Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kasa. Kin fi ni kyau Antina. Itama ta fada a lokacin da take kokarin kulle kofar gidanta. Sai suka yi dariya su dukka suka dinguma zuwa cikin Lifter dan sauka kasa. Suka nufi get din fita daga farfajiyar gidan kamar Umaimah ta tambaye ta Abdul-Sabur sai ta fasa. Su na fita sai taga Faduwa ta nufi wajen wata tsaleliyar mota mai kyawun gaske, kalar baka mai farin gilashi tar! Har shekin kyau take dan sabunta, ko ba'a fada ba ka san sabuwa ce fil! Daga ledarta. Cikin sauri Faduwa ta budewa Umaimah gidan baya, ta shiga tana sanda gami da yiwa mutumin data iske a cikin motar sallama. Ya amsa mata cike da fara'a gami da juyowa a tsanake ya dube ta. Abdul-Sabur Abdul-Rashid ta gani sai ta cika da mamaki tana tunanin inda ya samo aron mota dan bata taba ganinsa da mota ba. Faduwa ta bude gidan gaba ta zauna, ya tashi mota suka hau kan titi suka fara tafiya. Umaimah ta leka fuskarsa ta ce ''happy birhday''. Ya yi murmushi ya ce Na gode. Yayin da Faduwa ta hau magana ba kakkautawa dan ita bata gajiya da magana. 'Eh ko A,a ko ya ce rufemin baki kin fiye surutu' Abdul ya fada mata, yayin da Umaimah ta kunshe baki tana dariya dan ita dariya suke bata kamar wasu *yan tagwaye. Ita Faduwa ta cika magana, ta fuskanci tana damun Abdul-Sabur bashi da surutu. Suka isa wajen da ake ajiye motoci suka sami waje suka tsaya yayin da suka firfito zuwa cikin KL plaza. Suka nufi babban wajen cin abinci, babu abinda babu na ci abinci kasashe kala-kala sai wanda kake so zaka zaba. Suna zama aka kawo musu takarda mai rubuce da duk launin abincin da suke sayarwa a wajen. Sai kowa ya shiga cankar abinda ya fi so ya ci, shinkafa da salad sai *yar miyar gargajiya kaji kadai Umaimah ta zaba. Sai Abdul-Sabur ya ce a'a yayi mata kadan sai ta kara da wasu abinciccikan dan shi so yake a cika kan teburin dankar da abinci da abin makulashe. Ta yi murmushi ''ta ce to a kawo komai ma duk sai a hadu a ci. Ma'aikata sun ga ciniki sai suka hau rawar jiki suka garzaya a rude suka hau harhadowa, ma'aikata a layi suke ta zuwa suna ajiye farantai da kofuna a cike da kayan alatu. Faduwa ta zabura ta mike zata je kicin. Abdul-Sabur ya dakatar da ita da sauri. Ya ce, ''Kin fiye rawar kai, wa kika ga yana shiga kicin, kowa ba'a zaune yake ba su suke zasu kawo komai ba? Faduwa ta mike gami da tabe baki ta ce, ''Ka ga tafiyata, kai ma ka san babu yadda za'ayi in zo waje in zauna dam sai na motsa. Umaimah ta tuntsire da dariya ta bi Faduwa da kallo tana mamakin irin wannan hali nata. Abdul-Sabur ya yi dariya ya dubi Umaimah ya ce ''Kin fara ganin halin makwabciyarki ko? Haka take bata iya zama shiru. Umaimah ta sake tuntsirewa da dariya ta gyara zama ta dube shi ta ce ''Ina son halinta, tana burge ni dan tana da kirki sosai. Dama ka aure ta, da zan so haka wallahi. Ya yi firgigit ta dago da sauri ya dube ta cike da dinbun mamakin yadda aka yi wadannan kalamai suka fito daga bakinta a daidai wannan lokaci. Sai ya dan yatsune fuska ya tambaye ta me ta ce, dan yana tunanin kunnuwansa basu jiyo masa dai-dai ba. Data maimaita sai ya ji abun da ta fada dazu shi ta maimata. Ya gyara zama ya ce ''Me yasa kika yi wannan tunanin? Ta yi murmushi ta ce, ''Kamar yadda na fada dazu tana da kirki kuma ina tausayinta har yanzu bata taba yin auren fari ba. Sai ya sankare a zaune ya kasa amsa mata wannan tambaya. Faduwa ce ta taho dauke da babban faranti dauke da katan kek da wukar yankawa ta zo ta ajiye a gaban AbdulSabur. Ya yi murmushi ya ce, ''Ke ni fa ba wani kek da zan yanka. Faduwa ta yi dariya ta ce ''Sai ka yanka yanzu kuwa. Umaimah ta mike ta nufi kicin yayin da Abdul-Sabur ya ce, ''Au kema kicin din zaki shigar musu irin na Yayarki? Umaimah ta yi dariya ta kada kai ta tafi ba tare data ba shi amsa ba. Sai Faduwa ce ta amsa masa ta ce ''Kada fa ka takurawa kanwata ka bar mu yau mu wataya muna murna da zagayowar haihuwar dan uwanmu. Ya ce ''Allah Ya huci zuciyarku ban hana ku watayawa ba ai. Faduwa ta ciro kyamarar daukar hoto ta ce, ''Bari Umaimah ta zo sai mu fara daukar hoto, kuma ka yanka kek dinka. Yayana me zai hana mu bi yarinyar nan a hankali har ta saki jiki damu sannan mu bayyana mata manufarmu? Abdul-Sabur ya zabura ya dubi Faduwa a gigice ya tamabaya, ''Wacce manufa muke da ita a game da ita? Ta yi dariya ta gyara zama sannan ta kanne ido ta ce ''Ah maganar ka da ita mana, ni fa da gaske nake na maka sha'awarta. Kai ka fi cancanta ka auri yarinyar nan dan ina tausayawa rayuwarta, ta sha wahala gata marainiya. Na yarda dakai, zaka iya rike ta amana. Sai ya sulale ya mimmike a zaune akan kujerar da yake zaune, ya daga kai sama saboda tsabar tashin hankali, dimuwa, mamaki da firgici. Ya ji ko ya tsansa ba zai iya dagawa ba saboda sanyin jiki. Ya hau tambayr kansa da kansa. Wai shin me yake faruwa da ni ne a yau? Yau me yake shirin fado min cikin rayuwata ne haka? Me yasa Umaimah ta yi min sha,awar in auri Faduwa itama Faduwa ta yi min sha'awar ta yi min sha'awar in auri Umaimah? Shin mafarki nake yi ne ko idanuwana biyu? Anya kuwa ba hade min kai suka yi ba suke shirin su waina ni ba? Kai haba ya ma za'ayi a ce sun hada baki, yaushe suka san juna ma? Ya zanyi kuma menene ya kamata in yi? KARKSHEN LITTAFI NA 2.. _________(3)_____ Umaimah ta fito dauke da *yan gwangwanayen fulawar roba a hannayenta ta zo ta jera akan tebur, yadda teburin zai sake kayatuwa. Faduwa ta shiga tarwatun kiran jama'ar da suke zazzaune suna cin abinci, wai su zo su taya su yanka kek din birhday. Masu hali irin nata na rawar kai da son wasa suka ta so yuya guda har da wasu daga cikin ma'aikata, ana tafi ana fadin. ''Happy birhday Abdul'' kamar yadda suka ji Faduwa tana fada suma ita suke ta fada. Takaici ya hana Abdul-Sabur sakat ya ji dama bai zo wajen nan ba, a dole aka kewaye shi ana kirga daya har zuwa goma sannan ya yanka kek, aka hau tafawa kamar wani yaro karami. Sai Faduwa ta shiga daddatsa kek kowa yana caka da colali yana ci. Hotuna iri-iri Faduwa ta dinga yiwa Abdul-Sabur da Umaimah a kusa da shi, babu abinda Umaimah take sai murmushi dan tabbas ta shaki farin ciki a wannan fita. Bayan nan sai Faduwa ta yiwa jama'a godiya game da yi musu tayin su zauna su ci abinci tare da su, da yake kusan kowa an riga an kawo masa nasa abincin kan teburinsa sai suka ki zama suka koma in da suka fito suka zauna suka ci gaba da cin abincinsu. Suma su Faduwa suka zauna suka fara cin jifgin abincin da yake jere akan teburin gabansu, daga gani abincin nan ya fi karfin hanjinsu saboda yawa gashi kaloli dabandaban. Duk wanda ya shigo kafin ya zauna sai Faduwa ta kirashi tebur dinsu, ta yi masa ta yi in akwai abinda ya ke so a ciki ya zauna ya ci ba sai ya saya ba sun saya da yawa saboda bikin birhday da suke yi. Abinci kadan Abdul-Sabur ya ci sai ya daina ci yana daga zaune ya dubi Faduwa, ya juya ya dubi Umaimah, sai ya yi sauri ya sunkuyar da kai, yayin da kwalla ta cika masa ido yana tausayin kansu su dukka ukun. Kasancewarsu gaba dayansu marayu ne, kuma baki a kasar da babu danginsu. Haka su dukka ukun bagware ne, ba su da mai kula da su, kowannensu shi kadai a cikin gidansa kamar maye. Ya fi tausayin matan ma akan kansa, rayuwar mace a gurgunce ta ke muddin ta kai munzalin aure, kuma ba ta yi ba. Sai zuciyarsa ta shiga saka masa hanyoyi daban-daban da zai bi don magance wadannan matsalolin da suka addabe su. Faduwa ta dubi Umaimah ita ma ta dubeta, gaba daya suka tsurawa Abdul-Sabur idanu, tabbas sun ga ya sauya yanayinsa, ya shiga halin tunani a dai-dai lokacin da suke hayaniyarsu su kadai. Babu wacce ta tambaye shi me yasa saboda kowacce ta san dalilinsa na yin haka, sai dai dalilin kowacce daban, ya sha ban-bam da na dayar. Faduwa tasan tayi masa maganar ya auri Umaimah ta san maganar ce ta ke yi masa zillo a zuciyarsa, ita ma Umaimah ta san maganar data yi masa kan ya auri Faduwa ita ce ta toshe masa a kahon zuci. Abin da ba su sani ba shi ne, farin ciki maganarsu ta saka masa a rai, ko kuwa damuwa, ya amince ko kuwa bai amince ba? Shawarar da yayanke shine ya auri Faduwa Umaima kuma ya aurawa Dan Aunty..lolx.. Ehemm. Ko ya kukagani en uwa.? MAKWABTAKA 26 Kallon da suke yi masa shiyasa ya hanzarta farfadowa daga duniyar tunani ya karkato hankalinsa gare su, ya biye musu aka yi ta hayaniya da ciye-ciye. Karfe tara na dare suka baro 'KL plaza, kai tsaye suka wuce da motar wajen ajiye motocin da yake cikin gidansu. Yayin da suka firfito kowannensu cikin fara'a suke yiwa juna sallama da fatan Allah Ya tashe su lafiya. Faduwa da Umaimah suka nufi bangarensu, yayin da Abdul-Sabur ya nufi na sa bangaren. A cikin lift Faduwa da Umaimah hirarsu kawai suke yi cikin harshensu, wato Hausa. Wasa da dariya gami da dimbin nishadi ne ya tabbata a zukatansu. Kaunar juna, gami da rashin jin dadin rabuwa suke ji a cikin kalbinsu. Faduwa ce ta ba Umaimah hannu suka gaisa gami da rungume ta, ta sumbaci gefen kumatunta irin gaisuwarsu ta Larabawa, a lokacin da aka zo hawa na goma sha takwas wato gidanta. Lokacin rabuwarsu ta zo kenan amma fa a yau. Kalmar karshe da ta fadawa Umaimah ita ce 'Bissalam. Ta fice daga cikin lift yayin da kofar lift ta rufe kanta, umaimah da sauran jama'a suka karayin sama, a hawa na goma sha tara Umaimah ta fice ta nufi gidanta fuskarta cike da annuri, har waka take rerawa a hankali cikin harshenta na fulatanci. Wakar nan da suke yi a dandali ita da kawarta Matawata, wacce suke kiran junansu kawata, masoyiyata kuma makwabciyata. Abun tambaya a nan shine Faduwa ce ta maye gurbin Matawata, ko kuwa Abdul-Sabur ne? Asuba ta gari Fadu-maimah-sabur!!! Shigar kowannensu gida ba tare da bata lokaci ba ya yi wanka da kuma sallar isha'i, bayan saka rigunan baccinsu, sai suka haye gado yayin da kowannensu ya shiga tunanin dan uwansa suna masu tunano abubuwan da suka faru da su a dazun nan. Haduwarsu ta zame musu tamkar a mafarki, suna mamakin yadda haka ta kasance. Matsananciyar shakuwa da kaunar juna nan da nan ta wanzu a ransu. Bacci mai dadi ya kwashe su a lokaci daya, saboda sun gaji ya hadu da mafarkai kusan iri daya, abubuwan da suka faru dazun suke maimaita gani a mafarki. Umaimah ta yi firgigit ta bude ido tana mai murmushi a fuskarta sai ta ga ashe fa a mafarki ne, Abdul-Sabur ta yi mafarki yana yi mata magana. Ya ce da ita, ''Umaimah kinga abin da nake fada miki ko? Annabi (S.A.W) ya yi gaskiya da ya ce, ''dukkan musulmi dan uwan musulmi ne'' Ta yi firgigit ta tashi zaune ta dafe kirji gami da jinjina kai tana mai gasgata wannan maganar da ta ji a mafarki. Sai ta yi cimak ta sauko daga kan gado ta je jikin tagar dakinta ta daga labule ta leka gidan Abdul-Sabur. A tsaye ta gan shi a jikin tagarsa aka yi katari yana kallonta, sai ta sake firgita ta saki labulen tagar da sauri tana ambaton. ''Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Anya wannan mutum ne? Ta dade a tsaye a tsakar daki ta rike baki tana mamaki, can ta suri filo ta fito falo kan doguwar kujera ta zauna, bacci ya gagare ta, don haka ta tashi ta shiga kicin ta tsaya, ta dade a tsaye sannan ta tuna kishirwa ta ke ji, kasancewar an ci maiko dazu. Ta bude firij ta dauko robar ruwa ta tsiyaya a kofi ta kurba. Sai ta jiyo magana a waje kan baranda kamar muryar Abdul-Sabur. Cikin sanda ta bude kofar da zata kai barandar waje, tana budewa sai ga Abdul-Sabur muraran shi ma atsaye akan barandarsa ta kicin yana mai dubanta yana murmushi. Ya na magana amma a waya cikin wani yare wanda ba nata ba. Dan haka ba ta gane me yake cewa ba, sai ta yi sauri ta tura kofar ta rufe ta gaggauta kashe fitulun gidan gaba daya tana mai tottofa addo'o'i a kowacce kusurwa ta cikin gidan. Ta shige daki ta haye kan gado can cikin lungu ta kudundune a cikin bargo tana ta makyarkyata saboda tsoron daya kamata. Tana tunanin anya kuwa AbdulSabur mutum ne, ko kuwa aljani ne yake shigarsa don ya tsorata ta? Da kyar ta yi bacci bayan da ta daina jiyo maganarsa da kuma motsin shige da fitar da yake yi a cikin gidansa. Ko bayan da ta yi baccin ma mafarkinsa ta ci gaba da yi har yanzu dai nasihohin yake yi mata a mafarki, wannan karon kuma babin mace ta yiwa mijinta biyayya yake bayani. TIkon Allah, wannan shi ake kira boyayyen al'amari, ko mene ne ma'anar hakan? Allah Shi Ya barwa kanSa sani. Asuba ta gari Fadumaimasabur. *************** Dif Umaimah ta bace kwana biyar ma ba su sake ganinta ba, haka ba sa jin motsinta a gidan, a makaranta ta ke yini idan ta taso sai ta wuce Bukit bing tang ta ci abinci a restaurant bayan ta zazzagaya malls sannan ta dawo gida da daddare ta kwanta, ko fitila ba ta kunnawa balle a san tana ciki. Amma koda yaushe MAKWABTAnta suna cikin ranta, kuma ba ta da mummunan zato a kansu, saboda ta saba da zaman kadaici, shi yasa ba ta damu ta neme su ba. Ranar juma'a bayan masallci tana cikin tunaninsu, sai kuwa ta ji bugun kofa gami da jiyo muryoyinsu, babu tantama tasan su ne sai ta rasa dalilin jin farin ciki a cikin zuciyarta. Da sauri ta bude musu kofa bayan ta zumbula dogon hijab. Yadda ta ke murna da ganinsu har sun fita murna, saboda dariyar da ta ga suna bangalawa. Ta yi musu iso zuwa cikin falonta suka shigo suka zauna akan doguwar kujera su biyu a jere. Ta zauna a kujerar da ta ke fuskantarsu cike da ladabi ta duka ta gaishe su, sannan ta koma ta gyara zama ta dube su ta yi dariya, ta furta kalmar da gaba dayansu suka dimauce, aka hau kallon-kallo. Cewa ta yi, ''Kun ba ni sha'awa da na ganku a tare, Allah Ya tabbatar da alkhairi, mafarkina ya zamo gaskiya. Musamman Faduwa ta fi Abdul-Sabur rashin fahimtar abin da Umaimah ta ke nufi, ga rashin wadatacciyar Hausa, ga rashin sanin ainihin kan maganar, saboda ba ta san maganar da Umaimah ta fadawa Abdul-Sabur ba a kanta. Ita ma kuma yanzun nan ta sake furtawa AbdulSabur sabuwar maganarsa da Umaimah shi ne ma dalilin da yasa ta taso shi a gaba don su zo su ganta duk da ita ma tana tsoron furatawa Umaimah wannan batu. Tana gudun kada ta ki amincewa kuma ta shiga gudunsu, don tasan halinta. Duk da Abdul-Sabur bai bata goyon baya ba akan aniyarta ta hada shi da soyayya da Umaimah ba, har ya kan yi fushin gan-gan idan tayi masa maganar, amma ta san nokewa yake yana so yana kaiwa kasuwa. Shi ma kuma ya kasa fada mata abin da yake zuciyar Umaimah na yunkurin hada aure da ta ke yi. Faduwa ce ta takurawa Umaimah da tambayoyi akan ta yi mata FASHIN-BAKI akan maganar da ta yi dazun. Hausa cikin Hausa Umaimah ta sake rikita mata kwakwalwa, sai Faduwa ta dawo turanci dan ta ji Hausar ta gagare ta, duk da haka Umaimah ta goce ba ta bari ta fahimci abin da ta ke nufi ba. Abdul-Sabur ya gane, dariya kawai yake kyakyata musu daga karshe dai ya kawar da hirar ya shigo musu da wata hirar wacce ta shafi kowannensu, wato hirar makaranta da shirin fara jarabawa. Umaimah ta mike cikin nutsuwa ta ke tafiya ta nufi kicin dinta, ba jimawa ta fito hannayenta dauke da kwalin lemo da kuma kofuna guda uku, ta kawo tsakiyar kujeru (center table) ta shiga tsaiyaya musu, ta durkusa ta mikawa kowannensu sannan ta sake tashi ta shiga kicin. Faduwa ta dubi Abdul-Sabur ta yi murmushi, magana ta ke yi masa cikin rada. Ta ce ''Ka ga abin da nake fada maka ko? Yarinyar nan ta dace da rayuwarka, nutsattsiya ce ga ladabi. Sai ya harareta ta kawai ya sunkuyar da kai, sai ta kyalkyale da dariya. Umaimah ce ta fito dauke da farantin tangaran da 'cake' da biskit a cikinsa ta kawo ta ajiye a gabansu, ta koma ta zauna suka ci gaba da hira da kallon talabijin. Faduwa ta kurbi lemo, ta gyara zama ta ce, ''Umaimah ba ruwanki da neman MAKWABTANki ko za ki shekara ba ki gansu ba ko? Umaimah ta yi sauri ta dubi Abdul-Sabur, yayin da ya yi saurin kawar da kansa gefe tamkar bai san abin da suke cewa ba. Kunyarsa ta ke ji saboda nasihohin da ya dade yana yi mata akan ta sauya wannan mugun halin na kin mutane. Ta yi saurin sauya hira, amma sai Faduwa ta sake jeho mata wata tambayar. Ta ce, ''Ba kya neman mutane a waya ko ba ki zo inda muke ba, sai mu dinga gaisawa a waya, koda yake ko lambobinmu ma ba ki karba ba. Wannan karon ma Umaimah Abdul-Sabur ta sake kallo, yayin da yaki yarda su hada idanu, ya ci gaba da matsa remote yana sauya tasha a talabijin. Faduwa ta ce, ''Ba ni lambarki, ga tawa. Ta dauko wayarta tana jiran Umaimah ta karanto mata lambobin. Takaicin tonar asirin da Faduwa ke kokarin yi mata ta toshe zuciyarta, ba ta so aka yi wannan hira agaban Abdul-Sabur ba, saboda kada ya zaci ba ta sauya ra'ayinta ba har yanzu. Cikin sanyin murya ta ke ba wa Faduwa amsa ''Ai ba ni da waya. Don firgita Faduwa har da dafe kirji, ta dauki dogon salati kai ka ce mutuwa aka yi. Ta ce ''Kamar ya ya baki da waya? Ta bata ne ko ba ki taba yin waya ba daman can a rayuwarki? Umaimah ta yi dan murmushin karfin hali, ta ce ''Ban taba yin waya ba daman can a rayuwata. Kallo daya Abdul-Sabur ya yi musu ya juyar da kansa ya ci gaba da kallon talabijin. Faduwa ta zungure shi, ta ce ''Aboki, ka ji ikon Allah, wai Umaimah ba ta da waya, a rayuwarta ma bata yi waya ba, ko ta zaci a ruga take har yanzu? Su dukka ukun suka kyalkyale da dariya. Abdul-Sabur ya ce, ''Matsalata da ke ke nan, kin cika kwakwazo, meye abun mamaki don bata da waya? Kowa fa da ra'ayinsa. Faduwa ta ce, ''Da mamaki mana yadda duniyar nan ta ci gaba, almajirai a cikin kauye ma rike waya suke yi balle ita da ta ke birni. Birnin ma irin Malaysia, a Malaysia ma a babban birnin Kaula Lumfur, kuma a jami'a. Haba Umaimah me yasa haka, ya ya kike da *yan gidanku, samarinki, da kawayenki? Abdul-Sabur ya tsurawa Umaimah ido yana jira ya ji amsar da zata bayar, sai ta ki magama ta sunkuyar da kanta kasa, murmushi kadai ta ke yi. Faduwa dai ba ta daina mamaki ba, haka ba ta daina yi mata tsiya ba, har sai da Abdul-Sabur ya mike tsaye ya ce zai tafi masallaci, ya ji ana kiran sallar la'asar. Faduwa ta tashi ta bi shi suka fice. Umaimah ta raka su har kofar bakin lift suka yiwa juna godiya, sallama, gami da fatan alkhairi suka shige lift suka tafi, ita kuma ta p dawo gida tana maijin sanyi a ranta, kasancewar a halin yanzu tana samun baki a gidanta, ta sami wadanda suka san da ita suka damu da lafiyarta, wadanda zata yi hira da su har su saka ta dariya. Bayan kwanaki biyu da zuwan su Faduwa gidanta, ranar lahadi da yamma Umaimah ta shirya ta rufo gidanta ta shiga gidan Faduwa don ta gaishe ta. Faduwa ta yi matukar mamaki gami da farin cikin ganinta. Ta mike da sauri ta rungume Umaimah ta kamo hannunta ta zaunar da ita akan kujera. Sai a lokacin Umaimah ta dubi mata biyu da suke zaune a kan sauran kujerun. Ashe baki gare ta, daya inyamura, daya *yar Malaysia. Uhum! Faduwa mai mutane, kawayenta kala-kala daga kowacce kusurwa ta duniya tana da kawaye mata da maza. Umaimah ta daga musu hannu ta gaishe su, gaisuwar dai ta hello da hi ce, don ba ta ga alamar musulunci a tattare da su balle ta yi musu sallama. Suka amsa mata cikin fara'a su ma yayin da Faduwa ta gabatarwa kawayenta Umaimah, sannan ta gabatar da su ga Umaimah. Sun jima suna hira bayan sun ci, sun sha, Umaimah ta yi musu sallama kasancewar magruba ta kusa. Su ma lambar wayar Umaimah suke tambaya. Faduwa ta yi sauri ta ce, ''Ina da ita, zan baku anjima. Saboda ta ga Umaimah ta rasa amsar da zata ba su. Bayan tafiyar Umaimah sun dade suna yiwa Faduwa zancenta cewar, tana da kirki ga hankali. Sannan ta ba su sha'awa yarinya kyakkyawar gaske kamar ba *yar Africa ba. Faduwa ta yi musu alkawarin zata kawo musu Umaimah har gidajensu wata rana. Misalin karfe goma na safiyar wata litinin Umaimah ta bude barandar kiicin dinta don shanya hankicin da ta gama goge-gogen gidanta. A tsaye ta iske Abdul-Sabur shi ma akan barandarsa yana shan iska, sun kwana biyu ba su hadu ba ko akan hanya. Ta dan razana da ganinsa, ta yi kamar zata koma ciki, sai ta daure, ta dake, kasancewar ta daure kanta da dankwali duk da riga da wandon bacci ne a jikinta, amma dogaye ne ba kanana ba. Suna hada ido sai suka yiwa juna murmushi, ta duka ta gaishe shi. ''Umaimah daman kina nan? Kwana biyu kin buya. Abdul ya tambaye ta. Cikin kadabi ta ba shi amsa. ''Ina nan, lafiya kalau. Ta ci gaba da shanya, ya gyara tsayuwa ya ce, ''Ba a ganinki sosai, ko makaranta ce? Koda yake masu ganinki suna ganinki, Faduwa ta ce kusan kullum sai kun hadu, idan ba ta je gidanki ba, ke kina zuwa. Har ma kun je unguwa jiya tare. Umaimah ta yi murmushi, ta gyada kai ta ce, ''Haka ne. Ya gyada kai, ya ce ''Yana da kyau, kuma na ji dadi da samun wannan canjin. Ki ci gaba da yin hakan, saboda zaman kadaici ba dadi. Ta yi dariya ta ce, ''Insha Allah zan ci gaba da yin haka. Ya ce, ''To na gode idan ba zaki damu ba da yamma mu hadu a gidan Faduwa ina son magana da ke. Sai ta ji zuciyarta ta harba nan da nan ta ji hankalinta ya tashi, ta shiga mamakin dalilin neman ta da yake yi. Mamaki cike a fuskarta a bayyane ta dube shi cikin sanyayyiyar murya ta tambaye shi, ''Lafiya? Ya yi murmushi ya gyada kai, ya ce, ''Kar ki damu, ba wata matsala ba ce face alkhairi. Ta gyada kai a sanyaye ta ce, ''Allah Ya kaimu yammar. Ta juta ta shiga gida. Ta dade a zaune akan kujera tana sake-sake a zuciyarta tana ayyano mata abubuwa daban-daban da ya sa yake nemanta anjima a gidan Faduwa. Ko dai maganar nan da ta yi masa za'a tayar, wacce ta yi masa na ya auri Faduwa, yake so ta maimata a gaban Faduwa? Idan dai haka ne ai ta kwana gidan sauki, sai ta maimaita ba wani abu ba ne, alkhairi ta ke so ta hada. Daga karshe ta mike cimak ta je ta yi wanka, ta shirya ta fito zuwa makaranta tana da darasi da karfe goma sha biyu. Dai-dai get din gidansu ta ci karo da Abdul-Sabur da Faduwa a cikin tsaleliyar motarsa za su fita da alama makaranta za su tafi. Sai da suka rage gilashin motar ta hango su, sannan ta gane su ne, suka yi mata izini ta shigo su tafi. Zata yi gardama Abdul ya ce ta shigo su tafi ba ya bukatar wani bayaninta. Ta bude gidan baya ta zauna, ya ja mota suka fara tafiya. MAKWABTAKA 27 Daga dukkan alamu dalibai da malamai a yau sun cika da mamaki da suka ga Umaimah tana magana da wasu bil'adama har ma da shiga motarsu. Sai kowa ya yi ta kallon Abdul-Sabur da Faduwa suna ta yi musu jinjina bisa namijin kokarin da suka yi har Umaimah ta aminta da su. Musamman kawayenta *yan Nigeria kuma *yan garinsu suka yi tsuru-tsuru suna kallonta suna kallon mutanen da suke cikin mota, da alama dai sun san ba *yan uwanta ba ne, amma kuma ga shi ta saba da su. Abdul-Sabur ya dubi Umaimah, ya ce, ''Karfe nawa za ki tashi in zo in dauke ki? Ta girgiza kai, ta ce, ''Kar ka damu, zan dawo da kaina, ai ba dadewa zan yi ba yau. Faduwa ta ce, ''To mu zauna ki shiga ki yi lecture ki fito mu ma sai ki raka mu tamu makarantar da yamma sai mu dawo tare. Umaimah ta kyalkyale da dariya ta ce, ''Haba Aunty Faduwa, ya za'a yi ku zauna ku jira ni kamar wata Sarki? Ku je makarantarku. Kada ku jira ni, ni ai ba ni da nisa, na gode Allah Ya saka muku da alkhairi. Faduwa da Abdul-Sabur ma suka yi mata fatan alkhairi, ya ja motarsa suka tafi, yayin da Umaimah ta juya ta dubi dumbin idanuwan da suke kallonta. Ta shiga karanto kula'uzai a zuciyarta don kada baki ya kamata. Tabbas an saka mata ido a makarantar nan hakan ya samo asali ne ta sanadiyyar rashin kula su da ta ke yi, kuma jama'a da dama suna son shiga harkarta. ************************* Umaimah ba ta baro gidanta ba sai bayan da ta idar da sallar magruba. Ta ci sa'a kuwa tana shigowa gidan Faduwa ko zama ba ta yi ba, Abdul-Sabur ma ya shigo, Umaimah ta dube su ta yi murmushi. Ta ce, ''Ku yi min afuwa na makara ban zo da yamma ba kamar yadda na yi alkawarin zan zo, na yi bacci ne ban tashi ba sai bayan la'asar sosai, shine ya sa na bari sai da na yi sallar magruba sannan na shigo. Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce ''Ba damuwa, tunda yamma na zo muke ta jiranki ga shi na samu na je masallaci na yi sallah nima,

Chapter 16 of 33