muhimmanci a gurinsa
Baidau lokaciba yakawo aikar ganin dagash din baya falon yasa yashiga ciki yakai mai
Dagash yace Dan Allah karkayi nisa katsaya a kusa Dan zan iya nemanka yace to yallabai
Shima yashiga cikin masu jimamin duk da baisan abinda kefaruwaba duk dai yaga manyan mutane ne
Zayyad ne yayi nasarrar ganin anty tadawo hayyacinta
Tana farfadowa ta tashi tana banson ganinshi
Natsaneshi karkubari yazo kusadani
Zayyad yace anty kikwantar da hankalinki a asibiti kike
Cikin tsawa tace kamatsa min a hanya nawuce bazan zauna ba wallahi
Tafiya zanyi zayyad ganin kaman bata hayyacinta yasa yaketa bata hakuri akan tayi hakuri ruwan da aka samata yakare
Harara ta watsa mishi tayi hanyar waje kai ko Dan kwali babu gashin nan hargadon baya gashi yaji gyara amma bata damu a yadda take ba ta fito abinta
Dagowar da malam Abdul megadin dagash zaiyi suka hada ido anty cikin dimuwa murya narawa yace maryam
Itama cikin kuka tace yaya Abdul duk falon aka mike daddy king ne yayi karfin halin cewa kasan tane
Yaya Abdul yace kanwatace anty ta durkushe tana kuka mai bantausayi
Yaya Abdul yafito ya matso yakama hanun ta shima yana kuka yace maryam ina kikashiga bayan barin ki gida
Kindaga hankalin kowa ba inda bamu shiga nemanki ba maryam innan mu tana can balafiya tun bayan korarki da Abba yayi harta shi kanshi abban ma bashi da lafiya maryam duk adalilin rashinki
Dagash ne yafito rike da hanun maryam ganin mutane baisa yasake taba
Sai dai ganin anty durkushe itada megadinsa yasa yayi turus maryam ta fisge hanunta tayi gurin anty tarungumeta tana kuka anty kuka yaci karfinta takasa koda maganane
Alhaji Dan asabe yataso Yakama yaya Abdul yace malam Abdul kai namiji ne zamu fi samun gamshashshan bayani agunka
Kowa ya nutsu bakajin kukan kowa saina maryam da anty
Daddy king yace muna sararonka malam Abdul
Yaya Abdul yace maryam kanwatace uwadaya ubadaya
Nida yayana usman mukatafi Neman kudi cikin garin meduguri
Dawowar mu mukasamu mummunnar labarin dayafaru akan maryam
Munyi kuka mun nunawa mahaifinmu rashin dacewar abinda yayi kuma ya amsa laifinsa dashi akashiga Neman maryam amma shiru balabarinta
Wannan dalilin yasa inna mahafiyarmu takamu da ciwon barin jiki wanda har yanzu tana fama dashi
Abban mu dakadan kadan ciwo yakwantar dashi
Wannan dalilin yasa mukabar garin gwaza zuwa cikin garin meduguri nan ma zaman badadi ga marasa lafiya har biyu da muke dasu
Akamana kwatancen wani memaganin gargajiya a kano
Nan mukazo haya muka kama kasancewar yayan mu usman yasamu wani megida dayabashi mota yake tukawa to shiya yasa yaya usman yayi amfani da kudinsa ya kama mana haya gaba kidaya gidan kuwa
Kowacce mace da dakinta agidan baruwanmu da nuna banbanci
Ana haka watarana nazo wucewa naga anrubuta a neman gate man wato megadi kenan nan naturo application dina Allah dai yabani nasara megida Al'amin yadauki
Yanzu nakai kusan shekara goma a asibitin nan wannanshine takai caccan tarihinmu
Kowa labarin yagirgizashi sosai anty tabashi tausayi sosai hajiya kuwa inbanda hararata ba abinda takeyi
Kowa yakasa magana a falon ganin haka yasa yaya Abdul yace maryam ina abinda kika Haifa bayan barinki da cikin anty cikin kuka ta sake Rungume maryam tace gatanan yaya gatanan yaya takarasa tana kuka mecin rai
Gani sukayi alhaji imam yatashi cikin rudewa yace yanzu maryam kina nufin yarinyar nan yatace
aikuwa kallo yadawo kanshi
Mummy cikin kaduwa da jin zancen yace yaya kasan abinda kake fada kuwa
Ya za ayi wannan shegiyar yarinyar bayan agabanka kaji wanta yabada labarin komai kace yarkace
Cikin tsananin bacin rai alhaji imam yace ya isa haka Aisha karkisake sheganta min yarinya bashigiya bace nine ubanta Nine mahaifinta ba shegiyabace
Duk Wanda kefalon maganar tadakeshi mummy jiri mekarfi ke kokarin kayar da ita dagash yayi saurin kamata yazaunar da ita
Cikin sambatu mummy ta rike hanun al'amin tace Son kawunka ya haukace kaje kaduba minshi Dan Allah jama'a kutai makeni yadawo hayyacinsa
Alhaji imam yayi gyaran murya yace acikin hayyacina nake Aisha kece bakisani kuma a duk duniyar Wanda mukasan zancen mu goma ne cas
Yarana da na aikasu dauko maryam agarinsu su hudu
Sai kuma waliyyina da nata dakuma ladan
Saikuma ita maryam din sai abokina alhaji sudais saikuma ni kaina
Nan yakwashe komai yafada musu
Cikin tsananin rudani mummy gumi ne kawai yake tsatsstafo mata takasa magana kanta yamata nauyi sosai
maganar ta girgizata
Cikin kuka alhaji imam ya tsuguna gaban anty yace maryam ina rokonki da girman Allah kiyafemin wallahi ba ahalinabane kaddarace
Anty cikin kuka tace banson jin maganarka dalilinka narasa komai a rayuwata kasa iyayena sunkoreni suntsine min
Nashiga gararin rayuwa da rashin gata saboda ba abinda zakafa min nayarda dakai
Cikin kuka alhaji imam ya kalli maryam karama yace 'yata kiyafemin nasa muku ciwo azuciyarku
Maryam tajuya mai tanaa kuka takasa magana bata kaunar ganinshi ma ita
Yaya Abdul cikin kuka yakalli alhaji imam yace Ashe daman Kaine kayi sillar shigar ta gararin rayuwa alhaji
Ka aureta bada izinin ta Dana iyayentaba saboda zalunci na masu kudi
Daddy king yace haba Abdul kai yakamata ka tayashi bata hakuri da Neman afuwa
Shigowar su Aymana da suhaila da iyayensu sunji labarine sukazo gulma
Guru suka samu can kusa da hajiya zabbau tashiga basu labari daga farko
Sai yanzu daddyn dagash yayi magana yace maryam labarinki akwai tausayi acikinta Wanda nariga nasanidama
Amma meyasa kikabari shedan yayi galaba akanki kika aikata abinda kikamin
Alhaji imam yace meta aikata
Caraf hajiya zabbau tace kwarto takawo daki
Alhaji imam yace karya ne wallahi sati daya nayi da maryam na fahimci hallinta bazata aikataba
Daddy yace haba imam yazaka ce haka bayan nagani nakuma ji
Alhaji imam yace kasake bincike
Megadin gidan daddy yashigo shida yan sanda rike da kwarton
Megadi yace kugafarceni alhaji tunda ana wai kwarto aka kama agidan nasan badai ta gate ya wuceba
Yasa nayi tunanin ta kofar baya yafito shiyasa nayi sauri zagayawa yayi dai dai da lokacin da wannan saurayin take fitowa na damkeshi nabawa security shi
Sun mishi duka sosai yace turo shi akayi
aikuwa kowa yadau salati a falon hajiyar suhaila tace wallahi bamu yarda ba anbashi kudine kawai Dan ya karyata
Alhaji Dan asabe yadaka mata tsawa yace ya isa haka hajiya
Zayyad dai kunya yakamashi ganin abinda mum dinsa tayi
Hajiya zabbau zatayi magana daddy yadaka mata matsawa
Mummyn aymana dai zufa yagama wanketa tas
Jiki yadau rawa dagash matsowa yayi kusa da kwarton nan yazabga mishi mari yace yimaga wasu mutane ne suka turoka
Cikin sauri yace hajiya zabbau
Falon yadau salati anty asiya tafashe da kuka itada shafa'atu saboda takaicin abinda ummynsu ta aikata
Nan da nan kwarto yayi bayanin komai yadda suka tsara shida ita
Kowa yakadu a falon hajiyar zayyad da mum din aymana duk sunyi tsuru tsuru suna tsoron kar hajiya zabbau ta tona musu asiri tace harda hadin bakinsu aciki
Daddy duk dauriyar sa saida yazubar da hawayen rabuwa da anty saboda mace mace ta gari wacce dalilinta yafara ganin haske a rauwarsa
Gashi tashi daya ansa ya rabuda ita rabuwa ta har abada Dan babu yadda za ayi tadawo gidansa saki uku yamata
Cikin kuka yace zabbau kincuceni kincuci kanki ina mai tabbatar miki kema bazan barki haka banzaba
Hajiya zabbau tace Dan Allah alhaji kayafemin wallahi zuciyace hakan bazata sake faruwaba
Saiji sukayi daddy yace nasakeki saki uku karkisake kikoma gidana daga asibitin nan
Cikin razananniyar kara tace shikenan nashiga ukuna
Na wa yasameni Dan haka wallahi kowa ma sai asiransa ya tonu
Nan hajiya zabbau ta tona asirin kowa alhaji Dan asabe yayi salati yace au yanzu hajiya duk wannan abinda ake kullawa kece silla
Kije nasakeki saki daya bazan iya zama da mai hali irin nakiba
Daddy King kam dama ga zuciya cikin zafin rai yayi wa mum din aymana itama saki har uku yace wallahi yayi danasanin hada zuri'a da ita
Ya kalli dagash yace ina son kasake aymana yanzun nan saboda uwarta tafara girba abinda tashuka idan ta waye gari taga daga ita har yar tata zaurawa ne hakan zaisa sugane rayuwa umarni nake baka ba Neman shawararka nakeba
Dagash kuwa daman jira yake
Zaiyi magana daddynsa yace baza ayi ahakaba kabarsu Allah yashiryesu
Daddy king yace kabarni yaya Dan Allah karka hanani
alhaji Dan asabe yace kamata yayi kabashi umarni yasakesu gaba daya saboda hakan zaikowa musu sanin rayuwa dama tare sukaje gidan kuma tare zasu bari saboda mugun hali na iyayensu mata
Muryar anty sukaji tanacewa alhaji kacucemu sanadiyar abinda ka aikata gashi kasa yadawo wa kamillaliyar 'yata Wanda na Dade ina tattalinta
Rana daya yatashi a banza
Alhaji imam dake zaune jinabinda anty tace hankalinsa yatashi yace nashiga uku mekike nufi da wannan Kalmar
Anty cikin kuka tace ina nufin Allah yayi wadan da kazalinta sakkayya tahanyar yiwa yarka ciki
Yace innalillahiwainnanirraihinraju'un allahumma ajirni fimusibatihi wakalifni khairun minha
Tabbas abinda kayi sai ammaka Wanda yafishi imma nasharri ko na alkairi
Bansan inada yarinyaba amma cikin second dasanin hakan sonta ya nunku acikin zuciyata ina son 'yata nayi danasanin aykata abinda na aykata har yau gashi an min ninkin Wanda na aikata wannan jarabawace daga ubangiji nakuma karba
Anty tace maryam ina son kifada min waya miki ciki maryam kuka yakwace mata batasan amsar da zata bayarba Dan batasaniba
Kaman daga sukaji ance nine
Nawa maryam ciki kowa yajuya yana dagash da mamΓ ki
Cikin kuka maryam tace a a wallahi karku yarda dashi yafada kawai Dan yataimakeni
Asalima ranar da abin yafaru yaya bayagari yayi tafiya zuwa America
Dagash yadaga hanu daya sama yace na rantse da Allah ninawa maryam ciki
Kan mummy yakasa daukar tention kawai saitazube kasa asume
Next page
Your comment is needed
Much love to your nice comments dear
*Signed by ummu afan* π»
[15/07, 1:13 PM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
ππππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
*Dedicated to sis su'adat kawar amana ina alfahari dake sosai sis inajin dadin kulawarki sosai aikaina Allah yakara dankon zumunci sosai*
_Wannan sakon gaisuwa ummy Al'amin dagash group admin Allah yabaki lafiya yasa kaffarace
Mun ba dadi da rashin lafiyarki sosai_
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 6β£1β£to6β£5β£
Dagash yayi saurin taro mummy
Anty asiya dake kuka kaman ranta zai fita tayi saurin nemo ruwa takawo mishi
Kan mummy na cinyar dagash yace kiyi hakuri mummy yazama dolene nafadi gaskiya
saboda Nima ba ason raina hakan yafaru ba kaddarace
Kafin yakara magana Aymana ta taso taje gurin daddyn ta tace kagani ko daddy kunga abinda muke fada muku daman munfada adakinsa take kwana baka yarda ba
Wani razanar nan tsawa taji andaka ma dagash cikin tsanin bacin rai yace duk abinda yafaru aikece sila sanadiyar abinda kika aikata hakan yafaru
Mummy ce tasake fashewa da kuka ta kalli daddyn Al'amin cikin kuka tace alhaji kaga abinda duk yadawo kaina ko
Kaga yadda Allah yake al'amarinsa ko tabbas nayarda ba maiyi sai Allah
Ashe abin duk a gindina yake Ashe duk kaina zai dawo tasake fashewa da kuka tace YAYANA da DANA
Sai kuka duk wadda kefalon bawanda mummy bata bashi tausayiba sai anty da zuciyarta yadake sosai
al'amin yace mummy pls stop crying Nima bayadda kike zatobane mummy dalilin maryam nagyara rayuwata maryam kaddarace ki yarda Dani
Kallon takaicin da daddyn dagash yake mishi yasa dagash yaji badadi yace dadi Ba laifi nabane daddy ya daga mishi hanu ba abinda za akacemin
Amanar Dana baka kenan asha baza iya rike min amana ba kenan Ashe zaka iya aikata hakan akan kan yar ywarka shafa'atu ko bazaeefa kenan
Dagash ya gigice saboda yaji maganar daddynsa ba dadin sauraro
Daddyn king yace ya isa haka yaya
Prince yimin bayani meyafaru kafin faruwar hakan
Nan yakwashe komai yafada musu
Ran daddy king yabaci sosai ya kalli aymana yace bazan tsine mikiba kar abin yafi haka amma duniya ce ummu aymana kije gaki gata ya kalli mummyn aymana cikin bacin rai yace kin bata min yarinya bazan taba yafe miki ba
Aymana cikin kuka tace wallahi daddy Nima ba laifina bane mummyne tace kaini gidan boka wai akan amin maganin da zaisa
Yaya yadaina sauron kowa saini sai yadda mukayi dashi
Yazama ko mummynsa yaji bayason gani
Saini
Daddy da alhaji Dan asabe suka dau salati daddy ya kalli dagash cikin bacin rai yace AL'AMIN ina maka umarni da kasaki Aymana yanzu anan umarni nabaka ba yardaka nake nema ba
Dagash ganin Daddy King baitaba kiransa da sunansa na yasa yasan tabbas dagaske yake
Daman shima hakan yake nema
Yace nasaketa saki daya Aymana ta rusa ihu tace daddy Dan Allah kayi hakuri yamaidani wallahi ina sonshi
Daddy king yace Allah yamaka albarka
Sai yanzu Alhaji imam yayi magana saboda halin dayake ciki
Yace bawanda yayi sanadiyar komai saini Al'amin baka da laifi
Ko bakai ka aikata hakan ba dama sai ninkin abinda na aikata yadawo min
Sai banso yadawo min akan kamillaiyar 'ya ba amma ba komai Allah yafimusanin abinda yasa yayi hakan nayi nadamar abinda na aikata wallahi
Nayi danasanin abinda nayi gashi yau komai yadawo minsabo 'yata da Dan kanwata Wanda nafiso a rayuwata Allah kenan
Shiyasan hikiman yin hakan
Alhaji sudais yace kayi hakuri abokina Allah yagafarta mana gaba daya
Anty datake aikin kuka maryam kwance akan cinyarta zazzabi yarufeta sosai kuka kawai suke sosai
Anty ta daga kan maryam ta ajiye a kasan carpet ta karasa gaban mummyn dagash
Ta tsunguna tace hajiya ina fatan yanzu kinga matsiyata da dabbo binda idon ki
Na tabbatar yanzu dai bawani sauran bashi tsakanin mu donkinga matsiyatan da idon ki
Anty na kuka tace ina fatan kinga asalin maryam kice asalinta kinci mana mutunci kintozartamu
Duk saboda muna talakawa marasa abin duniya marasa gata kin kyamacemu kin nuna muba mutane bane kece kawai mutum
To ina fatan a yanzu kinga matsiyacin uban maryam dakika nema ko
Mummyn dagash dai bata iya magana saboda kuka da danasanin abinda ta aikata wa anty da maryam Ashe maryam jininta bata saniba take ta cin mutuncinsu
Anty ta kalli hajiya zabbau tace kekam ba abinda zance miki tunda ga sakayya ma kinfara gani
Ta karasa gaban daddyn Al'amin ta durkusa ta fashe da kuka tace alhaji ba abinda zamuce dakai sai Allah yasaka maka da gidan aljanna
Kasomu a lokacin da ake kyamarmu ka kaunace mu kasu turta mu daga ni har 'yata
Wallahi wallahi alhaji ban ji zafinka ba kokadan saboda kowaye Yakama matarshi da wani a haka hukuncin da kayanke zai yanke
Kayafe laifukan Dana maka a iya zama dakai mungode sosai Allah yakara arziki
Daddy hawaye ne ya sauko mishi yana ta kokarin kar hawayen ya sauko amma ina yariga yasauko yayi rashin mata tagari yama kasa magana
Kaman daga sama anty taji anacewa Yakama ta mutashi muje Dan saura awa daya a daura auren
Anty tajuya takalli me maganar auren taga daddyn King ne tace aure kuma Alhaji
Yace a ai babu Wanda ya isa ya hana daurin auren nan sai Allah saboda kutashi mutafi
Anty tayi murmushi tace kayi hakuri alhaji za a iya daura na sauran amma banda maryam bazan taba yarda da auran ta da al'amin don dama Ba ason raina Dana mummynshi za ayiba
Idan har auran kukeso kuwa maryam tace kuna da ikon aura mata koda driver zan amince amma ba al'aminba
Cikin tsanain gigicewa Al'amin yace Haba anty mena miki haka da zaki rabani da rayuwata lokaci daya
Anty tace baka min komai Ba al'amin amma inason na nunawa mummynka muma muna rana talaka ba matsiyaci bane shima akwai abinda za a nema agurinshi har akasa samu Dan kudi basa sayan komai
Ta kalli yaya Abdul tace tashi muje ka kaimu gida gurin innata naganta na nemi gafararta
Daddy King yace a a maryam kibari akaiku anty tace kayi hakuri zamuje kawai basai ankaimu ba
Nan daddy yayi magana yace muje nakaiku gidan da kaina anty zatayi magana yadaga mata yace banason musu maryam
Badan anty taso ba ta tasa hanu tadaga maryam a kasa sai anty asiya tayi saurin tayata suka fita zuwa motan Daddy
Zayyad yace daddy suhaila fa bazatasan abinda ta aikata illabace itama harsai yasaketa
Idan aka yi haka andaure mata gindi tayi ta shirme kenan
Alhaji Dan asabe ya kalli dagash yace al'amin mekakejira da suhaila ne
Daddy king yace abarta ai ataga aya idan me hankalice
Alhaji Dan asabe yace no baza ayi hakaba Yakama ta duk a hukuntasu
Saboda haka kasake ta nace
Al'amin dakanshi yagama daukan zafi akan kalaman anty datace bazata aura mishi maryam taya zaifara rayuwa ba maryam
Yana jin umarnin daddyn zayyad akan yasaki suhaila
Yace nasaketa saki daya
Suhaila tafashe da kuka takaici daddyn dagash yace duk abinda kukasa ya aikata bashine masalahaba
Da kunbarshi kawai ya dau hakuri aishi babbane koba komai watarana rana komai zai wuce amma tunda haka takansance sai muce Allah yakiyaye gaba yakalli mummy yace Aisha kiyi hakuri kitashi kibar kukan haka duk abin da zaifaru yariga yafaru ba yadda muka iya
Kinga koba komai kindau darasi akan rayuwa kitashi amaidake gida
Ya kalli daddy king yace kutashi kuje nasan yanzu bakin sunkaraso
Zanje nadawo yakalli alhaji imam yace tafiyan nan hardaku Yakama ta kutashi mutafi
Alhaji imam da alhaji sudais suka tashi jiki a sanyaye suka yi gurin motarsu
Mummy dai ba bakin magana Shafa'atu ta taimaka mata suka tashi sukayi motar dagash Wanda acikin zai maida mummy gida
Dagash yashiga motar yakasa tada motar zayyad ne yakaraso yace koma kujera kawai barin yi driving din
Dagash baiyi musuba Dan yasan bazai iya tukawa ba
Yaya Abdul shiyake nunawa daddy hanya harsuka iso kofar wani gida Wanda kaf layin nan ba makaskanci a cikin jerin gidajen layin
Dai dai lokacin da yaya nura yayi parking shima a mashin dinsa tsohuwa tasha wahala sosai
Yaya Abdul dake cikin motar daddy yace alhamdullila ga yayan ma yadawo
Cikin murna anty takama maryam suka fito daga motar
Ganin motoci a kodar gidansu yasa yaya usman yatsaya
Ganin wacce tafito cikin dankareyiyar mota yasa yakame agun
Yace maryam itama cikin kuka tace na'am yaya zata tsuguna yayi saurin dagota yace a a mushiga ciki maryam
Ganin yaya Abdul ya fito tare da alhajin dabai sain kowayeba
Yasa yace a a Abdul Ashe tare kuke
Yace ai dabaki ma dayawa
Yaya usman yace a sannunku da zuwa bara amuku iso yakarasa cikin gidan
anty suna cikin gidan taga wata mata wacce bata San ko wacece bace
Matar nan tace a asannunku da zuwa baki mukayi
Jin magana yasa sauran matan suka firfito ganin maryam dawata balarabiyar budurwar yarinya
Yaya aliya dake jinyar inna itama tafito ganin maryam taganeta cikin tsananin mamaki tace maryam
Anty takarasa ta rungume yaya aliya tana kuka itama yaya aliyar kuka take yi
Maryam karama itakanta abin yabata tausayi
Cikin kuka anty tace yaya aliya ina innarmu yaya aliya ta nuna mata cikin dakin
Anty tashige duk yan gidan sunji mamaki jin cewa wai maryam ce wannan tadawo balarabiya haka
Wasu kuma suce Ashe yawon karuwancin ya karbeta
Yaya aliya ta kalli maryam karama tace karaso mana 'yata koba ' fada minba ke yar maryam ce
Maryam tarungume yaya aliya tana kuka itama nan itada yaya aliya sukayita kuka
Anty najikin inna tana kuka Dan inna batada maraba da gawa
Tace innan mu kitashi ga maryam dinki tadawo inna kitashi Dan Allah
Yaya aliya suka shigo tace ai tana jinki baki ga tana binki da idoba
Maganace bazata iya ba
Sai ganin hawaye sukayi yana sauka daga fuskar inna
Yaya aliya tace Inna dole kiyi kukan farinciki don mucire tsammanin sake ganin maryam araye
Kafin wani lokaci anwa su daddy daddy shinfida
Anfito da Abba ma danshi jikinsa yafi na inna sauki
Nan da nan akabayyana komai gaskiya tayi halinta Abba yafashe da kuka yace ina maryamun take matso kusadani maryam
Cikin kuka anty takarasa gabanshi yadafa kanta yace maryam da ina da lafiya Dana saka gwiwo wina akasa nanemi gafara
Dan Allah maryam kiyafemin yanke hukunci cikin fushi danayi
Alhaji imam yasake magana yace Dan inasake Neman afuwa abisa lafin Dana aikata nine silar komai
Abba yace ba komai Allah ya yafemana gana daya
Kaddarace Allah ya Riga ya rubuta
Yaya usman ya kalli anty yace maryam kiyafewa alhaji
Tunda Allah ma ana masa lefi yana yafewa daddyn al'amin ma yace hakane maryam kita maka kiyafe masa kodan yardake tsakaninku
Cikin kuka anty tace shikenan na yafe mai Allah ya yafemana gaba daya
Wani sanyi da dadi da kuma rashin nauyi alhaji imam yaji yaziyarce shi Wanda yadade rabonda yaji hakan a rayuwarsa
Yayi hamdala wa ubangiji
Yasake godiya agaresu gaba kidaya
Yaya nura yace maganar auren yarinya kuma a daura kar a daga Allah yasanya alkairi
Yaya Abdul yace Nima abinda Nagani kenan
Shiyasan mutuncinta zai riketa bisa amana Allah yabasu zaman lafiya
Anty tace ina rokon ko andaura tarewar abarshi bayanzuba
Daddyn al'amin yace ba komai maryam ai auran shine mai wuyan tarewar ko yaushe sai ta tare
alhaji imam yace wa yaya usman idan babu damuwa ina son acikin satin nan zan fitar da su Abba da inna jinya kansa waje
Daddyn al'amin yace wannan yayi hakan ma Allah yasaka da alkairi
Yaya usman yafasheda kuka yace anya innanmu zata tashi kuwa jikin nata yayi tsannani sosai
Alhaji imam yace ai rayuwa da mutuwa duk suna hanun Allah ne ballema irin wannan ciwon a kasan waje ba wani bu bane dazai gagaresu da izninin Allah
Ya Abdul yace mungode Allah yasaka da alkairi yajikan mahaifa badan sun mutuba
alhaji sudais yace sai mu hanzarta muje a daura auran saboda lokaci na tafiya
Yaya usman yace to barin shirya Dan dawowata daga kasuwa kenan ma
Bayan fitansu ne yaya aliya da anty sukayi ta bawa maryam hakuri anty tace maryam yakikeso nayi ne Nima sanin kanki ne ba ason raina hakan zai faruba
Maryam cikin kuka tace anty wallahi a halin yanzu ba mahalukin da na tsana irin yaya Al'amin bana son ganinshi Dan Allah anty karkibari a daura amin aure dashi wallahi bana sonshi
Yaya aliya tace Haba 'yata kiyi hakuri dan kinga ai bashi akaduba aka yarda da maganar auren ba mahaifinsane yadda ya rikeku
Ba abinda zamu ce dashi sai dai Allah yabiyashi da gidan aljanna
Dan haka dole kikoyi son al'amin a ranki kodan babanshi yadda ya rikeki
Haka maryam ta yita rera Dan kukokinta mai bantausayi bazasu fahimci yadda take jimabane aranta
Karfe biyar da rabi na yamma dai dai
Akashaida daurin auren AL'AMIN SU'AD DA MARYAM AHMAD DA KUMA ZAYYAD DA AMARYASA RAHMA
DA FAISAL DA AMARYASA SHAFA'ATU
Masha Allah ya halarci dumbin jama'a Wanda ba a taba tsam maniba ma yazo
Dagash baitaba zaton dashi za adaura ba jin auranshi akafara daurawa yasa ya sauke ajiyar zuciya yaji kaman an mishi albishir da gidan aljanna yayiwa Allah godiya daya mallaka mishi maryam a matsayin mata
Zayyad ne ya karo gurinsa yana tsokanarsa yace ango kasha kamshi
Dagash yayi murmushi yace wa ni kudai Kune Kunsha kamshi saboda yadda naga kanku na rawa saikace farin shiga
Zayyad yafashe da dariya yace za abi na Allah ai farinshigan ne
Dagash yace a fannin sunna ba
Zayyad yabata rai yace dadina dakai Dan iskane wallahi kai ana sallah ai ba a magana
Faisal dake bayan zayyad yace fada mishi dai Dan dama dai shikadai yarage da Vicky nikam wallahi nadade da rabuwa da wannan harkar
Dagash yace karma karabu da harkan zanyi maganinka ne ai tunda gashi nabaka kanwata
Zayyad yafashe da dariya yace Allah yabaki hakuri da na baka tawa kanwar amma baka rabuda Vicky ba
Faisal yace fada masa dai
Dagash zaiyi magana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 18