Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dauki dana na tafi jikina a sanyaye ina ta hawaye ina jin bakin cikin wulakancin da ya tarki yi min, da kyar nake tafiya ga ciki ga goyo, nauyi jikit. Na fara jin alamun nakuda dan lokacin haihuwar ya cika. Na wuce gidan Zulayha Senegal na iske ta tana ta caba ado sai na ga ta yi min kallon banza. Na gaishe ta, na shaida mata na kawo mata Bilal ta rike min zan je unguwar Dosa yanzu zan dawo, zan dauko mai aiki.... Ban rufe bakina ba ta ce, ''dauki danki ki tafi da shi, nima unguwa zan je. Na fice a sanyaye na nufi titi na tare dan acaba na hau. Banda kuka babu abin da nake yi. A gaban mai babur aka saka Bilal duk da ya yi kankanta a zaunar da shi a nan babu yadda zan yi, tsinin cikina bazai bari na zaunar da shi a gaba na ba, haka ba zan iya yin goyo ba. A lokacin ana taron siyasa a garin, kowanne titi a garin Kaduna motoci ne (go slow). Don haka sai muyi mintuna talatin akan titi daya kafin mu matsa gaba. Kwatsam ina kan babur a cikin rana ni da dana, da mai acaba mun galabaita. Juyawar nan da zan yi, sai na ga galleliyar motar Zulayha a gefena, koda na sake wurga ido itace a gefe namiji ne yake tukawa. Sun yi luf a cikin AC babu ruwansu da kura, zafi, balle hayakin *yan acaba, dariya suke yi suna hira da shewa, har da tafawa da hannu. Ko da na dubi mai tukawar sai na ga AbdulBasi ne. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Na dinga fada a bayyane, yayin da dan acaban ya gigice, ya fara tambayata ko lafiya? Na barke da kuka, yayin da jikina ya dau karkarwa cewa nake, ''Ga miji na can da MAKWABCIYATA suna cin amanata. Zulayha ce ta fara ganina, muka hada ido, sai ta zunguro Abdul-Basi ta nuna ni ga mu nan a kusa da su, muna daf da su. Sai jikinsu ya yi sanyi suka kasa hada ido da ni. Mun jima kafin a bada hannu, su ka ja da gudu suka tafi suka bar mu a baya muna gurgurwa. Na ga masifa a ranar, na ji kamar na hadiyi zuciya na mutu. Dan acaban ya yi ta yimin nasiha yana bani hakuri, suna gabana ina hango motarsu, hanyar kawo suka yi da alama garin ma zasu bari gaba daya. Gudu muke yi kawai a hanya, to ni dai ban san me ya faru ba, sai na ji mu gijif! Mun watse a titi, mun yi karo da wani babur din mun fadi. Na fadi a kan cikin nawa, yayin da dana Bilal aka cilla shi a gefen titi ya fadi. Ya kurje a fuska da kafafuwa, ni ma fuskata, gwiwoyin hannu da kafafuwana duk jini. Dan acabar ya karye, ya yin da daya mai acabar ya suma. Nan dai na mike tsaye wuriwuri ban damu da ciwon da yake jikina ba, dana kawai na ke nema. A can gefe aka tsinto min shi, jini gaje-gaje na rushe da kuka na rungumeshi.... Umaimah ta fashe da kuka, yayin da tausayinta ya lullube zuciyoyin wadanda ta ke ba wa labarin. Faduwa ta ce, ''Sannu *yar uwata, ashe kin sha wuya ke ma? Umaimah ta nisa ta sa toilet paper ta share hawaye, ta ci gaba da cewa. ''Alhamdu lillah a kowanne hali nake, sai aka fasa tafiyar unguwar Dosa, aka kawo motar asibiti (ambulance) aka zuba mu a ciki, an sace min jakata, waya ta na hango akan titi har wani ya dauke na karbi abuna. Wayar Abdul-Basi nake ta yiwa flashing don ba ni da kudi a wayar, amma ya ki kira na. Na yi flashin fiye da sau goma ina so na sanar masa mun yi hatsari, muna asibiti ya ki kira na, da na dame shi ma ya kashe wayarsa. Su Bara'atu na yiwa flashing suka kira ni na sanar musu halin da nake ciki, na fada musu sunan asibitin. Suka gigice ba jimawa kuwa sai gata da Haj. Bishra sun zo, ni dai ta dana nake yi, ban damu da kaina ba. Babu dinki a raunin sai dai aka wanke ciwukan aka saka mana auduga da iodine. Mun sha zafi, aka ba mu allurai da magunguna duk kyauta. Sai aka zo maganar dan cikina suka ce ya bugu, amma na koma asibitin da nake awo na ga likita ya yi sauri a fitar da jaririn. Bara'atu da Haj. Bishra na sa su tsayar mana da me tasi, muka hau muka kama hanyar gida. Fadi suke, ''Umaimah ma tafi gida kuwa ba asibitin da kike awo ba zamu je? Saboda maganar dan cikin nan naki. Ki kira mai gidan ki fada masa halin da kike ciki mana. Sai suka ga na barke da kuka, suka gigice ainun, suna tambaya ta, da kyar na iya fada musu abin da idanuwana suka hango min, wato Zulayhat Senegal da mijina Abdul-Basi a mota suna tafe suna hira da shewa. Sai na ga sun hada ido sun sunkuyar da kai kasa, da alama dai sun san komai, don na ga ba su yi mamaki ba. Bara'atu ta fara magana, sai Aunty Bishra ta dinga zungurarta, wai ta yi shiru. Na ce, ''Au daman har da abin da zaku iya boyemin? Me kuwa za ku boye min bayan na gani da idona? Sai Bara'atu ta gyara zama ta dinga ba ni labarin abubuwan da suke faruwa wanda ban san da su ba. Tun ina fahimtarta har na gigice na fita daga hayyacina, na dora hannu aka na mimmike a cikin tasi kamar wacce zata sume. Ga ciwo a fuskata, ga kuka ina yi, ga dana yana nasa kukan saboda azabar ciwo... Faduwa ta ce, ''Me suka fada miki? Umaimah ta goge hawaye, ta ce, ''Labarin dawowar da yake yi da wuri ya shige gidanta ya ci abinci, ko ya dauketa suje restaurant su ci. Da yadda ta ke zuwa ofis dinsa daga dukkan alamu kuma suna neman juna. Yanzu haka wannan fitar da suka yi garin su Zulay zasu je Zariya maganar aurensu, ni ban sani ba,,,,, Abdul-Sabur ya ce ''Allah Sarki, da kin yi hakuri kin zauna da ita. Me ye kishiya? Ko wacce ta zauna da halinta. Umaimah ta tabe baki ta ce, ''Ban ki zama da ita ba ita ta fitar da ni dole, Ya zan yi tunda an kore ni? Faduwa ta ce, ''Ya aka yi da cikin a ranar? Umaimah ta sake goge hawaye, ta ce, ''Ba muje asibitin ba, gida na je na kwanta ni da dana, MAKWABTA suna jinyarmu. Su AbdulBasi ba su dawo ba sai karfe goma sha daya na dare. Ya shigo yana bata rai don kada ma na yi masa maganar dazu. Sai ya tsorata da yaga ciwon jikinmu, ya shiga karkarwa. Ban iya yi masa magana ba sai Bara'atu ce ta ba shi labari. Ya fito da makulli ya kinkimi Bilal ya ce, ta kamo ni mu je asibiti a sake bincikarmu musamman ma dan cikin. Haushinsa kawai na ke ji, muka duru a mota har da Bara'atu muka je. Muna isa saiga Zulayha ita ma ta biyo mu a motarta, ban san wanda ya fada mata ba ma. A gigice ta hau kissa da kisisina, wai ita tausayi. Likita yayi scanning a cikina ya ce, ''Baby ta mutu a ciki, za su ba ni gado zuwa gobe a yi tiyata. Cikin dare nakuda ta taso da kaina na haifi *ya ta fara jawur mai kyan gaske, amma ba ta da rai. Kwanana uku a asibiti a kwance, abin takaici Zulayha ce a kaina ita ya barwa kudin komai, tunda shi yana ofis sai dare yake zuwa su tafi gida tare, sun daina boyemin komai ma a gabana ake hirar soyayya, wasa da dariya. Abincinta nake ci, haka dana a hannunta yake kacokan ita ke kula da shi. Na yi kuka, na sha takaici, ba yadda zan yi sai kallo da ido. Bara'atu na sake dora min da wasu bayanan ma da ban sani ba, ashe an dade ana cin amanata. Su ma MAKWABTAn abin da suke takaici ta girme shi, ya fi ta kyau, ya fi ta ilimi ba ajinsa ba ce. Me zai yi da tsohuwar *yar duniya? Kanta har da farar fufura, shi da yake da mata kamar ni fara, yarinya mai kyau da ilimi? Amsar ita ce ta fini iya duniyanci, bariki zalla, wayo, iya tattali da rashin kunya, sai kuma asirai da ta dogara da shi, ta haka ya fara sonta. Aka sallamo ni na dawo gida zan karbi dana sai ta hana ni, wai na bari sai na gama jego tukun na ita zata kular min da shi. Tsabar kissa ce da son jan ra'ayin Abdul-Basi ba don Allah ba ne, na hakura na bar sa. Ta goya shi ta sauke, ta yi masa rawa, ta kai shi kantina siyayya kalakala. Uban kuma sai ya yi ta jin dadi. Wata asabar suka shirya a motarta shi da ita suka tafi Gombe wajen mahaifansa, zai gabatar da ita a matsayin amaryar da zai aura. Kudin cefane kawai ya wurgo min kan cinyata, ya ce mu mun tafi Gombe sai goben za mu dawo. Na san da ita za su tafi, na daure ban tambaye shi ba balle na yi korafi, ya samu damar yi min rashin mutunci. Ya kada kai ya fice da jakar kayansa. Na tafi wundo da gudu ina lekensa, na ga ya shige gidanta fiye da mintuna ashirin, sannan suka fito a tare, ashe shaddar jikinsu iri daya ce. Ita ta dinko musu daga Senegal sun yi kyau, sai kamshi suke yi. Ina saka ran za su miko min dana kafin su wuce, sai na ga har da shi da kayansa suka shige mota, an yi masa kwalliya shi ma. Na manta rabon da na ga dariyar Abdul-Basi amma tunda suka shiga mota suka fara hira da dariya, har da kyakyatawa. Na sake bin daya wundon da gudu don na ga fatarsu daga get, to ko na gani ma ba komai zai kara min ba banda tsabagen takaici da kunar zuci. Suna tafiya na sulale na zauna na dora hannu aka na surnano da wasu zazzafan hawaye mai radadin fita. Kafin hawayen ya diro kasa sai na ga Haj. Bishra a tsaye a gabana, na yi sauri na goge hawayena ina kokarin wayancewa. Sai ta ce, ''Kada ma ki bata hawayenki *yata, ki kwantar da hankalinki, ki saka musu ido kawai, komai ya yi farko zai yi karshe. Da yarinta jikinki shi yasa kike amincewa kowa alhali ana cutar da ke. Ba Zulayha kadai ba, duk wasu da kike mu'amala da su a gidan nan sai kin yi takatsan-tsan, kuma kin rufe bakinki, kin boye sirrinki. Ba ta fada min ba dai baro-baro saboda gudun haddasa husuma a matsayinta na babba, amma tabbas na san akwai wata magana a kasa. Sai ta tashe ni tsaye ta zaunar da ni akan kujera ta ci gaba da yi min nasihohi masu kwantar da hankali, sai na ji dan sanyi a raina. Na yi mata godiya ta tafi na kasa cin abinci, shi ya sa ban dafa ba. Daga lemo da biskit sai ruwa na yi ta sha, a lokacin ina da kiba tunda na yi wannan ramar har yau ban mayar da jikina ba. Da na tuna da son da Alhaji surukina ya ke yi min, sai ban damu ba nasan da kyar zai amince ya bar Abdul-Basi ya yi wannan auren. Mahaifiyarsa ce dai na ke zaton zata amince, don duk abin da *ya*yanta suke so shi ta ke so, ba ta hana su. Na dukufa ina ta addu'a ina kuka akan Allah Ya dawo da hankalin mijina kaina, don na ga ba ya sona yanzu. Bara'atu kawata, makwabciyata ta shigo gidan da yamma da sababbin gulma, ita ba kwantar min da hankali ta zo ta yi ba, irin na Haj. Bishra, sai ma tayar min da hankali ta sake yi. Mijinta ne yake sanar mata da komai, duk hirar da suke yi da Abdul-Basi akan Zulayha. Wai shi Zulayha ta fiye masa ni, gara ya auri babba mai hankali wacce ta san tattalin miji ba irina ba, raino kadai yake yi. Ni ma na saki baki na yi ta fada mata irin wulakancin da yake yi min, Allah Sarki! Kuruciya dangin hauka. Ba su dawo ba sai washegari lahadi, da daddare ya dawo gida bai yi min bayanin komai ba ya shige dakinsa ya kwanta kamar yadda ya saba, ya raba daki da ni yanzu. Da sassafe ya fice wajen aiki ko kudin cefane bai bani ba, ina sallah na ji fitarsa. Misalin karfe goma da rabi na safe na ci kuka na gaji, na fito barandar waje na tsaya ina mai kallon gidan Zulayha, sai kawai na yi ido hudu da Babangida dan gidan Yayata a zaune akan kujera, dana Bilal akan cinyarsa. Yana ganina ya zabura ya ce, ''Aunty Umaimah''. Bilal ma ya hau tsalle da murna da ganina. Na yi matukar razana da ganin Babangida, na dafe kirji na ce, ''Lah yaushe ka zo? Ya ce, ''Ni da Abba muka zo jiya, ai na dawo Kano gaba daya za'a saka ni a makaranta a nan. Anti Zulayha ta ce min ba kya nan ni daman a wajenki zan zauna'' Sai ya mike da sauri ya ajiye Bilal yana shirin ya zagayo wajena. Sai na ce, ''Ka taho da Bilal shi ma. Ya dauko shi suka taho, a falo na jiyo muryarta ta ce, ya koma ya zauna babu inda za su je. Sai na ji shiru ba su zagayo ba. Na fusata ainun na kwalla kiran sunansa, amma kiri-kiri matar nan ta hana shi amsawa. Ban dauki gyalena ba sai na fita na shiga gidan haka nan. Na iske su a zaune a gabanta sun yi tsuru-tsuru, kana ganinsu kasan a takure suke. Ita kadai ce a gidan yaranta duk sun tafi makaranta. Na yi sallama sam ba ta amsa min ba, na wuce kai tsaye na dauki Bilal na kama hannun Babangida na ja, ai kuwa sai ta rike shi ta ja. Ta ce, ''Ki tafi da danki, wannan dai ba ke kika haifa ba, kuma ba ke kika ba ni ba, Kakarsa ce ta ba ni da ubansa, don haka sai a bar min dana. Na auna mata harara, na ce, ''Kin manta wace ce ta haife shi? Idan kin manta ki tuna, dana ne, dan yayata ne uwa daya uba daya, don haka ni na fi cancanta na rike shi ba ke ba. Sai ta sake shi ta gyada kai, ta ce, ''dauke su ki tafi da su, na ji *ya*yanki ne amma ki sani daukar *ya*yan nan da kika yi daga wajena zai zai janyo miki bacin ran da za ki dauwama da shi bai gushe ba. Ni Haj. Zulayha ba a ja da ni, yaro bai san wuta ba sai ya dafa ta. Idan kin san wata ba ki san wata ba, da sannu za ki banbance zuma da madaci. Na sake auna mata harara na ce, ''Allah Ya fi ki ai, duk abin da ya same ni daga Allah ne ba dai mutum ba. Ta rike baki tana mamaki, sai ta gyada kai, ta ce, ''Au har kin yi baki? Kin yi wayon yi min rashin kunya? Tabbas sai na zame miki duhu a cikin rayuwarki, sai kin yi dana-sani da ba ki zage ni ba. Na ja wani dogon tsaki ba tare da na tanka mata ba, na fice da *ya*yana muka shiga gidana. Sai na ji sanyin kasurgumin bacin ran da nake ciki da na ganni da yarana suna taya ni hira. Amma ina mai tsananin mamaki da takaicin kawo Babangida a dalilin Zulayha ba a dalilina ba. Babu irin magiyar da ban yiwa Abdul-Basi ba tun farkon aurenmu ya dawo da Babangida wajena, amma fur! Ya ki sai ga shi yanzu ya dauko shi tun kafin ma ya aure ta ya damka mata shi. Na san halin kissa da kisisinar Zulayha ta yi musu dadin baki ne shi yasa suke ganin ita zata iya rike su alhalin nan gaba wahalar da su zata yi. Na san zata fadawa Abdul-Basi zai yi fushi da ni amma ban zaci har zai yanke min irin wannan hukuncin ba.... Sai ta dafe kai ta surnano da hawaye. Faduwa ta dafe kirji, ta ce, ''Ba dai dukanki ya yi ba akan haka? Kafin ta amsa Abdul-Sabur ya amshe da cewa. ''Ba dai saki ya baki ba? Umaimah ta sharce hawaye mai hade da majina, ''Ina fita tayi masa waya wajen azahar sai ga shi a gida. Na yi mamaki da ganinsa daidai wannan lokacin. A fusace ya fado mana cikin falon, muna cin abinci. A gigice muka mike don tsorata, ya daka min tsawa ya tambaye ni. ''Me ya kai ki gidan Zulayha kika zage ta? Na ce, ''Ban zage ta ba, ni karya ta ke yi min'' Ya dakamin tsawa, ya fada cike da fusata, ''Ita ta ke yi miki karya? Sa'ar ki ce? Daman ta ce kin zama fitsararriya, don haka ki kwashi yaran nan ki mayar da su, amma ki durkusa ki ba ta hakuri kada ki sake shiga gidanta. Na tambaye shi har Bilal din ma a wajenta zai zauna? Ba saboda rashin lafiya ba ne aka ba ta ba, yanzu kuwa ai na warke ni zan rike dana. Sai na ji ya kwashe ni da mari dau! Na durkushe na rike kunci. Ya fada cikin kakkausar murya. ''Daga yau idan ina magana kina yi sai na saba miki. Banza! Ballagaza, saunar mata. Yaushe aka gama rainonki da zaki iya rainon wasu? Yaushe kika gama sanin ciwon kanki balle ki san ciwon wani? To tunda bakyajin maganata ki shirya kayanki gobe na saki a mota ki koma Dugge can ki zauna a gidanku, sai ki yi musu fitsarar a kauye, ba a nan ba. Dama tsiyar bakauye ke nan, ya zo birni ya sha jar miya ya nuna maka ya fi ka iya tafiya a kan tiles. Na ji kamar almara, na kasa kuka, na kasa magana. Ya ja hannun yaran suna ta tsala kuka, har da ihu ya kai su wajen Zulayha, sannan ya shiga motarsa ya koma ofis. Sai a lokacin na fara rusa kuka ni kadai a daki, amma na tsorata da maganar kora ta da ya yi, na san tonan asirina ya zo idan ya sake ni na koma Ruga da zama. Har dare jikina rawa ya ke yi, ina ta addu'ar Allah Ya huci zuciyarsa kada ya dawo da fushi ya sake ni. Ya dawo tunda magruba, na ga tsayuwar motarsa amma ba gidana ya shigo ba, gidan Zulayha ya shiga inda ya ci lafiyayyen abincin da ta dafa masa. Ni kuwa da yake bai bar min kudin abinci ba, sai na dafa shinkafa da wake da mai da yaji, dan na ga yana sonsa. Na kakkalato kudi na aika aka siyo min salad da tumatir da *yar albasa na yayyanka masa don na burge shi. Bai shigo gidan ba sai sha dayan dare. Na durkusa na gaishe shi ya yi banza da ni kamar bai san da wanzuwata a gurin ba, na yunkura zan je na dauko abinci, sai ya ce dawo nan, bana son abincinki munafuka. Na tsorata da jin wannan kalma da ta fito daga bakinsa. Na dawo na durkusa, sai ya fara zayyano min maganganu kalakala na tsakani na da shi, amma ya ji maganar nan a waje a ofis ma aka fada masa. Sai jikina ya hau rawa na ce, ''Ni ban fadawa kowa ba. Ya daka min tsawa ya ce, ''Ki fada min da wacce ku ke hira a gidan nan idan bani nan, ko kuma yanzu na yi kasa-kasa da ke, bakar makira kina tafiya a sum-sumke, amma sai tsabar bakin munafurci da tozarci. Can na tuno aminiyata Bara'atu ce kadai nake irin wannan hirar da ita. Sai na ce, ''Na san dai mu kan yi hira da Bara'atu. Ya ce, ''To zamana da ke ya kare tunda ba kya iya boyemin sirrina. Bara'atu kike fadawa ita kuma ta ke kwashewa ta fadawa mijinta, shi kuma ya je ofis yana yadawa ga abokan aikinmu. Na yi ta ba shi hakuri, na ce, ''Ba zan kara ba. Ya yi banza da ni, ya shiga daki sai ya fito min da farar takarda mai kunshe da bakin sako. Na bude na karanta tun a gabansa, saki daya ya rubuta min, wanda tunda nake a rayuwata ban taba jin tashin hankali ba sai irin na ranar. Allah Ya sa ban manta ambaton innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ba. Na yi ta fada ina mai-maitawa kamar yadda malamin islamiyyarmu ya ce mu dinga yi da zarar mun hadu da bala'i. Ya damke gashina ya kai ni dakina ya ce, na fara hada kayana gobe da safe zai saka ni a mota na tafi garinmu. Ina makyarkyata ina hada kayana a lokacin na nemi hawaye na rasa, saboda masifa ta yi masifa, tashin hankalina rabuwa da karamin dana Bilal ga Babamgida da aka dauko shi daga gidan tarbiyya, wajen rufin asiri aka kawo shi wajen wahala, inda za a iya gurbata masa tarbiyya, shi ma zan fi so da an bar shi a Gombe ya fi komai a gare ni. Yana ta zagina ta uwa ta uba, yana ambaton albasa ba ta yi halin ruwa ba, ban yi halin Nasiba ba, ba don albarkacin Nasiba ba ai da tuni ya sake ni. Alhali na fi yi masa biyayya ma akan Nasiba, na fi ta wayewa da sanin tattalin miji... Abdul-Sabur ya kumbura ya yi suntum kai ka ce Abdul-Basi ne a gabansa, ko Zulayha sai harare-harare yake zuciyar nan na ta tafasa don takaici. Faduwa kuwa sai girgiza kai ta ke, kira ta ke, ''Lahaula wala kuwwata illah billah. Umaimah ta zubo da hawayen takaici, ta ce, ''Na kwana ban runtsa ba a zaune, ina ta sake-saken inda zan nufa don ba zan iya zama a tsakiyar Matawata da Ilah ba, ga gulmar gari, ga tsangwamar matan uba, ga talauci da rashin lafiyar mahaifina babu kudin magani. Daman Abdul-Basi ne mai siya ya aika masa, ni ma na tara dan kudi na kunshe idan na je na ba shi, yanzu duk babu mai ba mu. Gari ya waye na tashi na yi wanka na yi sallah tun da asubah. Sai da na jima da kimtsawa sannan na ji Abdul-Basi ya shiga wanka, misalin karfe shida da rabi, bakar abaya na saka a jikina sai na zindimo bakin hijabi na fice da sauri na nufi gidan Bara'atu zuciyata tana ta tafasa. Ba su bude gida ba ma ni na kwankwasa, na san sun tashi tunda mijinta ma Ma'aikacin Banki ne. Ta yi mamaki da ganina, gami da hawaye face-face a idona. ''Lafiya Umaimah? Ta tambaye ni a dan duburce Na ce, ''Na zo ne na yi miki sallama na kuma yi miki godiya. Na ji abin da duk kika fadawa mijinki shi kuma ya je ya yada a ofis har Abdul-Basi ya zo ya sake ni a dalilin haka. Amma wallahi Bara'atu kin ba ni mamaki, ban taba tunanin MAKWABTAKA takan iya komawa cuta ba. Yanzu duk yadda na dauke ki a gurina ki rasa abin da zaki saka min da shi, sai ki kwashe duk maganar da muka yi da ke ki fadawa mijinki, shi kuma don rashin lissafi kamar shi namiji wai ya buge da kwasar maganar mata yana kaiwa gurin aiki. Sai ta hau fada da daga murya don mijinta ya ji ya fito. Ta na cewa, ''Kamar yaya, me kike nufi? Ni da mijina munafukai ne ke nan? To mun fada din ke dai kawai kishi ne ya dame ki za a auro miki wayayyiya *yar birni, kin tsorata za ki gudu, amma mu ina ruwanmu? Idan ma na fada ni na gayyatoki kizo ki fada min? Surutai dai da cin mutunci ya yi ta fitowa daga bakin Bara'atu, na yi kasake ina kallonta cike da tsananin mamaki, makwabciyar da na amincewa ce yau ta ke min wannan tonan sililin.MAKWABTAKA 20 Na tuno cin amanar da Matawata ma ta yi min na hado da cin amanar da Zulayha ta yi min, sai na ji a raina na tsani duk wani MAKWABCINA. Na kudira a raina har abada ko gaisuwa babu tsakanina da MAKWABTANA, haka na dai na ba da hakkin MAKWABTAKA.. Umaimah ta fashe da kuka mai cin rai. Abdul-Sabur ya yi doguwar ajiyar zuciya, ya gyara zama ya ce, ''Ke wanne sirrinsa ne kika barbaza a waje wanda ya ba shi haushi haka har da saki? Kin san fa maza ba sa son kananan maganganu irin na mata, amma shi ma ai duk wannan bai kai ga saki ba. Umaimah ta ci gaba da kuka, abin da kuwa ba ta sani ba, kukanta yana tayar da hankali ga duk mai raunin zuciya. Sai suka shiga rarrashinta suna mika mata toilet paper tana ta sharcewa. Sai can ta nisa ta ci gaba da magana, ''Allah Sarki kuruciya mai dadi, rashin sani ya fi dare duhu. Ba wani abu na fada ba wanda ya wuce hirar da nake ba ku yanzu. Hirar garinmu na ba ta, ta kuruciyarmu da waken dandali. Da hirar yanda Abdul-Basi ya hadu da yayata Nasiba har aka yi aure, dawowata wajensu da zamana a wajensu, da shiga makaranta. Don ita bata san Nasiba ba a lokacin ba a yi mata aure ba, ba sa gidan, wadan da suka zauna da Nasiba sun bar gidan. Kuma da bakinta ta tambaye ni wai wacece Nasiba da ta ke jin su Haj. Bishra suna ta maganarta, wai an ce yayata ce? Shi ne na bata labari, na hada mata da labarina da Ilah da Matawata sai kuma labarinsa da Zulayha a lokacin da maganar cin amanar da ake yi min ban sani ba. Ita ma Bara'atun ta ke karamin da abubuwan da idanuwanta suka gani, ko wanda mijinta ya jiyo a ofis ya fada mata. To amma ka san magana idan ta zamana ta koma ta gulma, to yadda za'a jujjuya ta sai ka ji ba iri daya ba ce da yadda ta ke tun fil'azal. Yadda Kamal mijim Bara'atu ya je yake fada a ofis cewa ya yi, Abdul-Basi dan birni ne, dan masu kudi da sarauta a Gombe, amma saboda neman kyau ya shiga Ruga ya auro mai tallar nono Nasiba Yayata ke nan, wai don ta haifa masa kyawawan *ya*ya. Da ta rasu ya koma nacewa kanwar bayan shi ya rike ta ya ce sai ya aure ta, ba ta sonsa, tana ta wulakanta shi ya yi ta cusa kudi aka raba ta da saurayinta da ta ke matukar so mai suna Ilah, ta zo gidan ba ta sonsa. To burinsa ya cika ya sami fararen *ya*ya, amma fa duk maza ne ya fi son *ya mace don ta kawo masa jari. Kun ji yadda aka juya zancen, kuma dai shi ma ya tsane ni ya fasa zama da ni akan Zulayha shi ne ya sa ya yi saki, amma ba don maganar nan kadai ba. Faduwa ta gyada kai, ta ce, ''Tabbas haka ne, nima abin da zan fada kenan kika riga ni. Abdul-sabur ya kurbi lemo ya ce, ''Haka ya ke yanzu na fuskanci maganar. Ya dai so ya sake ki ne ya rasa dalili, kuma ba ya so ace ya sake ki a dalilin zai yi aure. Umaimah ta langwabe kai gefe, ta ce, ''Sai na ji Kamal yana magana da Abdul-Basi a waya, wai ya zo gidansa ya fitar da ni ga shi nan na zo gidansa ina ta takalar matarsa da fada. To shi ba ya son tashin hankali, ya za a yi na zo gidansa na tayar musu da hankali da sassafen nan? Sai na ji muryar Abdul-Basi yana kwalla min kira a bakin matattakalar gidan. Na fito da sauri jikina yana rawa. Bayanai nake yi masa cewar ni ba fada na zo na yi da ita ba, sallama zan yi mata. Ai kuwa ban rufe bakina ba na ji ya rufe ni da duka ta ko'ina, yana zagi yana jana ya wurga ni a cikin mota. Da gudu MAKWABTA suka kawo min agaji, amma ina! Har ya kulle ni a mota. Haj. Bishra har da hawayenta ta shiga yi masa fada tana cewa, ''Haba AbdulBasi kashe yarinyar na kake so ka yi bayan cin amana da cin mutuncin da Zulayha take mata a gidan nan tana hakuri, kuma har da duka da zagi? Sai ya balbale ta da rashin kunya, wai babu ruwanta da iyalansa. Ina daga cikin mota na bude mata takardar sakin da ke kunshe a cikin rigata. Ta gilas ta karanta, sai ta fashe da kuka ta shiga gida. Kalmar karshe da ta fada kafin ta tafi ita ce, ''Ki yi hakuri Allah Zai musanya miki da miji mafi aikhairi. ''Insha Allah''. Inji Abdul-Sabur. Faduwa ta ce, ''Kayanki fa, ya bari kin koma kin dauko? Ta ce, ''Eh, gidan amaryarsa ya shiga ko in ce farkarsa don ba a yi auren ba suke holewarsu. Ta lalata shi, salihin mutum ne Abdul-Basi, ban taba jinsa da neman mata ba, amma sai ga shi kowa ya san abin da suke aikatawa da Zulayha Senegal. Yana shiga na bude kofar da gudu na hau samana Allah Ya sa bai kulle ba na jawo katuwar akwatina da na shirya ta tun cikin dare na ratayo jakata mai dauke da tarkacen kayan kwalliyata na fito, har nazo matattakala zan sauka na tuna takarduna na firamare da sakandire, da na diploma da na yi akan na'ura mai kwakwalwa (computer) suna cikin akwatin da yake ajiye muhimman takardunsa na garzaya da gudu na dauko a cikin ambulan na cusa su a cikin riga don idan ya gani zai kwace tunda ya yi niyyar yin mugunta, baya son ci gabana. Ina saukowa sai na ji an ambaci sunana, wata *yar karamar murya daga kan barandar Zulayha. Na daga kai da sauri sai na ga Bilal dina ne ya tashi daga barci daga shi sai pampers. Yana murna yana tsalle yana fadin, ''Ga Umma'' Sai Babangida ya fito da gudu ya ce, ''Aunty Umaimah ina za ki je na ga kin dauko akwati?

Chapter 12 of 33