dashi
Maryam na tsugune har shafa takawo yace oya jeki abinki shafa ta tafi tana tauasayawa maryam
Dagash ya kalli maryam yace ke tadago manya mayan idonta tazubamishi masu rikitar da mekallonsu
Dagash gabanshine yafadi yayi saurin dai daita kanshi yace dauki tsintsinyar nan ki share compound din nan yanzu
Maryam tace to batare da sake kallon inda yakeba
Tafara sharanta
Faisal yace haba dagash yazakayi haka kuma baka ganin yanzu tadawo daga school dan kabarta taje huta
Zayyad gaskiya hakan baidace ba itafa batasan ma abinda tayiba ganizatayi mugunta ne kawai
Dagash yayi dariyar mugunta yace kungama nawa kukagani banataba
Tafi karfin tabada hakuri saboda girman kai tana chick little girl din ta hartasan raini zankoya mata hankali agidan nan
Zayyad yagane DAGASH dai sokawai yakeyi tabashi hakuri itakuma yarinyar tanuna batasan wannan ba
Faisal yace Maryam yakirata tana sharar tabari tazo yace bashi hakuri kitafi kiyi huta
Maryam tayi murmushin takaici tace yaya duk da bansan sunankaba
Ban wa yaya al'amin komai ba kawai dai yasani aikin ne saboda ya isa yasa ni dan yana matsayin babban yayana saboda haka zanyi zangama insha Allah
Ta wuce su abinta yacigaba da shararta ta
Zayyad ya bushe da dariya yace wa Faisal yaufa maza ya hadu da dai dai dashi
Magaanrsu ce tadawo dashi daga tunanin dayatafi yace haryanzu ba haifi yarinyar da zata min raini inkyaletaba dani da ita zanga metaurin kai idan na zaneta
Zayyad yace a a mutumina kar ayihaka kaganyarinyace karama
Karkabari raini yashga tsakaninku da ita kΓ ja girmanka kawai please
Maryam tagama dan dama gidan Ba datti kawai muguntace irin nashi
Ta isa gurin ta durkusa tace yaya nagama
Cikin fusata yace dan ubanki waye yayan naki
Ba maryam ba harsu zayyad rasa bakin magana sukayi
Maryam tayi shiru zakin yabata mata rai sosai saboda bata son tsawa antynta bata mata
Tadaga kai tace haba yaya bakasan allah yatsine wa Wanda yazagi iyayensa ba
Karasa abinda zaka sakawa daddy dashi saizagi
Danni a yanzu banida wani ubanda dayawuce daddy a rayuwata kagakuwa dan kazageni kaman shikaga tunda ubanmu daya
Tana kawowa nan tayi gaba abinta
Dagash yatashi dasauri zayyad yayi saurin shangabansa yace haba man be a man mana
Kuma fa yarinyar nan gaskiya tafada kai dan'uwantane danme zakazageta
Bayan nafada maka karkabari raini yashiga tsakanin Ku
Idon al'amin yakada yayi ja saboda bacin rai bai taba irin haka koda daga gurin abokanshiba sai akan yarinya karama yar talakawa
Juyawa yayi gurin mota yanufa abinshi yafada yayiwa motar key yafita daga gidan
Maryam nashiga part dinsu taga anty a falo tayi kwalliya cikin material doguwar Riga
Tayi kyau sosai
Maryam tayi murmushi tace anty kinyi kyau sosai
Anty tace Yakika dade sosai haka yanzu karfe shida da minti ashirin
Kafin maryam tayi magana shafa yashigo cikin falon maryam tayi saurin cewa anty tace Bakomai anty kinsan sabuwar zuwa sai a hankali
Shafa tagaida cikin ladabi anty ta ansa mata ya school tace alhmdll anty
Tanemi guri tazauna anty tace shafa'atu tashi kije kici abinci gashican a dining
Shafa tace to anty batayi musu taje dining din taja tazauna tafara serving kanta abinci maryam kam tuni tashige wanka
Tashirya cikin Riga da wondo Pakistan tafito tayi dining taga anty shafa a dining din taje zauna sukaci abin suna dan taba hirarsu
Sosai shafa taji dadin abinci sakwarace da miyar egusi da naman rago
Anty tayi kasancewar yau itace da daddy tayi mishi. Special food haka
****
Al'amin na isa gidanshi yayi parking yafito abinshi cikin zafin rai da kunar zuciya
Su aymana suna ganinshi sukatashi sannu da dawowa
Ya daga musu hanu ya isa bayason surutu
Suhaila tace to , suka nemi guri suka zauna aymana tace yau kuma kowa yataboshi
Suhaila tace wayasan mishi
Nan kowacce tacigaba da abinda yake gabanta
Prince kuwa bayan yafito daga wanka yasa kaya marasa nauyi saboda zuwa sallah magriba
Yana fitowa yawuce mosque abinshi
****
Daddy kwance kan cinyar anty a bedroom din shi kusan karfe goma nadare
Yana lissafa mata abubuwan da yamallakane da kadarorinsa
Saida yagama zaiyyana mata komai anty tace allah yakara daukaka ya sa kafihaka alhajina Ameen Ameen maryam
Can tace amma Alhaji kagama lissafomin banji kace kanada gidan marayuba kokuma malarantun islamiyya da daisauran aikin lada
Daddy yayi shiru yace bantaba wannan tunaninba maryam amma yanzu ya kikeso ayi
Tace yauwa alhajina inason acikin filayenka da kake dasu a akowani state mezai hana ka ware kwaya daddaya a Gina maka gidan marayu
Sannan kabi anguwan wannin talakawa kagina musu masallatai da su Bohol da fanfuna
Nasan dan kayi wannan na komai bane acikin arzikin da Allah yabaka ko yakace alhajina
Daddy yatashi daga kwanciyar dayake yace hakane maryam insha Allahu zakiji amfara duk aiyukan nan dakika lissafa nan ba da dewaba
Anty tace kai amma naji Sosai daka dauki shawarata alhajina allah yakara budi
Dad yace ameen daddy yadade Yana nazarin maganar anty yagane kuskurensa sosai yagodewa Allah dayabashi anty a matsayin mata
****
Shafa tana zaune a part din su tana karatun waec su nazeefa kuma kallo saboda suna hutun semester
Sai maryam tashigo falonsu nazeefa da sallamarta
Afnan tajuyo taga maryamce tace meyakawoki nan kekuma
Maryam batareda ta kallesuba kafinma tayi magana shafa'atu tace a a maryam ya akayi maryam tace anty assignments zanyi nazo ki aramin laptop dinki danyi design din page din zansaka water mark ne
Shafa tace OK badamuwa bara na dauko miki ta tashi zata dauko mata sai nazeefa ta tareta tace mezakiyi shafa
Shafa tace zandauko mata laptop dina ne kobakuji bane
Afnan tace baza a bayarba a Ba ubanta tane yasai laptop dinba
Shafa ranta yabaci tace yasakuke Abu kaman wasu kananan yarane
Afnan tace shafa akan wannan agolar kike mana rashin kunya
Shafa tace nayi din kuma nagani data shigo gurina tazo bagurinku ballantana kuce baza a bayar ba nawane bana kuba
Shafa batayi aune aune ba taji saukar mari a fuskarta tas
Tayi saurin rike gurin takalli me marin ummynsuce
Hajiya zabbau tace wawiyar yarinya Mara kishin kai
Yanzu saboda wata yar matsiyatar kikewa yayunki rashin kunya wato bazakiji magana ba ko
Shafa tajuya ta kalli inda maryam ketsaye taga bata gurin
Ran shafa yabaci sosai tawuce dakinta cikin fushi tana jiran daddy ya dawo
Maryam kuwa ranta yagama baci tayi alkawarin bazata sake tambayar komaiba saboda gudun fituna
***
Washagari Yakama asabar dad yana zaune ya falonsa shafa tazo tazauna tagaisheshi
Ya amsa yace shafa'atu ya akayi ne tabashi labarin abinda yafaru dad yace jeki kiraminsu nazeefan
Ta tashi taje kiransu
DAGASH ne yashi cikin kananun kaya kamar kullum ya gaida dad ya amsa yace son ya akayi ne maganar ayyukan nan amfara ko
dagash ya yace ai tunda kabani umarni nasa akafara aikin a kowani state kuma zasu gama lokacin da aka diba musu
Amma dad wai meyasa kake wasting dukiyarka hakane kwata kwata bangane makaba dad
Dad tayi murmushi irin nasu namanya yace Al'aminu kenan kaima zaka fahimta amma sai nangaba
Dagash ya daga kafadu irin alright allah yakaimu lakacin dazaka fahimtar dani din
Mum ce tashigo dagash yagaisheta tace son ya duk karame ne meyake damunka ne
Yace mom yanzu dai yunwa nakeji break fast please tahado mai komai atirai
Yace mom nifa yau kezakibani
Dad yayi murmushi yace ai daman kasaba yau yanshagwabar suna kusa kenan
Mom murmushi tayi tace yazanyi wai ace mutum yagirma besan yagirma ba
Da yaranka zanji koda kai dad dai dariya yake musu
Shidai bece komaiba yadauko tiren abinci tazauna gaban mummy tafara feeding dinsa su nazeefa da afnan ne suka shigo
Suka zauna gaban daddy
Daddy yahada rai Ashe bakuda kunya Ashe haka kuke zakusa kanwarku agaba kuna zagi harda ce mata gidan ubanta bane
Ku kinsan yadda naku rayuwar zata kasance nan gaba idan akace yaubani kuma ba dan uwan naku dakuke takama dashi
Yanuna Dagash
Yace Ashe haka kuke Karin yayi wata maganar
Hajiya zabbau ta fito daga part dinta
Tace amma alhaji aibahaka ake shariyaba ita munafukar agolar data fada maka karya da gaskiya har kazo kahau yaranka dafada ai ba Gaskiya tafada dan ba haka akayiba
Daddy yace to ita wacce kike zargin ba ita tafada
Mehankalin yarkice tafada komai yakalli shafa yace jeki kira min maryam
Shafa maryam suka fito maryam sanye da katon hijabi harkasa ya balain mata kyau tayi shirin zuwa islamyya ne
Ta zauna tagaida daddy ya amsa tagaida mum ta amsa bayabo ba fallasa tagaida uban gayyar wato dagash
Sai alokacin yadago ido yakalleta gabanshi ne yasake fadauwa wai meyasa idan yaga chick little girl din nan sai yasamu wannan feelings din ne
Ya watsama harara Wanda ita batamasan yanayiba
Dad yace maryam kiyi hakuri kinji da abinda yan uwanki suka miki inafatan baki fada wa antynki ba maryam tayi murmushi tace la haba daddy ai ba komai Yakamata anayi nafada wa anty ba daddy bata saniba
Hajiya zabbau ta dau salati tace mezangani
Wato damuwarka ma kar uwarta tasani
[22/06, 6:35 PM] SIS UMMY: Daddy ya kalleta cikin takaici bayason fada mata maganganu a gaban yara ne shiyasa yake kyaleta
Yace wa maryam allah yamiki albarka kinji tace amin daddy ya kalli shafa yace shafa'atu allah ya miki albarka yasa kidure da da halinki nagari tace amin daddy
Ya kalli dagash da mom take ta bashi break yace Son tunda ba inda zakaje inaso kakai maryam tazabi laptop da waya
Kowanne ta dauka abata da resit
Yace shafa'atu idan bakya komai kuje tare kema kicanzo wayarki daga nan
Shafa tace to daddy mungode
Maryam tayi godiya shafa taja hanun maryam suka fita
Gudun kar ayi irinta ranar yaya ya tafi yabar maryam gwamma suje gurin motar sujirashi
Sai da yagama yangarshi yagama Jan ajinsa kafin yatashi yayi waje cike da takaici abinda yasa daddy yake yawan hadashi a lamarin wannan Mara kunyar yarinyar ba
Shafa tabude gaba tashiga maryam tabude gidan baya tashiga abinta
Yana zuwa ya kalli maryam ta madubi yace ina zanje dake da wannan labulen haka
.maryam duk da tasan da ita yakeyi hakan baisa tadago ido ta kalleshi ba
Next page
Naji dadin adduarku akaina kuma allah ya karba dan nasamu lafiya nagode da kaunarku agareni allah yabar zumunci
Your comments is needed fans
More comment more typing
*Signed by ummu afan* π»
[26/06, 11:55 AM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
ππππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUSE WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
I DEDICATE THIS PAGE TO YOU AGAIN SIS FATIMA SUNISI SANATA (TEEMERH MAKEOVER)
GASKIYA INA ALFAHARI DAKE OVER SIS ALLAH YABAR ZUMUNCI INAJIN DADIN NICE COMMENT DINKI KEEP IT UP β€
_π‘AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ π‘
Ina matukar alfahari da comment dinku gaskiya sosai da sosai
Comment harda read more π€much love to your love and care
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 1β£3β£
Dagash ganin yana mata Magana tayi shiru yace ke wai badake nake ba ne
Shafa'atu taga alamun horn din mota tamaida hankalinta kan motar dake shigowa
akuwa bakuwar mota suka gani
Wazatagani wadanda sukafito da ga motar ne yasata fatinciki
Ta kalli yaya al'amin tace yaya ga friend dina sunzo
Yace to mezan miki tayi shiru tunda tasan amsar tafito tazagayo ta gurin maryam tabude tace maryam ga mayafina tunda duguwar rigace ajikin ki
Maryam tadago kai tace a a anty meyasa zansa wannan kuma tace au bakiji me yaya yace ba
Maryam tace au yayi maganane banjiba
Shafa hankalinta yatashi dan karyace marayam tamishi rashin kunya
Nan shafa ta maimaita mata mata abinda yace
Maryam tace OK banji bane ai Dana koma ciki na dauko wani
Shafa tace a a basai kinkomaba ganawa kuje kudawo nayi bakine kizabo min wayar mekyau kawai
Maryam tace OK shafa tabata mayafin takarba ta manta kanta ba dankwali sai gashinta da takama shi da riborm gashi har yawuce gadon bayanta
Shafa taji mamakin gashi irin na maryam dan bata taba ganin gashinta
Tadauka kullum acucine takesawa
Shafa tace maryam saikin koma gaba yaya bazai yarda kina baya yana Jan mota ba
Maryam tayi murmushi tace to anty zankoma
Maryam tafito tabude gidan gaba tashiga takauda kanta tana kallon window nagefenta
Dagash kuwa saidaya gama wayarsa Sannan ya tashi motar sukatafi
Tafiya yake a hankali yana sauraran wakar Akon
Suna gurin dagash yayi parking nan da nan maikata suka fara zuwa kwasar gaisuwa
Agurin megidansu
amma babu Wanda dagash yadaga ido ya kalla bare ya amsa mishi
Takaici Yakama maryam tace yanzu wannan wulakancin dame yayi kama haka harda wadanda suka girmeshi amma yake wulakanta dan Adam haka
amma insha Allah anan sai ta nuna mishi bakowa zaiyiwa haka yabishi ba
Tana zaune a motar tacigaba da zama taki fitowa shikuma Dagash yake waiwayowa
Dagash yashiga ciki anbashi masauki yazauna amma yarinyar bata fitoba wai metake nufine
Kojiratake yace tafito aikuwa saidai sukwana anan
Maryam takira daya Daga cikin maaikatan tabashi sako yazabo mata latest phone da akeyayai yanzu guda biyu iri daya
Sai kuma laptop mekyau shima yace angama ranki Dade kozakishiga kizaba da kanki
Maryam tace karkadamu kazabo min kawai
Ba afi minti goma ba saigashi yakawo mata su daga kasan manyan bwayoyine shima laptop din kansa abin kallo ne
Tayi godiya yatafi wayar yamata kyau sosai iridaya Dana shafa tasa aka kawo musu
Dagash yagaji dazama cikin zafin rai yataso yafito yabude kofar motar gefen da Maryam yace kewai dan zaikarasa zagin kome yatuna kuma yafasa zaginta oho
Yace ni sa'an wasankine kokuma jirakike nace kifito saboda kin isa kome
Maryam tafito tace haba yaya kai meyasa kullum acikin zafin rai da nuna kowa banza ne a idonka
Duk girman mutum bai isa ka amsa gaisuwarsaba
Ninadauka wa mu yara kakewa Ashe harda wadanda suka girmeka
Gaskiya naji kunya sosai shiya naji bazan iya jerawa dakai ace tare muke ba a yi tunanin halinmu daya
Tashin hankali ran maza yabaci wai yau shine mace zatace tana jinkunyar jerawa dashi macen ma karamar yarinya
Cikin tsanin bacin rai yafigeta har mayafinta yafadi saboda santsin gashinta ga yawa amma baibita kan mayafinba
Maryam cikin tashin hankali kanta ba dan kwali gashi duguwar rigar dake jikinta yabude daga wuya sosai har ana iya hango lafiyayyun dukiyar fulaninta dasuka hade da juna
Yashigo maryam tace dan allah yaya kayi hakuri dan allah wallahi bazansakeba
Dagash yajuyo yaga abinda yasa takebashi hakuri haka da wuri
Maryam hartafara kuka ita damuwarta ma jikinta ne taya zatakoma gida a haka mezatace wa anty idan taganta a haka
Dagash besan sanda yataka burki akan titiba
Saboda ganin surar dabe taba ganiba
Cikin tashin hankali ya dafe Kanshi
Yafara maganar zuci yace wai mehakan yake nufi
Karamar yarinyar kaman wannan ta mallaki abinda manyan mata baigansu atare dasuba
Kukanta ne yadawo dashi daga duniyar tunin da yafada ga shi hada wani uban go slow a hanya
Sai ya ankara ya ja motar sukayi baitsaya koina ba sai wani boutique dinsa yashiga da kanshi yadauko mayafi babba mekyau sosai shibai tsaya duba colour ba yadauko
Yashiga motar ta saka kanta acikin cinyo tana kuka
Cikin tsawa yace enough malama wannan kukan naki yacika min kunne
Tadago daniyar tasake bashi hakuri saitaga yana miko mata mayafi cikin farinciki ta karba
Yayi tsaki yace ashe rashin kunyar nakarya itadai bata kulashiba tunda tarufe jikinta ai shikenan
abinda yabashi mamaki duk kukan datayi baisa idonta yacanza launi ba
Har yanzu sunan kaman madara dan haske
Suna isa gida tafito a motar takwashe kayanta tabar mishi motar abude
Yace ke zonan kotasan allah yayi mutum
Cikin mamaki dagash OK munzo gidako zakishigo hanuna
Itakuwa maryam tayi alkwarin bazata sake shiga motar Dagash ba
***
Bayan wata uku soyayya tsakanin alhaji dan asabe da maman rahama abin ba ace komai har antsaida ranar aure nan sati daya za adaura auren
Mum din zayyad bakaramin hauka tayiba amma wannan karon alhaji dan asabe yayi nisa baya jin kira
Sosai ake shirye shirye biki
Maryam da rahma sunji dadi sosai kasanewarsu gari daya
Anyi bikin maman rahama da dad din zayyad ta tare agidanta
Sai dai muce allah yabada zaman lafiya
***
Shekaru sunja dan shafa'atu tana nan a university level two
Yayinda maryam kuwa da rahma suna SS3 karatu yafara zafi sosai
Dagash kuwa abun tunbaya damunshi yanzu yafara damunshi yanzu
Wai meye dalilin daya yana yawan tunanin wannan maraya kunyar yarinyar ne
Yarasa meke damunsa
Aymana da suhaila kuwa haryanzu ba cikin kobatan wata bawacce ta tabayi
Kuma dukansu zugan kawayene acewarsu haihuwa da wuri zaisa mijin ya tsanesu
Gashi kowacce ya bude mata tafkeken boutique yanzu sunzama manyan mata
Business kawai suka agaba ba abinda yadamesu
Komai suke so suna samu
*****
Daddy zaune suna cin abinci da anty sai anty ta tashi dasauri tayi bathroom
aikuwa daddy yabi bayanta yaga amai take dakanshi ya taimaka mata tashirya yace suje asibiti
Suna zuwa kuwa gwajin farko akamishi albishir da cikin anty
Daddy yaji dadi sosai saikace ba ataba mishi haiuwa ba
Bayan sundowa gida yace Yakama ta muje umara gabakidayan mu mutanen gidan
Dan nagodewa allah akan ni'imar daya karamin
Anty tayi murmushi batace komai ba
Duk ilahirin mutanen gidan kaf daddy yasa akamusu visa
Mum din al'amin itadai abin mamaki yakebata canjawar mijinta lokaci daya haka
Maryam tace anty yanzu ni yazakuyi dani kenan saurafa sati daya mufara exam's
Anty tace ai daddynki yagama komai maryam gidan yayanku zaki koma har saboda jarabawar Ku
Maryam ta zumbura baki tace kai anty kinsan allah matan shi basu da kirki
Kawai kubarni naje gidansu rahma
Anty tayi murmushi yace maryam kenan ai nan alhaji yazaba miki kinga bazaki ce mishi bazakijeba ko
Maryam tace anty kuma zaku dade a can ko
Anty tace a a tunda naji yace fa zamukai two months a can
Maryam ta gwalo ido tace Kai yanzu wata biyu zanyi banganki ba
Anty tayi murmushi tace karkidamu kinga ke exam zakuyi idan kuma bakyason zama kedai a gurin yayan naku zan fasa tafiyar sai muzauna
Maryam tayi murmushi tace a a anty na karki damu allah yadawo daku lafiya
Kuma kimin addua allah yacika min burina nazama BARRISTER MARYAM insha Allah
anty tayi murmushi tace maryam ai kullum cikin addua nake miki insha Allah zaki barrister
Maryam ta rungume anty tana me alfahari da ita
Next page
Your comments is needed fans
More comments more typing
*Signed by ummu afan*π»
[26/06, 11:55 AM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
ππππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
I DEDICATE THIS PAGE TO YOU SIS FATIMA ZAHRA β€GASKIYA INA ALFAHARI DAKE OVER SIS ALLAH YABAR ZUMUNCI INAJIN DADIN NICE COMMENT DINKIπ§‘ KEEP IT UP β€
_π‘AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ π‘
Jinjina gareki sis ummy allah yasaka da alkairi kina kokari wajen ganin komai yatafi dai dai allah yabar zumunci sosaiβ€β€β€
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 1β£4β£TO1β£6β£
Yaune girgin su daddy zai daga karfe goma nadare zasu tashi
Shiyasa tunsafe suke ta shirye shirye
Dagash yana dakin mom dinsa yace yanzu mummy shikenan haka zanyi ta rayuwa da snack da juice ba cin abinci
Mummy tayi murmushi tace to kozaka shirya mutafi ainima basan barinka nakeba
Kawai dan dai kaizaka cigaba da kula da business dinku ne tunda daddynka yadauki hutun almost two months zamuyi a saudiya
Kuma ina ganin ni daga can ma zanyi gida naga nawa yan uwan
Al'amin yace gaskiya zanzo nima nan da sati biyu
Da banzan iya zaman wahala ba mom
Mummy tace shikenan ma saikazo din yanzu dai ga danbun kaji da danbun nama duk namaka
Sai kuma snacks Dagash yace that's my mom allah yakara miki lafiya mum
Mum tayi murmushi tace amin Son
Mummy tazauna jikin gadonta fuskarta yacanja
Tarike hanun al'amin tana son yin magana
Al'amin yace lafiya kuwa mom meyasa fuskarki yacanja
Mom taja nunfashi tace Kaine son wallahi nayi tunanin auren dakayi zaisa kacanja kadaina shan giya kadaina Neman mata amma bako daya son
Al'amin yace oh my God mom kicigaba da min addua mummy zan daina kodanke ma tunda bakyaso
amma fa mummy wannan yarinyar nan dakikasani itace dai Vicky bana naman mata barkate mom
Mummy ranta yabaci tace yanzu son har ka dubeni kace wai har yanzu wannan wacce nasanine baka canja wataba
Anfada maka Abu mai kyau kakeyi ne
Wannan halin naka yana daga cikin abinda yasa nakeson tafiyan nan saboda nayi ma addua a kaba dakin allah nayi addua sosai allah yashirya min kai
Al'amin yace mummy insha Allah adduarki takusa karbuwa
Zandaina mom amma kinsan sai a hankali
Mummy tace to allah yasa kadaina din
Gashi mahaifinka yadauki son duniya ya daura maka baya iya ganin kayi badai dai ba yama magana
al'amin yayi murmushi yace ai ina alfahari daku a matsayin iyaye mom allah yadawo mundaku lafiya
Mum tace amin amin son
**
Maryam tagama shirya wa anty kayanta tsaf
Itama tashirya nata akwati biyu tadeba
Anty tace yauwa maryam kingama to zonan
Maryam taje kusa da anty tazauna
Anty tace kinga dai gidan dazakije maryam duk ba sa'anki dan allah kimusu biyayya karki rainasu idan sunsaki Abu kiyi kinji ko
Sannann kuma kikama kanki dan yayanki ne amma fa ba muharraminki bane
Kinajina ko maryam tace inaji anty na
anty tace allah yamiki albarka maryam tace amin amin antyna
***
Su shafa'atu kuwa suma sunata shirye shiryen su kowacce tagama shirya kayanta Hajiya zabbau baki harkunne
Za'ayi tafiya gabakidaya family ba barmata 'ya'ya kogudayaba
Inba asiya ba itakuwa asiya suna India da mijinta ma
Sun gama hada komai suka fiffito falo
Dagash yafito da kayan mummynsa daga part dinta
Karfe Tara nadare kowa yashiga mota zuwa air port
Al'amin shiyake jan mummynshi da daddy
Anty kuma suna motar driver itada shafa da Maryam
Hajiya zabbau ma su uku da ita da nazeefa da afnan
Jirgin su yatashi karfe goma dai dai maryam batasan zatayi kuka ba saida taga da gaske ne fa anty ta tafi
Al'amin takaicin kukan yakamashi yace ke wai wace irin dabbar yarinyace
Ke yarinyar goyece dan anyi tafiya zakikama yiwa mutane kuka
Maryam kuwa ba abinda tafara tunawa sai labarin da shafa'atu tabata akan yayan nasu idan mummy zatayi tafiya
Aikuwa batasan lokacin datafashe da dariyaba sosai
Takaici Yakama al'amin ya danko ta yace ke ubanme mekikewa dariya
Maryam taji matsa tace badakai nakeyiba
Natuna da wani kato ne kaman kai idan maman shi zatayi tafiya
Yashiga damuwa kenan wani lokacinma harkuka yakeyi
Dagash abin yabashi dariya dan yasan dashi takeyi
Take raina mai hankali
Baibari taga dariyar ba saboda bayason raini
Yace oya shiga mota mutafi
Batayi musu ba tashiga
Dagash yadau hanyar gidan shi
Suna isa tabude tafito yana gaba tana binshi abaya suka shiga falon
Aymana kwance kan 3sitter ansha kwalliya cikin matsatstsun Riga da wando dan burge megida
Haka ma suhaila cikin duguwar rigane itama ya matseta sosai
Ganin dagash da Maryam suka hada rai dan ita aymana ma tun farkon ganinta da Maryam bata mata ba bata sake mata saboda kishin kyau da allah yamata
Suhaila tace sannu da zuwa bai amsaba ya wuce abinshi aymana tagaisheshi bai amsa ba
Maryam tasamu daya daga cikin kujerun falon tazauna abinta tace sannunku anty
Aymana tace kekuma suwaye anty naki Suhaila tace tambayeta dai
Suhaila tace towaima meyakawoki gidan nan ba dai dagaske bane anan zaki zauna ko
Maryam batace komai murmushi kawai ta tashi suka ga tayi part din dagash
Aykuwa Aymana tace kutuman uba wabaki daman shiga wajen mijinmun
Maryam tadafa goshi tace ya ilahi wallahi bana son magana kubarni mana please
Jin haya niyar aymana dagash yafito yaga sunsa maryam a tsakiya
Ya hade rai yace kukuma lafiya
Cikin muryarta medadi tace yaya bacci nakeji kuma kayana yana bayan motarka kuma bansan inda zan kwanta
Baka nunamin dakina ba takarasa maganar cikin shagwaba
Batare da yayi maganaba ya komaciki yadauko key din motar yace gashi maza kije
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 18