Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na dawo a dai dai ke ma kin zo. Ta yi tsuru-tsuru tana jiran abin da zai ce mata, ta ji shiru bai yi magana ba, Faduwa ce kawai ke ta zuba kamar bushasshiyar kanya. Labarinta ta ke ta ba su tun tana firamare yadda ta yi kin ji. Suka sha dariyarsu har da kyakyatawa. Abdul-Sabur ya gyara zama ya dubi Umaimah ya ambaci sunan, sai ta ji wani abu ya tsargo daga kirjinta don fargaba. Cikin lallausar murya ta amsa masa gami da tsura masa ido tana son ta ji abin da yake shirin fada. ''Kina da lambar wayar *yan gidanku? Ya tambaye ta. Nan da nan ta cika da mamakin irin wannan tambaya da ta fito daga bakinsa. Sai ta rasa amsar da zata ba shi. Ya lura da hakan sai ya yi murmushi ya mika hannu kan teburin da ya ke gabansu ya dauko wani dan madaidaicin kwali ya hau budewa. Ya zaro wata tsaleliyar waya kirar Nokia E5 ya mika mata, ya sake zaro layin waya ya mika mata, ta karba a sanyaye kuma cike da mamaki, tambaya ce a cike da bakinta ta gagara furtawa. Faduwa ta ce, ''Wayarki ce yayanmu ya siyo mana iri daya, nima kinga tawa can a caji. Umaimah ta dubi Abdul-Sabur da sauri shi ma ya dube ta, sai ta sunkuyar da kai kasa ta yi dan murmushi. Ta ce, ''Na gode Yayanmu, amma ka yi hakuri bana so in saka ka asara in karbi wayar in ajiye ta don ba zan yi amfani da ita ba. Abdul-Sabur ya tsuke fuska, ya ce, ''Ni dai na baki, idan kin so za ki iya jefarwa a bola. Daga dukkan alamu Umaimah ba ta ji dadin wannan kalmar da ta fito daga bakin Abdul-Sabur ba, nan da nan sai ta ji hawayen takaici ya fara kwaranya daga idanuwanta. Faduwa ta zabura ta je ta rike ta tana mai lallashinta tana ba ta hakuri. Ta juyo ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Ka sa ta kuka fa saboda kalmar da ka fada mata. Kasan fa ita *yar a lallaba ce. Ya yi ajiyar zuciya ya daga gira, ya ci gaba da kallon talabijin bai ce da su komai ba. Umaimah ta hasala ta ajiye wayar akan tebur ta zabura ta mike tsaye zata fice, Faduwa ta rike ta tana ba ta baki. Cikin kuka Umaimah ta ke magana, ta ce, ''Anti ki kyale ni in tafi gida, shi ya fi min sauki. Ni bana son waya, bana bukatar in rike waya a rayuwata. Faduwa ta ce, 'Duk da haka tunda ya siyo miki sai ki karba ki yi godiya, bai kamata a gabansa ki ce ba kya so ba. Yana da dalilinsa da yasa ya ce ki rike waya. Ki dauka ki sakata a caji ta kwana, sannan ki saka layinki in an kira ki dauka daman ba a ce sai kin kira kowa ba. Umaimah ta girgiza kai ta ce, ''Ba zan tafi da ita ba da gaske nake, bana so in rike waya. A fusace ta warci mukulllin gidanta ta fice, Faduwa zata bi ta Abdul-Sabur ya dakatar da ita da hannu alamar ta tsaya kada ta bi ta. Faduwa ta dawo ta zauna a sanyaye. Ta ce, ''Haba Abdul kai da kasan lallabata ake yi ya zaka yi mata gatse-gatse alhali kasan halinta baudaddiyar yarinya ce. Ya yi murmushi, ya ce, ''Ina sane na yi mata haka, akwai dalili. Faduwa ta gyara zama ta tambaya, ''Me ye dalilin? Ya yi murmushi ya ce, ''Za ki ji nan gaba. Faduwa ta ce, ''Koma dai maye dalilinka ka jawo mana yanzu, tunda ranta ya baci sai mun yi rabin shekara muna bin kanta kafin ta fara kula mu. Ai ka fi kowa sanin wahalar da muka sha kafin ma ta fara amsa gaisuwarmu. Mun samu ta fara karkatowa kuma ka dagula mana lamuranmu. Yanzu ga shi soyayyar da nake shiri ginawa a tsakaninku ka rusa min. Ya harare ta, ya ce, ''Waye zai yi soyayyar da karamar yarinyar da har yanzu ba ta mallaki hankalin kanta ba? Ni ai ba haka nake ba. Faduwa ta bude baki don mamaki tana duban AbdulSabur, ta ce, ''Yau kuma da bakinka kake fadar haka? Nasan kana sonta. Wai me yake faruwa ne a tsakaninku, ta yi maka laifi ne? Abdul-Sabur ya yunkura ya mike ya ce, ''Ki saka mata wayar a caji ta kwana da safe ki saka mata layi ki kai mata. Faduwa ta amsa masa da ''to'' cike da ladabi. Ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba, ya nufi gidansa. Da alama dai babu walwala a tattare da shi yau. Faduwa ta kamu da mamakin halin fushi da Abdul-Sabur ya shiga yau wanda ba ta taba gani ba. Alhali tunda safe suke tare ba ta ga bacin rai tattare da shi ba, sai yanzu. Ta aiwatar da abin da ya umarce ta da ta yi. Gari na wayewa karfe takwas na safe a kofar gidan Umaimah ta yi mata. Ta danna kararrawa. Umaimah ta yi mamaki da jin ana danna mata kofa, amma mamakin ba shi da yawa tasan dayan biyun, idan ba Faduwa ba ce, Abdul-Sabur ne, kuma zancen dai na waya ne. Daman idanunta biyu tana zaune a falo tana kallon wani film baccin safe ta gagari idanunta na daren ma kadan ta yi, ta rasa dalilinta na shiga wannan damuwa, saboda sun sami dan sabani da Abdul-Sabur. Ta tashi da sauri ta je ta bude kofar, tabbas tunaninta ya zama gaskiya, Faduwa ta gani tsaye a bakin kofarta fuskarta cike da murmushi. Ita ma ta yi mata murmushi gami da yi mata izini ta shigo. Suka shiga suka zauna Faduwa ta zaro waya ta mika mata Umaimah ta langwabar da kai gefe tana shirin bude shafin wani sabon kukan. Cikin shesshekar kuka ta ce, ''Bana son na rike waya a rayuwata shi ne kadai dalilina na kin hada waya. Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Umaimah, kada ki zama mace mai yawan taurin kai, ma'ana mai gardama, kasancewarki mace wacce zata yi aure ta zauna a karkashin wani bai dace ace haka halinki yake ba. Maza ba sa son mace mai gardama, musamman Yayana AbdulSabur mutum ne mai saukin kai, ba ya shiri da mai gardama. Tunda ya siyo ya baki ya kamata ki karba ki yi godiya. Yanzu ma shi ya aiko ni ya ce na kawo miki, ki karba ki rike ba dadi mayar da hannun kyauta baya. Umaimah ta mika hannu a hankali ta karba ta ajiye a gefenta a sanyaye, sannan Faduwa ta ji dadi a ranta. Faduwa ta zaro wayarta ta kira lambar Umaimah nan da nan ta hau ruri. Umaimah ta tsurawa wayar ido da kallo. Faduwa ta ce, ''Ita ce lambata, ki yi saving Umaimah ta gyada kai ba tare da ta ce komai ba. Faduwa ta mike ta nufi hanyar fita yayin da Umaimah ta ke yi mata rakiya har bakin kofa. Faduwa ba ta daina yi mata nasihohi ba, akan ta cire damuwa, ba a kanta aka fara samun matsalar rayuwa ba, haka ba a kanta za a kare ba. Don haka ta saki jikinta ta yi walwalarta ta saba da sababbin mutanen da ba su santa a baya ba. Bayan Faduwa ta tafi Umaimah ta dawo ta zauna a kusa da wayar ta buga tagumi tana tunani da sakesaken yadda zata salwantar da wannan waya kada ma ta jawo mata matsala da tone-tone. Don ita ta buya a duniyar da babu wanda ya santa, ba ta so a tono ta. Wayarta ce ta hau ruri abinka da rashin sabo, sai ta daka tsalle ta mike tsaye, ta tsorata tana shirin ta zura da gudu. Sannan hankalinta ya kawo kan wayar ta tuna ashe waya ta yi sam ta manta. Ta dawo ta zauna tana ajiyar zuciya, yayin da ta jawo wayar tana ta kallo har ta katse ba ta amsa ba. Daga dukkan alamu ta gane lambar irin ta dazu ce, ta Faduwa ce. Ba ta gama kallon lambar ba aka sake kira, ta amsa a sanyaye ta yi mata sallama. Faduwa ce ke magana cikin walwala, ta ce, ''Yauwa, ita ce lambar tawa na kira in shaida miki na iso gida lafiya. Kuma ga cajar wayarki a gidana duk sanda kike son caji ki zo ki dauka. Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''To na gode Antina, Allah huta gajiya, Allah Ya bar zumunci. Suka kashe wayar a tare. Umaimah ta hau gunguni tana magana ita kadai, ''kawai ta takura min da kira, shiyasa ma suka hada min wayar dan su hanani sukuni. ***************** Tunda Umaimah ta ajiye wayar a daki a karkashin filo fiye da kwanaki uku ba ta sake waiwayarta ba. Babu irin kiran da Faduwa ba ta yi mata ba shiru babu amsa, haka idan ta fice zuwa makaranta tunda safe har yamma likis ba ta dawowa gida. Shin darasi ne yake hana ta ta shi da wuri ko kuwa saboda wayar da aka hada mata ne, ta zame mata tamkar dodo a gidan shi yasa take guduwa? Oho! AbdulSabur ya lura da hakan cewar ba ta dawowa da wuri, tunda aka bata waya don haka bai taba garajen kiranta ba ma kada ta zaci manufar hada wayar ke nan. Yana tsaye akan barandar gidansa tun daga can kololuwar nesa ya hango tana dawowa daga makaranta a yammacin wannan rana. Yana daga sama ya zuba mata ido yana kallo, tafiya ta ke kanta a sunkuye a kasa, ba ta kallon kowa, sai ya shiga mamaki irin wannan hali nata na ko in kula da mutane. Kafin ta hau sama sai ya yi saurin barin barandar don kada ma su hadu. Ya lura a kufele ta ke da shi saboda ya yi mata mummunan laifi da ya fitar da kudinsa ya sai mata waya, kuma ya tilasta mata ta karba dole. Tana shiga dakinta wayarta ta dau ruri karkashin filo, da farko sai ta razana har da dafe kirji taji kara a karkashin filonta. Can ta tuna ashe waya ce, ta mika hannu da sauri ta dauka, ta ga Dr. Faduwa ce. Kafin ta amsa waya ta katse, missed call 49 ta gani duk na Dr. Faduwa har cajin waya ya kusa karewa. Sai ta yi tagumi tana tunani, ita kanta ta san ba ta kyautatawa Faduwa ba, nauyi da kunyarta suka addabe ta. Faduwa mai kaunarta ce, bai kamata ta dinga share ta ba tabbas. Faduwa ce ta ke kira har yanzu, kunya ya hana ta dauka, don haka ta yanke hukuncin tashi ta tafi gidan Faduwa a wannan lokaci, wannan ita ce hanya kadai da Faduwa zata goge wannan abin da ta saka a rai cewar wulakanci ne ya hana ta daukar waya. Ta ci sa'a ta iske Faduwa a gida, tana ganin Umaimah sai ta yi farin ciki gami da ja mata kunne ta murde a hankali. Ta ce, ''Kin cika taurin kunne Umaima, kin jefar da wayar ko? Umaimah ta yi murmushi ta fito da wayar daga aljihun wandonta (jeans) ta nuna mata. Ta ce, ''Ban yar ba, a gida nake manta ta idan zanje makaranta. Faduwa ta kwashe da dariya, ta ce, ''Au wayar ta ki ma kike mantawa a gida? Lallai a gaishe ki, tsabar wayar ba ta gabanki ke nan. Anya Umaimah rayuwa zata yiwu a haka? Ya kamata ki sauya ra'ayinki. Nawa kike a shekaru, rayuwar ma yanzu kika fara da har zaki zama haka. Umaimah ta zauna a sanyaye ta yi ajiyar zuciya, ta yi tagumi tana duban Faduwa, ita dai ba ta gajiya da yi mata nasiha. Ta karbi wayar ta dudduba sai ta kyalkyale ta yi dariya. Ta ce, ''Ban da ni babu wanda yake yi miki waya? Umaimah ta gyada kai, ta ce, ''Babu wanda ya taba kirana. Faduwa ta ce, ''Abdul-Sabur bai taba kiranki ba? Ai yana da lambarki tunda shi ya siyo mana sim card din. Kafin Faduwa ta rufe bakinta sai taji kaurin abincin data dora yana shirin kamawa nan da nan ta arta da gudu zuwa kicin. Shigarta kicin ke da wuya sai AbdulSabur ya yi sallama gami da daga labulen kofar falon ya shigo cikin nutsuwa. Nan da nan Umaimah ta daga kai da sauri ta dubi mai shigowa, sannan ta amsa sallamar ita ma cikin nutsuwa. Sai ta yi sauri ta sunkuyar da kanta kasa don kunya da nauyin abin da ta yi masa. Kan ka ce kwabo ta sulalo daga kan kujera ta gaishe shi cikin harshen Hausa. Ya fada cike da fara'a ''ta shi ki zauna ba sai kin sauko daga kan kujera ba in za ki gaishe ni. Ina Faduwa? Ta nuna kicin da yatsanta ta fada cikin girmamawa, ''Tana kicin yanzu ta shiga. Ya kwallawa Faduwa kira ta fito da sauri tana mai maraba da zuwan MAKWABCINTA kuma abokinta. Su dukka ukun a zaune suke akan kujeru, Faduwa ce ke ta labari, tunda Umaimah ta sunkuyar da kanta kasa ta tattakure ba ta sake dagowa ta dube su ba. Wayar Umaimah akan tebur (center table) ta fara ruri, ma'ana tana nunawa caji ya kusa karewa wato (battery low), su dukka ukun suka kalli junansu. Faduwa ta yi murmushi, ta ce, ''Ga cajarki can a wajen soket, ki saka wayar a caji ga ta nan har zata mutu kamar a kasarmu Nigeria inda ake rashin wuta har caji ya kare waya ta mutu. Daga Abdul-Sabur har Umaimah babu wanda ya yi magana. Umaimah ta mike a sanyaye ta dauki wayar, ta je ta saka ta a caji, daga nan ta dubi kofar fita, ta juyo a hankali ta dube su ta yi dan murmushi, ta yi musu sallama ta ce zata tafi gida. Faduwa ta zabura ta ce, ''Me yasa zaki tafi gida alhali muna zaune muna hira har an dora mana abinci ya kusa dahuwa. Umaimah ta yi murmushi, ta ce ''Alhamdulillah ai a koshe nake, ban dade da cin abinci ba. Faduwa ta yatsune fuska ta ce, 'Ko ba zaki ci abinci ba, ai sai ki zauna ayi hira in kin je gidan ma ke kadai ce me za ki yi? naku akulun IB MAKWABTAKA 28 Umaimah ta kara kutsa kai kofar fita, ta ce, ''Ai ina da ayyukan yi ne a gidan, kuma ina so na yi karatu. Faduwa ta juya ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Ka taya ni rokonta ta ki zama. Ya dubi Faduwa ya juya ya dubi Umaimah sai ya juya ya ci gaba da kallon talabijin bai ce da su komai ba. Faduwa ta yi ajiyar zuciya ta tabe baki, ta mike tsaye kafin ta daga kai har Umaimah ta bace daga bakin kofar, ba ita babu ko inuwarta. Faduwa ta wawuro wayar Umaimah da cajar da sauri ta biyo ta waje tana kwalla kiran sunanta. Umaimah da Faduwa sun dade a tsaye a bakin lift suna magana, Faduwa tana nuna rashin kyautawa da Umaimah ta ke yi wajen rashin sakin jiki su saba har yanzu. Ita kuma Umaimah tana amfani da wasu hujjojinta wajen kare kanta. Daga karshe ta karbi wayarta suka yi sallama ta tafi gidanta. Faduwa ma ta dawo gida, ta iske Abdul-Sabur a zaune a inda ta bar shi. Babu yadda Faduwa ba ta yi da Abdul-Sabur ba akan ya ce wani abu game da al'amarin Umaimah, ya ki magana. Faduwa ta shiga zulumi akan wannan sauyin al'amari da yake gudana tsakanin Abdul da Umaimah Bello. Ta fara tambayar kanta, ''Shin Abdul-Sabur ya yi fushi ne da Umaimah ko kuwa da ni yake fushi ni da na kawo maganar so ya ji ya tsani daga ni har Umaimah? Don Faduwa ta fuskanci baya son maganar soyayya ballantana maganar aure a rayuwarsa. Ko kuwa wata *yar aljana ce ta aure shi ya ke gudun bil'adama? Allah Shi Ya barwa kansa sani. Ta bi Abdul-Sabur da kallo a lokacin da ya yi cimak ya mike har ya fice da alama babu walwala a fuskarsa, babu annuri sam a tare da shi. Faduwa ta yi tagumi tana tunani, Umaimah ta dagulawa yayanta lissafi, ya fara shiga halin da bata saba ganinshi a ciki ba. Ita dai a da wasa da dariya suke yi a koda yaushe baya fushi. Ta jiyo kauri a kicin, abincinta ya fara konewa, ta zabura da gudu ta shiga kicin tana magana ita kadai a lokacin da ta ke kashe wutar. Ta ce, ''Uhm, ina can ina tunani abincina zai kone a banza saboda son hada soyayyar da ba mai yiwuwa ba. Allah Ya yi mana jagora Ya zaba mana abin da ya fi alkhairi. *********************** Abdul-Sabur ne ya fito daga get din gidansu cikin tsaleliyar motarsa da sanyin safiyar laraba da alama dai sauri yake zai tafi makaranta. Dai-dai lokacin Umaimah ma ta fito kamar ta ci da kai don sauri. Ita ma rataye da jakar na'ura mai kwakwalwa a kafada (laptop). Tana hada ido da shi sai ta yi turus da alama ta dan razana, taso a ce akwai lungu da zata shige ta buya da ta labe idan ya tafi sai ta fito. Ya gangara gefe ya tsaya yana jiranta ta karaso tana tafe tana sanda dole dai ta iso gare shi dai-dai saitin tagar da yake zaune. Sai yayi sauri ya sauke gilashi ya leko da kai ya dube ta ya yi murmushi, sannan ya ambaci sunanta. Ta yi dan murmushi ta duka ta gaishe shi. Ya ce, ''Ina za ki je ne? Ta ce, ''Makaranta, ina da jarabawa. Ya gyada kai, ya ce, ''Af ku ma kun fara jarabawar, ni ma jarabawar zan yi. Ki shigo in fara sauke ki sai na wuce. Ta girgiza kai, ta ce, ''A'a ka tafi kawai zan karasa ai da sauran awa daya kafin mu shiga har zan karasa ma ba a fara ba, kada ka makara. Ya girgiza kai gami da yunkurawa ya bude mata kofar gaba ya ce, ''Ki shigo in kai ki ba damuwa ai. Nauyi, kunya da fargaba ne suka rufto mata a cikin zuciyarta. Nauyinsa ta ke ji, saboda ba su saba ba, ba ta san wacce irin hirar zata yi masa ba, ga shi daga ita sai shi yau babu Faduwa sarkin hira. Kunyarsa ta ke ji saboda abubuwan da ta yi masa a baya da kuma rashin kyautawar da ta yi masa akan tsaleliyar wayar da ya fitar da zunzurutun kudinsa ya saya mata ta ce bata so. Sannan fargaba ta ke kada jama'ar makarantarsu su ganta da shi kamar yadda rannan aka jeru ana kallonta da su. Dadinta ma wancan lokacin akwai Faduwa a zaune a gidan gaba, yau kuwa daga ita sai shi. Shin wanne irin kallo da fassara mutane za su yi mata game da wannan canjin da suka gani? Hannayenta da kafafuwanta har karkarwa suke da ta zo shiga motar ta zauna a hankali ta rufo kofar motar, ya ja suka fara tafiya. Duk da makarantar babu nisa daga gidansu, amma ta kagu su karasa ya sauke ta ya tafi ya bar ta. Tunda ta sunkuyar da kanta kasa ta damki jakarta kai ka ce in an ce kulle zata ce cas ta arta da gudu. Kallo daya ya yi mata, sai ya dauke kai ya lura da halin da ta shiga, don haka ya fasa jero mata dimbum tambayoyin da suke cikin ransa. Ya kunna CD yayin da wani kida mai dadi ya fara tashi gami da wata zazzakar waka tana fitowa, wakar ba da Hausa aka yi ta ba, haka ba da Turanci ba ce. Ta dago da kai a hankali ta dube shi, kauyanci ya hana ta jero masa tambayoyi game da wakar. Ko ba ta fada ba tabbas ya san tana so ta tambaye shi wannan wanne yare ne? Da suka hada ido sai ta yi sauri ta sunkuyar da kai kasa, ya yi murmushi ya dube ta. Ya ce, ''Kina da tambaya ne? Ta ce, ''A'a. Ya ce ''To ni ina da tambaya. Kin san sunan mawakin kuma da sunan yaren da ya ke wakar? Ta yi murmushi, ta ce, ''ba zan sani ba, saboda yaren Hausa, Fulatanci da Turanci kadai nake ji, shi kuwa ba irin su ya ke yi ba. Ya gyada kai, ya ce, ''Haka ne, amma ai ya kamata ki tambaye ni saboda ki karu, kin san tambaya tana kara ilimi, haka duk yaron da zai yi kokari a rayuwarsa za ki ga yana da yawan tambaya. Ko ba haka ba? Umaimah ta yi murmushi ta gyada kai ba tare da ta dube shi ba, kuma ba ta yi magana ba. Ya ce ''Wannan mawakin sunansa 'Akuri Afomsa' dan kasar Ghana ne, da yaren 'Asanti' yake wakar. Ya na magana akan soyayya yana fadar zafin rabuwar da ya ji a lokacin da ya rasa budurwarsa. Umaimah ta dago da sauri ta dube shi, sai ya yi mamakin kallon da ta yi masa tamkar tana tuhumarsa da wani laifi game da furucinsa. Ya dan yatsune fuska, ya ce, ''Lafiya ko na yi laifi ne da na fada miki fassarar wakar? Ko dai kina ganin kamar ina tsokanarki ne dan kin baro Ilah ko Abdul-Basi? Ta girgiza kai ba tare da ta yi murmushi ba ko magana. Daga nan Abdul-Sabur ya ja bakinsa ya yi shiru, don ya fuskanci duk nacinsa Umaimah ba zata saba da shi ba, ba ta da niyyar yin hakan. Sabuwar waka ce ya sake sakawa, ita ma dai mawakin Ghana ne mai suna 'Kwabula-Kwabula, shima da yaren Asanti ya ke rerowa, Umaimah ta tambaya. ''Ita kuma wannan akan me ya ke yinta? Abdul-Sabur ya yi mamaki da jin wannan tambayar ta Umaimah, sai ya ji farin ciki a ransa. Ya ce, ''Ya na waka ne akan mutuwa da ta raba shi da wadanda ya fi so a duniya, wato mahaifansa, da kuma masoyiyarsa. Umaimah ta yi shiru kanta a sunkuye a kasa tana dagowa sai ya ga kwalla ta cika mata idanu. ''Lafiya kike hawaye? Abdul-Sabur ya tambaya cikin gigicewa mai tsanani. Ta yi sauri ta sharce hawaye da gefen gyalenta. Ta girgiza kai ta ce, ''Wani abu na tuna shine ya sani kuka. Abdul-Sabur ya ce, ''Yafindo ko? Yi hakuri ba ke kadai ba ce marainiya. Ki tuna fa ni da Faduwa babu uwa babu uba, gara ke da sauki tunda Baffa yana nan. Fatanmu Allah Ya gafarta musu, Ya saka su a aljanna, Allah Ya kai mu inda suka je a sa'a. Babu wanda zai yi saura a duniya. Ta sake surnano da hawaye mai radadi, ta ce, Amin. Shi wannan mawaki bai yi waka akan yara kanana da suka rasa uwarsu ba alhali bata mutu ba? Abdul-Sabur ta ji hankalinsa ya tashi da wannan tambayar tata, ya fahimci da *ya*yanta da ta baro ta ke. Sai ya girgiza kai, ya ce, ''Bai yi waka a kansu ba. Amma ai yaro don ya rabu da mahaifiyarsa alhali tana raye a duniya bai zama maraya ba, za su hadu wata rana. Dai-dai lokacin da ya zo makarantar ya sami waje ya tsaya sannan ya yi mata fatan samun nasarar jarabawa. Ta amsa da, ''Na gode, sai anjima. Ta yunkura zata fice, sai ta ji ya kira sunanta. Ta juyo da jajayen idanunta da suka jike sharkaf da hawaye, ta dube shi. Ya ce, ''Ina wayarki? Ta yi saurin sunkuyar da kai kasa, amsa ta gagare ta. Ya yi ajiyar zuciya ya ce, ''Kin baro ta a gida ko? To abin da nake bukata a wajenki shi ne, ki yi min alfarma ki nemo min lambar wayar Hanif a wajen abokanku, na san suna waya a junansu, ke ce dai ba kya waya da su. Ki karbo min lambar ina so in yi amfani da ita. Yau nake so kada ki ce min kuma kin manta. Ta gyada kai da alama dai ta cika da mamaki amma bata iya tambayarsa meyasa ba. Ta fita daga motar, tana shirin rufowa ta sake ji ya ambaci sunanta, sai ta fasa rufe kofar ta amsa masa cikin ladabi. Ya ce, ''Karfe nawa zaki tashi ne yau? Ta ce, ''Karfe sha biyu. Ya ce, ''Ni sha daya zan tashi zan biyo miki mu koma gida, sai in karbi lambar Hanif din, kada ki manta ki karbar min. ''Me zaka yi da lambar Hanif? Ta tambaya cike da damuwa. Ya fada cike da gadara, ''Me ake yi da lambar waya bayan kira? Zan kira shi ne kawai, kada ki damu bawai zan tona ki ba ne daga inda kika buya. Insha Allahu sai alkhairi. Ta dan yi jugum can ta gyada kai, ta ce, ''Zan tambayo maka lambar amma sai da yamma zan dawo gida, kada ka damu ba sai ka zo daukana ba. Ya gyada kai, ya ce, ''Ba damuwa, sai kin dawo din, Allah Ya bada sa'ar jarabawa. Ta amsa masa da, ''Amin na gode. Ta gaggauta rufo masa kofar mota ta yi saurin barin wajen. Ta kuwa yi sa'a babu jama'a a farfajiyar makarantar sosai, kasancewar sassafe ne. Abdul-Sabur ya dade a zaune a cikin mota kamar ba shi ne mai saurin nan ba, ya kasa tukawa ya tafi kasancewar damuwa, tausayi gami da jimamin hawayen da ya gani ya zubo daga idanuwan Umaimah. Tabbas Umaimah ta kasance abar tausayi, kuma abar tausayawa. Ta kasance marainiya, kuma ta bar danta ko *ya*yanta tamkar marayu. Zafafan hawaye ya dinga digowa daga cikin idanuwansa, har ya isa makaranta. Ya tuno da mahaifansa musamman mahaifiyarsa da ta sha fama da su suna kanana. Mutuwa ta dauke ta ga shi yanzu sun kawo karfin da za su iya taimakonta, amma ba ta nan. Tabbas duk mutumin da ya yi kokarin raba uwa da danta imaninsa ragagge ne, saboda tsananin soyayyar da uwa ta ke yiwa danta. Allah ne kadai isasshe, Shi ne mai rayawa, kuma mai kashewa, bayan Shi babu wanda zai raba soyayyar nan. ***************** Abdul-Sabur bai sake haduwa da Umaima ba sai bayan kwanaki uku, wato ranar asabar da yamma. Tabbas ya san gudunsa ta ke yi shi yasa ba ta yarda ta hadu da shi ba. Yana kwance akan doguwar kujerar falonsa ya hangota a tsaye akan baranda tana shakar daddadar iskar da ta ke busowa a yammacin wannan rana bayan da ruwan saman da aka yini ana yi ya dauke dif! Ya yi wuf ya mike ya fito barandarsa sai gasu kiri- kiri suna kallon juna. Ya yi mata murmushi gami da yi mata cikakkiyar sallama. Ta amsa masa ita ma gami da gaishe shi. Ya amsa mata cike da fara'a, ya ce ''Ya ya jarabawar? Karatun ne ya sa kika buya? To Allah Ya taimaka. Ta ce, ''Amin. Ga sakonka ma na karbo ba mu hadu ba shi yasa ban baka ba. Ya ji dadi da jin haka, sai ya yi dariya, ya ce, ''Yauwa na gode, amma ki ajiye min zuwa gobe da safe misalin karfe goma na safe mu hadu a gidan Faduwa. A ciki-ciki ta amsa masa, daga dukkan alamu ya fara takurawa rayuwarta fa. Tana jin nauyinsa ba zata iya yi masa musu ba. Abdul-Sabur ya lura da canji daga fuskarta, amma sai ya yi kamar bai san ta yi fushi ba, ya

Chapter 17 of 33