tsara komai
Wayar daddyn ce tayi kara yadaga yaga babban danshi ne zayyad
Yace a a mutan Spain kodai kana hanya ne zayyad yace yes dad zamu yi landing by two so aturo driver yadauko ni
Daddynshi yace that's my boy ai kanwarka zata zo ta daukoka yace OK dad
Mom dinsu tayi murmushi tace sarkin rigima zai dawo kunnen mu ba sakat kuma
Daddyn suhaila yayi murmishi yace ina ruwanki da rigimarsa dan daddy ne
Tace shima sai yazo yafito da nashi matar a hadasu da yar uwarshi
Daddyn suhaila yace da dai yafi kam
Dakyar mom din suhaila ta rarrasheta akan tayi shiru ai kowacce da salonta zata zauna kuma ba abinda AYMANA zata nuna miki
Kema ai kina da kyau sosai nasan idan har kika aureshi zaisoki fiye da yar uwatasa ma
Murmushi tayi jin abinda uwarta ce hartasami kwarin gwiwa
*****
Zayyad yakira wayar AL'AMIN
alokacin al'amin yashiga wanka sai da yafito yaga miss call yabari idan yagama shiryawa saiya kirashi
Yana kan goge kanshi da hadaddan towel din shi Wanda ba abinda yake fitarwa said kamshi danzan iyacewa al'amin kamshi nature dinshi ne
Wayarce akasake kira da yadauka yana murmushi zayyad yace DAGASH DAGASH DAGASH
AL'AMIN yayi murmushi kawai yace to dan iska zakafara ko
Zayyad yace aikaji matsala ta dakai kaikuma to by 2 pm zanyi landing a airport
AL'AMIN yace waw amma naji dadin dawowarka sosai but yau ina da theater a hospital by two da sai nazo airport din na dauka
Zayyad yace no bad don't worry your self suhaila zatazo ta daukeni
Daganan al'amin baisake cewa komai ba sukayi sallama
Yana gama shirinsa cikin wani suit mai balain kyau sosai dan bazan iya fada muku irin kyau da AL'AMIN yayi ba
Ya dauki farin glass din shi Wanda yakara bayyanar da anihin kyau da Allah yaba al'amin
Yadauko brief case din shi ya rataye yayi waje
******
Bayan sati biyu
Al'amin zaune a office dinshi yana duba patience dinsa bayan aiki yayi sauki ne sai yaji anyi nock yace yes come in
Bakowabane sai zayyad yashigo da sallama
AL'AMIN ya amsa yace kaji dan iska saikace wani mutumin kirki
Sukayi dariya gaba dayansu tare da tafa hanu
Zayyad yace da nabanzane
Zayyad yace wai harkura zatace wa kare maye
Al'amin murmushi kawai yayi Wanda dama baya yin abinda yafi haka
Zayyad yace ango ango amma kasan Allah dasu daddy zasu ji magana ta subarka kazabi mata da kanka
amma suntashi sunhada ka da suhaila da Aymana duk da suhaila kanwatace nasan bata cikin tsarin macen da kake so tazama mallakinka
AL'AMIN yadago yakalleshi kadan yace kaifa kafiye surutu
Zayyad yace ba surubane nasan waye kai nasan irin macen da kadade kana lissafa min
Wanda duk cikin su babu wacce takeda wannan qualities din
DAGASH baice komaiba yaduba wristwatch din shi yace kai yakamata muje muyi lunch fa
Zayyad yace wai har yanzu baka dena komawa gida yin lunch ba bazaka bar mom ta hutaba
DAGASH yace idan nabarta ta huta nikuma sai inci abinci a ina
Zayyad yace common Ga wurarancin abinci nan bila adadin agari
DAGASH yace Allah yasauwake
Inzaka ta tashi katashi idan kuma bazaka tajeba natafi abuna
Zayyad yace zaka Rina ai dan ba mutunci kaganiba dan iska
Suka fita zuwa gidansu al'amin
Mummyn al'amin nazaune a daya daga cikin kujerun falonta taji sallamar dan nata
Ta amsa tace Son baka gajiya da zirga zirga a hanyar nan wai kai kazo abinci ko
Zayyad yace kema dai kyafada mom nace mishi muzabi restaurant mai kyau murinka zuwa lunch yace Allah yasauwake
Mom tayi murmishi tace aikuwa nakusa hutawa nan da two months dai ai sai dai yaje gidan shi yaci ko
DAGASH ya yamutsa fuska yace Allah yasauwake naci jagwalgwalon yara kullum gunki zanci abinci
Mom tayi murmushi tace wa zayyad kaji wata sabuwa kuma wai su suhaila ne yara
To suhailar ce yayarin ya kokuma Aymanan ce yarinyar dukansu babu wacce bata kai 25 years ba
DAGASH yace amman dai ai agurina yarane tunda babu wacce ta girmeni acikinsu
Zayyad yace uban son girma
Mom tayi murmushi tace kai son wai ina zaka kai wannan murdaddan halin nakane
DAGASH yace mom am hungry fa
Tace kuje dining area your food is ready
That's my lovely mom yabata kiss a kumatu ya wuce abinshi
Mom tace wato son kagama rainani ko zayyad yayi murmushi yabi bayan abokinshi
****
Aymana zaune cikin bedroom dinta tana waya da kawarta dake Dubai mai suna sauda
Sauda tayi dariya daga wayar tace amma gaskiya kawata na tayaki murnar samun gwarzon namiji Kaman wannan gayen da kika turo min hotonsa
Kuma kikace dan yayan dad dinki ne amma nibantaba ganinshi ba
Aymana tayi murmushi tace a ina zaki ganshi tunda kogidan mukaje bama haduwa
Sauda tace hakane saidai maganar suhaila yanzu miji daya zaku hada da suhaila yar jiji dakai din nan
Aymana tayi murmushi tace to Allah na tuba wazata ja wa ajin bayan babu abinda zata nunamin
Kawai kowatata tafish sheta
Sauda tace hakane amma kawata akwai magana amma sai na dawo zamuyi maganar
Aymana tace OK Allah yadawo dake lafiya sukayi sallama
Aymana tashiga tunanin ya al'amin acikin zuciyarta Allah yasani ta Dade tana kaunar ya al'amin dama rashin ganin fuska ne yasa ta kama bakinta
Dan zata iya rantsewa bata taba ganin dariyar bawan allahn nan ba kullum fuska a murtuke Kaman wani boss
Tashi tafito falonsu kuyanginta suka zube suna kwasar gaisuwa ta watsa musu harara tace dan uwarku kuna jiran nasa takalmin da kaina ne kafin tarufe baki wata daga cikin su tadauko sifas din nata tashiga saka mata
Wasu kuma Allah ya huce ran gimbiya
Tace nikumin shiru wawayen kawai tawuce fuuuuuuu
Tana shiga falon mummynta taga bakowa dan haka ta wuce zuwa bedroom kawai direct
Tana shiga ta tarar da ita zaune kuyan ganta suna mata massarge din kafar
Ganin Aymana ta shigo yasa sukafita dan sunsan halinta yanzu saitaci mutunci su
Mummynta tace lpy kuwa aymana tace wallahi mummy yanzu dan Allah dan daddy yabawa ya al'amin ni sai yaki zuwa ma mudan gana
Kuma wallahi nasan yana zuwa wajen waccen banzar suhailar nice dai bayaso tafashe da kuka
Mummynta tace wayafada miki yana zuwa gurin dayar itama fa bason ta yakeba
Kinga ai gwamma kema yar warsace ko
A hankali zaifara sonki
Itadin banza kuma indai al'amin ne zaizo ki kwantar da hankalinki
Naji abban ki namagana dashi dazu akan yazo Ku gana
Aymana tayi murmushi tace Yauwa mumyy wallahi har hankalina ya kwanta
***
AL'AMIN zaune a office din daddynshi dama duk Thursday da Friday yana zuwa office din daddynshi idan yadawo daga aiki dan 12 yake tashi
Bayan sungama hada duk wasu file daddy yace Son kaje gurin yaran kuwa
Kasan anriga an tsaida lokacin bikin ko
Nan two months za ayi
AL'AMIN yace nasani dad zanje insha Allah idan nasamu dama yace alright kayi kokari kajiko
Yana kwance akan godonshi yanashan whisky wayarshi tadau kara yadauka yaga Vichy ce cikin tsawa yace wayace kikirani by this time a round
Tace am sorry sweet heart dama nakiraka ne naji lafiyarka yace kina ina ne tace gida yace kijirani zanzo yanzu
Baijira ta ce wani abuba yakashe wayar shi
Murna ta kama Vicky dan tasan tayi missing din shi sosai
Dan idan abin baya kanshi saiyafi wata be nemeta duk da dama itatake nemanshi nan da ta tashi ta shirya cikin wasu matsatstsun kaya Wanda tasan zeyaba dasu sosai
Sannan kuma ta fesa turarrukan dayabata tadinga amfani da su idan zaizo gareta danshi mutumne me tsafta sosai
Haka kuwa akayi ranar a hotel suka kwana da Vicky
Ya tashi da asuba yayi wanka yaje masallaci daganan kuma ya wuce gida abinshi
Vicky koda ta tashi taga bayanan tasan badawowa zaiyi ba dan haka halinsa yake
Kudi taga yazube mata kan bed din ta kwasa tana murna
Ita tasan daga ita DAGASH baya kula kowacce yarinya kuma yana kashe mata kudi sai dai tana tsoron ranar da zaisan ba shikadai take kulawa ba
***
BAYAN KWANA HUDU
Al'amin yashirya danzuwa gidansu suhaila da umarnin dad
Zayyad daman baya gari shiyasa kawai yashirya tsaf cikin wasu suit mai kyau golden colour na cikin fari sai necktie dinma golden kai gaskiya yayi kyau sosai
Yafito ya wa mum din shi sallama
Tace waw Son wannan kwalliya haka lalle agaida suhaila ta ciri tuta
Baice komai ba ya wuce abinshi saboda yasan tsokanarshi kawai takeyi
Danshi ko yaushe cikin kamshi da ado yake
Mom tayi murmushi tace miskli wannan matan naka ma ai su shiga ukunsu
Hajiya zabbau ce ta fito tana waya tanemi daya daga cikin kujerun falon tazauna
Tsakaninsu bamai cewa wata kala haka suke zamansu
Suhaila kuwa tunda mom din Al'amin takira mummynta tace yau Al'amin yana zuwa gurinta
Dadi yakasheta sosai aka hau gyaran jiki tasaka 'yan aikin gidansu suka shirya mata abinci na musamman karfe biyar na yamma Al'amin yayi parking a gurin ajiye motoci na gidan
Bai fito a motar ba dan kasaita da jinkai
Suhaila ta karaso cikin yanga da yauki da rashin kamun kai Riga da wando tasaka sun matseta gashi taci kitson attach Ga kwalliya da musamman ta dauko me kwalliya tamata na musamman
Tayafa dan karamin mayafi Wanda dashi da babu duk daya
Hanu tasa tabude mishi kofan tana sannu dazuwa doctor
Sai daya dau lokaci kafin yasa kafa a waje yace Yauwa
Tace mushiga daga ciki kugaisa da mummy
Yamata wani wawan kallo yace kezaki fada min abinda zanyi
Tayi saurin girgiza kai yace stupid
Da kyar yaja kafa zuwa cikin gidan cike izza da kasaita
Tana biyedashi har falon gidan nan anriga an ajiye komai na motsa baki
a yatsine yake kallon komai Kaman yaga kashi duk da haduwa irin na falon
Tazauna tana son magana amma tana shakka hakan yasa tayi shiru
Tayi karfin hali tace yasu mummy
Wani kallo yamata Wanda tarasa gane na menene kallon
Yacigaba da latsa wayarshi
Tashiga serving din shi abinci ganin bai hanata serving dinba tayi tunanin zai iyaci ne
Sai da tagama tace doctor have a food bai kalleta ba ballan tana tasamu amsarta
Can dai kusan minti goma yakalli agogon hanunshi
Yasa hanu a aljihunshi yacire band's na kudi 'yan dubu dubu ya ajiye akurar dayake yatashi Yakama hanyar waje
Takaici ya ishi suhaila ta tashi gwiwa a sanyaye tabi bayanshi kafin yakarasa fita suka hadu da mummyn suhaila
Yadan sake fuska kadan yace mummy an wuni lfiya tace lafiya kalau al'amin
.wato dan ba abokinka shine zaka wuce batare da mungaisa bako
Yace ba hakabane mom dama Inda niyar shiga mugaisa
Tace bakaci kamaiba zaka wuce yace bakomai mummy
Yanzu ma gidan daddy king zanyi shiyasa nake sauri kar akira magrib ban karasa ba
Tace OK to agaishesu ta kalli suhaila ta mata magana da ido akan tarakashi mana
Tarakashi har gurin motar shi yasa hanu yabude yashiga yatada motar yayi gaba abinshi kota kanta bebiba
Da kuka ta dawo falon tafada cinyar mum dinta tana kuka tace mumyy nashiga yafison Aymana kinga wai har sauri yake zaije gidan su
Mummy tayi murmushi tace yaro dai yaro ne waya fada miki yafi sonta dayafisonta ai gurinta zaifara zuwa amma gurinki yafara zuwa kafin zaije gunta
Gakuma makudan kudin daya ajiye miki Wanda bana tunanin zai bata kamarsu
Idan kika kwantar da hankali bakaramin dukiya zamu taraba dan kisan koshi AL'AMIN yafi dadinki kudi nesa bakusa ba Ballan tana kuma uwa uba kuma mahaifinsa Wanda komai nashi al'amin ne akai
Murmushi suhaila tayi tace kuma hakane maganarki mum
Suka kirga kudin dubu Dari biyu cas
Suhaila tayi wani ihu yace waw
AL'AMIN yana isa ana kiran magriba dan haka sai da yatsaya sukayi sallah a masallacin gidan sarki tare da memartaba suka fito suka karasa cikin gidan
Mummyn Aymana tace a a manya baki yau yarima ne agidan namu
Yadanyi yake kadan danshi idan akwai abinda yatsana to akirashi Prince
Aymana ce ta fito da gudu tana mummy ina ya al'amin din
Kunya Yakama memartaba dan tanuna zumudinta a fili
Hakan yasa yatashi yayi sama abinshi
Mummyn Aymana ma ta tashi tayi cikin gidan akabar Ayman da Prince
Yana ta aikin danna wayarshi
Tace yaya sannu da zuwa
Bai kalleta ba ballan tana ya amsa mata
Nan da nan ta kira kuyanginta tashga zaginsu tace waiku wasu irin dabbobine bakusan abinda Yakama ta kuyiba
Dayar tace ranki yadade kekikace sai kinbamu umarni zamudinga yi
Tayi tsaki tace kushirya wa ya Prince abinci
Aikuwa suka watse dan cika umarnin ta
Wani wawan kallo da DAGASH ya watsa ma ta yace how there you zaki kirani da Prince dan ubanki ni sa'an wasanki ne
Dama Kaman jira yakeyi ya huce takaicin masu kiranshi da Prince akanta
Ganin yadda yataso yasa taja dabaya sai takai bango kafin yabita ya wanke ta da mari
Yace dan ubanki insake jin sunan abinki ki sha sha beside ma wazaici
Kazamin abinci na masu aiki
Yasa kafa yataketa a kafa
Yacire kudi kamar yadda yaba wa suhaila itama haka ya wurgeta da su yayi hanyar waje
Da gudu tayi hanyar dakinta tafara kuka Kaman Allah ya aikota
Mummy tasauko dan daukar Abu taga kudi turus akasa
Tasa hanu tadauka tasan bazai wuce Al'amin bane yabaiwa Aymana
Tayi hanyar dakin Aymana tanashiga tasameta tanata kuka tace meyafaru Aymana nan aymana taba mummynta labarin komai
Mummy tace lalle ma al'amin yacika dan wulakanci shine harda mari akan abinda baikai yakawo ba
Kwantar da hankalinki duk abinshi nasan yana sonki wazaiki kyakkyawar mace kamarki Aymana kobaki Ga kudinki dayabar mini bane
Aymana tace aini kotakan kudinma banyiba dan takaici nan dai suma sukayi ta murnan samun kan al'amin
DAGASH zaune kan daya daga cikin kujerunsa na part din shi yana ganawa da managers din sa na companies dinsa
Akwai manager na DAGASH AIR LAND Dan Al'amin yana da jiragen sama a gida da wajen Nigeria shida ma haifinsa
Sai kuma manager din DAGASH BUILDING CONSTRUCTION COMPANY shima ba abinda basayi na harkar gine gine da kawata gida
Sai kuma DAGASH SHOPPING COMPLEX Wanda babu state din da bashi branch
Sai kuma DAGASH BARBING SALOON NA MAZA
DAGASH RESTAURANT wato gida jen abinci masu tsada duk nasane shida mahaifin
Bazan iya fado muku dinbin dukiya da wannan 'da yatara shida mahaifinsa ba
Bayan sun gama zaman ne ya sallamesu
Kafin yashiga wanka yana fitowa yashir ya cikin kayan training dinsa yayi waje
Yaje wani hadaddan gurin training ne na musamman Wanda aka kayatashi acikin gidan
Yana isa yaga kannan shi mata suma suna motsa jikin
Suna ganinshi sukafara wucewa daya bayan daya
Nazeefa tace sannu yaya
Yace yauwa abin yabasu mamaki dukansu yau yaya al'amin ne da amsa gaisuwa
Batare da ya kallesuba yace ke afanan da shafa kuzo nan Dan uwarku yaushe nafara wasa daku dazaku wuce Baku gaisheni ba
Afanan da shafa jikinsu yadau rawa sukace Dan Allah yaya kayi hakuri wallahi bazamu sakeba
Cikin tsawa yace will u keep quite my friend
Shiru sukayi harda kama bakin da hanu
Yace oya kuje kudauko tsintsinya kushare compound din nan gabadaya
Da mamaki suka kalli juna Dan basu taba sharaba
Yasake daga musu wata tswar tukun suka watse da gudu zuwa cika umarninsa
*****
Al'amin kwance yana charting a wayarsa yaga massage yashigo yaduba yaga sabuwar number ce
Aka rubuta good morning my suld mate
Tsaki yayi yacigaba da abin yakeyi
Suhailace tamishi kusan kullum sai ta mishi massage
Ita kuma Aymana kira take dayake ita tana da private number dinsa
Sai yaga dama yake dagawa
Idan baiga dama ba kozata kira sau hamsin ba zai dauka ba
*Next page*
*Tofa masu karatu koyazata kaya Ga wadannan gidaje guda biyu
Wato Aymana da suhaila
Kowacce da tunanin ta akanshi
Kubiyo ni ummu afan dan yanzu fa akafara fans duk wannan shimfidane
Pls your comments is needed fans
More comment more typing
Ina alfahari daku over
Sign by ummu afan* π»
[26/06, 11:52 AM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
πππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUSE WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
I DEDICATE THIS PAGE TO YOU MOM IMAN &HANIFA love your comment sis Allah yabar zumunci πππππ
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 3β£
DAD din Al'amin zaune a office dinsa shida wasu baki da yayi suna tattaunawa
Can yaji alamun sakon waya yashi go phone dinshi
Sai yaduba yaga sakon wani general meeting ne na manyan mutane Wanda za a yi a gudanar a garin Abuja nan da sati uku azama cikin azumi kenan
Dan nan da sati biyu za akama azumi
Bayan ya salla mesu ne yadauki wayarshi yakira amininsa alhaji Dan asabe yace kasamu sako kuwa
Alhaji Dan asabe yace na maganar meeting ko
Dad din al'amin yace yes hakane
Wai nan da 3 weeks cikin azumi kenan ko
Alhaji Dan asabe yace kwarai kuwa
Yace to Allah yakaimu
******
Bayan sati biyu
Dagash da iyayensa suna zaune a falonsu suna kasafin zakkan da zasu cire sukai masallaci
Inbanda zakka ba abinda suke yi wa talaka wanda zasu jidadi shima zakkan inaga Dan dole ne yasa suke fitarwa
Suna mugun kyamar talaka sosai
Dad yakalli mom din al'amin yace hajiya Aisha kaman nawane zasu isheki hidiman azumi da ma sallah baki daya murmushi tayi tace konawa kaban nasan zasu isa
Murmushi yayi Dan yasan wayonta baya taba cemata ta yanke kudin dazai ba ta tafada sai dai tabarshi da zabinsa
Yakalli hajiya zabbau yace kefa hajiya zabbau nawa kike da bukata tabata rai tace 10 million murmushi yayi yace OK zan miki transfer a accounts dinki
Tace bakatambayan na yara ba
Daddyn al'amin yamata wani kallo yace da kekadai mezakiyi da million goma keda yarinkine zan tura miki kimusu abinda suke da bukata
Al'amin dai kala baice ba danshi kam dama sai suyi magana sau Dari baice komai ba
Mom din al'amin tace am al'haji kaga bikin nan dad matsowa yakeyi kasan Bayan sallah ne da sati biyu
Yakamata acikin azumin nan zamu Dubai da ni da suhaila da Aymana kowacce ta hado lefenta da kanta abinda ransu yakeso su dauka koya kagani
Dad din Al'amin yace badamuwa afara nema muku visa sai kuje ko azumi da sati dayane ko
Tace yauwa hakan yayi
Daddy ne ya kalli Dagash dayake ta danna wayarsa kaman baya jinsu
Yayi murmushi yace kai son anya kuwa baka da ciwon magana kuwa tunda muka zauna muke ta magana amma kai bakace komai ba
Dagash yayi murmishi yace dad to mezance komai kayi yayi ai
Dad yace to ya maganar order din shaddo din danasa ayimana zadai kasa ko karkasa nayi asarar kudina fa Dan suna da tsada kuma akalla zau kawo har yadiddika kusan talatin na mana order nida kai
Kuma is over 5 million kaga kuwa ba banzan yadi bane da kake siya dubu hamsin dubu sittin
DAGASH yayi dariya yace kai dad meyasa zaka bata kudin ka haka Bayan kasan basawa zanyiba
Mom tace aikuwa baka isaba auren ka guda kasa kananan kaya a a badaniba shiga zakayi me kyau Dan ina buri sosai a wannan biki Allah dai ya nuna mana
DAGASH murmushi yasake wanda har kumatunsa suka lotsa sosai Dan sai yayi murmushi suke lotsawa nashi
Yace kai mom rigima yatashi yayi hanyar waje abinshi
Mom tayi murmushi tace kagani ko yagama rainani wai nice ma rigimar gabadaya
Dad murmishi yayi yace ai gaskiyarsa ne kedin wasace tace au harda kaima kabi bayansa
Takaicine Yakama hajiya zabbau ta tashi tayi cikin gida fuuuuuiu
Tana ta nanata kayan daya musu order nasawa kawai ajiki shine wai har na million biyar kuma wai guda talatin kenan
Gaskiya tana danasanin rashin samun 'da namiji da Alhaji su'ad
Dubi fa yadda yake rawan jiki akan komai daya shafi Al'amin
*****
Washagri akatashi da azumin RAMADAN Al'amin ne zaune a office dinshi yana aiki sai akayi nocking door yace yes come in
Akashigo bakowabace sai Vicky
Yana ganinta ya hada rai yace who ask to come with out my permission
Cikin sanyin jiki tace am sorry sir wallahi nazo nace maka ina son zanyi tafiyane zan je garinmu
Nayi takiran wayarka baka dauka that's why I decided to come here and meet u
Ya watsa mata harara yacigaba da aikinsa Vicky dai ta gaji da tsayuwa shikuma bece tazauna ba
Kuma idan tazauna tashiga uku dashi harsai yabata umarnin zama suna haka
Zayyad yashigo ganin Vicky a office din yasashi kallon DAGASH yace man Ana azumin ma baza bar wani abunba
Dagash ko dagowa beyiba ballan tana zayyad yasamu amsarsa
Zayyad yayi murmushi yace yaufa abin sun motsa
Sai daya gama abinda yakeyi yadago ya kalli Vicky yace oya fada mishi abinda ya kawoki office din nan
Vicky ta kalli zayyad tamishi bayani yace OK I understand
yajiyo yacigaba da kallon dagash yaga shima shiyake kallo
Dagash yace Dan iska kaji abinda yakawota ko zayyad yace a naji abinda fada min amma kasan jin dai dole yadda kuma ba dolebane ko yakarasa yana dariya
Dagash yace kar Allah yasa kayarda ma mana Dan uwarka
Zayyda yayi dariya
Abinshi
Dagash ya kalli Vicky yace jeki zan miki transfer ta account tace nagode
Sai anjima koya kalleta tana fita tayi gidan saurayinta daman karya take taga lokacin azumine yazo ba ma.ganin AL'AMIN zatayi ba harsai Bayan sallah to itakuma bazata iya hakurin one months ba shiyasa kawai suka shirya da saurayinta zasutafi gida shakawa tunda duk yan Enugu ne su
Zayyad yace ya dagash zakaje meeting din nan kuwa
Dagash ya ce a a idan dady ma yaje ai ya wadatar mezanje namusu
Zayyada yace nazata zakajene ai
Nima na shirya amma tunda bazaka ba shikenan normal ne wai kunyi waya da Faisal kuwa
Dagash yace nadai ga miss call dinshi dazu ina son sai na koma gidan zan kirashi
Zayyad yace ai kaji matsalata dakai wai muma sai ka nuna mana halin naku 'ya'ayan sarauta
Haba ai kafin yarufe baki Al'amin yadauki trowing pillow akasa ya wurgeshi dashi
Zayyad yayi dariya yace ai kaji kuma gashi bakason gaskiya
****
Suhaila zaune itada mom dinta suna rubuta abinda suke bukata a game da shirye shiryen bikin
Sallama sukaji mom ta amsa driver din gidan su AL'amin ne yagaishe da mom da harda suhaila amma suhaila bata amsa ba yace daman hajiyace ta aikoni nakawo wa suhaila wanann
Yabasu mom ta bude taga Visa ne da passport
Tace zata kira taka muku bayani mom din suhaila tace to agaisheta
Yana fita suhaila ta hau murna tace waw mom Allah yakashe yabamu wallahi zasuga diban kayan hauka dazanyi
Mom dinma tace au da kiragama mana ayi bake ai zagewa zakiyi kidebi abubuwa masu tsada baruwanki da kudin sunyi yawa zasu iya biya
Nima kimana tsaraba nida kannanki
Suhaila tayi murmushi tace karkidamu mom ai kema akwati daya zanzaba miki na fitan biki
Shewa sukayi kaman wasu kawaye suka tafa abinsu duniyar tamusu dadi
****
AYMANA kuwa da Visa dinta ya iso hanun ta itama murna sunyi sosai ganin anga na banza
Mom dinta tace tare zasuje itama zataje sayan kayan kitchen din amarya haka kuwa akayi akashirya tafiya harda ita
Ranar rabara Yakama takwas ga watan Ramadan a ranar ne su mum din Al'amin da su suhaila da aymana da mom dinta suka wuce Dubai
Washagari kuma su dad suka dauki hanyar abuja shida amininsa dad din zayyad
Mota daya suka dauka driver kawai yajasu suka tafi batare da security ba
Dad din zayyad yace suje kawai amota basai sun jirgiba
Dadyn al'amin tunda yake ya manta rabon da ya je abuja amota a DAGASH AIR LAND suke tafiya
amma wannan karon dai yabi ra ayin abokin nashi alhaji Dan asabe suka tafi a lafiyyan mota me tsadar gaskiya sai da aka dauko bakanike yasake ma motar check up mekyau ya tabbatar musu ba matsala
Kafin suka dau hanya ba a son ran dagash sukatafi a mota ba
Ganin daddyn
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 18