Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ajiye, don tashin hankalin abubuwan da suke fitowa daga bakin Faduwa. Suka dunguma zuwa kan kujerun da suke falon, suka fara kallon wani film da ake yi a MBC Action mai suna NIKITA Faduwa ta dubi Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Umamah, zan so naji tarihinki. Kina karamarki me yasa kika shiga damuwa haka? Naga shekarunki ba suyi nisan da zaki damu ba don ba ki yi aure ba. Meye matsalarki? Yayin da Abdul-Sabur ya ware ido da kunnuwa yana kallo, yana kuma saurarenta don ya kagu ya ji ko ita wace ce. Sai kunya ta rufe Umaimah, ta yi murmushi ta sunkuyar da kai gami da sosa goshi. Ba ta san ta inda zata fara amsa wannan tambayoyi da Faduwa ta jero mata ba, tana da nauyi amsawa sosai. Abdul-Sabur ya gyara zama ya ce, ''Mu da ke mun zama *yan uwa masu kaunar juna da tausayawa. Kamar faduwa yaune na farajin labarinta, na ji na sake shakuwa da ita, kuma zanyi tattalinta wajen kula da walwalarta da taimakonta da shawarwari. To haka musulmai ya kamata su kasance musamman na MAKWABTA. Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Haka ya ke, ka ba ni labarinka tukunna sai in bada nawa. Abdul-Sabur da Faduwa suka kwashe da dariya ya ce, ''Labarina kike so ki ji kafin ki bani naki? To ki gyara zama ki karkade kunnenki kisha labari. Ni da Faduwa za,a sami wanda rayuwarsa ta fi abin tausayi. Faduwa da Umaimah suka gyara zama suka zuba masa na mujiya suna kallo, suka baza na zomo suna saurarensa, dan sun kagu ya fara fada. LABARIN ABDUL-SABUR Ya ce, ''Sunana Abdul-Sabur, sunan mahaifina AbdulRashid, Mahifiyata kuwa Habiba. Mahaifina mutumin kasar Ghana ne a cikin garin Accra, duk da asalinsa Bakano ne mahaifansa zama ya kai su Accra aka haife shi a can. Mahaifiyata kuwa mutumiyar Kano ce, wani gari da ake kira Gwarzo. Kasuwanci tsakanin Accra zuwa Lagos, zuwa Kano shine sana,ar da mahaifina yake yi, shi da *yan uwansa da abokansa a dalilin haka ne ya zo Kano harya hadu da Mahaifiyata. Aka yi rufa-rufa aka hada baki da tsohon da ya ke yi musu masauki a Kano mai suna Malam Barau, ya ce shi ne mahaifinsa, aka ba shi auren mahaifiyata Habibah ba tare da danginta sun san gaskiyar magana ba. Bayan anyi biki suka zauna a unguwar kofar Nassarawa kusa da gidan Sarki, gida daya suke zaune da Malam Barau. Don haka Mahaifiyata ta zaci Malam Barau shi ne surukinta, wanda ya haifi mijinta, ko kuma yaya ga mahaifinsa uwa daya uba daya. Suna zaune zama na girmama juna da martaba juna, har Allah Ya albarkace su da samun haihuwa, aka haifi ni Abdul-Sabur sunana, Malam Barau ya zaba ya saka min, banci sunan kowa ba. Shekaruna hudu a duniya aka haifi kanwata aka saka mata suna Khausar. Ni da Khausar muka taso cikin kuncin rayuwa, shi kan shi gidan Malam Barau din dan karami ne, matansa biyu da *ya*ya kwatsam. A cikin gidan aka yanki daki daya kacal aka zagaye mana babu kicin sai dai muyi a kofar daki, ban daki kuwa sai dai mu dauki buta mu zagaya gidan Malam Barau mu bi dogon layin shiga bandaki. Babu maganar makarantar boko ma a nan a zube muke tare da yaran unguwa, sai dai muna zuwa makarantar allo safe da yamma. Mahaifina matafiyi ne, bai cika zama a gida ba saboda yanayin kasuwancinsa tsakanin kano da Lagos, zuwa Accra bai daina ba, kuma ya fi dadewa Accra ashe can ne garinsu, can ya fi sabawa a can ya fi zama. Mu sai ya shafe watanni shida baizo ba. Kayan abinci ya kare babu kudi, sai mu yi ta fama, bara ce kawai ba ma yi. Allah Sarki uwa, Mahaifiyarmu Umma Habiba muke kiranta ta sha wahala da mu. Saboda tsabar surfe da daka har zannuwanta yayyagewa suke yi, ba ma a maganar hannayenta duk sunyi kanta, don kawai ta ba mu abinci muci. Allah sarki rayuwa kowa da kalar tasa jarabawan. Allah ya yayewa kowa kunci na rayuwar sa yasa mu haye jarabawar rayuwar dunia. Aameen. Babu irin sana'ar da ba ta yi ba, har da irin sana'ar nan da mata suke yi a kasuwar rimi ta siyar da tsofaffin kayan sakawa. Ba zan manta ba aka ba ta dillancin wasu kaya atamfofi da leshina akan ta je ta siyar za a bata lada ashe kayan sata ne, sai mai kaya ta kama kayanta a wajen siyarwa da aka bi diddigi aka gane mahaifiyata ce ta siyar, aka taho da *yan sanda aka kama ta har gida. Kwanan Ummana Habiba biyar a daure a ofishin *yan sanda, hankalina ya yi matukar tashi. Daga lokacin na kuduri niyyar neman sana'ar yi kowacce iri ce, idan dai halak ce, don na hana mahaifiyata irin wannan wahala. Malam Barau ne ya dinga kai kawo da kyar aka fito da ita da sharadin sai ta biya mutane kudinsu, ita kuwa ba ita ba ce ta kashe kudi, lada aka bata wanda bai kai ya kawo ba. Data yiwa matar data sato kayan ta bata talla maganar cewar ta kawo wadannan kudi su mayar, sai ta ce ita tuni ta kashe kudi. Tsohuwar fankar mu, tsohon gadon mu mai rumfa na karfe su muka fitar muka siyar muka biya bashi muka koma bacci akan tsofaffin tabarmi da tsummokaan kayanmu., don ko tsohuwar katifa bamu da ita.... Abdul-Sabur ya cije lebe yayin da hawaye mai zafi ya yi ta kwaranyowa masa. Ya kasa ci gaba da magana saboda tsananin kunar da zuciyarsa ke yi masa. Faduwa ma ta matse hawaye ta girgiza kai ta ce, Allah Sarki ka sake tuna min da uwata ita kadai na sani a duniya ta tafi ta bar ni. Umaimah ta runtse ido sai hawaye ya bulbulo daga idanuwanta masu radadin fita, tabbas itama ta tuna da tata tsuhuwar. Abdul-Sabur ya sa hannu a aljihu ya zaro hankici ya sharbe ido da hanci ya ci gaba da cewa. ''Duk abin nan da ake wai sunan mahaifina yana raye a duniya ya yi tafiyarsa ya bar mu. Abinci da yake bari da kudin cefane bai fi na wata guda ba, sai ya je ya yi watanni shida kuma sannan ya zo ya yi wata daya ya koma. Sutura sai da sallah zai yi mana guda daya-daya su ma ba na kirki ba kafin shekara ta zagayo sun kece. Mahaifiyata ta so ta dinga rike hannun Khausar suna zuwa bara, na hana su, na ce su zauna a gida ni zan fita nema. Shekaruna goma sha daya na saba da dako a kasuwar *yan rodi da ke kofar ruwa, nan cikin jihar Kano. Tokar itace ce muke daukowa aka mu ke kaiwa masu karafe, su bamu naira biyu ko uku, a yini dai baifi na sami naira biyar ba. Ba zan manta ba akwai wata rana da na dauko toka aka cikin wani katon daro ashe akwai garwashi a ciki ban sani ba, tururin zafinne ya cinye kwalin da na dora a kaina ya soma cinye gashin kaina, sai da ya fara kona fatar kaina sannan na ji zafi na yi wurgi da daron, sai ga gashina kamar anyi gobara. Ranar babu kudi saboda na zubar da toka ga ciwo a kaina ba zan iya zuwa na nemo wata ba. Da kafa na taho gida ga nisa, ga yunwa, ga ciwo. Ina zuwa gida na iske taron jama,a aka shaidamin daga Accra aka aiko da wasikar cewar, mahaifina ya rasu. Na gigice, na tambaya ina gawar aka ce an binnne shi a can. Sai na yi mamaki me yasa ba a kawo shi ba wajen mahaifinsa da *yan uwansa ba an binne shi? Mun yi kuka sosai, musamman mahaifiyata, ashe ita tasan tashin hankalin da zata shiga nan gaba. Muna nan dai a haka har ta gama takaba, ni nake fita inayin dako na kawo muci garau-garau mu kwanta. Sai naga Malam Barau da abokan mahaifana su uku suma *yan Ghana ne sun shigo bangarenmu suka kira Mahaifiyata suka zazzauna. Sai aka koremu waje ni da kanwata suka ce za su yi magana. Na kama hannun kanwata muka fice, na zaunar da ita a kofar gida, sai na dawo na labe ina so na ji abin da yake faruwa. Kamar yadda Umma Habibah ta girgiza ta razana da jin bayanansu, haka nima na dimauce, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Abdul-Sabur ya yi shiru ya dafe kai ya kasa ci gaba da magana. ''Me ya ke faruwa?'' Umaimah ta tambata a gigice. AbdulSabur ya dago da jajayen idanuwansa ya dube su. Ya ce, ''Allah Ya yi mana maganin masifa, kada Allah Ya maimaita mana bala,i. Wato gaskiya ce aka fede ta daga wuya har bindi. Malam Barau ya fadi duk kulla-kullar da aka harhada wajen auren Umma Habibah aka ce shi ne mahaifinsa alhali shi bai san shi ba, sai a sanadiyyar kasuwanci. Malam Barau ya kara da cewa shi ya ke basu masauki idan sun kawo kaya daga Ghana. Ashe zaman nan da muke yi agidan Malam Barau haya ce muke yi, duk shekara mahaifina yana biya. Don haka babu hadin mahaifina da Kano, danginsa dukka suna Accra. Wadannan da suke tare da Malam Barau sune abokansa daga Accra su ma suke zuwa tare da mahaifina, su ne ma suka kawowa Malam Barau labarin rasuwarsa. Sun shaida cewar iyaye da kakannin mahaifina *yan Accra ne. Mahaifinsa ya rasu Mahaifiyarsa na nan a raye wato kakarmu. Kuma yana da *yan uwa da yawa wadanda suke uwa daya uba daya, da wadan da suke uba daya kawai. Sannan yana da mata biyu a can da *ya*ya takwas. Bai fada musu ya yi aure a Kano ba har ya haifi *ya*ya biyu ba, sai bayan rasuwarsa aka fada musu sun ce babu ruwansu tunda bai fada musu da bakinsa ba. Suka rabe gadonsu duk da hotunanmu da aka nuna musu a cikin kayansa. Kenan mu mun tashi a tutar babu, ba mu da gado a can, a she a nan ma ba gidanmu ba ne. ''Allah Ya isa tsakanina da ku da shi da ya mutu, kun ci amanata.'' Kalmar da Ummana Habibah ta dinga fada ke nan, ta tashi da gudu ta shiga daki tana kuka. Subhanallahi! Sai na sulale na tsuguna na rike kai, har su Malam Barau suka fito suka iske ni a inda na labe. Sai suka tausaya min. Baba Mukhtar daya daga cikin abokan Babana ne ya jawo hannuna ya rike ya ce, ''Yi hakuri Abdul-Sabur ka zama jarumin namiji ka taimaki mahaifiyarka da kanwarka. Gata daya zaka yiwa kanka a duniya shi ne ka yi karatu, ka shiga makaranta ka dage ka yo karatu duk runtsi, sannan rayuwarka zata yi haske. Ya damko kudi daga aljihunsa ya mika min, sauran abokansa ma suka bani kudi mai auki kuwa, suna tafiya ban shiga gida ba, sai na je na kama hannun kanwata. Na ce da ita, ''Zo muje nu shiga makarantar boko. Da rana tsaka head master makarantar gwamnati ta unguwarmu ya ganni a cikin ofishinsa. Na yi masa bayani ya fahimce ni amma bai gamsu ba har sai ya ga manya na, ya ce na je na taho da wani babba. Na je na sami Malam Barau na shaida masa, sai ya yi dariya ya ce, kada na bata lokacina wajen yin boko, na tafi kasuwa kawai. Na fito na je na sami mahaifiyata na ce, ta zo ana nemanta a makarantar boko. Sai ta yi mamaki da jin haka, ta hau rawar jiki ta dafe kirji ta tambaye ni ko lafiya. Na shaida mata lafiya kalau, Khausar ma na can a ofishin shugaban makaranta shi ya ce na kira babba. Sai ta gigice ta dauka laifi ta yi, ta hau karkarwar jiki muka dunguma muka je. Da muka isa sai ta tambaye shi ko lafiya, me muka yi? Sai shugaban makarantar ya yi mamaki da jin kalaman mahaifiyata, amma sai ya yi mata bayanin abin da na zo da shi. Ta girgiza kai ta ce, ''Ba ni na turo su ba, ba ni da kudin da zan iya saka su a makarantar boko. Shugaban makarantar ya ce, ''Ah babu abinda za ki biya makarantar gwamnati ce, sai kayan makaranta da litattafai, wasu littattafan ma ana basu a makarantar. Ta ce, ''Ba ni da kudin siyen kayan makarantar ma, idan ma ya fara zuwa makarantar waye zai je ya yi dako ya samo mana abin da zamu ci? Ai shi ne mai fita nema dan haka ba ma son karatun. Na fito da kudi daga aljihuna na ce, ''Ina da kudi, Baba Mukhtar ne ya ba ni suka ce na shiga makarantar boko shi ne kadai zan yi wa kaina gata. Shugaban makarantar ya yi farin ciki dajin haka. Ya ce, ''Wannan haka yake yaro, ka daure ka yi karatu. Hajiya ki barshi ya yi karatu don inganta rayuwarku gaba daya''. Ba ta da ta cewa, sai ta yi min addu'ar Allah Ya sa albarka a karatun da zanyi, sai dai Khausar ce ake ta shawara a kanta, na ce a saka mu a aji daya. Daga makarantar kasuwa muka wuce da Ummanmu Habibah ta yankar mana yadin makaranta, aka kawo wajen tela ta dinka mana, muka fara zuwa makaranta. A aji daya aka sakamu, *yan ajin namu duk yara ne dai-dai Khausar, na fi duk *yan ajin girma a haka dai nake zuwa duk da tsokanar da nake sha a wajen yara wai gardi a cikin yara da dai shauransu. Ban damu ba haka nake zuwa makaranta idan na dawo na tafi kasuwa neman kudi, sana,a kala-kala babu irin wacce bana yi ta karfi. In samo kudi na zo muyi tuwon masara miyar kuka, kullum shine abincin mu. Malam Barau ya yi mana mutunci bama biyan haya a kyauta muke zaune, ya ga babu yadda zamu yi. Nine monita a ajinmu na fi kowa kokari daga ni sai kanwata Khausar ta iya karatu radau a baki, nan da nan ta fara iya rubutu itama kai ka ce daman an taba koya mana a gida. Muna aji uku na firamare Malam Barau ya rasu, ko wata daya bai yi ba iyalansa suka ba mu lokaci mu tashi daga gidansu. Tashin hankali ya same mu, ba mu da mafita sai dai mu koma Gwarzo wajen danginta, duk da bata da uwa da uba tana da *yan uwanta da dakinta na gado duk da na kasa ne. Can muka kaura muka zauna, sai na samu aka yimin cuku-cuku na shiga sakandiren maza ta kwana, na bar Khausar a gida suna ta sana'ar cura fura ita da Ummarmu. Ba laifi talauci ya ragu saboda rayuwar kauye ta fi ta birni sauki, duk inda kaa samu rogo da gyada ka ci na naira biyar sai ka yini kana shan ruwa. Mahaifiyata ta yi wani auren a cikin Gwarzo ta tafi da Khausar ni aka bari a cikin gida wajen dangi yau na kwana a nan gidan, idan an min gori na koma wani gidan. Har na fi so na koma makaranta idan mun yi hutu dan na fi jin dadin makarantar, saboda ina tare da abokaina *ya*yan masu hali dakikai, ni nake ba su amsa su kuma su bani kudi ko biskit da madara. Allah ba Ya hadawa mutum daya komai, ni ya bani kokari Ya hanani dukiya, su Ya yaye musu talauci, Ya dauke kwakwalwar. Mahaifiyata ta haifi *yan biyu a gidan sabon mijinta mace da namiji, Hassan da hussaina. Da ta sami ciki na biyu kuma a garin haihuwa ta sami matsala har ta rasu a garin haihuwa, ta mutu ba ta haifi cikin ba. Muka zamo babu uwa babu uba.... 'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Faduwa da Umaimah suka hada baki suka fada. ''Allah Sarki, Allah Ya jikanta. Inji Umaimah. Faduwa ta rushe da kuka, daga dukkan alamu ta tuna ranar da ta rasa ta ta mahaifiyar ta rasu. Abdul-Sabur ya goge hawaye ya ci gaba da cewa. ''Dangin Baban Hassan da Usaina suka dauke su, ni da kanwata ce abun tausayi. Ina makaranta ina tunanin Khausar saboda na san babu mai kula da ita. Sannan idan na dawo ba jin dadin halin da nake zuwa na iske ba nake ji, abinci a wulakance ake ba ta, haka babu mai kulawa da lafiyarta da tarbiyarta. Ba zan manta ba, muka yi fada da wani dan yayar Ummarmu mai suna Gali, ya yi min gori wai shegu wadanda ba'a san asalin Babansu ba. Tun daga lokacin na kuduri aniyar sai na nemo dangin Mahaifina. Ina aji hudu a sakandire na daina zuwa makaranta na shiga aikin gona sosai, muka sami amfanin gona a gonar Mahaifiyata data bar mana gado, na siyar da abinci buhubuhu na kunshe kudina na boye. Na dawo Kano na sami Yaya Bala babban dan Malam Barau na ce ya kai ni wajen da su Baba Mukhtar suke sauka, abokan Babana. Na ci sa'a kuwa sun zo gari a lokacin, ya kai ni har masaukinsu. Sai suka yi mamaki da ganina, bayan mun gaisa sannan na shaida musu Ummana Habibah ta rasu, sun girgiza da jin haka sun tausayamin gami da yi mata addu'a Allah Ya jikanta da rahama. Na ce musu so nake su kaini wajen dangin Mahaifina a Accra. Sai suka hau kame-kame da alama basa so su kai ni, na ce ni dai ina so na je na gansu. Yadda na fuskanta gudun wahala suke, sun dauki ba ni da kudin mota. Da na nuna musu kudina sai nan da nan suka yarda zan bi Baba Mukhtar dan shine zai tafi kwanakin. Muka ci gaba da hira na shaida masa cewar zan tafi da kanwata Khausar. Ya ce, a,a na ja dai ni kadai tukunna, na ce a'a nafi so naje da kanwata tunda Kakarmu na nan mu zauna tare da ita saboda bamu da kowa a nan. Muka shirya ranar tafiya ya ce na je mu shiryo mu zo mu tafi wani satin. Na ke na sanarwa Khausar, ya amince, sannan muka je muka yi wa dangin Mahaifiyata sallama na ce zan bi wani dan uwan Babana Accra za mu ga dangin Mahaifinmu. Wasu sun amince, wasu basu amince ba, daman ba amincewar su muke nema ba, don babu wanda ya ke tsninana mana komai. Zumuncin yanzu ya zama kamar shuka gyada a bakin kurege. Kawu mai kudi ne Yaya ne ga Umma Habibah Babansu daya ya dage ba zamu ta fi ba saboda ba'a san wanda zamu bi ba yadda duniyar nan ta zama abar tsoro. Sai na je na kirawo Baba Mukhtar ya je har Gwarzo ya yi musu bayani. Sun gamsu ya san Mahaifinmu amma dole aka ce sai an hada mu da wani Babba ya raka mu. Da aka yi shawara sai aka ce Shehune zai raka mu shine mai bin Ummana Habibah a dakinsu, muka dungumo muka taho tare zuwa Kano tashar Unguwa uku, muka wuce kai tsaye, muka hau doguwar motar nan zuwa Lagos da magruba. Ba mu isa Lagos ba sai da sassafe, sallah kadai muka yi muka sayi gayan biredi da ruwa muka ci muka sake shiga wata mota wacce zata kaimu har Accra. Tafiya yankin azaba, mun gaji likis ga yunwa, saboda wahala ta yi ta amai saboda rashin sabon shiga mota da ba ta yi. Ledoji aka yi ta bata tana cikawa ana jefawa ta wundo. Da muka zo bodar Abijan, Immigration suka tsayar da mu suka sa kowa ya firfito suka ce kowa ya fito da passport dinsa. Masu shi suka fito da su, irin su Baba Mukhtar. Mu da ba mu da shi sai hankalinmu ya tashi. Baba Mukhtar ya ce, na kwantar da hankalina dan kudi kawai zamu rike a hannu maimakon Passport sai mu sunna musu cin hanci, sai zance ya wuce. Haka kuwa aka yi, na rike naira hamsin na bawa Khausar da Kawu Shehu suma suka rike, da aka zo kanmu sai muka mika musu kudi, suka karbe aka ce mu koma cikin mota mu zauna, aka ci gaba da tafiya (cin hanci ruwan dare). Haka da muka zo bodar Togo ma immigration suka tsayar da nu irin na bodar Abijan aka yi, naira hamsin ta raba mu da su muka wuce daga nan har cikin Accra babu matsala kuma. GHANA, ACCRA Mun isa Accra daf da magruba muka sauka a tashar Aflawu, daga nan muka dauki tasi muka nufi 'Lagon New town' a in da gidan Kakarmu ya ke. Sunanta Husaina suna kiranta da Ummana Fuse. Da yake ta san labarinmu daga wajen Baba Mukhtar, tana ganin Baba Mukhtar da yara biyi jikinta ya bata mu ne, sai ta fashe da kuka ta rungume mu. Mahaifina kamarsu daya sak da mahaifiyarsa, haka Khausar tayi kama da su sak, bakake ne sannan ba su da tsayi sosai masu dogon hanci. Ni kuwa da mahaifiyata nayi kama, don ita farar bafillatana ce, doguwa ga ido da hanci. Ghana kasa ce da take dauke da kabilu daban-daban, arna sunfi yawa duk inda kaga musulmi Bahaushe, to zuwa ya yi kamar daga Niger ko Nigeria. Manyan yaren kasar guda biyu ne, Ankara da Asanti. *Yan yaren Asanti su ne asalin *yan Ghana sun fitone daga Kumasi, akasarinsu gajeru ne bakake. Ankarawa kuwa farare ne masu bille sunfi *yan kabilar Asanti kyau. Su ma ana tunanin zuwa suka yi shekaru aru-aru da suka wauce. Sunan kudinsu CEDIS wanda ko rabin darajar Naira bai kai ba, idan ka ji ance Cedis 1000 tabbata bai wuce naira 10 ba. Washegari kakarmu Ummana Fuse ta aika aka hado mata *ya*ya da jikokinta ta gabatar damu. Babu tantama kowa ya shaida mu ma *ya*yansa ne, daman can suna da labarinmu. Da bakinsa ya shaida musu cewar ya yi aure a Nigeria har yana da *ya*ya biyu, amma fa sai daf da zai mutu ya fada. Mu ne dai bai fada mana ba yana da wasu matan da yara a can. Gado dai an rabe, daman ba wani abin kirki ya bari ba. Sai suka yi ta zukewa kowa yana gudun wahala aka rasa mai rike mu. Ummana Fuse itace dolenmu don haka wajenta muka zauna. Gida ne a gine ginin sumunti daki biyu da tsakar gida, *ya*yanta suka gina mata a unguwa mai kyau. Bayan wannan kuwa babu wani abu da suke ajiye mata, komai ita ta ke nema ta yiwa kanta. Sana'ar kera tukwane na kasa take yi kuma ba wani kudin kirki ta ke samu a yini. Ta shaida mana cewa a garin nan babu mai zaman banza, kowa fita yake ya nemi abinda zai ci,tun daga safe zuwa dare. Idan ka zauna a gida babu mai baka, haka mata da maza, yara da manya suke yi. Ga su da nuna kabilanci, Hausawa koma na ce Musulmi ba su da karfi a kasar wajen yin mulki ko samun aikin gwamnati. Babu karatu babu aikin gwamnati don haka sana'ar karfice ta wajaba akansu. Ummana Fuse ta sa aka samo min aikin jiran shago a wani kantin dan uwanta da yake kasuwar Art Traditional Tourism inda suke siyar da kayan gargajiya, kamar takalman fata, abin wuya na dutsuna, gangam hula dara, kayan kinta (yadi) da dai sauransu. A nanne zaka ga Turawa daga kasashe daban-daban suna zuwa suna kallo, kuma suna siya. Abinka da Nasara asarar duniya, sun fi sha'awar irin wadannan abubuwan na gargajiya. Ciniki ake yi sosaikullum nake zuwa tun daga safe har zuwa magruba. Cedis dubu biyar yake ba ni kwatankwacin naira dari kudin Nigeria, kasancewar kudin Ghana ba shi da daraja kamar yadda na fada a baya. Cedis dubu biyar din nan abinci kadai nake iya ci na rana da dare, shi ma kuma ba don na koshi ba, kuma babu nama. Dukunu da Tankwa nake ci kullum, shi zai fi kosar da ni, don ya fi arha. Umaimah ta dubo shi, ya ce, ''Meye dukunu da tankwa kuma? Abdul-Sabur ya yi murmushi ya ce, ''Abincin *yan Ghana ke nan. Dukunu shi ne kamar tuwo, tankwa kuwa ita ce miyar da ake ci da shi. Idan aka jika masara ta kwama sai aje a markado sai a dan dafa ya yi kauri shi ke nan sai a ci da tankwa. Tankwa kuwa kayan miya ne da attaruhu, albasa da tumatir ake murjewa a asanka. Kanwata Khausar kuwa a kasuwar Agulgoshi aka kai ta nan ce kasuwar da ake siyar da danyen kaya buhu-buhu, ana saukewa daga mota-mota. Shagon wata mata mai suna Hajiya Momi tana sayr da bainci, Khausar ta ke taya ta dafawa da siyarwa. Suna siyar da shinkafa da miya, Dukunu, muri da Algilma, su yi miyar gyada ko miyar kwakwa. Idan kuna neman muguwar mata aka samu Hajiya Momi to aja layi a tsaya, saboda bata da tausayi ta wahalar da kanwata Khausar, ba kudi ta ke ba ta ba, abincin rana da na dare ne kawai ta ke ci ta koshi. Sai shegen fada da duka kullun ta ke yi mata bayan aikin da ya fi karfinta, da ta ke jifga mata. Idan ku kaga daron da ta ke dauka a kanta ta kai markadem kayan miya da markaden masarar yin Dukunu sai kun tausaya mata duk da dai ba wani nisa ne ke da akwai ba tsakanin inda suke kasuwancin da gurin kai markaden. Gashin tsakiyar kanta har saisayewa ya ke yi saboda daukar kaya. Idan abinci ya yi kwantai akai zata dora mata ta yi zagayawa gari sai ta siyar. MAKWABTAKA 15 Khausar kullum tana kuka da zarar gari ya waye saboda fargabar wahalar da zata je ta tarar a kasuwa. Ni da kakata abin nan ya fara isarmu ita ba kudi ta ke kawo mana ba, don ba ta biyanta komai. Da kakata ta yiwa Hajiya Momi magana akan ta rangwanta mata wahala, ta kuma dinga biynata kudi, sai ta ce sai dai idan ta daina aikin saboda abincin da ta ke ci ma ai na kudi ne, mai yawa. Dole muka bar Khausar ta ci gaba da yi don idan ba ta yi ba wa zai ba ta abinci ta ci, kowa yana ta kansa? Ana cikin wannan hali ne sai Allah Ya kawo wani kawunmu Hamza koma in ce Kakanmu don shine auta a dakin su Ummana Fuse. Ya fi shekara ashirin a England, ya auri baturiya ya haifi yaransa Turawa guda uku, Babban namijin ne zaiyi sa'ana sauran kuma dukka mata, sai a lokacin ya fara kawo su kasarsa. Da Uncle Hamza ya zo gidan Ummana Fuse ya ganmu sai ya tambaye ta mu su waye? Sai ta zauna ta bashi tarihinmu kakaf. Sai ya tausaya mana daman ya ji labarin rasuwar Babanmu ta waya. Ya tambaya yanzu me muke yi karatu ko aiki? Ummana Fuse ta fada masa cewar ni ina tsare kanti, Khausar tana siyarwa wata abinci a kasuwa. Ya tambaye ni nawa ake biyanmu, na koro masa bayanin cewa babu abin da muke samu banda abinci, sai ya girgiza kai. Ya ce, ''A'a wannan ba sana'a ba ce, gara mu koma makaranta. Kamar yadda na fada muku a baya ana nunawa Hausawa, Musulmai kabilanci. Ba a bari suyi karatu, idan sun kutsa sunyi karatun ma babu aikin gwamnati. Ya ce kafin

Chapter 7 of 33