Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tsananin son juna. Sai na ji garin ya fita a raina ma gaba daya, gara na koma Kaduna. Na shirya na tafi ba tare da hutu ya kare ba... Abdul-Sabur ya yi shuru yana kallonta, can ya ce, ''Amma me ta ce masa? Anya kuwa ba hadaku ta yi ba? Umaimah ta ce, ''Hadamu ta yi mana, ba abin da na fada mata ta je ta fada masa ba. Ashe ce masa ta yi na ce ya fita harka ta, ni yanzu ba ajinsa ba ce, sai dan boko. Wai na ce me zanyi da almajiri, gardi mai bara? Faduwa ta ce, ''Subhanallahi. Ita kuwa a wanne dalili ta yi miki haka? Kafin Umaimah ta yi magana, Abdul-Sabur ya ce, ''Hassada don ita ba ta da saurayi? Umaimah ta runtse ido ta zubo da hawaye mai zafi ta ce, ''Ashe ita ma sonsa ta ke. Yadda ta ke zuga ni haka a can bangaren ta ke ta binsa tana min kazafi kala-kala, har da cewa, an zubar min da ciki a birni. Har sai da ya ji babu abin da zai yi da ni sannan ta yi kokarin cusa kanta wajensa, ba shi da zabi don babu yadda zai yi, amma zancen so ni ce kadai macen da yake so a duniya. In ba rashin wayewa ba me yasa ba zai kira ni ya zaunar da ni ya tambaye ni ba, ko ya aiko mahaifansa su bincika? Ni kuma da yarinta sai nayi ta boyewa Yafindona ko ta tambaye ni idan taga ina damuwa sai in ki fada. Shekara ba ta dawo ba aka zo min da labarin anyi auren Matawata da Ilahna. Suma ne kawai ban yi ba, amma na gigice, sai da Nasiba ta rike ni dan da faduwa zan yi. Kuka muke ta yi ni da Nasiba tun Yaya Abdul-Basi yana ba mu hakuri, har ya ji haushi ya kwakkwayemu, ya ce, ni da nake karatu ina ni ina maganar saurayi a kauye, almajiri dan Ruga? Ina ma auren zai yiwu? Ni da zuciyata ne kadai muka san halin da muke ciki, wannan bakauyen almajirin ya fi min samarin Birni sai dubu, don shine farin cikina. Duk tsananin bacin ran da nake ciki idan na ga Ilah sai na ji sanyi, don zai lallashe ni ya ba ni labaru masu dadi. Wannan shi ne cin amana da musgunawar da MAKWABTANA suka fara yi min a rayuwa.... Umaimah ta sa gefen hannunta ta sharce hawaye mai radadi. ''Yi shiru daina kuka. Inji Abdul-Sabur da Faduwa, Su ma tausayinta ya rufe su. Ta ce, ''Ban koma garinmu ba, har sai da na shiga aji hudu na sakandire shi ma ba zuwan dadi ba ne, kawai Yaya Abdul-Basi ya ce mu zo gida ana nemanmu, ashe Yafindonmu ce ta rasu. ''Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Inji Faduwa da AbdulSabur, yayin da kuka ya barkewa Umaimah. Ta dade tana yi kafin su lallashe ta, ta ci gaba da labarin. Ta girgiza kai ta ce. ''Da aka yi sadakan bakwai dole muka shirya zamu koma Kaduna, saboda watan haihuwar Nasiba ne, ta samu ciki da kyar ya zauna mata. Ilah ya zo ya yi min gaisuwa a tsaitsaye, amma Matawata ga ni ga-ta, a jikin zanar gidan su Ilah ta ki yi min magana. Ciki ne ma da ita a lokacin, har wata rangwada ta ke yi tana shafa cikin. Wai har na zama abar zolaya a wajen Matawata duk amincin da ke tsakanina da ita. Zuciyata sai ta yi ta tafasa idan na jiyo masoyina Ilah da aminiyata Matawata suna hira a gidansu. Tunda a gidan iyayensa aka ba su daki, mu kuma katangar gidan mu daya don haka ana jiyo hirarrakin da ake yi a tsakanin gidajen biyu. Muka koma Kaduna muka yi jugum-jugum cikin damuwa, mu dukkanmu. Bayan sati uku dai-dai da rasuwar Yafindo sai haihuwa ta tasowa Nasiba aka kaita asibiti. Allahu Akbar haihuwar ta zo da matsala, likitoci suka yi iya kokarinsu wajen ceto uwar da *yar abu ya ci tura.. Sai kuka ya hana Umaimah ta ci gaba da magana. Faduwa ta zabura ta ce, 'Ba dai ta rasu ba? Umaimah ta gyada kai cikin kuka mai tsanani. Ta ce, ''Yayata Nasiba ta rasu ita da *yar cikin dukka. Sai Faduwa ta rungume ta ita ma kukan ta ke taya ta don tausayi. Abdul-Sabur ya yi ta girgiza kai kalmar ''Sorry-sorry. Kadai ya ke ambato. Umaimah ta matse hawaye ta gyara zama ta ci gaba da cewa, ''Na yi kuka, har yau ina kan yin kuka amma ba zasu dawo ba, sun tafi, sun tafi kenan. Na damu matuka, amma sai Yaya Abdul-Basi ya fi ni damuwa, har na fi shi tawakkali, shi har sai da aka yi ta rike shi don ya rike makara ya ki ya saki, da za a saka ta a kushewarta. Ta sha addu'a kuwa a wajensa, ya ce, ''Nasiba, ke ce matar da na taba so, nake so, kuma zan dauwama ina so a duniya. Ki sani GANGAR JIKINMU ce kawai zata rabu, amma ruhin mu yana tare..'' Hawaye ya yi ta kwaranyowa daga idanuwan su dukka ukun. Har zuwa lokaci mai tsawo kowannensu yana matsar hawaye, sannan Umaimah ta ci gaba da magana. ''Aka kai Babangida Gombe wajen kakarsa wato Hajiyan Abdul-Basi, ni kuma da kayana kacokan aka dawo da ni Dugge, sai kunci ya karu. Na dawo gidanmu dakin Yafindo bata duniya, sannan babu kawata abokiyar hirata Matawata, babu masoyina mai saka ni farin ciki, wato, Ilah. Allah Ya sa Sabitu ya zo a lokacin, da shi kadai nake hira na dan ji dadi, don shi kadai ya rage min a duniya, daga shi sai Baffana. Baffa kuwa ya tsufa, ciwociwo kala-kala. Kishiyoyin Yafindo Inna da Nene suka saka ni a gaba suna ta yi min habaici wai karya ta kare dan birni ya dawo kauye. Kullum sai su yi ta zafuta ta da dungure kai, dole sai na fito daga daki na taya su surfe da girki. Na ga tashin hankali don na manta yadda ake surfe da cin gabza. Yaya na iya, dole na yi ta cusawa cikina duk abin da na samu, don kada yunwa ta kashe ni. Matawata ta haihu, yawanci ma a gidanmu aka yi girkegirke da taron *yan suna, sai na yi mamaki da na ji sunan jaririyar, wai MARIYA, sunan Yafindona ne don dai nasan danginsa kakaf da nata babu Mariya. Ba su gayyace ni ba suna haka tashin hankali ya hana ni fitowa daga daki, sai kuka nake yi yadda ku ka san na tsaga kasa na shige ta rufe ni na huta don tashin hankali. Hakika na ji haushin cin amanar da aka yi min, na shiga zargin ni ce ban sani ba watakila tuntuni ma suna son junansu. Kamshin suyar naman rago da dan Akuya har cikin dakina, amma ko hanji ba a san min ba, raina ya yi ta biyawa. Babban tashin hankalina ma shi ne gulmata da aka dasa kungiya-kungiya ana ta yi, wai na ki auren bakauye na koma birni, ga shi na rasa dan birni na dawo kauyen, Ilah ya yi aurensa yanzu bakin ciki zai kashe ni na ma kasa fitowa cikin jama'a. Su Nene ne masu kara zuga magulmatan, koma dai mene ne na fauwalawa Allah komai, Shi ne mai sakayya. Ba'a yi watanni shida ba kuwa Allah Mai komai da kowa sai da Ya yi min sakayya a bisa abubuwan da duk aka yi min... Faduwa ta dafa kirji tare da yin ajiyar zuciya, ta ce, ''Me ya faru da su? Umaimah ta yi nata takaitaccen murmushin, ta ce, ''Uhum, Allah ba azzalumin bawanSa ba ne. Ashe tunda Ilah ya auri Matawata ba ya jin dadin zama da ita, bayan rashin son da yake yi mata ta cika makirci da hada husuma. Ta hada shi da *yan uwansa saboda fada da take yi da matansu, ta raba shi da abokansa ta dawo tana hada iyayensa fada. Kullum ba ta shiri da surukarta rashin kunya ta ke yi mata sosai, shi kuma Baffansa yana bin bayan Matawata don haka sai a yi ta rigima, Ilah mai hakuri ne yana zaune ba ya magana duk abin da zata yi ba ya iya tsawatar mata. Mahaifiyarsa har kuka ta ke tana cewa, ta yi asarar haihuwa, idan har danta zai auro macen da zata yi mata rashin kunya a gabansa ya kasa magana. Allah kada Ka tsayar da ni ranar shaida, an ce bokaye ta ke bi ta shanye shi, ba ya ganin laifinta sam! Amma Allah Ya fi ta, sai kuwa aka kama ta da laifin kwartanci ita da tsohon saurayinta lawwali. Gari gaba daya sun shaida, har aka rakota gida da waka ana ga kwartuwa. A take Ilah ya yi mata saki uku, ina daga dakina nake jiyo komai. Ban fito ba ma balle ace tsegumi sai na ji a raina ban ji dadin wannan bakin al'amarin ba. Domin dukkan musulmi dan uwan musulmi ne, Allah Ya rufa mana asiri, Ya sa mu gama da duniya lafiya, Ya sa mu fi karfin zuciyarmu. Abdul-Sabur da Faduwa suka amsa da ''Amin''. Umaimah ta kurbi ruwan sanyi ta dago da ido ta dube su, ta yi murmushi don ta ga sun kammala hankalinsu kacokam a kanta, ita suke kallo. Ta ci gaba da cewa, ''Ai ba'a yi wata ba sai na ji an ce ga Ilah can da Baffana a wajen Baffana suna maganata a aure, Ilah har yana kuka yana bada hakuri. Na ji zuciyata ta fusata na kudiri niyyar duk wanda ya kira ni akan maganar sai na fadi ba dadi, kuma ba zan yarda ba, don a lokacin ko ganinsa bana son yi. Ina cikin tunani ne na ji Baffana ya kwallamin kira, na saka hijabina na fito na same su a zaure. Na durkushe a gefe na gaishe su, sai Baffana ya fara bayanin. Ya ce, ''Ga Ilah ya dawo daman makircin Matawata ne ya raba ku. Na girgiza kai na ce, ''Baffa ka yi min afuwa ka bar maganar nan, don maganar nan ba mai yiwuwa ba ce. Na hakura da Ilah tuntuni, ya je ya auri wata. Wato sai da ya rasa Matawata zai tuno da ni? Ai ba a 6ari a kwashe dukka. Nan fa Baffana, Ilah da Baffansa suka hau dogon fillanci, ni wata kalmar hakurin ma sai a ranar na taba jinta a fullanci. Suka yi ta magiya Ilah yana sake fada min duk abubuwan da ya faru tun farko. Wai ashe sanda na aike ta wajensa sakon da ta fada masa daban ne ba wanda na fada mata ba ne, cewa ta yi na ce na fi karfinsa yanzu, ya cire ma maganar aure a tsakaninmu. Sai ya ce tace min ya gode tunda wulakancin da zan yi masa kenan. Sai ni kuma ta dawo ta ce min, ya ce, me zai yi da ni na je birni na zama *yar iska ragowar maza? Sai a lokacin ya fadi duk abubuwan da ta fada masa a kaina, ni ma na fada muka gane Matawata ce munafuka, sai zuciyata ta yi sanyi na amince zan aure shi. Muka watse daga zauren kowannenmu cike da farin ciki. Dare, Safe, da yamma Ilah yana wajena, koda yaushe sai ya zo zance, hade da hidimomin da ya saba yi min tuntuni. Kamar: atamfa ce, mangoro, rake, kaji da dai sauransu. Ita ma Matawata tana jiyo hirarmu da shewarmu daga zaurensu, don gidanmu ne a tsakiyar nasu. Bakin ciki ya rufe ta, ta rasa inda zata saka kanta. Rannan har da fitowa tana zage-zage tamkar mahaukaciya, yara kuwa suka hau yi mata wakar kwartuwa. Idan aka yi sata ko kwartanci a kauye ka shiga uku, gara ma ka bar garin zai fiye maka sauki. Muna ta shirye-shiryen aurenmu Ilah ya siyo siminti ya ce zai sumulce bangon dakina sannan ya yi dabe a kasa, saboda na saba da gidajen birni. Muka shiryawa kanmu rayuwar jin dadi ta aure, irin tamu ta talakawa dai, har yake cewa yana so ya koma Kaltingo da zama wani Alhaji da ya zauna a gidansa ya ce zai bude shago ya dinga jire masa. Muna tunanin nan da wata uku a yi aurenmu. Allah Mai yadda Ya so da bawanSa, ashe dai Ilah ba mijina ba ne har abada. Faduwa da Abdul-Sabur suka zabura suka ce, ''Shi ma ya rasu? Umaimah ta matse hawaye ta ce, ''Ilah bai rasu ba, har yanzu yana nan a raye, koda yake yanzu ban san halin da suke ciki ba. ''To me ya faru? Abdul-Sabur ya tambaya cike da zumudi. Ta yi shuru kanta a sunkuye a kasa, da alama dai tana jin ciwon tuna abubuwan da suka faru da ita ne a baya. Faduwa ta shafa kafadarta tana jijjigawa, kamar me lallashin jariri. Kalmar, ''Ma'alesh, ma'alesh''. Ta ke ta ambatowa, ma'ana 'yi hakuri'. Umaimah ta dago da jajayan idanuwanta ta dube su, ta ce, ''Kun san me ya faru? Baban Abdul-Basi ne ya dawo wajen Dagacin garinmu aka kira Baffana aka yi shawara, wai na maye gurbin Yayata marigayiya. Ma'ana na auri Yaya Abdul-Basi, babu wanda bai amince ba a cikinsu. Kwatsam ni da Ilah muna zaune wannan bakin labarin ya zo mana muka gigice nan da nan sai kuka ya barke mana. Mun yi tunanin guduwa ma dai muka fasa, Ilah ya yi min nasiha ya ba ni hakuri, na yi iya kokarina a fasa auren nan aka fi karfina. Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Ba kya ganin auren Abdul-Basi ya fi miki Ilah, tunda Abdul-Basin kin san shi, kin san halinsa, yana da kirki? Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ba maganar kirki muke ba kadai, maganar so da shakuwa shi ne aure. Faduwa ta ce, ''Haka so yake ba ruwansa da kudi ko birni''. Umaimah ta ce, ''Son da nake yi wa Yaya Abdul-Basi na *yan uwantaka ne ba na aure ba, Ilah kuwa shi ne farin cikina, shi ne abinda nake tunawa na ji dadi a zuciyata. Daga dukkan alamu Yaya Abdul-Basi ma ba ya son hadin nan, an fi karfinsa ne, babu yadda zai yi. Amma shi ma ya kasa cire Nasiba a ransa. Aka tarka ta mu aka yi auren aka dawo da ni gidan nan dai na Nasiba, ba a dawo da Babangida ba wajena, saboda Abdul-Basi ya mayar da ni makarantar boko, aji biyar. Yana kai ni da safe na dawo a motar haya idan an ta shi, sai dare yake dawowa. Bai taba kusanta ta ba, wata da watanni ina dakina yana dakinsa. Ina tunanin Ilahna yana tunanin Nasibarsa. Ya fada min baro-baro cewar shi fa Nasiba yake so har yanzu, da zata dawo su zauna da ya fi masa. Ni ma na fada masa da zai sake ni na koma wajen Ilahna na zauna da ya fi min zama a gidansa. Bai damu ba nima ban damu ba da maganar da muka fadawa juna saboda kowa gaskiyar abin da yake ransa ya fada ke nan. Ba ya damuwa da girkina, balle kwalliyata, haka ni ma ba na damuwa da na yi masa komai. 'Zo na kai ki makaranta, ungo kudin makaranta, karbi kudin cefane. Shikenan maganar da ta ke hadamu. Hakan ya fiye min dadi a rai ni kuwa. Daga baya ya fara warewa yake yawan shiga harka ta, yawan jana da hira da kai ni unguwanni wuraren shakatawa. Ya mayar da ni islamiyya, ranar asabar da lahadi yake kai ni ya dauko ni, ya dawo da yi min home work da dai sauran kulawa. Ni ce nake ta baudewa don ban fitar da ran komawa wajen masoyina ba Ilah. Da ya dau hutu ya kai ni gidansu Gombe, muka ga Babangida, ya girma yana zuwa makaranta. Daga nan na roke shi ya karasa da ni Dugge, kai tsaye ya ce 'a'a idan dai su Baffa ne zai je ya gano su ba sai na je ba' wai shi nan da tsiya kishi yake, ya san Ilah nake so na je na gani. Na yi ta kuka da ihu har sai da surukata ta ce, ya tashi ya kai ni garinmu na kwana biyu sannan ya koma ya dawo da ni. Ya dinga harbamin harara da ya ga ina murna a mota saboda tsananin kishi. Ai kuwa mun kai musu goma ta arziki, kayan abinci, ya diddika da atamfofi, gidanmu da gidan Dagaci. Da aka gama gaggaisawa sai Abdul-Basi ya tafi ya barni. Kudi mai yawa na kunso na kawowa tsohona a dunkule a boye na ba shi, ya yi ta mamaki yana tambaya ta ina na samo kudin nan? Na shaida masa kudin makaranta ne da ragowar kudin cefane nake tarawa. Ya yi godiya ya shi min albarka ya yiwa mahaifiyata da yayata addu'a Allah Ya sada su da rahama. Na gyara zama na tambaye shi Ilah, sai na ga ya girgiza kai ya tabe baki, ya ce, 'Ilah sai addu'a Allah Ya hadashi da jarababbiyar mata!. Ina jin haka gabana ya yanke ya fadi, na ce, 'Lafiya? Baffana ya yi shiru can ya dago ya dube ni, ya ga yadda na dimauce. Ya ce, 'Ki rike mijinki, ki rabu da Ilah ba mijin da zaki yi tunanin za ki aura ba ne. Sai na sulale kamar zan kwanta na sume don fargaba. Baffa ya ce, ''Yarinyar nan Matawata auren kisan wuta ta yi na sati uku ta fito ta yi idda ta dawo wajen Ilah, yanzu haka suna tare tana gidan na ji ance ma wani cikin ne da ita. Don haka ki je ki kama mijinki ki manta da Ilah a rayuwarki. Na matse hawaye na ce, ''Idan Allah Ya so Baffa na hakura da Ilah a rayuwata. Na koma daki a sanyaye sai na ji dama Yaya Abdul-Basi bai tafi ba na bishi mu koma, don bana son garin ko kadan. Matawata ta ji labari na zo, washegari da sassafe ta shigo gidan ta same ni har kofar dakina ta zazzage min habaici iri-iri. Wai Ilah nata ne duk naci da sihirce-sihircena dole na hakura na bar mata shi. Ban rama ba ta yi ta gaji ta tafi. Wasika doguwa da ajami Ilah ya aiko ,in da daddare yana mai ba ni hakuri da yi min fatan alkhairi, ya kuma roke ni da na taya shi da addu'a, rayuwarsa tana cikin kunci don bai yi sa'ar abokiyar zama ta gari ba. Ban gama karantawa ba ma na yayyaga na zubar a shara. Ban yarda na hadu da shi ba har na yi mako a garin, sannan Yaya Abdul-Basi ya zo ya dauke ni muka tafi. Tun a hanya ya ga alamu ina cikin damuwa, da ya dame ni da tambaya sai na rushe da kuka. Na shaida masa Ilah ya sake mayar da Matawata a dakinsa. Wani dogon tsaki na ji ya ja, sannan ya watso min wata hargitsattsiyar harara. Ya ce, 'Idan bai mayar da ita ba ke zai saka a dakin? Wallahi Umaimah ki rufawa kanki asiri, ki sani fa kina kona kanki ne, da auren wani a kanki amma kike tunanin wani katon banza, har kina kishi akan ya maida tsohuwar matarsa. To ina ruwanki? Ya shiga yi min nasihohi masu ratsa jiki ya ce, gara ni da shi dukka mu yi wa kanmu fada mu manta da Nasiba da Ilah mu fuskanci sabuwar rayuwa, Allah ne kadai Ya san dalilin da Ya raba mu da wadanda muka fi so, Ya hada junanmu. MAKWABTAKA 19 Tun lokacin na yiwa kaina fada, na nutsu na fara kokarin cusawa raina zama da AbdulBasi a matsayin miji na, shi ma haka. Sai bayan ma da na gama sakandire sannan muka budewa kanmu sabuwar rayuwar jin dadi da son juna. Abdul-Basi ya dawo yana sona tamkar Nasiba, don na juye ta sak! Da na yi kiba, ni ma na cire Ilah a raina, na daukeshi a matsayin munafiki na barshi da Matawata can su karata da bakin munafincinsu... Abdul-Sabur ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Ya aka yi kika zo nan kasar kika baro masoyinki Abdul-Basi a can? Sai ta yi murmushi karfin hali, ta ce, ''Kai ma tun da ka ganni a nan kasar alhali ina da aure a can kasan sai dai idan da wata matsala ne. Kuma ai da sauran kuka wai anci gumba an hana maye, me aka yi a hawa bishiyar bare a tsinko reshenta? Sai Abdul-Sabur da Faduwa suka hada idanu. Sannan Faduwa ta dafe kirji, ta ce, ''Me ya hada ku? Umaimah ta tabe baki ta ce, ''MAKWABTANA ne suka hada mu, MAKWABTAKA! ''Kamar yaya? AbdulSabur ya tambaya cike da fargaba. Umaimah ta yi shuru kanta a sunkuye a kasa, kamar me tunani. Can ta dago ta dube su, idanuwanta a cike da kwallah. Ta ce, 'Na kasance mai saurin yarda da amincewa mutane, na saba da Makwabtana da *ya*yansu tun lokacin marigayiya don haka nake jinsu tamkar dangina. Kamar yadda na fada a baya gidaje takwas ne a farfajiyar, sama da kasa guda hudu. Mu muna sama kasanmu kuma wata mata ce mai suna Hajiya Ladidi, *yan garin Minna ne aiki ya kawo mijinta Kaduna, suna yaren Nufe da *ya*yanta hudu ta girme ni harta kusan haifata ma. Sai gidaje biyu da suke fuskantar namu wata beyarabiya ce amma musulmace mai suna Zulaiha Senegal. Tana zuwa Senegal tana dinko kayan mata da maza shaddoji da yadiddika tana siyarwa *yan siyasa da matan masu kudi. Tana ji da gayu da rawar kai tana abu kamar wata budurwa alhali ta ajiye karatan *ya*ya guda uku. Samari maza guda biyu har daya ya gama sakandire ya shiga jami'a, daya ya na daf da gama sakandire, sai mace ita ce a sakandire aji uku. Ta rabu da baban yaran tun suna kanana ta zo ta kama haya ta ke kasuwanci, ta ke kula da *ya*yanta. Ba laifi matar tana da kirki da yawan fara'a da jan mutane a jikinta, bakinta rairai-rai saboda iya magana, don haka gidanta kullum a cike da mutane yake, mata da maza, kawayenta da kawayen *ya*yanta, *yan uwanta da *yan uwan tsohon mijinta zuwa suke yi tana maraba da kowa. Ta ja ni a jiki sosai muka saba tun lokacin Nasiba, shakuwarmu ta fi yawa a lokacin da na dawo ni kadai, ba ni da abokiyar shawara sai ita. Gidaje hudun kuwa da suke gefenmu, gidan wasu kabilu ne ba musulmai ba ne, wa da kani, daya sama daya a kasa da matansu, ko na ce dadironsu, wadannan ba ma harka da su. Sai dayan ginin Hajiya Bishra a kasa, mijinta ya mutu ya bar ta da yara, amma fa duk ta aurar da *ya*yanta. *Yan mata biyu ne suka rage mata sa'annina ne, Nana da Wahida, suna neman gurbin karatu a Kaduna Polytechnic. Sai saman su wata amarya ce ba su dade da tarewa ba, mai suna Bara'atu ta riga ni aure har ta haifi *yan biyu. Ita ma kawance muke yi na hakika kamar yadda mai gidanta Kamal da maigidana suke yi saboda su dukka banki daya suke aiki. Duk wani sirrina, na gidanmu can Dugge dama tsakani na da mijjina da kawata Bara'atu nake tattaunawa saboda na yarda da ita. Mijina sai ya yi ta jiyo maganarsa ya rasa daga inda magana ta ke fitowa. Ban tashi ganewa ba har sai da abu ya kwabe, a lokacin da bazan iya gyarawa ba... Kamar yaya? Abdul-Sabur ya tambaye ta cike da rashin fahimta. Cikin jimami Umaimah ta ce, ''Matsalata da Bara'atu ke nan, sai ni da Zulaiha Senegal. Auntyna nake kiranta koda yaushe sai na dauki kayan abinci kamar idan zanyi wainar shinkafa ko alala, to ban iya sosai ba, ita take koya min. Ko ta shigo da kanta har gidana ta koya min, ta koya min yadda zanyi magana da miji, da yadda ake tafiya da kissa gami da kisisina. Na dauke ta tamkar *yar uwata Nasiba, saboda yadda ta ke nuna min, sai na zaci tana sona. Abdul-Basi ya fara min fada akan na dinga ja da baya da Makwabtana, dan ya ga na bawa Makwabta gaskiya fiye da shi mijina. Ni kuwa a wajena dole ne na shiga makwabta saboda zaman gidan ya yi min yawa ni kadai, ga yawan dauke wuta haka ga mijina baya dawowa sai karfe takwas ko tara na dare tun karfe bakwai na safe. Idan ma na zauna ni kadai tunani ne ya ke addabata na yi ta kuka. Da jimamin rashin mahaifiyata ko *yar uwata zan ji ko kuma da takaicin cin amanar da Matawata ta yi min ta raba ni da wanda nake so? Makwabta nake shiga in sha hira, suma su shigo min, amma a ce a raba wannan karfaffan zumunci ba zai yiwu ba. Don haka ban ji maganar Abdul-Basi ba, na ci gaba da huldata da su. Muna nan a haka na samu ciki, na haifi dana santalele, mai kama da mahaifinsa, aka saka masa suna Bilal. Abdul-Sabur da Faduwa suka bude baki don tsananin mamaki. Tambayarta suke yi, ''Au ashe kin taba haihuwa? Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Ina da dana yana can a gidansu. Abdul-Sabur ya ce ''Ke kuwa me ya raba ki da mijinki da danki kika taho kika bar su? Umaimah ta ce ''Kaddara ce wacce ta riga fata, kaddara ta sanadin amincewa MAKWABTAKA da na yo. Kafin na yaye Bilal sai na sami wani cikin, ni dai tun daga wannan lokacin na rasa kan mijina, sai na ga kamar ya daina sona, ya tsane ni. Ya daina shiga harkata, kullum sai ya dawo gida a koshe ya ce ya ci abinci a waje. Ashe ni ce ban sani ba Zulayha Senegal ta kwace min mijina, tun baya biye ta har ya fara. Ashe tunda magruba ya ke dawowa sai ya shige gidanta a can zai ci abinci, ya yi kallo, ni kuwa ina cikin duhu idan babu wuta ina jiransa ya dawo ya tayar min da janareto don ba zan iya tayar da shi ba, ya yi min tauri. Ban san wainar da ake toyawa ba MAKWABTA duk sun sani babu wacce ta fada min, sai dai suna gefe suna tausayamin, idan suka ganni a gidanta, ko suka ganta a gidana. Ni ma dai na ga a lokacin ta fiye bugun cikina ta ji irin zaman da nake yi da mijina, ban boye mata ba na fada mata irin canjin da na ga ni daga wajensa, sai ta yi murmushin mugunta. Ta-kai-ta-kawo sai in zo in ganta a kicin dina tana min barbaden magani a cikin kwanukan abincina. Rannan kuma na kama ta ta budamin gas cooker wajen da ake ajiye silinda ta jefa min wani abu, ashe laya ce. Matattakalata duk ruwan rubutu ne idan na fito nake gani, sai na yi ta mamaki, amma kuma ko kusa zuciyata ba ta taba yi miin zargin tana bi na da sharri ba. Kuma ban daina kula ta ba. Wata ranar asabar da safe cikina ya tsufa ina son na je na nemo mai aiki a unguwar Dosa, wata Hajiya Balaraba babar kawata ce ta ke samowa, ta yi min waya ta ce an kawo masu aiki da yawa na zo na dauka. Kasancewar watan haihuwata ne gani da karamin da bai fi shekara daya da rabi ba, ba ya tafiya ma a lokacin sosai, ga shi daf da watan azumi za,a fara aiki zai yi min yawa dole na sami mataimakiya. Na dade da fada masa zan nemi mai aiki, ya kuma yarda, sai na sanar masa a safiyar ya zo ya kai ni na dauko mai aikin. Ya daka min tsawa ya ce, ba zai kai ni ba. Na shiga yi masa bayani cikin ladabi duk da haka ya ce, ba zai je ba sai dai ni na je. Na ce ya ba ni kudin tasi drop na je na dawo, ya ce ba zai bayar ba. Na duba jakata na ga kudin dari biyu ne kawai, ba zasu ishe ni daukar tasi zuwa da dawowa ba. Sai na kuduri niyyar hawan acaba na yi sauri na je na dawo, in yaso Haj. Balaraba sai ta ba ni na dawowar. Na ce to ya rike min dana na je yanzu na dawo. Abin mamaki sai ya daka min tsawa. Ya ce, ''dauki danki ki tafi da shi, ba zan rike ba nima ina da wajen zuwa. Kuma ki tafi da makullanki don bazan jire miki gida ba. Na

Chapter 11 of 33