Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na suffanta ciwon na gane irin ciwon Ibrahim ne, don haka na cire rai da shi a rayuwa. Tun daga wannan lokaci hankalina ya yi Nigeria, na ji ina so na zo na gana da mahaifina tunda ransa. Saboda ban san shi ba sai a hoto, ga babu dan uwana Ibrahim shi ne daman ya san su, wanda ko ba ran mahaifinmu zai iya kawo ni na ga dangin ubana ko da kuwa aurena ne ya zo. Mahaifiyata ta dage ta ce ba zan je ba, don ba son mu suke yi ba. Tana tsoro kada ma na zo su cuceni, ko su hada baki su hallakar da ni, tunda ta ji labari su *yan Nigeria suna da hadamar gado, kuma za su iya yin komai a kan gado . Kuma ta fuskanci matansa ba sa son mu, da akwai yadda za su yi da sun soke sunanmu daga cikin *ya*yansa, *ya*yansu ne *ya*ya. Na ji ba dadi don na sawa raina ina son zuwan, to amma babban dalilin da yasa na hakura ba ni da kudin jirgi. Muna nan haka rayuwa ba dadi, rana daya ba zato ba tsammani zuciyar mahaifiyata ta buga, sai dai kawai ta fadi aka dauki gawarta. Tsakaninta da yayana shekara guda dai-dai. Nima mutuwa ce kawai ban yi ba, saboda na girgiza, na dimauce zan iya cewa dai na zautu tamkar kwakwalwata ta tabu. Ta fashe da kuka mai tsanani. Ya yin da Umaima da Abdul-sabur suka razana har suna hada baki ''Mama ce ta mutu? Faduwa ta gyada kai ta ce, ''Mamana ta rasu, ta tafi ta bar ni, ni kadai a duniya. Tun daga wannan Lokaci na daina zuwa aiki kwata-kwata. Faduwa ta gyada kai ta ce, ''Mamana ta rasu, ta tafi ta bar ni, ni kadai a duniya. Tun daga lokacin nan na daina zuwa aiki kwata-kwata don ko naje shirme zan yi, yanayin aiki na kuwa sai da nutsuwa. Babu yadda dangin mahaifiyata ba su yi ba na je aikina nayi hakuri na maida komai ba komai ba. Na fada musu baro-baro, ba zan je ba, tun *yan ofishinmu na ba ni dama suna daga min kafa har suka fara turomin da doguwar wasikar gargadi (warning letter) cewar, ko na dawo aiki, ko a kore ni. Daga karshe dai naga wasikar kora daga aiki, ban damu ba daman haka nake so. Na hada *yan abubuwan da aka ba ni na daga cikin dan abin da Mahaifiyata ta bar min na gado, na sayi tikiti na kaura Saudiya wajen danginta na can na zauna da su a 'Tayif. Bayan mutuwar Mahaifiyata na kira lambar gidanmu ta Nigeria ina so na shaidawa Mahaifina rasuwarta, sai matarsa ta dauka, na ce ta bashi muyi magana, ta ce min ba ya kusa. Na shaida mata sakon da zata fada masa, a shelake ta amsa min gami da ajiye waya tun ban gama magana ba. Sai na kira Baffana daya daga cikin su wanda yake zaune a Kano Baffa Mansur na shaida masa abubuwan da yake wakana, ya yi min alkawarin zai sanar da shi idan ya je duba shi, don shi ma jikin ya tsananta. Na yi kuka, kullum cikinsa nake yi har yau saboda bani da kowa, ba ni da komai, daman dai na san Allah (S.W.T) ne kadai gatana. Rayuwata ta tsananta a 'Tayif' ba na ganin dai-dai duk inda na je sai naga kaman ana min kora da hali, sun kosa da ni. Duk da masu arziki ne abinci da sutura ba sa wuya sai na ga suna yi min habaici game da mijinsu suna gudun kada mazansu su ce suna sona saboda Allah Ya yi min fara'a, hira da saurin sabo da mutane. Duk na tsargu na fara zama mujiya a cikin jama,a. Dole na tarkato na dawo Cairo don na tantance cewar na wuce zama a gaban wasu. Na zo na bude gidana na zauna, ina cin dan abin da na samo, daya kare sai na fara shiga garari. Egypt ba kudi ba kamar Saudiya ba komai a wadace, a Egypt ma'aikaci mai daukar albashi kukan babu yake yi, albashin bashi da yawa balle ni da bana aiki. Bayan shekara ne na ga ya dace na kira na ji jikin mahaifina tunda kozai mutu babu mai kirana ya ji hakin da nake ciki, ina kira gidanmu, wani kanina mai suna Salahuddin ne ya dauk wayar, sai yake shaidamin ai mahaifinmu ya shekara da mutuwa... Faduwa ta girgiza kai ta yi murmushin takaici, yayin da Abdul-Sabur da Umaimah suka zazzare ido don tashin hankali. ''Ya rasu amma ba su fada miki ba? Im ji Abdul-Sabur. Faduwa ta fashe da kuka, ta ce, ''Ba su fada min ba, saboda bana cikin lissafin *ya *yansa. Raina ya yi matukar baci, na yi ta fada, a lokacin na kira Baffanaina daya bayan daya na wanke su tas da bakaken maganganu, na ce yanzu har Mahaifina ya shekara ya shekara da rasuwa a kasa fada min. Sai suka hau kame-kame wai saboda suna gudun kada zuciyata ta buga abubuwan su yi min yawa, ga mutuwar dan uwana da mahaifiyata, ya za a yi a fada min mutuwar mahaifina, daman so suke a kwana biyu tukunna. Babu abin da na ce musu, sai na kashe waya, na fi sati ina kuka a daki ni kadai, sai da kanwar mahaifiyata ta zo ta tambaye ni ko lafiya? Na shaida mata duk abin da ya faru. Nan da nan ta hado taron gaggawa, kowa sai da ransa ya baci da ya ji abin da aka yi min, suka ce ai ba za a zura musu ido aci gaba da cutata ba, dole a kwatarmin hakkina tunda sun nuna ba su san mutunci ba, sai an raba abin da ya bari da ni. Suka ba ni waya na kira gidan a gabansu na bude magana(speaker). Cikin harshen Hausa na yi magana dasu a waya dangina basu ji abin da muka ce ba, amma na fassara musu daga baya abin da aka ce. Matan Babana na tambaya me da me Mahaifina ya bari? Suka hau kame-kame wai bai bar komai ba, duk sun kare a asibiti. Ko gidan ma da suke ciki na aro ne. Sai na katse waya na bugawa Baffa Adamu waya, shi yana jin larabci na tambaye shi gadon Mahaifina, sai ya ce fili ya bari guda daya. Da na kira Baffa Mansur kuwa shi ma a cikin harshen Larabci mukayi magana, kowa yana ji. Sai ya ce baibar komai ba sai shaguna guda uku a kasuwa da mota biyu tirela. Daga jin haka mun san ba su da gaskiya, don haka aka ce na shirya kawai na tafi Nigeria, na je na shigar da kara na karbi hakkina. Suka hadamin kudin jirgi, amma sai da na sami wanda ya ke da tabbas ya san gidanmu na sokoto amma a Abuja yake a zaune. Don haka Abuja na nufa gidan da matarsa su ma sakkwatawa ne, unguwarsu daya da mahaifina ni kuma a asibitinmu na sansu sun kawo dansu wata shekarar muke waya da su har bayan sun tafi. Hira ta kawo hira suka gane mahaifina... Umaimah ta gyara zama ta ce,''Ya aka yi kika je?'' Abdul-Sabur ya ja doguawar ajiyar zuciya, ya gyada kai. Ya ce, ''Ikon Allah, rayuwa kenan. Yaya ta kasance tsakaninki da su?'' Faduwa ta tabe baki ta ce, ''Inda ranka a duniya za ka sha kallo. Wasu mutane gani suke kamar ba zasu mutu ba, sun kauro duniya ke nan, ba sa tsoron Allah. Sun manta inda wancan ya je su ma za su je ne ko ba jima ko ba dade. Da na isa Nigeria garin Abuja aka kai ni garinmu Sokoto cikin gidan Babana. Sai ga ni a zaune a falonsa, ga ni ga hotunansa a kusa da ni, amma baya nan. Allah Ya yanke haduwarmu har abada. Na ga kannene rututu, dangi kamar tururuwa kowa ya taho ya ga Faduwa, suna murna ina murna, yayin da aka dinga jeremin kwanukan abinci da kyaututtuka iri-iri kamar Muhutai, atamfofi, leshina, kwarya da dai sauransu. Kowa so yake ya yi hira da ni, kai ka ce suna sona. Wasu daga cikinsu kauyawa ne futik babu boko, wasu kuwa *yan gayu ne masu kudi. Su ka ce ma idan na huta zasu kai ni Kano, Kaduna da Abuja wajen *yan uwa (cousins) da suke auren manyan masu kudi a can. An ba ni su a waya mun gaggaisa na ce musu idanna na gama da sokoto za,a kawo ni sun yi murna da jin haka. Wasu turanci muke yi da su, wasu Larabci, wasu kuwa hausa kawai suka iya sai mu yara. Sai da na shafe kwanaki goma cur babu wanda ya yi min maganar gadona, sai dai a gaisa, a yi hira wasa da dariyaa, a tulo min abinci da kayan marmari a gyaramin gado na kwanta in yi bacci washe gari in tashi a ci gaba da haka. Sai na nemi a taro min kannen Mahaifina da manyan kannena da iyayensu mata, duk muka hadu a babban falon gidan. Na bude baki na yi magana cikin harshen Hausa yadda kowannensu zai gane. Na ce, na zo ne na karbi gadon mahaifina don na kasa ganewa duk wanda na tambaya me ya bari, abin da zai fadamin daban ne. Me ya bari, kuma ina nawa kason? Sai aka hau kallon-kallo, wata matarsa wacce ita tafi tsana ta ta dinga bayani irin na rashin gaskiya, wai gidan nan kawai ya bari duk asibiti ya cinye kudin, an siyar da kadarorinsa gaba daya. Gidan ma ba dukka ba dole sai an siyar da rabi an biya masa bashin da ake binsa. Ni kuma abin da na gida dai an gama raba shi, don naga kowa ya kama nasa bangaren an yi toshe-toshe da likelike. Baffa Adamu ya ce na yi hakuri na koma kasarmu idan komai ya daidaita za a turomin da kashina. Na fusata na ce da shi, ina fili da ka fada min yana da shi? Na juya na dubi Baffa Mansur, da ya ce min yana da shaguna a kasuwa, na tambayeshi. Na ce, ''Ina shagunan da ka fada min ya bari a kasuwa da motoci? Duk ba ni da kaso a ciki ke nan? Na yi kuka sosai don takaici na dube su dukkansu na ce, ''To na gane abin da dukka kuke nufi, kun cire ni daga cikin *ya*yan gidan nan, kun rabe gadon ku banda ni. A wajen Allah ina da hakki ku ka danne, to duk wanda ya ci kashina ko da kwayar zarra ce ban yafe ba, zai biya ni a ranar da bashi da abin da zai ba ni sai ladansa. In da Mutumin daya tara dukiyar da ku ka cinye ya je dukkanmu nan zamu je, kuma ba kowa ya jawo min wannan wulakancin ba sai shi da kansa Mahaifina da ya nuna muku ni ba komai ba ce, kuma bai damu da ni ba. Sai suka hau timin tsawa da fada, wai kada na yi musu rashin kunya. Kannena har da masu cewa, za su dake ni idan na sake yiwa iyayensu rashin kunya. Da yake zuciyata ta kekashe ban yi shiru ba ni ma fadan na ke na ce su zo su dake ni idan sun so ma su kashe ni. Aka shiga tsakani aka kai ni bangaren masaukina. Cikin dare Baffa Adamu ya aiko na zo gidansa yana nemana. Da farko na ki zuwa sai da ya aiko matarsa ta zo, ta tafi da ni ya dauke ni a mota ya kai ni gidan wani dattijo, a she shine alakalin daya raba gadon. Aka daukomin takardun da aka yi rabon gadon. Ga sunayen magada nan, amma babu sunana, sannan ga dumbin dukiyar da ya bari, shagunan kasuwa, filaye da tireloli, amma babu nawa duk an rabe musu. Wanda da ace an raba da ni da na yi sallama da talauci. Baffa Adamu ya dube ni fuskarsa cike da nadama. Ya ce da ni, ''Faduwa ina tsoron ranar da zan mutu Allah Ya tuhume ni da laifin ban fada miki gaskiya ba. Saboda ni dai banci gadon ki ba ko sisi. Allah ba zai tuhume ni da wannan ba, amma zai tuhume ni da nasan komai na boye miki. Na yi ta kuka na ci gaba da yi musu bayanin halin da nake ciki a can Egypt ba ni da komai, ba ni da kowa. Alkali ya ce, ''Shawara biyu zan ba ki, ki zabi wacce ta fi miki sauki. Ta farko ko kiyi hakuri ki bar wa Allah cutar da akayi miki, ko kuma ki nemo kudi ki dauki lauyoyi su tsaya miki ki karbi hakkinki. Amma ki sani za a iya shekara goma ana ta shari'ar nan ba tare da ta kare ba. Allah ya raba mu da son zucia. MAKWABTAKA 13 Na tashi na fice don takaici, Baffa l Adamu ya dawo dani gida babu abin da yake sai ba ni hakuri yana neman gafarata. Yana sake ba ne labarin mugun hali irin na matan babana cewar, karfi da yaji suka hana mahaifina maganarmu, don da koda yaushe yana maganar zaije ya dauko Faduwa ta dawo wajensa ko ya je ya ganki, ya ba ki wani abu daga cikin dukiyoyinsa, wanda zan ci gaba da karatu. Sai su ce bazai je ba ni me yasa ban taba zuwa ba? Kuma duk *ya*yan da yake da su sama da ashirin ba su ishe shi ba sai ya je neman wata. Dole ya hakura ya janye wannan zance na zuwa Egypt don ba yadda zai yi. Na ce da shi, ''Don kansu, kowa ya yi na gari zai gani. Nawa rayuwar duniyar ta ke ne? Washegari da sassafe na hada kayana na ce, tafiya Abuja zan yi, daman ta Abuja na zo. Baffa Adamu ya hada ni da babban dansa ya kai ni har Abuja gidan *yarsa Ummul Kursim na zauna na gama kwanakina don daman wata guda ne booking din tikitina, na komawa Egypt. Gidan Ummulkursi ne tamkar aljannar duniya tana auren Sanata, komai gashinan a wadace kamar ba a Nigeria nake ba. Ta zazzagaya da ni garin Abuja na ga gidaje, sai a lokacin nasan ashe Nigeria tana da kyau da arziki haka. Sai a lokacin na ji zuciyata ta fara warwarewa daga kuncin da nake ciki, ta ba ni hakuri bisa abubuwan da *yan uwana suka yi min. Ta yi min alkawari idan har zan iya zama a kasar nan ita kuwa zata yi wa mijinta magana ya samar min aiki a asibiti mai kyau inda za a biyani da kyau, na kama gidan haya nayi zamana har Allah Ya fito min da miji. Na yi sha,awar shawarar nan da ta ba ni, amma na ce mata zan koma Cairo tukunna na sanarwa dangina, na kuma yi musu sallama. Kafin na tahi sai da ta kai ni Kaduna wajen daya *yar uwar tamu, ita take auren Manajan wani babban banki, kudi kam ba,a magana. Muka dungumo muka je Kano wajen Hajiya Lami itama kakarmu daya, ita ma ta kafu a gidan, mijinta hamshakin dan kasuwa ne, su dukka sun yi min kyautar kudi da kaya. Da muka koma Abuja a ranar da zan tafi Sanata ya yi min yayyafin dallar, har sai da na tsorata don yawa. Allah Mai jinkan bawanSa, Ya hana ni a can Ya bude min anan. Na yi kukan farin ciki, gami da godiya mai dumbin yawa. Duk da haka Ummul Kursim ba ta barni haka ba sai da ta ba ni shaddoji da leshina dinkakku ta ce na dinga sakawa a can, ta kara bani daloli da yawa. Lallai ba dukka aka taru aka zama daya ba, wani mai kirki, wani bashi da kirki, wani mai kyauta wani marowaci. Wani mai tausayi, wani kuwa mugu ne, haka mutanen suke ciki. Suka kaini filin jirgi suka saka ni a jirgi na taho Cairo. Da na ba wa dangina labari sai suka yi takaici, suka tayani da addu ar Allah Ya saka min. Shawarar Ummul Kursim kuwa tuni suka yi facali da ita, suka ce bazan koma Nigeria ba, gara na hakura na yi zamana a cikinsu. To ba ni da zabi saboda na sallama rayuwar ma gaba daya ba ta min dadi. Ina zaune ina canja dalolina a hankali ina ci, talauci ya daina nukurkusata. Na dade ina cikin rufin asiri ina kashe dalolin nan, amma da suka dauko karewa sai hankalina ya tashi na tabbatar zan koma gidan jiya na kashewa zai gagare ni, don haka na koma neman aiki. A asibitin da na yi aiki na fara zuwa na roke su, su mayar da ni sai suka ki. Babu ta kan babban da ban bi ina roko, durkuso har kasa kuka da hawaye suka cemin sun cike gurbina da wata, ba su da inda za su saka ni. Na bazama gari duk wani asibiti da kuka sani a Cairo sai da na mika takarduna na neman aiki, kai har ma wasu asibitoci na wasu jihohin sai da na tuttuta wasu na je da kaina, wasu na aika ta internate ko na ba wa wani sako ya kai min. Amma babu wanda ya kira ni interview, don haka babu aiki. Ina cikin hali na rashi da wahala da fargabar neman aiki, sai dai a *yan uwana wanda ya dubi Allah ya ba ni dan kudi, wasu sai na roka ko su ba ni ko su hana. Babu irin wulakancin da bana gani, ga shi ba ni da saurayi ko daya balle so na ya sa ya tallafe ni ya kwantarmin da hankali. Ana cikin wannan hali sai na hadu da Gaddafi, a makarantar lafiya ajinmu daya a jami,a. Ban yi mamakin ganinsa ba, don shima likita ne, amma tunda muka gama karatu ban san inda yake ba. Yana ganina ya rungume ni cikin farin ciki muka gaisa. Hakika na ga sauyi a fatarsa da kayan da yake sanye a jikinsa, domin tsadaddu ne, kudi ya zauna masa matuka. Ya tambaye ni ''ina maigida? Ina yara? Ya kuma wajen aiki? Sai ya ga alamar damuwa nan da nan a fuskata, jikina ya yi sanyi don na rasa amsar da zan ba shi. ''Faduwa lapia kika sauya nan da nan? Ya tambaye ni yana kallona cikin yanayin tuhuma. Cikin hawaye na amsa masa dukkan tambayar da ya yi min, amsar ita ce babu. Ba ni da uwa, ba uba babu dan uwa, babu aiki balle *ya*ya. 'Subhanallah! Subhanallah!! Kalmar da yake ambato ke nan. Ya ja hannuna zuwa ga kyakkyawar motarsa muka zauna, ya roki na share hawayena na yi masa bayanin matsalolina. Tunda na fara magana ya fara girgiza kai don tausayina. Hawaye ya kasa tsayawa a idona, har na sa shima yana zubarwa. 'Faduwa kwantar da hankalinki, zan taimaka iya karfina. Kalmar da ya fara fada min kenan har tasa na tsagaita da kukan. Ya fara ba ni labarin yadda rayuwa ta yi masa kyau. Ya ce, da muka gama karatu sai ya tafi Malaysia karatu akan likita ya karanci kwarewa akan fannin tiyata ya zama Sugical Doctor Consultant. Yana gama karatu sai ya sami aiki a wani babban asibiti anan cikin babban birnin Kaula Lumpur ana biyansa albashi mai kyau. An bashi gida mai kyawun gaske, ana cirewa a albashinsa har ya zama nasa. Ya dawo gida ya yi aure ya tafi da matarsa suna zaune a can lafiya kalau cikin so da kaunar juna yanzu yaransu guda biyu mace da namiji su ma har sunyi nisa a makaranta. Ya ce washe gari zai koma Malaysia, zai karbi lambata da photocopy din takardu da E-mail address dina ya tafi da su, zai fadamin halin da ake ciki game da neman aiki. Wai amma na je na fara tuntubar dangina sun yarda sannan zai zo ya karbi takardun a ranar da daddare, saboda washegari zai wuce. Na ce, kada ma ya damu, babu abin da dangina za su ce ko su yarda ko kada su yarda ni dai zan tafi saboda yanzu da na rasa babu wanda ya dauki nauyina, babu wanda ya ke tayani yawon neman aiki, don haka yanzu na gane zan bi duk wata hanya wacce rayuwa zata yi min dadi idan dai ba hanyar sabon Ubangiji ba ce. Na ba shi adireshin gidanmu da lambar wayata, na ce don Allah da daddare ya zo ya karba zan hada masa su. Ya ce, ba don ma bai gama harhada takardun da ya zo nema ba da mun tafi ya ga gidan a lokacin, na ce masa, ba komai ya zo da daddaren. Sai na fasa shiga neman aikin na koma gida na shiga tsara takarduna, yadda suna gani zasu dauke ni. Na dukufa ina addu,a ina kuka, ina rokon Allah Ya tabbatar min da tafiyar nan, kuma Ya sa alkhairi a cikinta. Har karfe goma na dare banga Gaddafi ba, na yi ta kiran wayarsa bai amsa ba, sai na shiga zargin karya ya zukala min, nan da nan murna ta koma ciki. Sai na ji wayata tana ruri, ina dubawa na ga sunansa ne, a guje na amsa. Ya ce, 'Ga ni a kofar gidanki, ki fito. Na ce, ya shigo babu damuwa. Bayan ya shigo falona na dinga jere masa abinci da lemo da na yini ina shirya masa, don ya ji dadi ni ma ya taimake ni. Ya ji dadi da ganin abincin nan saboda yunwar da ta ke addabarsa yini guda bai ci abinci ba, yana ta yawon harhado kan takardunsa. Ya ci ya sha ya mike kafa muka yi ta hira muna kallo talabijin har karfe daya saura, sai da ya fara gyangyadi ya tashi ya yi haramar tafiya bayan na zuba masa takardun da duk ya bukata a ambulan na bashi. Ya kara ba ni hakuri a bisa bakar rayuwar da nake ciki. Ya ba ni tabbacin zai taimake ni insha Allahu. Allah Sarki, abokina kudi mai yawa ya bani da lambobin wayarsa ta gida da ta ofis na can Malaysia. Na yi masa godiaya ya tafi, yana isa Malaysia ya kira ya fada min ya isa bayan kwanaki biyu ya sake shaida min cewar ya fara nema min aiki. Abu kamar wasa an shafe watanni uku babu aiki, hankalina ya yi matukar tashi, na dameshi da waya safe da rana, ina rokonsa ya taimake ni. Har matarsa ta fara kishi da ni, tana cewa wai na rabu da mijinta kada na sake kiransa. Duk bayanin da bayanin da ya yi mata cewar ni kawarsa ce, karatu muka yi tare, amma ba ta yarda ba, kasan mata da kishi. Ban damu ba duk yana daya daga jarrabawa daga Allah. Daga karshe Gaddafi ya fitomin da sakamakon karshe cewar ba zan iya samun aiki a Malaysia ba, sai dai idan zan dawo karatu. Sai dai in zabi bangare daya na karanta har tsawon shekaru biyu ina gamawa sai su ba ni aiki ba tare da wani Cuku-cuku ba. Na ce masa duk wannan ba matsala ba ce, amma ina zan sami kudin da zan dawo Malaysia na yi karatu? Ina zan sami kudin abinci da na hayar gida? Gaddafi ya ce min, duk ba matsala ba ce, zai fada min hanyar da zan bi na sami tallafi daga Gamnatin tarayya. Ya turomin forms ta internate duk na cike na yi ta kaiwa. Kafin lokaci ya yi Gamnati ta yarda zata ba ni tallafin karatu har sai na gama. Kudin makaranta, abinci, kudin hayar gida duk sun biya min wadataccen kudi. Sai da komai ya kankama na shapawa dangina labari, kadanne suka yarjemin, duk ba su bani goyon baya ba. Na nuna musu ba neman shawararsu nake yi ba ina dai yi musu sallama ne tafiya kamar da kasa inji mai ciwon ido. Gaddafi ya taimaka min na sami gida, muka je makaranta ya ya taimaka min nayi registration ina karantar bangaren mata (Gynea). Sai na tsinci kaina cikin sabuwar rayuwa a Malaysia tare da sababbin mutane ba wadanda na sani a da ba. Na yi kokarin na zubar da bakin cikin da yake damuna a baya, na nemo farin ciki na sakawa zuciyata ba don komai ba, sai don kawai na taimaki kaina duniya da lahira. Na yi hakuri, nayi tawakalli na yarda Allah Yana sane da ni, duk yadda Ya tsaro min rayuwata dole haka za a yi. Na yarda da kaddara, yanzu ina shekara ta biyu a karatuna, ina gamawa ina da kujerar aikina a Subang Jaya Hospital idan har na ci jarabawata, wacce ba na fargabar zan fadi. Umaimah da Abdul-Sabur sun buga tagumi suna kallon Faduwa. Tausayinta ya cika musu zuciya, baiwar Allah sai murmushi ta ke don tawakkali. Nan da nan sabon tunani ya kutso zuciyar Umaimah ta tabbatar ashe ba ita kadai ce ta ke da matsala ba a rayuwa. Sai ta ji Faduwa ta burgeta ta da mayar da komai ba komai ba ta ci gaba da rayuwarta cikin kawaye da abokai tana walwala tamkar ba ta da matsalar rayuwa. Amma ita sam ta kasa yin hakan. ''ina ma zuciyata ta sami juriya da tawakkali irin na Faduwa? Umaimah ke fada a zuciyarta. Faduwa ce ta katse tunaninta data ambaci sunanta. Ta ce ''Umaimah, kalle ni nan ki gani. Kinga alamar damuwa ko fushi a fuskata? To haka kowa ya ke dannewa ya manta da komai. Shekaruna talatin da takwas a duniya amma banyi auren fari ba, nan da *yan shekaru zan shiga layin tsofaffi wadanda haihuwa zata dauke musu kuma ban haifi ko daya ba. Har yanzu Allah Bai kawo min miji ba, ga shi ina son aure. Ya ya na iya, sai in daina dariya ko kuma sai na tsani mutanen da babu ruwansu, su suka doramin? Allah ne Yake jarraba ni ya ga yaya zanyi idan Ya doramin masifa. Insha Allah Zai yaye min ko ban samuba a duniya Zai yaye min a lahira. Na yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau. Sai ta kyalkyale da dariya saboda yadda ta ga sun tsura mata ido suna kallonta kai kace talabijin suka saka a gaba. Su dukka suka yi murmushi, gami da jan doguwar ajjiyar zuciya. Abdul-Sabur ya ce, ''Ni har na rasa ma abin da zance da ke, saboda tsabagen tausayi. Sannu Faduwa, sannu da kokarin hakuri gami da juriya. Allah Ya jikan nahaifanki da dan uwanki, ke kuma Allah Ya warware miki. Wallahi ni dai ina ganinki amma ban taba tunanin a cikin wannan halin ki ke cika ba, don ba mu taba zama munyi yi hira irin hakaba. Na ga dai alamar dai ba ki da miji, sai na yi tunanin ko mutuwa ya yi ko rabuwa kuka yi yaranki na can kasarku. Faduwa ta girgiza kai ta ce, ''Babu ko daya, haka nake ni kadai, ba ni da kowa. Umaimah ta ce, ''Allah Sarki, Allah Ya jikansu, mu kuma Ya kyautata namu zuwan. Faduwa ta share hawaye ta ce, ''Ameen, na gode.'' Su dukka sun kasa cin sandwich din, ruwan shayin ne suka kukkurba suka

Chapter 6 of 33