmar 'maye ta sake hassalata. Ba ta yi wata-wata ba ta tsayar da tasi ta shige ta tafi gida. Ta nemi nishadin zuciyarta ta rasa, sai takaici da ya taru ya yi mata dankar. Ta yi da na sanin zama a gidan nan saboda takurawar da Abdul-Sabur yake yi mata. Tabbas dole ta tashi daga gidannan da zarar kudin hayarta na shekara ya kare gara ta nemi inda babu bakar fata ko daya balle ya yi tunanin yi mata magana. Tana fitowa daga tasi ta ci karo da Dr. Faduwa ita da kawayenta sun fito daga cikin get daga dukkan alamu rako su tayi za su shiga tasi su tafi gida. Don haka ta yi saurin tsayar da ya kawo Umaimah, ta yi ta kallon Umaimah tana so su hada ido ta yi mata magana, yayin da Umaima ta ki kallon inda suke balle su gaisa. Ta zaro kudin mota ta biya ta saba jakarta, ta kawar da kanta gefe ta kara gaba. Dr. Faduwa ta bi ta da kallo kawai tana girgiza kai da alama tana mamakin hali irin na Umainah. **************************************** Jiki da jini, dare daya Allah Ya ke sauke ciwo sauki kuwa sai ahankali. Kwana daya da yini guda cur ta yi tana ciwon ciki mai tsanani, tun tana kan gado tana murkususu har ciwo ya tsananta ta fado kasa. Juyi kawai ta ke a tsakar daki babu abin da ta ke ambato sai, ''Wayyo Allah, wayyo Allah cikina, Allah Ka taimake ni. Idan ciwon ya dan lafa kadan sai ta rufe ido ta fara dan bacci, can sai ciwo ya dawo ya turniketa, ta sake kwalla kiran sunan Allah, tana neman agajinSa. Allahu Akbar, Shi kadai ne mai yaye ciwo a duk sanda Ya so. Addu'a ta ke, kuka ta ke, murkususu ta ke yi ita kadai, amma ciwon bai dauke ba ga shi ta kasa tashi zaune ma balle ta tashi tsaye tayi tafiya. Tun cikin dare Abdul-Sabur yake ta kasa kunne yana sake saurarawa shi dai kamar daga dakin yarinyar nan yana jin ihu ana kiran Allah-Allah. Don haka a zaune ya kwana, idan aka jima sai ya tashi ya bude wundo ya yi ta leken gidanta bai ga kowa ba, kuma bai daina jiyo karar ba. Ya bude baramda ya fito ya tsaya yana ta sauraro, tabbas ihun mace ne, kuma daga saitin dakin yake fitowa. Tabbas yau ba lafiya akwai matsala! To amma ya za'a yi ya sani? Ta ina zai iya taimakonta? Abin da ya kwana ya yini ke nan yana zulumi. Ya saukko ya hau benensu kofar gidanta ya tsaya. Ya tabbatar ta ciki aka datse. Ihun take yi kuma sosai yana jiyo ta, sai yai kamar zai buga mata kofa sai ya tuno sakon jan kunnen da ta bayar a bashi, don haka sai ya fasa. Ya juya zai koma gida sai ya ji ba zai iyaba, ya sauko gidan Dr. Faduwa da yake kasan na Umaimah a hawa na goma sha takwas ta ke. Ya ci sa,a ma kofarta a bude don ita mace ce mai jama,a ta yi baki, wasu mata ne guda biyu *yan Indiya suna ta hira. A yadda ta gan shi ta san ba ta jin dadi, saboda ba ya walwala, sai ta shiga tambayarsa ko lafiya? Ya yi murmushin karfin hali ya gaishe ta da kawayenta, sai ya roki Dr. Faduwa ta fito waje suyi magana. Ta biyo shi a gigice, yayin da zuciyarta ta ke ta kadawa don fargabar abin da zai fada mata. Cikin zumudi ta ke tambayarsa, ''Lafiya?'' Ya girgiza kai, magana ya ke cikin marairaciyar murya. Ya ce, ''Faduwa, ki yi hakuri, ki taimaka min ki taimakawa addininki, ki yi don bin sunnar Manzon Allah (S.A.W) ki yi don hakkin MAKWABTAKA'' Sai ta dafe kiriji ta fara hawaye nan da nan ta rikice daman rikirkitacciyar ce, ma,ana tana da saurin gigicewa. Nan da nan Larabci ya hautsine bakinta ta manta ma Abdul-Sabur ba ya jin larabci. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Abdul-Sabur ishfi? Ya girgiza kai ya fada cikin harshen Turanci, ''Ki yi mini turanci don na fahimce ki. Ki kwantar da hankalinki, ba wani abu bane illa matsala ce ta faru ga makociyarmu. Waccan yarinyar ta hawa goma sha tara. Ina ga kwana ta yi a kwance ba ta da lafiya, ina jin ta kasa ta shi ta bude kofa. Ina tsoron ka da ta mutu a cikin gida ita kadai don ba ta da lafiya sosai. Dr. Faduwa ta murtike fuska, tare da aika masa harara, ta tabe baki yayin da ta yi saurin goge hawayen da ya cika mata ido. Ta murje idanuwan radau ta dube shi. Ta ce, ''Tunda nake a rayuwata ban taba ganin mutum mai laushi da rashin zuciya irinka ba. Haka tunda nake ban taba ganin mutum mai taurin da bakar zuciya ba irin na wancan yarinyar, fitsararriya ce marar kunya, wacce ba ta son mutane, mai bakar aniya. Ko a cikin satin nan na hadu da ita a bakin get ta harare ni da *yan uwana ta wuce. To ni kuwa me zan yi da ita? Shawara ta karshe da

Chapter 2 of 33