sukaga zugar abokansu sun tahowa tashi sukayi suka karbesu nan danan zayyad masu rabon take away sukafara
Komai na girma akayi
Shafa'atu takira wayar daddy yadaga yace shafa'atu ya akayi tace Daddy junior yana ta kuka
Daddy yace asha fito gamunan kofar gida kikawa minshi
Nakaiwa mahaifiyarsa
Haka kuwa akayi dadddy ya shiga mota sai gidansu anty
Yanazuwa kuwa akakirata tafi cikin doguwar hijabinta kamar yadda tasaba yace maryam shine kotakan Dana bakyayi kinmanta dashi
Anty tace Haba ya zanyi namanta da duk wani abunda yashafeka a rayuwa ina sanedashi
Ai nasan yana hanun da bazai wahala ba koba agun shafa'atu ka karboshiba
Daddy yayi murmushi yace kwarai na yarda yana ranki tasa hanu ta karbe lil al'amin daga hanun daddy
Yace maryam kiyafemin kaddarace wacce bamu isa mukauce mataba
Zabbau ta cuceni cutar da bazan taba maida kamanta ba
Asarar mace kamarki ai babban abune a rayuwar kowane magidanci
Haka kuma samun ki sa ace babban a rayuwa
Anty bazata iya tsayawa jin maganganun daddy ba yasa tashige cikin gida tana kuka
Shima daddy mota yafada yatayar Allah ne kawai yakaishi gida
Anty nashiga yaya aliya tayi saurin karbar lil al'amin ganin yadda anty tashigo a rude
Tace maryam lafiya anty tace yaya aliya nayi rashin miji da bazan taba maida kamarsaba
alhaji yakaunaceni ya nuna min kauna tashi daya sunrabamu rabu ta har abada
Dan ina mai tabbatar miki da ace saki daya yamin nidakaina zankoma gidana
Amma kash ya yanke alakar my gaba daya bazan taba samun wadda zai nuna min kauna kamarshi ba
Gani sukayi hanun inna na motsi alamun magana takeson yi
Washagari misali karfe Tara safe yaya Abdul yatafi gurin aikinsa wato gadinsa
Yaje yakarba agurin abokin aikin nasa
Yana zaune Al'amin yashigo da motarsa cikin asibitin yana tiyata ne karfe goma shiyasa yashigo amma dabazai shigo ba
Ganin ya Abdul a gate Al'amin bai karasa parking dinba yafito yace Haba malam Abdul mekadawo nan gurin kuma ai kafi karfin nan kuma yanzu
Kayi school ne yaya Abdul yace ai tunda daga secondary school bankaraba
Yallabai kabarni kawai wallahi ina jin dadin aikina
Dagash yace kajirani zanfito daga tiyata by 12 pm zamuyi magana amma banason kacigaba da budewa mutane gate
Yadauki mukullin office din shi yace gashi kaje office kajirani
Yace ina shi malam haladun yacigaba da aikin kawai Kafin asamo wani
***
Bayan kwana biyu Alhaji imam yagama komai na tafiyan su inna da malam jinya
Anty da yaya aliya da yaya Abdul dasu za atafi
Yayin da maryam zatabi mahaifinta zuwa libiya
Dansuma sunji komai yanzu maryam kawai suke dokin gani barinma hajiyarsu mummyn dagash
Tana ta Allah Allah taga jinin imam dinta
****
Hajiyar dagash ne zaune kan kujerarta da carbi a hanunta tana lazumi sai daddy yashigo
Yaga tana ta aikin tunanin nata nafama yace
Wai bazaki daina wannan damuwarba Aisha yakikeson nayi ne narasa maryam
Kema kina son kisawa kanki damuwa
Mummyn al'amin tace to yakakeson nayi alhaji dawani ido zan kalli maryam harta yafemin
Alhaji yace wata maryam din ai maryam tadade da yafe miki ai bata da ruko kedai Yakama ta idansun dawo ki je hargida kisake Neman afuwa
Mummyn tace inasukaje daddy yamata bayani komai tace hakan ma Yayi
To ina maryam akawo min 'yata tazauna dani koda na yan kwanakine
Wallahi alhaji tunfarkon danaga maryam naji tashiga raina kawai dai naringa karyata hakan ne saboda tazo a matsayin yar talakawa
Daddy Yayi murmushi yace tashi kikawo min coffee zanshiga ciki
Yatashi yahaura samanshi itakanta mummy mijin nata yabata tausayi tabbas yana son matarshi Dan gashi harda wasu raman wahala jinyar zuciya sukafito mashi
****
Dagash kwance cikin falonsa shikadai yana tunanin
Maryam wai yaushe ne za abashi dama yaje yaganta yaushe ne zasu bashi matarshi
Daddynsa king yace karyaje gareta a yanzu harsai ta huce shin yaushe ne maryam dinsa zata huce ta fahimceshi
Shidin masoyinta ne nagaskiya
Kai ina bazai iya watannin da akaniba mishi Kafin yagantaba saboda gone zaitafi libiya
Next page
Your comments is needed fan
*Signed by ummu afan* π»
[15/07, 1:14 PM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
ππππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest,
Dedicated to lovely son afan
Allah ya albarkaci rayuwarka my son much care ππππππ
Talle talle talle ππΌππΌππΌ
*KAI NE SILA*
Shahararren novel dake zuwa muku daga alkalamin *sis sameehat*
Marubuciyar littatafan soyayya domin nishadinku
Karkusake a Baku labari yanan a social media masu bukatar littafin *KAINE SILA*
sumata magana da wannan number din ta watspp 08033975309
_π‘AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ π‘
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 6β£7β£to7β£0β£
Maryam kwance kan cinyar kakanta hajiyar su mummy kenan
Tunda maryam tazo gidan tazama yar gatan kowa
Kowa na cikin gidan jida maryam yake kaman su lasheta
Barinma kakarta hajiyarsu mummy ai tana matukar kaunar maryam sosai tunda ta ganta kullum suna tare
Haka alhaji nura babban yayan su mummy ma shima yana nunawa maryam kulawa sosai yayinda matarshi hajiya mami itama bakaramin gatantawa maryam takeba
Maryam dai tazama yar lelen kowa shiyasa shagwaba yakaru
Maryam ta kalli kakarta tace hajiya ina da tambaya wai Ku asalinku larabawane
Hajiya tayi murmushi tace sosai kuwa maryam asalin yan saudiya kuwa Neman kudi yafito da kakanku kasar libiya
Maryam tayi murmushi tace haba
ai dagani ba tambaya hakan ya nuna ma
Hajiya tayi murmushi tace meya nuna miki hakan maryam tayi murmushi tace caf kinganki kuwa hajiya kintsufa amma har yanzu kyanki nanan
Hajiya tayi murmushi tace kayya maryam ina wani kyau to mamanki ta Aisha kuma kice mata me itada ubanki ai duk sun kwashe kyan
Maryam tayi dariya tace kai hajiya wannan ai zagine dawayo sukayi dariya gaba dayansu
Ameelat tashigo agajiye tazauna sharaf gaban su
Maryam tace yan makaranta andawo ameelat tace wallahi kinsan sabon shiga wallahi gaskiya university yana da wuya
Maryam tace a a fa banyardaba wallahi sai dai kekikeson yamiki wahala
Ameelat tace a zakice haka mana tunda ke kinsamu kinyi aurenki da mijinki kinga kuwa koyanzu kika koma school wallahi bazai baki wahalaba saboda bakida fargabar komai a gabanki
Maryam ta watsa mata harara tace zakifara ko ameelat tace to karya akayi ba matar auren baceke
Hajiya tace to zaku farako ameelat tace rabuda da ita hajiya bata son gaskiya
Tasamu handsome guy kaman brother Al'amin tadinga mana yanga wallahi tanasonshi
Tana fada haka tadauki jakarta ta gudu
Maryam tabita da gudu aguje suka shiga ciki da gudu
Ameelat tashige dakinta ta kulle kofar
Maryam tace wallahi zaki fito kisameni zanyi maganinki
Ameelat yar alhaji nura ce ta hudu
a mata subiyu suka rage da ameelat da kanwarta suhaima meshekaru takwas
Ameelat zasuyi sa'oi da maryam kuma itama yanzu take shekarar farko a university ameelat takasance yarinya me hankali sosai
Bata da burin da yawuce tayi aure kafin tacigaba da karatu sai dai kash abbanta yaki yace sai taje two hundred level kafin ya aurar da ita
Tunda maryam tazo gidan ameelat tasamu kawa kuma yar uwa tare suke komai
Ameelat takancewa Maryam wallahi kinyi sa'ar miji yar uwa samun mutum kaman brother ai sai an tona
Maryam zata hada tace batason hirarshi shiyasa abin yazama tsokana a tsakaninsu
Bayan sati biyu
Dagash zaune a falon daddy yana rokarsa akan yabarshi yaje libiya daddy yace bayanzu bafa son
Kasake hakuri sai lolacin daya dace kaje zansanar dakai kaje kaga matarka
Mummy tace to alhaji muje tare mana ya rakani
Daddy yace kedai kawai kice zaki min wayo kikai danki yaga matarsa
Mummy tayi murmushi tace kodaya nidai banason tafiya nikadaine
.daddy yace shikenan badamuwa kuje din
amma danaso sai ita yarinyar tagama saukowa daga fushin nata kinsanfa abinda ciwo sosai
Mummy tace hakane kam amma ai gwamma yaje can suhadu yabata hakuri
Nan dai dagash yaji dadin barinshi da akayi sutafi da mummy
Mummy tace saikaje kashiraya mana komai nanda jibi sai mutafi dagash yace that's my mom
Dadddy Yayi murmushi yace kai dai bazaka girma ba tsofai tsofai dakai karinga shagwaba
Mummy tace aifa ai yanzu lil al'amin Yakama ta kabarwa shagwabar haka
Dagash yace ai harkintuna min boy
Insha Allah harcan zanje naduba su antyn
Daddy dai baice komai ba
Direct office dinshi yawuce ya bar komai hanun zayyad
Zayyad yace wai dagaske ne zakabi maryam tokabari akawo maka itamana
Dagash yace caf waya fada zan iya hakurin harsai lokacin da akaga damar kawomin mata wallahi bazan iyaba
Tunda aini ba dutsebane ina bukatar matata
Kusadani
Zayyad yace to yanzu kokaje ma ai dagawa kanka hankali zakayi kawai Dan idan kana ganinta damuwar taka zatafi yawa
Dagash yace wayafada maka sata agaba zanyi ina kallo tana halal dina intsaya kallonta haka kawai
Zayyad yace amma dakacika marakunya dagash yayi murmushi dake kara masa kyau da kwarjini
Yace zancen kakeso wayasanima komudawo da Dan libiya
Zayyad yace ai zaka rina wallahi kai ba
Sai a hankali Allah yasa taki bada hadin kai muga ta rashin kunyarka
Murmushi kawai dagash yayi kafin ya dialing number din wani abokin business dinshi
Yanagama wayar zayyad ya kalleshi yace muje gidana mana ko rahma tana da sako gurin kawarta
Dagash yace kudai dason saka yara su raina mutum
Nifa kaga inason maryam ko tobazan taba bari ta rainaniba saboda banason raini
Zayyad yace lalle bakasan soyayya ba ina ruwanta da raini
Niyanzu kaga rahama sai yadda tayi dani wallahi binta nakeyi kamar rakumi da akala
Kuma kaima bazaka gane hakanba sai randa katare dataka amaryar ka kwashi zumarta da kyau kashiga hanunta
Dan wallahi auran yaran nan alkairi babba atare damu Dan yanzu gaskiya nasamu nutsuwa ban nemi komai daga matata na rasaba
Dagash yace lalle nayarda kayi nisa a soyayya zayyad wannan irin zance haka
Wai ina Faisal ne yace caf aina kwana banganshiba
Dagash yace barin kira number dinshi muji
Yayi ta ringing ba adagaba saida yakusan tsinkewa aka daga
Faisal ne yace wai kai Dan iska mutum yana hutawarsa kadameni da kira haka
Zayyad ya karbi wayar yace ato fada masadai wai tambayata yake ina kakene kwana biyu
Shine nace nima banganka ba Dan idan nafada mai amarya ce arikeka zai tsaya min wasu maganganune nasu na gauraye
Faisal yace ina dagash din zayyad yace gashi yamika wa dagash wayar dagash ya watsawa zayyad banzan kallo yace duk kugama
Badai iskanci bane abin naku duk kugama wai damma nima inada matar
Zayyad yayi murmushi suka gamawa Faisal yabawa dagash wayarsa yace mukarasa ko
Dagash baiyi maganaba yaje sukashiga motar zayyad suka nufi gidan zayyad
Mortar zayyad na parking rahama tafito cikin kwalliya tatsaya tana jiran karasowarshi shima ganin matarshi ya manta da dagash suke tare motar yabude yafita yanufeta itama karasowa tayi tarumgemeshi cak zayyad ya dauketa zuwa cikin gida
Dagash ya rintse ido yace God help me tare da dafa goshinsa
Yace duk abinda kuke kucigaba zanrama shiwanyancan Dan iskar nakirashi wai yazan katse wa mutum jindadinsa
Shikuma wannan yadauketa suka shige
Key din motarma a Jiki zayyad yabari saboda ya rude ganin kwalliyar matarshi
Murmushi dagash yayi yatada motar yayi gaba abinsa yace kazo ka karbi motarka agida
A ranar yagama musu komai saboda a yadda yakeji bazai iya kai jibin da mummy tace ba
Gaskiya yana cikin wani hali na matukar bukatar matarsa
Gidansu ya koma yace mummy nagama komai jirgin karfe goma zamubi
Mummy ta takalleshi tace haka nace maka ya marairaice yace haba mummy ai dagobe da jibin duk dayane a gurin Allah
Mummy Dan nata yabata tausayi tagane abinda yake damunsa tabbas Dan ta yashiryu da tana kyautata zaton yabar wanann yarinyar Victoria take ko wa
Zatasan yadda zatayi abashi matarsa sudawo gida gudun komawa ruwa
Ta kalleshi tace shikenan Allah yakaimu goben dagash yace Yauwa mummy kokefa
Nazeefa da afnan nesukadawo daga anguwa dagash ya kallesu yace kai kuzonan daga ina afnan tace gurin ummy muke
Dagash ya watsa mata wani banzan kallo ubanwa kuka tambaya dazaku fita
Duk suka rikice dagash yace barin fada kafin nadawo daga tafiya acikin samarinku da kuke Tarawa mutane akofar gida kufitar da na aure
Wallahi kokuma duk nabadaku ga masu gadi kunsan zan iyako suka daga kai dasauri
Yace kutashi Kuban guru guri shashai kawai
Washagari jirgin su dagash da mummy yadaga zuwa libiya
Maryam zaune falon hakiya mami itada ameelat hajiya mami tafito da kula tazauna itama cikin yaranta ta kalli maryam tace Yauwa 'yata gawannan maza cinye kiban kulan inakallonki
Maryam tace Yauwa mamana ta kalli ameelat ta mata gwalo itakuwa ameelat dariyar maryam takeyi Dan kwata kwata talura maryam bata Masan abinda maminta take dirka mataba
Maryam tace zodai muci badan halinkaba ameelat
Ameelat tace wa ni aisaike yargatan mami kedai akace kici nima dai nasan kitchen din zanje nadiba
Hajiya mami tace a munjidai sauki Kofi kidebo mata madara a fridge maisanyi
Ameelat ta tashi tana dariyar mugunta dantasan yadda mutane suke kyan kayan maminta sosai kwararriyace akan harkar maganin mata
Taje tadebo madarar da maminta take nufi
Takawo
Maryam taci iya cinta tace mamina nakoshi
Mami tace daure kikarasa yar mami haka dai maryam take fama dakayan ciye ciye da shayaye shaye Dana wanka
Sosai hajiya mami take gyarata saboda tasan komai dayafaru da ita taji komai agurin mamin dagash
Sosai maryam take ganin canji ajikinta amma saitayi la'akari da canjin rayuwa datasamu ga farincinkin haduwa da danginta ga tsananin soyayyar families dinta suke nuna mata
Jikin yasake tsanain kyau ,laushi ,tsantsi dasheki
Gacikowar datayi ta kotaina kirjinta suncika fam ga diri mezaman kansa
Itadai maryam har tsoro kyan datakeyi yakebata gashi duk sati saitaje
Saloon gyaran gashi itada ameelat sosai maryam tasake gogewa da wayewa sosai
Ameelat na zaune tace tana shiryarwa tace Dan Allah maryam kifito kefa idan kinshiga wanka kamar zakisake fata maryam ta fito tana goge ruwan jikinta tace wai harkingama shiryawane
Ameelat tace mezanjira tunda saloon zamuje ai a can zamuyi makeup din
Maryam tace hakanefa kinga kuwa ai shirina bazaiyi wahalaba
Ameelat ta kalli agogo tace Dan kiyi sauri tunda kinsan daga saloon zamuje gidan anty naila kinsan tace muje ko
Anty naila kanwar su mummy ce dake aure cikin libiya itama akwai autar su mummy kuma mesuna nasreen itama tana aure a cikin garin libiya
Maryam tazabo wani doguwar Riga ja mai adon ash ajinta na duwatsu mai tsadar gaske sosai
Anty nasreen ce ta takawo mata lokacin dataje India da mijin baifi ma satiba
Tasaka tayu Rollin da mayafin batayi kwalliyaba saboda a saloon za a musu
Tadauki bag dinta da high heel dinta ash colour tabalain kyau sosai duk da ba kwalliya komai a fuskarta
Tana fitowa ameelat tace kai maryam kinga yadda kikayi kyau kuwa inama brother nanan yabiya kudin kwalliyar nan
Maryam ta zabga mata harara tace kekuma bakida aiki sai shirme motar ameelat suka nufa maryam tubude tashiga
Ameelat kuma taja motar suka fita
Zuwa saloon anmusu gyaran gashi sosai masu saloon suka yaba da kyan yan matan nan kamar su sacesu bakamar ma maryam tayi balain kyau sosai gashi anmusu makeup tayi kyau sosai
Gaskiya Wanda yasan maryam ada yanzu idan yaganta zaisha wahala kafin yashaidata
Ta hana acika mata makeup a fuska gira kawai aka gyara sai power sai jambaki maroon black kai tayi kyau matuka
Direct gidan anty naila suka wuce
Sunsha hira sosai da ita sai da suka kai kusan karfe takwas nadare kafin nan suka mata sallama tayi tayi sutsaya su kwana amma ameelat taki tace gobe tana da test a school
***
Suna parking ameelat ta fito itakuwa maryam tana chart ne ma abinta saidata gama yangarta kafin ta fito
Tafiya takeyi tana chart a waya tana dariya alamun dai abinda take karantawa yana bata dariya
Batayi tsama niba kawai taci karo da mutum
Wayar tafadi
Tadago da sauri Dan tabada hakuri tasan lefintane suka hada ido hudu itada PRINCE AL'AMIN DAGASH
Next page
Your comment is needed fans
*Signed by ummu afan* π»
[15/07, 1:14 PM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
ππππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
Dedicated this page to masoyan maryam da maryam wato anty da maryam karama ππππ
Talle talle talle ππΌππΌππΌ
*KAI NE SILA*
Shahararren novel dake zuwa muku daga alkalamin *sis sameehat*
Marubuciyar littatafan soyayya domin nishadinku
Karkusake a Baku labari yanan a social media masu bukatar littafin *KAINE SILA*
sumata magana da wannan number din ta watspp 08033975309
_π‘AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ π‘
Much love to you π
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 7β£1β£to7β£5β£
Cikin tsananin mamaki da rudewa maryam take kallon dagash yayin dashikuma dagash ya hade rai kamar baitaba dariyaba Prince sak kawai
Cike da takaici maryam tafasa daukar wayartata dafadi kasa
Takauce zata wuce abinta
Jitayi ya riko hanunta yace dawo nan batareda ya kalletaba
Maryam kuwa tace lafiya malam kasake min hanu mana
Cike da mamaki dagash ya kalleta yaga ba alamun wasa a fuskarta
Yace what mekikace maryam cikin dauriya tace saboda banaso
Cikin tsananin mamaki dagash ke kallonta yace nikikefadawa wannan maganar maryam tace a mana batare da takalleshiba
Saboda yadda zuciyarta kematukar tsoron dagash amma tadaure Dan samawa kanta mutunci
Kallonta yayi tsaf batayi tsammaniba taji bakinsa cikin nata ya hada tayi yinkurin kacewa amma takasa
ameelat ce tabiyo bayanta ganin ta Dade batada shigoba ga mummyn na tambayarta
Ganin abinda kefaruwa yasa ta tsaya turus bata karasaba
A hankali takoma cikin sanda takoma shiru
Mummyn dagash tace ina maryam din ameelat tarasa mezatace wa mummy tace am am am tashiga in ina dai mummy tagane
Ameelat tace tana waya a waje ne
Mummy tace ok hajiya mami tace shine zata tsaya a waje a daran nan
Ameelat tace yanzu zata shigo
Dagash baisaketa ba sai dayaji horn din mota alamun alamun dai motace zatashigo
Sai yasaketa yana saketa maryam tafasheda kuka tayi cikin gida da gudu
Murmushi dagash yayi yadauki wayarta a kasa yayi part din dayake sauka idan yazo
Itakuwa maryam batasan da mutane a falonba tashigo da gudu zatayi dakinsu ganin mummyn dagash yasa tayi turus ga hawaye nan caba caba a fuskarta
Hajiya mami tace a a maryam ya dakuka kuma meyafaru
Karasowa tayi tatsuguna tagaida mummyn da mami
Suka amsa
Mummyn dagash tace zonan yar albarka zogurin mummuynki taji duminki
Maryam batayi musuba ta matsa kusada mummy
Mummy ta rungumeta tace Allah yamiki albarka 'yata kiyafewa mummynki abinda ta aikata abisa rashin sani
Maryam tace bakomai mummy nibantaba rikeki a raina
Mummy tace yauwa yar albarka
Allah yayi miki albarka
Maryam tayi saurin dafa kanta alamun yana mata ciwo mummy tace lafiya tace kaina yake ciwo
Hajiya mami tace subahanalla tashi kije kikwanta yanzu ameela zata kawo miki magani aikuwa maryam batayi musuba Dan daman hakan take bukata
Daki tawuce tafada kan bed dinsu tana kuka ameelat data fito daga wanka tace a a amarya ansha kamshi
Wannan irin soyayya haka lalle kunyi missing dinjunanku tunda abinma ankasa hakuri tundaga waje
Maryam tadago kanta ta watsa wa ameelat harara
Ameelat tace wallahi dariya kike bani kema fa kinasonshi kuma kinawani kaiwa kasuwa
Maryam batace komaiba tana kukanta tashiga bathroom tayi wanka ta fito tashirya cikin sleeping dress dinta fari tas dashi me tsantsi takwanta taja bargo abinta
Ameelat tace yau ba hira kenan tun yanzu zaki kwanta maryam tace bansani
ameelat tayi dariya tace ai shikenan sai nashigo natafi falo
Kowa ya hallara a falon ana al'amin yace inason nabiya ma naga su anty asibiti
Alhaji nura yace ai babanka imam ma yanacan yau kwanansa biyu datafiya dubosu
Ance jikin nasu dasauki sosai
Wai ina my daughter ne Banga tazo wa Abba oyoyo ba
Hajiya mami tace kanta naciwo shine nace taje ta kwanta Abba ashsha tasha magani ko
Ameelat tace a nakaimata dagash yace wani irin magani kikabata ameelat tace panadol
Yace ai bakowani ciwonkai akeshan panadol
Barin dubo jikin nata Abba mummy tace a a son ai tayi bacci kabarta kawai sai gobe kuma
Abba yace a a barshi yadubota ko akwai taimakon da za abata kafin safiya
Hajiyar su tace ikon Allah lalle maryamu yargatan kowace yanzu ciwonkai ne yatada hankalin Ku haka nikam ba abinda yadameni
Ameelat tace caf ai wallahi watakila ma kinfi kowa damuwa duk akayi dariya
Abba yace dubo ta kaji al'amin
Sum sum dagash ya wuce zuwa bedroom din ameelat inda ya tabbatar nan zaiga maryam
Yana shiga yaga dakin da duhu sakamakon kashe wutar dakin da akayi
Sa hanu yayi ya kunna wutar
Idonshi yasauka akan maryam dake bacci cikin nutsuwa tayi kyau sosai
Karasawa yayi yahau gadon yashiga cikin bargon shima
Cikin bacci maryam taji kaman ana lalubata tabude ido zatayi ihu ina ai ya hade bakinsu guri daya
Sai dayayi ra'ayi kafin yasaketa maryam tamaida numfashi tafashe da kuka tace nifa banason irin abinda kakemin banaso
Yanzu idan wani yashigo fa yace suzo mana kawai mekike nufine da ni
Yakike Neman haramta min abinda Allah ya hallatamin ne
Kobakisan kedin halas dinabace
Oyo bakyasona ko to meye dalilin ki nakina
Baki maryam tasake tana kallonshi tace
Tana ganin karfin hali irin na mutumin ne
Yace yes kalleni da kyau nimijinki ne al'amin
Maryam tadafa kai tace ya Allah tasauko daga kan bed din sai batakai ga daga kafaba ta koma tazauna saboda bazata iya tafiya da wadan nan kayan a gaban dagash ba
Ganin haka yasa dagash murmushi tareda lumshe ido
Tace Dan Allah kafita zankwanta al'amin yace idan kikasake cewa nafita anan zan kwana kitashi kawai kizo muyi magana
Maryam ta kalli dakin dakyau ta hango zurmukeken hijabin ameelat me hanu ai kuwa tasura tayi waje
Tasaka tana fita falo taga su Abba ne da sauri takarasa tace sannu da dawowa yace yauwa yar Abba ya kannaki
Murmushi maryam tayi tace nasha magani Abba yayi sauki
Hajiya mami tace a kodai daman na rashin ganin Abba ne
Murmushi alhaji nura yayi yace wai haka maryam
Murmushi kawai tayi
Mummy kuwa maryam nafitowa tasan al'amin ta guduwa saboda a razane tafado falon ganin mutane yasa ta dai daita nutsuwarta
Mummy tace zo yargidan mummy naji kan naki maryam ta matsa kusada mummy
Mummy tace tashi muje ciki 'yata
Dakin da mummy take sauka nan suka shiga
Mummy tace nasan bacci kikeji maryam son ne yadameki kika gudu
Hau kikwanta a gado bazaki komai dakinba zai zo yasameni
Kunya Yakama maryam Dan batayi tunanin mummy taganeba
Murmushi tayi ganin maryam takasa dago kanta
Tace kisaki jikin dani maryam nima mahaifiyarkice kinjiko
Maryam tadaga kai alamun to
Ba musu ta hau takwanta abinta
Next page
Love u love your nice comment
*Signed by ummu afan* π»
[15/07, 1:14 PM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
ππππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
Dedicated to all my fans wadan da nasani da Wanda bansaniba ina alfahari da kaunarku a gareni
Talle talle talle ππΌππΌππΌ
*KAI NE SILA*
Shahararren novel dake zuwa muku daga alkalamin *sis sameehat*
Marubuciyar littatafan soyayya domin nishadinku
Karkusake a Baku labari yanan a social media masu bukatar littafin *KAINE SILA*
sumata magana da wannan number din ta watspp 08033975309
Jinjina agareki Ummy khaleel marubuciyar GIDA DAYA wannan page din naki ne Allah yakara basira ya yaraya zuri'a
π *AL'AMIN
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 18