Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta zana ta dawo. **************************************** A lokacin da gaba daya makarantun jami'o'in suka gama jarabawa suka yi hutu, dalibai suka fara yayewa, yayin da Umaimah ta ji a ranta, daman zata iya tafiya kasarta hutu itama don ta gaji da zaman kadaici, sai dai kash! Ba zata iya tafiya ba don ba ta so a san tana raye. Jifa-jifa ta ke hango Faduwa da Abdul-Sabur da alama su ma wannan hutun ba zasu tafi gida ba. Suna nan, don haka sai ta dan ji sanyi a ranata, ta ji ashe ba ita kadai ba ce wacce zata zauna. Duk da ba ta tunanin za su dauke mata kewar komai. Idan taji kamar zuciyarta zata fashe don tunani, sai ta shirya ta fita wuraren shan iska, inda zata ga jama'a daban-daban da abubuwa masu ban sha,awa. Malaysia kasa ce wacce babu abinda suka saka a gaba irin shakatawa musamman daga yamma zuwa dare. Idan ka shiga cikin KL inda tulin malls suke babu abin da zaka dinga jiyowa sai sautin kida. A gefen tituna kuwa jama,a ne da'ira-da'ira sun zage abubuwan kallo kamar masu wasa da maciji, masu kada giraya (giter), masu rufa ido. Kida kuwa duk kusurwar da ka zo giftawa da irin sautinsa, kasancewar baki musamman Turawa suna shigowa sosai don shakatawa. A yau Umaimah yawon nata ne ya motsa don ba ta san takamaimai inda zata nufa ba, zaman gidan ne ya ishe ta niyyarta tunda yamma idan ta fita sai dayan dare zata shigo gida. Don kwanaki biyu ta yi tana bacci ta gaji da kwanciya. Da ta je sayan tikitin jirgin kasa sai ta tamabayesu, ina ne tasha ta karshe idan aka tafi daga nan? Matar mai sayr da tikiti ta zayyano mata cewar. ''Yanzu jirgi zai zo daga KL Centaral, ya shigo ta 'Tunsamban Than' ya zo nan 'Maharjalela', sai ku tafi 'Hangtuah', sai 'Imbi' sannan 'Bukit bin tang, Umaimah ta ce, ''Idan ya wuce Bukit bin tang, sai ya tafi ina? Matar ta ce, ''Zai tafi 'Raja Chuland', 'Bukit nenas' 'Dang Wangi', 'Medantuanku', 'Chow kit' sai ya tsaya a 'Titi Wangsa' sannan ya juyo...'' Umaimah ta yi murmushi, saboda ta ji yawon da akalla zata kai sha biyun dare a hanya. Sai ta tambaya nawa ne kudinta daga Maharjalela zuwa Titi wangsa? Matar ta ce, ''Riggit goma sha uku''. Ta zaro ta biya ta wuce, zuciyarta cike da annuri. Ana ta turmutsitsin shiga jirgi mutumin da ke gabanta ya yi sa'ar samun kujera ya zauna. Ita kuwa a tsaye ta ke ta rike karfe. Bayan ya zauna ya juto ya dubi mutanen da suke tsaye a kansa. Abdul-Sabur ne sai yayi ido hudu da Umaimah itama sai yanzu taga fuskarsa, sai ya yi zuruf ya mike tsaye kai ka ce bawa ne ya ga ubangidansa. Yayin da ita kuma take kokarin kawar da kai gefe har da matsawa da da hanya ma cikin mutane zata kutsa ta bace masa. Cikin harshen Turanci yake magana, don haka duk jama'a na jin abin da yake fada kuma sun zuba musu ido. Ya ce, ''Zo ki zauna, ki zauna ga kujera. Umaimah zo ki zauna. Har sau uku, don babu yadda zata yi ido ya yi mata yawa ta lallabo ta zauna cikin sanda kanta a sunkuye a kasa. Ranta a bace don bata so hadu da wanda ta sani a yammacin nan, saboda ta fito da niyyar yawatawa ta ga gari, gari ya ganta. Ba ta son wani mahaluki ya dame ta kuma. Jirgi dai sai tafiya yake yana tsayawa a tasoshisa dabandaban, ya sauke wasu ya kwashi wasu. Sai ta ga AbdulSabur ba shi da niyyar sauka ta dago ta dube shi, shima ya dube ta sai ya yi mata murmushi, Ya ce, ''Ai ba'a zo Bukit bin tang ba na san a nan za ki sauka, ni ma haka can zan je. Ta tabe baki ta sunkuyar da kai kasa cikin rashin kulawa da zancensa. Ba jimawa aka sanar, 'Bukit bin tang', ya juyo ya kalle ta, sai ta rataya jakarta ta yunkura ta tashi, ta bi bayansa su da dandazon jama,a. Yayin da ta tabbatar ya wuce gaba, sai ta noke ta ki fita ta kutsa lungu cikin mutane ta sami kujera ta yi zamanta a wani bangaren. Ba ta dago da kanta ba sai da ta tabbatar an rufe jirgi yadda bazai iya dawowa ba. Ai kuwa ta hango shi yana ta waiwaye-waiwaye yana nemanta, har ya so ya ba ta tausayi, amma kuma taji sakayau kamar an cire mata kaya da ya sauka. MAKWABTAKA 9 Duk ta karaci yawonta da bata lokacinta a karfe goma ta hawo jirgi ta juyo gida. Da suka zo tashar 'Bukit bin tang' sai suka sauke fasinjoji suka dibi wasu. Kwatsam sai ta ga AbdulSabur ya nufo ta kai tsaye, idanuwansa a kanta suke. A ranta ta ce, ''Ga mayen nan, kamar aljani, duk inda na sa kafata sai na ganshi ko da kuwa kasar na bari. Anya kuwa wannan mutum ne? Ta hada girar sama da kasaa, don tasan ta yi masa laifi kada ma ya ga fuskar tambayarta wani abu. Sai ta cika da mamaki a lokacin da ta ga fara,arsa yadda ka san ba ta taba saba masa ba. Ya yi mata sallama gami da yi mata sannu da dawowa. Ta gyada kai kawai ba ta amsa masa ba, suka ci gaba da tafiya babu abin da yake yi illa kakkare ta da yake, don kada a matseta a lungu saboda karatan da suka cunkushe cikin jirgin. Jirgi ya cika makil saboda kowa ya na so ya koma gida, don dare ya yi. Har yanzu su duk a tsaitsaye suke sun rike igiya babu kujerar zama. Motsi kadan ta yi sai ya juyo ya kalle ta cikin tattausar murya yake yi mata sannu. Sai ta ji kamar ta kurma ihu don takaicin ya shiga harkarta. A haka dai har suka karasa 'Maharjalela'. Babu yadda ta iya, dole ta fito dan niyyarta ta ki fita a wuce da ita wata unguwar, sannan ta dawo idan ya tafi. Kamar yasan haka ta ke nufi, sai da ya tabbatar ya saka ta a gaba suka fito tare. Tafiya kawai take kanta a sunkuye a kasa, tambaya kala-kala da labaru ya ke rero mata, wadanda basu shafe ta ba, ba su shafi tsarin rayuwarta ba. 'Yes ko 'No kawai ta ke jero masa. Har suka sauko daga tashar jirgin suka nufo gida. Tambayrta yake, ya ya kwarin jikinta, cikin ya daina ciwo ko? Ta dago kai ta dube shi a fusace ta galla masa harara ta girgiza kai don takaici gami da dorawa da dan siririn tsaki. Cikin harshen turanci suke magana ta ce, ''Kai.... Kai Abdul-Sabaur, bazan boye maka ba, a gaskiya kana takurawa rayuwata da yawa. Ka sani na baro garinmu, kasarmu na zo kasar da ba a taba sanina ba, ni ma bansan kowa ba, saboda gudun takura. Me yasa zaka nemi saika sanni dole? Bana son damuwa, don Allah ka yi hakuri ka daina shigar min harka, na fi jin dadin rayuwata ni kadai. Murmushi ya yi mata, ya ce, ''Allah Sarki yarinta. Umaimah ki yi hakuri, ki kara hakuri, ko ba ki fada min da baki ba, na san kin takura a yanayinki da nake gani, na san na dame ki. Amma ita rayuwar duniya da kike gani kowa hakuri yake da ita, kuma kowa yana da matsala, wata matsalar ma har ta fi ta ki. A matsayinki na musulma ai ba wannan hukuncin za ki yanke ba na tahowa inda ba asanki ba, kuma ki ki yarda ki saba da kowa idan kika yi haka kamar kinyi fushi ne da kaddarar da Allah Ya dora miki. Musulmi na gari yana fara,a yana mai godiya ga Allah a lokacin da yake cikin tsanani. Ba ki taba jin kissar nan ta wani mutum ba? Wanda bakin cikin duniya ya dame shi, ya je Ka'aba yana dawafi, yana cikin damuwa, yana ta addu'a. Sai ya hadu da wata mata, wacce suke zagaye tare. Fara'a matar ta ke ti fuskarta cike da annuri, gata kyakyktawar gaske. Sai ta burge shi ta bashi sha'awa ya ji dama shine ya sami irin farin cikin da take ciki. Tun yana fada aransa, har ya fito ya tambayeta. Ya ce, 'Yah ke wannan mata, ke kuwa wanne irin farin ciki kike yi haka ne? Daga ganinki ba ki da matsala a duniya. Sai matar ta sake yin murmushi, ta ce, 'bawan Allah ni ce kuwa nake da damuwa, saboda mai gidana ne ya tafi kiwo tunda safe bai dawoba har dare ya yi, ashe mutuwa ya yi a can, sai na aika babban dana ya je ya nemo shi daya tafi shima maciji ya sare shi ya mutu, ma kaji shiru na fita neman su na bar karamin jariri kafin in dawo gida na zo na tarar kura ta cinye shi. Na dawo bani da kowa yanzu a duniya Allah Ya karbe abunSa. Godiyar Allah ce kawai da wadatar zuci yasa kaga ina dariya. Tun daga wannan lokaci mutumin ya daina damuwa da matsalarsa ya ji ashe shi tashi matsalar shafar mai ce. To haka akeso musulmi na gari ya kasance. Umaimah ta dubeshi yayin da jikinta ya yi sanyi, ba ta kara magana ba har suka shiga bakin get. Ta kama hanyar gidanta shima ya nufi bangarensa. Kalmar karshe da ya furta a gare ta, ita ce, ''Bissalam. Ta amsa da ''Ma'assalam. Ta wuce gida yana mai tsananin mamaki da irin kwakwalwa da dadadan kalamai masu tausasawa irin na Abdul-Sabur. Mutum ko shaidan ne sai jikinsa ya yi sanyi idan ya fara yi maka nasiha. Tabbas Abdul-Sabur mutum ne mai rikon addini da iya xama da jama. Amma ita duk da haka bata tunanin taci gaba da zama a gidan nan, don ta ga sannu a hankali AbdulSabur zai sa ta saba da MAKWABTA, ita kuwa ba ta son su saba sam. Sai yau Abdul-Sabur ya fara jin sanyi a ransa a game da Umaimah, yau ce rana ta farko da ta fara bude bakinta ta yi masa doguwar magana, har da ya yi tunanin ko batajin turanci ne sosai shi yasa ba ta son magana. Sai ya ji ta iya Turanci sosai, sai ka ce a kasar Turawa ta yi karatun tubalinta (Primary da secondary). Daga dukkan alamu zaici galaba a kanta, ya fara rusa mata bakar akidar nan da ta saka a ranta, ta kin gaisawa da makwabtanta. Asuba ta gari Abdumaimah !!! *************** *************** A lokacin da Dr. Faduwa ta ga Umaimah a tsaye a kofar falonta sai da ta razana, a lokacin data bude kofa tana shara da sanyin safiyar lahadi. Dr. Faduwa cike da mamaki ta tsurawa Umaimah ido tana kallo, don tana kokonton ko ba ita ba ce, ko kuma mafarki ta ke yi? Umaimah ta lura da hakan, don haka sai ta yi murmushi ta gaisheta. Dr. Faduwa ta tambaya, *Yan mata kuwa, daga ina? Umamimah ta yi mamaki da jin wannan tambayar, don haka sai ta kasa amsa mata. Ta ce, ''Tabbas za ki yi mamakin ganina a gidanki a yau, kuma a dai-dai wannan lokaci, amma kada ki yi mamaki alkhairi ne ya kawo ni. Ko ba ki san sunana ba na san kin san fuskata, ni makwabciyarki ce, sunana Umaimah Bello. Dr. Faduwa ta yi murmushi, ta ce, ''Na gane ki Umaimah, zo ki zauna. Suka dungumaa suka isa cikin falo suka zauna. Yayin da Umaimah ta sunkuyar da kai kasa ba tare da ta san ta inda zata fara ba. ''Ina sauraronki *yan mata''. Inji Faduwa. Umaimah ta dago a hankali ta dube ta, ta yi murmushi. Ta ce, ''Na zo na gaishe da ke, kuma na ba ki hakuri, sannan na yi miki sallama zan tashi daga gidan nan yau, shi ne na ga ya dace na yi muku sallama. Don Allah ki taya ni fadawa abokinki Abdul-Sabur. Dr. Faduwa ta dade tana dubanta ba tare da ta san abin da zata fada mata ba, saboda mamaki da takaici. Can ta yi murmushin karfin hali, ta ce, ''Daman kin shekara ne a gidan ko ba kudin shekara kika biya ba? Umaimah ta sunkuyar da kai kasa ta yi dan murmushi. Ta ce, ''A,a kudin shekara na biya, yanzu watannina tara ina dai so na tashi ne kawai. ''Saboda kin tsani MAKWABTANki ko? Faduwa ta fada cikin gatsali. Sai tambayar ta yi wa kwakwalwar Umaimah nauyi, cike da mamaki ta dago da sauri ta dubi Faduwa tana tuhumarta da idanu. Dr. Faduwa ta sake zaro ido ta dubeta duba irin na ido cikin ido, ta ce, ''Kwarai kuwa zaki tashi saboda kin tsani makwabtanki, suna takura miki da gaisuwa. Sun ishe ki da yi miki sallama a duk sanda ku ka hadu a bakin get a matsayinku na musulmai ku dukka. Babu wannan kaunar ta musulmi da yake yi wa dan uwansa musulmi a zuciyarki. Sai hawaye ya cikawa Umaimah ido ta girgiza kai, ta ce, ''Ba haka ba ne, ina dai so na tashi ne kawai don ra'ayin kaina. Faduwa ta gyada kai, ta ce ''Bazan hana ki yim abin da kike so kiyi ba, haka ba zan sauya miki ra'ayinki ba, kuma ba zan daina yi miki addu'a ba, da fatan alkhairi a rayuwarki ko ba kya tare da mu. Sai dai ina so ki sani kuma ki saka a ranki, kin yi asarar makwabci na gari, mai mutunci da tausayi da sanin ya kamata, wato Abdul-Sabur. Kin tsane shi har tsanarsa ta shafe ni, to ki cire ni ma a ciki don ni tuni na cire shafinki a rayuwata, tunda ba kya so a bawa juna hakkin makwantaka na rabu da ke. Abdul-Sabur ne ba zai iya ba, du ba ki ga duk irin wulakancin da kike yi masa amma bai damu ba, kuma bai daina ba. Kar ki dauka don ke mace ce, kuma mai kyau, a,a ko maza ne haka yake kula da MAKWABTA, don shi cikakken musulmi ne, mai rikon addini duk wata sunnah Manzon Allah (S.A.W) yana rike da ita. Bari na baki wani labarin da ba ki sani ba, ba don Abdul-Sabur ba, da babu wanda zai san kina cikin gidanki kin kwana kina ciwo. Ke ko mutuwa kika yi babu wanda zai sani, don babu wanda ya damu da rayuwarki. Shi ne ya damu da ke, ya ke lura da shige da ficenki, ya ke lura da motsinki a lokacin da kike cikin gidanki. Har ya gano ba ki da lafiya, kamar wancan lokacin da ya sani na zo na duba ko lafiya ya yi sati baiji motsinki ba, kika tula masa kasa a ido, kika ce mu fita harkarki. Ni daman tun daga ranar nai alkawari na rabu da ke. Amma da ya zo min da maganar ciwo in daure in zo in taimake ki a matsayina na likita, dole na je na duba ki saboda zuciyar musulunci da tsabagen magiya da wa,azin da ya saka ni a gaba yana yi. Don haka ki kula da duniya, kuma kisan darajar mutum, ki tabbata za ki mutu halinki na gari shi zai bi ki, kuma shaidar mutane itace shaidar lahira. Umaima ta doka uban tagumi tana mai surnano da hawaye. Ta dade ba ta iya furta kalma daya ba, tana dubam Faduwa tana sauraron labarin da ta ke ba ta na Abdul-Sabur tun daga farko har karshe. Umaimah ta matse hawaye ta dubi Faduwa ta fara magana cikin sassanyar murya a sanadiyyar sanyin da jikinta ya yi. Ta ce, ''Duk abinda kika fada min gaskiya ne kuma nasan duk kuskuren da nake yi, in takaice miki ko a mafarkina Allah Ya nuna min gaskiya. Domin ina yawan mafarki akan makwabtana, sai na ga na shiga hali na tsoro ko na halaka, sai na ga Abdul-Sabur ya zo ya fitar da ni. Na san Ubangijina Yana nuna min darajar makwabtana. Ko a daren jiya na ga na fada rami AbdulSabur ya zo ya fito da ni, wasu lokutan shi kadai, wasu lokuta har da ke. To ashe ke nan Allah Ya na nuna min cewar, kuskure nake yi ke nan da bana kula ku? Nasan ina cikin halaka saboda rashin kyautatawa MAKWABTA, bana so wannan dalili ya sa na halaka shi ne na yanke hukuncin na tashi kawai. Dr. Faduwa ta tambaye ta cike da mamaki, ta ce, ''Kin gwammace gara ki tashi daga gidan ki sauya hakinki na zauna da makwabtanki lafiya? Umaimah ta sunkuyar da kanta kasa can ta dago ta dubi Faduwa ta gyada kai. Ta ce, ''Tabbas ina da dalilina da suka sa ba zan sauya ra'ayina ba akan MAKWABTA. Faduwa ta shiga jinjina kai ba tare da ta sake cewa komai ba. Tsabar mamaki Umaimah ta ke ba ta, ga ta *yar yarinya sai taurin zuciya. A hankali Faduwa ta mika hannu kan teburin da ke gabansu ta dauko wayarta ba ta yi wata-wata ba, ta danno lambar Abdul-Sabur. Ba jimawa ya amsa cikin harshen Turanci suke magana. Faduwa ta fada cike da zolaya, ''Kai da Allah tashi daga baccin nan mu mata ma mun tashi tun asuba balle kai namiji. Ya sake yin juyi ya yi mika, ya ce, ''Ki kyale ni, yau ba ni da wurin zuwa. Ta ce, ''Ko baka da wurin zuwa a da, yanzu ka sami wajen zuwa. Ka zo gidana za ku yi sallama da makwabciyarka, mai shirin tashi daga gidan nan da sanyin safiyar nan. Sai ya mutsike ido ya ce, ''Ban fahimce ki ba Faduwa, wa kenan? Ta yi dariya, ta ce makwabciyarka wacce gidanka ke kallon nata. Ya shiga jero mata yambayoyin da ba ta san amsarsu ba. ''Me yasa zata tashi? Me akayi mata? Kewa ya fada miki zata tashi? Inji Abdul-Sabur. ''Ni ma ban sani ba, ga ta a gidana ka zo kawai ku yi sallama. Tana gama fadar haka ta kashe wayar. Ya dade a zaune bai iya tashi tsaye ba, don yana tunanin mafarki yake yi. Can dai ya katse tunanin da yake yi, ya mike tsaye. Kai tsaye ban daki ya shiga ya yi wanka. Fiye da minti ashirin bai fito ba, Faduwa ta sake rangada masa waya, ya ce ga shi nan zuwa. Aka shafe mintuna biyar bai bayyana ba, har Umaimah ta fara kosawa zata tafi, Faduwa na lallashinta ta yi hakuri ya zo. A karo na uku Faduwa ta kira shi, sai ya tabbatar mata ba zai zo ba ya san karya ta ke yi shi har ya koma ya sake kwantawa. Sai da ya ji ta yi magana cikin fushi, sannan ya shiga bata hakuri gami da yi mata alkawari ga shi nan zuwa. Bai wuce mintuna biyar ba ya bayyana a falon Faduwa, sai da ya ga Umaimah ya gasgata maganar Faduwa, don har ya taho bai yarda ba. Mamaki mabaiyyani ya fito daga fuskarsa, ya dubi Umaimah ya dubi Faduwa, can dai ya zauna, sannan ya sake yi musu sallama suka amsa a lokaci guda. Har zuwa wasu *ya dakikai babu wanda ya yi magana a cikinsu, sannan Faduwa ta dubi Umaimah. Ta ce, ''Ga shi ya zo kuma kinyi shiru. Umaimah ta sake dukar da kai kasa ta ce, ''Ko bai zo ba na ce ki yi masa sallama zan tashi yau daga gidan nan. Ina muku godiya da fatan alkhairi. Abdul-Sabur ya gyara zama ya dubi Umaimah ya ce ''Yarinya, me ya sa za ki tashi ke da ko shekara ba ki yo ba a gidan nan? Sannan ga makarantarku a kusa da gidan ko mota ba kya hawa? Ina kike so ki koma? Umaimah ta dago a hankali ta dube shi, ta ce, ''Damansara zan koma. ''Damansara? Inji Abdul-Sabur da Faduwa suka tambaya a lokaci guda. Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Eh, Damansara. ''Damansara ta yi nisa da makarantarku, kin san da cewa sai kin shiga mota ko? Sabanin nan da kike zuwa makaranta da kafa. In ji Abdul-Sabur. Umaimah ta gyada kai, ta ce, ''Eh na sani. Abdul-Sabur ya cika da mamaki, ya ce, ''Me yasa kike so ki tashi? Anyi miki laifi ne na ga ko shekara ba ki yi ba? Ta gyada kai, ta ce, ''Eh Faduwa ta yi ajiyar zuciya, ta ce, ''Babu irin tambayoyin da ban yi mata ba da nasihohi amma ta ki ji don haka ka kyale ta ka yi mata fatan alheri, don idan ka takurata da tambaya ma kuka zata yi. Abdul-Sabur ya yi shiru yana tunani, can ya dubi Umaimah. Ya ce, ''Akwai wata matsala ne da ta sa dole za ki bar gidan nan? Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ba komai. Ya juya ya dubi Faduwa ya ce, ''Ke ma ba ta fada miki dalilanta ba? Faduwa ta tabe baki, ta ce, ''Ni a su wa da zata fadamin? Amsar da ta ke baka ita ta bani. Abdul-Sabur ya shafa dan siririn gemun da ya zagaye bakinsa, ya ce, ''Nasan dalilinki Umaimah, mu ne matsalarki, musamman ma ni da kike ganin ina takura miki. Ki yi min alfarma ki zauna har zuwa lokacin da za ki cika shekara, nan da watanni uku ni zan tashi na bar gidan. Ki ci gana da zama a nan saboda ya fi kusa da makarantarku, tunda makarantarmu tana Subang Jaya, ni zan koma can kusa da makarantarmu. Faduwa ba ta da matsala ita ba zata takura miki ba, daman ni nake takurawa ta je wajenki. Umaimah ta sake dunkufar da kai kasa saboda nauyin maganar da Abdul-Sabur yake yi. Can ta bude baki zata yi magana sai ya dakatar da ita. Ya ce, ''Kar ki damu, alfarma kawai na ce ki yi min, na san akwai takura, amma don Allah ki daure kar ki tashi, ki zauna. Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ina so na tashi ne kawai ba don ku ba, har ma na sami gida a can na biya na wata uku. Abdul-Sabur ya ce, ''Wannan ba matsala ba ce, kina iya cewa kin fasa tunda ba ki shiga ba, kuma ba ki bata musu lokaci ba, za su dawo miki da kudinki. Faduwa dai ta dade tana dubansu ta cika da al'ajabi. Can ta ce, ''Ai kin fada dazu kin ce saboda mu zaki tashi saboda kin san ba kya kyautatawa makwabtanki. Allah Ya ke nuna miki a mafarki shi yasa kike so ki tashi ba kya so ki halaka, don ba za ki iya sauyawa ba. Abdul-Sabur ya sake lankwashe kafa daya akan daya yana girgizawa, kallon Umaimah kawai yake yi yana so ya ji amsar da zata bayar, sai ta sunkuyar da kanta kasa don ba zata iya dubansa ba. Ya ambaci sunanta cikin wata sanyayyiyar murya, ya kara da cewa. Umaimah, me ye matsalarki ne a gaba daya rayuwarki? Ta dago a hankali ta dube shi da luhu-luhun idanuwanta da suka cika da hawaye. Sai ta girgiza kai alamar babu komai. Ya ce, ''Ko ba ki fada ba, duba daya za a yi miki a san kina da matsala. Kin baro kasarki Nigeria kin zo Malaysia da zummar yin karatu kamata ya yi ki kasance cikin walwala, ko ba a ganki da kowa ba, ya kamata a ganki da kawaye *yar kasarku, amma babu kowa ke kadai kike rayuwarki. Babu ko daya da na taba ganin ku tare. Babban abin da ya ba ni mamaki shi ne, na lura ko wayar hannu ba ki da shi, ba kya kiran *yan gida su ma ba sa kiranki. Ta yaya za,a yi ace iyayenki su turo ki wannan kasa mai nisa su manta da ke ko a waya ba satuntubarki. Umaimah ta fara kuka wiwi, kan ka ce kwabo hankalin Faduwa da Abdul-Sabur ya yi mummunan tashi. Faduwa ta zaro toilet paper ta mika mata don ta share hawayenta. Sai suka shiga lallashinta suna ba ta hakuri. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''yi hakuri ki daina kuka, ba ke kadai ba ce mai matsala, mu dukkanmu nan da kika gani muna da matsaloli manyamanya, wadanda da zamu bude miki mai yiyuwa ma ki ji taki shafar mai ce akan tamu. Amma kinga mun ci gaba da rayuwa, muna gaisawa da mutane, muna da kawaye, muna dariya ba ma jin haushin kowa saboda munyi tawakkali, mun dogara da Allah Shi Ya dora mana, Shi zai yaye mana. Haka ake so duk wani musulmi ya kasance, akwai irinmu da yawa a duniya masu matsaloli da suka linka naki sun yi hakuri suna ratuwarsu cikin walwala idan kin gansu ma ba za ki taba zaton sun taba yin kuka ba a duniya, amma suna bude baki suna fada miki matsalarsu sai kin yi musu hawaye. Umaimah ina mai baki shawara ki cire damuwa a ranki, a matsayinki na musulma duk abin da ta dame ki, ki roki Allah Ya yaye miki, idan wani abu kika rasa ki yi addu'a Allah Ya musnya miki da mafificin alkhairi. Kada kuma laifin wani ya shafi wani kamar yadda kika hada mu gaba dayan mu kika tsana, ba a yin haka, kin ji kanwata. Ina fatan zaki dauki shawarata ki fasa tashi, ki kawo mim rasitin na biyan kudin da kika yi na sabon gidan, zan je na yi musu magana za su dawo miki da kudinki In shaa Allah idan har ba kya son zaman a gidan ni zan tashi nan da watanni uku, sai ki ci gaba da zuwa makaranta hankalinki a kwance. Daga karshe ina yi miki addu,a Allah Ya yaye miki damuwar da ke damunki, Ya ba ki hakuri, Ya sauko miki da walwala a cikin zuciyarki. Ya kare ki daga sharrin masu sharri. Ya ba ki sa,ar jarabawa. Umaimai tana sharce hawaye tama amsa masa da ''Amin.'' ,,, ,,, ,,, ,,, sai an kara kaimi wajen commnt kafin mu kara yawan rubutu... MAKWABTAKA 11 Ta yunkura zata mike gami da yi musu godiya da sallama, sai Faduwa ta mike ta jawo hannunta ta zaunar. Ta ce, ''ba zaki tafi ba, sai mun ci abinci safe (break fast)'' Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''na koshi, na gode. Abdul-Sabur da Faduwa suka hada baki. ''A'a sai kin ci. Yaushe garin ya waye da har kika karya kumallo? Faduwa ta shiga kicin da sauri ta jona ruwan zafi a buta (kettle). Ta jona toaster a inda ta shiga gasa musu biredi da wainar kwai, wato (sandwich). Minti goma sha biyar ya yi yawa komai ya hadu akan dinning table. Ta umarce su da su karaso kan tebur su ci abinci. Umaimah da Aabdul-Sabur da suka dade a zaune suna kallom Talabijin ba tare da dayansu ya sake yin tari ba tun bayan shigan Faduwa kicin, sai yanzu suka motsa suka karaso kan dinning table suka zauna inda kowa ya shiga hada shayi a cikin kofin da yake gabansu. Faduwa sarkin surutu ta dubi Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Allah Sarki *yar yarinya mai kyau, kina da kyau ga ki fara kamar *yan kasarmu Misira kamar ba *yan Nigeria ba. Sai Umaimah da Abdul-Sabur suka kalli juna suka yi murmushi. Abdul-Sabur ya ce, ''An ce miki babu farare kyawawa a Nigeria? *Yan kasarku ne farare kawai? ''Ina ne garinku a Nigeria? Faduwa ta tambayi Umaimah. Yayin da Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Gombe''. Abdul-Sabur ya ce, ''Yauwa ma san ke bafillatana ce ina ganinki na gane haka. Mamaki marar misaltuwa ka ke gani a idon Umaimah, ta ke tambayar kanta da kanta a inda ya san Gombe har yasan Fulani ne a garin. Da ya lura da hakan sai ya dubeta ya yi murmushi, ya ce, ''Kina mamaki yanda na san YARENKI ko? To kibar mamaki, mu dukka nan da kika gani *yan asalin Nigeria ne, kuma Hausa/Fulani. Umaimah ta daina juya shayin ta zuba musu ido tana kallon fuskokin kowannensu. Babu alamar *yan Nigeria a tattare da su musamman ma Faduwa. Ta ina za,a hada Faduwa Balarabiya sak gashinta har tsantsarta mai laushi, farinta tas babu digon baki a jikinta, hanci har baka irin na Larabawan asali amma ace mata *yar Nigeria? Lallai wannan ma so yake ya raina mata hankali. Har ta ji ta tsane shi, tana tunanin rusa duk nasihohin da ya yi mata. Don a zatonta mai tsoron Allah ne a she makaryaci ne? Inji zuciyar Umaimah. Faduwa da Abdul-Sabur sai dariya suke ta yi, saboda kallon karyatawar da suka ga Umaimah na yo musu barobaro. Faduwa ta tambayi Umaimah, ''Kina mamaki ne? Ba ki yarda ba ko? Umaimah ta gyada kai, ta ce ''Eh, ban yarda ba gaskiya. Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''To Faduwa kiyi mata Hausa sai ta yarda. Nan ma dai Umaimah ta sake zaro ido da taji an ambaci yarenta na Hausa. Ta sake cika da mamakin yadda yasan Nigeria har ya san kabilun

Chapter 4 of 33