Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
duk sun farfasa. Umma tayi musu tsawa cikin ba cin rai ta shiga yi musu fada tana nuna musu ba su kyauta ba. Budar bakin Umar ke da wuya, sai ya ce 'Yauwa ga Umaimar ki maimata abin da kika ce a kanta, ni kuma na shiga daki na dauko kur'ani mu yi alwala mu dukka ukun mu dafa, Allah Ya wargaza mai karya.MAKWABTAKA 22 Sai na ji wata gagarumar fargaba yadda ku ka san zuciyata zata fito waje. Na dafe kirji cikin rawar jiki da rawar murya na tambaye su, ''Lafiya, me na yi? Sai Salame ta aiko min harara sama da kasa, ta murguda baki ta sake gyara damarar da ta yi ta shirin dambe. Ta ce, ''Kai da ita dukka munafikai ne, bakinku daya, ko me zaku fada min ba zan yarda ba, amanata kuke ci. 'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Allahumma ajirni fi masibatin wa akhlif ni khairan minha. Addu'ar da na fara fada ke nan a bayyane, yayin da na dafe kirji da hannu daya na rike kai da hannu daya. Kan ka ce kwabo na rikice da kuka, yayin da Umar ma ya fara hawaye don haushin kazafin da ta yi mana. Umma ma ta fusata ta ce, ''Duk ku yi min shuru, Salame wacce hujja gare ki ta cewa suna cin amanarki? Salame ta rike kugu tana girgiza idanunta mursisi babu ko digon kunya, ta dube ni ta juya ta dube shi. Ta ce ''Ga su nan da ran Allah ba zan musu karya ba, ko a gabana ko a bayan idona ba su da buri irin su ga junansu su yu hira. Bini-bini sai ta shigo in ta ga yana nan haka sai ta tarki cewa zata je gidan Lamijo, shi kuma sai ya ce ku shirya in kai ku. Ta madubi ma lekenta yake sai kuma ga lambarta a wayarsa daga ta yi flashin sai ya kira, ya fice kofar gida ya yi mata waya. Kila ma suna haduwa a wani wajen... Ba ta rufe bakinta ba sai na rusa kuka na ce, ''Tsakanina da ke Salame sai Allah ya isa, kin yi mana kazafi don ni ban taba sanin kalar lambar Umar ba, ba mu taba waya da shi ba...'' Umar ya dube ta cike da takaici, ya ce, ''Salame, ki ji tsoron Allah, ke makira ce, kuma idan ba ki nemi gafarar wannan baiwar Allah ba baza ki gama da duniya lafiya ba. Zato kike yi kawai saboda shaidan ya yi miki huduba a zuciyarki. Waya kuwa da kika ji ina yi ba da wata nake ba illa kanwar abokina da aka turo bautar kasa a nan Gombe daga Kano, ba tasan kowa ba a nan na hada ta da wata mata ma'aikaciyarmu ta samo mata gidan haya ta zauna. Sunanta Aisha babu abin da ya hada sunan Umaimah da nata. Sai Salame ta sake rikicewa wai ita za mu mayar *yar iska, marar wayo shi yasa kwana biyu idan zata dauki wayata sai ta ga bana so, don kada ta ga lambarsa ne. Takaici ya sa na fice ina sharbar kuka, na bar Umma da sulhu. Ina shiga daki na fada kan katifa ina rusa kuka, wayata ce ta yi kara, sai na ga lambar Lamijo. Gabana ya sake faduwa, na san labari ya isa gare ta. Na danna a sanyaye ina sauraron abin da zata fada min, zagi ko kuwa rarrashi? Na ji ta cike da fara'a sai ta ce min, ''Albishir! Albishir!! Albishir!!! Har sau uku. Na tashi na goge hawaye na dafe kirji na kagu na ji abin da zata fada min. Ta ce, ''Tafiyarku ta tabbata, an gama komai. Ki shirya gobe ke da Hanif inji Alhaji mijina zai kai ku Abuja ku yi passport da takardunku na ainihi (original) za ku kai federal ministry of education da autentication. Sai na yi ajiyar zuciya mai dadi, na kumshe ido, na zabura na ce, ''Da gaske kike? Alhamdu lillah ke da mijinki Allah Ya saka muku da gidan aljanna. Na gode, na gode. Godiya nake yi mata har ta gaji da amsawa ta kashe wayar, sai na ji zuciyata ta dan yi sanyi daga tafasar da ta ke yi. Na tashi zumbur na fara hada *yar jakata ta tafiya, duk da ba ta fada min kwanaki nawa zamu yi ba, na san dai dole zamu kwana don haka kaya kala biyu na dauka, da katuwar ambulan da na saka takarduna na makarantun da na yi (original certificate). Umma na shigowa na tare ta da farin ciki, na fara shaida mata abin da Lamijo ta fada min yanzu. Sai ta tabe baki ta harare ni. Ta ce, ''Ni ba a zaman munafunci da ni da cin amana, biri ya yi kama da mutum, kwana biyu sai na jiyo ki a daki kina ta waya wanda a da ba kya yi. To ni lafiya nake zaune da MAKWABTANA ba zaki zo ki raba ni da su ba. Idan kin san irin haka zaki yi ta yi, to ki hada kayanki ki yi gaba, shegen kwashekwashe ne da yarda irin na Lamijo ta kwaso ki daga cewa wata daya an shude watanni uku.. Ba ta rufe bakinta ba, sai na ji jiri ya kwashe ni don tashin hankali. Na laluba bango na jingina na zauna na rike kai da hannayena biyu na takure ina ta addu'a Allah Ya yi min agaji, dan na shiga garari, na shiga masifa. Ba ni da mafita sai Allah ne kadai zai fitar da ni. Na kasa magana don ba ni da bakin da zan yi mata bayanin komai ta yarda da ni. Ba ni da masaniya a bisa wayar dare da ta ce ina yi, bayan Lamijo babu mai kirana a duniya, ni ma ita kadai nake kira. Sabon layi ne na siya saboda MAKWABTANA da kawayena na Kaduna suna ta kirana suna yi min maganar Abdul-Basi, wacce ta ke tayar min da hankali, don haka na karya layin na watsar.... Umaimah ta ci gaba da sharce hawaye. Abdul-Sabur ya sake luntsomowa cikin tausayinta, kallonta kawai ya tsaya yana yi, yayin da zuciyarsa ta ke suya tana konewa. Yayin da Faduwa ce mai karfin halin yin magana. Fadi ta ke, ''Allahu Akbar! Sannu yarinya, kin sha takaicin rayuwa ashe. Umaimah ta cije lebe ta kasa ci gaba da magana, har sai da ta dauki lokaci mai tsawo ta yi ajiyar zuciya, ta ci gaba da cewa. ''Rayuwa ke nan tana da wahala, fatanmu dai mu gama da duniya lafiya. Yaro ya ji dadi idan na tuna sanda nake karama ban san bakin ciki ba. Ga uwa ga uba, ga *yar uwa, ga dan uwa, ga kawa ga saurayina. Ba ni da aiki sai rawa da waka, walwala da nishadi kullum amma dubi lokaci guda Allah Ya kwace duk wannan farin cikin ya koma kadaici, ku san kowa nawa ya kare, ba ni da komai, ku san kowa ya tsane ni. Allah mai yadda Ya so da bayinSa. Na gode maSa a kowanne hali Ya bar ni a ciki. Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Kinyi gaskiya yarinya, Allah Yana jarrabar bayinSa ta kowacce hanya. Ki ci gaba da tawakkali Allah Zai yaye miki komai da izininSa, Ya hada ki da madadinsu, Ya dawo miki da wasu daga cikin farin cikin da kika rasa. Umaimah ta gyada kai cikin gamsuwa, ta ce, ''Haka ne, na gode. Faduwa ta ce, ''Yaya na ga kuna kokarin kammala labari alhalin ba ki gama ba mu karshen labarin ba. Yadda aka yi kika zo Malaysia da rabuwarku da su. Umaimah ta ce, ''Ai kawai na fuskanci Ummar Lamijo ta gaji da zamana so ta ke ta kore ni, *yar ce take tausarta kullum. Na shiga daki na kwanta babu barci, sai tunani da kuka har asuba. Na tashi na shirya da sassafe ina jiran isowar Hanif da Babansa. Karfe bakwai da rabi a cikin gidan ta yi musu, suka iske Umma a zaune a tsakar gida, ni kuma na gama shara ke nen. Muka gaisa da su na dauko jakata na rataya na durkusa na yiwa Umma sallama ta amsamin da kyar. Sai ta dinga fada tana sake nanatawa 'a yi dai a hankali, kuma ko me mutum zai yi yayi bisa amana. Da alama dai surukinta bai fahimce ta ba, amma ni na fahimci abin da ta ke nufi, tunda na zama maci amana zan kwacewa Lamijo miji ke nan. Shi kuwa bawan Allah hidima yake yi min saboda dansa da matarsa da yake matukar son abin da su ke so. Muka tafi hanyar Abuja cikin hadaddiyar mota CRB ruwan zuma, sabuwa ce Gar! A ledarta, sai kamshi da sanyin AC ke tashi. Hanif da mahaifinsa suna ta farin ciki annuri fal a fuskarsu, ina baya ina yake da kyar nake kakalo hira da dariya, amma fa hawaye na ke sharcewa a boye. Ba mu karasa Abuja ba sai Lamijo ta kira shi, ta dinga zazzaga magana cikin daga murya, sai na ga ya kalle ni ta madubi yayin da ya ce bari zai kirata idan mun isa, yana tuki ne. Ya yi sauri ya katse wayar, tun daga lokacin na ji ya daina magana, da alama ransa ya baci, jikinsa ya yi sanyi, sai na shiga fargaba kada fa zuga Lamijo suka yi ta shiga zargina. Kai tsaye muka wuce Federal ministry of education daga shigarmu Abuja, ba mu bi layi ba muka bibbiya aka buga mana tambari a jikin takardunmu (stamp) shaidar zamu yi karatu a kasar waje. Sannan muka wuce Ministry of forin affairs suma kai tsaye ya wuce da mu kasancewar yasan wasu daga cikin ma'aikatan don ya yi aiki sosai a wurare daban-daban a nan Abuja. Kafin la'asar har mun gama ya wuce da mu gidansa, da yake unguwar Asokoro. Gida ne babba da get ga wajen ajiye motoci, manyan faluka biyu da wajen cin abinci (dinning area), dakuna hudu kowanne da bandakinsa sai katon kicin guda daya. Mai aikinsa inyamuri da matarsa a boy's kuarters, su ne masu share gidan. An share tsaf an goge, an yi mana girki an jera akan tebur dan sun san da zuwanmu. Muna shiga Alhaji ya nunawa kowannenmu daki daya nasa da bandakai a ciki, kowannenmu ya shiga don ya kimtsa kamar wanka da sallah. Da muka idar muka fito dinnin table don cin abinci saboda muna jin yunwa. Kunyar Alhaji da ladabi ya hana na zauna akan teburi daya mu ci abinci, suka yi ta rokona na ki hawa mu ci, sai Alhaji ya ce, Hanif ya zuba min ya kai min dakina. Na shiga daki na ci abinci yayin da nake jiyo hirarsu a falo. Can na ji Alhaji yana Magana a waya yana cewa. ''Lamijo me yake faruwa ne, wai Umaimah ba kawarki ba ce? Waye ya zuga ki? To ni gaskiya bana son haka, kuma tafiyar nan kamar ta tafi ta gama tunda an gama yi mata komai. Idan kinga ba ta tafi ba to Hanif ma ba zai je ba ke nan. Haba me yasa ku mata ba ku da tunani ne? Tunda abun naki har da zargi to bari na bar gidan na je hotel na kwana. Na bar ta da Hanif su kwana, gobe zamu dawo da sassafe har mun gama abin da zamu yi''. Inji Alhaji yake karadi a waya shi da matarsa, kawata, aminiyata Lamijo, a kokacin da take tuhumarsa, ta ke zargin kada ya ce yana sona ko mu ci amanarta a Abuja. Sai na dafe kirji na mike tsaye yayin da na ji tamkar ba a raye nake ba, dama na hadiyi zuciya na mutu mana na huta. Anya kuwa lafiya irin wadannan bala'ai suke ta rufto min? Duk mutumin da na amincewa sai ya ci amanata. Na tambayi kaina da kaina, yayin da nake magana a bayyane. 'Me yasa kowa ya tsane ni yanzu alhali kuwa ada kowa yana sona? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Na durkusa ina fada yayin da kuka ya hana ni sakat, na kasa ci gaba da cin abincin, ga yunwa ina matukar ji ko abincin safe ban ci ba, sai dan lemo da Alhaji ya siya mana a hanya. Hanif ne ya yi ta kallonsa a falo yana ta nishadinsa, amma ni kadai a dakina ina ta juyi babu barci saboda gagarumar fargaba da kunar zuci. Yadda na ga dare haka na ga safiya na tashi da wuri na yi wanka na takure a lungu gado. Hanif ne da sassafe yake buga min kofa, wai na fito na zo mu karya kumallo, Babansa ya yi waya ya ce mu shirya da wuri ga shi nan zai zo mu wuce Gomben. An shirya mana abin karin kumallo na gani na fada an jera akan dinnin table. Tura abincin nan kawai nake yi a cikina ba don ina jin dadin ci ba, sai saboda kada yunwa ta kashe ni ko kada Hanif ya gane ina cikin halin damuwa. Hira kawai yake yi min cikin farin ciki da dokin zamu je Malaysia, sai ya ce da ni ya ga kamar yanzu ban damu ba alhali a da har na fi shi dokin tafiya. 'Eh ko 'a'a kawai nake ta binsa da shi har muka kammala, sai muka ji tsayuwar motar Alhaji ya iso. Ya aiko ya ce ace mu fito ba zai shigo ba. Muka debo kayanmu muka fito muka iske shi a zaune a cikin mota, gaba daya ya daina wannan fara'ar tasa. Cikin sanyin jiki na gaishe shi ya amsa min cikin sanyayyiyar murya, muka shiga mota muka tafi. Hanif ne kadai mai walwala da surutu ni da Babansa dai to ga mu nan ne dai kawai babu mai son yin magana. La'asar sakaliya suka sauke ni a kofar gidan Umma na yi musu godiya da sallama na shiga gida su kuma suka wuce. Na yi mata sallama, fuskarta babu fara'a ta amsa min, na shaida mata mun iso, ko ta kalle ni ma ta dauke kai. Sumi-sumi na shiga dakina sai na firgita da na ga an hada min dukkan kayayyakina da na baza a gidan a lungu daya. Kamar takalmana, sosona daga bandaki da dai sauransu. Katifar da na lallaye da zanin gado an jingineta a tsaye. Daga nan jikina ya ba ni zamana ya zo karshe a gidan nan, don haka na shiga tunanin inda zan nufa, Abu na farko da na fara yi shi ne, na ware kayan da na fi so kamar kala biyar na bar sauran don ban san yadda zan iya kinkimar rusheshiyar akwatin nan na shiga gari ba. Na zuba a karamar jaka, soso, brush da makilin gami da takalma kala biyu. Saura na dura su a cikin babbar akwatin na rufe na jingineta a gefe. Na shimfida katifar na hau na zauna a hankali. Ina cikin fargaba musamman da na ji tahowar Umma. Tana shigowa sai ta harare ni ta harari katifarta da na shimfida ta tabe baki ta ce, ''Umaimah, yanzu dare ya yi idan Allah Ya kaimu gobe ki shirya da sassafe ki koma garinku ki jira fitowar tafiyarku a can. Bana son zamanki a gidan nan tunda kin fara jawo min fitina, ina tsoron rayuwa, musamman *yar autata da nake son dorewar zamanta a gidan mijinta. Ta zaci zan razana da maganganunta sai taga ko kadan ban rude ba. Na ce mata, ''To Umma Allah Ya nuna mana goben lafiya, na gode ma da karamcin da aka yi min, Allah Ya saka da alkhairi''. Ta fice a fusace, tana fita hannuna yana karkarwa sai na kira Lamijo don na sanar mata gobe zan koma gida. Na yi mata godiya da sallama na roketa idan tafiyarmu ta zo ta sanarmin ta waya. Don na ga akwai waya a Dukku zan dinga fitowa ina kiran ta kullum ina jin labarin tafiya. Sai taki amsa wayar, har ta fara katsewa (rejecting), ina kira sai ta katse. Muka dinga haka fiye da sau goma, mamaki cike da zuciyata. Daga karshe sai na tura mata rubutaccen sako na yi mata duk wadannan bayanai. Har gari ya waye ba ta ba ni amsa ba. Na daina kuka saboda masifar ta yi masifa, addu'a kawai nake yi ina neman mafita, ina so Allah Ya musanya min da muhallin da ya fi irin wanda nake ciki daraja da kwanciyar hankali. Na shirya na fito rataye da karamar jakata na bar babbar a dakin. Na durkusa a gaban Umma na gaisheta.. Na ce, ''Zan tafi Sai ta hararenim ta ce, ''Ban ganki da kaya ba? Na yi murmushin takaici, na ce, ''Zan je na samo mai tasi ne yanzu zan dawo. Ta tabe baki ta ce, ''Kina da kudin motarko? Na yi murmushi na ce, Eh Ban sani ba ko idan na ce ba ni da shi zata ba ni ne ko ba banin zataiba, oho. Ba ni da kudin kirki a jakata, *yan canji ne kawai wanda bai wuce ya kai ni tasha ba.MAKWABTAKA 23 Ina fitowa na ci karo da Salame da mijnta Umar, har yau inajin haushin kallon banzar da ta yi min, ta yi tsaki da tsartar da yawu ta bude gaban motar mijinta ta zauna, ta daka masa tsawa. Ta ce, ''Ja mu je mana, wa kake jira? Ya fisgi mota ya tafi suka bar ni, sai a lokacin na fara kuka. Ina tsaye a kofar gida na dubi gabas da yamma, kudu da arewa ban san inda zan nufa ba. Na yi ta tafiya da kafa na nufi hanyar tashar garinmu da nisa sosai, amma da kafa na je. Sannan na tuna ba ni da kudin da zai kai ni garinmu. A bakin tasha a kofar shagon wata tsohuwar mata mai siyar da abinci da ma'aikatanta da yawa, na zauna na huta. Sannan na karasa gabanta na durkusa a gaban Hajiyar na gaishe ta ina hawaye, na sanar mata ina so na dinga tayata aiki, na ce amma ba ni da wajen zama. Da farko ta ki amincewa, amma da kawarta ta ce, ''ki dauki kyakkyawar yarinyar nan ko don saboda ita ma za ki sami samu masu saya kin san mazan nan suna da son kyawawa. Ai wannan yarinyar kadara ce kar ki bari ta kubuce miki. Sai na ji zuciyata ta harba, na kasa gane abin da matar nan ta ke nufi. Nan da nan Hajiya babba ta yarda ta umarce ni da na shiga cikin shagon da kayana, sai da magriba suke tashi sai mu dunguma mu tafi gida. Na shiga shagon kujeru ne da tebura yayin da duk masu dafa abincin sun yi kama da karuwai, suka hau yi min kallon banza saboda hassada. Dana ajiye jakar kayana a loko sai na koma bakin baranda na hau kan benci na zauna, jikina sanyi kalau. Daya daga cikin ma'aikatan ce ta yi min tsawa wai na zo na karbi abinci na mika ciki, ina ganin masu siya suna ta shiga ciki na sami waje na zauna. Sai na tashi jikina yana rawa na karbi farantin abincin na shiga ciki ba tare da na san wanda zan ba wa ba, maza ne dankar a ciki. Kallona suke sama da kasa, duk da na yafa gyale. Amma sai duk na tsargu. Nan da nan na juya waje na koma wajen matar da ta aiko ni na ce wa zan ba wa? Ta harare ni ta ce, ''Ki ce ina Ali Ali mai mangyada? Sai na koma ciki muryata na karkarwa na tambaya, sai ya yi dariya ya ce, ''Zo nan *yar shila, ga ni nan. Zagayo nan. Na je na ajiye a gabansa sai na ga ya kawowa hannuna cafka, na yi sauri na zame, sai suka kwashe da dariya shi da abokansa. Su ka ce, ''Wannan sabuwar zuwa ce dai ko? Shi yasa ba ta san dawan garin ba. Ali Ali ya ce, ''Haka ne, bakuwa ce dan ko jiya ma na zo ba ta nan. Ke yarinya ki saki jikinki da mu, mune masu yi muku ciniki, gara ma ki saba da mu don a jikinmu zaki sami abin duniya, don shi kika fito nema. Idan kuwa kina bukatar manda sai ki bayar da gishiri. Yana maganar yana kanne min ido kamar tsohon maye. Na shiga zargin anya kuwa ban fada mugun hannu ba? Anya ba a cikin karuwai nake ba? Ai kuwa sai na tsinkayo maza suna kaiwa mata cafka, duk wacce ta zo ajiye abinci sai na ga maza suna wawurarta. Da aka ce na zo na kai abinci a karo na biyu sai na sake lullube jikina na dauki farantin abincin na mikawa wani Alhaji mai katon ciki da gemu, ga shan taba. Yana ganina sai ya zabura ya ce, ''Wai Allah! Wannan halittar fa daga ina? Lallai Hajiya ta yi tsintuwa mai kyau. Ta zo mu yi magana ko nawa ne zan biya don na samu wannan yarinya. Ya dinga dagamin gira alamar iskanci tsantsa a kansa. Rana ta yi aka ce na je na zubo abinci da zai ishe ni na zo na ci akan baranda. Ina kusa da Hajiya babba ta shiga yi min nasiha da lallashin cewar, na kwantar da hankalina na saki jiki da abokan cinikayyarmu. Na kasa gane me ta ke nufi, in bari maza su ringa taba ni yadda suke tattaba sauran ko me...? Abdul-Sabur ya girgiza kai yayin da takaici ya hana shi magana, sai cika yake yana batsewa kai ka ce shirin dambe yake yi. Faduwa kuwa salati ta ke yi tana zabura tana dafe kirji. Umaimah ta langwabar da kai, ta ce, ''Da na idar da sallar la'asar sai na rataya jakata na zo na durkusa a gaban Hajiya babba. Na ce, ''Ki ba ni kwatancen gidanki zan je na sanarwa uwar dakina cewar na sami aiki a wajenki'' Ta girgiza kai ta ce, ''Mai zai hana ki bari sai gobe ki je da wuri zai fi sauki. Na girgiza kai na ce, ''To, bari na yi sauri na je na dawo kafin ku tashi a nan kusa ne unguwar. Ta ce, ''To ajiye jakarki mana, tunda yanzu za ki je ki dawo. Na rasa wannan wayo na matar nan, ko da yake bai kamata na yi mamakin gogewarta akan hikimomi irin haka ba, tunda ta manyanta, kuma gashi idanunta a bude suke tas! Na ce, ''Ai kayanta ne zan mayar mata na debo nawa, ban zaci zan sami aikin ba zuwa dai na yi na tambaya, yanzu da na samu shi ne zan je na sanar mata. Ta ce, to na je na dawo da wuri, na sauke ajiyar zuciya da na ji ta ambaci haka, na tashi jikina yana bari kai ka ce cafko ni za a yi, sai sauri nake yi kamar zan kifa ina yi ina waiwayen baya. Na haye acaba don ina tunanin kudin jakata zai ishe ni na biya shi. ''ina za ki je? Inji Faduwa. Umaimah ta ja fasali, ta ce, ''Wallahi ban sani ba, sai da mai acaba ya fara tafiya yana tambayata ina zai kaini? Fiye da sau uku sannan na fara tunanin inda zan je. Can na ce, ''Ka kai ni ma'aikatar ilimi (ministry of education). Koda ya tambaye ni wacce unguwa ban sani ba. Sai ya ce, ''Koda yake ita ce dai guda daya, bari na kai ki can... Abdul-Sabur ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Me zaki yi a ministry of education? Tambayarsu zancen tafiya zaki yi? Ta girgiza kai, ta ce, ''Na san mijin Lamijo a can yake aiki, sannan ne ina fadar sunansa za su san shi, wajensa zan je na tambaye shi ranar tafiya. A bakin get dan acaba ya ajiye ni na biya shi na shiga ciki a tsorace, ina tsoron kada a koro ni ko ace min ba nan yake ba. Har kasa na durkusa na gaishe da masu gadi, daga dukkan alamu sunji dadin gaisuwar da na yi musu, suka amsa cike da fara'a. Na tambaye su shi da cikakken sunansa Alhaji Nasir Nafada. Sai suka ce ''yana ciki ga motarsa ma bai tashi daga aiki ba. Na ce, ''Ina ne ofisshinsa? Suka fara kwatanta min da hannu, sai suka fuskanci ban gane ba, daya ya taso da sauri ya ce na biyo shi a baya zai kai ni can. Akan bene yake can ciki, ya kai ni har cikin ofishin gami da sanar masa, ''Alhaji ka yi bakuwa. Yana dago ido sai ya ga ni ce, don haka sai na ga ya dan firgita kuma ya cika da mamaki. Ya ambaci sunana, sannan ya ce na shigo ga kujera na zauna. Na yi wa maigadi godiya ya fita ya rufo mana kofa. Maimakon na zauna sai na durkushe a gabansa na barke da kuka mai tsanani ina magana, amma kuka ya hana ni ya fahimce ni. Ya tausaya min matuka, hankalinsa ya tashi, har kwalla ta cika masa ido. Rokona yake na tashi na zauna, na daina kukan na nutsu.. Da kyar na tsagaita da kukan na tashi na zauna, shi ma ya zauna a tasa kujerar yana ta ba ni hakuri cikin Fulatanci muke magana, shi ma bafillace ne. Da kansa ya ce, ''Duk na san halin da kike ciki Umaimah, wannan abu da ya faru da ke kulalliya ce aka hada miki, kawarki Lamijo zuga ta aka yi amma ita ai mai sonki ce. Na sharce hawaye na ce, ''Ummarta ma ta kore ni daga gidanta shi ne na zo na shaida maka bana gari zan koma Rugarmu Dugge, ga shi babu waya balle na ji ranar tafiyarmu. Ko zaka fada min takamaimai ranar da zamu tafi na dawo, ko kuma na karbi lambarka idan har ba zai zama matsala ba na dinga fitowa daga Dugge na zo Dukku na dinga kiranka ina jin labarin tafiya? Sai ya girgiza kai don tausayi, ya yi shiru yana kallona, har tsawon wani lokaci mai tsawo. Can ya dauko wayarsa ya buga, sai na ji ya ambaci, ''Ranka ya dade permanent sectery na kira ne game da maganar tafiya karatun yaran nan Malaysia. Ka ce a cikin satin nan ne wacce ce takamaimiyar ranar tafiyar? Saboda akwai yarinya daya a nan *yar Dugge ce, zata koma Ruga ba su da waya balle ta sani ta fito. Sai ya ce, ''Rana ita yau ne tafiya, talata, amma ranar ake so su hallara a Gombe za a dibe su a mota a kai su Abuja su kwana litinin a sake tantance su a can, sannan talata su wuce. Da ya gama wayar ya yi min duk wadannan bayanai, sai naji sanyi a zuciyata, kamar zanyi tsalle. Sai a lokacin ya ga fara'ata shi ma da alama ya ji sanyi a ransa. Ya miko min lemo da ruwa ya ce, na sha ya shiga tambayata me ye takamaiman tarihin rayuwata? Na langwabe kai na ba shi tarihina kakaf da inda na hadu da matarsa har zuwa rana irin ta yau da muka rabu da ita, wanda bansan dalilin rabuwarmu ba. Sai ya girgiza kai ya ce, ''Na tausaya miki Umaimah, ki yi hakuri Allah Yana bayan mai gaskiya. Ki yi min alkawarin idan kin je wannan kasar zaki kama kanki, ki rike mutuncinki, ki yi abin da ya kai ki, ki dawo gida lafiya. Idan kika yi haka insha Allah sai kin fita daban da *yan rugarku. Sai kin zama abar kwatance a garinku, zaki zama abar alfahari ga gwamnatin garinmu. Idan kika yi min wannan alkawari zan ji dadi, kuma zan taimake ki kamar yadda dolena na taimaki dana na cikina Hanif. Sai na sulalo na durkusa a gabansa. Na ce, ''Allah Shine shaidata, idan na tafi can ba ka ganina Allah Yana ganina, na yi alkawarin zan kama mutumcina, abin da naje yi shi zan yi insha Allah Baba ba zan ba ka kunya ba. Sai ya ji dadi ya yi murmushi, ya ce na tashi na zauna. Na mike tsaye na duka na ce, ''Dare ya fara yi zan tafi garinmu don ba ni da inda zan kwana a nan. Ya ciro bandir din kudi mai yawa ya miko min, sai hannuna ya hau karkarwa don razana da yawan kyautar. Na yi godiya na fito akan ranar lahadi in fito da wuri na zarto gidan gwamna a nan zamu taru a yi mana jawabin karshe. Da na fito daga ofishin na duba kudin *yan naira dari-dari ne dubu goma ke nan. Tasi na hau ban kula masu acaba ba, na nufi Dukku daga Dukku na hau motar garinmu. Daga bakin garin acaba ne dole zai shiga da kai cikin rigagenmu. Ban isa Dugge ba sai bayan sallar isha'i, sai *yan gida suka yi mamaki da ganina

Chapter 14 of 33