Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Kar ki tafi ki bar mu, ni ma zan bi ki Gomben. Sai ta fashe da kuka cikin rurin kukan ta ci gaba da magana, ta ce, ''Sai na daga ido na dube su na yi musu addu'a, na ce ''Allah Ya kare ku, Ya raya ku na ba wa Allah amanarku. Na ja akwatina da sauri na tafi, suna ganin na tafi sai suka fashe da kuka suna kiran sunana. Na tsugunna a bakin motar Abdul-Basi na toshe kunnuwana da hannayena biyu saboda sautin kukansu tamkar darmar wuta ake caka min a dodon kunnena.... Kuka ya ci karfinta sosai, yayin da ta kifa kai akan dinning table din da ta ke ta yi ta rusawa. Hawaye mai yawa ya yi ta zubowa daga idanunwan Abdul-Sabur da Faduwa su ma saboda tausayi. Lokaci mai tsawo suka dauka kowa ya kasa magana. Umaimah ta dago da kanta ta sa toilet peper ta goge hawayen da ya bata mata fuska, yayin da idanuwanta suka yi jajawur ta ci gaba da cewa. ''Har yanzu wani lokacin sai na ji kamar kukansu ne a cikin kunnuwana, sai na yi ta tunanin ko a wanne hali suke ciki? Na san Allah ba zai bari su wulakanta ba insha Allah. Ya fito a fusace na yi sauri na mike tsaye kada ya sake dukana, ya harari akwatina ya bude bayan mota ya wuce ya shiga mota ya kunna. Sai na kinkimi akwatina na saka a cikin bayan motar na mayar na rufe. Na sake daga ido na dubi su Bilal har yanzu ba su gushe daga wajen ba, ba su daina kallona ba suna kuka suna kiran sunana ba. Na sake daga kai na dubi wundon kicin sai ga Zulayha a labe ita da *yarta suna nuna ni suna dariyar mugunta. Na yi sauri na bude gidan baya na zauna don na san gidan gaba ya haramta a gare ni yanzu a wajensa. A fusace ya fisgi motar sauran MAKWABTA sun fito sun jeru suna daga min hannu suna nuna min jimami a gare ni, har da kabilun mazan nan da suke zaune a gidan su ma sun tausaya min har da yi min hawaye. Ya kai ni tasha ya fito ya bude bayan mota ya kira masu lodi ya ce su saka kayan a motar Gombe, daga Gombe zai biya direba ya wuce da ni Dugge, ya kai ni har gida ya damka ni a hannun mahaifana. Da suka ji ciniki sai suka rugo suka kira direban ya garzayo da kansa don ya caski kudi. Nan da nan ya amince da bukatun Abdul-Basi, kudi mai yawa ya ba shi ya juya ya tafi ya bar ni da dirobobi a tsaye. Bai ma sake waigowa ba balle ya ga na shiga ko ban shiga ba. Ko sisi bai ba ni ba, bayan kuma ya san ba ni da ko sisi a jakata. Na yi ta rusa kuka a motar ana kallona, wasu na ba ni hakuri, wasu na tambayar me aka yi min. Har mota ta tashi muka tafi ban daina kuka ba, idanuwana kamar za su zazzago su fado don zafi da kumburi ga ja da suka yi, sai na yi tawakkali na zaro carbi na yi ta jan ''Lahaula wala kuwwata illa billahil alaihil azim. Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifli khairan minha''. Ba adadi har muka isa Gombe. Na yi kamar na ki wucewa garinmu na tafi gidan iyayensa na sanar musu ko za su sa ya mayar da ni, sai na ga gara na hakura da shi tunda ya daina sona, so yake ya rabu da ni ta kowanne hali. Direba ya kai ni Dugge da misalin karfe biyar na yamma, sai yara suka hau murna da ihu sun zaci na taho musu da tsaraba kamar yadda na saba zo musu da su alewa, biskit, cingam, biredi, lemo, ayaba. Har na tafi kullum sai na rabawa yara alewa kwali-kwali nake saya. Wannan karon babu komai, nima makoshina a bushe yake ba ci ba sha a hanya, pure water guda daya wata mata da ta zauna a kusa da ni ta ba ni na sha, bayan shi ban ci komai ba ina ji ina gani, ina jin yunwa ba ni da kudin siya, duk *yan mota suna ta ciye-ciye. Abdul-Sabur ya ce, ''Allah Sarki, abu bai yi dadi ba. Daman shi aure a karkashin bishiyar dabino ake daura shi, a raba shi a karkashin bishiyar aduwa, ko darbejiya. Ma'ana bishiyar dabino zaki, bishiyar aduwa kaya, ko darbejiya daci. Allah Ya kyauta, Ya kare mu daga sakin aure, ai ni bana son na ji anyi sakin aure. Bana burin na auri macen da zan iya saki da bakina sai dai mutuwa ta raba mu. Faduwa ta ce, ''Ai ko ba ka fada ba kai ai mai laushi ne, macen da ta aure ka sai dai ta nemo rigima da kanta, amma kai ba ka da matsala. Umaimah ta yi murmushin karfin hali ta ci gaba da cewa, ''Ilah da almajirinsa da Sabitu kanina sai suka zuba min ido suna yi min kallon rashin fahimta da suka ga na fito daga mota jikina sanyi kalau, ido ya yi min jawur alamar kuka da na sha. Sun san ba lafiya ba, kuma ba su taba ganin na zo ni kadai ba babu Abdul-Basi, kuma a motar haya. Direba ya sauko min da akwatina, yara suka kinkima suka kai min ciki. Na sunkuyar da kai na shige cikin gida. A zaure na ga Baffa jin sunana da ya yi yasa ya tashi zaune. Kira ya ke, ''Ina Bilal zo nan ja'iri. Sai na girgiza kai na ce, ''Baffa ni kadai na zo, na baro shi a Kaduna. Ya ce, ''Af ke da Basi'un ne? Na sunkuyar da kai ina shirin fasa kuka, sai na daure na ce, ''Shi ma bai zo ba. Sai ya yi jigum can ya nisa ya ce, ''Zuwan lafiya kuwa kika yi ko ce miki aka yi na mutu ne? Na fara kuka, na ce, ''A'a babu wanda ya ce ka mutu. A nan ya fara fuskantar wani abu ba lafiya ba, shi ma ba ya so yara su ji ko matansa, sai ya yi sauri. Ya ce, ''Je ki ciki ki huta kin sha hanya. Na shiga na gaishe da su Nene sun yi carko-carko a tsakar gida suna jiran labari marar dadi. Na shige dakin Yafindo wanda ya zama dakin Sabitu. Na yi sallah na jira abincin dare, tuwon dawa ne miyar kuka lami shatab a haka na cuccusa saboda yunwa. Sabitu ya shigo ya zauna kusa da ni ya gaishe ni ya shiga tambayata. Cikin rada na ba shi labari, amma na ce kada ya fadawa kowa sai ya dafe kai ya yi shiru da alama hankalinshi ya tashi matuka. Ya ce da ni, ''Ai ko kada ki fadawa Baffa, kada jininsa ya hau. Ki shirya ki je Gombe ki sanarwa iyayensa za su mayar da auren tunda *yan mutumci ne. Na ce, ''Ai ba ni da kudin mota'' Ya ce, ''Zan ba ki idan kin tashi tafiya. Da safe Baffa ya tambaye ni lafiya? Sai na shirga masa karya na ce, umara ya tafi ya ce na dawo gidansu Gombe na zauna, ni kuma na ce gara na zo gida. Ya ce, ''Ban da abinki me ye abin zuwa nan ki zauna Allah Ya rufa miki asiri kina zaman birni, me yasa za ki waiwayi baya? Na ce, ''Ai zan dinga zuwa Gombe ina dawowa'' Sai ya yi addu'a Allah Ya dawo da shi lafiya, na ce, ''Amin. Duk da ban fada ba matan Babana dai suna ta zarge-zarge anya kuwa ba karya na ke yi ba, aurena ne ya mutu irin wannan katuwar akwati dana ciko da kaya? Matawata ma yara suke fadamin ta kirasu tana tambayarsu ko sakina aka yi, na dawo gida? Sai suka ce mata, a'a mijina ne ya tafi Makka na dawo gida, Ta ce, ''Allah Ya sa a sake ta ma. Ilah ma ya tambayi Sabitu anya kuwa lafiya ya ga na zo a jejjeme? Sabitu ya ce, ''Lafiya kalau mijin ne ya yi tafiya shi ne ta zo Gombe daga nan ta karaso gida. Bayan kwana biyu na shirya na dauki kayana kala biyu a *yar jakata na kira Sabitu ya ba ni isasshen kudin motar Gombe zuwa da dawowa. Na kama hanya. Na isa da rana na iske Hajiyar Abdul-Basi, ta kalle ni ta watsar, don ba haka ta saba yi min ba, sai na tsorata na zube na gaishe ta. Idan na yi mata Fulatanci sai ta amsamin da Hausa, sai na rasa wannan dalili. Na fara yi mata bayani sai ta katse ni, ta ce, ta ji duk abubuwan da na shuka, ai ba a kaina aka fara yin kishiya ba da zan dagawa danta hankali don zai yi aure. Na shiga yi mata bayani dalla-dalla sai ta dinga amsawa a shelake, ban yi mamaki ba don irin dinkakkun kayan Senegal wanda Zulayha ta ke siyarwa ta kawo mata, saboda a lokacin ma irinsu ne a jikinta. Don haka Zulayha ta fi ni kirki, don ta fi ni kudi tunda ni bana dinko mata kaya na kawo. Daman mahaifinsa ne ke son mu ita ta fi son ya auri *yar mai kudi, *yan birni don dai rabon Babangida da Bilal ne, babu yadda ta iya. Sai na fashe mata da kuka na durkushe a gaban matar nan ko rarrashina ba ta yi ba, na yi ta yi har na gaji na daina. Na tambaye ta ina Alhaji, sai ta ce da ni, ''Me za ki yi masa? Na ce ''Zan fada masa cewar Yaya Abdul-Basi ya sake ni''. Sai ta ce, ''Wa yace miki bai sani ba? Shi zai hana a sake ki ko shi yake zaune da ku? Zulayha ta kira ni a waya a dai-dai lokacin da kika gama min zagi, wai kin kwace Babangida ke za ki rike tunda dan yayarki ne. Ban da munafunci nima da na hana ki rike shi yanzu na dauka na ba ta saboda na ga gidan maiko ko? To duk na ji zagin da kika yi min. Abdul-Basi ma ya bugo ya tabbatar min kin yi har kin shiga gidan kin kwaso *ya*yan kina masa rashin kunya don kin koshi, kinsha jar miya, kin taka matsayin da ba ki isa ki taka ba, saboda samun guri. Sannan kika yada sirrinmu a makwabta har ofis ake gulmarsa, to me zai yi da ke dan ba son kai da rashin kunya irin ta mutanen kauye ba? Hannu na dora aka ina salati ina kuka, ina kuma rantserantsen ban fadi haka ba, sharri ne kawai aka kulla min. Da Halamu Littafin nan ya fara isan ku. In bakwaso kuyi magana sai a canxa wani. MAKWABTAKA 21 sai ganin fitowar Ja'afar nagani. Ya fito a fusace ya daka min tsawa, ya ce, ''Ke Umaimah ki rufe mana baki, kin ishe mu da kuka tun dazu. Sai na nutsu na rufe bakina na hau makyarkyata kada ya yi min duka, don gidansu na tako na zo. Hajiyarsu ta ce, ''Yauwa gara ka fada mata, kukanta ba zai amfane ta da komai ba, domin mun gano bakin munafunci da kwantingwilarta. Ya karaso ya zauna ya dade kansa a sunkuye a kasa kamar mai tunani, sai can ya dago ya dube mu, ya girgiza kai don takaici. Ya ce, ''Har yanzu daman ana zama na zalunci da jahilci, gami da makirci a duniya? Haba wannan abu da me ya yi kama? Hajiya ta ce, ''Fada mata dai ta ji, an gano ta yanzu, da dai an dauka mai tarbiyya ce, ashe kallon kitse ake yiwa rogo. An dai ji kunya wai kura da satar tsumma. Ya ce, ''Ke dai za a fadawa Hajiya ba Umaimah ba. Kin yi kuskure da kika ba wa danki damar auren karuwa, ya rabu da matarsa ta arziki. Sai dadi ya sa na yi ajiyar zuciya. Ta kuwa fusata da jin batunsa, ta hau zaginsa. Tana cewa, ''Au dama da ni kake, da ka ke cewa ana zalunci, jahilci da makirci? Ya girgiza kai, ya ce, ''Ya ya zan ce miki haka? Da azzalumar karuwar nan nake da shi yaya Abdul-Basin da suka sami yarinya karama marainiya suna wahalarwa. Ta daka masa tsawa, ta ce, ''Ku tashi daga gabana bana son ganinku. Muka mike sadaf-sadaf muka fice, yayin da muke ta jiyo bambamin fadanta. Da muka fito waje sai na ce da shi, ''Ina Alhaji? Ya ce, ''Ya tafi umarar maulid shi da Sarki''. Na ce, ''Ja'afar ya ya zan yi? Ka taya ni fada masa idan ya yi waya, halin da nake ciki''. Ya ce, ''Ki yi shuru, ki daina kuka, ki bari Alhaji ya dawo a tsanake zan same shi na fada masa, zancen bana waya ba ne. Saura kwana uku ya dawo sai na zo mu yi maganar, yanzu dai bari na kai ki tasha ki koma. Na ce, ''To Allah Ya kaimu. Ya dauko mukullin motarsa ya fito da motar, na bude gidan baya na takure yana ta ba ni baki, yaro mai hankalin manya duk da ya girme ni ma. Ya fara wucewa da ni wajen cin abinci (restaurant) ya siya min shinkafa da miya da kaji, ina ji ina gani kamshin tururu amma na kasa ci. Yana rokona da kyar na ci rabi muka fito muka tafi. Harya kama hanyar tasha zai saka ni a motar garinmu, sai na ce ya kai ni gidan kawata Lamijo dake unguwar Checheniya, tare muka yi firamare a Kaduna, ta dawo Gombe tai sakandire daman *yan Gombe ne aiki ya kaisu Kaduna a lokacin. Ta yi aure a nan cikin garin Gombe, ta auri wani hamshakin mai kudi da mulki. Duk zuwan da muke yi ni da Abdul-Basi sai ya kai ni gidan na yini, ita ma idan ta je Kaduna da yake da yayarta da ta yi aure, sai ta zo gidana ta yiyi ko ta kwana. Da farko Ja'afar ya ki amincewa ya kai ni, sai da na yi masa bayanin cewar, so nake na jira Alhaji a gidan ba sai na sha wahalar komawa da dawowa ba. Ya ce ''Kina ganin za ki zauna a gidan har kwana uku ba matsala? Na ce, ''Ba matsala tana da wadataccen dakuna a gidanta. Ya amince ya kai ni har cikin get din gidan, ta hango ni ta wundo ta fito da gudu ta tare ni da murna, muka yi sallama da Ja'afar. Ya ce, zai kira ni idan Alhaji ya dawo, sai ya zo ya dauke ni muje wajensa. Bayan ta hada min goma ta arziki muka fara hira, sai na fara kuka ina ba ta labarin matsalata. Tabbas ta tausaya min, ta ba ni goyon baya na zauna a gidanta har Alhaji ya dawo, sannan ta yi min addu'a Allah Ya sa na koma dakina. Da daddare dan mijinta ya shigo wani matashi yaro, a shekarar ya gama sakandire, sunansa Hanif. Da takardunsa a hannu ya zo neman Babansa... Faduwa ta ce, ''Dan mijinta kamar ya ya? Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''Ke fa Hausa ba ta ishe ki ba. Ana nufin mijin yana da wata matar da kuma gidajensu daban-daban. Kuma girkin amaryar ne shi ne dansa ya zo nemansa. Ko ba haka kike nufi ba Umaimah? Ta yi murmushi, ta ce, ''Haka nake nufi kuwa. Alh. Rabi'u Damuna sunan mijin kawata, matansa biyu ne, ita ce ta uku, kowacce kuma gidanta daban, saboda mai kudi ne. Ina zaune Lamijo da Hanif suna hirar tafiya karatu Malaysia tun bana fahimta har na fara fahimta, tun ban damu ba har na tsoma baki ina jero musu tambayoyi. Ya ce, ai ba Babansa ba ne zai biya ba, gwamnati ce ta yi alkawarin duk *yan asalin garin wanda ya gama sakandire ya keda credit tara za a biya masa. Sai na ga ai ni ma na cancanci shiga cikin wadanda ake neman nan. Sai na fara fadawa kawata to ko nima na dauko takarduna, mijinta ya taimakamin? Ta ce, a,a ya ya za'a yi haka alhali ga shawarar da aka yi za a zartar? Sai Hanif ya shiga ba ni kwarin gwiwa yana murna ya sami *yar uwa, ya ce, sai mu tafi tare. Ya tafi akan zan hada takarduna da nasa a ba wa babansa ya nemar mana tallafi daga gwamnati (schoolership), tunda ana damawa da shi a gwamnati, shi ma kusa ne. Lamido ta shiga yimin nasiha gara auren shi ne mutuncina da na je kasar waje karatu ace na zama *ya iska. Na gyara zama na sake bude mata cikina ta ji duk halin da nake ciki a Kaduna, Gombe da can Dugge garinmu. Na tabbatar mata Abdul-Basi ba ya sona, ba zai mayar da ni ba, ko na koma Zulayha ba zata bar ni mu zauna lafiya ba. Ga mahaifiyarsa ta tarko tsana ko ita ba zata bari ya mayar da ni ba. Idan na zauna a garinmu gori da wuya ne za su gallabe ni. Sai ta yi saranda ta yi amanna na bar kasar. Amma ta shawarce ni na jira zuwa kwana ukun surukina ya dawo a ji abin da zai ce. Na dukufa ina ta addu'ar neman zabin Allah mafi alkhairi tsakanin zuwana karatu Malaysia da komawata gidan mijina. Na yi ta yin wannan addu'ar istihara da Manzon Allah (S.W.A) ya ce mu dinga yi zamu ji abin da ya fi alkhairi ya fi kwanciya a ran mai yinta.. Faduwa ta ce, ''Ya ya addu'ar ta ke? Umaimah ta ce, ''Sallah raka'a biyu ce a karanta Fatiha da kowacce surah, sannan a karanta wannan addu'ar:Allahumma inni astihiruka bi ilmika, wa astakdiruka bi kudaratika, wa as'aluka min fadlukal azim, fa'innaka takdiru wala akdaru, wa ta'alamu wala a'alam, wa anta allamul guyub, Allahumma in kunta ta'amu an hazal amru kairan li fi dini, wa ma'ashiyi, wa akibati amri au kala ajili amri, wa'ajilihi, fakdurhuli, wa yassarhuli, summa barakli fihi, wa in kunta ta'alamul annahazal amra, sharranlifi dini wa ma'a shiyi, wa akibati amri, au kala fi ajili amri, wa'ajilihi, fasrifhu anna wasrifni anhu, wa kudirli kaira haisu kana summa Ardinibihi.'' A ranar da Ja'afar ya ce Alhaji zai dawo na ji shiru bai neme ni a waya ba. Sai na kira shi bai dauka ba. Na ce, to ko shigowar dare ya yi, bari na bari sai gobe na sake kira. Washegari har yamma Ja'afar bai kira ni ba, na kira bai dauka ba. Hankalinmu ya tashi ni da kawata babu abin da ba mu saka a ranmu ba. Na tabbatar mata sai dai idan Hajiyarsa ce ta hana shi fadawa Alhaji shi yasa bai dauki wayata ba. Sai Lamijo ta kira da layinta ya dauka da ta fara yi masa maganata sai ya katse wayar, da muka sake kira sai muka jita a kashe murus. Na yi ta kuka Lamijo na ba ni hakuri, ta shawarce ni na je na debo takarduna ta yi min alkawari zata tsaya min har sai na sami tafiya, domin mijinta yana ji da ita. Sai abin da ta ce kasancewar ba ta haihu ba har yanzu da ita ake cin amarcin, kasa-kasa da ita yake zuwa. Ta bani kudin mota na garzaya Dugge takarduna kadai na kwaso na ajiye wadancan kayan na dauko wasu kala uku, na kunso a jaka. Na sake barkawa Baffa karya, amma Sabitu na fada masa komai. Da farko ya tsorata ya ce, kada na je kasar Turawa su kashe ni. Na yi dariya kawai, na san rashin wayewa yake damunsa. Na jaddada masa insha Allah ba matsala zan je lafiya na dawo lafiya, sai ya yi min addu'a Allah Ya ba ni sa'a. Na dawo Gombe a ranar, na kawowa Lamijo takarduna, daman ta gama fadawa mijinta ya san da zancen. Da ya duba sai ya gyada kai ya ce, na cancanta a ba ni tallafi in je karatu dan na cinye jarabawata dukka. Sannan ya ce na yi photocopy na ba shi na ajiye original a wajena. Ta sake ba ni tabbaci na je na kwantar da hankalina komai zai dai-daita nan da watanni biyu zuwa uku komai zai kammala, za'a yi tafiyar. Sai a lokacin hankalina ya tashi yadda zan zauna har tsawon watanni uku a garinmu, wai! Abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Dama ya lafiyar Kura bare kuma ta yi hauka? Ni kam na san tawa ta kare, asirin da bana son ya tonu ne a kauyenmu shi zai tonu. Da muka kebe da Lamijo na shaida mata ni fa bana so na zauna da yawa a garinmu, don ban ce musu aurena ya mutu ba, ta ce, to na zo mu zauna a gidanta mana. Na ce, a'a ba zai yiwu ba, sai dai ta samo min aikin wanke-wanke da shara na yi, don na sami gidan zama har lokacin tafiya ya yi. Ta girgiza kai ta ce, ''Allah Ya sauwake na barki ki yi wanke-wanke da shara. A karshe dai muka tsayar da shawarar na zauna da mahaifiyarta, daman ba ta da karamar yarinya a gabanta, Lamijo ce *yar autarta tare suke zama, gashi ta yi aure ta bar ta ita kadai. Umma mahaifiyar Lamijo ba ta ki ni ba da muka je, sai ta amince na zauna tare da ita, unguwar Herwagana gidan ya ke. Ai kuwa ba ta yi da-na-sanin zuwana ba, na zame mata abar alfahari, bacci ne kadai bana yi mata, amma ko tsinke bana barinta ta dauke. Bayan zuwana da sati biyu na ga ya dace na je gida na sanarwa Sabitu kada ya ji shiru ban dawo ba ya dauka Turawa sun sace ni ya fito da maganar. Na shirya na tafi Dugge, na zaunar da shi na ba shi labarin halin da ake ciki. Ya ji dadi da ganina, don gaskiya har ya tashi hankalinsa. Baffa kuwa karya dai na sake shimfida masa, na ce AbdulBasi ya dawo zan koma Kaduna, kuma ina tunanin zamu kaura wata kasar nan da *yan watanni, zan zo na yi masa sallama idan dai tafiyar ta tabbata. Ya ce, 'To Allah Ya kaiku lafiya. Na zabgawa *yan gida karya na kwashi kayana dukka na nufi birni na ci gaba da zama da Umman Lamijo. Tafiya kamar zata yiwu kamar ba zata yiwu ba, sai da aka zarce watanni hudu ma, abinka da gwamnati kuma sai masu hanya. Na takaice muku ma dai sai tafiya ta fara shiriricewa kamar an fasa. Hankalina ya tashi na gigice, ga shi an ce lokacin karatu ya karato, idan ba mu je akan lokaci ba sai dai mu bari sai wata shekarar. Na sankare a kwance ina kuka, ina tunanin yadda zan koma garinmu na ci gaba da rayuwa. Na rame kai ka ce ban taba cin lomar tuwo bakina ba, rama da koke-koke ma sai sanda MAKWABTANA a nan Gombe suka sake banka min wata kullalliyar. 'kamar ya ya, a nan Gomben kika yi MAKWABTA har suka kulla miki kullalliya? Abdul-Sabur ne ya tambaye ta cike da takaici. Umaimah ta yi murmushin karfin hali, sannan ta zubo da hawaye ta yi sauri ta sa hannunta ta goge, ta ci gaba da cewa. 'Ina zaune da Ummar Lamijo lafiya cikin jin dadin juna ba tsangwama ta lura dai ina cikin damuwa don idan na zauna sai ta ga na yi tagumi. Cikin dare idan ta farka sai ta gan ni a zaune, kwanciya ta gagara sai shesshekar kuka. Ta dinga yi min nasihohi, ta ce na yi tawakkali na yi hakuri komai mai wucewa ne. Ta yi ta shawarta ta na dinga shiga gidan Salame makwabciyarsu ita ma dai duk sa'armu ce, kawar Lamijo ce sosai kafin ta yi aure, kullum tana shiga tana hira, sai na cewa Ummar Lamijo a'a zan dinga zama a gida ni kadai. Ita kuwa Salame tun farkon zuwana ta ke ta nacin na dinga shigowa gidanta idan ta shigo gidan. Ko ta yi ta aiko *ya*yanta wai na zo zata yi min wata magana, hankalina ya tashi na suri gyale a gigice na je, sai na iske daman ba komai zata fada min ba, hira kawai ta ke so mu yi. Sai na dan zauna mata kadan sannan na tashi na shigo gida. Kamar da hantsi idan mijinta ya tafi aiki yaranta suka tafi makaranta, Umma ta shiga daki baccin hantsin da ta saba, da yake ta manyanta tana shan magungunan ciwuka kala-kala. Sai na dauki gyalena na shiga gidan Salame mu yi ta hira, hirar ma ta Lamijo ce kawai don babu wani wanda muka sani tare, bayan Lamijo. Sai na ga tana ta bugun cikina tana so ta ji ni budurwa ce ko bazawara, ni *yar uwarsu ce ko kawa ce, na kauro Gombe gaba daya da zama ko zan koma garinmu? Bana ba ta amsa sosai, don haka ba ta san komai nawa ba, idan taga kamar bana so sai ta canza hira, mu koma hirar makaranta. Na fara sakin jiki da Salame, dimbun damuwar da nake ciki ta ragu saboda tana dauke min kewa. Daga na shiga gidanta sai ka ga ta tare ni da murna, ta yi ta kawo min kayan ciye-ciye, yadda, yadda ku kasan ta ba ni babu. Na ji dadi da zama da Salame, na yi farin ciki da Allah Ya bani madadin Matawata kawata, kuma makwabciyata mai sona. Duk sanda zan je gidan Lamijo tare da Salame muke zuwa, ta sa mijinta ya kaimu, ina baya suna gaba ana ta hira. Umar sunansa, mutum mai yawan fara'a da son hira, har Lamijo ta ke zolayarmu wai kada fa mu didare mu barta da zagayen baranda, ma'ana kada dukka kawayenta ne a dalilinta muka san juna, kada mu hade kai mu ware ta, don ta ga shakuwar ta kai shakuwa. Wata rana da daddare muna kwance a tsakar gida ni da Umma, sai muke ta jiyo hayaniya a tsakanin Salame da mijinta Umar su ma a tsakar gidansu, da yake katangarmu daya da su. Hayaniya sai karuwa ta ke yi, har yana cewa sai ya sake ta. Na dafe kirji na tashi zaune, Umma ma ta zauna muka shiga fargaba. Ta ce, kafarta ke ciwo naje na ba su hakuri, na je na ce inji ta ta ce su daina. Na saka gyalena jikina yana rawa har naje bakin kofa na juyo, na zo na durkusa a gaban Umma. Na ce, 'Umma ki daure ki zo mu shiga tunda babu nisa, ki yi musu magana da kanki za su fi ji tunda ke babba ce, na ga kamar fadan ba karami ba ne, tunda na ji dukkansu ransu a bace yake, kada ayi batacciya. Ta ce, 'To dauko min gyale na a daki. Na shiga da sauri na dauko mata ina rike da hannunta muna doddogarawa har muka isa cikin gidansu. Muka iske su kaca-kaca kowa ido yayi masa jajawur, baki yana kumfa da alama sun kai kololuwar bacin rai. Yaransu suna ta kuka ga wayoyinsu a kasa

Chapter 13 of 33