You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
nan ana ta hidima kowa najira yaga amarya
Karfe takwas na dare motar amarya yatsaya acikin gidan
Yan kawo amarya mutum hudune sai Kuma maryam da rahama yazama su shida kenan
Sosai yan uwan daddy sukazo sukatafi da amaryarsu zuwa part din ta
Matan megari uku sai maman rahama su suka rako anty gidan kai maman rahama ta jinjinawa kudin da aka kashe a sashin maryam
Sosai rahama take ta kauyanci maryam kam duk da gidan yamata kyau feye da tunaninta ga Kuma wannan ajannar duniyar wai aciki zasu zauna itada atynta
Bata nuna ba kokadan kai maryam akwai kama aji sosai ta kama kanta
Tana sanye cikin doguwar rigar metsada tayi Rollin da mayafin ga Kuma gashinta daya yayi mata kaman tasa acuci
Kai duk wacce ya kalli maryam sai yasake kallonta saboda hallitar da Allah yamata maryam ta hadu iya haduwa can bedroom aka wuce da antynta ita Kuma tasamu waje a falon ta zauna tana ta game da wayar antynta
Ga wayar tadace da ita Dan bakaramin wayace ba
Rahama tace maryam kizo muje kisha kallon dakinki
Ba abinda babu aciki maryam ta kebe baki tace Dan Allah rahama kizo kizauna da alamu gidan akwai yan rainin hankali
Rahama tace kanki akeji nikam saina Ba ido na abinci rahama tashiga abinta
Maryam tanacikin game dinta taci ance sannufa maryam tadaga ido takallesu da alamu su girmemata nesa bakusa
Sukace kinacikin yan kawo amarya kenan maryam tace yar amaryarce ma.
Nazeefa da afanan suka kalli juna
Afnan tace yanzu kina nufin kice yar matar dadyn
Maryam tace kina mamakine
Nazeefa tace Ashe dai akwai aiki to mukuma mune 'ya'yan megidan
Maryam tayi murmushi tace kuce da yayuna nake magana
Afnan tace suwaye yayunki Allah yasawwake dan gin matsiyata anzo cin arziki
Maryam duk da zaginsu yabata haushi yacimata rai hakan baisa ta tanka musuba
Ta girgiza kai tace Allah yashirya tabar musu falon
Nazeefa tace shigiya saikace aljana anzo gidan daula to wallahi bazamu taba barinki kisake agidan Ba
Aiko uwarta ma bazata sharuwa bare ita
Suka yi tsaki sukayi waje abinsu
Wagari karfe Tara na rana yan kawo amarya suka tafi abinsu ciki harda maman rahama da rahama
Sosai rahama da maryam sukayi kukan rabuwa da juna
Akabar daga maryam sai anty
Koina kamshi yake agidan maryam ta wuce dakinta kawai tahau tunanin sabuwar rayuwar dazasu fara acikin gidan nan
Da daddare karfe Tara nadare daddy yashigo falonsa yaga mom da ummy kowacce taci adon abinta
Amma fa na mom din al'amin dabanne saboda ta haska falon sosai
Mom tace sannu da dawowa yace yauwa uwargidata
Mom tayi murmushi Dan tasan tsokanarta zaiyi
Ya kalli Hajiya zabbau yace kaga amarya agurin su'ad ba maganane Kuma Hajiya zabbau
.tayi kicin kicin da rai tace amaryar ka nacan tana jiranka badainiba
Daddy yace oh hakane ko to yanzu dai ba wannan Ba zan gabatar da muku da ita kusanta tasanku amtsayinku na wandan da suke sama da ita
Hajiya zabbau tace bama so karkirata taga kaman ta isane akakirata
Daddy yace nikuma inaso yadauki waya yakira anty ita harma tafara bacci
Yace maryam tayi maganar kamar me bacci yace sorry natasheki kizo kisameni a falona
Anty tace kai alhajina ina zansan inda falon yake yace OK bara nazo nataho dake
Yana kashe wayar yayi part din anty
Hajiya zabbau tasaka salati tace nashiga uku mezangani ni zabbau
Mom din al'amin tayi banza da ita kaman batajitaba Dan ita kam tayi alkawarin baruwan da matar daddy
Alhaji yafara shigowa falon kafin sukaji wata zazzakar murya tayi sallama
aikuwa Hajiya zabbau ta kai kallonta kan mesallamar saida gabanta yafadi Ra's
Ya yarinya ce ma Ashe amaryar yar haba ai dole yayi ta rawar kai mata kamar itatayi kanta
Anty sanye cikin lifayarta kyau mai kyau tace sannun Ku bawanda ya amsa mata
Anty tanemi gefen one sitter ta zauna abinta
Daddy yafara magana kamar haka yace to maryam ga yan uwanki Kuma yayunki kidaukesu kaman ciki daya kuka fito yanuna Hajiya Aisha yace wannan itace uwargidana
Saikuma ya nuna Hajiya zabbau yace wannan Kuma amaryata kenna wacce kike bi
Itadai anty ganin mom din al'amin saitaga kaman ma tafita kyau sosai mata kaman itatayi kanta haka
Nan daddy yayi ta mata bayanin gidan
Mom kuwa sosai itama anty tayi mata kyau matsalarta kawai talauci
Mummy ta tashi tawa daddy sallama Hajiya zabbau Kuma tace yanzu alhaji karasa wacce zaka hada mu kishi da ita sai yar cikinmu wannan ai al'amin ma yagirme meta nesa bakusa daga wallahi dubeta fa
Daddy yace kekika haifeta karewa fuuuuuuu tawuce zuwa part din ta cike da haushin bakar maganar daddy
Anty ta tashi zata wuce daddy ya ruko hanunta yace inazaki Kuma tace zanje na kwanta ne yace a ina aike da kwanna dakinki Kuma sai nan da kwana uku a dakin mjinki zaki kwana
Anty tace to maryam fa itakadai a dakin nan
Alhaji yace karkidamu BBakomai ba abinda zaisameta
Anty batayi musuba tabi angonta
Sunyi sallah godiyarsu da angonta
Hmmmmm ranar dai daddy ansha amarci sosai
Dan bai ragawa anty ba kuma yaji dadin kasancewa da ita
To sai muce daddy asha amarci lafiya
Next page
Your comments is needed
More comments more typing
*Signed by ummu afan* π»π»
[26/06, 11:55 AM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
ππππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
I DEDICATE THIS PAGE TO YOU SIS ADDA KHADY TA YAYA SHAMSU GASKIYA INA ALFAHARI DAKE OVER SIS ALLAH YABAR ZUMUNCI INAJIN DADIN NICE COMMENT DINKI KEEP IT UP β€
_π‘AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ π‘
Ina matukar alfahari da comment dinku gaskiya sosai da sosai
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 1β£1β£
MARYAM ta farka tsakar dare ta laluba gadon bata ji motsin atinta kuma tare suka kwanta aikuwa tasake bude idon da kyau taga tabbas bata nan
Ta tashi tafi falo ta dudduba koina bata ganta saita taba main kofar su taji abude sai tasa key kawai tadawo tazauna a kan kujera tace oh ni maryam
Yauce rana tafarko da muka raba dakin kwana da antyna
yanzu da mutuwa tayi fa shikenan haka zanyi ta kwana nikadaiko
Kai no antyna bazata mutu yanzu sai dai mu mutu tare
Ta share hawayen da yazubo mata ta koma bedroom din anty ta kwata akan bed takashe wuta
Tayi adduarta na bacci abinta ta kwanta
Sosai maryam taji dadin baccinta cikin kwanciyar hankali
Washagari da karfe goma na safe kafin daddy ya bar anty ta fito
Tayi part dinta Allah yataimaketa ba kowa a falon
Tana zuwa taji kamshi sosai ya gauraye part din tasan aikin maryam ne
Ta wuce kitchen tace maryam rigima duk ya akayi kika iya aiki da kayan kitchen din nan
Maryam tajuyo tana murmushi tace anty ai a school dinmu na federal abuja idan zamu catering duk irin wadan nan ne kayan aciki
Anty tace o hakane fa yanzu me kika dafama mana kinsan fa nizanba daddynki abinci
Maryam tayi murmushi tace ai nagama komai mummy kawai yanzu ina dafa coffee ne
Anty tace Allah yamiki albarka maryam tace amin antyna
Kintashi lafiya anty ta lakuce mata hanci tace bansaniba sai yanzu kikaganni sukayi dariya
Anty tace kihada komai a tire zanshirya nazo nakaiwa alhaji abinci ko
Maryam tace to anty angama
anty tayi murmushi kawai tawuce dakinta sake wanka tayi tafito cikin atamfa super Holland metsadar gaske tayi kyau tana ta kacaniyar daurin Dan kwali
Sai maryam tashigo tayi sallama tace kai anty na kinga yadda kikayi kyau kuwa
Kawo Dan kwalin na miki anty batayi musuba tabata ai kuwa tamata daurinta mai kyau kaman kar akunce
Ga jelan kitso daya da anty maryam ta kitse mata bakin gashin
Kai idan kuka anty sai kun so kusake kallonta
Maryam tace waw gaskiya anty kinyi kyau ina wayarki muyi hoto
Anty tace a a bazan dauka da wacce batayi wanka ba
Maryam tayi murmushi tace haka ko anty shikenan dadin abinma yanzu zan je nayi wankan
Kuma fa karki rokeni muyi hoton Dan nima zanki yarda anty tayi murmushi ta janyo maryam ajikinta tace maza daukemu nan maryam tayi ta musu hotuna
Sunyi balain kyau sosai duk da kayan bacci ne ajikin maryam hakan beyana pictures dikyau ba
Anty tace kekinga ina abincin alhajin maryam tace yana falo anty tadauka tayi falon daddy da shi tana zuwa tajera komai a dining area
Kafin taje suka fito da daddy
Daddy Yayi mamakin ganin abincin yace wato saida kikaba kanki wahala ko
Anty tayi murmushi tace bani nayiba yarkace fa
Yayi murmushi yace a bazanci abinci yata nasama ta albarka
Anty tashiga serving dinsa suna daddy na cikin cin abinci yaji dadin abinci matuka
Yana ta santi anty na dariya yayi taci taki tace yaci kawai itama zataci anjima
Maryam ce tafito cikin doguwar hijabi ta tsugunu har kasa tagaida dadi
Ya amsa sannu da kokari ko yar daddy allah yamiki albarka tace amin dadi
Ta tashi takoma abinta daddy yace zonnan yata kishiga kigai da su mummyn ki ko
Maryam tace to daddy tace shiga part din mummyn Al'amin tasameta a kwance a falo har kasa ta durkusa tagaida mum
Mumnyn al'amin jin wani zazzakar murya yasata kallon me wannan murya ganin yarinya kaman itata tayi kanta Dan kyau
Aranta tace kai masha Allah gaskiya a rayuwarta bata taba ganin mekyau kaman yarinyar nan ba
Tababbas kobata saniba wannan itace yar amaryar alhaji
Mummy tace naji nagode Amma daga yau bana bukatar gaisuwarki kinajina ko
Maryam tace naji ta tashi jiki a sanyaye tafita tayi part din su Hajiya zabbau ai nan rashin mutuncin da aka mata yafi haka sosai
Dan na irin zagin da basu mata ba haka ta daure batace musu komai ba tafito abinta
Mummyn al'amin itafa harcikin zuciyarta tsoron talaka takeyi sosai saboda gani take kaman zasu cutar da ita
To tuntasowarta ta taso cikin kudi kuma ba yar Nigeria bace kawai dai zama suke a abuja
To yanzu ma duk yan uwanta sunkoma kasarsu na libiya bata San talauciba Sam a rayuwarta ita
Shiyasa tsanar su maryam azuciyarta amma bawai Dan kishin ta aure mata mijiba
Maryam takoma part din su tace to yanayin gidan kenan kuma allah yasauwake
Zanyi hakuri da komai amma bazan bar acima ma anty mutunciba
Ta zage ta gyara koina sai kamshi tasaka turaren wuta kai masha Allah kawai za a ce kafin tashiga bedroom din ta tayi wanka bathroom ta fito tasaka Riga da skirts din English wear tayi parking gashinta da riborm kai tsaya zayya na muku kyau irin na maryam abin ma bazaiyuwuba
Ta fito falonsu tazauna tana game dinta da wayar anty
Anty kuwa daddy nacin abincinshi saiga DAGASH yashigo direct gurin dining din ya wuce
Ganin anty yasa DAGASH mamaki no Wonder daddy ya rikice Ashe dai yaga meyagani ai wannan yarinyace ma
A yana bayan dadinsa wallahi yayi murmushi acikin ranshi
Yace dad good morning dad yace morning Son ya iyalan naka yayi shiru Dan iyakacin gaisuwarshi kenan
anty tace ina kwana ga mamakin Daddy saiyaji Al'amin yace lafiya
Daddy yabar mamakinshi a rai
Gaskiya ya yarda maryam me sa ace tashi daya al'amin ya amsa gaisuwarta
Anty kuwa aranta tace to gaskiya wannan dai dagani gata yamai yawa da alamun girmankai a taredashi duba ga yadda ya amsa gaisuwarta
Ita anty bata San taci sa ama daya amsa mataba a hakan
Anty tace inazuwa daddy yace inazaki kuma maryam tace zanleka maryamne
Yace OK
Daddy ya kalli Al'amin yace muci abinci mana Son
DAGASH abinci yamishi har ranshi amma sai yatambaya yace wayayi abincin Daddy yace kanwarka
Dagash yace to allah yasauwake naci jagwalgwalon yaran nan dad
Daddy yace aibasu afnan nake nufiba kanwarka maryam yar amarya ta
Dagash yayi murmurshi yace kai dad you're so funny yanzu wannan yar matar taka hartana da yarinyar dazata yi abinci harkasa agaba kaci kana santi
Daddy yace au matar tawace ma yar mata ko Dan baka da kunya to ai tahaifeka
Dagash yayi murmushin dole yace tunda ta auri daddy na ba amma wannan wallahi na girmeta bare har yartayi kwabarta wainaci allah yasauwake
Daddy yayi murmushi yace lalle son damatar nawa kake gwada shekaru ko
Dagash yace dad kenan nidai kaga tashina zanje gurin mom nayi break karnayi Lattin zuwa hospital
Daddy tashi yayi bayan yagama yaje suka gaisa da su mummy
Hajiya zabbau kam ko kallo be ishetaba tunda yakwana da amarya
*****
Bayan sati biyu da bikin dad
Yau Monday maryam zatafara zuwa school wata tsaddadiyar makarantar da 'ya'yansa sukayi Wanda duk nan suka gama gama sai shafa atu datake s s 3 yanzu kuma daman itace autar daddy tagirme maryam dakusan shekaru 3 zuwa 4 dad yasa maryam a makarntarsu
Yaune za a bata class
Uniform din rigace fara medogon hanu sai kuma ramin skirt dai dai gwiwa dark green colour sai karamin farin hijabi dai dai gwiwa
Sai kuma rigar sanyi kalar skirt din me karamin hanu
Sai farin combos dinta da farin sucks dinta har gwiwa yadda ba aganinn kafarta
Ba abinda yafi burgeni da ita karamin farin glass data saka Wanda yayi balain mata kyau sosai
Anty tace kai maryam kinyi kyau sosai harna hangoki acikin kayanku na lauyoyi
Maryam tayi murmushi Wanda murmushin maryam ma kawai abin kallone ta runguem anty tace allah ya amsa bakinki anty na
anty tace maryam inason duk sallah dazaki yi kiringa saka alhaji a adduarki Dan yamana abin ba bamutaba tsammaniba
Inason duk abinda yaransa suke miki kiyi hakuri kodan alhaji kinji
Maryam tace shikenan anty na namiki alkawarin bazan taba kulasuba kuma daddy kullum nayi sallah ina roka mishi allah anty tace yauwa yar albarka
Nan anty tadafa kanta tamata adduoin neman tsari daga sharrin shaidan da mutane
Maryam ta dauki dark green din katon school din ta
Tafita zuwa inda daddy yake a falo
Al'amin na gefen daddy yana break fast
Hankalinsa na kan abincinsa
Sai yaji wani zazzakar murya medadi tana gaida daddy
Daddy ya amsa yace kai kai gaskiya 'yata tafito students dinta kinyi kyau ko
Daddy yace ina ita shafa'atun tazo maza nasaukeku
Dan dagakaina nakeson kai maryam saboda agama mata registration da wuri tashiga class idan na hada tada driver baza concentrate akanku da wuri ba
Shafa'atu tafito itama cikin shiga irin na maryam amma ita shafa'atu tana da hula red alamun dai tana da mukami a school din
Basu taba haduwa da maryam ba saboda ita shafa'atu bata cika shiga sabgar da banataba
Halinta yaso yayi shige Dana AL'AMIN idan taga dama saitayi wuni adaki ba ruwanta
Daddy yace yauwa shafa'atu kinfito ko ga yar uwarki nan kanwarki kinji kiriketa amana abinda bata saniba kinuna mata
Shafa'atu tace to daddy insha Allah ta kalli maryam tace sister kinyi kyau maryam tace nagode
Dagash kam tun kallo daya dawa maryam ya kame kawai yana mamaki dama a talakawa ana samun irin wadan nan mutane koyace hallita
Shidai yasan yana dakyau sosai amma yau yaga hallitar data fishi kyau
Sai kuma wani zuciyar yace kai kuma ina ruwanka da lissafa kyanta sai yayi tsaki da karfi baisan da karfi yayiba
Daddy dake amsa waya yajiyo ya kalli DAGASH yace Son kayi hakuri kakai su maryam school saboda amata komai yadda yakamata
Ankirani muna da meeting yanzu munyi baki daga abuja
Dagash zaiyi magana daddy yace haba Son yaufa ba Hospital zakaba so please ka kabar zuwa office din kawai tunda kaga ma meeting zamushiga
dagash baisake magana ba yaciro wayarshi yashiga dannawa
Maryam kuwa tunda ta saukar dakai kasa take wasa da hanunta bata sake kallon kowaba
Shafa'atu taji ummynta nakira taje kiran
Ummy ne dasu nazeefa
Afnan tace wai Ashe yarinyar nan itama makaranta yasakata
Shafa tace a lafiya kuwa ko akwai wani abune
Ummy tace zonan autata kinsan mezakimin tace a a ina son kigallazawa yar banza kihanata sakewa a makarantar
Nazeefa tace kici ubanta idan tamiki raini dama gashi ke head girl ce karki bari taji dadin makarantar
Afnan tace kuma wallahi idan kika ga daddy yabata kudi kikwace tunda bakudin ubanta bane
Shafa tace naji zan iya tafiya ummy tace jeki yar albarka
Kar akiraki sai kin dawo
Shafa tayi gaba abinta ta na girgiza kai ita haushima suka bata wallahi tayi tsaki
Tana zuwa falon taga ba yaya Al'amin takalli maryam dake zaune tace maryam ina yayan maryam tace yafita cikin sanyin muryarta
Shafa'at tazaro ido waje tace munshiga uku maryam yaya bayason jira tashi muje dasauri
Itakuwa maryam bata iya tafiya da sauri ba a rayuwarta saboda shafa taruga aguje zuwa gurin motar
Tana haki tabude gaba tashiga
Bai kalletaba yaduba yaga baiga dayar yarinyarba yace kekadai ce daman tace a a
Cikin tsaknanin mamaki yace Dan ubanta nizanjirata shafa tace yaya kayi hakuri batasan nibane gata can tanazuwa yakalli inda take nuna mishi yaga wani irin taku da maryam takeyi
Yace OK yangama takeyi ko kafin shafa ta yi magana harya tashi motar yayi hanyar gate
Shafa tace yaya kayi hakuri Dan allah kaman fa ba yanbace haka tafiyarta yake
dagash cikin tsawa yace will keep quite or not
Itakuwa maryam ganin ya figi motar yaki jiranta ita kuma harga allah dasauri matake tafiyar
Karasawa gurin baba maigadi tayi sannu baba yace yauwa yarinya tace baba driver nake nema
Nan baba megadi yakira sani driver tace sannu kawu yace yauwa
Tace school za akaini yace to ranki yadade yayi saurin bude mata gidan baya tashiga ya rufe sai kuma security daya yashiga gidan gaba suka harba kan titi
Sun wuce motar dagash akan titi sakamakon wayar dayakeyi
Saidaya gama kafin yacigaba datafiya kusan atare sukayi parking
Da sauri security din motar su maryam yayi saurin zuwa yabude wa dagash kofa
Itakuma maryam tana kokarin bude kofar dakanta sai sani driver yayi saurin bude mishi
Abin ya matukar bawa dagash mamaki Dan kokallon inda yake batayiba ballan tana yasa ran zata bashi hakuri
Shafa tace maryam maryam tatsaya can tace kibari kushiga da yaya yamiki komai da kanshi zaifi sauri
Maryam tadanyi murmushi Wanda yasake fito da fararen hakorinta masu kyau da sheki
Tace Bakomai anty shafa kinga daddy yariga yayi komai kawai zanje nagabatar da kainane abani class karkidamu zanyi komai dakaina
Tasai zata wuce shafa tace am sorry maryam teachers din gabadayansu turawane
Maryam tayi murmushi tace don't worry my sis handle it thanks for love and care
Shafa dai tacika da mamaki tace maryam karkice nadameki
Kije kiba yaya hakuri yaji haushin rashin fitowarki da wurifa
Maryam tace mena mishi dazanbashi hakuri anty
Ban mishi komaiba saboda nibazan bashi hakuriba
Ya wuce tayi cikin school din confidence kaman wacce tasan koina a school din
Dagash kusan mutuwan tsaye yayi Dan duk abinda yafaru akunnenshi
kuyi maneji da wannan fans banida lafiya needs your prayer pls π€²π»
Next page
Your comments is needed fans
*Signed by ummu afan* π»
[26/06, 11:55 AM] SIS UMMY: [22/06, 4:12 PM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
ππππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUSE WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
I DEDICATE THIS PAGE TO YOU SIS UMMY HANIF GASKIYA INA ALFAHARI DAKE OVER SIS ALLAH YABAR ZUMUNCI INAJIN DADIN NICE COMMENT DINKI KEEP IT UP β€INA JIN YADDA KIKE SON AL'AMIN DAGASH DAGA BAKIN SIS UMMY PROUD OF Uβ€
_π‘AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ π‘
Ina matukar alfahari da comment dinku gaskiya sosai da sosai
Comment harda read more π€much love to your love and care
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 1β£2β£
Cikin tsananin bacin rai Dagash yashiga motarshi yayi gaba cike da mamakin abinda yarinya karama kamar wannan chick little girl din tayi mishi
Direct office din zayyad ya wuce zayyad yana cikin duba patience dinsa yaga Dagash ya banko kofar yashigo cikin tsananin bacin rai kokallon inda zayyad yake beba yawuce resting room din zayyad
Zayyad yacigaba da aikinsa yagama duba patience saiga Faisal yashigo yabiyo mishi suje lunch ne
Zayyad yace mutuminka fa naciki naga yashigo a fusace
Faisal yace DAGASH kakenufi
Zayyad yace shifa nan suka shiga resting room din
Ganin dagash sukayi yabude kwalbar whisky kawai yana tasha
Zayyad yayi saurin dauke kwalbar dan yana da karfi metsadace sosai dan kadan akesha
Faisal yace haba dagash yakakeson kawa kanka illa haka
dagash cikin tsawa yace who is she dazata rainani irin haka
Ya kallesu yace can u imaging A Secondary school girl tamin rainin da mace me master's ma bata da wannan right taminshi
By the way ma yar matsiyata ce fa
Zayyad da Faisal suka kalli juna dan sunsan tabbas wannan yarinyar kowacece ta debo ruwan dafa kanta
Faisal yace subahanalla a ina kuka hadu har rainin yashiga tsakanin haka
Dagash yayi murmushi mugunta yace yar amaryar daddy ce
Zayyad da Faisal sukace kai yanzu dama amaryar dad tana darinya ne
Faisal yace wallahi I told irin tadade kawai tana karatun nan ne
Dagash yabasu labarin abinda yafaru kaf
Zayyad yafashe da dariya kai amma fa yarinyar nan jarumace sosai
Kuma kace secondary school kodai waec zata gyara
Dagash yace to a S S one. Ma take
Shafa'atu ta girmeta sosai
Zayyad yace dan allah man karka ce saika hukun tata kaga mamanta bazataji dadi
Beside ma daddy bazaiji dadi ba
Inaganin kawai kakirata kafada mata dokokinka saita kiyaye agaba
Sai da sukayita bashi baki akan yayi hakuri karyace zai hukuntata
Yace ayaji amma fa tabbas sai tabashi hakurin rashin kunyar data mishi
Zayyad yace a hakan ma yayi
Anjima saimushiga gidan tare
Itakuwa maryam cikin sa a tagama komai ammata interview tacinye tsaf akabata class dinta na Government
Wanda daman shine burinta S S 1 akabata nan danan akabata komai da komai na su material din da ake amfani da su a school din
Hardasu games wear dinta tazabi basket ball
Clubs kuma tazabi press club
Karfe biyar da rabi aketashi driver yazo yadaukesu
Shafa tace maryam ya school yakika ina fatan dai yamiki bansamu na nemiki bane saboda anamana orientation na na exams
Maryam tayi murmushi tace Bakomai anty shafa kuma school din yamin hundreds % fatan dai shine allah yabar wa daddy lafiya yarabashida sharrin makiya
Shafa taji dadin adduar maryam akan tace ameen maryam allah yataimaka gashi munkusa tafiya mubarku maryam tace wallahi Gaskiya kam zanyi kewarki sosai dan dagani you are so kind and nice person
Shafa tayi murmushi tace nagode sosai kanwata da yabonki akaina
Driver na parking dinsu aka bude musu kofa sukayi gaba itada shafa
Murya sukaji ance kai kuzonan shafa ce tafara juyawa taga yaya ne zaune a lambun gidan suna shan iska da abokanshi su yaya Faisal da zayyad
Maryam tayi kaman bata jiba tayi gaba abinta shafa tayi saurin kamota tace maryam yaya nakiranmu
Maryam tace OK kai akasa take tafiyarta batadago ba balle ta kalleshi
Tunda su zayyad suka hango ta sukace tsarki ya tabbata ga mahalliccin wannan hallita
Faisal yace Ashe yarinyar metsadace dole tayi abinda tayi wallahi
Zayyad kuma yace shi wallahi sai yau yahadu da halittar datafi DAGASH kyau
duk abinda sukeyi sungama kular da Dagash
Yace dalla malamai kusauraramin karkusa yarinya tarainamu please
Wannan chick little girl din kutsaya kuna lissafin kyanta a ina kyan yake balle har a tsaya ana ta Abu daya please ya isa inma zaku kubari sai kukadai
Zayyad da Faisal dai abinda yahanasu dariya ganin karasowar su maryam ne
Maryam tadurkusa tagaida su zayyad suka amsa da fara'arsu suna musu ya school
Abin yasake kona ran DAGASH wato tafi karfin tagaisheshi kenan ko
Shikuwa dagash besan halin maryam bane idan tagaisheka soka daya kayi banza da ita to dakai dakashi daya ta dauke Ku
Tunda tagaidashi a falo yaki amsawa shikenan kuma
Dagash yace washafa jeki dauko min tsintsinya a gurin masu aiki tana jin haka yasa shafa tasan mezaiyi