Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a dai-dai wannan lokaci. Ba su firgita ba don sun ganni a nutse na, cikin farin ciki da tsarabata kala-kala. Sai da garin Allah Ya waye sannan labari ya kai ko'ina aka ce na iso. Masu zuwa sannu da zuwa suka yi ta shigo min, ina ta rabon lemon bawo da biredi, yara kuwa suna ta karbar alewa. Na zauna na korawa Baffa da matansa bayanan karyar cewar, an tura mijina AbdulBasi aiki kasar Turawa da ni zai tafi, wani satin ne tafiyar. Dama idan kun tuna can baya na fada masa zamu kaura daga kasar nan. Baffa ya yi murna ya yi mana addu'ar fatan alkhairi, yayin da matansa suka nuna hassadarsu kiri-kiri a fuska ba haka suka so ba. Labari ya cika gari cewar Umaimah da mijinta za su kaura Turai da zama, har zuwa kallona suke yi har da masu shafa jikina wai suma su kwashi albarka. Allah Ya sa suma wataran su je. Bakin ciki ya rufe Matawata, kawayenmu suka dinga fada min irin mugayen fatan da ta ke yi min, wai dama ace mijina ya sake ni ya fasa tafiya Turai da ni na dawo rugar nan na zauna na ganta da Ilah bakin ciki ya kashe ni. Na sake godewa Allah da Ya sa na rufe bakina ban fadi aurena ya mutu ba, masu jin dadin suna da yawa. Sabitu ne da ni a cikin dakinmu mun saka fitilar kwai a gaba da littafi kai ka ce karatu muke biyawa, nan kuwa hira muke yi ta sirri. Na ba shi labarin zamana a Gombe tas da duk yadda aka yi. Na ba shi labarin tafiyata nan da *yan kwanaki. Sai ya fara hawaye ya tausaya min akan kunci da na shiga da kazafi da aka yi min. Sai ya nuna fargabarsa akan wannan tafiya da zan yi kasar da ban san kowa ba, kuma ba ni da kowa. Yana tsoro kada na je na fada hannun muyagu su cutar da ni, ko halin mutuwa a rasa *yan uwana. Na roke shi da ya kwantar da hankalinsa insha Allah zan je lafiya na dawo lafiya. Ina so ya rufamin asiri, kada ya fadawa kowa gaskiyar magana, saboda idan Baffa ya ji ni kadai na tafi hankalinsa zai tashi, ga shi da hawan jini. Ranar lahadi da sassafe na shirya tafiya na fito na fara sallama da *yan cikin gida, sannan na lelleka MAKWABTA har wajen mahaifiyar Ilah na shiga da yake har goben tana sona. Ta rungume ni ta fashe da kuka. Matawata ta kama kugu tana ta girgiza ta cika taf don fushi kamar zata fashe wai don na shigo gidan. Tun zuwana sai a ranar na ga Ilah, sai dai na jiyo muryarsa daga cikin gidanmu. Ya kalle ni sau daya nima na kalle shi mu dukkanmu sai muka sunkuyar da kai kasa, tsoron matarsa ya hana ya yi min magana. Na fice na bar ta a nan ni kyankyami ma ta ba ni, duk ta kazance da wani kodadden zani daurin kirji, ba riga. Kanta buyaya ba dankwali ba kitso, gashin nan duk ya kakkarye, bututu jikinta da jar kasa don babu sumunti, haihuwa kawai ta ke yi ciki da goyo. A lokacin ma tsohon ciki ne da ita. Baffa da Sabitu ne suka rako ni har kofar fita daga gari, idan Sabitu ya kalle ni sai idanuwansa ya cika da kwalla. Ya ce da ni, ''Adda Umaimah za ki je lafiya ki dawo lafiya ki same mu lafiya a cikin izinin Ubangiji. Kada ki manta kin tafi kin bar ni ba ni da kowa sai tsohon nan, ba Yafindo, ba Nasiba yanzu ke ma babu ke.... Muka rushe da kuka mu dukka har Baffa. Can Baffa ya ce, ''Umaimah fatana a gare ki shi ne ki je ki dawo lafiya, Allah Ya kare ki daga sharrin makiya, idan kin dawo kin same ni a raye to Alhamdulillah, amma idan kin dawo kin iske na mutu to ki yi min addu'a, Allah Ya jikaina. Tsufa ya zo min, lafiya ta yi karanci a gare ni, don haka ina daf da tafiya. Na yafe miki duk abin da kika yi min a duniya. Allah Ya tsare ki Ya ba ku zaman lafiya ke da mijinki da zuri'a ta gari. Sai muka sake fashewa da kuka, na kankame Baffa na ji kamar na fasa tafiyar. Da kyar na sake shi na juya na fara tafiya zuwa bishiyar da masu acaba suke tsayawa. Ina waiwayensu suna tsaye a inda na bar su, kowannensu yana sharce hawaye yana daga min hannu.. Umaimah ta rushe da kuka yayin da ta kasa ci gaba da labarin. Hawaye ya cika idanun Abdul-Sabur da Faduwa su ma. Ta ci gaba da cewa, ''Na hau acaba ina ta rusa kuka, ban daina ba har na isa garin Dukku na shiga motar Gombe. Na isa gidan gwamna a kurarren lokaci har an yi nisa a taro da kyar aka bar ni na kutsa cikin masu tafiya. MAKWABTAKA 24 Mai girma gwamna ya yi mana jawabai masu dadi gami da nasihohi masu ratsa jiki cewar mu yi karatu sosai mu ci jarabawa, babu ruwanmu da shiga kungiyar *yan iska, mu kama kanmu mu rike mutuncin garinmu da kasarmu. Sannan ya yi mana yayyafin albishir cewa kowanne dalibi daga cikinmu mu dari daya cur maza tamanin mata ashirin ya biya mana zunzurutun kudin makaranta har na tsawon shekaru ukun da zamu yi mu kammala karatun digiri dinmu. Sannan an budewa kowannenmu account a banki duk karshen wata za a dinga turo mana da kudin abinci da gidan haya, har dalla dari biyar. Sannan aka raba mana na'ura mai kwakwalwa (laptop) kowa daidaiya kauta. Iyayen yara suka yi jawabin godiya, yayin da aka yi addu'a aka tashi kowa ya je ya yi sallama da iyaye da *yan uwansa, yayin da ni da Hanif muka yi wajen Babansa. Ya ji dadi sosai da isowata, amma ya tambaye ni ina akwatin kayana, sai na nuna masa jakata a rataye a kafadata na ce, ba ni da jaka sai wannan kaya kala uku ne a ciki, sai tarkacen kayan kwalliyata da hotunana da takardun makaranta. Sai ya tausaya min, ya ce ni idan muka isa Abuja zai fadawa abokinsa wanda su ne jami'an Gwamnatin da za su raka mu har can Malaysia zai ba shi kudi ya sissiya min akwati mai taya karama, wacce ake ja da suturu na tsukewa wadanda ba atamfofi ba, don kada na fita daban. Sannan ya kara da cewa, 'iyaye sun karawa *ya*yansu kudi da zasu dinga kashewa, don haka zan baki kudi daidai da yadda zan ba wa Hanif ku dinga kashewa har shekara. Ku bude account a banki daban ku turo min da account number zan sakawa kowannenku naira miliyan daidaiya, zan canja muku zuwa dallar. Sai na durkushe a gabansa ina kuka ina ta godiya Hanif ma sai ya durkusa ya yi godiya. Abdul-Sabur ya buda baki don mamaki, ya ce, ''Allah Sarki bayin Allah ba sa karewa a duniya. Faduwa ta ce, ''Lamijo matarsa kuwa ta sani? Umaimah ta goge hawaye ta ce, ''Ba ta sani ba, don tun lokacin da ta fara nuna kishi da zargi ya nuna ya cire hannunsa daga kaina, ya nuna mata Hanif ne kawai zai tafi. Ya gargadi Hanif kada ya fada mata da ni za a tafi. Alhaji. Rabi'u ya hadamu da abokinsa Alh. Sani ya dinga kula da mu, daga Abuja har Malaysia. Ya ba shi kudi mai yawa ya rike muma ya ba mu dallar dari bibbiyu mu rike a hannunmu kafin mu gane gari mu fara kashewa. Muka dunguma cikin birnin tarayya a cikin zungurazunguran mota (bus) mai sanyin A.C ta gidan gwamnati. A hadadden hotel aka sauke mu a Abuja, mata dakunansu daban mu uku-uku, maza ma dakunansu daban. Washe gari aka kai mu Embassy inda aka sake tantance mu kowa da takardunsa (original) a wajensa, da takardunmu da aka turawa kowa daga makarantarsa a Malaysia (admission letter), babu wanda ya sami matsala, aka mayar da mu hotel muka sake kwana. ''Kin yi kawaye amma daga cikin *yan matan nan dai ko, kuna hira? Faduwa ta tambayi Umaimah. Murmushi Umaimah ta yi, ta ce ''Ai tuni na sawa raina babu ni babu duk wani bil'adama a duniya, mace ko namiji, yaro ko babba. Abdul-Sabur ya tuntsire da dariya ya ce, ''Ba ke babu bil'adama sai jinnu? Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Ai gara na hadu da jinnu da na hadu da bil'adama don sun wahalar da ni. Don haka ba na kula kowacce kawa, na girmi wasu, wasu sun girme ni, wasu shekarunmu daya. Sun shisshige min sun ga babu fuska har sun rabu da ni. Mai girman kai suka dauke ni, *yar wulakanci, suna tunanin ni *yar wani hamshakin mai kudi ne, musamman da suka ga Alhaji Sani yana ta kula da ni da Hanif. A Abuja Alhaji Sani ya yi min siyayyar kaya kamar riga da siket kala biyu, riga da wando (jeans) kala biyu, abaya kala biyu, *yan kananan gyaleluwa, takalma da jaka kala biyu. Ya zuba a cikin dandatsetsiyar akwati *yar madaidaiciya dai dai ta shiga jirgi ya kawo min. Ai tuni na yi wurgi da zannuwana kala daya na dauko wata super holland sabuwar riga da zani, kacokan na bawa wata miskina sadakar kayan da jakar. Abu kamar wasa ranar litinin da daddare sai gamu a jirgi Egypt air ne, da ya kwashe mu daga Abuja sai birnin Cairo. Wannan shi ne karo na farko da na taba hawa jirgin sama a rayuwata, don haka maganar kauyanci ma an san dole ne na yi shi. Faduwa ta hau tafa hannu tana murna ta ji an hau jirgin kasarsu, an sauka a garinsu. Ta ce, ''Ya ya kika ga Cairo? Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Airport ya yi, kuma an dibe mu a mota an kai mu wani hotel a cikin gari mai suna Novotel aka bamu daki mutum bibbiyu, ga abincin safe da na rana, sai yadda ka ga dama zaka diba. Awannai goma sha biyu muka yi daga shida na safe zuwa shida na yamma. Tun karfe biyar aka dawo da mu filin jirgi muka shiga muka fara lulawa doguwar tafiya daga Egypt zuwa Bounkok awa goma sha daya, daga Bonkok (Thailanda) zuwa Malaysia awa biyu. Abdul-Sabur ya ce, ''Au sai da kuka tsaya a Bonkok sannan kuka taho? Umaimah ta ce, ''Eh, mun yi transit na awa biyu an sauke fasinja kuma an debi wasu fasinjoji zuwa Malaysia. Mun iso Malaysia daf da magruba, ba mu sha wahalar binciken immigration ba saboda a tawagar gwamnati muka taho ga jami'an gwamnati wadanda suka san gari ga takardun kowa tsaf-tsaf. Kai tsaye cikin Kaula Lumfur (KL) aka shigo da mu wani babban hotel ni har yau na ban san wanne ne ba muka kwana. Washe gari aka hau rarraba mu, ashe ba mu dukka ba ne a makaranta daya, makarantu biyar ne za a rarraba mu ashirin-ashirin a kowacce makaranta. Ya danganta ashe da course din da ka zaba ka cike. A makarantarmu FTMS mu ashirin ne mata biyar maza goma sha biyar. Sai Intii Nilai su ma garin Nilai za su zauna su ashirin maza sha takwas mata biyu, sai su Hanif da suke 'Legenda, sannan wasu aka kai su 'Help Uneversity wasu kuwa 'Putra Jaya' aka kaisu, a 'Apiit University' kowa course mai kyau ya zaba kamar ni da nake karantar Software Engineering wasu medicine, wasu Computer Engineering da dai sauransu. Aka rarraba *yan rakiya kowannensu ya dauki tasa tawagar ashirin-ashirin zuwa garin da makarantar ta ke. A lokacin muka yi sallama da Hanif har ya yi kamar zai yi kuka, ni kuwa sai da na yi kukan ma. Ya tafi 'Legenda' kauye ne mu kuwa a cikin 'KL ne, na ci sa'a kuwa Alhaji Sani shine jami'inmu. Kai tsaye cikin makarantarmu FTMS mu muka nufa ba mu tsaya wata-wata ba aka nuna mana katon gidan haya a kusa da makaranta mata mu biyar bangarenmu daban, amma mutum bibbiyu a daki daya, daya dakin kuwa su uku ne. Ni da Aisha bingyal aka hada mu ita ma mai ji da kai ce kamata, don haka kowa ya juyawa kowa baya, tunda kowa da gadonsa. Washegari babu abin da muka yi sai cuku-cukun registration da cike-ciken forms. Da muka gama sai aka daddanka mana account number mu da ATM aka nuna mana bankin da zamu dinga zuwa daukar kudi. Bayan wannan sai Alhaji Sani ya ja ni zuwa banki daban ya bude min sabon account wanda Alhaji Rabi'u ya ce a bude min na musamman zai sako min naira miliyan daya. Alhaji Sani ya yi waya da jami'in da yake Lagenda ya umarce shi da ya budewa Hanif ma, ya turo masa da account number, haka kuwa aka yi aka budewa Hanif shi ma. Sai na ga duk sun sayi layuka ana ta musanya lamba, sai ni naki siya fur. Alhaji Sani ya ba ni waya na yi magana da Alhaji Rabi'u ya jajjada min zai sako wannan kudi da ya yi mana alkawari, na yi ta godiya. Tun kafin Alhaji Sani ya bar Malaysia ya tabbatar min an sako kudin nan muka je banki aka duba min dallar dubu takwas tabbas nasan na yi sallama da talauci a duniya. Ban san da yaren da zan yiwa bawan Allah nan godiya ba. Alhaji Sani ya sake kira min Alhaji Rabi'u a waya na fada masa da bakina na ga kudin sannan na sake yin godiya, ya sake yi min nasihohi da na yi karatu, kuma na kama kaina ban da bin samari da lalatattun kawaye. Wannan shine labarina. Umaimah ta dube su tana murmushi. Suka yi ajiyar zuciya a lokaci guda, Abdul-Sabur ya gyada kai. Ya ce, ''Wannan labari ya kayatar da ni kamar kada ya kare. To amma ya aka yi kika baro can Hostel kika dawo nan gidajen? Umaimah ta yi murmushi ta ce, ''Da na yi wata guda na gane gari, ina ta hira da malamai ina tambayarsu dokoki da tsarin karbar hayar gidajensu, sai na ji da sauki babu tsada ai zan iya kama gida ni kadai. Suka tabbatar min akwai gidajen haya kusa da makarantar nan wanda ba sai na hau mota ba zan iso. Ba ni da matsalar kudi, don haka na ba wa wani malami dan kasa ne cigiya, ba tare da bata lokaci ba ya samo min nan, na tarkato na dawo. Daman ba dadi nake ji da dukka daliban ba musamman Aisha Bingyal da muke daki daya, na kasa sakin jikina da ita, na kasa yin ko hira da ita balle mu saba. Dan Allah ta yi hakuri ta yafe min, wallahi ba halina ba ne tsoro nake ji saboda abubuwan da aka yi min a baya. Har yau haushina suke ji, na ware ni kadai, a ji kawai nake shiga a gama lecture na fito na dawo gida. Sai ta dauro dole a yi magana sannan nake magana da su. Kamar misali idan an ba mu group assignmen ko practical a lab. Ba ni da waya balle na kira Hanif ya ji labarina, ba ni da waya balle mu dinga gaisawa da Alhaji Rabi'u da Alhaji Sani, ban kira kowa ba balle a san ina raye ban ki ba dai ko Hanif yana da lambar wasu daga cikin *yan makarantarmu ya tambaye ni ace masa ina nan bana kula kowa. Ni kuwa bakin hali da kyaliya ba halina ba ne, saka ni aka yi dole na zama haka saboda duk wanda na amincewa sai ya zalunce ni. Ta sunkuyar da kai ta dafe ta yi shiru, tana mai takaicin abubuwan da ta tuna a baya. Abdul-Sabur da Faduwa kuwa suka zuba mata ido kawai suna kallonta, suna masu tsananin tausayinta. Can ya yi gyaran murya ya fara magana cikin rarrashi da nasiha. ''Umaimah, na san MAKWABTAKA da kawaye sunyi miki ba dai-dai ba, amma kada wannan yasa ki zaci duk wasu MAKWABTA da zaki yi nan gaba su ma halinsu daya, ki dauka su daban mu daban. Ki dauke ni a matsayin babban yayanki Faduwa kuwa idan ba ki dauke ta uwa ba, to ki dauke ta a matsayin kanwar uwa (Aunty) saboda ke yarinya ce karama a cikinmu, babu zancen yi miki gulma, kazafi, cin amana da dai sauran tarkace. Rashin ilimi ne su ma can da kuruciya yasa suka yi miki haka. Umaimah, rayuwa ba zata yiwu a haka ba, babu yadda za a yi ki ware ki ce kin daina gaisawa da kowa a duniya musamman MAKWABTA. Ina kara baki hakuri da ki cire duk wannan ra'ayi naki ki kyautatawa MAKWABTA da duk wanda Allah Ya hadaku zama tare.... Faduwa ta ci gaba da cewa, ''Da kika ba mu tarihin rayuwarki sai na ji na fara sonki da na ji dalilinki, don a da haushinki nake ji, saboda nuna mana tsana kirikiri da kike yi. Yanzu mun zama daya, ke ma kanki idan kina shigowa cikinmu rayuwa a Malaysia zata fi yi miki dadi akan rayuwar kuncin da kike ciki ke kadai. Ki shigo cikinmu mu zauna tare, mu yi hira, mu zaga gari tare mu ba wa juna shawara. Allah Ya hada mu da babban Yaya Abdul-Sabur mai kaifin hankali, hakuri da hangen nesa, shi yake ba ni shawara koda yaushe. Ki dinga sauraron abubuwan da yake fada miki idan kika bi ba zaki yi nadama ba. Dadin kalaman Faduwa sai ya yi mata kama da na Matawata koda yaushe tana ce mata. ''Umaimah mu hada kanmu, kada mu yi fada kawaye su yi mana dariya, don haushin kawancenmu ake ji a garin nan, an kasa kunne ana so aji wata baraka a tsakaninmu. Amma a karshe ita ta fara cin amanata a duniya. Ta dago ta dubi Abdul-Sabur murmushi kadai ya yi mata yana yi mata kallo na tausayi da tsan-tsar kulawa. Sai ta gan shi sak Ilah haka yake yi mata, karshe ya ci amanarta. Sai ta ji da kyar idan zata amincewa da wadannan mutane kamar yadda suke tunanin zata yi. Ta yi zumbur ta mike tsaye ta wawuri mukullin gidanta babu abin da ta fi so irin ta ganta a gidanta ita kadai. Faduwa ta ce, ''Ki bari mu yi sallar azahar a jam,i, Abdul ya ja mu sai mu yi addu'a Allah Ya yayewa kowa damuwarsa, Ya biya mana bukatunmu, Ya kare mu daga sharrin makiya, Ya ba mu zaman lafiya a tsakaninmu. Umaimah har ta kai bakin kofa ta fara tafiya don ta gaji da dadin bakin Faduwa, har ta fara ganin kamar cutarta ta ke shirin yi. Faduwa ta mike da sauri cikin wasa zata je ta kamo hannunta ta dawo da ita, sai ta ga Umaimah ta zabura ta ja da baya a firgice. Abdul-Sabur ya dagawa Faduwa hannu alamar ta dawo ta zauna ta rabu da ita ta tafi. Umaimah ta juya da sauri ta fice daga cikin gidan, sai ta ji ta tamkar wacce ta fito daga kurkuku don ta takura da yawa zaman da ta yi a cikinsu na tsawon awoyi. Wai me me ya kai ta wannan katobarar a gurin mutane? Me yasa ta manta aminci ne duk ya jawo mata matsala a rayuwa? Ta shige lift ta haye sama ta isa gidanta, hannunta na rawa ta bude gidanta ta shige ta mayar da kofa ta kulle ta je ta haye kan kujera ta takure tana huci don an taso mata da dumbin takaici da abubuwan bakin cikin da aka guma mata a baya. Abdul-Sabur ya dubi Faduwa ya ce, ''Kin ga abin da nake fada miki ko? Daman na ce ki yiwa yarinyar nan uziri tana da dalilinta na yin haka, ashe an sha ta, ta warke shi yasa ta shiga tsoronmu. Ki bari a hankali zata gane mu su waye, kuma da wacce manufa muke bin ta. Ta sha wuya ne a rayuwa, ta rasa kowa, ta rasa komai tana karamarta. Umaimah ta cancanci a tausaya mata, a rarrashe ta, a daina damuwa da duk wasu halaye mararsa dadi da zata nuna. Ita a ganinta idan ta yi haka shi ne zata sami sauki a rayuwarta. Faduwa ta ce, ''Ai dole ta tsorata da mutane, sun ci amanarta, to Allah Ya sa mu dace. Abdul-Sabur ya ce, ''Amin Yayin da ya mike gami da yin mika da hamma. Ya dubi Faduwa ya ce, ''Yau kin hana mu baccin safe, daman ke baki iya ba. Da tuni sai yanzu zan tashi na yi sallah sannan na karya kumallo, amma yanzu cin abinci biyu kika sa mu. Daman ke yini kike kina dora tukunya, kullum bakinki yana ciye-ciye. Suka kwashe da dariya su dukka. Faduwa ta ce, ''Au kana nufin ban sami ladanka ba, na zaunar da yarinyar da ka dade kana so ta amsa gaisuwarka ma balle ta zauna da kai ku ci abinci a teburi guda ku yi hira. Ai na yi jihadi ba don ni ba wallahi har abada ba zata amsa maka ba. MAKWABATAKA 25 Ya juya ya tafi yayin da Faduwa ta tura kofarta ta rufe. Sallah ta yi ta kwanta, ta dade bacci bai dauketa ba tana tuna labarin Umaimah shi ya fi sosa mata zuciya. Abdul-Sabur ma haka da ya yi sallah a masallaci sai ya koma gida ya kwanta, labarin Umaimah shi ne yake yi masa reto a zuciya yana tausayinta yana tunanin hanyoyin da zai bi ya kawar mata da damuwar da ta addabe ta. Yayin da Umaimah ma bayan ta yi sallah ta kwanta bacci ya gagari idanuwanta, labarin Faduwa da Abdul-Sabur ne ya ke yi mata kewaye a zuciyarta. Hakika ashe ba ita kadai ba ce ta fuskanci matsalar rayuwa a duniya, a she su marayune, ba su da aure ba *ya*ya. Gara ita ma da ta taba auren har ta haifi da, ko ba ta sake aure a duniya ba nan gaba babu damuwa, ko mutuwa ta yi ta bar wanda za a kalla a tuna da ita a yi mata addu'a. Ba kamar Faduwa ma ita mace ta fi ba ta tausayi ta girma har ta manyanta babu aure, tabbas ta cancanci a tausaya mata. Ta shiga jero addu'oi Allah Ya fitowa da Faduwa miji na gari ta yi aure ko sau daya ne ta samu ta haihu. Asuba ta gari Abdul-fadu-maimah!!! ********************** Faduwa da Abdul-Sabur ne suke zaune a gidan cin abinci na Golden Folk da yake cikin KL. Faduwa ta kurbi lemo ta dubi abokinta Abdul-Sabur ta tabe baki cikin harshen Hausa suke magana kamar yadda suka yiwa juna alkawari sun daina yiwa juna Turanci sai Hausa. Ta ce, ''Mai hali baya fasa halinsa, da Umaimah nake, ka ga yau kwana hudu ke nan rabuwarmu ba mu sake jin motsinta ba balle mu ganta. Abdul-Sabur ya ce, ''Ta daina ma fitowa baranda, amma dazu ta fito da safe ta tsaya. Ta iske ni a tsaye a baranda kallo daya ta yi min ta sunkuyar da kai ba ta gaishe ni ba. Sai na ki yi mata sallama don idan na yi mata zata ji na takura mata, dole sai ta amsa tunda a musulunce ne. Faduwa ta gyara zama ta kai lomar salad a bakinta, ta ce, ''Yaya kuka yi daga karshe? Abdul-Sabur ya ce, ''Tsayawa na yi ina kallonta kawai, sai ta bata rai ta turo baki ta dube ni, ta ce, ina kwana? Irin na takura mata din nan. Sai na yi murmushi na ce mata, assalamu alaikum. Ta juya ta shige gida ta rufe kofa. Suka kwashe da dariya su dukka. Faduwa ta ce, ''Har yanzu fa ba son zamanta ta ke da mu ba, gani ta ke mun takure ta. Abdul-Sabur ya ce, ''Za ta ware nan gaba mu rage shisshige mata, idan ada bata san mu ko su waye ba yanzu ta sani. *Yan uwanta musulmai, Hausawa, duk inda ta je zata dawo ta neme mu. Yarinyar tana burge ni ne haka kawai, ban san dalili ba. Ba wai nace tana kyautatawa ba amma sai ta kalle ka ta harare ka kuma sai ta ji kunyar ka ta sunkuyar da kai, ta kasa hada ido da kai. Faduwa ta ce, ''Ba ka karsa ba, ba ka ce ga ta da kyau, fara mai gashi, ga dirin jiki dai-dai kauna ba. Abdul-Sabur ya harare ta, ya ce, ''Ni fa bana son ki dinaga kawo maganar so idan ana maganar zumunci. Faduwa ta ce, ''Ni dai na yi maka kamu, zan zauna da ita na isar da wannan sako naka. Kafin ta dago da kai ta tsinkayo Abdul-Sabur ya kai bakin kofa zai fice, ta wawuro jakarta ta biyo shi da sauri. Daman ya biya kudin abincin ko rabi ba su ci ba, ya tashi ya bar abincin. Wai shi nan fushi ya yi. Ta yi ta bin sa tana yi masa magana ya kyaleta har sai da ta sauko, ta shiga ba shi hakuri. Ta ce, ta fasa ba zata fadawa Umaimah ba, daman wasa take yi masa, sannan ya fara amsa mata. Su ka shiga jirgin kasa suka koma gida. Ranar lahadi da sanyin safiya misalin karfe tara, sai ga Faduwa a tsaye a kofar gidan Umaimah tana ta danna kararrawa. Yayin da tsoro, fargaba, gami da dimaucewa suka ruftowa Umaimah. Tayi figigit ta fito daga cikin bargonta ta diro daga kan gado ba shiri ta ruga da gudu zuwa bakin kofa, ta leka ta jikin *yar huda dan taga me buga mata kofa. Sai kuwa ta hango Faduwa dan haka mamakin sai ya ragu. Ta bude mata da sauri gami da yi mata murmushi da sannu da zuwa. Faduwa ta ji dadi da taga ta karbe ta da farin ciki, itama sai ta sake samun kwarin gwiwa ta shigo da fara'ar ta. Umaimah na gaba Faduwa tana biye da ita har kan kujerun falo suka zauna suka sake gaisawa. Zata je ta dauko mata shayi da lemo Faduwa ta tsayar da ita ta ce ta bar shi a koshe take daman ta zo ne dan ta sanar mata yau ranar haihuwar Abdul-Sabur ta zagayo (birhday) suna gaiyatar walima da yamma. Umaimah tayi dim! Kadan sannan tayi gyaran murya ta gyara zama zata yi magana, Faduwa ta daga mata hannu ta katse ta. Ta ce ''Kada ki ba mu wani uziri ki ce ba za ki sami damar zuwa ba dole ki je. Ki shirya da yamma ki fito ni da ke da Abdul ne kadai. Sai Umaimah ta yi murmushi ta langwabe kai ta ce ''to Allah Ya kaimu anjiman din zan je. Faduwa ta yi dariya ta mike da sauri ta dafa kafadarta ta ce, ''Yauwa Baby na zan biyo miki anjima sai mu tafi. Umaimah ta raka ta har bakin kofa suka yi sallama kowannensu cike da fara'a. Ta tafi sannan Umaimah ta dawo ta zauna tana ta fargaba da sake-saken yadda zata bijire taki zuwa dan bata son zuwan kwata-kwata. Tana idar da sallar la'asar sai ta sake fesa wanka ta tsala ado da wasu sababbin kayanta wanda bata taba sakawa ba, riga fara me layi-layi baki da bakin dogon wando (jeans) sai ta sami dan yalolon gyale ta nade kanta da shi kalar fari da baki ne, sannan ta saka takalmi coge mai tsini sosai da bakar jaka mai kyawun gaske. Ta dora da farin gilashi a fuskarta mai hasken gilashi. Tana gama shiryawa tana tsaye a gaban madubi tana sake saka hoda da jagira sai ta ji kararrawar kofar gidanta tana kara ko kokonto bata yi ta san Faduwa ce. Sai ta fito da sauri bata bata lokacin ta ba na lekawa sai ta bude kofar ta fito gaba daya. Faduwar ce kuwa itama ta dandasa ado ku san kwalli iri daya suka yi a tare. ''Kin yi kyau kanwata. ''Faduwa ta fada a lokacin da take kallon Umamai sama da

Chapter 15 of 33