Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi ido biyu da juna. Ya mike tsaye cikin mamaki kuma a fusace, itama ta mike, ta lura da haushinta da ya ji amma ita ba ta ' ma gane shi ba. . "Na lura yarinyar. nan ba ki da kunya, ba ki da mutunci! Uban wa ya kawo ki Asibitin nan?" Ta kalleshi sama da kasa ta buga mai Tsaki tare da Harara ta ce, "Sa'a ka yi ban iya Zagi ba da na ma ka wadanda ya fi naka ciwo. Kuma karka'yarda ka sake zan min Uba". Sai an Zaga me ki ka isa ki yi? Dama nemanki na ke, yau sai na miki rashin mutuncin da ba za ki manta da shi ba". "Banyi tsammani ba". ‘ Ta ba shi amsa kai tsaye. "’Me kike nufi?" Ta kada mai Idanunta wanda sai da ya sa yaji gabansa ya fadi. ' Wannan ne lokaci na farko da bama Mace ba, lokaci na farko da aka taBa kallonsa ido cikin ido ba tare da shakka k0 tsoro ba. nace, "Ban tsammanin zaka iya ba. Ina nufin yanayinka da alamunka bana zaton ka Iya rashin mutunci , sabo da a yadda na ga alamarka girman jiki ne kawai kayi, amma har yanzu tunaninka da ayyukanka har kwakwalwarka ta yara ce ba su girma ba. Yaro k0 ban tsammanin ya san meye rashin mutunci balle ya iya, sunansa kawai ka sani, don haka ka bari in Kwakwalwarka da tunaninka sun gama girma sai Ka zo mu kara rashin mutunci, in ka gwada min na 'YAN BIRNI ni .kuma sai in gwada ma ka na 'YAN KAUYE": Tuni Sabeer ya kara harzuka, idonsa ya kada ya yi ja ya kasa furta ma ta komai, kuma ya kasa ma ta komai, sai azabar zuciya kamar za ta kashe shi. . Tun-tuni Ibrahim ya ji hayaniyarsu ya fifo ya tsaya a kofar ya -harde hannu yana kallonsu yana murmushi. . -’ Cikin qunar zuciya Sabeer ya Ce ma ta, "Fita Asibitin nan tun da ba na Ubanki ba ne, ba zakiga Likitan ba, kuma yau sai na nuna miki halin yarint Ya- zaro- Belt dinsa da karfin tsiya ya kai ma ta duka, ta yi saurin sa hannu kuwa ta tisge. Mamakinta ya‘sa shi bude Baki. _ "Bi a hankali Yaro kar (Body bulding) din da kayi ya yaudareka; kar ka ganni Mace ka raina min Wayo daga Kauye na ke, na ci Tuwon Dusa na ci na Dawa, kar ka nemi raina ni. Kuma da na san Asibitin nan na Mahaifinka ne da ban soma takoshi ba." Ta ja mai dogon Tsaki ta juya za ta fita, wani kololon Bakinciki ya. tokare masa zuciya, ya rasa me zai ma ta. Ba ta ankara ba ko ta taka Sunul ta fadi qasa ta daku. . - "Wash Allah". Ta fada "Wayyo! Bayana". Sabeer ya Kyalkyale da. dariyar mugunta yace,"Su Budurwar Kauye masu karfi an sha Kasa". Ya matsa dab da ita yasa kafa ya' takéta .sai da tayi Kara yace"Duk karfin Budurwar Kauye ba ta isa ta kai Namiji ba, musamman na Birni, BIRNIN ma na GAYU Ya Kara taketa da Karfinshi ya ce, "Dama neman‘ki na ke tun rashin mutuncin da ki ka min ban manta ba, kin hanani sukuni kin hanani Bacci' kin hanani cin Abinci, kin sani yawan tunanin wannan mummunar fuskar taki, har ta zauna a kwakwalwata. Yau wannan hannun da ya watsa min Nono sai na Balleshi". Nan ya kai daya Kafar ya danne Yatsun da qarfi" ‘ Ta sa ihun Azaba, sai da hannun yayi jini sabo da irin takalman da yasa ba na wasa ba ne. "Wayyo Inna zai kasheni Ibrahim ne ya matso wurin da sauri ya janyesa. "Kai- Sabeer ba ka da hankali za ka kashe- 'yar mutane?" "Kyaleni in ma ta illa, gobe idan ta. ganni za ta canja hanya. Kuma wannan kadan ma ta gani." ‘ Ibrahim ne ya taimaka ma ta ta tashi gami da dressing din hannun cikin . gaggawa ya samu jinin ya tsaya, amma bai yi nasarar tsayar da jinin ba. Hankalinsa ya tashi, gaba daya ya rude, bai taBa tsammanin abin nasu zai yi tsanani haka ba da bai bari hakan ya faru ba. ' Nan ya sa hannun cikin qankara ya sa ma ta Magani sannan ya daure da Bandeji ya nufi ciki don dauko Allura ya mata. Bayan fitarsa Sabeer ya harareta ya ce, "Kalli 'yanda ki ka zama abin tausayi...azaba kadai ta canjaki." "Allah Ya isa Ta fada cikin zafin zuciya. - "Kuma kai ne abin tausayi ba ni ba, don ni kam ban iya bin 'yan fage in yiwa mutum illa ba sai ‘dai in fuskance "shi. Ka ji kunya da ka nuna qarlinka akan Mace". Ta ja Tsaki gami da matsawa dab da shi, bai ankara ba ta ja farar Rigarsa ta goge Jinin da ke zuba a hannunta gaba daya ta bata masa Rigar. ' ‘ Ya daga hannu zai Mareta, tuni ‘ta manta ciwon da ke hannunta ta cafke Hannun ta gantsara masa Cizo ta fita da gudu. " i . Inna dai ba ta ankara ba sai ganin Deeda tayi ta fito da gudu a rude ta bita. "Ke Deeda!!!”. ' Can kuma sai ga Sabeer ya biyota da gudunsa. ‘ ‘ Inna fa hankalinta ya tashi, ta bisu tana,"Deeda! Deeda!! Deeda! ! !" Daga qarshe dai ta gaji ta hakura don ba‘ za ta iya gudunsu ba. ‘ - Sai da suka yi nisa sosai har suka fita Asibitin sannan Sabeer ya yi nasarar kamata ‘ Ba ta saurara masa ba' ta yi na ‘maza turesa da qarfinta. ' Sai da ya fada cikin wani ruwan dake a bakin hanya. . Tana' ganin ya' kai qasa kuwa ta arta ana Kare, ba ta tsaya k0 ina'ba sai da ta kai Gida, ta nufi daki ta rufe tana haki gami da tuno abin da ya faru kamar a wani Mafarki k0 Almara. . lnna dai hankalinta a tashe ta nemi abin hawa ta kOma bayan ta gama neman Deeda ba ta ganta ba, ta tafi tana addu'ar Allah Yasa ta koma Gida. Sabeer ya mike cikin takaici da bakin ciki da Bacin rai, duk’ Kunya ta kamashi da ya ga Yara da wasu Mutane suna kallonsa. Wasu 'yan Mata kuwa har dariya suke suna mai da‘ yadda abin ya faru, da alama a idonsu aka yi. Da kyar ya iya daga kafa ya miqe ya wuce kai sunkuye takaici da kunya sun lulluBesa, ya rasa ma ina za shi. Shi 'dai bai gane hanyoyin ba, don haka dolensa ya koma cikin Asibitin, ga‘ shi 'ba Waya a hannunsa, haka' dolensa ya sunkuyar da kai yana Boye fuska ya koma cikin Asibitin yana kaucewa jama'a yana kulla tsiyar da zai ma ta Ibrahim yana ganinsa ya fashe da dariya ya ja shi wani Office da ba kowa ya ce, "Sabeer kai ne haka k0 Ido na ne?" Cikin zafin rai ya ce, "Wannan Aljanar Yarinyar in na kamata k0 sai na harbe yar banza! Ni zata yiwa haka?" "Ya isa haka Sabeer. Yanzu dai abin da ya faru ya faru ba yadda ka iya, ka koma Gida ka canja Kaya ka barni in yi aiki Please tun da na san yau ma kai kam ka tashi'ba za kuma kayi aikin ba" Ya Bata fuska. "Uncle IB ka san ni ban gama sanin hanyoyin garinnanba, Please ka 20 ka mai da ni Ibrahim ya cira kai ya kallesa ya ce, "'Ka yi hakuri Sabeer ba zan iya barin aikina in yi naka ba, yanzu mafa marasa lafiya na dakatar ina sauraronka. Please har yaushe komai sai an maka kai ba Yaro karami bane, in ba zaka iya komawa ba zan ma (Diver) din Office magana ya mayar da kai Gida, amma ni dai ba zan bar aikina ba". Sabeer ya yi fishi ya fisge Key din Motar ya fita, Ibrahim ya bisa da kallo sannan yaci gaba da Aikinsa da niyyar in ya gama’zai je inda suka hadu da yarinyar nan ya nemi Gidan su. %%%%%%%%%% Sabeer kuwa, sai da ya gama zagaye_ kafin ya kai ga gane hanyar Gida, ga shi ba dama ya kira Abokansa za su masa dariya. Haka ya yi ta shan wahala kafin ya isa Gida ya koma ya samu Momi ta dawo, wato Hajiya Amina, sai dai bai bi ta inda ta ke ba ya wuce ya cire kaya ya shiga Wanka. . Ya jima kwance cikin Ruwa a (Bat Tap) yana tunanin irin abin da zai ma yarinyar nan da inda zai sake ganinta, sai dai hakan ya gagara, tunaninsa bai samu maganin matsalarsa ba. Nan tunani ya fado masa, kawai ya kira Abokansa don su tayashi nemanta da kuma ba shi shawarar irin rashin mutuncin da zasu ma ta. Bayan ya fito ya ji kiran (Door Bell) na Bangarensa, bai kula ba sai da ya sa Kaya ganin an matsa ya fita ya bude. Momi ce tsaye tace, "Lafiya Saber tun dazu ina tsaye, ina ka shiga?" ’ ' Ya dan sunkuyar da kai yace, "Momi ina Wanka ne Shigo mana,'dama ina shirin inna fita zanje in gaishe ki. Kin dawo laflya k0?" : "Lafiya kalau". Ta amsa masa lokacin da ta ke zama ta ce, "Yayunka duk suna gaisheka.‘ . - ' ' Daddynku ya fada min komai' game da_ dawowarka, sai ka dage ka koyi 'Aiki, in da hali ma harka Karo ilimi a fannin da kafiso, duk da Asibitin muna da Likitoci, amma akwai bukatar ka a Asibitin. _. Ina so ka daukeni kamar Mahaifiyarka, duk abin da ya shige ma duhu ka 20 ka sameni Bangarena na Shawara k0 wani abu. _ Sannan ina fatan ba ka da matsala da Ma'aikata masu kula da Bangarenka da Abincinka suna gyara ma ka Side dinka ya kamata, yadda kuma ka ke so?, duk abincin'da ke bukata order kawai za ka yi..." "Na sani Momi ba sai kin bata bakinkiba Ya katseta. "Nan Gidanmu ne Gidan Ubana ba sai an bani ko ance in tambaya ba. . Sannan Sister ita ce Mamana ita ce komai na, kar ki yi qokarin zama Mamana ki zauna a matsayin .Matar Babana ina ga hakan zaifi mana ni dake Sannan Uncle IB yana tare da ni, duk - bukatata shi kadai ya isa ba sai kin sa Baki ba‘ In koyi aiki k0 kar in. koya, wannan ba matsalarki bane Batayi mamakin halinsa ba, ta yi wani murmushi irin ta manyan Mata da idonsu ya bude tace To shi ke nan tunda haka ka ke so, muje a haka-tun da kafi son in, rikeka a matsayin dan ‘Mijina‘ Fine, ni kam na kware wajen iya,rike ‘dangantaka tunda rikon dan kishiya kakeson nai maka ina maraba'da hakan. inaso ka ,sani bani da matsaia da kai, bazan cutar da kai,ba amma fa kar ka shiga gonata kayi kokarin tsayawa a matsayinka". "Kema ina son ki tsaya a iyakarki". "Da kyau". Ta fada tare da girgiza kai ta fita. Ya bita da wani matsiyacin kallo gami da rufe gofar Falon ya koma ciki. , Wani radadi yaji ya ziyarci" hannunsa, nan ya mai da kallonsa kan hannun, ya yi jawur har ya soma kumbura. ' Ya ja dogon Tsaki, haushin Deeda da tsanarta ya Kara shigarsa, don gurin da ta gantsara masa Cizo ne. "Amma wannan akwai 'yar rainin wayo...ni 2a ta fadawa bafar magana? Me take nufi da na girma amma hAlayena ba su girma ba? Tana nufin ni yaro ne Nan ya mike yana kallon kansa a Madubi tun daga sama har Kasa, duk ta yamutsashi kwana biyu kawai. banzar yarinya yar KAU YE mummunar yarinya za ta sani a gaba... zan mata rashin mutunci To amma me zan ma ta?” Waya ya dauko ya bugawa Abokansa yana musu neman gaggawa. Cikin minti talatin suka hallara. "Lafiya Sabeer irin wannan neman gaggawa?" "Ba lafiya ba Ya fada a qule. "Wata Aljanar Yarinya ce ta sani a gaba, ta daga min hankali", Salim ya kalli Nura sannan ya kalli Nura sannan ya kalli Sabeer din ya ce, "Ba dai mutuniyarka da ta watsa ma No... ." Wani mugun kallo da ya masa ya sa shi gum da Bakinsa bai Karasa ba. Ya ce, "Na ganota". Sabeer din ya ce,"Shawara na ke so ku bani. wane rashin mutunci zan ma ta?" Nura ya ce, "Me zai hana ka yiwa banza lahani, wato ka banke banza da Mata sai 'ta Karye ta dawo me Kafa daya?" , Saber ya girgiza kai. "Not Bad Kai kuma ,fa Salim, me ka ke gani?" Salim yace, "Hakan da ya fada dai-dai "ne" k0 ka kadeta ko ka yi hayan wasu su saceta ta, Bace Bat na kwana biyu a rufeta inda k0 Hannunta ba za ta gani ba don Duhu, ta Yini kwana da Yunwa.." ' . Sabeer ya ce, "1 Hope shawaranku ya yi aiki, Nura ya ce, "In dai har muka yi yadda na ce dole ya taBata. In ta zama Gurguwa ai ta .nakasa". Sabeer yace "Ba wannan ba, samun inda take ma bala'i ne". "Zamu nemota a same aren da muka hadu da ita zamu nemota, zan mata ,abin da ba za,,,,'yan Samari". Muryar Ibrahim ne suka mai da hankalinsu garcshi. 'yana wannan murmushin nasa ya ce '-'.da;abin da zaku yi a rayuwa kuke ku ke planing tsarawa da yafi muku". ya yi dariya gami da fadawa jikin unless ib yace kaida Sister ’kune rayuwata (My whole world) ya yi, murmushi ya ce kadai fadi, amma ba Uncle IB bane zai zauna ma. da Mata 'yar KAUYE ba. Ka tuna ya fada tare da murmushi ya Bata fuska. Ya ce, "Uncle IB karka Bata min rai, kasan na tsani 'yar Kauyen nan da aure amma nafi tsanar yarinyar nan (I hate her the most)". . Ibrahim ya ce, "Ni zan fita dama na leko dubaka ne zan fita ni ina da abinyi bani ’da' lokacin tsanar wasu k0 daukan fansa, in kuma ba'ka bar maganar ba sai na fadawa Sister". ' Ya langaBe kai. " ’Yace Uncle IB kar ka min haka mana". "Na dai fada ma ka ka zaba daukar fansa .ko Bacin ran Sisiter". Nan ya fice ya barshi. Ya maida kallonsa kanSu Salim ya ce,‘ "Guy plan cancel" Nura ya ce, "Wai kana nufin kana tsoron Uncle IB da Yayarka?" Sabeer ya ce, "Sabeer bai tsoron kowa, bai kuma shakkar kowa just that ina son Sister da Uncle IB (and 1' respect them a lot) ban san Batawa Sister rai, kuma sabo da wannan Aljanar ba zan 'Batawa Sister rai ba, sai dai duk randa na hadu da ita sai na ma ta illa fiye da wanda ta min". Yana magana yana kallon inda ta dankara masa Cizo. £££££££££££££ da tambaya da bincike a Unguwar, Ibrahim ya gano Gidan Tabawa inda‘ Deeda ke zaune. Tana daki k0 tana shirya kaya ranta a Bace sabo da washe gari za ta tafi Gidan Aikinta. Yaro ya shigo. "Wai .ana sallama da budurwar da ke Gidan nan". ' Inna mai F ura ta kallo Yaron. ",Waye ne "Wani me Mota ne". Yaronn ya bata amsa a takaice. "Jirani". ' ‘ Nan ta shiga ciki ta dauki Hijabi 'tabi bayan Yaron. "Mu je Yana zaune cikin Motarsa a Kofar Gidan ya hango Yaro da Inna. Mamaki ya kamashi. Ya yi saurin fitowa daga Motar lokacin da suke isowa. Innan ta kalleshi kallon tambaya. Kallon da take masa ya sa ya sha jinin Jikinsa. Tabbas ko k0 ba a fada masa ba ya san ko Uwarta ko Kakarta ce. Ya kalli Inna da kyau, ya ga irin shigar: da tayi ' ’ A ransa ya ce "Lallai wannan yarinya ta san inda ta yi gado..." . Inna ta katse mai tunani ta ce, "Gani; naji an ce kana sallama da Budurwar Gidan". . Ibrahim ya kalleta da kyau ya rasa ma me zaice mata. ‘ Tsayuwar da ta yi ta riqe kugunta yasa yaso tuntsurewa da dariya amma sai dake yace "Budurwa' na'ce ba tsohuwa ba Ta kallesa da kyau ta ‘ce, "A Gidan nice budurwa k0 kana musu ne? Me ya kawoka, me ka ke? nema?" ' ta tsareshi da ido. Gaba daya ma ya rude ya rasa me zai ce ma ta. yanata.soshe-soshe da kame-kame, can dai ta tausaya masa tace, "jikata ka ke nema me za kai mata ya sauke numfashi ya ce, "‘Dama ta je Asibiti ganin Likita ne to sai suka samu saBani da kanina ta taf1 ba ta ga Likitanba na 20 in ba ta ha'Kuri kuma in ji meye matsalar don ni Likita ne". ‘ ta zaro Ido ta washe Baki. "Aiban sani ba. ‘ wannan ciki za ka shigo. Dama haka Likitocin- suke na birni har Gida suke biyi marar lafiya? Ikon Allah, ai Deedan tana Ciki shigo ‘ har ciki. A tsakar gida ta shimfida masa Tabarma sannan ta shiga Ciki‘ ta kamo hannun Deeda. ke fito ga Likita har Gida ya 20 duba ki". ‘ Deeda ta kalleta cikin mamaki. "Likita?" "EH". Ta amsa ma ta a takaice. "Ashe da rabon za ki ga Likita kafin ki tafi Zo mu je". ' ' Ta ja'ta har Tsakar Gida wurinsa. "Likita ga Jikar tawa”. Deeda ta kallesa cikin mamaki. "Likita har Gida?" Ta ja Kujeran- zama na tsakar Gida ta zauna, ya yin da Innar ta zauna a gefensa. Deeda ta gaisheshi Sannan ta tambaya. "Anya ni kuwa ka zo nema? K0 ka Bata ne?" "A'a ke na 20 nema. Sunana Dr. Ibrahim, ni ne Likitan da ki ka zo gani da safe ku ka samu saBani da Kanina". ' Ta girgiza kai. "0h!" Gami da dan yamutsa fuska. "Wannan qanin na ka?" Ya yi murmushi gami da cewa, "Ina ji dai kuna da (Allergy) da juna, duk lokacin da aka ambaceki sai launin fuskarsa ta canja, ‘kema haka tun randa ku ka' hadu jininku bai zo daya Na 20 in ga hannunki ne in ba ki haquri sannan in ji me ye matsalarki Kallonshi ta ke tana murmushi. A ranta ta ce, "Akwai bambanci tsakaninsa da qaninsa. Shi mutum .ne mai sanyin hali da kirki. Haduwar farko na gane hakan. Shi ko wancan haduwar farko na gane halinsa 'mara kyau. 'Jin tayi shiru ba ta amsa ba Inna ta yi carab Ta amsa. "Likita hannunta dai da sauqi, mu Mutan Kauye ne muna da. dabara da namu Magun'gunan irin wannan CiWon. - Zan dai' yi ma ka bayanin babbar matsalar duk da yanzu taji sauki ciwon da kansa ya baje". Nan ta soma zayyana masa ciwon Deeda tun tana karama har zuwa girmanta da shigowar su Birni ya soma bajewa da kansa a hankali. Ya dan yi shiru na tsawon lokaci 'yana kallon Hannayenta. Ya so ya fuskanci matsalar sai dai duk da hakan sai ya yi bincike. Ya ce, "Na fahimta Kaka, sai dai duk da hakan tana buqatar zuwa Asibiti sabo da a can ne zamu yi duk wasu gwaje—gwaje don gane ainahin ciwon, duk da dai yanzu ya washe ba matsala, amma 'gaba zai iya dawowa, duk da ban tabbatar da wane ciwo bane, amma dai ba abun damuwa bane, in ma ta sha Magani to da yardar Allah za ta rabu da shi. Don haka gobe in Allah Ya kaimu ta sameni a Asibiti karfe goma." murna ta lulluBeta. , :Na gode Likita." Mun gode, duk da goben zata tafi amma" zata ganka. kafin ta tafi". Ya mike yana fadin allah ya kaimu goben, Inna tana ta godiya, deeds kuws kallonSa take tana mamakin’ kirki iron nasa “ya mike ya kalleta ya ce, 'miss Deeda inga hannun naki?" .ta-‘ sunkuyar dakai ta mika masa hannun ya kalla ba tare da ya taBata ba ya ce, "Kina da jiki 'mai kyau don bai kumbura ba, in dai yana miki radadi ki sha (Pain Reliver) Paracetamol da ,to"Na gode" Nan ya yi sallama da su ya wuce. Deeda ta bishi da kallo ya yin da Inna ta rakashi har iofa. Ta dawo ta samu Deeda zaune ta yi- Tagumi. ' tace, "Deeda kina tunanin tafiya ne? Karki damu Allah na tare da ke ina tare da ke idan kin‘ ga ana saki abin da ba dai- daiba ko ba kya so zan dauko ki mu dawo ". Ta“ dan yi murmushi ta ce, "Inna haka ne, ina tunanin tafiya sai dai na‘ fi tunanin barin karatuna duk da na koyi abu da yawa na iya abubuwa da yawa karatu da rubutu, turanci da ma abu da yawa. Haka na samu ilimin Addini‘ sosai a Makarantar wanda da ban san su ba.. - Alhamdu lillahi da zaman da na yi a {Gidan Tabawa da gatan da ta min, sai dai ilimi ba ya qarewa, yanzu na soma dandanarshi zan so in ci ~gaba'da samunsa. Sai dai ilimi ana samunsa ta kowacce fuska, duniyar ~gaba dayanta Makaranta ce, kamar yadda na koyi wani abu yanzu na fahimta, akwai mutanen kirki akwai na tsiya. Inna duba bambanci tsakanin wannan Likitan da qaninsa. Mutum mai nutsuwa mai kirki mai mutunci. Kaninsa kuwa..." ‘ Ta ja dogon numfashi. "Bana son ma tunashi balle maganarsa. Inna kar ki damu ina maraba da sabuwar rayuwar da zan shiga, a wurina wani sabon Makaranta ne na koyon wani sabon i‘limin rayuwa. Idan Allah Ya kaimu gobe zan je Asibitin zan roqi Tabawa mubiya tacan» sai mu wuce. Insha Allahu akwai‘haske a tattare data tafiyar da zan yi". ' .Inna ta yi 'murmushi. ‘ :"Na ji dadi Deeda yadda ki ka kwantar da hankalinki ba ki daga hankalinki akan tafiyar ba. Allah Ya taimaka ya sa alheri. Muna gari daya, zan dinga zuwa dubaki, za ki dinga zuwa kema in kin samu dama". Haka suka kusan kwana- suna hira gami da tsara yadda tafiyar za ta kasance. . Innan ta ci gaba da yi ma ta nasiha da bata shawara akan zaman rayuwa da kuma sababbin mutanen da za ta tarar ta yi mu'amala da su. ya kuke ganin zaman deeda DA saber zai kasance a birnin gayu anyama zasu hadu kuwa? h shared a profile . birnin gayu chapter6 Deeda kuwa ita ya fara gani, duk da kuwa akwai wadanda suka rigata; sabo da ita ya fara cewa a kira masa. . Tare suka shiga da Inna. Ta yi sallama, ya dago kai yana murmushi ya amSa ma ta sallamar. Ya kalli Inna ya yi dariyar tsokana ya ce, "Su Kaka 'yan mata, an iso?" . Ta yi dariya ta ce "Ya ka ganni ras da ni, duk Budurwar da mu “ka jera sai a 'daukeni an barta". . Yace, "Kwarai kuwa..Ai Kaka-“kin yi fice , 'Deeda dai kallonsu take tana dariya Kwarai halayen Ibfahim yana burgeta, duk da‘ alamu sun nuna dan masu hali ne ga ilimi ga wayewa amma ba shi da girman kai sai saukin kai sannan, 'ga dukkan alamu mutum ne mai halin kwarai. ‘ ‘ ' ' . Bayan ya gama barkwancinsa da Inna ya mai da hankalinsa kan Deeda ya ce, "Malama Deeda zan fara da miki tambayoyi kafin in kai ga ‘ maganar Ciwonki. ‘ Tambayoyin da zan miku kamar cikakken sunanki, shekarunki da sauran‘ su, sabo da ina son bude miki (Folder) don rubuta komai game da ciwonki, ne nan gaba in kin zo sai a dauko koda ba ni zan ganki ba wani Likitan ne in ya karanta zai san komai game da rashin lafiyarki. Ina fatan kin fahimta?" Ta girgiza masa kai. "Na .fahimta". Cikin‘nutsuwa ya ke ma ta tambayar tana ba shi amsa har suka gama, ya dinga ma ta tambaya game da Tarihin ciwon na ta tana ba shi amsa, amma wani lokacin Inna ta kan tsoma Baki har suka gama suka je ya ma ta gwaje- gwajen da ya dace sannan ya ba ta magani ya kalleta ya ce, "Kar ki damu ba wani matsala ba ce na tashin hankali, kamar yadda ki ka gani yanzu Fatarki ta fara washewa in kin Sha maganin nan zai taimaka miki sauran duk ilahirin jikinki ya wartsake. ; Sannan' irin ciwonki ba a cika samunsa ta nan ba, yana wuya a samu masu irin wannan Ciwon, shi yasa ma ba za a fahimci mene ne ba sabo da ba kowa ya san ko ya taba jin irin ciwon ba sai Likitoci irin mu. Jikinki da fatar jikinki baya son inda ki keda yanayin wurin da ki ke zaune, misali; Ruwan Garinku, yanayin Abincin wurin da irin Iskar Garin da aka Haifeki ki ka girma, kina da (Allegy) da wannan garin yankin wurin gaba daya, don haka da ki ka bar garin ki ka shigo nan sai aka yi dace jikinki ya karBi yanayin inda ki ka dawo, don haka fatarki da jinin jikinki ya fara washewa ya mike da kansa daga yamutsewar da ya yi. Ga mutum mai irin jikinki ba .kowanne irin Abinci da ruwa zai karbe ki ba. Kai hatta kaya zuwa mayukan da 2aki dinga amfani da .,shi ba kowanne Jikinki zai karBa ba, dan haka a duk lokacin da ki ka fara cin wani abu ki ka fahimci canji a jikinki ki yi saurin kiyayewa, haka kaya da sauran abin da ya Shafi‘ jikinki. Daga.kin yi amfani da abu ki ka ga ya canji a jikinki to ki yi saurin barin abun, in kin kiyaye insha Allahu ba za a samu matsala ba. Yanzu» ga Magani‘ da kuma sunayen irin Abincin da ’za ki kiyaye cin su da kuma irin abin da ya kamata ki dinga ci, duk ba wani abu mai ' wuya bane da zai gagara". . Nan Deeda ta yi shiru tana jinsa tana kuma tunanin Ciwonta Wane irin ciwo ne da ba ta taBa ji k0 ganin me; irinsa ba? Ikon Allah! Allah mai yarda ya so!! "Allah Ya kare ya kuma ba ki laflya Deeda". "Alhamdu lillah, Likita ina godiya, yau na samu haske akan abin da ya shige mini duhu. Na gode, Allah Ya saka ma ka da alkhairinSa". ' . Deeda ta fada‘tana' kallonsa. Ya ma ta murmushi yace,’ "Karki damu Allah Ya Yi mana jagora ya bamu LAFIYA, sai ki kiyaye kuma ki dinga shan magani". "Zan kiyaye insha Allah. Na gode". Inna mai Fura tace, "’Likita Kudi fa? Kamar nawa za mu biya?" Ya yi dan'daria ya ce, Kaka 'yan Mata nan Asibitin ai, na kyauta ne, k0: farkon zuwanku ba a fadi muku ba "An fada mana Likita, sai dai in magani ma kyauta ne da kudin Katin Ya yi' murmushi yace, "Duk kyauta ne sai dai in bamu da maganin mu rubuta a siya a waje". , "Ikon Allah! To yanzu Likita da kudinka ka ke siyan maganin? ’ Inna ta fada, kuma ta sa masa ido alamar amsa ta ke jira. Ya yi dariya sosai ya yin da Deeda duk kunya ta kamata saboda tambayar Inna. Ibrahim ya ce, "Kaka 'yan mata ai nima biyana ake, ina na ke da kudin daukan nauyin Asibitin nan? . ' Ai Likitocin 'muna da yawa, ‘kowa da fanninsa. Ni dai ina fannin Fata ne, wato masu matsala irin na su Deeda da makamantansu. Me Asibitin shi ke biyanmu da kuma sauran masu kudi masu neman Lada, sukan ba ‘da gudunmawar .Magunguna da sauran abin da :Asibiti ke bukata k0 kudaden biyan Ma'aikata da sauransu don neman Lada da taimakawa Talakawa marasa hali." "Ikon Allah!” In ji Inna. . "Irinimu ke nan? Kai! Allah Ya saka musu da alkhairi, Allah Ya yi musu albarka, Allah Ya sa sauran masu Kudinmu su yi koyi da hakan ‘Amin". Ibrahim ya fada yana dariya. Suka mike, Inna ta ce, "Mun gode Likita, Allah Ya yi ma ka albarka". Ibrahim ya amsa da, "Amin' Ya kara da cewa, "In dai

Chapter 5 of 25