Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MAKWABTAKA Na Jamila Umar Tank Ebook publish by - http://hausaebooks.cf PART 1 A cikin jerin dogayen gininnikan da suke kan titin Maharjalele, Kaula Lumpur babban birnim Malaysia. Da misalin karfe takwas na safiyar litinin, ga sanyin safiya, ga sanyi daga gandun dajin da yake gefen gidajensu yana kadowa. Iskar da ke kadawa ta yi dai-dai da yanayin garin saboda zafi-zafin da ake yi. Nan da nan sai mazauna garin suka sami nishadi da walwala a wannan safiyar. Motoci na gani na fada ne suke ta giftawa a wannan titin, yayin da wasu jama'a da yawa suke ta wurwucewa da kafafuwansu. Halittar Ubangiji kala-kala, Allah daya gari bam-bam, kowacce kasa da nata yanayin haka da irin kalar halittunta. Matansu sanye suke da riga da siket na yadi (material) mai kama da atamfa, sai dan guntun hijabi iyaka kirji, wasu kuwa riga da wando suke sakawa (jeans da blause), sai su saka hijabi ko dankwali babba. *Yan mata *yan gayu kuwa gajeren wando suke sakawa iya cinyarsu da *yar shimi. Mazansu kuwa sukan daura zani da riga ko riga da wando da hula mai kama da Pakistan launin bakake ko wasu kalolin. *Yan gajeru ne yawancinsu, farare tas-tas masu gajeran hanci da luhu luhun idanuwa, suna da gashi mai tsayi da tsanani laushi da baki. Kusan gaba dayansu musulmai ne kadan ne suke yin wani addinin. Amma duk da haka ba sa shari,ar musulunci, kowa yana holewarsa yadda yake so. Akwai bakaken indiyawa wadanda asalinsu bayi ne aka kawo su suma yanzu sun zama *yan kasar suna addinin Hindu. Sunan kudinsu Riggit, yana da daraja sosai idan aka hada shi da Naira dan har ya fi Saudi Riyad daraja. Umaimah Bello tsaleliyar budurwa matashiya wacce shekarunta basu wuce ashirin da biyar ba. Bakar fatace *yar Africa amma tafi wasu fararen fatar kyau nesa ba kusaba. Fara ce sosai idan ta shiga cikin fararen ba dukka ba ne zasu nuna mata fari ba, haka hanci, idanuwa masu kyau, baki dan madaidaici gani da gashi mai tsawo da laushi. Kirar jikinta kuwa ba kowacce mace ba ce ta sami irin wannan kirar. Umaimah doguwa ce ba tsawo tsololo ba, marar kiba amma ba bushashshiya ba. Tsaye take akan barandar gidanta, bene hawa na goma sha tara, tana kallon kasa tana shakar daddadan yanayin garin. Daga gani babu tambaya ta sami nishadi saboda annurin da yake kwaranya a fuskarta. Matsatstsan lemon zaki ne ta matse a kofin tangaran (fresh orange juice) a hannunta. Idan ta leka ta kalli titi, sai ta kurbi lemon nan mai sanyi. Kallon kowannensu take daya bayan daya, ta ga suna tafe a nutse cikin nishsdi. Sabanin tadda *yan kasarta suke Nigeria, kowa yana tafe a zabure kai ka ce koro shi aka yi, wasu suna tafe suna lissafin kudin cefane saboda masifa da suka sha mana kai. Sai tausayi ya rufeta har kwalla ta cika mata ido, musamman da ta tuno danginta na karkara Fulani masu kiwon shanu. Ta fada a bayyane, ''Allah Ka kawowa kasata Nigeria agaji, mu ma mu samu ci gaba kamar *yan kasar Malaysia. Tana daga ido ta kalli ginin gidajen da suke fuskantar gidanta, sai ta yi arba da mutumin nan mai nacin kallonta shi ma a tsaye yake a barandarsa. Daman ta ji ajikinta ana kallonta kamar yadda ya saba. Ta galla masa harara, ta ja dogon tsaki ta shige gida cike da tsananin takaici, musamman yanda ya ganta daga ita sai *yar yaloluwar rigar bacci koriya iya gwiwarta, kanta babu dankwali. Ya yi murmushi yana shirin ya gaishe ta sai ta koma cikin gida da sauri. Tana shiga falonta sai ta daga labule ta leka barandar ta ga baya nan, daga nan ta tabbatar daman don ita yake fitowa ya tsaya da ta koma shi ma ya bar wajen. Ta kuduri niyyar shirya masa rashin mutunci muddin ya ci gaba da takura mata da hana ta sakewa a farfajiyar gidanta. Bakar fata ne, amma daga ganinsa ba dan Nigeria ba ne. Koma dai dan wacce kasa ne yana da kyau da kyawun sura, dogo ne sosai mai dan kiba kadan, fari ne sol, mai hanci da gwarza-gwarzan idanuwa, mai yawan fara,a gami da fararen hakora a jere reras a cikin bakinsa madaidaici. Daga ganinsa yana da tsafta dan dan gayu ne na karshen zamani. Tun daga gashin kansa zuwa gemunsa zaka gane tsaftarsa koda yaushe zaka ga suna sheki, kamshin turarensa kuwa tun daga benenta take fara jiyowa. Ta daga ido ta kalli agogo, karfe takwas saura kwata. Tana da darasi (lecture) karfe tara don haka sai ta hanzarta fadawa wanka, kan ka ce kwabo ya gama shiryawa ta fito tsaf sanye da riga me dogon hannu launin ruwan hoda (pink blause), wando (jeans) baki da takalmi (cover shoe pink) sai dan hijabinta baki iya kirji irin na *yan kasar Malaysia. *Yar karamar jakar (computer laptop) ta ratayo a kafadarta ta rufo gidanta, ta fito. Ta hadu da jama,a da yawa a lift (*yan Malaysia, Chinese, Indian) da sauransu, amma ba su ishe ta kallo ba balle ta yi musu murmushi saboda bata sha,awar ta saba da MAKWABTANTA. Tana isa kasa ta fito daga lift ta kama gabanta sannan ta nufo get din fita. Abun mamaki sai ta ci karo da mutumin na mai nacin kallonta, wanda gidansa yake saitin gidanta shima a hawa na goma sha tara yake, amma gininsu daban sai dai get dinsu daya saboda duk gida daya ne. Nan danan ta sake tsuke fuska ta kara daga kafa tana sauri, domin taga ya fara mata wannan murmushin nasa. Yana da niyyar ya gaisheta, ita kuma bata bukatar hakan. Saurin da take ya wuce misali, don haka nan da nan ta bace masa, sai da ta waiga ta ga ba ta hango shi ba, sannan ta rage tafiya ta ci gaba da tafiyarta a nutse. Tana hawan matattakala zata tsallaka gada zuwa daya hannun kasancewar kasashen da aka ci gaba ba,a tsallaka titin mota sai dai su bi ta gada. Hawan matattakala da wuya sai ta ji ta gaji likis, kasancewar hawan da yawa. Kwatsam ta ji wata lallausar murya a gefenta cikin harshen turanci ana yi mata sannu da aiki. Ta waiga da sauri, sai ta ga mutuminta, makwabcinta. Ta yi mamaki da ganinsa saboda ta dade da tsere masa, sai dai idan ta lunguna ya biyo ba ta titi ba, don ta waiwaya ba ta ga kowa na biye da ita ba. Cikin harshen turanci yake magana, sai da ya jero mata tambayoyi har guda uku ba ta amsa masa ko guda daya ba, harya fara tunanin ko ba ta jin turanci ne? Sai ya shiga yi mata maganar gwarawa ya fara kacaccala Turancin yadda ko dan koyo zai gane. Ya ce, ''Are you from Sudan? Libya? Egypt? Ethopia? Or Mali?'' Sai ta harare shi ta kawar da kai ta ci gaba da tafiya. Hat yanzu dai yana biye da ita yadda ta ke sauri haka shi ma yake yi. ''What is your name? Yasan dai dole tasan wannan kalmar, sai ya sake ganin wata sabuwar harara daga gare ta, ta kalle shi sama da kasa , cikin takaici ta ce, ''MAYE kawai, sai nacin tsiya !'' Ta yi murmushi ya ce, ''Your name is Maye? Wow nice name. A zatonsa ta ce sunanta maye. Ya bita yana ta bayani cukin harshen Turanci, duk magana daya sai ya ambbaci sunan nan ''MAYE. Sai takaici ya sake karuwa a zuciyar Umaimah ta rasa yadda zatayi dashi, kalmar karshe da ya fada mata ita ce. ''My name is Abdul-Sabur'' Da ya ga da gaske ta kufula sai ya kyale ta, ta wuce ta nufi hanyar makarantarsu ko tantama babu a FTMS GLOBAL COLLEGE ta ke yi, don ya ga ta nufi hanyar makarantar. Idan kuwa *yar jami,ace ya za a yi ta ce ba ta jin Turanci? Sai dai idan idan ba ta da niyyar amsa masa ne, wannan hujjar mai karbuwace. Tunda ta sunkuyar da kanta kasa tana tafiya ba ta kara dagowaba balle ta waiwayo bayanta. Ba ta tsaya a ko'ina ba sai a cikin ajinsu, a inda ta sami kujera ta zauna. Zamanta ke da wuya sai Malami ya shigo ajin ya fara yi musu darasi akan abin da ta ke karantawa, wato soft ware engineering. **************************************** Washe gari misalin karfe goma na safe Umaimah ta sake fitowa ta nufi makaranta sanye ta ke da bakar abaya, sauri ta ke saboda tana da test karfe goma sha daya. Yau ma a bakin get ta ci karo da mutumin nata Abdul-Sabur, shi ma zai fita. Sanye yake da wata nakar (suit). Sai da ta yi da gaske ta gane shi, don ya sauya taga ya kara kyau. Ya yi mata murmushi sannan ya yi mata sallama gami da dorawa da ambaton sunan nan da yake zaton sunanta ne, wato, ''MAYE''. Nan da nan ta ji ya bata mata rai, ta harare shi ta wuce ba tare da ta amsa masa ba. Sai ya shiga mamakin yadda *yar musulma ta ke da bakar zuciya haka ko sallama ba ta amsawa. Ba shi kadai ta ke yiwa haka ba,daga dukkan alamu harda sauran MAKWABTAN, don ya ga yadda ta ke tafiya a fusace ba ta ko kallon inda suke. Tunda yaga Dr, Faduwa ta wuce ba su gaisa ba ya san tabbas abin ya fi karfin Dr. Faduwa, watakila ta gwada sau daya ta ga babu riba, dole ta kyale ta don ba don haka ba ya san yadda ta ke da matukar son mutane, gata da fara,a ko ka ganta ko ba ka ganta ba zata yi maka magana. Ya tsaya suka gaisa da Dr. Faduwa, sannan suka dunguma su uku suka yi bakin titi. Umaima na gabansu su biyu suna baya suna ta hirarsu cikin harshen Nasara (English). Dr. Faduwa balarabiyar Egypt ce. Allah Ya yi halittarsa anan saboda ko a larabawan ma kafin ka sami mai kyauwu irin na Faduwa sai ka bincika. Bata da tsayi kuma tana da *yar kiba amma a dire take, hanci dogo, ga manyan idanuwa, da lallausan gashi har yana taba cinyarta dan ma koda yaushe tana cikin yanke shi. Gata *yar gayun gaske ce tana shiga suturunta na larabawa a mutunce, kallo daya zaka yi mata ka tabbatar likita ce dan sana,ar ta dace da surarta. >>>>>>>>> MAKWABTAKA <<<<<<<<< PART 1 A cikin jerin dogayen gininnikan da suke kan titin Maharjalele, Kaula Lumpur babban birnim Malaysia. Da misalin karfe takwas na safiyar litinin, ga sanyin safiya, ga sanyi daga gandun dajin da yake gefen gidajensu yana kadowa. Iskar da ke kadawa ta yi dai-dai da yanayin garin saboda zafi-zafin da ake yi. Nan da nan sai mazauna garin suka sami nishadi da walwala a wannan safiyar. Motoci na gani na fada ne suke ta giftawa a wannan titin, yayin da wasu jama'a da yawa suke ta wurwucewa da kafafuwansu. Halittar Ubangiji kala-kala, Allah daya gari bam-bam, kowacce kasa da nata yanayin haka da irin kalar halittunta. Matansu sanye suke da riga da siket na yadi (material) mai kama da atamfa, sai dan guntun hijabi iyaka kirji, wasu kuwa riga da wando suke sakawa (jeans da blause), sai su saka hijabi ko dankwali babba. *Yan mata *yan gayu kuwa gajeren wando suke sakawa iya cinyarsu da *yar shimi. Mazansu kuwa sukan daura zani da riga ko riga da wando da hula mai kama da Pakistan launin bakake ko wasu kalolin. *Yan gajeru ne yawancinsu, farare tas-tas masu gajeran hanci da luhu luhun idanuwa, suna da gashi mai tsayi da tsanani laushi da baki. Kusan gaba dayansu musulmai ne kadan ne suke yin wani addinin. Amma duk da haka ba sa shari,ar musulunci, kowa yana holewarsa yadda yake so. Akwai bakaken indiyawa wadanda asalinsu bayi ne aka kawo su suma yanzu sun zama *yan kasar suna addinin Hindu. Sunan kudinsu Riggit, yana da daraja sosai idan aka hada shi da Naira dan har ya fi Saudi Riyad daraja. Umaimah Bello tsaleliyar budurwa matashiya wacce shekarunta basu wuce ashirin da biyar ba. Bakar fatace *yar Africa amma tafi wasu fararen fatar kyau nesa ba kusaba. Fara ce sosai idan ta shiga cikin fararen ba dukka ba ne zasu nuna mata fari ba, haka hanci, idanuwa masu kyau, baki dan madaidaici gani da gashi mai tsawo da laushi. Kirar jikinta kuwa ba kowacce mace ba ce ta sami irin wannan kirar. Umaimah doguwa ce ba tsawo tsololo ba, marar kiba amma ba bushashshiya ba. Tsaye take akan barandar gidanta, bene hawa na goma sha tara, tana kallon kasa tana shakar daddadan yanayin garin. Daga gani babu tambaya ta sami nishadi saboda annurin da yake kwaranya a fuskarta. Matsatstsan lemon zaki ne ta matse a kofin tangaran (fresh orange juice) a hannunta. Idan ta leka ta kalli titi, sai ta kurbi lemon nan mai sanyi. Kallon kowannensu take daya bayan daya, ta ga suna tafe a nutse cikin nishsdi. Sabanin tadda *yan kasarta suke Nigeria, kowa yana tafe a zabure kai ka ce koro shi aka yi, wasu suna tafe suna lissafin kudin cefane saboda masifa da suka sha mana kai. Sai tausayi ya rufeta har kwalla ta cika mata ido, musamman da ta tuno danginta na karkara Fulani masu kiwon shanu. Ta fada a bayyane, ''Allah Ka kawowa kasata Nigeria agaji, mu ma mu samu ci gaba kamar *yan kasar Malaysia. Tana daga ido ta kalli ginin gidajen da suke fuskantar gidanta, sai ta yi arba da mutumin nan mai nacin kallonta shi ma a tsaye yake a barandarsa. Daman ta ji ajikinta ana kallonta kamar yadda ya saba. Ta galla masa harara, ta ja dogon tsaki ta shige gida cike da tsananin takaici, musamman yanda ya ganta daga ita sai *yar yaloluwar rigar bacci koriya iya gwiwarta, kanta babu dankwali. Ya yi murmushi yana shirin ya gaishe ta sai ta koma cikin gida da sauri. Tana shiga falonta sai ta daga labule ta leka barandar ta ga baya nan, daga nan ta tabbatar daman don ita yake fitowa ya tsaya da ta koma shi ma ya bar wajen. Ta kuduri niyyar shirya masa rashin mutunci muddin ya ci gaba da takura mata da hana ta sakewa a farfajiyar gidanta. Bakar fata ne, amma daga ganinsa ba dan Nigeria ba ne. Koma dai dan wacce kasa ne yana da kyau da kyawun sura, dogo ne sosai mai dan kiba kadan, fari ne sol, mai hanci da gwarza-gwarzan idanuwa, mai yawan fara,a gami da fararen hakora a jere reras a cikin bakinsa madaidaici. Daga ganinsa yana da tsafta dan dan gayu ne na karshen zamani. Tun daga gashin kansa zuwa gemunsa zaka gane tsaftarsa koda yaushe zaka ga suna sheki, kamshin turarensa kuwa tun daga benenta take fara jiyowa. Ta daga ido ta kalli agogo, karfe takwas saura kwata. Tana da darasi (lecture) karfe tara don haka sai ta hanzarta fadawa wanka, kan ka ce kwabo ya gama shiryawa ta fito tsaf sanye da riga me dogon hannu launin ruwan hoda (pink blause), wando (jeans) baki da takalmi (cover shoe pink) sai dan hijabinta baki iya kirji irin na *yan kasar Malaysia. *Yar karamar jakar (computer laptop) ta ratayo a kafadarta ta rufo gidanta, ta fito. Ta hadu da jama,a da yawa a lift (*yan Malaysia, Chinese, Indian) da sauransu, amma ba su ishe ta kallo ba balle ta yi musu murmushi saboda bata sha,awar ta saba da MAKWABTANTA. Tana isa kasa ta fito daga lift ta kama gabanta sannan ta nufo get din fita. Abun mamaki sai ta ci karo da mutumin na mai nacin kallonta, wanda gidansa yake saitin gidanta shima a hawa na goma sha tara yake, amma gininsu daban sai dai get dinsu daya saboda duk gida daya ne. Nan danan ta sake tsuke fuska ta kara daga kafa tana sauri, domin taga ya fara mata wannan murmushin nasa. Yana da niyyar ya gaisheta, ita kuma bata bukatar hakan. Saurin da take ya wuce misali, don haka nan da nan ta bace masa, sai da ta waiga ta ga ba ta hango shi ba, sannan ta rage tafiya ta ci gaba da tafiyarta a nutse. Tana hawan matattakala zata tsallaka gada zuwa daya hannun kasancewar kasashen da aka ci gaba ba,a tsallaka titin mota sai dai su bi ta gada. Hawan matattakala da wuya sai ta ji ta gaji likis, kasancewar hawan da yawa. Kwatsam ta ji wata lallausar murya a gefenta cikin harshen turanci ana yi mata sannu da aiki. Ta waiga da sauri, sai ta ga mutuminta, makwabcinta. Ta yi mamaki da ganinsa saboda ta dade da tsere masa, sai dai idan ta lunguna ya biyo ba ta titi ba, don ta waiwaya ba ta ga kowa na biye da ita ba. Cikin harshen turanci yake magana, sai da ya jero mata tambayoyi har guda uku ba ta amsa masa ko guda daya ba, harya fara tunanin ko ba ta jin turanci ne? Sai ya shiga yi mata maganar gwarawa ya fara kacaccala Turancin yadda ko dan koyo zai gane. Ya ce, ''Are you from Sudan? Libya? Egypt? Ethopia? Or Mali?'' Sai ta harare shi ta kawar da kai ta ci gaba da tafiya. Hat yanzu dai yana biye da ita yadda ta ke sauri haka shi ma yake yi. ''What is your name? Yasan dai dole tasan wannan kalmar, sai ya sake ganin wata sabuwar harara daga gare ta, ta kalle shi sama da kasa , cikin takaici ta ce, ''MAYE kawai, sai nacin tsiya !'' Ta yi murmushi ya ce, ''Your name is Maye? Wow nice name. A zatonsa ta ce sunanta maye. Ya bita yana ta bayani cukin harshen Turanci, duk magana daya sai ya ambbaci sunan nan ''MAYE. Sai takaici ya sake karuwa a zuciyar Umaimah ta rasa yadda zatayi dashi, kalmar karshe da ya fada mata ita ce. ''My name is Abdul-Sabur'' Da ya ga da gaske ta kufula sai ya kyale ta, ta wuce ta nufi hanyar makarantarsu ko tantama babu a FTMS GLOBAL COLLEGE ta ke yi, don ya ga ta nufi hanyar makarantar. Idan kuwa *yar jami,ace ya za a yi ta ce ba ta jin Turanci? Sai dai idan idan ba ta da niyyar amsa masa ne, wannan hujjar mai karbuwace. Tunda ta sunkuyar da kanta kasa tana tafiya ba ta kara dagowaba balle ta waiwayo bayanta. Ba ta tsaya a ko'ina ba sai a cikin ajinsu, a inda ta sami kujera ta zauna. Zamanta ke da wuya sai Malami ya shigo ajin ya fara yi musu darasi akan abin da ta ke karantawa, wato soft ware engineering. **************************************** Washe gari misalin karfe goma na safe Umaimah ta sake fitowa ta nufi makaranta sanye ta ke da bakar abaya, sauri ta ke saboda tana da test karfe goma sha daya. Yau ma a bakin get ta ci karo da mutumin nata Abdul-Sabur, shi ma zai fita. Sanye yake da wata nakar (suit). Sai da ta yi da gaske ta gane shi, don ya sauya taga ya kara kyau. Ya yi mata murmushi sannan ya yi mata sallama gami da dorawa da ambaton sunan nan da yake zaton sunanta ne, wato, ''MAYE''. Nan da nan ta ji ya bata mata rai, ta harare shi ta wuce ba tare da ta amsa masa ba. Sai ya shiga mamakin yadda *yar musulma ta ke da bakar zuciya haka ko sallama ba ta amsawa. Ba shi kadai ta ke yiwa haka ba,daga dukkan alamu harda sauran MAKWABTAN, don ya ga yadda ta ke tafiya a fusace ba ta ko kallon inda suke. Tunda yaga Dr, Faduwa ta wuce ba su gaisa ba ya san tabbas abin ya fi karfin Dr. Faduwa, watakila ta gwada sau daya ta ga babu riba, dole ta kyale ta don ba don haka ba ya san yadda ta ke da matukar son mutane, gata da fara,a ko ka ganta ko ba ka ganta ba zata yi maka magana. Ya tsaya suka gaisa da Dr. Faduwa, sannan suka dunguma su uku suka yi bakin titi. Umaima na gabansu su biyu suna baya suna ta hirarsu cikin harshen Nasara (English). Dr. Faduwa balarabiyar Egypt ce. Allah Ya yi halittarsa anan saboda ko a larabawan ma kafin ka sami mai kyauwu irin na Faduwa sai ka bincika. Bata da tsayi kuma tana da *yar kiba amma a dire take, hanci dogo, ga manyan idanuwa, da lallausan gashi har yana taba cinyarta dan ma koda yaushe tana cikin yanke shi. Gata *yar gayun gaske ce tana shiga suturunta na larabawa a mutunce, kallo daya zaka yi mata ka tabbatar likita ce dan sana,ar ta dace da surarta. MAKWABTAKA 3 Manyan ledoji biyu ta cika makil da kaya, don haka ta fara tunanin hawa tasi wacce zata kai ta har kofar gida zai fi yi mata sauki don idan ta ce zata bi jirgi zata sha wuyar hawa da sauka benaye. Don haka saita tsaya a titi ta tsayar da tasi ba tare da bata lokaci ba, ta shige ita da kayanta dukka. Ta sanar masa inda zata je, ya danna meter suka nausa. Da suka isa unguwar sai ta dinga nuna masa hanya har bakin get din gidan su. Ta biyashi Riggit 10 ne cif-cif, sannan ta jido ledojinta ta fito mai tasi yaja motarsa ya tafi abinsa. Kamar daga sama ta ji wata murya wacce ta ke kokarin gusar mata da farin cikin da ta kunso daga BB Plaza. Kalmar ''MAYE'' ta ji ya ambata, Ta waiwayo a fusace Abdul-Sabur ne ya nufo ta da farin cikin sa. Ta ji kamar ta kifa masa mari, sai tayi tsaki ta juya da sauri yayin da nauyin ledojin hannunta suke rinjayarta. Cikin harshen Turanci ya ce, ''Maye, taimakonki da leda daya, saboda naga kayan sun yi miki nauyi. Ba ta amsa masa ba, sai ta ci gaba da tafiya, ya kai hannu zai karba ta daka masa tsawa. Cikin harshen Hausa yau ma ta yi masa magana. Kai ! Ka kyale ni, dole ne? Duk da ba ya jin yarenta ya ga alamar fushi a fuskarta, ya san fada take yi masa. Don haka sai ya sakar mata ledarta ya tsaya cak yana kallonta har ta haye branda, ta ci gaba da jan Ledojinta sannan ta shige lift ta haye sama. Masu suna daga zaune suna kallonsa daga dukkan alamu suna tausaya masa saboda kacaccalawar da ta yi masa. Ya wuce gidansa ransa ba dadi, babu abin da bai saka ba a ransa game da Umaimah, ya kudira har karshen rayuwarsa ya daina kula ta. Tunda Umaimah ta shiga gida ta rufe dukkan wundunanta da kofofinta ta kashe fitulun dakunan falo da korido, kicin dinta ne kawai da fitila. Ac da talabijin ce kawai a kukkunne. Wanka, Salla, cin abinci, karatu bacci da kallo kawai ta ke yi acikin gidannan ita kadai, sai da ta shafe sati guda cur ba ta leka wundo ba ma balle ta fito baranda ko ta fito waje. Tana ta kallon yanda ake ta bukukuwan kirsimeti a talabijin, ba ta damu ta ga kowa ba kamar yadda ba ta so itama aganta. Dama a ce ba sai ta fita makaranta ba za,a dinga turo mata darasin da za a koya mata ta computer, ba dan dole ba ba zata sake lekowa waje ba, don ita wannan rayuwar ta ita kadai ta fiye mata dadi. A ranar ne da daddare misalin karfe goma na dare, ta ji ana buga mata kofa. Mamaki marar misaltuwa ne ya rufo mata, don tunda ta ke a gidan nan ba ta taba yin baki ba, ba ta da kowa a kasar nan. *Yar karamar shimi ce a jikinta da gajeran wando nan danan ta yayimi zubulelen hijabinta ta saka tana sanda ta zo ta leka ta hudar da ke jikin kofa. Sai ta ga wata mace duk da batasan sunanta ba, tasan MAKWABCIYARTA ce, sun sha haduwa a lift ko a bakin get amma basa magana. Kawar Abdul-Sabur ce, don tana yawan ganin su tare, wato Dr.Faduwa. Sai taki budewa, kuma har

Chapter 1 of 33