Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Dad)". Wato ina ina kwana?" . Yavfada da murmushinsa ya amsa da‘, "(Morning Son). Na ji dadin ganinka kWarai; alamar ’ dai baka son in auto maka 'yar Kauyen mu".. Sabeer ya Kara bata fuska ya dauki. Coffée din da aka riga aka hada masa yana kokarin kaiwa Baki ya ce "Ni dai an takura min‘kawai, lokacin dana ke Medicine mun yi da kai da sharadin ba. zaka sani yin aiki dole ba, kace min ilimi kawai ka keso nayi, kana'so in cika maka burinka in zama Likita,’ duk da bana so sabo da kai na daure na jure wahalarsa na yi ta karatu ba ji ba gani na takura kaina, amma shi ne yanzu ka Bullo mintanan. . Gaskiya Daddy ba ka min adalci ba, ni gaskiya bana son wani wahalar aiki". Kalamansa sun ‘Batawa Mahaifinsa ,rai sun ‘ kuma kufulashi. Ya matsa kusada shi ya ce, "Inbakayi aiki ba. me zakayi?"Ya fada cikin' basala. ' . .koso "Kake ka kare rayuwarka a haka ba zakayi . komai,ba‘ baka da exPRIENCE) baka da wata dabara‘, . inna mutu wa2ai kula Ma da dukiyar? . Ka san yadda zuciyata kemin inna . ganka haka baka komai sai Sakarci? ‘ ' Lokaci ya yi da za ka nitsu kasan Ciwon kanka Sabir ya kufula shima ya hau dokin zuciya ya ce, "Me yasa zan yi aikin wahala in nemi > kudi tunda Mahaifina nada kudi, 'yan uwana na da Sabo da me zan nemi kudin yanzu ba lokaci bane da zan nemi kudi, lokaci ne da zan more . rayuwata, inji dadi Haka kawai rana tsaka kace zaka shiga tsakanina da jin dadina ka zama , kana so ka doramin nauyin da, ba naWa ba, in ka takura min da maganar aure da a'iki Daddy bazamu‘ _ _,shiryaba,mezakayi? 1‘ 'Mezakayi me zaka iya yi- inji Daddyn ya..." Ya fada ' cikin zafin rai. . . "Bari in fada ma ka, kudin da kake gani ka’ke gadara da su nawa ne ni na nemesu da gumina da wahalata ba zan bari ka Barnatar dasu a banza ba, idan zaka nutsu ka san me kakeyi, ka nutsi, inba hakaba kuwa za ka sha mamaki." ‘ Wane mamaki zan sha? Nima bana bukatar kudinka, nima ina da nawa kudin, kudin da Mahaifiyata ta mutu ta bar min, "Sabir ibrahim. ya kirashi cikin tsawa. Ya yin da ‘ Mahaifinsa ya wanke shi da mari. Tsananin Bacin rai bakinciki ‘ya hanasa magana. Ya yin da Sabir din ya juya rike da fuska zai tafi Ibrahim! ya tsai da shi. Sabir ya jawo hannunsa zuwa gaban Mahaifin nasa ya ce"Ma za ka bashi haKuri,‘ kar ka kuskura ka. sake yiwa Mahaifinka irin wannan magana in kana so ka gama da duniyar nan lafiya.’ Ba Mahaifinka. kadai .ba, ka koyi girmama manyanka ‘na gaba ‘ da kai, kuruciya da iskar samartaka' ba. hauka bane, kowa ma ya yi Wannan lokacin ya wuce, meye laifin Mahaifinka don yana nuna maka Kauna,’ ya damu da'rayuwarka, yana so kasan ciwon kanka da zafin kanka shi ne zaka dinga yi masa magana cikin wannan harshen? Ka yi hankali da duniya, maza. ka bawa Mahaifinka hakuri". Kansa sunkuye idonsa ya yi ja zuciyarsa kamar za ta kashe shi ya bawa Mahaifinsa haquri (Sorry ‘ Daddy Ya kama kunne. Ba zan sake ba, ka yi hakuri Daddy ka yafe min» ' Tausayinsa da Kaunarsa ne suka shige shi lokaci guda. , ' Ya dafa kafadarsa yace "Na yafe maka Sabir. Ina‘ so ka sani Babanka na sonka sosai (Just)‘ how that i love you) girgiza masa kai ya yi ya fita ya bar falon, Babansa ya bishi da kallo cikin tsananin son dansa da kuma tausaya masa...in akwai abin da ya tsana bai wuce Bacin ran dansa ba. Bayan fitarsa ya mai da kallonsa kan Ibrahim? cikin damuwa ya ce, "Ibrahim na yi kuskure, na yi. “ babban kUSkure-~iyayena sun min 'gata amma' ba kamar yadda na yiwa dana ba, son dana yasa nayi . ~ babban kuskure na Bata masa rayuwa, ban san ta yaya zan soma‘ gyara wannan kuskurenvda na yi ba, soyayyata gareshi ya: Bata tarbiyyarsa. ’ _ Ibrahim ya kallesa cikin tausayawa ya ce Kwarai Daddy kayi .kuskure sosai wurin tarbiyyar ‘ ~ Sabir,‘ yanzu gyarashi ta hanyar tsawa ko fada ba zai yi gareshi ba, don ba zai taBa fahimta ba Yace yayi nisa canja tunaninsa zai yi wuya sai anbi Wasu hanyoyi cikin dabara da. kuma masa adddu'a harmu cimmasa Karka damu Daddy inshal AllahuSabir Zai fahimta‘ a hankali ya isa garesa ya ,zaunar da shi Daddy ka kwantar da hankalinka, kar ciwon hawan jininka Wanda bayason yawan tunani ya tashi na san ma dai baka sha magani ba, nan ya'dauko maganinsa tare'da‘ruwan ya mika masa _ ya sha sannan ya rakashi daki ya kwantar'da shi yace daddy ka kwantar da ’ka huta kadan kafin ka fita office , . Sabir ne zaune a karamin falonsa'cikin idonsa jawur kamar zai zubar da hawaye. ' Ya dauko Wayarsa don ya kira ‘wacce ke kwantar masa da hankali. Sister ya kira sunanta'cikin.., muryar kuka. Sister please ki dawo ki zoki daukeni ina: missing dinki' sosai, Daddy baya sona, yanzu quntata min yake son yi. Sister bana son zama a Nigeria ki dawo please, Daddy da Uncle IB fada suke min, basasona. Yi‘ shiru Sabir takatseshi.“Kayi hakuri .ka ga duk hankalina yatashi, wa ya fada maka Daddy baya sonka, .ka san Daddy yafi sonka akan kowa, kuma Sister na sonka, « yanzu- kaifa ba yaro bane, 'Sabir dina‘yanzu babban . mutum ne ka manta~ ‘ .alkawarin da kai yiwa Sister dinkane...ka manta kace ‘ min zaka nunaWa Daddy cewa ka girma kaima za-ka ‘ iya daukar nauyin Asibiti da kulada Business dinsa? .me yasa tun daga yanzu ka soma nunamin kasawarka? Sabir dine yanzu, zaka iya komai, ‘ ga Uncle IB yana tare da‘ kai, zai taimaka maka Sabir ka san‘. Sister na sonka sosai, damuwarka 'zai daga min‘ hankali har in kasa mai‘da hankali akan abin da- ya kawoni in yi a nan Sabir ka yi kokari ka daure kayi abin da Daddy keso..kanajina "Eh ina .ji Sister". Ya fada cikin sanyin murya. ‘ ‘ \ . . . zan yi kokarin danne zuciyata , nan gaba. Ki; kula da kanki Sister (llové you) ta yi ‘ dariya‘ ta ce ka kula da kanka da Daddy da Uncle IB ‘ zan yi duk abin da kika ce Sister na san Sabir dama ‘ yana jin maganata yanzu zan shiga Asibiti kai ma ka tashi ku shiga Asibiti'“To Sister sai an jima"Nan sukai,sallama ya dago .kai’ gami da - jan:dogon numfashi. "Kaje ka tabbatar .masa da kaima' kana kaunarsa, kuma za ka yi duk abin da ya‘ ke so Bata fUSka yayi” ' Uncle lb kaima ka san abu mai wuya ne yin abin da Daddy yaks so". "Na sani Sabir". Ibrahim ya katseshi. Amma duk da hakan kaje ka fada mai don kWanciyar hankalinsa". ‘ Ba‘don yaso ba ya mike yanufi falon Dadin‘ ya ’sameshi kwance rufe a gadonsa da hannunsa. daya... Sabir ya durkusagabansa ya jawo hannunsa yace am “sorry dadi. Ya fada murya kasa-kasa."Daddy ka yafe min ba .zan sake ba, Mahaifin‘ nasa ya yi murmushin'jin dadi, duk“ da ya san ba har‘ zuci yake fada ba, ganin kulawarsa garesa ya faranta ransa. Yace"Allah Ya taimaka Sabir Yau zaka' fara xuwa Asibiti da Ibrahim, ina fatan za ka ba da himma da kOkari Wurin duba marasa lafiya Kar kasa wasa k0 sakaci da rayukan al'umma" Ya kau da kai alamar bai son maganar ya ce"Daddy zan je dai in fara koyon aiki ba in kai ga duba mara lafiyar,,,,, ‘ "Sabir abin da ka‘karantane sannan da ka gama ka yi (Service) wane koyon aiki ya yi ma ka saura?” . Ibrahim ne ya shiga tsakani ya ce "Daddy ka san ya jima da yi, kuma ba (Practics) yake yi ba, amma dai a hankali zai gane ai muna tare yanzu, dolensa zai koya sabo da Daddy da kuma gujewa auren 'YAR KAUYE!" Ya fada cikin" tsokana. .Sabir ya qufula ya- fisge Key din Mota. a hannun Ibrahim din ya fita tare da fadin, "Ina mota zan jiraka‘in 'ka gama da Daddy din". ‘ . Suka bishi da kallo har ya fice. Daddy ya mai da kallonsa kan Ibrahim ya ce"Na rasa me ke damun Sabir, wace irin rayuwa ’ya ke sowa kansa, yana girma amma yana gudun (Responsibilities) dinsa Ibrahim don Allah ina so ka taimaki Sabir ya '‘san me yake yi, ya zama (Seriousc). Ibrahim ina .kishi da kyashinka, ina kyashin me yasa Sabir ba kamarka bane? Ina kishin me yasa dana ba irinka bane? Me yasa jinina ba zai zama irin ka ba sai dan riko? Ibrahim kullum kana cewa na da zuriata don haka komai zaka iya mama muddin bai sabawa‘ Shari'ah ba, ka‘tuno kalamanka Ibrahim Dr. Sulaiman ya fada yana kallonsa ido cikin ido. Ibrahim ya girgiza kai tare‘ da fadin, "Eh Daddy na tuno komai ban manta ba, banda kalamai nama harda irin taimakonku da alkhairinku kun kyautatama rayuwata, kun min duk abin da iyaye za su yiwa dansu, don haka na yiwa kaina alkawarin yi muku biyayya da yi muku duk wani abu da da nagari dan halal zai yiwa iyayensa da zuciya daya ba cuta ba cutarwa". Dr. Sulaiman ya yi ajiyar zuciya ya ce, “Na ji dadin haka. Ibrahim lokaci ya yi da mu ma zaka mana (F avour) taimako kamar yadda muka yi maka, a matsayina na uba na yi kuskure nayi kokarin gyara' kuskurena ,amma hakan ya gagara sabo da rashin’ fahimtar da ke tsakaninmu da dana Sabir. Ibrahim ina so ka mai da sabir kamarka, ina so Sabir ya zama kaman. Ibrahim (Smart, lntelegent) mutum mai kwazo, hikima da dabara wanda ya san ciwon kansa,. za ka iya Ibrahim?" "zan yi iya dukkan qokarina Daddy k0 ba ka ' fada ba Daddy dama wannan ita ce niyyata na taimakawa, Sabir ya samu ingantacciyar rayuwa kuma ya samu tsira har a gobe Kiyama, ba duniya kadai nake so in taimakawa Sabir ya samu ba, har da Lahira wanda ita ce Matabbata. Kafin kai na yima wata wannan alkawari kuma na yiwa kaina. Sai dai dama tuni kaine ka shiga tsakanina da ’cika wannan alkawarin sabo da k0 ya ya ba ka so a batawa Sabir k0 a cusguna masa, kai ka kyale Sabir ya yi duk abin da ya ke so ya yi duk abin da ya ga dama, wani bai isa ya hanashi k0 ya sa shi ba, don haka wannan magana da ka fada min yanzu ya kawo min sauki sosai, kuma na ji dadin hakan, Sai ka’bimu‘ da addu'a'da fatan Allah Ya bamu ikon inganta masa rayuwa. . Sabir ina jin’sa tamkar‘ Kanina na jini, ina matuqar kaunarsa kamar yadda ka ke kaunarsa, don haka zan baka karfina da kokarina dari bisa dari ; wurin inganta masa rayuwa da fatan za ka bani hadin kai sosai." Dr. Sulaiman ya fada, "Zan baka dukkan wani hadin kai. Sai dai don Allah ka bishi a hankali i ‘ kar a Bata masa rai Ibrahim ya yi murmushi ya Ce, "Daddy sai ka kau da kai". ‘ Dr. Sulaiman ya ce, "Ba zan iya ganin Sabir cikin bacin rai ba, sai dai ina ga zan yi tafiya ma‘ sabo da kar ma in ga wani hali da zai shiga, zan barshi (In your care) ka kula da shi, duk da zan yi kewarsa -‘ gara in yi kewarsa da in ganshi cikin yanayi na. quntata ko na takura." ' ‘ Ibrahim ya ce"Duk yadda ka yi daidai ne ‘ Daddy. Bari muje Asibitin".To Allah Ya taimaka, Ya bada'sa'a". ‘ Nan sukai sallama Ibrahim ya fita, ya yin da Dr. Sulaiman ya kwanta yana tunanin dansa a ransa da yadda rayuwarsa za ta kasance sabir ya fito daga zuriar ALHAJI BALA-RABE ABUBAKAR Wanda ake_ma Zuri'ar lakani da BIRNIN GAYU. Ba don arzikinsu kadai ba, har da shaharar da suka yi da ilimin zamani wanda a wannan lokaci ba kowa ke yi ba. ' Alhaji Balarabe Kaka ne ga Mahaifin Sabir Dr. Sulaiman. Ya yi zamani da' Turawa, kuma ya yi rayuwa ~dasu, ya yi zama da su a engla ' Asalinsu mutanen Kano ne. Sunada ' zuriarsu a gauraye suke Hausa-Fulani Lokacin da Alhaji Balarabe ya dawo daga ingila ne bayan ya yi karatu kuma ya yi aiki da su harna tsawon shekaru ya dawo Kano tare da Matarsa da 'ya'yansa. . ‘ Ya dawo da kudi maSu yawan gaske, ya sayi makeken Fili ya ' gina gida a Estate guda Wanda a wannan lokaci ya zamana abin kallo da ‘sha'awa sabo da gini ne irin na kasar waje' da da yawan mutane akan gidan suke fara ganin ‘irin wanna“ gidan... Wannan yasa -' akai ma gidan lakabi' ‘daBIRNIN gAYU saboda irin yanayin' ginin, da tsarinsa da kyansa da .kuma yadda‘ ~' suke rayuwarsu irin na Turawa'ne tamkar ba Hausawaba" 'Tsarin ° rayuwarsu ba irin . tsarin rayuwar Bahaushe, bane haka dabi'unsu da ; akidarsu. A hankali zuri'ar Alhaji Balarabe ta cika" da yara ‘maZa da mata, shi da qannensa da sauran danginsa sukai ta hayayyafa, Zuri'a ta girma ta 'cika, ta bazu kota ina,rasuwarsa, 'ya'yansa , ‘ ,suka ci gaba da tafiyar da ,tsarin rayuwars kan yadda ya‘bari. Zuri'a ce mai cike da 'yan: Boko, 'yan Kasuwa, 'yan Siyasa. Ba dai kalar da babu.‘ Hatta masu (Uniform) akwai a zuriyar, wato manyan Sojoji; 'yan Sandadasauransu A hankali Suka dinga fita daga BIRNIN GAYU, wato gidansu na gado, kowa'ya kama gabansa yaje yayi irin kalar gininsa da yake so. Amma sai ya dora BIRNIN GAYUN nan sbd sunan laqani ne da shaida na zuriyar Yawancin auren gida suka dinga yi, wato, AURE‘N DANGI, shi'yasa kusan kowa dan uwan kowanene azuriyar. Dr. .Sulaiman 'ya kasance babba a cikin gidansu, wurin nasu‘ Mahaifin su"uku, ne da- qannensa duka maza. . " lyayensu duka sun' rasu; saidai kafin su rasu kowa‘ ya kama gabansa dukkansu kowanne- da matarsa suna da yara suna zumunci ta hanyar ziyartar' juna in Sun .samu‘". lokaci daga harkokinsu sai dai gaskiya ba wani shaquwa a tsakanin yaransu, in an yi la'akari irin akidar da suka tashi da ita ba ruwan koWa da kowa ba mai shiga harkar wani sai-ta kama, don haka Dr Sulaiman yake nasa rayuwar daban da yaransa Dr. Sulaiman- ya riqe manya-manyam mukaman Gwamna‘ti a cikin tarihin rayuwarsa. Bayan ya kammala karatun Digirinsa na uku ne a kasar Sweesland ya cancanci zama (Doctor sai ya dawo qasa Nigeria. da zama inda nan ya gina wani qaton Asibiti da ya yi masa lakabi da sunan Mahaifiyarsa HAJIYA RABI HOSPITAL sabo da sha'awarsa‘. ga taimakawa qasarsa. lYa riqé mukamin comisionan ilimi na Jiha har tsawon‘ ‘ shekara takwas. Bayan shudewar Gwamnatin ne sabuWar gwamnati ta sake nadashi a matsayin kWamishinan lafiya, inda bai dade ba da wannan mukamin Sunansa ya fito cikin jerin mutanen da ; ‘Fadar Shu‘gaban Kasa ta lissafa a matsayin .Ministoci. ' ' Anan ma dai Gwamnatin Tarayya ta sake : nadashi ;Ministan Ilimi na qasa gaba daya har zuwa qarshen zangin Mulkin na' wannan qarnin Alhaji Dr. Sulaiman ya mallaki manya~ manyan Kamfanunuwan da ake ji dasu a kasarnan. , ._dr Sulaiman ya yi matan aure uku. ' Matarsa ta farko ita ce Hajiya Sande wacce 'yar uwarsace; Ita ta°fara haifa masa 'ya Mace mai suna ' Farida, wacce Dr. Sulaiman ke‘ ji da ita sosai. Tana da shekara biyar a duniya Allah Ya yi ma ta rasuwa, ba tare da ta sake haihuwa ba. Anan' Dr. Sulaiman ya sake auren Hajiya Amina. . ’wannan karon ba' 'yar— uwarsa bane, 'yar aminin Mahaifinsa ne ya ba shi ita. . . Bayan Hajiya Amina ta haifa yaran ne Zulaiha da Rufaida rikon Fadila ya gagareta, _. rainonta ya Kare ahannun 'yan aiki. ' farida ta kasance cikin kewa da kadaici sabo ba mai janta a jiki' sai Mahaifinta wanda kullum baya nan, harkokin gabansa basa bari ya ‘ kusanta da ita, ’ Zuwan Ibrahim 'gidan ya dan kawo ma ta sassauci. Wanda dane. ga abokin Dr. ‘Sulaiman wanda ya samu hatsarin Mota shi da Matarsa suka- rasu a.take. A cikin zuriyarsu 'akai' ta kame-kamen mai rikonsa, don haka Dr. Sulaimanya daukoshi ya kawoshi. gidansa ya bawa Hajiya Amina amana don shi bai san‘ma irin rikon da ake yiwa yarsa ba. Farida na da shekara bakwai,‘ Ibrahim nada shekara hudu Shi ya zame mata abokin ‘wasanta, yana" debe mata kewa, har goyo tana masa, ta bashi abincisuje Ma‘karanta tare, yana rabin Aji .itakuma tana Aji uku, ya yin da kulawarsu,-kayan sawarsu da kOmai na hanmin masu Aiki. ‘ . Wata Kanwar Dr. Sulaiman neta~zo gidan taga irin halin‘ da suke ciki,"tayi saurin sanar _ shi, sai» suyi ciwo su kwanta ma Hajiya’ Amina .ba ta da labari,‘ ita da yaranta kuwa basuma cika zama qasarba kasar yarda take ta naci da‘ qokarin samun da namiji, amma ikon Allah k0 Ciki bata - sake yiba. Bayan Dr. Sulaiman ya samu labarih abin da ke faruwa, ranshi ya baci, ya yi niyyar yin maganin Hajiya Amina, tana qasar waje k0 sai ji ta yi ya yi aure, ya _auro Hajiya Fatima 'yar hamshakin mai kudi Bafillatana"fara sol, kyakkyawa mai ilimi', ga Wayewa _Riqon 'Farida da 'Ibrahim ya"—koma hannunta ta rungumesu. ko— hannu ~biyu kamar yayanta So, “Kauna' da — Kulawa da 'Gata ba Wanda ba ta‘ nuna musU' har suka manta da rayuwar ‘ kadaicinsu. Hakan ya jefa soyayyarta ‘a'Zuciyar Dr: Sulaiman sosai. Suka yi wata irin shakuwa. Dr Sulaiman ganin ya» gama .sauka a Mukamansa, kuma ya tara dukiya .mai-dumbin: '_ yawa, ga kuma._ manyan - Kamfanoninsa‘ da Asibitinsa na aiki yadda ya kamata, hakan ya tattara Yaransa da Matansa Hajiya. Fatima da Kasuwancinsa ya ‘koma kasar Canada, ya yin da‘ ya bar Hajiya Amina a Nigeria da Yaranta. shi kansa Dr. Sulaiman sai dai -wayewar ta ratsashi sosai, haka bokon ya shigesa sosai akan addini. Tana burin gyara rayuwar gidan ' Wannan magana na Hajiya Fatima» ya shiga kwakwalwarSu sosai, musamman Farida da takeda'wayo so Sai dai burin Hajiya Fatima bai kai ga cika ba allabYa karBi ranta ta hanyar haihuwar Sabir Kwarai - Fatima da Ibrahim sunyi kuka" Sun yi rashin Uwa' mai .sonsu da qaunarsu Haka suka ’shiga’halin MARAICi da shi ’" da yaransab dukda Yana da‘ wata-Matar, amman " jinta yake ba kamar Hajiya Fatima,ba ‘ Rainon Sabir 'ya koma hannun‘ farida qanuwar Dr. Sulaiman, musamman ya daukota-‘ta dawo Canada’sabo da rainon Sabir, don kuwa bata da aure, tana gida ta samu saBani da Mijinta har auren ya mutu. Tare suka zauna' su Farida da shared a profile . birnin gayu chapter4 Ibrahim. suka yi rainon sabir. Yana da shekara uku a duniya Auntynsa ta yi aure.) ' , Farida da Ibrahim da masu aiki da shi kansa Dr. Suleiman din sun: sukaita rainon Sabir ya saba dasu sosai ya shaqu da Farida sosai, komai Sister: haka ya dauketa tamkar uwarsa, bashi da magana da‘ ya wuce na Sister. ‘Sun dauki son duniya sun daura masa , musamman Dr. Sulaiman yadda yake Bata Sabir abin ba,a magana duk abin da yake so shi zai'yi, ba a sa shi ba a hanashi. Haka ya tashi sakale, gata ya yi masa yawa. a wajen Dr. Sulaiman tamkar bashi da wasu ‘ ‘ya'yan. duk da yana kaunarsu amma soyayyar Sabir daban take a zuciyarsa da ransa, don haka duk abin da Sabir keso ya zauna ba mai hanashi. Farida abin na damunta, duk yadda ta yi kokarin gyara Sabir sai Daddy ya rushe, tana matuqar son sabir; haka nan bata mance kaunar da Mahaifiyatsa ta nuna musu, sannan nasiharta da burinta yana nan a tsakar kanta. Farida, Ibrahim, Sabir tare suka tashi, suka girma cikin so da shakuwa, ya yin da farida ke musu komai a matsayinta na babbar yayarsu. Sun taso kuma sun girma a Canada, anan suka yi, karatunsu, daga Farida har; Ibrahim Medicine suka karanta, don dukkansu wannan' ne burinsu. ' ‘ Haka- tana da burin ta dawo gida Nigeria ta yi aiki a'Asibitin.‘ Mahaifinta. Kullum tana; cikin .katu bin.cike akan Mata; ta kware akan sanin ciwon Mata da matsalolinsu Ya yin da’ 'Shi kuma Ibrahim ya karanci bangaren fata bayan ya zama cikakken ,Likita ya Sake kOmawa karatu na, ‘ shekara uku don kwarewa akan sanin ciwon Fata Shi kuwa Sabir, bayan ya gama Secondary - School dinsa da yaki karatun ma sabo da duk- abin da yake'so a duniya yana da shi, kuma zai samu sabir Mutum ne Wanda ya ki jinin wahala k0 kadan, baya'son abinda zai Wahalar da shi‘. ' Cikin‘dabara 'Farida da Mahaidinsa suka sa ya fara karatu Da da farko Business‘ya soya'; karanta amma ; sai ' Farida‘ tace ‘masma" 'yana, da kwakwalwa ‘mai zai hana ya Zama Likita kamar: yadda ita da Ibrahim suka karanta (Medicine) sai , su tari su riRe Asibitin Mahaifinsu. ,ta Kara nuna masa cewa burin Mahaifiyarsa ce hakan Sabir ya amince ya ; ‘ fara karatunsa na Medicine " a University of Albena da ke Canada. ’ ; ' Bayan gama karatunsa ne‘ Mahaifinsa‘ ya ~ shirya musu tafiya hutu tare dan-Shi, suka tafi yawon bude ido qasashe daban-daban suka yi Umarah a Saudi sannan suka Wuce Nigeria» Wannan karon shi ne karo na farko da Sabir ya zo Nigeria yaga 'yan uwansa da danginsa na gun Uwa da Uba. Basuf1 Sati ba ya daga musu hankali suka koma Canada. Zulaiha da Rufaida na tare da Mahaifiyarsu a Nigeria haka nan duk sun gama ‘ ‘karatunsu‘ suna aiki a Kamfanin Mahaifinsa , kafin su yi aure. dr Sulaiman ya kasance tsakanin Canada 'da Nigeria. _ Farida da Ibrahim na son dawowa Nigeria amma Mahaifinsu ya hanasu sabo da kawai su zauna da Sabir a Canada, .don ya ce shi ba zai dawo Nigeria ba, rayuwar da- Sabir ke yi a Canada yana mugun dagawa Farida hankali. Ta shiga‘ damuwa sosai saboda ‘ko ta hanashi bazai hanubA, haka Daddy ya hanasu’ takura masa k0 su yi mishi abin da’baya so. . Sabir kyakkyawan Matashi ne, dogo fari tas sakalalle dan masu naira mai ji ‘da. ilimi 'da kuma wayewa, wanda gata ta masa yawa, ' Yana yadda yake so da naira, ya shiga Mota mai tsadar da ya ga dama, ya sa mai tsada,’ ya taka mai tsada, ba shi da wata rayuwa da ya. wuce na jin dadi da hOlewa. Addini dai bai damesa ba, yana dai Sallah, lokacin da ya ga dama, haka 'yan mata kuwa canjasu yake'kamar riga. ’ Duk wata 'yar mai kudi da ke ji da kanta wurin kyau da ilimi da aji irin wanda iyayensu , ke‘turosu karatu daga Nigeria; ba wacce Sabir bai yi yayinta ya kyaleta ba. Tsananin suyi wata biyu zuwa uku da Mace ya yar da ita. Haka ma sauran Matan fararen Fata, ba kalar Mace mai kyau da Sabir bai yi yayinta ya zubar ba. Hat gobe 'yan mata binsa-suke, yana musu . yadda ya ga dama. A cewarsa shi yanzu ya gaji da 'yan mata . wai kyawawa sun kare, shi k0 mutum ne mai son abu mai kyau, komai nasa a rayuwa mai kyau da sha’awa yake so. _ Ya yin da yaki jinin mummunan abu, k0 da kuwa dabba ne k0 Sutura. ‘ A fili ya ke nuna kyamar mummunan abu. Wani lokacin in ya ga mummunan dabba bayan kyamarsu ma‘har da tsoronsu yake ' Akwai ran da yaje Asibitin da su Farida da Ibrahim ke aiki suka samu an kawo hatsari ba kyan gani, mutumin kansa ya kumbura ” sosai, gaba daya halittarsa ya canja'. Koda Sabir - ya ganshi, ‘ ya yi tsananin firgita, sai da ya suma sabo da firgita. a Haka ranar yakwana a tsorace yayi ba bacci haka ya qankame Ibrahim a jikinsa ya' kwana Farida na masa addu'a. Da‘ taimakon Allurar Bacci ya‘samu bacci da kyar saida ya kusa sati kafin ya dawo daidai tun kuwa daga wannan ranan bai sake zuwa Asibitinba ko da wasa ba . .' ’Wannan rayuwa ta'Sabir yana mummunan ,daga hankalin Farida. Sam bai san meye rayuwa ba , 'Su tsoratar da Sabir ga ‘ mutuwa. ya san kwanciyar Kabari, su inganta‘ . masa' rayuwarsa ta duniya da lahira _tun kafin '~ ‘lokaci ya kure musu gaba daya. ‘ _ Wannan ne yasa ‘farida ta ‘fuskanci’" Mahaifnsu ta sanar da‘ shi illar rayuwar da ya ' kyale Sabir yana yi, dole ya san na yi da amanar, da Allah Ya ba shi na 'ya'yansa. ‘ Farida ta 'yi iya qokarinta sosai nason ganin jawo hankalin Daddy ya fahimci ‘ halin da 'Sabir yake ciki- ammai sai ya kasa ganewa har’ zuwa lokacin da suka dawo Nigeria don yin auren Farida da kannenta Rufaida-da Zulaihat. Da‘kansa ya lura da rayuwar da Sabir yake ba abin da ya tayar masa 'da hankali kamar yadda ya ga Sabir yana shan giya kamar ruwa .Haka nan Sabir sosai akan abin da ya ke so in an hanashi Ranar ‘da Daddy ya kamashi da giya ya hanashi sha rana ta farko ke nan da ya fara hana shi wani abu a rayuwa. Ranar ko ya ga rigimar. Sabir, nan da nan. ya birkice musu, 'ga Sabir da wani irin fishi da zuciya mara kyau. ' ' ‘Sai da ya dagawa kowa hankali a ranar. ' ‘ Tun daga lokacin hankalin Baban nasu ya fara tashi sabo da ‘yadda ’ya ga Sabir na shan giya;ne kuma ya saba da' ita haka to zata iya taba lafiyarsa~ ' 'innalilahi' Wa inna ilaillinaju ’un Abin' da Daddy ke fada kenan cikin tashin hankali. ' Farida ta matso garesa tare da Ibrahim 'ta ‘ ce, "Daddy abin» da nake kokarin- ka gane ke nan tun-tuni ka kasa. ‘ Dubi~ irin rayuwar da Sabir yake, wannan ‘ kadan ma ka gani, mu da ke rayuwa da shi-mu muke ganin rayuwarsa. .. Daddy kai iyayenka sun maka yadda kai ina Sabir'kuwa? Na yarda suna da wani irin ' akida, amma ba‘ su hallaka ma ka rayuwa ba, don da sun maka haka da yau ba ka kai matsayin da kake ba. . ' ' - ' Kai mutum ne da ya san'me yake, mai ilimi, hikima da basira. “ Kowa ya san kai dattijon kirki ne, kowa- ya San kai na Kwarai ne. Daddy‘ ka dubi Sabir, kana ganin inya girma ya kai shekarunka ba za a dinga yi mishi kallon’ dattijon banza‘ ba?‘ Daddy wannan soyayyar da ka ke yiwa Sabir ta hallakar da shi, ta kashe masa rayuwa. - Daddy duba da sauran yaran Abokanka wandanda suke sa'annin juna da Sabir, dubi yanayin hankalinsu da nutsuwarsu, sunanjin maganan iyayensu‘, suna ginnama na gaba dasu ‘ ' Daddy ~ kana Mahaifin Sabir ammn yanzu baka isa ka sa shi ko‘ ka hanashi k0 ka tsawatar masa ba, sabo da tun yana yaro baka mai haka ba sai yanzu Daddy wannan' rayuwar ba shi ne wacce Mahaifiyarsa taso masanba da shi“ da mu. .duka, haddakai. Tana son nuna mana kyakkyawar rayuwa don! muci ribar duniya da lahira‘. . Ina jin takaicin rashin cika burinta sabo da baka bamu dama‘ ba, duk da na yi aure zanci gaba da rikon Sabir kamar dana,ne ,Mijina ba shi da matsala, ka san zai iya yiwa Sabir komai; zamu yi Kokarin gyara masa rayuwa "in har ka‘ amince". . Hawayen nadama ya zubowa Daddy yace‘ "Tabbas na' tafka kuskure" babba, ’ zan- yi"kokarin gyarawa. ‘ Ban san na yiwa Sabir illah ba; sai da._, na gani da idona Tabbas sa'anninsa sun masa, fintinkau A wurare da dama, duk da ya fisu da komai, ba abin da ya rasa tun daga kan dukiya, .asali, gata, kyan halitta." . Sai' dai Sabir yana sakarci,

Chapter 3 of 25