Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya tafi zai samo min makarantar sakandire ta kudi na karasa karatuna, tunda har na kai aji na hudu a can, kuma ya fuskanci ina da kokari, ina magana da Turanci sosai. Ita kuma Khausar tunda ba ta yi nisa a karatu ba zai samar mata makarantar koyon sana,a ta koyo ta dinga yi. Sai Ummana Fuse ta ce a saka ta a makarantar koyon rinin kamfala, amma babu makarantar anan kusa sai a Abrkan ake yi. Sai dai idan ta koma gidan kanwarta Umma Aisha da ta ke unguwar Dukuma ya fi kusa da Abekan. Shikenan sai aka tsayar da wannan shawara kafin ya koma England sai da ya tabbatar na fara zuwa makaranta, Khausar ta khaura gidan Ummna Aisha da ke Dakuma da zama, tana zuwa Abekan koyon kamfala. Ya yi mana alkawarin zai dinga aiko mana da kudin makaranta (school fees), da kudin motar zuwa da dawowa har mu gama. Abu daya ne ba mu ji dadi ba, shi ne da aka raba mu ni da Khausar domin tunda muke a rayuwarmu ba mu taba rabuwa ba. Ta yi ta kuka kullum ana ba ta hakuri haka ni ma idan na shiga bacci, sai na yi ta kuka ni kadai don tausayinta, bata da kowa sai ni na rage mata, haka ni ma ita ta rage min. Koda yake muna ganin kakarmu mai tausayinmu muna jin dadi, sai kadan daga cikin dangi masu kula mu kamar su Uncle Hamza da ya zo ya taimake mu. Duk wanda ya taimaki wani Allah Zai taimake shi...'' Umaimah ta yi ajiyar zuciya ta ce, ''Ya ya aka yi kuma? Abdul-Sabur ya yi dan murmushi, ya ce, ''Suna kiran motar hayarsu Bus da suna Toro-toro, kullum sai na hau toro-toro na tafi makaranta idan an taso na hau na dawo gida. Na ga bambanci tsakanin karatun Kano da na Accra, a Kano na fi *yan ajinmu kokari, tunda na shiga makaranta daga firamare har zuwa sakandire ni ne monita dan kokarina, amma a Accra ni nake zuwa na karshe a ajinmu har ana tunanin a mayar da ni ajin baya. Allah Ya taikama Malamin ajinmu ya ce a kyale ni ya ga alamar ina da kwazo da saurin koyo, watakila idan na dage na saba da *yan ajin zan yi kokari. Turancin su daban da namu, domin su suna kwaikwayon irin na turawa ne sosai ba kamar anan Nigeria ba da kowa yake yin yadda ya ke so. Hausawa suna turanci kamar da Hausa suke magana, Yarbawa suna yi kamar da Yarbanci, haka Igbo da sauran kabilu (broken English). Idan ka ji dan Ghana yana Turanci sai ka rantse a Turai ya girma, saboda kowacce kalma suna furta ta dai-dai da yadda Turawan suke furtawa. Tabbas yadda Malamin ajinmu ya fada haka ne, rashin sabo, fargaba da gane turancinsu ne ya sa na zama komabaya a ajinmu ba wai rashin kokarin ba ne. Amma da shekara ta zagayo sai warware gaba daya na rikide, ni da *yan ajin ake damawa. Da muka gama aji hudu muka wuce aji na biyar nan ne na gagari maza, ba ma matan ajin ba. Mu uku ne muke gumurzu akan karbar na daya. Idan na tashi daga makaranta da yamma sai na tafi 'Zarbarma Land' sunan unguwar ke nan, akasarin *yan unguwar Zabarmawa ne, ma'ana daga kasar Niger suke. Suna sana'ar canjin kudi, wasu na siyar da albasa, leda da fina-finan Hausa ko pure water. Ko na je unguwar Zango nan kuma *yan Nigeria ne, a nan ne za ku ga masu bara kutare, makafi da guragu. Nan na ke samun abin yi irin su dako, ko jiran shago ko tallata kaya a cikin kasuwa na je na zazzagaya na yi ciniki na kawo a sallame ni da dan kudi kalilan na ci abinci, na rago sauran na ba wa kakata ko na boye na ci abinci a makaranta idan an fito break.... Faduwa ta girgiza kai alamar tausayi, ta ce, Allah Sarki, ina kanwarka Khausar, a wanne hali ta ke ciki a can unguwa mai nisa Dukuma?'' Abdul-Sabur ya yi murmushin karfin hali ya ce, ''Tana can tunda ta je sai da ta shekara ba ta zo unguwarmu ba, ni ne dai duk sanda na bushi iska nake zuwa na ganta, haka kakarmu tana kokarin zuwa. Idan ta samo kwancen atamfofi sai ta zuba a leda ta je ta kai mata. Rayuwar Khausar abin tausayi ce a can, gida ne da yake cike da *yan mata, *ya*ya da jikoki na Ummana Aisha. Wasu *yan makaranta, wasu babu karatun, wasu ustazai wasu kuwa *yan iska. *Yan mata sunfi goma don haka sai rigingimu da tsegungumi, sun tsani Khausar, sharrace-sharrece kalakala idan an rasa wani abu ace ita ta dauka ayi ta zaginta ana dungureta. Sai daga baya aga abin ko a kama wacce ta sace a cikinsu Haka kowacce ta ke ciyar da kanta, don haka dole Khausar ta fita nema. Kudin motar zuwa da dawowa Abekan ba ya da matsala Uncle Hamza ya turowa Ummana Aisha tana ba ta, sai na siyen abinci ne da na zirga-zirga don daga makarantar wani lokaci suna hawa toro-toro su je wasu unguwannin koyon aiki kamar unguwar Nima, Guinea kwanakir ko Mamubi. Suna yini acan tun daga safe har marece. Ina iyakacin kokarina wajen kawo mata agaji da *yan kudade, biredi ko fanke da zata dinga yaga tana ci a duk lokacin da ta ji alamar yunwa zata yi mata illa. Rayuwa kenan, komai mai wucewa ne, dadi ko wahala.... Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Haka ne, babu abin da yake dauwamamme a duniya. Ya ce, ''Khausa ta rame saboda kewa ta, ga tsangwama da rashin wadataccen abinci. Sai na bata shawara ta dinga zuwa kasuwa tana rini ranar asabar da lahadi sai ta dan adana kudin da ta samo ta dinga cin abinci a makaranta. Da kai na na kai ta wata karamar kasuwa da ake kira Malata, anfi siyar da gwanjo a kasuwar, anan na samar mata aiki a shagon wata mata mai suna Mrs. Ibrahim don bana so na kai ta shagon maza saboda lalata. Ghana ba kamar Nigeria ba ne, inda ADDINI da AL'ADA suka saka kunyaa idon mutane, sukan rike mace a bainal nasi ba komai ba ne. Don haka zinace-zinace ya yi yawa, saboda arna sun fi yawa. Da farko Mrs. Ibrahim ta ki yarda ta dauke ta aiki data ji an ce sai asabar da lahadi kadai zata dinga zuwa, ta fi son wacce zata dinga zuwa kullum. Na dinga rokar ta har da durkusawa a kasa ina zubar da hawaye ina cewa ta taimaka mana mu marayu ne kuma baki ne a kasar dan bamu da inda zamu je mu sami wani aikin in ba a wajenta ba. Nan danan ta ji zuciyarta ta karaya sai ta tausaya mana ta amince. Sai na ji hankalina ya kwanta dan naga hankalin Kausar ya kwanta, ta kuwa ci sa'a ta hadu da uwar daki mai kyauta da tausayi. Tana bata lada fiye da kudin aikin yadda ta dauke ta. Allahu Akbar! Rayuwa kenan Allah Yana bayan wanda Ya dogara da Shi. Shekara biyu ne daman ake yi a makarantar koyar kamfala, Allah cikin ikonSa Khausar ta kammala, aka bata satifiket dan haka Ummana Fuse ta daukota, ta dawo da ita gidanta sai farin ciki ya kama mu. A waya na shaidawa Uncle Hamza cewar Khausar ta kammala makaranta tana neman jari za ta dinga yin rinin a gida. Ummana Fuse ta karbi waya ta sake yi masa bayani ta roke shi daya sake jurewa ya ci gaba da taimakon mu, dan mu marayu ne Allah zai taimakesa shima. Ya ce babu matsala, Khausar ta rubuta abubuwan da take bukata da yawan kudaden dan ya turo mata da kudin. Akwai wani bangare a gidanmu tsohon waje ne, bangarensa na gado ya ce ya bata aro ta dauka sai ta dinga yin rinin a ciki. Daya turo mata da kudin sai muka dauko masana suka tona mata ramukan, muka je kasuwa muka hado duk abubuwan da ake bukata a wajen rinin. Ni da Ummana Fuse sai muke dan taya ta duk da bamu san yadda ake yi ba amma muna taya ta da miko wannan, zubo wancan kamo wadancan. Idan tayi rina ta buga kamfalu kamar turmi goma ko ashirin sai ta kai kasuwa ta sararwa masu shagunan da suke sayar da atamfofi, shaddoji da kamfalu. Khausar ta zamo ita take bani kudin abinci idan zan tafi makaranta a lokacin ina ajin karshe ina shirin fita. Muka zamo ba'a sauke tukunya a gidan Ummana Fuse abincin safe, rana da na dare duk muna dafawa saboda cinikin kamfalar da Khausar take samu. Hankali a kwance nake ta karatu yadda ya kamata dan haka na ci jarabawa sosai fiye da tunanin mutane. Daga cikin darussa guda tara da muke yi na ci A1 shida, B1 biyu C1, kuma sciences na yi. Koda na fadawa Uncle Hamza abunda na ci a jarabawa sai ya yi farin ciki ya kuma yi min alkawari zai nemar min makaranta a jami'a mai kyau a Ingila sai in karanci Medicine ko Engineering. Farin ciki ya lullubemu, Ummana Fuse ta ce nayi shuru da bakina kada na fadawa *yan uba da sauran *yan uwa masu hassada sai dai kawai suji tafiya. Na ja bakina na yi shuru inajin *yan hassada kuwa suna ta surutai wai mu ne tsintacciyar mage an ci jarabawa an rasa kudin shiga jami'a. Da aka fada maka Hamza zai iya biya maka kudin jami'a ne? Wanan me shegiyar rowar? Ummana Fuse ta ce in yi musu shuru kada in ce komai. Allah cikin ikonSa shekara na zagayowa Uncle Hamza ya yi waya ya ce in hada takarduna in kai gidan abokinsa zai kai masa Ingila, ina rawar jiki na hada na kaiwa abokin. Bayan tafiyar abokinsa da watanni uku sai ya turo min da komai na tafiya kamar tikiti da biza aka tabbatar min na sami shiga jami'ar Cambridge da take cikin Ingila. Na yi sallama da kakata da kanwata ina kuka suna kuka, makiya suka sha takaici a lokacin da na zaga dangi ina mai musu sallama tafiya ta tabbata. Na tafi Ingila karatu cikin kwanciyar hankali, sai dai matsalolin da ba'a rasa ba daga matarsa da *ya*yansa ba sa so na, saboda tsabar ba su saba ganin bako a gidansu bakar fata ba, da kuma yahudancin da yake cikin ransu. Ko kudi ko kaya zai ba ni, sai dai da dubara kuma a boye, saboda matar sai ta hana shi baro-baro a gabana. Kun san Nasara bai iya boye-boye ba da gulma, gar da gar suke abubuwansu. Ban damu ba saboda na saba da irin wadannan tsangame-tsangwame a baya. Karatuna na saka a gaba don shi zau fishshe ni. Da zaman ya gagara ma sai na shawarci Uncle Hamza nace ina so na koma zama a cikin makaranta a rukunin gidajen dalibai da yake cikin makaranta. Ina so mu zauna gida daya da abokina Usman shima dan Accra ne. Uncle Hamza ya yarda ya biyamin duk abin da na bukata na kudin haya, kayan abinci da dai sauransu. Lokacin wayar hannu ba ta wadata ba sosai a Accra, sai dai na kira wani gida a kusa da gidan su Ummana Fuse na ce a kira su, bayan mintuna ashirin sai na sake kira mu yi magana da su. Kullum suna cemin ba su da wata matsala kasancewar aikin rinin kamfala ya karbi Khausar, an fara saninta ana ta kawo mata aiki, suna samun na cefane. Amma duk da haka idan na sami mai tafiya ko kuma transfer ta banki sai na kundige rabin kudin da Uncle Hamza ya ke ba ni na tura musu, don su sake jin dadin rayuwarsu. Kasancewar akwai ayyukan yi a England da na gane gari, sai na dinga fita ina yin ayyuka irin na awannin nan a biya ni. Kamar ba da abinci a hotel, goge-goge da share-share a ofisoshi, duk ranar da ba ni da darasi. Alhamdulillahi na samu kudi mai yawa a wannan harkar, saboda na iya aikin karfi, kuma ba ni da girman kai. Sabanin abokaina *ya*yan masu hali, wadanda iyayensu ne suke turo su karatu sun kuma jifgo musu dukiya mai yawa saboda gata, kada ma *yan Nigeria su ji labari sun fi kowa irin wannan wadaka da kudi. Ina turawa su Khausar kudi masu yawa da kayan sakawa daga English wears har atamfofin super Hollanda yayin da mahassada suka shiga aikinsu na hassada da yada labarun karya. Wai sai dai idan ba karatu na je ba, damfara nake ina turo musu da kaya da kudi haka. Idan su Khausar suka fada min sai na yi dariya na ce su rabu da su, kuma su toshe kunnuwansu ko sun ji su ki ji. Abinka da Babba sai Ummana Fuse ta shiga yimin nasihohi tana cewa, kada na yarda na biyewa abokan banza na fada harkar banza. Kada na sake na yi sata ko damfara dan na turo musu da kudi, su rinin kamfalar nan ma ya ishe su, su ci abinci. Na yi mata rantsuwa bana banayin wannan harkar inda ina yi da Uncle Hamza ya sani tuntuni, kuma da zai sanar da ita koma ya koro ni gida. Kuma can kasa ce mai tsaro kana yi za,a kama ka, na'urorin daukar hotuna a ko'ina. Khausar daman a bayana ta ke, tasan halina don haka ba ta damu da sharci-fadin mutane ba, ita ce mai hana Ummana Fuse zato. A waya suke fara fada min cewar, Khausar ta sami saurayi yana so ya aure ta, sunansa Isah. A Accra yake zaune yana sana'ar siyar da gwanjo, amma dan asalin garin Kita ne dan Yaren Aibe. Umaimah ta ce ''duk kasar Ghana ne? Ya ce ''Ai garin Kita nan ne ma asalin Ghana dan dai yanzu garin duk babu mutane sosai ruwa ya cinye su, saboda suna da katon teku wanda ya ke fita har kasashen turawa. Akwai gidajen tarihi da suke wajen idan ku ka je zaku ga jinin bayin da turawa suka kashe, idan bayin suka yi gardama ko rashin lafiya, ko idan suka yiwa mace baiwa ciki sai su harbe ta anan dan basa son su haihu da su. Ban bawa Khausar goyon baya ba, don ban cika son auren Accra ba, dama zata sami dan Kano mana ta aura ta dawo gida don ni har yanzu ban fitar da ran zan kaura gida ba, don tarbiyar Ghana ba ta yi min ba, ga su da nuna kabilanci. Da na ji maganar aure tana kara kankama sai na fito baro-baro na fada musu ra'ayina cewar, bana so a yi auren nan, na fi so ta auri Bakano. Haba sai Ummana na Fuse ta hauni da fada, ta zage ni tas har da koke-koke a waya, wai dama har yanzu ba na kaunarsu, su dangin mahaifina, na fi son dangin mahaifiyata duk wahalar nan da ta yi da mu dama niyyarmu mu gudu mu bar ta wata rana? Kun san tsoho da rikicewa, yanzu ya lauya maka magna. Hankalina ya tashi na shiga lallashi ina gyara lafazina. Da kyar dai ma samu ta huce da ni, don da ta daina zuwa ta dauki wayar ma idan na bugo sai dai Khausar ta zo. Daga baya ma na hada musu wayar a gidan (land line) suka huta zirga-zirgar daukar waya gidan mutane kullum.... ''Ya yi dariya. Umaimah ta yi murmushi ta girgiza kai, ta ce ''Kai! Me yasa ba ka so kamwarka ta yi aure alhali ta yi shekara ashirin koma fiye da haka tunda ba karatu take yi ba ai gara auren. Abdul-Sabur ya gyara zama ya yi dariya, ya ce ''Haka ne, na gode da wannan tambaya taki. Ina da dalilaina masu yawa. Kinga macen Ghana dole ta fita nema don idan ma baki da sana'a ko aiki babu mai auranki. Na tabbata yaron da yake son Khausar ya zo wajenta ne a dalilin ya ga tana da sana'a, tana samun kudi, kuma ga ni Yayanta a turai, ina turo musu da dukiya. Da ace ba ta da komai ba ma zai zo ba. Haka idan an yi auren raba dai-dai za a dinga yi ta yi wani aikin ciyarwar, ya yi wani shima. A lokacin ne ma zata fi zagewa tana yin rini tun karfi don takai masa wadataccen kudi. Na biyu, tarbiyar yaran da zata haifa ba zata yi kyau ba, saboda al'adunsu kamar babu musulunci a ciki. Na uku, bana so na tafi na bar ta ita kadai a kasar, na santa da mako, tuni zata gigice ta rame da koke-koke don ba ni da ra'ayin sake zama a Accra kuma, idan bana turai to ina Nigeria, Abuja da Kano.'' Faduwa ta yi murmushi ta ce, ''Ashe ba ka auri *yar Ghana ba?'' Ya tuntsire da dariya, ya girgiza kai, ya ce, ''Ban auri *yar Ghana ba. Ina can suka fadamin an saka rana, don haka suna bukatar kudi masu yawa saboda shagalin bikin da ake a can ya baci. Bidi'a ce zallah. Umaimah ta ce, ''Ai daman ko a Nigeria al'adar auren Hausawa gidan mata suna shan wuya, bayan kayan daki da gara. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, can mata ba sa kai kayan gara, duk miji ne zai yi. A inda suke kashe kudi a wajen shagalin biki ne sai a fi sati mata suna daukar girki ba na wasa ba, kuma mai dadi da nama cusu-cusu. A biki dole ne ka yanka sa ko shanu, rago ko raguna, bayan kaji. Saboda bikin ne mata suke hada kungiya (meeting) suna taro duk karshen wata suna tara kudi ana ajiyewa don idan biki ya kama wata a cikin kudin da aka tara za a siya mata abubuwa don ta rage nauyi. Suna fara aiki ranar juma'a da daddare a yi kunshi nan ma taro ne za a yi mata tuli a kan kujeru a kofar gida, abinci kala-kala, iyayen amarya dole su sayiwa *yarsu leshi mai tsadar gaske ta saka a wannan rana. Washe gari asabar sai a yi Ashadi shima amarya sai ta canza kaya tsadaddu kamar kala uku ko biyar. Duk sai da na kundige wadannan kudade na aiko musu suka sha shagalinsu, na bita da addu'ar fatan fatan alkhairi. Da na kammala karatun degree dina da kaina na biya na wuce na yi masters dina. A lokacin na mallaki gidan haya babba ni kadai, da motar hawa. Sai dai naje ofishin Uncle Hamza na gaishe shi a can dan kiyayyara tayi tsamari tsakanina da iyalansa har babban dansa ya ja min kunne kada in sake zuwa gidansu, idan ya sake ganina sai ya harbe ni. Don haka sai na fadawa Uncle Hamza sai dai na dinga ganinsa a ofis ko kan titi. To yawanci ma sai ya zo ya same ni a makaranta ko a gidana mu yo maganar da zamuyi, don so yake idan na gama karatu ya gutsuro wasu daga cikin dukiyarsa ya fara aikena Indonesia da Swizerland ina saro masa shaddoji, leshina na mata da huluna sana'arsa ke nan. Amma ya lura *ya*yansa da matarsa suna kacaccala masa dukiya sai ya je kasuwa ya tarar sun je sun karbe ciniki bada izininsa ba. Haka kuwa akayi, ina gama karatu ya hadani da wani Ishaya babban yaronsa dan Nigeria ne shi ma, muka je kasashe uku ya nunamin wuraren sa suke saro kaya. MAKWABTAKA 16 Zuwana cikin shagon sai na ruguza cutar da suke yi masa wajen lissafin bogi, na saka musu ido don ba su isa su yi min wayo ba, na fi su ilimi. Sabanin Uncle Hamza wanda bai yi makaranta ba. Bakin jini na yi sosai a wajen ma'aikatan dan suna ganin ba karamin tauye musu rayuwa nayi ba, sun daina samun kudin cuta. Da akwai yadda zasu yi da sun kawar da ni daga doron kasa. Ganin wannan riba mai yawa da Uncle Hamza ya yi sai ya sake yarjewa da ni ya fi so na kasance tare da dukiyarsa. Ya sa na zo muka zauna muka tattauna abin da za a yi kowa ya ji dadi tsakanin ni da shi. Ya ce, kada na damu da sai na yi aiki, duk tafiya daya idan aka saro kaya sai a bari a siyar sannan a raba gida hudu. Shi kashi biyu, ma'aikatan kashi daya, ni kashi daya. Na yi murna da jin haka, don kudin da zan dinga samu ya fi albashina na watanni shida ma. Na amince na yi godiya muka ci gaba da yin haka. Sai a lokacin da na karbi ribata ta farko na shirya na taho Accra ganin gida, shekaruna shidda rabona da gida. Na ga Ummana Fuse ta kara tsufa yayin da Khausar ta yamutse saboda wahala, ba ta jin dadin auren, azzalumin miji ta samu yana yi mata wayo tana nemowa yana karbewa. Duk sun yi mamaki da ganina, na girma na yi kyau, na yi fari kal, ga wata kasumba da na tara. Ina isowa na tari sabuwar motar da na auno tun ban zoba na turo, a ita na ke yawo gidan *yan uwa da abokai. Sai kallo na ake ana sha'awar ni'imar da Allah Ya yi min a rayuwa, mahassada suna ta surutai, babu abin da ba su ce ba. Sane nake yi, damfara, yankan aljihu da dai sauransu haka suke cewa. Ban damu ba, don ko sauraron su bana yi. Uncle Hamza ya yi bakin jini a wajen dangi makusantansa, wadanda suka fini kusanci da shi. Wai har ya dauko bare ya saka shi a harkar arziki su bai dauki *ya*yansu ba. Nan fa kowacce ta fara buga masa waya tana balokoko da magiya ita ma ya turo ya kai danta England. Dogon turanci yake musu, bayanai ne kawai da lallashi, a cikin bayanan nasa kuwa ba zai yiwu ba ne kawai su yi hakuri. Kaina da kafata na yi ta taimakon dangi mabukata, suna ta godiya, masu kushewa suna karba sai dai idan na tafi su zaga. Na canja fasalin gidan kakata, na canjawa Kanwata ita ma duk abubuwan da ta ke da bukata. Na kara mata jari, na kuma bata hakuri gami da yi mata nasihohi akan ta yi hakuri ta ci gaba da biyayyar aure. Na kira mijinta muka gaisa, na yi masa kyauta mai tsoka, sannan na yi masa wa'azi cikin siyasa akan ya sani mace kiwo ce Allah Ya ba shi, Allah zai tambaye shi yadda ya yi da ababan kiwon nan da aka ba shi a ranar tsayuwa. Ya fahimci abin da nake nufi, shi ne ya rage sosai zaluncin da yake yi mata, daman dai ba su taba haihuwa ba, saukinta kenan. Na koma England harka ta sake budewa, na samu Uncle Hamza yana samu, ina murna yana murna haka muka yi da bawan Allah nan har tsawon shekaru biyar. A lokacin ne hassadar iyalansa ta fito baro-baro *ya*yansa suka zo har ofishina suka cakume ni suka fito da ni, wai na bar musu dukiyar mahaifinsu ya tsufa yanzu zasu ci gaba da kula da ita. Babu yadda zai yi a gabansa na harhada na fice yana hawaye, ina hawaye. Ya san kawai rusa shi zasu yi, tunda duk *yan shaye-shaye ne su da uwarsu. Uncle Hamza ya koma gida ya zauna ya zuba musu ido sai abin da suka kawo masa yake karba, sai lokacin ya ga illar auren Ahlul-kitabi, nasara asarar duniya. Oho, sunyi ta banza don ni duk ribata da ake ba ni suna boye a banki, kuma na riga na san hanya nasan mutanen kamfanin su ma sun san ni. Da jarin na je na kawo kayan na canja gari na bude shagona a can. A hankali aka gane ni, nima na sami masu siya. A hankali na sami ma'aikata da teloli. Amma kafin na fara sai da na je na shawarci Uncle Hamza ya ce ya ba ni izini na yi, ya yi min fatan alkhairi. Sai a lokacin na sami nutsuwa nake zuwa Accra akai-kai, wani zuwa dana yi na iske auren Khausar dai ya ki yiwuwa, sai da suka rabu ta dawo gida suka zauna da Ummana Fuse. Na ma fi jin dadi da aka yi haka, ga shi ba haihuwa suke yi ba, sai rigima kullum, har dukanta yake yi. Na ba ta shawara ta koma makaranta ta yi yaki da jahilci, ta kudi ce ana koyar da kowanne darasi da Turanci tsabarsa kuma ka sami kwali mai daraja kamar kowacce sakandire. Ta yarda ta shiga ta fara daga aji daya na sakandire, don ta iya aikin firamare. Ina can dai a Ingila, na sami labarin daga Khausar cewar ta yi hutun makaranta, sai na yi musu biza ita da Ummana Fuse, na turo musu kudi suka sayi tikiti suka zo suka same ni a Ingila. Wata guda suka shafe tare da ni ina ta yawatawa da su, duk wani wajen shakatawa sai da na kaisu. Kwanakin su biyu a gidan Uncle Hamza, sannan suka dawo gidana. To a wannan zuwanne abokina Shamsu dan Nigeria garinsu Minna, Niger State banufe ne. Ya ga Khausar kanwata ya ce yana sonta, shima tare muka yi karatu yana aiki a Abuja, amma yana zuwa Ingila akaiakai. Sai na ce, a,a ba zai yuwuba, shi da ya ke saurayi bai yi auren fari ba, ita kuwa bazawara ce duk da ma ba ta taba haihuwa ba. Ya girme ni nesa ba kusa ba, ba yaro ba ne, don alokacin ya yi shekara arba'in. Ita kuwa ba ta wuce talatin ba. Ya ce, shi dai yana sonta, zai aureta kuma. Sai na ga ita ma ta karkata da sonsa. Ban hana ta ba, na fi kowa farin ciki idan har za a yi auren saboda nasan Shamsu na san halinsa, yana da kirki ga rikom addini. Uwa-uba dan Nigeria ne a can zai zauna da ita, wanda shi ne ra'ayina daman tuntuni. Da ta ji na ce Nigeria zamu wuce daga nan ni da su Khausar, sai ya yi murna don kawai za'ayi ta, ta kare, ma,ana idan ya biyo mu Nigeria sai ya kai ta iyayensa su ganta a tsayar da maganar aure ko ma a daura kawai tunda gani ga Ummana Fuse, ga dangin mu a can. Mun riga shi iso Nigeria san nan ya biyo mu daga baya. A waya ya sanar da ni ya iso Mina, na ba shi adireshin inda zai same mu. A gwarzo muka sauka, sun sha mamaki da ganinmu, don sun zata ma ba ma raye. Tun sanda Baba Mukhtar ya kai mu ya dawo babu wanda yasan halin da muke ciki. Sai muka zama tamkar taurari abin haskawa a kauyen nan. Aka dinga tururuwar zuwa ganin mu ana kawo mana abinci kala-kala. Kannena Hassana da Usaina su na fi damuwa da na gani, Alhamdulillah suna cikin rayuwar rufin asiri kasancewar mahaifinsu tsayayye ne me neman na kansa ne. Na siya musu kayan sakawa da kayan kwalliya kai ka ce lefe ne suma aka hada

Chapter 8 of 33