Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tare da su. Ledojin Nasiba sun fi na kowa yawa, da muka shiga gida ta zazzage sai kowa ya shiga mamaki, har da mahaifina, da yake yana gida bai bi tawagar Dagaci ba. ''Waye ya ba ki duk wadannan kayan? Baffa ne ya tambayi Nasiba. Ta ce, ''Wasu daga cikin kayan a can aka rabawa kowannen mu, wadannan kuwa ni kadai wani mutum ya ba ni. Amma ka tambayi mai martaba ya san mutumin da ya bani kayan, na ga sun kebe suna magana. Baffa ya jinjina kai ya bude ya sake bubbudewa, atamfofi ne manya guda biyu, leshina masu tsada guda biyu, shaddoji guda uku turare da kudi mai yawa. Yayin da ka ga kishi da hassada a wajen Nene da Inna, kishiyoyin Yafindo. Suka fara cewa, kada a karbi kayan nan a mayarwa Dagaci ya ajiye ya mayar musu, saboda ba a san ko dan yankan kai bane, ko dan iska ne ya yi asirin da zata yi ta binsa. Surutai dai barkatai na rashin ilimi da hassada muraran. Baffa ya zugu matuka, ya dura kaya a jaka ya tafi fada. Yafindo ba ta ce musu komai ba, don so suke ta ce a'a a yi fada, sun hade kai suna ta musguna mata, to ita kuma sai Allah Ya yi ta mace ce mai kawaici, sam ba ta nuna damuwarta akan irin wannan lamarin, wai a zartar da hukunci a kan nata ta nuna ta damu? A'a ba ta da haka. Mu ma ba mu tsira ba, sun tsane mu, daga zagi sai dunguri, komai muka yi ba dai-dai ba. Dagaci yana ganin Baffanmu sai ya ce, ''Yauwa daman yanzu zan aika a kira ka. Nasiba ta yi miji a birni, yaro dan boko mai ilimin addini da na zamani. Kyakkyawan bafullatani dan asalin, dan sarauta, ya ganta a wajen taro ya dasa, har ya fadawa mahaifinsa shi ne suka sa aka kira ni aka tambayi mahaifinta, na ce bai zo ba. Aka ce na isar da wannan sako nasu cewar suna neman iri a wajen ka na neman auren yarinyar nan. Ba ka kusa sai na ga idan na zartar da hukunci akan yarinyar nan ba zaka ce komai ba, don haka na amsa musu da cewar, babu damuwa an ba su ita. Mahaifina ya yi murna, ya duka ya yi godiya, ya ce duk abin da Dagaci ya zartar shi ne dai-dai. Gaba daya magana ya bari a hannunsa har a gama Hada-Hadar auren. Ya bar wadannan kaya gaba daya a hannun Dagaci. Baffa ya dawo gida ya sanar mana da yadda suka yi, sai gida ya hargitse mu da mahaifiyarmu muka dau kokekoke, musamman Nasiba ihu ta ke ta yi, har da yada zani wai ba ta so, saurayinta Kamilu ta fi so. Baffa ma ya dinga kuka yana bamu hakuri, ya ce, babu yadda zai yi ne yana jin nauyin Dagaci. Yayin da kishiyoyin Yafindo suka hau shewa da habaicehabaice wai kuda wajen kwadayi ya kan mutu, da aka ga kaya an bude ana murna, ashe za'a je a siyarwa da mai kudi *ya. Wa ya sani ma ko dan yankan kai ne ana yin auren ya kashe ta ya gudu ba a san asalinsa ba. Idan suka fadi haka, sai Yafindo ta sake tsorata ta rusa kuka, nima ina yi Nasiba tana yi, kaninmu Sabitu yana yi. Gida ya hargitse har makwabta suka shigo suna tambaya ko lafiya? Aka fara yamudidi da maganar a cikin garin, maganar ba ta bugu ba sosai sai asabar din da angon ya zo da iyayensa maza, a cikin wata dankareriyar mota baka. Abunka da Ruga ba a saba ganin mota mai kyau ba, sai aka hau guje-guje, wasu suka haye bishiya, wasu suka labe a bayan Zana, wai ga yan yankan kai nan.....'' Suka kyalkyale da dariya su dukka. Ba kamar Faduwa ma har da hawaye ta ke yi dan dariya. Abdul-Sabur ya ce, ''Ikon Allah ashe da gaske ana irin wannan rayuwa a kasarmu. Yaya aka yi kuma da suka zo? Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Mu dai muna daga gabagaba muna kallon *yan birni. Sunan saurayin da yake son auren Nasiba Abdul-Basi, ya hadu karshe inji samari. Dan Fulani, dogo, kyakkyawan gaske dan boko. A lokacin yana hada digiri dinsa a jami'ar Ahmadu Bello (A.B.U Zaria) bai gama ba. Mahaifinsa ma mai arziki ne da sarauta a Gombe, tare da shi suka zo da *yan uwan mahaifin. Aka yiwa Nasiba kwalliya da daya daga cikin leshinan da ya bata aka sa kawayenta biyu suka rako ta fada ta gaishe su. Duk da hawayen da yake zuba daga idanuwanta, amma ta yi kyau. Abdul-Basi kallonta kawai yake yi, na so da kauna. Mahaifina yana kusa da Dagaci aka gama magana sun nema kuma aka yi musu alkawari an ba su. Sai suka yi musu yayyafin naira, wacce sai da su kansu su Dagaci suka tsorata suka tafi suka bar *yan gari da yamadidi da zance. Watan Nasiba ya kama a garinmu, duk lungu da sako hirar kawai ake yi, yayin da Nasiba ta kaura daki ta dunkule a lungu ta bude shafin kuka. Hakuri kadai iyayenmu suke ba ta, da fatan alkhairi a cikin wannan lamari mai ban mamaki.... Faduwa ta kurbi lemo ta dubi Umaimah, ta ce ''Yaya ta kasance kuma? Umaimah ta ce, ''A takaice dai an yi auren amma ba yadda iyayensa suka so a yi da wurwuri ba. Abdul-Basi mai ilimi ne, ya ce su bari a shekara tukunna shi da ita su gama fahimtar juna, kada a yi tana kokekoke tana jin tsoronsa, shi ma a sannan ya kammala karatunsa. Da motar haya yake zuwa garinmu, dan acaba ya shiga da shi har kofar gidanmu. Ya shigo zaurenmu ya zauna akan tabarmar kaba a kira masa ita. Ta kudundune a lungu ta ki magana, sai dai ya yi hira da kawayenta. Inda ya burgeni sai ya daina cusa mata kudi sai dai ya yi mata kyaututtuka kadan-kadan ya fi so ya sami soyayyarta ba don kudinsa ba. Haka yake zuwa dandali ya zauna idan ana gada yana sauraron dadadar wakokinmu na gargajiya. Ranar kasuwa ma sai dai kawai mu gan shi tsakiyarmu idan muna Hada-Hadar cin kasuwarmu. Ni ce *yar gaban goshinsa daman na cika rawar kai, sai na yi tsalle na dane shi, ya ba ni kudi na siyo mana gyafa, magarya, kantu, mu shimfida tabarma mu zauna mu ci. Ita kuwa Nasiba ko tana walwala da ta gan shi sai ta bata rai, ta hau murgude-murguden baki, kawayenta suna ta shakiyanci suna sake tura ta. Sai su yi ta ce mata, ''Ka ga amarya, dan ta ga angonta har wani fari ta ke yi da ido. Shi ma ya shiga a yi ta zolayarta, dole ta yi dariya. Wasawasa har ta saki jiki da shi suke hirarsu rangadadai. Kafin ayi auren sai da ya sa su Baffa suka je gidansu suka gani, Nasiba ma da ni da kawayenta mun taba zuwa gidansu muka gaishe da mahaifiyarsa. Gida ne mai get na bulo da bulo a cikin garin Gombe. Hajiyarsa ta yi murna da ganinmu, ta yi mana kyauta ta girma. Ita ma tana son Nasiba sosai, ta roke ta data auri danta su zauna lafiya dan babu abinda ta fi so a duniya wanda ya wuce abunda *ya*yanta su ke so musamman ma Abdul-Basi, tafi sonsa gashi ba dan fari ba kuma ba auta ba. Aka zo muka sha biki a kauyenmu, irin wanda ba a taba yin irinsa ba. A lokacin an tura shi bautar kasa a Kaduna, a can aka wuce da amaryar. Muka je muka ga gida kamar ba a kasar nan ba, kuma gidan bene ne. Shi ma benen ba mu taba hawa ba, ya zama abin kwatance a wajenmu. Amarya tana son angonta kamar yadda yake matukar sonta, suka yi zamansu lafiya a can Kaduna. Sai da ya dade bai kawo ta ba, amma sanda ya kawo ta sai suka ganta da ciki. A lokacin duka-duka shekarunta ba su wu ce goma sha hudu ba a duniya. **************************** Ni da saurayina Ilah muna ta ci gaba da shakuwa don a lokacin ba zancen soyayya ba ne. Ta kai ta kawo duk garin an san shakuwarmu. Ko kiwo ni nake rako shi ni da kawata Matawata. Wata rana wasu baki manyan Alarammomi suka zo garinmu gidan Dagaci suka yi wa'azi suka bada shawara akan ya kamata a tura yara makarantar allo. Wato yawon almajiranci don a sami Malamai a garin, su ma nan gaba su koyar da na bayanmu. Sun yi gaskiya don gaskiya kam babu ilimi a garin, haka muke kara zube yara da manyanmu. 'Dirga da dirge' haka ne karatun da ake koya mana ba Fikhu, ba Tauhid, ba Hadis. Sallah kuwa duk yadda muka ga dama muke ta dungurawa. Da Dagaci ya yi yekuwa (sanarwa) aka hada dattawan gari ya sanar da shawarar wadannan malamai sai iyayen yara da yawa suka ki yarda, kalilan ne suka amince. Mahaifin Ilah ne yayarda zai tura yaransa biyu kananan wato Ilah da yayansa Sule. Mahaifina ya yarda zai tura dansa kwaya daya dan karami Sabitu kanina. Sai wasu kalilan da iyayensu suka amince. Muka yi ta kuka da zasu tafi yawon almajirancin nan da tabarma da akwatunan su aka. Ni abin ma ya yimin yawa, ga saurayina zai tafi ga dan karamin kanina da nake so zai tafi ya bar ni. Har kofar gari na dinga bin su da gudu ina kuka, Matawata ta ruko ni, ita ma da Ilah kukan suke yi. Ina ji ina gani suka tafi suka barni, garin Kaltingo aka kai Ilah karatu, yayin da Sabitu aka kai shi Numan. Sauran yara aka kai wasu Mubi, Jalingo da Adamawa da dai sauransu. Na dawo bana jin dadin garin a sanadiyyar rashin Ilah, babu mai siya min Rake, Kifi Mangwaro, in ci. Babu mai taya ni hira, saboda haka kullum ni da Matawata ba mu da hira sai tasa, tana matukar tausayamin, musamman idan ta ga na zauna ina ta kuka. Har waka na yi masa da YARENMU na Fulatanci ina bayyana yadda na yi rashinsa a tare da ni.... Tana zuwa nan ta kyalkyale da dariya. Abdul-Sabur ya ce, ''Gaskiya sai kin rera mana mun ji, don nima din da kika gan ni ina jin Fulatanci kadankadan. Faduwa ma ta yi dariya ta ce, ''Ki rera mana ko kadan ne mu ji. Umaima ta sake tuntsurewa da dariya, ta ce, ''Yau dai kun saka ni a lungu bayan labari har waka zaku sani na yi? To bari na rera muku kadan ku ji. ''Baba warnanu Inna warnanu Udilli uwartai Sayinde in gartatai Wure in imirintima Mi huidi a warti'' Ma'ana ''Baba ka zo Inna ki zo Ya tafi bai dawo ba Yaushe zaka dawo? Ka zo ina jiranka Na yi mafarki ka dawo. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Allah Sarki sabo, dan na san a lokacin ba ki san soyayya ba, don shekarunki ba su wuce tara ba a duniya zuwa goma. Umaimah ta gyada kai, ta ce, ''Haka ne, ban kai shekaru goma ba a lokacin. Babu yadda iyayenmu ba su yi ba a kawo Nasiba gida ta haihu, Abdul-Basi ya ki yarda ya ce, tana zuwa asibiti awo, kuma can zata haihu likitoci za su fi kula da ita. Ai da ta haihu ya sa kaninsa Ja'afar ya zo ya fada, ya ce a zabo masu zuwa suna kamar mata goma, za a aiko da mota a dauke su ana gobe suna. Mahaifiyarmu ba ta je ba, saboda alkunya *yar farinta ce, sai dai ta hada duk kayan da ta tanada kamar su yajin daddawa, rigunan jarirai, atamfofi masu arha, kwallin jarirai da guru da layoyi irin namu na Fulani dai da ake daurawa yara a wuya da hannaye. ( kafin ilimi ya shigo mu musan babu kyau ) Ta hada su cikin ledoji ta ce akai mata. Kishiyoyinta ne suka shirya su da sauran matan dangi da ni muka tafi. Inna zata dawo Nene ce zata zauna da ita, har sai anyi arba'in a haka aka shawarta. Muka je muka iske ta gida cike da mutane, bayan mai aikinta Talatuwa, ga kanwar baban Abdul-Basi a gidan tana kula da ita. Dakuna biyu ne kacal a gidan, sai falo da bandaki daya da kicin. Saboda taro dole ya koma gidan abokansa yake kwana. Nasiba ta saba da MAKWABTANTA masu kirki, girke-girke kala-kala suke yi mana su kawo mana. Gidaje takwas ne a farfajiyar get din, an zagaye da katanga doguwa. Sama da kasa ne flat guda hudu kenan, daga dukkan alamu gidajen haya ne a unguwar Rimi, Kaduna. Na tsinci kaina ina walwala a cikin birni, na harhada labarun abubuwan da na gani a birni zan ba wa Matawata idan na koma garinmu da Ilah idan ya zo da sallah, don an ce za su zo sallah. Sai naga duk mun zama *yan kauye a ranar suna, saboda kwalliyar *yan birni ba irin tamu ba ce. Bayan shudiyar atamfa da muka saka irin ta Fulani da jagira da dige-digen baki dabe-dabe a fuska, ga wata damara da na ci duk a dole gayu ne na yi na kure adaka, ni da iyayen nawa mu dukka, don ma Nasiba tana hanamu wani abun da ba karamin kwaba fuskarmu zamu yi ba da baki.. Suka kwashe da dariya su dukka ukun. Nima na kashe da daria.. Sai na tuna lokacin da Mal. Habu Imamu yakai Hannah Makarantar F.G.G.C Kazaure... Haka itama taci Uban damara kamar zataje dandali... Sai kuma Gobe idan Allah yakai mu. Sai kuma kumin apuwa na rashin jina jiya saka makon rashin wutan nepa.MAKWABTAKA 18 Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Ai gefe muka koma muna kallon makadan zamani irin nasu na Kaduna. Mun dai dauki hotuna wanda idan na gan su yanzu sai na yi ta dariya, mun yi wani wuki-wuki kamar ace kulle mu arce. Allah Ya raba mu da duhun kai da talauci. Amin. Su Faduwa suka hada baki su dukka suka amsa mata da, ''Amin''. Abdul-Sabur ya ce, ''Kinga birni daga dukkan alamu ya birge ki. Kin yarda kin koma Ruga kuwa? Umaimah ta harare shi kadan, ta yi gatsine ta ce, ''Cabdi! Ban koma ba, kamar ka sani zama na na yi ni da Nene har sai da aka yi arba'in. ''Ya sunan jaririn ko jaririyar da aka haifa? Umaimah ta ce, ''Namiji ne, sunan Mahaifin Abdul-Basi aka saka masa Salisu, amma Babangida ake kiransa. Da suka yi arba'in Nene ta ce, na shirya za mu koma gida, sai na ki saboda har na shiga islamiyya ni da yaran makwabta. Ga wuta, ruwa, kallon talabijin, bayan ruwan sanyi na firij da lemuna kala-kala (juice) da fanka da A,c, ana dauke wuta sai a tayar da Generator. Abinci mai rai da lafiya kala-kala, shinkafa kullum wanda a Ruga sai da sallah kadai, nama, taliya, makaroni da dai sauransu. A Central bank Abdul-Basi yake bautar kasa suna biyansa ba laifi, amma mutum ne mai kokarin ciyarwa. Sai a lokacin ne ma na fara koyon Hausa don bayan Fullancin ba ma yin Hausa sai kadan-kadan. Nasiba ta ce a bar ni a wajenta, bayan ta yi shawara da maigidanta ya amince a sallami Talatuwa mai aiki, ni na ci gaba da taya ta raino da aikin gida. Farin ciki ya rufe ni na ci gaba da zamana, Nene kadai aka mayar Dugge a motar da Baban Abdul-Basi ya aiko a dauke ta, bayan an hada mata goma ta arziki, da nata da na iyayenmu... Faduwa ta ce, ''An daurawa jaririn guru da layun? Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Mun daura masa mana, Babansa ne ya ciccisge ya zubar ya yi mana fada, ya ce ba ya so a sake daura masa irin wannan. Nan birni ne ba sa yin irin wadannan abubuwan. Abdul-Sabur ya ce, ''Sai suka saka ki a makarantar boko? Umaimah ta ce, ''An saka ni a makarantar boko, nima da girmana na shiga makaranta ajin *yan Nursery duk na fi su girma. To ban iya komai ba, duk sa'annina a aji uku suke na firamare, ban damu ba ina jin dadin sabuwar makarantata da kuma sabuwar rayuwata. Yaya Abdul-Basi ya ga da gaske na kasa koyon ABCD sai ya dage duk ranar asabar da lahadi da safe ko a ranakun aiki da daddare yana koyamin har da duka da bulala idan yaga ina noke-noke bana so na koya. Dole na tsaya na dinga koyo, har haushi Nasiba ta ke ji wataran idan ta ga ya dake ni, tana ganin ya takurawa rayuwata. Ya kan ce mana nan gaba za ku san gata nake yi muku ba zalunci ba ne. Ita ma dai suna nasu karatun idan ya gama da ni, ita ma dai da kadan ta wuce ABCD. Islamiyyar matan aure ya saka ta tana zuwa ranar asabar da lahadi daga takwas na safe zuwa karfe goma sha biyu. Sai na rike mata danta ta je ta dawo. Rayuwa ta fara yi mana kyau, can ma a Ruga wadata ta fara iske su, don kansa da kafarsa Yaya Abdul-Basi yana kai musu kayan abinci buhu-buhu, haka ma Babansa da yake mai arziki ne kuma mai yawan kyauta yana aika musu. Sai da na shekara ba mu je gida ba, da muka tashi zuwa sai muka je a gogenmu, lokacin birni ya fara ratsa jininmu. Sai muka zama abin sha'awa a wajen *yan garin Dugge, suna addu'ar dama su ne mu. Na iske Ilah ya zo gida ganin gida, sai farin ciki ya lullube mu. Na gan shi ya yi baki ya rame, amma fa akwai karatu. Ni da dan guntun abin da na koya zan kureshi, sai na ga ashe ya min nisa fintinkau. Ya iya rubutawa ya karanta kur'ani, ni da shi da kawata Matawata ne muke zama muyi ta ba wa juna labari, kowa ya bada labarin garin da yake da abubuwan da suka faru. Na ke ta basu labarin Kaduna da irin hadaddun da nake tare da su a gida da makaranta. Na dinga nuna musu yadda ake rubutun boko, da irin kayan dadin da ake ci a birni, ga wuta ga ruwa da kayan more rayuwa. Matawata ta yi ta bamu labarin dandali da sababbin wakokin da aka fitar wadanda ba mu iya ba, saboda ba ma nan. Ilah ya ba mu labarin Kaltingo da irin duka, bara da aikin da suke tika a makarantarsu ta almajirai. Yana cikin ba mu labari na fashe da kuka saboda tausayinsa shi da dan kanina Sabitu. Sai shi ma Ilah ya fara kuka, Matawata tana bamu hakuri. Na riga shi komawa Kaduna a garin na bar shi, nan ma sai da muka yi kukan rabuwa ni da Ilah har da Matawata ma ta sha kuka. Allah Sarki, sabo turken wawa. Abdul-Sabur da Faduwa sai jinjina kai suke yi saboda tausayawa. Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Muka dawo Kaduna muka ci gaba da rayuwarmu, mu hudu a gida. Ni da Babangida a dakinmu daya, Nasiba da mijinta a daki daya. Bankin Yaya Abdul-Basi ya yi bautar kasa ne suka rike shi ya fara aiki a wajen, suna biyansa kuwa albashi mai kyau. Ya sauya mota, ya sauya mana kayan gida gaba daya (furniture). Da a risho muke girki ya siyo mana gas cooker ya ga Nasiba ta sake hankali da wayewa zata iya amfani da gas don ada tsoro yake ji karta tashi gobara. Kowa ya kalli Nasiba da danta ya san suna cikin jin dadi da kwanciyar hankali, kyakkyawan yaro, lafiyayye, dan gata mai kama da mahaifiyarsa. Duk wani abu na sakawa, ci, sha ko na wasanni irin na yara Yaya Abdul-Basi ya siyowa dansa, saboda tsananin son da yake yi masa. Haka Nasiba ita ma duk wani abu na kwalliya da ya gani a wajen makwabta ko matan abokansa zai siyo ya kawo mata. Ni ma haka, duk abin da nake bukata ba ya kyashi yana siya min... Abdul-Sabur ya ce, ''Allah Sarki, Allah Ya sakawa AbdulBasi da alkhairi. Umaimah ta yi murmushi, tare da jinjina kai, ta ce, ''Amin. Nan da nan rayuwa ta sauya mana, duhu ya kauce, haske ya zo. Mun sami ilimi a maimakon jahilci, mun samu rufin asiri a maimakon talauci. Yaya Abdul-Basi yana farin ciki da ni, saboda ina kula da dansa sosai, kai ka ce ni na haife shi, saboda yadda yake sona har fiye da mahaifiyarsa. Allah dai Ya sakawa wannan mijin yayar tawa da alkhairi, don ya koyar da ni abubuwa da dama. Wadanda ko a makaranta ban koya ba. Mutum ne mai tausayi da kulawa, tattali da sanin darajar dan Adam. Idan ya so akwai sakin fuska a yi ta wasa da dariya, idan ya ki sai ya sha mur don ba ya son raini, daga ni har matar tasa sai mu nutsu idan muka ga irin yanayin. Ina gama Nursery sai kwakwalwata ta bude sai aka cilla ni gaba, daga aji daya sai na tafi aji uku, daga uku sai na yi biyar. Gaskiya ne na cancanci a tsallake min aji, don Yaya Abdul-Basi ya koyar da ni tsaf a gida. Dai-dai lokacin na fara girma, shekaruna sun kai goma sha uku a duniya. Haka idan na je garinmu sai na nutsu na daina baragada, saboda na ga yadda kowacce mace ta ke kama kanta. A lokacin Ilah ya dawo gida don ya yi sauka, ya zama kato har da gemu. Sai muka shiga gaisuwa ta mutunci da girmama juna gami da jin kunyar juna. Sai a lokacin na tabbatar har yanzu Ilah yana raina bai sauya ba. Ina sonsa matuka, ina jin dadin hira da shi. Matawata ta sha mamaki da ta ga har a lokacin ban daina kula Ilah ba, ta zaci na yi samari a birni, na manta da shi, ba ta san a birni ni kwaila ba ce, duk da ina samun samarin bana kula su Ilah ne kadai a raina. Ilah ya zama malam kowa sai ya durkusa yake gaishe shi, yara da manya da tsofaffi mata da maza. Ya bude makarantar Tsangaya, ma'ana makarantar allo a kofar gidansu shi da *yan uwansa kolawa ne suke koyar da karatu sosai irin su Alifun, Ba,un, an daina karatun dadirga da dirge. Yakan shiga gidajen iyayenmu mata ya koya musu. Na ji dadi da ganin wannan sauyi a Rugarmu. Kanina Sabitu shi bai dawo ba, don bai karasa sauka ba. Amma an ce ya kusa saukewa, wata shekarar zai dawo gida. Tunda ya tafi ba mu hadu ba shekara da shekaru, ko zai zo hutu ni bana nan. Idan na zo shi kuma sai ace ya tafi. Ina so na gan shi don ance ya girma har ya fini girma. Ni ma dai ina ta yakar jahilcin da ya mamaye iyayena mata da maza. Ina ta kokarin koya musu sallah don dai duk tsawon shekarun nan ba sallar suke yi ba, dungure ne kawai. Baffana da Yafindo ne kadai suka yarda suke gyarawa, Inna da Nene ki suka yi suka ce ba ni da kunya, yaushe aka haife ni da zan koya musu sallah? Haihuwa ta tsayawa Nasiba ita da mijinta, sai suka shiga damuwa suna ta yawo a asibitoci ganin likita. Babangida ya girma har ya shiga pree-nusery. Ni kuma na shiga sakandire mai kyau mai tsada, Federal Girls college da take unguwar Malali, ina zuwa ta jeka-ka-dawo. Ina aji biyu na sakandire na je garinmu Dugge hutu, ni kadai ce ma na je a lokacin ban da Nasiba. A lokacin mummunan labari ya zo mana an kashe samarin garinmu su biyar a hanya gaba dayansu abokan Ilah ne, har da yayansa daya Abashe. Ashe *yan fashi ne duk dare suke fita su tare hanya da mugayen makamai su kashe su kwace dukiya. Ilah ya yi kuka sosai ya razana matuka, yake ba ni labari bayan an yi sadakar bakwai. Ya ce, sun sha cewa ya zo su yi sana'ar da za su sami kudi ya bar maluntar nan, sai ya ki binsu, bai san me suke ba, amma yasan jahilai ne ba abin kirki suke yi ba. Shi kuwa da darajarsa a gari kowa yana gaishe shi, malam sama malam kasa ina shi ina biyewa zauna-gari banza? Ya ce, ko ranar da za a kashe su ma tare suke kwance su shida a daki daya suka farka cikin dare suka ce ya zo su je wani waje, sai ya ki zuwa suka fice suka barshi, sai gawarsu ya gani da safe. Allahu Akbar! Allah Ya shiryi zuriyarmu gaba daya.... Abdul-Sabur da Faduwa sai girgiza kai suke don babu dadi abin. Umaimah ta langwabar da kai cikin sanyin murya, ta ce, ''Sai na ji Ilah ya kara burge ni, na ji na sake sonsa. Ya tambaye ni yaushe nake so mu yi aure don mahaifinsa ya ce ya kamata ya fitar da mata ya yi aure, duk sa'anninsa sun hayayyafa. Yana gama fada min haka sai na ji kunyarsa ta lullube ni, na rufe ido na tashi da sauri na shiga gida. Na ji dadi da jin batunsa, duk da bana son kauye, amma idan dai zan auri Ilah na yarda na dawo Ruga mu zauna tare. Na kira kawata Matawata na bata labarin yadda muka yi da Ilah na ce ta je ta bashi amsar tambayar da ya yi min don na kasa fada masa amsa saboda kunya. Na ce ta ce masa ya tura Babansa ya je ya sami Baffana su yi maganar na san Baffana zai kira ni ya tambaye ni ko ina sonsa. Ni kuma sai na ce eh, shikenan sai a cire ni daga makaranta mu yi aure. Matawata ta ce, ''to shikenan, bari in je in same shi gashi can a tsaye a kofar gidansu. Ta tafi wajensa ina lungu a labe ina lekensu, a gabana ta isa wajen Ilah suka kebe suna magana, daga nesa nake bana jiyo abin da suke fada. Sai na ga Ilah yana fada yana wurga hannu, sannan ya juya ya shiga gida a fusace. Hankalina ya tashi na je da gudu na tambayi Matawata me ya ce? Sai ta tabe baki ta ce, ''Ya ce shi ai bai ce zai aure ki ba, bayan kin je birni samarin birni sun lalata ki me zai yi da saura? Sai na sankare a tsaye hawaye ya cika min ido, na daure na shiga gida ba tare da na bari an san halin da nake ciki ba, kwana da kwanaki. Kullum Matawata na gefena tana zuga ni wai na rabu da Ilah fa dan iska ne, ba malamin kirki ba ne, kawai yana labewa da guzuma ne yana harbin karsana. Ko wannan fashin da abokansa suke yi tare suke zuwa, shi da yake malami ne sai ya tauna layar zana ya bata. Wani lokacin naki yarda da maganarta, wani lokaci kuma na yarda dom ina ganin ma a wanne dalili zata min karya ni da aminiyata kuma MAKWABCIYATA? Idan muka hadu da Ilah sai ya harare ni, nima na rama ya wuce, na wuce alhali muna

Chapter 10 of 33