Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ci gaba da yi mata tambayoyi game da jarabawa, eh ko a'a kadai ta ke ambato yayin da ta shiga tunanin yadda zata shige gida ta rabu da shi. Da ya gane sai ya yi mata sallama ya shige abunsa ya barta a tsaye tana hararar kofarsa. Asuba ta gari Umaimah Bello!! **************** Washe gari ranar Lahadi kenan ta dade tana sake-sake a ranta ta ji kamar ta je gidan Faduwa su hadu ko kada ta je. Karfe goma har ta wuce da minti goma Umaimah na zaune a falonta bayan ta shirya tsaf ta kasa tashi ta fito. A bayyane ta ke mita, ''Wai shi wannan mutumin ba zai daina shiga harka ta ba? Lallai-lallai sai ya yi min katsalandan a cikin al'amurana? Ni daman tunda na ga ya siyo min waya na san akwai abin da yake shiryawa. Ina ruwansa da lambar Hanif? Wayarta ce ta dau kara, ta zabura ta dauko ta duba, lambar Faduwa ce ta shigo. Sai bayan da ta gama hararar wayar gami da siraran tsaki guda uku a jejjere, sannan ta dannan wayar ta kunbura kumatu ta rada sallama kamar dole. Baiwar Allah, Faduwa ba ta san abin da ake yi mata ba a nan, ita sai fara'arta ta ke tana kyakyata dariya. Ta ce, ''Umaimah kin tashi kuwa? Ga mu nan a nan mun hadu muna jiranki. ''Kun hadu kuna jirana ke da su wa? Umaimah ta tambaya cike da kidimewa. Faduwa ta sake kyalkyalewa da dariya ta ce, ''Matsoraciya, mai gudun mutane. To mu biyu ne ni da Abdul. Ta murguda baki sau biyu, sannan ta ce ''Na fito ina hanyar zuwa gidanki ma. ''Sai kin karaso''. Inji faduwa. Sannan suka kashe wayar su dukka biyun. Bayan ajiye wayarsu da kimanin mintina biyar, Umaimah Bello ta bayyana a gaban Abdul-Sabur da Faduwa. Zuciyarta babu dadi, amma tana karfin hali tana ta yin murmushi da ba ta shirya ba. Da ta duka ta gaishe su sai ta sami kujera a gefen su ta zauna tana mai tsananin fargabar abin da zai ce mata. Abdul-Sabur ya gyara zama ya karkata gaba dayansa yana dubanta, ya ambaci sunanta sannan ya dora da bayanai. ''Umaimah, dalilin da yasa na ce ki nemo min lambar Hanif ba wani abu ba ne illa ina so ki kira shi da layinki ku gaisa, ba wai in kun gaisa yau shikenan ba, a'a ku ci gaba da gaisawa har ma ku dinga ziyartar juna tamkar ke da kaninki Sabitu. Dalilina shi ne, ko za ki ki kula kowa a Malaysia bai kamata ki ki kula Hanif ba, saboda dalilan da kika fi ni saninsu. Hanif mai kaunarki ne, haka mahaifinsa ya yi miki halaccin da bai kamata ki yarda su ba. Umaimah ta zuba masa ido kawai tana kallonsa, ji ta ke tamkar ta kurma ihu saboda dabaibayin da yake shirin lauya mata. Tabbas gaskiya yake fada mata, kuma ta yarda da hakan, amma fa ba karamin aiki yake shirin ya ballo mata ba a safiyar wannan rana. Ta fada a ranta, ''Me ya kawo ni wannan gida da zama da har na hadu da mutum mai naci da shisshigi? Na yi da sanin saninka Abdul-Sabur. Gaskia dole na tada Umaimah ta koma wani anguwar daban. Wannan takuran da mai yayi kama.. MAKWABTAKA 29 Ba ta gama tunaninta ba ya katse ta, ya ce, ''Ina lambar tasa? A sanyaye ta mika masa karamar takarda wacce ke dauke da sunan Hanif da lambar wayar daga kasan sunan. Ya karba ya duba ya tabbatar lambar ingatacciya ce, sai ya dago ya dube ta. Ta yi kicin-kicin da fuska tabbas ba za a dauki lokaci mai tsawo ba zata fashe da kuka. Don haka sai ya murtike fuska ya fuskanci ana fara lallashinta zata rushe da kuka, koma ta sami damar yin fushi ta fice. Ya fada cikin kasaitacciyar murya, ''Ba ni wayarki. Ta mika masa nan da nan. Ya tambaye ta, ''Akwai kudi? Ta girgiza kai, ta ce, ''Ban san ko akwai kudi a ciki ba. Ya shiga duba wayar ya ga ko sau daya ba ta kira wani ba balle a kira ta bayan Faduwa babu wanda ya taba kiran wayar. Ya yi ajiyar zuciya ya girgiza kai saboda takaici. Akwai kudi a ciikin wayar saboda layin da aka siya da kudi a ciki. Faduwa ta tsura musu ido tana kallon ikon Allah, tabbas ba don Abdul-Sabur ya gargade ta da kada ta yi magana ba, da tuni ta tunzura Umaimah da magana. Ya saka lambobin ya yi sabin sunan Hanif, sannan ya kira shi. Bugu daya ya dauka, Abdul-Sabur ya yi masa sallama, sannan ya gabatar da kansa. Ya ce, ''Sunana Abdul-Sabur, daga Kaula Lumpur, dan uwan Umaimah ne. Ina fatan ka san Umaimah Bello ko? Daga dukkan alamu Hanif ya cika da mamaki. Ya amsa cikin sauri. Kwarai na san Umaimah. Lafiya, me ya faru da ita? Abdul-Sabur ya ce, ''Lafiya kalau, wannan ma lambarta ce sai yanzu ta hada waya, shi ne zata yi maka magana. Abdul-Sabur ya mikawa Umaimah waya ta karba a sanyaye. Sai da Hanif ya ji muryarta ya saki jikinsa ya tabbatar ita din ce. Ya tambaye ta tambayoyi masu yawa, sai ta kasa amsawa nan da nan hawaye ya fara kwaranya. Ya ce, ''Anti Umaimah, me na miki ba kya nemana? Na kira Samir dan ajinku rannan na ce ya ba ki waya in gaishe ki ya ce ba kya yi masa magana, ba zai kai miki waya ba. Na kira Aisha Bingyal ita ma ta ce ba kwa magana ba zata kai miki waya ba. Na shigo garin naku ranar wata lahadi na ziyarci gidajen dukka *yan garinmu, na rasa mutum daya da ya san gidanki balle a rako ni. Haba Umaimah meye duniya? Me yasa kike gudun *yan kasarku, *yan uwanki don kin zo kasar fararen fata.... Ta katse shi cikin kuka, ta fara magana, ''Hanif, ba haka ba ne, ba gudunku nake yi ba wallahi wasu dalilaina suka sa na ware kaina daga gare ku. Ka yi hakuri Hanif, ka cewa Baba ma ya yafe min don Allah. Sai dukka biyun suka fashe da kuka, kuka ya ci karfin Umaimah har ta cire wayar daga kunnenta ta kifa kai akan gwiwarta. Abdul-Sabur ya yi sauri ya karba ya ci gaba da magana da Hanif. Hanif ya matse hawaye, ya ce, ''Na dade ba ni da lafiya watannin baya, ke ce ta farko wacce Babana ya tambaya saboda yana ganin ke ce tamkar *yar uwata makusanciyata, ke ya kamata ki zo kaina don har na fita hayyacina. Ya yi mamaki da aka ce ba a san inda kike ba, kuma tun ranar da muka iso rabona da ke kenan. Ya yi takaicin barina da kika yi, har yau yana tambaya ta ke. Na shaida masa kina nan lafiya, kuma kina Makaranta abokaina *yan makarantarku suna ganinki. Ko sanda ya turo mana da kudi watanni biyu da suka wuce ya ce in je in neme ki, in tambayeki ki kin sami kudin da ya turo miki? Shine lokacin da nake ta yiwa su Samir waya ba su nemo min ke ba, na zo da kaina ban ganki ba na hakura na koma, sannan na shaidawa Baba ban ganki ba. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Hanif kada ka damu, yanzu ga ka ga Umaimah, ga lambarta nan ka dauka. Kuma ka turomin da lambar Babanka ta wannan layin yanzu zata kira shi. Hanif ya sake matse hawaye ya ce' ''To, zan turo maka yanzu. Suka yi sallama suka kashe waya. Ba jimawa sako ya shigo Abdul-Sabur ya duba ya ga Hanif ne ya turo lambar Babansa. Ya dago ya dubi Umaimah har yanzu ba ta dago da kanta ba, tun sanda ta kifa kai akan cinya ba ta daina kuka ba. Ya ambaci sunanta, ta dago a hankali da jajayen idanuwanta ta dube shi. Ya ce ''Goge hawayenki ga lambar Baban Hanif zan kira ku yi magana. Hanif ya ce Babansa ya turo muku kudin da ya saba turo muku duk shekara. In ban manta ba kin ce miliyan dai-dai yake ba ku ko? Yana tambaya wai kin sami kudin a account dinki? Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Eh kudin ya shigo. Abdul-Sabur ya zazzare ido don mamaki ya kurawa Umaimah ido sai ta sunkuyar da kai kasa ya juya ya dubi Faduwa ta buga tagumi tana kallonsu. Ya sake juyowa ya kalli Umaimah sannan ya tambaye ta. ''Da kika sami kudin kin kira Baban Hanif kin yi masa godiya? Ta girgiza kai ta ce, ''Ba ni da lambarsa shi yasa ban kira ba. Ya yi shiru har zuwa lokaci mai tsawo, ya kasa magana. Can ya dago ya dubi Umaimah wacce har yanzu ta ke sharce hawaye da hankicin da Faduwa ta miko mata. Ya ce, ''A ganinki kin kyauta da ba ki yiwa mutumin da ya aiko miki da wadannan makudan kudi godiya ba Ta yi shiru ba ta amsa masa ba. Ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Allah Ya kyauta. Don ya fuskanci al'amarin Umaimah ya girma har yana so ya fi karfin tunaninsa. Sannan ya matsa lambar Baban Hanif. Ta yi ta ringin har ta katse bai amsa ba, yayin da Abdul-Sabur ya ci gaba da kira ba kakkautawa. Hankalin Umaimah ya tashi matuka zuciyarta ta hau dukan uku-uku tana fargabar abu biyu. Na farko, yadda Alh. Nasir zai karbe ta don dole zai yi fushi da ita saboda gaskiya ta tapka masa laifi. Na biyu, tana fargabar kada a kira shi a gaban Lamijo kawarta kishi ya kamata alhali sun boye mata zuwanta Malaysia. Ta yi zumbur ta mike tsaye kamar wacce aka mintsina. Ta ce, ''Kada ka yi masa maganata, sai ka tabbatar ba a gida yake ba saboda labarin da na baku game da yadda muka yi da matarsa Lamijo. Kafin Abdul-Sabur ya ce wani abu Alh. Nasir ya kira lambar da yaga Missed call rututu. Kafin ya amsa Abdul-Sabur ya ce da ita ta kwantar da hankalinta ta koma ta zauna ya san abin da zai ce masa. Ya dannan da sauri ya amsa, ''Hanif dan albarka, ya naga ka canja layi kuma, ko ka yarda wayar taka ne? In ji Baban Hanif. Abdul-Sabur ya dukar da kai kasa, ya ce, ''Alhaji ina wuni. Ba Hanif ba ne, yanzu dai Hanif din ya turo min da lambarka. Sunana Abdul-Sabur Abdul-Rashid, ni ma dan kasarku ne Nigeria. Kana hanya ne ko kana gida? Ina so na yi magana da kai. Alh. Nasir ya ji hankalinsa ya tashi matuka sai ya zaci wata matsala ce ta sami dansa, musamman da ya sha rashin lafiya kwanaki. Yana fargaba ko ciwon ne ya tashi. Nan da nan jikinsa ya dau bari, muryarsa ta yi ta makyarkyata ya tashi zaune daga kwanciyar da yake. Don alokacin da Malaysia suke karfe goma sha daya na safe, a Nigeria kuma karfe shida ne na yamma banbancin awanni bakwai ne a tsakani. Alh. Nasir ya ce, ''A'a, ai na fito kofar gida muna shirin yin sallar magruba. Lafiya, me yake faruwa ne? Abdul-Sabur ya ce, ''Lafiya kalau Alhaji kada ka damu, tunda sallah za ku yi idan ka idar ko gobe da safe za muyi maganar. Alh, nasir ya girgiza kai, yayin da ya yi wuf ya mike tsaye. Ya ce, ''Ba damuwa, ina ma Abuja ni kadai ne, ba'a kira sallar ba. Abdul-Sabur ya yi mumushi, ya ce, ''To ba damuwa ranka ya dade, a nan ina tare da *yarka kuma kawar matarka Umaimah. ''Umaima Bello! Umaimah!! Alh. Nasir ya tambaya ya sake nanata sunan. Abdul-Sabur ya ce, ''Sai yanzu ta hada waya tun zuwanta ba ta da waya. Muka kira Hanif ya turo mana lambar wayarka. Alh. Nasir ya ce, ''Wannnan wacce irin rayuwa ce? Me muka yi mata da ta ke gudunmu? Haba Malam kai ma ka san Umaimah ba ta kyauta min ba. Taimako da nake mata ba zan fasa ba saboda don Allah nake yi, a wajenSa nake neman lada. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Ka yi hakuri Alhaji, ba yanzu zaka fahimce ta ba, ni zan yi maka bayanin dalilinta. Kamar yadda ka sani Umaimah tana da matsaloli da tashin hankalin rashin uwa, *yar uwa, miji da kuma danta da dan *yar uwarta. Alh. Nasir ya gyada kai, ya ce, ''Haka yake, ta ba ni labari. To amma ai duk ya wuce, Allah Ya masanya mata rayuwa mafi alkhairi. A tunanina ta warware ta fitar da waccan matsalolin da suka addabi rayuwarta. To ashe in dai damuwa zata saka a ranta ba ta iya yin karatun ma daya kai ta kenan kudi ake kashewa a banza. Abdul-Sabur ya duka ya ce, ''Ranka ya dade tana karatu sosai ma kuwa, ba ta da matsala. Ga ta ku fara gaisawa tukunna. Umaimah ta dafe kirji tun sanda Abdul ya fara waya da Baban Hanif, saboda tashin hankali. Hawaye ne kawai yake zubowa face-face tana jiyo duk abin da suke cewa. Ta yi sallama cikin girmamawa da shesshekar kuka, sannan ta duka ta gaishe shi cikin harshen fulatanci. Ya amsa gami da tambayarta lafiyarta da kuma karatunta. Ya dora da nuna mata rashin kyautawarta da rashin tunani akan hukuncin da ta yankewa kanta na fita daga harkar kawaye da *yan uwa. Ba ta neman kowa ta yi dif! Kamar wacce ba ta duniyar. A matsayinsa na uba ya dade yana yi mata fada, nasiha da jan kunne busa kuskuren da ta tafka cikin harsunan nan uku, Hausa, Turanci da Fulatanci yarensu. Kalmar, ''I am sorry sir, Alhaji yi hakuri, Baba mutubi'am. Amsar da ta ke ta ba shi ke nan har ya yi mata sallama ya kashe waya. Da alama Baban Hanif ya yi fushi da Umaimah, amma hawayen nadama, tuban da ta ke yi da hakurin da ta dinga ba shi ya sanyaya masa zuciya matuka. Har ya dora mata doguwar addu'a kafin ya ajiye wayar. Wannan karon kukan dadi da samun sauki daga kullutun da ya dankare mata a zuciya ta ke fitarwa. Hakika yau Umaimah ta dan ji sanyi daga tsantsar damuwar da ta dade tana addabarta. Abdul-Sabur ya dauko wayarsa ya dauki lambar Hanif da ta babansa sannan ya mika mata wayarta. Kalmar da ya fada mata ta karshe wacce daga ita ya mike tsaye ya fice ita ce, ''Umaimah ki yi hakuri ki daina kuka, don ba zai yi miki maganin matsalarki ba. Ki yi addu'a sannan ki yi hakuri sai kuma ke da kanki ki gyara lamuranki da jama'a. Idan kika yi haka za ki inganta rayuwarki, kuma ki ji dadinta duniya da lahira. Sai anjimanku. Ya fice ya bar su a zaune, Umaimah ba ta daina kuka ba, sabon shafi ma ta bude na kuka. Yayin da Faduwa ta rungume ta tana lallashi tamkar wata *yar jaririyar goye. Umaimah ta kasa tafiya gida a gidan Faduwa ta yini, suka dafa abincin rana suka ci, suka yi sallar azahar da la'asar, suka yi kallon talabijin suka yi ta hira. Hakika Faduwa ta zauna ta bawa Umaimah shawara game da yadda zata yi mu'amala da jama'a. Ta gargade ta da ta canja halayenta, domin shi mutum rahma ne. Dole ta canja wannan ra'ayin nata na kin kula mutane da gudun danginta da *yan kasarta. Ya zama dole ta bi Abdul-Sabur a hankali har ya samar mata mafita. Amma ko da wasa Faduwa ba ta sako mata maganar soyayyar da ta ke shirin kullawa a tsakaninta da Abdul-Sabur ba, saboda kada Umaimah ta zaci da wata manufar yake kula da ita. Kuma tana gudun bacin ran Abdul-Sabur kada ta furta wata kalma da zai yi fushi da ita. Umaimah ta fara saduda, a yau ta fuskanci rashin kyautawarta barobaro a zahiri, wacce ta yiwa Alh. Nasir da dansa Hanif. ''Tabbas na san Abdul-Sabur mutum ne mai fadar gaskiya komai dacinta, haka yana kokarin kwatantawa. Ba ya fushi, kuma bai damu da duk bakar maganar da za a fada masa ba. Umaimah take fada a ranta. Umaimah ta sake yiwa Faduwa sha'awarsa don tabbas zata yi dace da miji na gari idan har hakan ta kasance. ******************* Tsakar dare misalin karfe uku Umaimah na zaune a tsakiyar gadonta, ta mike kafa don bacci ya kauracewa kwayar idanunta. Ta fuskanci kuka ma ba zai yi mata wannan magani ba, sai addu'a. Tana ta jan carbi tana karanto 'hailala da istigfari, sannan lahaula wala kuwwata illa billahil azim. Fitilar dakin Abdul-Sabur ce aka kunna nan da nan taga hasken ya hasko mata daki, don haka sai ta tsurawa dakin ido. Da alama ya tashi daga barci, shi yasa ya kunna fitilar. Ta tashi a hankali ta je jikin windo ta daga labule tana duban inuwarsa yana ta kai kawo a cikin dakinsa. Ba ta ankara ba sai ganinshi ta yi a jikin windonsa yana kallon windon dakinta, sai ta yi sauri ta durkusa tana kyautata zaton ya ganta. Sai ta ga ya gyara labule ya sake rufewa, ya koma ciki da alama magana yake yi a waya. Ya wuce zuwa falonsa sai ta ji motsi ya bude kofar kicin ya shiga. Tana jin karar bude firij ya zuba lemo a kofi ya sha, ya bude kofar barandar waje ya fito baranda duk tana sanda tana hango shi. A halin yanzu in ta yi sa'a zata iya jiyo abin da yake cewa, saboda dare ne kuma harshen Hausa ya ke magana. Tana tsaye a cikin kicin a makale a jikin kofa, sai dai kash, ba zata iya bude kofar baranda ta fito ba, saboda zai ganta. Babu tantama ta ji ya ambaci sunana Baban Hanif daga dukkan alamu da Alh. Nasir yake waya. Kwatsam sai ta ji ya ambaci sunanta baro-baro. Ya ce, ''Alh Umaimah tana da hankali, amma tana neman taimako wajen kula da ita don kada ta shiga wani hali na bakin cikin rayuwa, Allah ma dai Ya kiyaye. Ta yi wuki-wuki ta rasa yadda zata yi ta jiyo sauran abin da ya ke fada, don ya koma cikin gida ya rufo kofar. Tana hango inuwarsa a zaune akan dinning table yana hada shayi har yanzu wayar na sakale a kunnensa yana magana. Tabbas sun shafe fiye da awa guda cur suna maganarta. Ta jawo wayarta ta duba tsaf, babu lambar Abdul-Sabur a cikin lambobin da ta ke da su, lambobin mutane uku ne kacal a ciki, daga ta Faduwa, Hanif sai ta Babansa. Ta ji duk ta damu kanta, sai ta ji abin da suke fada amma kuma babu hanyar da zata ji don haka ta cirewa kanta damuwa, tasan koma me za su fada alkhairi ne. Duk laifin da ta yiwa Alh. Nasir tasan Abdul-Sabur yana da wayon da zai kare ta. Dole ma Alh. Nasir ya ji sanyi a ransa in dai Abdul-Sabur ya jawo masa hadisai da ayoyin alkur'ani. Jikinta ya yi sanyi ta tashi ta dauro alwala ta hau nafilfili har aka kira assalatu, ta yi sallah ta sha ragargazo addo'i akan Allah Ya yaye mata duk wani abu da yake damunta na kunci a rayuwarta. MAKWABTAKA 30 Washe gari litinin ce amma ita ba ta da jarabawa, don haka ba zata je makaranta yau ba. Ta fito ta tsaya akan baranda tana shakar sanyayyiyar iskar da ta ke kadawa. Abdul-Sabur ne ya hango ta, ya yi kamar zai fito su gaisa sai ya fasa ya fuskanci ba ta son a cika shisshege mata. Ya shirya tsaf cikin bakar riga da wando na suit ya fice kasa. Tana daga sama ta hango giftawarsa ya sauko, sai ya wuce zuwa gareji ya dauko motarsa. Bai dago da kansa ba balle tasan ya ganta a tunaninta bai san tana tsaye akan baranda tana kallonsa ba alhali ya sani. Tana tsaye tana leke har ya fita daga get din ya figi motar ya hau titi, daga dukkan alamu sauri yake yi yana da jarabawa da sassafen nan. ''Tabbas ka yi dace da hali na gari, Allah Ya ba ka mace ta gari Abdul-Sabur. Umaimah ta fada a cikin zuciyarta, yayin da hamma ta hana ta sakat saboda baccin da ta ke ji, ta kwana idonta biyu. Sai yanzu baccin ya zo. Hawaye ne yake kwararowa daga idanunta da zarar ta yi hamma, sai yinta take ba kakkautawa, mafita daya ce ta je ta kwanta ta yi bacci, amma sai ta cika tumbinta zata yi bacci daga dukkan alamu tabahuwa zata iya hana ta baccin. Kan ka ce kwabo ta shige kicin ta jona butar ruwan zafi (kettle), nan da nan ta tafasa ta hada shayi ta sha da biskit. Daman yawancin abincinta ke nan, ba ta cika cin abinci mai nauyi ba, shi yasa har yanzu kiba ta gagare ta. Da kyar ta ke takawa ta shiga daki, da rarrafe ta hau gado saboda tsananin baccin da ya yi mata nauyi a ido. Abu na farko da ta fara tunawa shine: ''Shin ko yaya Abdul-Sabur ya ke ji shima da ya kwana yana yawo yana waya bai runtsa ba? Da safe bai yi bacci ba ya fita zuwa makaranta. Ta fada a bayyane ''Ka ga bayin Allah masu kaunar *yan uwa musulmai, matsalar wani ta zama matsalarsu. Allah Ya saka masa da alkhairi. Daga nan ta rufe ido bacci mai dadin gaske ya rufeta, sai ta dora da mafarkai masu dadi. Umaimah ta yi mafarki Alh. Nasir ya zo yana fara'a yana ambaton sunanta har ya ce da ita tare muke da kawarki Lamijo zo mu je inda ta ke ku gaisa. Umaimah ta hau murna a cikin mafarkin tana fadin, ''Alhamdulillah da Lamijo ta fahimce ni ta bar zargina. Sai taga Abdul-Sabur ma a mafarkin ya yi murmushi ya gyada kai, ya ce, ''Dauki takalmanki sababbi ki saka ki je ku gaisa da kawarki. Ta yi zumbur ta bude ido, sai ta ga ashe mafarki ta ke yi. Hakika mafarkin nan ya bata mamaki matuka. Sai ta tofa addu'a Gabas da Yamma, Kudu da Arewa ta canja yanayin kwanciyarta ta ci gaba da barci. Mafarkai makamantan wadannan dai ta ci gaba da yi. Bacci ya yi bacci abu kamar wasa, har karfe uku saura mintina na rana sannan Umaimah ta farka daga baccin nan da ta ka yi, shi ma a sanadiyyar wayar da Hanif ya rangado mata ne ya tashe ta, ba don baccin ya ishe ta ba. Ta yi sauri ta mika hannu ta wawuro wayar ta duba sai ta ga sunan Hanif ne, nan da nan ta amsa. Hanif ya gaishe ta cikin ladabi, ''Anti fal bakinsa haka yake kiranta kamar yadda ya ke kiran Lamijo matar Babansa. ''Anti ya makaranta? Ya ya karatun jarabawar, koda yake fa Anti ba kwa tsoron jarabawa na ji labari irin pionts din da kike ja. Ance 4pointer ce ana kyautata zaton da first class za ki fita. Ashe ba'a banza ba da ba kya kula mutane boko ne kadai a gabanki. Ta tuntsure da dariya da bata shirya ba, sai ta nemi baccin da ya ke idanuwanta ta rasa. Ta ce da shi, ''Kai Hanif wa ya fada maka haka? Kai ne dai ka kirkiro hakan don ka tsokane ni. Ya ce, ''Wallahi an fada min, ba daga bakin mutum daya na ji haka ba, *yan ajinku ma sun fada min. Ke ki rantse in ba haka ba ne kamar yadda na rantse. Umaimah ta kyalkyale da dariya, ta ce, ''To meye abun rantse-rantse tunda ka ce haka ne, to abarshi a hakan. Hanif ya ce, ''Kin san haka ne ke ma. Amma ai abun alfahari ne ma a wajenki, ni da zan sami haka ai da na dinga dagawa ina alfahari a kasar nan da ma Nigeria gaba daya. Tanadi na musamman fa gwamna ya yiwa wanda ya fito da first class a cikinmu, kuma ya yi alkawarin zai biyawa wanda ya fita da first class kudin karatun master da PhD a kowacce kasa ya ke so yayi a duniya. Bayan babban aiki da za a bashi a gwamnatin garinmu. Ina ga ku biyu ne za ku sami wannan garabasar ke da wani Abba Ahmad dan makarantarmu. Umaimah ta yi murmushin farin ciki, ta lumshe ido ta ce, ''Alhamdu lillahi, kai ma fa idan ka dage zaka iya kamo mu ka fito da first class. Hanif ya kyalkyale da dariya, ya ce, ''A yaushe kuma bayan saura shekara daya da kadan mu gama, an cinye rabin karatu ina zan iya kamo ku? Mu dai ki barmu a second calass upper ko lower ma ai kwakwalwar ma ba iri daya ba ce. Baba ya ce kun kira shi jiya, ya yi farin ciki sosai, ya ce idan an yi hutu in dinga ziyartarki muna gaisawa. Kuma idan an yi hutu in tambayeki in kina so ki zo ki ga gida zai aiko mana da kudin tikiti. Sai ta ji kamar ya daba mata wuka a kirji, ta dafe kirji ta yi firgigit ta tashi ta zauna. Ta ce, ''A'a bazan je gida ba, sai na gama sai dai ka tafi kai kadai. Hanif ya ce, ''Ba ga irinta ba, mu ne masu yin nisa da littafi ku masu kokarin nan ba kwa yin nisa da littafinku, boko ya hana. Suka yi dariya su dukkansu, daga karshe suka yiwa juna fatan alkahairi da sallama suka kashe waya. Umaimah ta ji dadin hira da Hanif, yaro mai kirki da ladabi, sai ta ji sanyi a ranta tamkar ta ji muryar dan uwanta rabin jiki Sabitu. Tana duba agogo ta ga lokaci ya ja azahar har ta gota, sai ta yi wuf! Ta diro daga kan gado tana fadin, ''Astagfirullah! A'uzu billah, na makara azahar ta wuce ban yi sallah ba. Gaskiyarki Umaimah, sallah ita ce gaba da komai. Allah Yana hukunta masu aikata tarikul salat. Allah Ya mana jagora, Ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, amin!!! ************** Faduwa ce a tsaye a gaban kofar gidan Umaimah da yammacin ranar juma'a, Umaimah na bude kofa sai ta ga bakuwarta. Farin ciki ne ya duro mata mabayyani a fuskarta. Ta yi sauri ta rungume ta gami da ruko hannunta suka zo suka zauna a cikin falo akan kujerun nan nata na alfarma. Faduwa ta dube ta ta yi murmushi, ta ce, ''Ya na ga kin rame ko jarrabawa ce? Umaimah ta taba kashin wuyanta, ta ce, ''Jarabawa ce Anti, bana iya cin abincin kirki kullum. Faduwa ta ce, ''Bayan jarabawar fa, meye yake ramar da ke? Sai Umaimah ta yi kasake tana kallonta ta kasa amsa wannan tambayar. Faduwa ta yi dariya ta ce, ''Kin saka damuwa a ranki da yawan tunani, ga kuka kullum. Ki daina, babu kyau ko don lafiyarki ma, mu likitoci ba ma son haka. Nan da nan idanuwanta suka ciko da kwalla da alama da wani kukan zata fashe. Faduwa ta ce, ''Au tuno miki ma na yi? Shi ne za ki bude min sabon shafin kuka? A'a kada ki tayar min da hankalina, na zo mu yi hira wasa da dariya kuma zaki fashe da kuka? Umaimah ta yi sauri ta goge idanunta, ta yi murmushin karfin hali, ta ce, ''To na goge hawayen na daina kukan, mu yi hirar. Faduwa ta shafi kuncinta ta ce, ''Yauwa kanwata, ko ke fa rayuwa ma yanzu za

Chapter 18 of 33