bazaka fada min abinda yake damunka ba duk karame sai kace wani majinyaci
Al'amin dake gefe shima haba dad kasani mu a damuwa nima bantaba ganinka cikin wannan yanayinba
Dad yayi murmushi yace son karku damu akwai maganar danakeson muyi amma saina dawo daga abuja insha Allah zanfada muku koma menene
Dagash yace wa dad promise
Dad yace ye I promise dagash yayi murmushi yace to sweet mom kinji kina shaida idan yadawo zaifada mana koma menene tace ina shaida kam Allah yadawo shi lafiya muna nan jiranka
Dad yayi murmushi yaja hancin mum yace kajita kaman dagaske abinda sai da kika hada da danki kafin zaki San komai
Mom tayi murmushi tace ai dole da ban fada mishi da zaka ce zakafadane ai haka zaka ta damuwa muma mudamu
Dagash ya ce dad muje nakaika airport din idan kabiyewa momy saitasa ka makara
Dad yayi murmushi yace kwarai kuwa Son kaman kasani
Yace bara nayiwa ummynku sallama dagash yace dad ina waje
Dad yashiga gurin hajiya zabbau yanashiga yaganta kan bed dinta haba amaryata bazakifito kimin sallamaba
Tayi wani fari da ido tace ainaga kana tare da gimbiyarka ne shiyasa
Yayi murmushi zabbau Wai yaushe zaki rage kishin Aisha a rankine itama fa tana kishin sai dai tafiki wayo da wayewar dannewa
Kekuma kike fito danaki afili
Hajiya zabbau tace ai daman nasani sai ka kareta tunda bataba gold
Yayi murmushi yace naji yanzu dai zuwa nayi muyi sallama gobe zandawo kina bukatar wani abu
Tace a tace ina bukayar kudi kasan gobe asiya zata koma zan saya mata tsaraba
Murmushi yayi yaciro bandir yan dari biyar yabata
Yasan kawai magana take nema tasan kudin da yaba asiya jiya
Yafita tace sai kadawo yace Allah yasa
Yana fita yaga mummyn al'amin a falo tana jiransa brief din tadauka ta ratauy suka fito zuwa wajen mota tamishi adawo lafiya
***"
Karfe hudu dai dai dady suka sauka a air port
Waya yayi daman aka kawo mishi mota daga Villa
Wata haddadiyar mota his excellency ya ai ko maidashi
Yashiga da kanshi ya tuka zuwa mararraba
Dan idan yabiye na alhaji dan asabe bazasuzo
Alhalin shikadai yasan halin dayake ciki akan baiwai Allah nan
Next page
Your comment is needed fan's
More comment more typing
*Signed by ummu afan* π»
Tofa yau ga
.
[26/06, 11:54 AM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
πππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUSE WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
I DEDICATE THIS PAGE TO YOU sis Fatima sunusi sanata ina jin dadin comment din ki wallahi Allah yabar zumunci keep it upβ€
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 7β£
Daddy na isa kauyen mararrab sai yayi tambaya da a nuna mishi gidan mai gari
Har kofar gidan aka nuna mishi yayi parking yafito ya roki Wanda yaturo da ya taimaka ya kira mishi maigarin acikin gida
Yaron yashiga cikin gidan Jim kadan yafito yace yace yana zuwa dady yace yauwa yaro nagode ko zogawannan ya ciro five thousand a aljihunsa ya bashi sosai yayi ta godiya daddy abin yabashi mamaki wannan godiya haka saikace Wanda akaba million biyar danshi ya dauka a matsayin kudi
Maigari yafito daddy yayi nisa wajen mamakin Ashe haka talaka wasuke idan kamusu alkairi harcikin zuciyarsa yaji dadin adduar yaron nan sosai shika dai yayi murmushi
Maigari yamishi sallama ganin daddy babban mutum ne yasa ya mishi kwarjini ya mishi iso cikin gida
Daddy baiyi musuba dan yanason suyi maganar nutsuwa ne
Har dan karamin soron gidan megari yashiga dashi yasa aka kawo mishi sallaya aka shimfida mishi akan taburmar dayake shimfede a zauren gidan
Sosai daddy yake mamakin kanshi tunda yake a rayuwarsa yauce rana tafarko daya taba shiga gida makamancin wannan a rayuwarsa
Maigari suka gaisa da daddy yace sai dai kuma banshaida kaba alhaji
Daddy yayi murmushi yace gaskiya kam ba lalle ka sanniba
Nan dai daddy yafada mishi game zuwanshi dakuma sunanshi da akafisani a duniya
Mamaki yacika megari yace yanzu alhaji su'ad babangida da mukeji a labarai da jaridu shine agidana a zaurena
Daddy yayi murmushi yace gaskiya ne nine
Maigari yace ikon allah
allah yayi Gaskiya yanzu kuma akan mace kazo har wannan kauyen namu alhaji
Alhaji yayi murmushi yace toya za'ayi ai basaudayaba ba sau biyu ba munzo nida abokina amma taki kula mu ita aganinta ma cutarsu zamuyi
Maigari yace toya akayi kuka gane gidan data koma
Dad yace ai lokacin da mukadawo na farko nida abokina
Muka gurin datake a kulle sai muka tambayi wasu mutane sukace wallahi basusan inda takoma ba Amma dai zasu bincika mana idan sunsamu labarin inda suke zasu sanar damu na dauki number waya ta nabashi
Kuma da ikon allah wannan bawan allah su suka binciko mana inda takoma munje munje yakai sau biyar amma basauki abin taki saurarenmu ma to shine nace zanhada manya kamarku ko allah zaisa tagane da alkairi nake tafe bada sharriba
Maigari yace Hakane allah ya tabbatar da alkairi yanzu zan aika akirata
alhaji su'ad toshekenan maigari nagode sosai allah yakara girma
*******
Maryam zaune tana musu tankaden tuwo atsakar gida cikin katon hijabinta
Sallama akayi agidan wadanda suke kusa da masu sallama suka amsa yace wai inane dakin Maman maryam akace Gashi can inda waccen yarinyar take tankade
Yakarasa gurin maryam yace sannu tace yauwa yace wai Maigari yana kiran mamanki yanzu
Maryam cikin tashin hankali tace megari kuma anty dake cikin daki tafito tace kai wakekirana yace megari tace megari kuma meyafaru kuma
Yaron yace nima dai haka yace inzo inkiriki
Maryam tace anty munshiga uku allah yasadai bawani sharrin aka miki ba kamar yadda akasaba
Anty tayi murmushi tace karkidΓ mu maryam imma hakan ne yazanyi da mutane allah shizai sakamana
Tace wa yaron jeka inazuwa
Maryam ta tashi tabi anty daki tana kuka tace anty kinga irin abinda nake fada miki ko wallahi anty kiyarda kawai kiyi aurenki shine mutuncinmu
Amma mutanen gidan ba abinda basacewa waizaman kanki kikeyi
Anty tashare hawayenta tace to maryam yazanyi duk wadanda suke sona da aure cewa suke bazanje musu dakeba kinga kuma nibazanyi aure nabarki ananba bazai taba yiyuwaba
Maryam tace to anty ki amince da alhajin mana kawai dan Allah anty kibashi dama shifa yace zai rikemu duka anty
Anty murmushi tayi to maryam ya kikeso nayi nidaman nasan wannan alhajin bada gaske yakesona ba da dagaskene ai dazai dawo
Daman dai yayi niyyar cutar da mune kawai ai daman duk abinda nake yi inayi ne dan nagwada gaskiyarsa
Kuma kinga dayake daman bada gaske yakeba ai bai sake waiwayar nan dinba
Yanzu dai kizauna zanje nadawo maryam ta girgiza kai tace ai bazan iya zama ba anty muje tare kawai
Atare suka fito suka kullo kofarsu
Mutanen gidan suka fara gulma hade da shewa
Mutum daya ce batayi magana kuma. Ita tace to Maman maryam saikun dawo
Antyn maryam tace to zainaba tabata ajiyar key dinsu
Itama zainaba tana zaune agurin iyayenta zatayi sa'a da antyn maryam allah ne yayi mijjnta rasuwa shine tadawo gidan kiyayenta da zama
tana da yara biyu namjin dagin ubansa sundaukeshi sai macen wacce itace babba itakuma zata dan girmi maryam dashekara daya dan ita shekarunta shashida
amma tunda su maryam suka dawo gidan suka kulla kawance da yarinyar zainaba mesuna rahmah sosai sun shaku a iya zamansu dasu rayuwarsu Maman rahama wato zainaba yagyaru daga kazamai zuwa masu tsabta dan maryam dakanta take taya rahma wankin kayanta ta tayata tsifar kai to Maman rahma ganin irin sonda maryam takewa 'yartata Yasa itama suka saba da anty duk da kuwa mutanen gidan basa kaunasu anty acewarsu zaman kanta take to sudai su zainaba sun toshe kunnensu idan zasu fita haka suke basu ajiyar tana sonsu tsakaninta da allah bata kaunar abinda sauran yan gidan suke musu
Su anty suna isa gidan Maigari suka yi sallama sallamarce ta makale musu saboda Wanda suka gani
Dad yayi murmushi yace kinyi mamakin ganina ko ai nafada miki zandawo
Ya kalli maryam yace zo nan 'yata kizauna kusada daddy
Wannan Kalmar da dad yafada bakaramin dadi yawa maryam takarasa kusada dad tazauna a darare tana cewa ina wuni alhaji
Dad yayi murmushi yace bazan amsa gaisuwarki 'yata harsai kinkirani da daddy
Maryam daga ido takalli anty kafin maryam tayi magana anty tace daman Kaine megarin kenan kafin yabata amsa yasan magana tafada mishi
Sai maigari yayi sallama yashigo a a Ashe kunzo anty tayi saurin samun guru tazauna tagaida megari ya amsa yana tambayarta gida tace alhamdullilahi malam
Yace Masha Allah
Anty takasa hada ido da daddy tun bayan tambayar rainin data masa duk saitaji badadi ai koba komai yahaifeta kuma Wanda yace yanasonka ai bai canci haka da ga garetaba
Maigari ne yakatse mata tunaninta
Yafara mata bayanin dacewa tasan Alhaji yayi maganar yana nuna alhajin
Saida tadago ta kalli gefen da Alhaji yake aikuwa suka hada ido karaf
Maigari yacewa maryam tashiga cikin gida zai magana da mamanta maryam tace to
Ganin kartaji kunyar yarinyarta Yasa megari ya aika maryam cikin gida
Anty Tayi saurin mayar da kanta gefen maigari bayan fitar maryam
Megari yasake tambayar anty akaro nabiyu tace a nasanshi
Nan megari yashiga mata bayanin komai a tsanake
Anty tace naji malam dan Allah ina rokonshi daya bani lokaci nayi shawarar tukun
Megari yace Hakane amma inason duk shawarar dazakiyi kizauna kinutsu kikarbi wannan bawan allah
Kiyi aurenki kihuta da maganganun mutane akanki
Antyn maryam tafashe da kuka tace wannan dalilin Yasa nake gudu wa duk wani 'da namijin dayace yanasona saboda nasan ballebane idan yaji labarina ya yarda ya aureni
Dad yace haba kekuwa ai ba abinda zakifada min dazai sa naji bazan iya aurenkiba
Niban nemi kifada min komaiba inasonki haka
Megari yace a a alhaji dole kayi hakuri tabamu labarinta saboda halin rayuwa kuma itama zata fi samun sakewa agidan aurenta
Alhaji yace Hakane gaskiya amma indan tanine
Bani da damuwar hakan ni itanakeso ba asalintaba
Megari yaduba agogo yace karfe biyar na yamma yanzu kibari zuwa gobe kizo ina nemanki dan jin cikakken tarihinki da asalinki
Anty tace insha Allah zanzo Allah yakaimu goben
Sukace ameen megari yace barin Baku guri ko yashiga cikin gida
Dad yace duk da rashin sanin sunanki kinki kifada mana sunanki ina rokonki da kitaimakeni kisanar da ni sunanki
Anty tayi murmushi ganin yadda yakeyi saikace wani yaro abin yabata dariya
Batasan lokacin datace maryam ba
Dad yace maryam kuma ke maryam 'yata ma maryam
Anty tadaga kai alamun a hakane
Yace masha Allah sunan yadace dameshi
Anty tace nagode alhaji zamu koma gida saboda magriba yafara karatowa
Daddy yace hakane to nizankoma cikin abuja nakwana amma insha Allah gobe karfe takwas ina nan Dan matsayina a gurina
Murmushi anty tayi tace Allah ya nuna mana goben
Tashiga cikin gidan megari suka gaisa da mutanen gidan ta kira maryam suka fito
Suna fitowa suka ga alhaji da mwegari aguri mota megari ya mishi rakiya
Daddy ya kallo su anty dasuke fitowa yace wa maryam 'yata sallama murmushi maryam tayi to sai dasafe alhaji
Murmushi daddy yayi yasan sai a hankali zata saba da kiran shi da sunan da yadace
Anty maryam sun isa gida ta ce maryam karbo key a wajen maman rahma
Maryam taleka dakinsu rahma tace wa maman rahma
Mama key dakinmu zainaba tace yauwa maryam lafiya dai ko da kuka je gidan megari
Maryam tayi murmushi tace lafiya kalau wallahi mama
Maryam tace mama wai rahma bata dawoba har yanzu
Maman tace wallahi maryam aikinsan halinta idan an aiketa kaman an shuka dusa
Maryam tayi murmushi tace yanzu zata dawo mama ai unguwar ne da nisa
Bayan sallar isha ne maryam da anty suna dakinsu saboda ruwan da ake shekawa agarin ga sanyi maryam a anty sun kwanta abinsu maryam dai bacvi yayi awun gaba da ita amma anty kam bacci ya kaurace mata
*****
Anty asiya tana zaune tagama shiryawa zasuje gidan yaya al'amin acan zasu wuni yau saboda gobe zata wuce zari'a
hajiya zabba'u kallonsu kawai tana kebe baki tace nifa wallahi dazakiji shawarana da kunbar zuwa gidan mara kunyar yaron nan
Anty asiya yanzu ummy bakiji abinda ringa fada miki ba kenan
nazeefa tace wallahi nima bana jin dadin abinda ummy takeyi agidan nan
Afanan tace kuma ummy baki ganebane halin yaya ne haka abin nashi tashi tashi ne amma fa kebaya miki komai ma wallahi akan yadda yakewa mutane
Hajiya zabbau tace aisai kuyi tunda kunfi ganin mutuncin shi akan nawa duk abinda nakeyi ai donku nakeyinsa
Asiya tamusu alamun suyi shiru suka mata sallama suka fita
Suka ga mummy a falo suka gaisheta asiya badai tafiyaba
Asiya tayi murmishi tace a a mummy zamuje gidan yaya ne a can zamu wuni
Mummy tayi murmushi tace yayi kyau ina kishiyar tawa kuma kikabarta
Naxeefa tace ana hanun afnan yanzu zasu fito
Bata rufe bakiba afnan tafito dauke da shukrah yarinyar anty asiya yarinya kyakkyawa ga wayo shekararta biyu kenan yanzu
Mummy tace kai wannan irin kyau a kikayi gwamma atafi dake kar alhaji yazo yace saike
Takarasa maganar tana murmushi cikin wasa tanawa shukra
Afnan tace. ai kuwa mummy dake da ummy saidai kuyi hakuri danso kam daddy yafison shukra mummy tayi murmushi takalli shukra tace aikuwa baki isaba kinemi mijinki tunwuri
Sukayi dariya gaba daya suka wa mummy sallama suka fita
Suna isa gidan Al'amin sukaganshi yana shirin shiga mota yaga motar asiya sai yatsaya
Suka fito cike da farincikin samunshi agida suka karaso gurinshi suna murna yadan saki ranshi Dan yana balain son kanwarshi asiya sosai
Hanu yamika zai karbi shukra yace my girl zogurin daddy tana jin yace dady taje gunsa yadauketa yana mata wasa
Anty asiya tace yaya munzo mu wuni makane kasan gobe zan koma yace nasani kin kyauta
Amma zanje nadawo kushiga ciki ganin zuwa to yaya adawo lafiya yace Allah yasa sis
Yayi gaba binshi afnan tayi murmushi tace anty naxeefa kinga abinda yafaru kuwa ko takanmu baibiba
Anty asiya tace to ya San ranku ai yaya nawane
Naxeefa tace kwarai kuwa Anty asiya wallahi inbakeba wa ya isa yaya yawa murmushi haka inbakeba
Anty asiya tace aurekenan mai daraja saboda auren da kainane yake ganin mutunci na fiye danaku
Saboda haka kuma dazarar kunyi aure murmushi kawai sukayi suka karasa cikin gidan suna shiga suka ga suhaila kwance a falon tana kallon TV
Da sallama suka karasa cikin
Suhaila tadago kanta takallesu sai saita cigaba da kallonta batare da ta cedasu ufanba
Asiya suka kalli juna itada su afnan
Suka nemi guri suka zauna
Asiya tace sannu da gida suhaila
Suhaila tace yauwa sannunkufa Dan ita tatuna da yadda mijinsu ya wulakanta su yaki basu cake amam yabawa asiya takaicin hakan yasake kama suhaila tasake hade rai
Shukra da rigima taje kusada da suhaila tana so tadauki remote tayi wasada shi suhaila ta kalli su afnan tace kai kuzo kukamata mana bana son hayaniyafa
Asiya tace to Allah yasauwake naxeefa tace amin
Afnan takaici yakamata taje takamo hanun shukra suka dawo
Aymana tashigo falon suka hada dasu
Tace a a Mayan baki ne agidan namu su asiya Ashe baki wuceba
Asiya dasu aymana suka sake kallon juna ganin itada suke tunanin yar uwarsuce zata karbesu hanu biyu sai gani sukayi ma tane mi guri ta zauna tacigaba da charting abinta
Naxeefa tace anty asiya kina ganin menake gani kuwa
Asiya tace ina gani kuwa naxeefa
Afnan tafashe da dariya duk akajiyo ana kallonta su suhaila da aymana suka tsargu da dariyar ta
Anty asiya tace lafiya kekuma kike dariya afnan tace wallahi anty game din ne ya mugun bani dariya
amma barin kawo mana lemu musha ta tashi ta je tafkeken katuwar fridge takwaso musu drinks sosai
Ta ajiye musu ta je kitchen din gidan tasamu masu aikin tace Ku kawo mana snacks suka amsa mata da to
Aymana ta kalli drinks din a afnan takwaso tace ke afnan wannan ma ai almubazzarancine Baku uku bane zaki dauko muku sunfi takwas
Afnan tace ya isa haka Aymana tunda muka shigo bawacce ta San da mutane agurin to naga muba baki bane idan munga dama musa fridge din a mota mutafi dashi inaruwanki bakina da naki a dakiba kinga dakin kinki mukaje muka bude muka debo
Na Dan uwanmu ehe zatacigaba da magana Aymana tace afnan nikikewa rashin kunya haka Dan baki da kunya to barin fada miki asiya itace sa 'ar yita bakeba
Da harzaki bude baki kice. aymana saikace wata sa'arki shasha kawai
Afnan zata rama zagin anty asiya tadaga mata hanu tace karnasake jin bakinki afnan bata girmekiba ne
Afnan tayi shiru amman ta narkawa aymana harara
Itadai suhaila bata ce kaomaiba tana kallonta ne kaman bata San da mutane a falon ba
Can wajen karfe biyu saiga dagash ya shigo haba nan da nan su suhaila da aymana akafara gyara zama yana shigowa yace wa asiya kutashi mushiga ciki
Sukatashi sukabi bayan dagash
Takaici ya hanasu aymana magana
Aikuwa afanan bayan dagash yashige cike ta fashe da dariya wanda duk sunsan ma'anar dariyar ta
Suhaila tace lalle ma mutumin nan yacika Dan wulakanci wato yaja kannanshi sunyi cikin daki muka ma muyi tazama anan daman aikin mune ko
Aymana tsaki tay tarasa bakin magana
******
Washari da safe karfe takwas darabi daddy ya isa kofar gidan megari
Aykuwa megari yakarbeshi sosai ya aika akira mishi anty
Maryam tace anty yau kam basai najeba tunda naji lafiya har hankalina ya kwanta sosai
Antyn maryam tace a a aikuwa Yakama kizo mutafi Dan kema yau kisan wacece ke
Maryam taji gaban ta yafafi tace anty kina nufin yauzaki bada labarin asalinmu
Yau zansan dangina da mahaifina anty ta daga tare da shafa kan Maryam din tace maryam inason duk abi da kika ji kiyi hakuri da rayuwa kinji
Maryam jikinta hya matukar sanyi duk da karancin shekaru na maryam hakan bai hanata zargin wani abuba
Sun isa gidan maigari bayan sungaisa anty ta gaida daddy ya amsa fuska cike da farin ciki maryam ma tagaishesu suka gaisa gaba daya
Megari yace to malama muna saurarenki
Anty ta kalli maryam ma itatake kallo
LABARIN ANTYN MARYAM
Nidai asalin sunana MARYAM
Tace mu yan asalin garin medugurine acan wani kauye waishi gwaza
Mahafina yana da mata hudu kuma kowacce mata tana yara sunkai gomasha amma banda amaryar
Saboda haka gidanmu babban gidane sosai
Inna halima itace amarya agurin mahaifina kuma itace me yara bakwai cas biyar mata biyu maza
Nice karama acikinsu duk yayuna suna tasowa ake musu aure
Saboda haka al'adar garinmu yake yarinya bata wuce shekara hudu an aurar da ita duk acikin yaran gidan mu yaran dakin mu munfi kyau sosai saboda duk innar mu muke daukowa
Saboda haka yayu na tunkai sukai suke shekaru sha hudun suke da tsayayyun mazajensu suna gama primary school za a aurar dasu
Sabanin sauran yan matan gidan da ake musu hadin gida saboda rashin mane ma wannan dalilin yasaka tsanar innar mu acikin kishiyoyinta
Hakan baya damun inna saboda ita da Allah tadogara
Ba abinda yafi dafawa mutanen gidan hankali sai lokacin da innar mu ta haifeni a lokacin yayuna biyu sunyi aure saura biyu mata biyu maza
Allah yayi mun kyau da tsarin halitta ga uwa uba farin jini tun tasowata nake da farinjini kowa maryam kowa maryam
Dan sunan da mahahifina yasaka min kenan
Shima mahaifina Allah ya samishi kaunata fiyeda sauran yaranshi kakaf yafi nunamin so sosai hakan yasa wasu daga cikin yan uwana Wanda muke uba daya suka tsanane sosai
Next page
YOUR COMMENT IS NEEDED FANS
MORE COMMENT MORE TYPING
*signed by ummu afan* π»
[26/06, 11:54 AM] SIS UMMY: πππππππ
π‘π‘π‘π‘π‘π‘
πππππ
π‘π‘π‘π‘
πππ
π‘π‘
π
*BISSIMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM*
*Ummu Afan the Gorgeous writer of the year ,Author of 'YAN BIYAU NE &AKWAI LOKACI*
πGORGEOUSE WRITERS FORUMπ
π G.W.Fπ
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we are the best among the rest*
I DEDICATE THIS PAGE TO YOU SIS NAFFY RISKUYA GASKIYA INA ALFAHARI DAKE OVER SIS ALLAH YABAR ZUMUNCI INAJIN DADIN NICE COMMENT DINKI KEEP IT UP β€
_π‘AL'AMIN DAGASH FANS GROUP_ π‘
Ina matukar alfahari da comment dinku gaskiya sosai da sosai
Comment harda read more π€much love to your love and care
π *AL'AMIN DAGASH*
*PAGE* 8β£
Megari yace muna sauraronki malama maryam
Anty taciga ba da basu labarinta
Maryam dai tayi shiru tana sauraren uwarta
Anty tacigaba kamar haka
Nataso cikin soyayya da kauna acikin yan'uwana ammafa Wanda muke uwa daya
Ina da shekara goma akayi auren yayuna mata saboda saida suka ka gama karamar secondary school wato junior secondary school kenan na nan kauyen nasu na gwaza
Bada son ran abban mu sukayi ba Dan yanuna yafison suyi aure amma inna ta roki alfarmar ya asu sudanyi wannan karatun Dan Allah
Yace duk abinda yafaru ta kuka da kanta
Tace ta amince haka kuwa sukayi karatunsu sugama
Suka samu mazajensu kuwa duk acikin garin meduguri ba ma a kauyen ba
Wannan Abu ya bata ran kishiyoyin innan mu dansu yaransu kaf a kauyen gwaza suke aurensu basu samu shiga cikin garin meduguri aureba
Saigashi tashi daya halima zata aurar da yara har biyu a cikin meduguri
Anyi biki an watse ankai amare gidansu lafiya
Yazama saura ni da yayuna maza dama shi abban mu ba karfine dashi Dan haka idan kunva yaran gidan mu a makarantar boko to kowa iyayen mu matane kesamu
Yaya usman da yaya abdul sukayi shawarar suringa zuwa cikin meduguri aiki zaifi zaman banzan dasuke yi a matsayinsu na 'ya'ya maza ba mataba
Innan mu tamusu adduar samun nasara a rayuwa
Dama shibaba bamai matsawa wa 'ya'ya mazabane
Haka sukayi sallama da mu suka kama hanyar meduguri Neman kudi
Yazama saura nikadai a gaban innanta tadauki duk wani kulawa tabani
Bata barni nayi tallan komaiba saboda tsoron datake yi akaina
Dakanta take Neman kudinta da tabiya min bukatuna nagida Dana makaranta tunkafin nakai shekara goma akafa zuwa kamun kafa gurin abban mu
Abin dai har yafara wuce tunin Abba
Haryafara tunanin inagama primary zai aurar dani
Sai dai lokacin da nagama primary din Abba yayi niyar aurar dani innan mu tace Allah yakasheta batasan zancenba
Fada sosai sukayi har mutan gidan namusu dariya sunji dadin abinda yafaru kenan
Abban mu yace shikenan tunda tace yarta bazatayi aure yanzu ba amma tansani komai yabiyo baya baruwanshi
Innan mu tace ta amince ai haka yafada akan yayunta kuma Allah yatsare su to wannan ma Allah ne zai tsare mata ita
Yanzu yana bata hakuri tabarni yamin aure
Idan kuma taki karzo tana bashi hakuri idan akasamu akasin hakan bazaiji hakurinta ba
Tace ta amince shikenan tundaga ranar Abba yasa ido akan maryam na shi ido kawai baya magana
Ni maryam nataso cikin nutsuwa na hangen nesa
Daga makarantar boko saina islamiyya daga nan bata zuwa ko ina sai zaman dakin innan ta
.tana da kawa guda daya deeja
Hankalinsu yazo daya kullum deeja tana gidan mu muna karatun alkur'ani kokuma muyi bitar na boko
Ina da shekara shatakwas na gama secondary school nida kawata deeja
Deeja muna gamawa anasa ranar aurenta sati uku masu zuwa
Nikuma ansamu matsala sosai saboda samarin da suka kawo kayan baikonsu sunfi goma anrasa ya za adasu ma kuma nibanason ko mutum daya acikin su sai mutum daya kuma shi ba kayan baikonsa a gidanmu saboda bashida kudi
Talaka ne gaba dabaya bashida komai shiyasa ma baisamu daman kawo baikonsaba
Aliyu gadanga shine mutumin danakeso shiya kwanta min arai kuma Inna ta matasani kuma tana bani goyon baya akan hakan
Dan ita abinduniya baidameta kwanciyar hankali kawai take bukakata
Abbana yakirani da daddare naje hardakinsa nasameshi yace yar albarka nace na am Abba
Yace yanzu yar albarka haka zaki yitazama ba zakiyi aureba bayan ba masoyan kika rasaba
Kintsaya jiran wani shashan yaro dabashida sana'ar yi
Nace Abba Dan Allah kayi hakuri karka rabani da aliyu wallahi Abba shine nakeso
Abba ya fusata yace ke maryam dagake har uwarki Baku isaba wallahi
Bazaku maidani karamin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 18