Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da nake so * komai wuya komai dadi". “'Na ji". Nan ya mike ya fice. Momi murna ya lullubeta, tace lallai na yarda tabbas Deeda alheri ce a tare da ita dalilinta yau ta sa ta samu kamfani gaba' daya , "Wow! Amina'kudi kan kudi bari' ta_ Shigo in san ‘daba'run da zan yi in turata ta fara zuwa masa aiki. " yau‘. ,*.*j .*9*, *9* . Deeda ta ga fitar Sabeer, .don haka ta tashi ta koma cikin Falo ta samu ‘ Momi. Har za ta‘wuce ta kirata; "20 mana Deeda, magana‘zamuyi". "To Momi". . . Ta fada lokacin da take kokarin zaunawa., Momin ta ce, "Deeda magana zamu yi, don Allah ina so in rokeki wata alfarmane, wani aiki na ke so in qara miki, amma in zai miki yawa zan iya rage miki wasu daga cikin ayyukan da ki ke min”. ‘ "To ina jinki Momi". _"Wani aiki ne"? "Allah Yasa‘dai baif1 karfina ba". Momi ta gyara zama ta. ce, "Daman ina son ki dinga zuwa Bangaren dana kina kularmasa dashi, ne kina gyara masa‘ kamar yadda kike gyara min. , . " Deeda ta kalleta cikin ware ido da alamar zai yiwu? Ta‘ce; "Hajiya namiji nefa, kuma- bai da mata "Karkidamu, in ya fita da’ Safe sai ki gyara ki dawo‘ ba-zama za ki yi acan ba. kamar: girki 'in kin dafa kawai ki shirya a Table ki dawo‘ — Dana ne bashi da matsala ba zai miki «bin da ki ke tunani ba, ki yarda' da ni ba zan kaiki inda 2a a cutar da ke ba, kuma ba zan bada dama ya cutar'da ke ba, yaran gidan nan suna da tarbiyya ~suna: da halin girma. Please Deeda taimakona za kiyi". Haka Momi ta marairaice .tana' rokon Deeda, duk da ta .san‘ wani tsiyar Sabeer ya shirya mata DOn dole Deeda ta amince da buqatar Momi sannan sabo da Ibrahim, amma ba don ta so hakan ba. - Ta ce, ke nan Hajiya na ji zan dinga zuwa namasa in dawo, amma fa in ya némi ya keta min mutunci ba Zan kyale ba,~ zan dau mataki. Sannan zan yi magana da Inna mai Fura in ta amince shi ke nan". '~‘To' kar ki damu ba sai kin je ba ma zan sa a daukomin; ita zan nema mata Wurin zama a BiRNIN GAYU. ta dawo kusa da ke, inaga zaki fi Sakewa in kuna zuwa aikin tare da ita Deeda tayi wani lallausan.murmushin jin dadi. ' ‘ - Ta ce, na gode, za ki dawo da kaka kusa da ni "Kwarai Déeda. wannan qaramin aikine ne da zan iya yi sabo da abin da ki ke min :na. kyautatawa kuma wannan aiki da kika karba yau. Komai zan'iya sabo da farincikinki, don. Haka zan dauko Kakarki in dauki nauyinku, ,zan ba ku gurin zama da dukkan wani abu .na jin dadin rayuwa da zaisa ki farinciki". "Na gode Momi, Allah ya saka DA alkhairi "Ameen. Sai dai Deeda ina son ki fara aikin daga yau, sannan please ki bishi ahankali yana da saurin fishi’da'zuciya, yananda fada, amma ba shi da matsala, kar ki damu Deeda ta ce, "To hajiya na ji". A ranta kuma ‘té cr "Ni kuwa nasan fadansa da halinsa, kuma nasan ya yi hakanne donya kuntata min shi ya sa ya bullo ta nan, sai dai zan jure wulakancinsa". Nan ta mike ta yi ciki, ta canja shiga sannan ta dauki 'Waya~za ta bugawa Ibrahim. Kafin ta kai ga kiransa Wayarsa ta shigo. Ta yi. saurin .dauka tare da yin 'sallama "Daman ina shirin kiranka". ne yanxu ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin ’, yanzu aka yi Waya aka fada min abin da‘ ya daure min kai, ina tsammanin Sabeer ya samu Waya a wurin wani a gidan nan. Ya kira Legal Adviser dinmu da kuma MD. na Kamfaninmu da ke Lagos ya ce yana so'ya barwa Momi Kamfaninsa Ya za akayi Sabeer ya dauki Step din-nan ba tare da sanin Daddy ba,kuma na rasa dalilinsa, na son yin“haka, yana so a hada Takardu a kawo masa Deeda ta yi ajiyar 'zuciya ta Ce, "Sai yanzu na fahimci abin da ya sa Momi ta ke lallaBani. Wai Sabecr ya dauki wannan abin da tsananin da zai iya yin komai don kawai ya dau 'fansa ya nunamin matsayina." ' ne ' "Me ya faru?" Ibrahim ya tambaya. Nan ta labarta masa yadda akayi. Ya yi shieu na dan gajeren lokaci ya Ce, "Sabeer ne fa, "kadan daga aikinsa ke nan (He Will just do anything Crazy) don kawai ya cimma manufarsa. Sabeer fltinanne ne akan abin da ya sa gaba ko yayi niyya. Deeda ina gudun kar Sabeer ya cutar da_ ke, ban zaxa zai Bullo mikita‘wannan hanyar ba (He will to run you) za ki‘iYa kuwa?" "Zan iya Ibrahim in dai wahala ce ai ba ta kisa, wuya kuwa a cikinta aka haifeni a 'cikinta na tashi na girma". "Duk da haka Deeda in kin‘ga ba za ki iya yiba‘ to kibari kina ji?" - "Na ji". "Na gode". ' "Kar ka damu, ai Kudi Momi -za ta biyani' aiki na ne". . Dariya ya yi gami da girgiza'kai ya ajiye Wayar. ' ' "Deeda ke nan, wani lokaci halinta kama yake min da na Sabeer". Nan ya shiga tunanin. yadda zai tsai da_ deal din da sabiecr .ya_ yi_ da Momi Deeda kuwa Mayafinta ta dauko ta fito Momo da kanta ta rakata bangaren Sabeer. din Sun yi tafiya mai dan tsaWo tamkar ba a gida daya suke ba, akwai tazara tsakanin bangaren Momi da na su Sabeer. Sun sami Sabcer zaune falo ya dora kafa daya akan daya yana kadata yana jiran isowarsu. ' Tun daga falon Hajiya ta fahimci halin da gidan yake, gaba daya akwai Ta ce, "Sabecr ga Deeda, 'sai dai aiki za ta yi maka ta tafi. Kuma don Allah a kiyaye", . Kansa ya dage‘bai kulata ba, 'hakan ya sa ta wayance, ta ja Deeda tana ‘nuna mata cikin gidan kafin ya ma ta rashin kunya, ya kunyatala a gaban Deeda. ‘ cikin da kewayen gidan ta nuna ma ta, sannan ta juya ta tafi Ya zaune a Wurin' Dccda ba ta kula Shi ba ta hau yin abin da Ya ‘kawota. ' ,. Gyaran Kicin ta ta fara’ wanda 'ba wani datti 'a cikinsa sai sabo da ba girki ake a ciki ba, har'ta fita falon ta share ta goge,,ta gyara duk Barnar'da ya yi. " Yana ganin tana Moping‘ya qi tashi a wurin, kuma yaqi matsar da qafarsa, ita kuma ta Ki kulashi ta wuce. . ‘ "Ke mai aiki!" Ya fada cikin tsawa. "A gidanku haka aka koya miki? Kina ganin mutum ba‘ za ki gaishe shi' ba? Daman ''yan kauye Tala‘kawa ba hankaline da ku ba Ba ta ce masa komai ba, ta'dawo gami da rusunawa ta‘ ce. "Ina yini?" Kan da kai ya yi bai kulata ba, hakan ya sa ta wucewa. Ya sake kiranta. "Aikin nan bai- fita ba, sai kin sake, sannan idan kin gama akwai wani aikin a daki. Kuma kar ki zata-zan fita in barki ki yi yadda kika ’ga damane, ina nan idona akanki. . Nan ma'bata' musa masa ba, ta koma ta fara sake' goge-gogen ta sake sharan da moping din, hakan ya qular da shi, don'ko a fuskarta bai ga alamar ta ji haushi ba. . Nan ta20 wucewa ta gabansa yai ma ta wani mugun kallo. ke tsaya! " ’ Cak! Ta tsaya ba tare da ta Waigo ta kalleshi ba. ' "Ina fata kin soma ganin isata da power na, tun a nan kafin zuwa gaba‘ zan nuna' miki ke matsiyaciya ce, matsayinki a karkashin takalmina yake' Bai ‘Bata lokaci ba ya sa kafa ya doke robar da take. moping'din ruwan gaba daya. ya zube a wurin. yasa hannu ya hankadeta, suuu! kuwa ta tafi ta zame ta daku a kasan tayils din“ dakin. ’ ’ "Wayyo Allah na Ta fada kamar za tayi. kuka. ‘ ‘ ' Ya kyalkyale da darin mugunta ya ce,* "Sai na illa,ki na karya miki baya kin zo. baki da sauran amfani. Su Miss. Manager an zama Mss. House Girl. " "Mugu kawai, Allah Ya saka min abin da ka yi min, iyakar abin da zaka iya yi ke nan", "A'a ba iyakarsa ba ke nan," yanzu muka fara, mu je zuwa, oya! Ma za tashi ki goge ruWan da ya zube Nan ta mike da kyar ta nufl Kicin ta dauko wani mopan ta hau gogewa. Ranar dai har Kujeru sai da Sabccr yasa ta daga ta share but bango sai da ta' gage 'ba tare da ta huta ba, tana gamawa kuwa ta fara na‘dakinsa. , _ Anan ta galabaita sosai, Sabceq ya dau tsawon kwanaki yana, war gaza dakin, amma ya sa ta gyaransa a lokaci daya: ‘ Yamma lis ta mai da komai mazauninsa ta kimtsa komai_ ta ki‘ra masu Aiki aka gyara WindoWs din da ya farfasa. Shi ya yi mamakin yadda ta gyara. dakin yadda ya yi kyau‘ya tsaru ma; ya f1 na da. Ta gama ta shiga (Bathroom) shima ta hau aiki, ta- gama ko‘ina ya'dau Ramshi‘da baske. " ‘ A KOfar‘Bayin ta zauna tana hutawa, ga gajiya ta yi lis, ya shigo ya sameta, ya tausaya mara kwarai', gyan-gyadi ya dinga' kwasarta, tayi sauri ta miqe‘da ta tuna tana da girki, nan kuma ta nufi Kicin donyi masa girki, nan ta shiga kaiwa’da kawowa don bata san me za ta dafa ba, kuma ba ta iya‘ girkin’su ba 'don‘ita ‘kO Momi ba girki .take yi'ma ta ba Ta yi tsaye ta rasa abin yi, ‘Ya shigo ya sameta, .ganin dai a yau ya ma ta mugunta ya wahalar'da ita’ da yawa yasa ya Ce ta r tashi ta tafi ba sai ta girka ba Nan ta circ kai- ta kalleshi gami da kafa mai idanu tace, "Aikina ‘ne kuma saina yi, bana son 'wani tausayawarka ko’ sassaucinka dai ‘ina'da raina lafiya ta to duk aikin da ka bani yau kuma sai na yi". . "Fine, ‘ki‘ yi".-Ya fada cikin fishi. me kika dauki kanki? Don- kin samu na‘ miki saSsaui‘i shi ya yi miki dadi'ko ki yi girkin - yanzun nan, ina-son in, ga ~. dishis Abinci kamar kaloli shida da home made drinks nanda awa daya Nan ya banko' ma ta kafa ya; fice, ta bishi da kallon tsana da harara ta ce "Wannan gayen kasheni yakc son yi sai ‘dai zan nuna masa bai isa ba". ' ‘ ' Nan; ta dinga kaiwa "da kawowu, ga lokaci na tafiya, ga ba abin data iya. . ' Nan dabara‘ta fado mata ta kira Ibrahim a Waya, tayi sa'a ya dauka. ‘ Nan "ta fada masa matsalar, ya yi murmushi ya ce, ".Daga jin muryarki ba ki ‘sha'dakyau ahannun Sabce'r: ba". Uhm! Ka rabu da Wannan'qanin na ka, ban san da wane suna zan kirashi ba, ban 'yi‘ tSammanin yana da zuciya, ba ta ,dutse ne a kirjinsa". Ibrahim ya kwashe da dariya ya ce "Yanzu dai. bari in fada miki abin yi kafin sabon Boss dinki. ya 20 da Bulala", Ta yi kwafa‘ta ce, ".Ai na ga alama abin ' da yai'saura ya yike nan,‘ amma ni dai—dai na ke da shi". - ' Nan Ibrahim ya fada ma ta; wani Site na girke— girken-da za ta shiga a' lnternet, Wanda yawanci da irin.girke-girkensu masu girki ke yin koyi. . . Ya fada ma ta irin abincin da sabccr ya fl so, ya Kara da ce ma ta, "I'dan‘wannan bai yi ba taje gun. Chief Cook na gidan~ ta karBi Littafin girke- girke da~ kuma Menu na Abinci, k0 kuma zai yi Waya ya sa a kaWo ma ta", " Nan ta yi masa gOdiya, Sukai sallama. Ta sha wahala sosai 'wurin gwada dafa abin da ba ta taBa yi_ba, amma duk da hakan sai data nace ta yi komai kasancewar ta samu sauKi duk abin da take nema akwai shi' kuma akwai electroniac na girke girke kala—kala da haka 'ta “ ***“———————-——-—-—--—-—an . ta hada Abincin, amma kicin din ya yi kaca- kaca ya koma sama__ da Rasa. Haka ta hadasu‘ gun‘ guda ta tura ta kai maSa, ya sha. mamakin yadda ta gama a lokacin da ya bata, a gabanta ya bude ya dandana.. Tabbas Abincin ya yi dadi amma tsabar yar bata mata rai, ya sa kafa ya ture Abincin gaba daya ya zube Taji Bacin rai da wani irin. bakinciki, amma sai ta shanyeshi ta‘ce, "Allah Ya huci zuciyarka, zan sake wani yanzu". . . .haushinta ya ji ya Kamashi kamar ya ruféta 'da duka, burinshi guda yanzu ya ga ya quntata- ma ta ya bata mata rai, ’amma yarinyarnan k0 a jikinta, bayan ta kwashe‘ za ta fita yace ma ta, "Ba saikin Sake ba, bana buqata Ba ta‘kulashi' ba'ta fita ya bita da kallo, k0 me take ji da shi oho? "Ka ’ga 'yar Talaka da nunawa mutane Attitude". ‘ Ba ta jima da fita ba ta sake dawowa ta 'ce"YallaBai akwai wani aikin?" "Babu". Ya fada a hasale. "Na ga alama kina enjoying aikin ne". Ba ta- kulashi ba ta juya har ta fara tafiya ta tSaya ta Juyo ta 'ce, "YallaBai .an .kira' sallar magariba kar ka rasa jam'i, 'na ji ana‘kOkarin Shiga, na gyara bayin- sosai, za kaji ‘dadin yin Alwala". Ta fadi cikin sanyin murya. "Naji". Ya fadi, "Zan‘ yi- yanzu, na gode Murmushi ta yi masa tare. da daga masa kai ta fita. ' ‘ Ya tsinci kansa da tashi ya” yi Alwala, rabon da ya yi" sallah a jam'i ya manta. Nan ya zauna har iSha, .sannah ya dawo ya kwanta yana‘ tunani. ' Dccda kuwa tun data koma dama dai tana hulun sallah, kawai zubewa tayi a gado, bacci mai Karfi ya dauketa, wurin ka'rfe goma ta tashi, ta ji ko‘ina a jikinta ciwo‘ yake Wanka ta. shiga ta yi da ruwa mai zafi sannan ta'hau Computer don dUba lecrures din da aka yi na wannan ranar.don .bata Samu leqawa ba. tun safen. ‘ . - bayan ta gama abinda take ta dauko laptop ta lissafa kudaden hajiya‘tare da yi mata“Transfer-k amar yadda take mata a koWanné, ciniki Sannan ta dauki 'Waya “taga miss call din Ibrahim, tare dai Message dinsa, ~yana ma ta'sannu da yi ma ta‘addu,a da kuma fatan alkhairi. : a Murmushi ta yi'bashi ta bashi amsa da cewa"Na gode". ’ it I if. Q ii .it v 4* ,lbrahim yaje side din 'Sabccr,‘ yadda‘ ya‘ga ’ gurin ,-._ya tabbalar Dccda‘tayi aiki.‘ ‘ " "Allah Sarki.baiwar Allah!" Ya kalli Sabccr yace, "Amma naji dadi yadda nAga wurin nan da‘alamar ' zamu shirya‘ga- wayarka da komanka na dawo dasu, amma fa har yanzu sai dai in office zaka koma sabccr ya ba shi amsa. ' ' . "An fada maka. Waya daya ce. gareni Kuma dama office ko baka fada ba, ina nan dawowa, ‘ _ Sannan masu aiki 'da kake da ikon hanasu yi mini aiki, to na sa wanda na "ke da ikon sata aikin, kuma ‘ta yi. Na san dai za ka ji haushi in na 'cé maka ba ni na gyara wurin kamar yadda’na bata‘ba" "Sabccr take it easy; ni fa ba abokin gabarka bane", " " "Mallam' fita bana bukatarka”. Ibrahim bai masa musu ba. ya tashi ya bar . Sabccr ya dauki Wayar‘sa, Farida ya kira. Ya jima yana yi mata korafi akan Ibrahim, da kyar ta lallashi ya hakura. Nan 'ya‘ ce ' mata: 'yana . nan hanyar zuwa wurinta amma sai .ya gama "abin da' ya yi niyYa- , ' Taji dadi sosai, sannan tace masa ita ma tana nan daWOWa ta' samesu, zata daidaita tsakaninsu da Ibrahim. " ' ‘*v* _*v* ' .*b* qarfc bakwai dai—dai Dceda na side din Sabccr sai dai harta gama gyaran, ' falon da kicinsannan ta hau saman,‘ Kayan'sa ne ’a ‘watse tun daga. kan Takalma, kayans’a, _Waya, system _ Ta'tattara koma'i ta gyara sannan ta buga Rofar dakin amma baitashi ba. Ta jima a’tsaye 'tana- jiransa amma shiru. Ibrahim neya bugo mata waya,’ bayan sun gaisa, tace masa',‘ ta yi_ ta bUga qofa sabir shiru". ' v Ibrahim'yayi daeiya in dai Sabccr ' ne za ki kwana k'ina-jira, dole kisan dabarar da zaki yi ya tashi..Ni ina da marasa lafiya, sai an jimau' . r Shiru tayi tana tunanin abin yi. Can ta mike ta nufi Kicin ta hado masa kayan Tea da da Ginger .Tea"tare da Milk ta'hado da Ruwan zafi, sannan ta yanka Fruit ta nufo Dakin‘sa. ta jima tana tsaye a wurin, ta 'shiga k0 ta fasa. ' ' ‘ ‘ Can dai' ta daure ta tura KOfar, a, bude ta ke, duhu ne ya mamaye d' akin tamkar dare. - Nan ta aji‘ye kayak break din ta nufi Window ta zuge Labulen ’nan 'haske ya bayyana a Dakin, fuskar Sabeer 'da ke kwance yana fuskantar Window ya ji haske ya takura masa,-Tsaki ya' yi ya juya kai ya sake gyra kwanciya. Bata kulashi 'ba sai da ta. gama tattara dakin ta kimtsashi ta bude Fudge don gyara ciki, nan ta yi Ido biyu da abin da ya daga ma ta hankali. , Kwalaben (Strong Wzlsky) ‘guda " biyu ta gani, zuciyarta. ta ma ta zafi Wato Sabeer har yan‘zu yana da. hanyar da' » yake bi ya sha Giya tak0 tausaya 'masa don shi ‘bai san illar da yake -"'yiwa_ kansa da rayuwarsa ba; DA bai shaba ta tattarasu waje daya taje ta zubar ta ma’ye gurbinsu da Joice da‘ kuma ruwa, sannan ta shiga Ta gyra ta fito. Har yan'zu bai tashi ba, duk" shiga da fitar da take yi, bayan ta. gama'komai ta matso hannunta like ‘da Cup din tana ‘taya za ta soma tashinSa? .' Can dai ta matsa dafda shi tana kiran sunansa' ' "Sabeer‘!~ SabeerH Sabeer!!!" Ta ja Tsaki ta Bata fuska‘tace, "Yanzu'in yaji ya 'tada bala’i ya ce shi Ogana ne. Sarkin yan gadara da mulki". Don haka ta‘canja salo. "YallaBai yallabai har yanZu'Shinru ‘sai ma gyara kwanciya da ya sake ‘ Nan dabara‘ta fado'mata ganin yadda ya. kwanta ya bude. Baki ‘ kamar wani baccin qaramin Yaro ya sa ta dauko Cokali ta cikaShi da Tea ta juye masa a baki. Nan take ta ga ya soma lashe Baki. , Ta sake kai masa na biyu;'t‘a lura bude bakin ya qarayi ta’zuba masa yana, kuma fito da harshensa yana bi. yana lashewa. ’ ' Hakan ya bata. dariya ta matso daf da fuskarsa tana zuba masa can ta kuma qura masa ido tana ganin yadda ya ke sha tana dariya, tana kuma enjoying kamar Wacce ta samu tV. Ba ta ankara ba sai gami ta yi ya bude ido ya zura mata idanu Cikin mamaki ganin yadda ta sunkuyO daf da shi tamkar mai masa rada, hakan yasa. ya yi firgigit! Ya tashi ita kuma hakan ya tsoratata, gashi ya miqé ya fito daga' cikin Bargo daga ‘shi sai' Gajeren Wando, hakan ya sa ta buga ihu tare da sakin Kotin Shayin ya zube a jikin lallausar fatarsa da bai .saba. da wuya ba, wohoho sai zafi. ‘ Shima' wani Kara ya' saka, Karan azabar ruwan zafin ya. mike tsaye-yana tsalle. Dariya. ya bata, ta-kasa ‘daurewa ' ta zalle da tana cewa, ",Ka yi haKuri don Allah, .Wallahi ba da niyya na yi 'maka ba .Haushinta ya kara kamashi, ganin tana mai dariyar Mugunta, ya bita ta ruga da gudu, ya sake cin tuntube da sauran Ruwan Zafin' da ta ajiye a Tire din ya sake Zube'masa a kafa, gashi‘ daga‘ shi. Sai ‘gajéren Wanda. Wani ihun ya sake sakawa',’ : "wayyo Allah na Ganin hakan yasa ta debo ruwan' Sanyi ta sake watsa masa a Cinya tana ceWa, "Sony. Sir; Sannu YallaBai".- ‘ ‘ ' Ihun ruWan sanyin ya sake bayan na zafin. Ba'ta ankara ba ya cafko Dankwalinta tare da gashin ‘kanta ya hada ya damke ya.ja. da qarfi, ta sa Kara: itama tana kokarin‘ kwacewa‘ ya ce, "Muguwa Aljan'a"yar Kauye, so ki keki ‘ kaSheni da azaba? " Ki ka sake shigo min-daki sai na. cire miki gashin kanki 'na karya yatsun Kafarki~ daya- Aljana kawai!" Ya‘ ‘fadi‘ lokacin .da - yake kokarin cillar da ita. Sai da tata bugi'Gini ta tsugunna a wurin tana. maida numfashi da Ya yin da kuma sabeer ya nuf1 Fridge ya dauko qanqara'yana shafawa a inda (ruwan' Zafin ya zube 'masa. Wurin 'ya yi jawur! Kamar jini zai Bullo. Nan ’ya lura ‘ba Kwalabensa na (Strong Wisky) a cikin Fridgege din. ~ Tana‘kallon‘sa ya nufota 'da masifa. "InaKwalabe na? Ubanwa ya ce ki ta am n Frdge dina?" ‘ "Ba uban koWa’ ya ce in taba . sai‘kai. Nimai Aikinka ce, don biyana za ayi‘, aikina ne cire datti da daudar da ke cikin' Fridge dinka. Wannan' Giyar_ .da. ka san Kazanta da' illarta da ba zaka yi ta durawa cikinka_ita ba, ka sani na debésu na' zubar da su gaba daya, kuma k0 gobe ka sake ajiyewa sai na sake dibewa; na zubar da su!" ' " "Ke kin isa ki taba abin da na ajiye ko ki hanani' ‘shan abin.._da' naga dama? Kin san TSadar su kuwa? Da ke 'da duk zuriarku duka in kun taru ba , za ku iya sayansu'ba.." "Oho ,dai K0 me ma ka ceni dai na zubar, kuma k0 yanzu ma kasa- sai na fasa" Kafa ya daga zai‘ shureta; .Ta ruga da gudu, ya bita: Ganin -bazai : kamata' ba ya‘ sa' ya ~‘ wurgeta da wani karfe “ya sameta k0 ta fadi‘ ta kama mayafalitana,‘ "Wash! Allah Mugu Allah ' Ya saka min,kuma yau ba zan karasa ma ka ba; kuma gobe sai na kuma.'.." .Ganin ya nufota yasa'ta mike da'dingishi ta yi ciki tuna cewa, "Na san dai ba kai ,Sallah' ba, dama 'kayi Alwala ka yi Sallah k0 za ka. samu saukin zuciyarka, duk rashin Sallah ya hanaka samun nutsuwa da sukuni kullum kana'cikin fishi. Gwada yin sallah akan' lokaci, 'ka ga yadda za ka dinga samun nutsuwa." Tana maganar ba, ta daina ba‘har ta ‘bace. Ya yi tsaki ya ce, "Aljanar Yarinya duk_ ta gajiyar da ni'.‘. Ya koma yana tattara kayan da‘ suka watse a dakin, ya dora a tray din yana yin mita, "Aljana na duaketa aiki; amma ni take sa Aiki."Yar banzan Yarinya harta isa ta zubar min da..." - Ya_ kama kai lokacin da yaji kanshi mass zafi , wajen da ruwan Zafi ya konashi yana masa radadi. ' . a ‘Wayyo Allah Na tsani Yarinyar nan. (I hate this Girl] ya dauki Wayarsa ya kira AbokansaNura da Salim, don su sukai mitin akan abin da zai mata wanda Zai ma ta ciwo, sannan ya kuma kiran layin Momj ya ce ma ta yana son lambar Deeda. Cikin minti biyu'ta turo masa.. A lokacin da Ya kirata..Ta samu ta isa tana jinyar kafarta tana “‘ ' Wayarta ta yi Kara, da- 'kamar ba za ta dauka ba don ba ta gane Layin ba. Can‘ ta daure dauka. Kafin ta ce wani ,abu ya rigata. ' ' . "Deeeda. » ' _ Ta gane muryarsa don haka ba ta ce komaiba' "Deeda!" Ya Sake kiranta da kuma karfi. " “Ta'amsa. ' "Me ye, ni kam kar ka fasa min Kunne", Haushi ya ishe shi_ ya rasa ma me zai .ce ma ta. Ya manta ma abinda ya sa ya kirata"Na tsaneki Deeda". Ya ce a basale. "Na-tsaneki! Ihate you... .- "Nima haka". Ta bashi amsa. Cikin yanayi da alama na k0 in kula tace, "1 hate you toa. , ' Dama abin da ya sa ka» kirani ke 'nan? Daga ji na san. bu ka yi Salla ba, don da Ruwan Alwala ya_ taBa, jikinka, hasken Sallah ya taBa zuciyarka na san -da zuciyarka ta yi sanyi. Don haka Oga je ka yi sallah. Su YallaBai fitina, Sabeer rigima". . Ta ‘fada‘ cikin sigar‘ tsokana. da dariya‘. Ta kashe wayar. ‘ ~ ba tare DA ya bata amsa ba. zuciya da Wani ihun bakinciki yasa da Bacin rai. Ya yi wurgi da Wayar. . "Wannan Aljanar yarinyar sai ta. kasheni wata rana, ba ta jin komai »a~rayuwa, komai baya taBata. Anya ma Mutum -ce kuwa?" . Nan ya bude Fridge ta dauki Ruwan Sanyi ya sha, ya kuma watsa a kansa ko zai‘ samu sanyi a zuciyarsa, kansa ya yi masa sanyi. Wurgi' ya yi da Robar sannan ya shiga Wanka. —, , Ya jima kwance cikin bab sannan ya fito. Ganin ya kasa, samun kwanciyar hankali .da sanyin zuciya yasa' ya ‘yi Alwalar‘ ya fito ya yi Sallah ya kwanta akan .Sallayar idonsa a rufe, tunaninta kawai yake Wanda ba abin da ya tsana banda ganin mummunar fuskarta a nashi fadin Amma ta shiga zuciyarsa ta zauna sabo' da yadda ya satunaninta a gaba‘ da yadda zai yi ya qular da ita ya ga taji haushi Wannan yasa awa ashirin da hudu tana maqale a kwakwalwarsa da zuciyarsa. Deeda ta tayi Waya tana bawa Ibrahim ‘labarin tsiyarda suka kwasa da Sabe’er tana-yi yana Mota, Dariya ya dinga‘yi' ya‘ ce,."Na fada miki :Sabeee ba‘ sauki zaku kwashe da' shi ba,kuma ta da Sabcer daga Bacci shi 'yaf1 komai Wuya' - Ta ce, 'Wallahi Ibrahim Sabecr nada matsala‘. . .. t r'Sam‘baya .son Sallah,:yana wasa da Sallah, sai lOkacin 'da ya 'ga damayake Sallah, ga shaye— shaye.. Wallahi . rayuwarsa na cikin hadari". , ' . "'hakane .Deéda, wallahi nima abin .na damuna. . Sai dai na yarda da ke Dccda, na San. za‘ ki sa Sabeer a hanya". "Ibrahim ba abu mai sauki bane. 'Kana ganin ni ‘da Sabccr kamar Wuta da AudUga~ muke? .Ya tsane ni; ni'kuma na tSani halayensa. "Za ki 'gyara halayyar da ki ka tsana Deeda". ' ' ' Ajiye Wayar ta yi, don shi Ibrahim bai san wahalar da _take sha a hannun Sabecr‘ ba ne. A ranar da yamma Momi ta, taho da Inna _ mai Fura. Murna a gun Dccda kamar Sallah. A jikin inna ta yini a Wannan. rahar tana murna. Bangare guda Hajiya ta ware musu a Bangarenta daki da falo da kuma Bayi. Akwai komai a wurin da Zasu bukata; , Tuni Inna.‘ mai Fura ta maye .gurbin "Decda wurin' aikin Momi na‘ gyaran Bangarenta' da kula da Side dinta. Kuma'Momi na jin dadin hakan,tana jin ‘ :dadin zama. da‘ Inna, don tsabtarta‘ 'duk da tsohuwa ce amma da sauran karfinta kuma ba ta da qazanta, kuma ba ta ma Hajiya shos‘shigi, hakan ya burge Hajiya. 1 ‘ Sannan Deeda ta cigaba da kula mata da lissafin kudin Business dinta da kuma side din Sabeer‘ Wanda kullum cikin fada suke ba Wani jituwa. a tsakaninsu Sabccr ba karamin wahalar da Deeda ya ke ba, haka kawai tana tafiya saiya sama ta kafa ta fadi k0 ya jawo .hijabinta da karfi ya sake sai ta fadi, k0 kuma tana tafiya haka kawai ya watsa ma ta 'ruwan. sanyi, ya yin ,da ita kuma ba ta nuna mishi ta ji haushi hakan ya ke Kara qular da‘ Shi. Wani lokaCin ta Ce mishi yaro ne shi bai da wayo shi ya sa'yake'halin Yara k0 ta ce masa ' bai iya komai ba sai kashe kudi da. fada, .itabA' cikakken namiji bane da zai'tsaya yana Wahalar da Mace, jarumin Namiji sai dai ya fuskanci Namiji dan uwan‘sa, , ' Abin da yadi, ba shi haushi shine, kullum tana kwatanta real man da Ibrahim. ' Wani lokacin tare da Inna mai Fura suke zuwa Bangarensa kuma .da sassafe; duk Baccin da yake sai ya ta'shi k0 kuma, tasa Wa‘azi da ke magana kan’hukuncin wanda baya‘ sallah

Chapter 8 of 25