Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kallo ne. Da zarar Abdul-Sabur ya dube ta sai ya fara godiya ga Allah da Ya bashi Umaimah. Daga wajen Dinner aka dauko amarya sai aka nufi gidanta, Allah mai halitta ita kanta amarya bude baki ta yi tana kallon kayan alatu da ginin gidan kansa. Wasu abubuwan ma basu taba ganinsa ba duk zaman da suka yi a Malaysia. Ya dankara gida ya zuba kayan alfarma faluka kala-kala kowanne da kalar kujerunsa da labulayensa haka dakuna daban-daban gadaje iri-iri *yan kamfani. Haka bangaren Ummana Fuse itama ya hadu kai ka ce itama amaryar ce, katon falo, dinning area da dakuna guda biyu kowanne da bandakinsa a ciki, a ranar ta tare da kayanta ita da danginta na Ghana. Khausar kuma ta tafi da danginsu na gwarzo gidanta suka sauka acan. Babu abinda Umaimah take yi sai kukam dadi, ana ta lallashi gami da yi mata murna da addu'oin Allah Ya dauwamar da ita a gidanta ya basu zuriya ta gari. Kowacce ta ga kyakkyawan gida sai ta makale ta ce anan zata kwana, manya suka ce ba za'a batawa amarya da ango gidansu ba kowa ya fito ya tafi masaukin da aka ajiye su dazu ga motoci can a kofar gida suna jira. Dakyar amarya ta roka aka barta da kawayenta guda uku su taya ta kwana, Aisha, Faduwa da Khadija sai kuma *ya*yanta su Babangida. Abdul-Sabur ma a wajen abokansa ya kwana a hadadden Hotel din nan Nicon, amma fa su dukkansu amarya da angon a zaune suka kwana bacci ya gagare su dan murna da begen junansu suka hana masu taya su kwana bacci sai hira ta barke. Washe gari bayan kowa ya yi wanka daman Abdul-Sabur yayi magana abin karin kumallo da masu Hotel, sai suka shiryowa baki abinci kala-kala sai abunda kake so zaka zuba kowanne gida an mika na su. Bayan kowa ya ci sannan aka sake haduwa a gidan amarya, aka dinga hayaniya ana raye-raye aka sake kallon abun da ba'a karewa kallo jiya ba, sannan aka yi ta daukar hotuna ba adadi. Daga karshe aka dinga jifgowa amarya gudunmawa da yawa daga bangarori daban-daban. Kudi mai sunan kudi kuwa baya kirguwa, a take ta zama miloniya saboda manyan attajirai abokan Abdul-Sabur turawa basa harka da Naira daga Pounds sal Dallars haka suka dinga zarowa suna mika mata. Kawayenta da *yan Uwan ango sun yi kokari sun hada mata kudi da yawa. Haka Hanif ma ya aiko mata katuwar ambulan da kudi Naira dubu dari ya ce shi da sauran abokansa maza suka hada mata. Faduwa da Sagir ma kudinsu mai yawa a ambulam suma kuma Dalla ce suka bata. Ga babba da kansa Uncle Hamza ya yi musu yayyafin Pounds, gudunmawarsa ta fi ta kowa yawa. "Shin mafarki nake yi ko idanuwana biyu? Umaimah take tambayar zuciyarta. Dan ta rasa da bakin da zata yi wa jama'a godiya. Sai kuka kawai take yi da alama ana yin kukan dadi dan ita ta rabu da kukan bakin ciki kuma a rayuwarta. "Talauci a sauka lafiya, marhaban da zuwan arziki" Inji zuciyar Sabitu a lokacin da yake hango kudi yana ta ambaliya a hannun *yar Uwarsa. "Samun naku shine namu. In ji almajiri Sabitu. "Allah Ya bada zaman lafiya, mu mun tafi Umaimah sai watarana. Haka kowannensu yake ta fada a lokacin da suka shiga motocinsu zasu tafi. Dakyar aka banbare Babangida da Bilal daga jikin Umaimah, sai hankalin ta ya sake tashi matuka. Umaimah bata daina rusa kuka ba, wannan karon kukan na bakin cikin rabuwa da *yan uwa da kuma gida ne, dan kowa yabar gida, gida ya bar shi. Tana ji tana gani kowa ya tafi ya bar ta, Aisha da Umaimah suka rungume juna suka yi ta kuka ba adadi har sai da suka saka jama'a da dama kuka. Saboda tausayi, tabas sabo turken wawa ne. Faduwa da Sagir dinta kuwa ba su yi sallama gaba daya ba zasu tafi su dawo dan ba yanzu zasu koma Cairo ba sai ta zaga dangi ta nuna mijinta da *yarta. Bayan ta zagaya gidan danginta na Abuja, Kaduna da Zariya zasu wuce su gaisa da dangi. Sai ta wuce Kano nan ma akwai su daga nan sai su wuce Sokoto mai dungurungum in da cibiyar take, daga dukkan alamu zata dade a kasar. Abdul-Sabur ne ya dauki nauyin basu mota da direban da zai kewaya ko ina dasu. *** Kowa ya yoye babu kowa kuma gida ya rage daga amarya sai angonta sai kuma so da kauna sa suke tsakani. Dan Ummana Fuse ma da mai aikin da aka daukar mata duk gidan Khausar suka gudu, da taro ya watse sai ta ji zaman babu dadi, suka tafi can zasu yi kwanaki sannan su dawo. Dakyar Abdul-Sabur ya lallasheta ta shigo gidan daga bakin get, ya dauko nankici daga aljihunsa mai kamshin gaske ya mika mata, ta karba a sanyaye ta goge hawaye. Cikin tattausan lafazi yake magana. Ya ce "Yanzu Umaimah har kuka kike yi dan *yan uwanki sun kawo ki wajena sun tafi sun bar ki? A tunanina ni ne kadai mutum daya tak da zaki so ki dauwama tare da ni. Ta gyada kai ta ce "Haka ne. Ya ce "To meyasa kike kuka alhali kin gama kukan rabuwa da Baffa tun acan? Idan baki manta ba na taba fada miki cewar kin daina zubar da hawaye daga ranar da kika hadu da ni. Ki yi shiru ki daina kuka Umaimah Allah ne gatanki, Abdul-Sabur ne gatanki. Kin rabu da maraici daga yau, kin rabu da takaicin da namiji, kin rabu da cin amanar makwabtanki kuma kin rabu da babu insha Allah. Farin ciki ya rufe Umaimah ta yi sauri ta durkusa a gabansa ta yi masa godiya, ya girgiza kai ya mika hannu ya tashe ta tsaye. Ya ce "Ki daina yi min godiya, ke dolena ce babu abinda ba zan iya yi miki shi ba aduniya. Ta yi murmushi ta lumshe ido ta ce "Ko baka fada ba na san da haka, na yarda da tarbiyarka, ka cika dan halak. Na maka alkawarin nima zan zama baiwarka babu abinda ba zan iya yi ba in har zan kyautata maka. Ya yi ajiyar zuciya ya yi murmushi ya ce "Na yarda da tarbiyyarki nima kuma na yarda da son da kike yi min na tsakani da Allah. Mu je daki mu yi alwalla mu yi sallah raka'a biyu mu godewa Allah, mu kuma roke Shi Ya kare mu daga duk wata fitina da ke cikin aurenmu. Umaimah ta bishi suka shiga daya daga cikin maka-makan dakunan da suka jere a saman bene. Babu abinda yake tashi a cikin dakin daga sanyi Ac sai kamshi na alfarma. Tabbas idan kana cikin dakin nan ba zaka san yanayin da gari yake ciki ba, dare ko rana, zafi ko sanyi, guguwa ko ruwan sama. Dan haka ango da amarya suka yi lif a cikin ni'ima basu sake tunawa da hayaniyar waje ba, sai ka rantse babu bil adama a cikin gidan nan. Asuba ta gari Abduumimah. Abdul-Sabur yana jin dadin zama da amaryarsa sosai ya same ta mace mai ladabi da biyayya da godiya. Ba ta da kwadayi haka bata karya da dogon buri irin na *yan matan zamani, duk abunda ya bata sai ta karba da murna ta yi godiya. Ga ta mace mai kunya da tsoron Allah dan akwaita da ibada, ya yarda da ita ya san ko baya nan ba zata ci amanarsa ba. Tana masa biyayya matuka dan bai taba hana ta abu ta yi ba, haka bai taba saka ta abu tayi masa musu ba. Abunda ya kara masa sonta shine tana kula sosai da tsohuwar kakarsa wato Ummana Fuse. Ita ce mai yanken farcenta, ta tsefe ta wanke, ta kitse mata gashinta. Haka kawai sai Umaimah ta shiga kasuwa ta siyo mata atamfofi ta kai mata dinki, ta kawo ba tare da kowa ya sani ba kuma da kudinta. Sai dai Ummana Fuse ta fada musu shiyasa Khausar ma take matukar son Umaimah har take fadawa Abdul-Sabur cewar ashe ta so tayi kuskure da ta so hana shi auren Umaimah a Malaysia. Rayuwa kenan duk wanda yayi zalunci tun daga duniya zai fara ganin ba dai-dai ba. Sai ga Faduwa ta dawo daga Sokoto wurjanjan a gidan Umaimah hankalinta a tashe. Har hankalin su Abdul-Sabur ya tashi da suka ganta a haka, kafin ta basu labari. Ta fayyace musu irin abubuwan da ta gani a Sokoto shine ya tayar mata da hankali. Suka gyara zama suka tambaye ta me ta gani? Ta zauna ta basu labarin komai ta ce "A sakamakon hanata gadon Mahaifinta da suka yi sun hadu da bala'ai kala-kala gidan gaba daya babu wanda ya ci gaba. Talauci ya ruftowa, matan Babanta da *ya*yansu haka ma kawunnanta komai ya kare. Gaba daya kuka suke suna neman gafararta wai sunsan sun zalunce ta, yanzu abincin da zasu ci ma ya gaggaresu. Sai ita ta dinga taimaka musu duk da *yan kudin da suka rage ya kare a can. Yanzu ma akwai alkawuran da ta yi zata aiko musu da kudi idan ta koma Cairo. Har da masu rokarta a cikin kannenta wai zasu biyo ta Cairo ta samar musu aiki koda share-share ne saboda talaucin ya ishe su, ta ce a'a ba sai sun biyo ta ba zata dinga yi musu aike. Abdul-Sabur ma yayi alkawari idan ya tashi bayar da taimako zai dinga kai musu agaji. Sati guda cur Faduwa da Sagir suka sake yi a gidan su Umaimah sunji dadin karramawar dasu Umaimah suka yi musu sun ji dadin zama a Abuja dan an kewaya da su ko ina, suna ta sha'awar ango da amarya yadda suke zaune lafiya cikin tsantsar so da kauna. Ba'a son ransu suka rabu ba, sai suke ji kamar su ci gaba da zaman kamar yadda suka zauna a Malaysia. Idan suka zauna sai su raba dare suna hira, har sai da Sagir ya fara koyon Hausa sabida tsabar Hausa da yake ji idan suka hautsine da hira. Kyautar girma su Abdul-Sabur suka yi musu, suka kaisu filin jirgi suka hau suka tafi Abdul-Sabur yayi musu alkawari zasu zo Cairo suma su kwana biyu Asuba ta gari Abdulmaimah! ** Allah cikin ikonSa ya cikawa Abdul-Sabur gaba daya burinsa daya kudira na taimako, gaba daya alkawuran daya dauka sai da ya cika su, tun kafin shekara ta zagayo. Shi yayi komai a auren Sabitu da Aliya, haka Ilah da Furera, amma Baffa ya hana su tarewa a Gombe ya ce su ci gaba da zama a Dugge anan suka saba iyaye da kakanni. Gidajen sumunti Abdul-Sabur ya giggina musu a garin masu kyawun gaske, haka gidan Baffa gaba daya aka sauke na kasa aka kafa na siminti, sannan ya ginewa Dagaci nasa shima na siminti, sai suka haskaka garin. Ya gina katafaren gida a cikin Gombe a unguwar masu kudi, na Umaimah ne idan sun zo gari suke sauka. Dan zamanta a Gombe ya so ya fi na Abuja yawa saboda tana da abubuwan yi a garin dole sai tana nan zai yiwu. Abdul-Sabur ya fahimce ta, bashi da matsala ga saukin kai idan ta taho sai ya biyo ta su zauna. Umaimah bata manta da mutanen garinsu ba. Abubuwan da garin zai ci gaba take yi musu hanya a gwamnati, ana saka su a cikin lissafi yanzu. Rubutu take yi a jaridu da mujallu akan a dinga tunawa da Rugage ana tallafa musu da abubuwan more rayuwa kamar irin na burni. Dan suma mutane ne, *yan kasa, kuma *yan jiha. Dan suna jefa kuri'a idan lokacin zabe ya zo, saboda haka suna da alhaki akan gwamnati. Nan da nan ake sauraron kiranta dan su Hanif sun sami aiki a cikin gwamnati sune a gaba-gaba ana damawa da su a siyasa da mulki. A kowacce ma'aikata Umaimah sai ta ga kawarta ko abokinta ne da suka yi karatu a Malaysia masu rike da wajen dan haka nan da nan takardarta take isa gaban gwamna, kuma su saka baki ayi mata abunda take so. An kai ruwan fanfo garin Dugge, wutar lamtarki, service din waya, anyi titina, da uwa uba Makarantar boko da malamai kwararru. Da kanta ta zo ta tara iyayen yara ta yi musu nasihu na wayar da kai akan su saka yaransu a makarantu dan su yi ilimi kamar yadda ta yi, suma su inganta rayuwarsu. Tabbas Umaimah ita ce babbar musali, ita ce abar da zasu yi kwaikwayo da ita, nan da nan suka yi amanna da wannan kira nata su saka *yan*yansu a makarantu. Makarantun Islamiyya ta bude da kanta ta dauko malamai kwararru ta zuba suke koyarwa har da Sabitu da Ilah, tana biyanzu albashi duk wata.... Shafin karshe a shafe yake ma'ana rubutun ya ba ce don haka na ke sanar da ku cewa mun yi Bankwana da MAKWABTAKA ayau. Kuma nima nayi bankwana daku ayau. Alhamdulillahi. Ina godewa Allah da yardarSa da Amince war Sa daya nuna mana wannan lokacin na ranan karshe a littafin Makwabtaka. Ina mai godiya a gare ku en uwa da addu'oin ku da fatan alkhairi a gare ni. Nagode.. Nagode.. Nagode sosai Allah yabar xumunci. Ina kuma mai nemon afuwa da yafiya ga duk wanda na batawa ko wani maganar da baiji dadi ba ko wajen jinkirin post ko wajen kuskeren rubutu da sauran su. Na yafewa kowa tsakani na da ku baki daya. Allah ya yafe mana kura-kuren mu baki daya manya da kanana. Aamiin. Sannan ina mai nemon addu'r ku Auntyna bata jin dadin jikin ta kwana biyu kuma nima mun koma makaranta dukka muna baran addu'o'i daga bakunan ku masu Albarka. Allah yabiyawa kowa bukatun sa na Alkhairi... Aamiin. Sai wata rana... Wa'assalam.. Abbas Abdulkadir Hada Ebooks dinnan ya zo maku ne daga shafin http://hausaebooks.cf Ku ziyarci shafinmu don daukio wasu ebook din akan wannan adireshi http://hausaebooks.cf An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 33 of 33